Halacci
Halacci
jikina wanda hakan bakon abune agareni musamman akan mace wanda ada
kamar bera da mage nake kasancewa tsakanina da mace ,na tsammaci zata
fuskanci halin da na shiga a wannan lokaci har naji raina ya baci nayi tsaki wa
kaina kana na girgiza kaina domin in samu In fita daga wannan tunani dana ke,
amma amamakina sai naga ita ko ajikinta hakan yasa na dan ji salama domin na
tabbata bata tsinkayeni ina kallonta ba ballantana har tayi min wata fassarar.
Bayan ta sami wuri ta zauna ni kuma na kuma maida hankalina ga lecturer dake
take saidai aduk lokacin da hakan ta faru nakan yi saurin kauda kaina
alokacinda na farga.
A haka dai har muka gama lecture lecturer ya fit anima na mike na sake
yi mata kallon karshe cikin tsoro tsoro na fice daga hall din . A ranar dai bansan
ya suka kare ba ni dai lokaci azan iya zama awurin da take b a saboda nasan
har Allah ya kaimu dare nayi barci sai na tashi da safe na manta da abinda ya
faru jiya na kuma shiryawa na fita lecture, kasancewa ta bako yasa na fita da
kusan duk abinda ake koya mana na sanshi a baya ina gaba gaba wajen ansa
tambaya, kwatsam sai gata tashigo ajin ta wulka ta gaba na wuce ta zauna sai
kuwanaji kaina ya sara min adai dai lokacin da take wucewa , na dauki kusan
minti biyar ban koma cikin hayyacinaba abin kuma da yake kara ban mamaki
kuma shine akaramin tunani na na kasa fahimtar dalilin da yasa nake shiga
bayansa ba tare da na tsayaba kamar yadda sauran dalibai yan uwana suke yi,.
In takaita muku zance dai haka na kasance cikin gujewa duk wani abu da
zai hada ni da ita saboda in tseratar da tunanina saboda ni har cikin raina bansan
menene dalilin hakan ba kasancewar ban taba tsintar kaina acikin irin wnnan
Har na fara rashin lafiya wacce nake kyautata zaton cewa tunanin yarinyar nan
yana da kaso mai tsoka acikin dalilin rashin lafiayar da nake yi, domin kuwa
tunaninta kan sanyani mantawa da halinda nake ciki na daga yunwa ko koshi
har takaiga nakan kai qarfe biyar na yamma ba tare da na karya kumallo ba
sakamakon na fita da safe bann ci abinciba lecture kuma ta riqeni har karfe uku
na yamma , to idan naje daki amaimakon in nemi abinci sai kawai inji ta fado
min arai daganan kuma bani sake sanin wa yake kusa dani har sai na kusa karfe
acikin jiki na …
daga jarabawar mu ta qarshen wannan rabin shekarar nayi mata kallon karshe
wanda alokaci n tayi matuqar kidimar dani har na kasa yi mata Magana don
kuwa wani bakin tabarau tasan ya wanda da ka ganta kasan ba raini , hakan yasa
ko sallama ban iya yi mata ba , haka na dauki hanyar kano domin kuwa bazai
yiwu in tafi gida kai tsaye ba saboda yamma ta riga tayi sosai dole sai na kwana
Zuwa na gida sai yakasance kamar taki aka zubawa rashin lafiyata don
kuwa said a takaini ga ajiye ajumi gaba daya saboda gazawa, ahaka n a kasance
har aka qare hutu makaranta ta dawo aiki amma ina gida ina famar jinya har
said a na qara almost 40 days ahead sannan na koma makaranta kamar HIV
nan sai dai kallo daga nesa ko kuma kiran tsoro ta waya. Dan zaman da mukayi
agida ne har na fara iya jure yin Magana da ita ta waya jifa jifa har dai muka
dawo makaranta, wani abu da yayi matukar dauremin kai shine na rigata
dawowa wanda hakan yasa aranar na kirata da dare n ake tambayarta ra nda
zata dawo sai take cemin sai wani lokaci , kawai sai naji labarin ta shigo
wanshekare.
A wannan karon kuma sai abin yayi worse don kuwa na fara kasa iya
boye damuwata har takai ga mutane sun fara fuskantar akwai abin da ke
rubuta text awayana na tura mata misalign karfe uku na rana bayan na gama
lecture na ranar na tafi hostel… txts din ya kunshi sako ne kamar na neman
shawara akan naga wata inaso amma na rasa yadda zanyi sai nake so ta bani
shawara , hakan nayi ne don inji irin ra’ayinta shin zata bani kwarin guiwa ko
kuwa za ta sarar dani. Abu n mamaki kafin karfe hudu sai naji kiranta awaya
ganin haka yasa na yanke naje na recharge din layi na sannan na kirata , bayan
mun gaisa sai take cewa dani “naga text “ sai na amasa mata da cewa “eh to
yanzu mecece shawaraeki akai” ta danyi shiru da farko wanda hakan yasa na
dan razana kadan kafin daga baya tace “ina ganin…. Kawai ….. kawai ka
sameta ka fada mata” alokacin sai naji kaina yayi min nauyi na nemi in kasa
kara furta wani abu sai dai daga baya nace “haka kike gani?” “Eh mana hakan
zaifi” “idan zan iya kenan?” yar dariya tayi kadan kana tace “eh idan zaka iya
ka sameta ka fadi mata in kuma baza ka iya ba sai ka sami number wayarta ka
kira ta ka sanar da ita” nan ma shiru na sakeyi don kuwa kaina ya daure na rasa
me zan fadi sai daga baya nace “Shikenan nag ode zan gwada in gani duk abin
day a wakana zan baki labari” muka yi sallama na kasha wayata , daga nan na
shiga zullumin wace hanya zan bi in iya fadi mata qudurina ban Ankara ba sai
dai naji an a kiran sallar magrib don hankalina ya bar jikina kwata-kwata har na
Bayan anyi sallar Isha’I kuwa nayi niyyar in kira ta awaya in sanar daita
amma sai taraddadi ya hanani don kuwa na kasa natsuwa da zuciyata sai kusan
karfe tara na dare Na fita don wai in sami wuri kebantacce wanda zan zauna in
kirata amma sai nayi ta yawo cikin makarantar ko ina naje sai inji kamar akwai
wanda zai interrupting dina ahaka har saida na kai Lecture theatre na
makarantar na zauna kan daya daga cikin kujerun dake wajen LT din sannan na
kirata tana fara ringing gabana ya fara fadi kamar sojoji sun kewaye ni da
amma ni sai na kasa amsawa akaron farko saida ta sakeyin sallama sannan na
amsa da “wa’alaikumussalam” bayan mun gaisa sai nace “dama akan maganar
da mukayi dake dazune …” sai na tsaya anan ban iya sake fadin wani abu ba
saida taji shirun yayi yawane sannan tace “hello!” na amsa “hello” nima sai tace
“inajinka” na sake dagewa don inyi Magana amma sai na gagara saida ta sake
yin Magana sannan nace “amm…. Agaskiya wannan yarinyar da na baki labari
ba wata bace face ..ke” na fadi hakan cikin karfin hali don alokacin na tabbata
har muryata rawa take, wani babban abinda ya sake karya min wuya shine da
tace min bataji a binda na fadi ba don ji nayi dama ban fara maganar ba da sai in
hakura kawai in bar abin azuciyata don na riga nagama bawa zuciyata tabbacin
bazata karbeni ba. Na sakeyin karfin hali nace “abinda nake nufi shine :kece
wannan yarinyar” still sai naji tayi shiru nayi zaton ko ta gane manufata ne
amma da nace “kin fahimceni ?” sai tace “Gaskiya ban gane ba” hakan da ta
fadi ya matuqar qonamin rai kawai sai nace “ok kiyi hakuri wani lokaci na gaya
miki..” sai tace “to shikenan” mukayi sallama na kashe wayata na kwanta cikin
kujerar duk da kasancewarta simintine amma sam ban kawo hakaa araina ba
haka na cigaba da zama awuri nnan sauro na cizona amma sam bana ji har saida
na tsinkayi kaina cikin wani duhu wanda ya dan fadar min da gaba sannan ne na
Ankara cewa 11:00pm tayi har an kashe Gen. din makaranta, haka na tashi na
nufi daki kamar wanda babu laka ajikinsa alokacin na ji cikina yana min zafi
nan na tabbatar ban ci abinciba adaren ,alokacin na dora tukunya don sama wa
kaina masalaha. Ranar haka na kwana cikin zulumi don na dauki tsawon lokaci
ban yi barci ba
Dagari yawaye na fita lecture haka nayi ta boye boye don kar mu hadu da
ita har muka tashi , da dare yayi misalign karfe goma da rabi na dare na kirata
kuma amma alokacin sai na sami kwarin guiwa nace da ita “na kirata amma na
kasa fada mata kudirina” sai tace “yanxu ya kenan zakayi” ni kuma sai nace
“so nake yanzu zan tura miki sunanta a text da department din da take in Allah
yasa kin gane ta sai ki isar minda sakona gareta” shiru tayi da farko kana tace
“to shikenan Allah yasa na santa” nace “amen”daga nan sai na rubuta sako
kamar haka.
Department:Maths/Chemistry
(school of science)
Na tura mata na kashe wayata na kwanta barci amma sai barcin yaki zuwa har
buya don kar mu hadu amma sai ya kasance dole sai mun hadu domin tun
sunan na buya ina jira karfe takwas tayi mushiga Practical chemistry na dauki
Chemistry lab din kawai sai naci karo da ita zata wuce, kamar atsorace ta
gaisheni na amsa nima atsorace saidai kawai dakewa da nayi ahaka dai muka
kasance ranar sai dai satar kallo muke wa junan mu har aka tashi na koma
hostel cike da zulumi, ina jirace da dare domin in kirata in tambayeta labarin
kasuwa.
Hmm Allah dai shikyauta aikin sabon shiga, tun da na dawo hostel
akwance nake har aka kira sallar magrib sannan na tashi jikina ba kwari na nufi
masallaci don inyi alwala inbi jam’in salla, bayan an idar da salla kuwa sai na
dawo na zauna kan wata waiters seat dake tushen bishiyar bedi (darbejiya)
wacce ke gaban block C na shiga saqe saqen abin da ban ma san taya na faraba.
Ahaka har lokacin sallar isha’I yayi na tashi na koma masallaci don gabatar da
salla, na dade ina addu’o’I don neman yardarm allah da kuma neman zabin sa
akan abinda yafi alkairi gareni bayan dan lokaci kuma na tashi na koma daki na
kwanta sam na manta da cewa rabon cikina da ansar wani abu tun safiya, nan
fan a fara jin ca nji a jikina amma sam tunanina bai kawomin dalilin fuska ntar
wannan chanjin ba ,har wajen qarfe goma sannan na dawo hayyacina bayaga
cewa ba barci nayi ba duk tsawon lokacin da na dauka akwance, hakan kuwa ya
zauna nayi kokarin mikewa amma sai naji idona yanayi min gizo nan take na
fuskan ci cewa lallai yunwace ke rarakata, alokacin sai na fara tunanin mafita
agareni ,dakyar na sauka daga kan gadon na fara kici-kicin dafa koda rowan
zafine In durawa cikina amma sai na nemi abin kunna wuta na rasa alokacin
kuwa babu kowa adakin duk sun fita zuwa wasu harkonkin nasu ni guma
saboda ganda tare da taimakon yanayin da nake ciki na rashin jin dadin jikina
yasa na koma na zauna said a naga dare ya fara nisa tukunna sannan na yakice
na fita zuwa wani canteen cikin super market din makarantar wato shagon dan
Zaune nake ina gyangyadi har saida na tsinkayi duhu cikin dakin sannan
na tabbatar da cewa qarfe sha daya tayi don haka na zari wayata na fita na dauki
lokaci kafin inkirata hakanan dana kira tana shiga gabana yafara faduwa don
fargaba bugun zuciyata ya qaru don har rintsa ido nakeyi don dai kawai inji ko
zai sassauta, tana amsawa ta fara gaisheni na amsa mata cikin dari-dari kana
daga baya nayi shiru, itama haka shirun tayi sai bayan kusan 30 seconds sannan
nace
Ni: …am .. dama akan maganarmu ta jiya na kira domin inji yadda kuka
kare da ita…. (na qarasa maganar aciki tare da rakon wasu kalamai
Ita : (tayi shiru na tsawon lokaci har hakan yasa na sake fadin)
Ni:… kinyi shiru bakice komaiba, kin sameta? Ya kukayi da ita? (duk
Ni: kamar tsawon wane lokaci? Awa daya? Sati daya? Ko wata daya?
Ita (a ciki-ciki) sati daya
Ita: eh!
Ni: ok shikenan na gode zan cigaba da jira har lokaci n da zaki waiwayeni
Haka muka cigaba da yiwa juna kallon tsoro har kusan kwana shida babu
abinda yake hadani da ita sai ko gaisuwa in Allah ya qaddari haduwarmu don
haduwarma sai dai in kirata qaddarar ubangiji don kuwa bana son duk wani abu
da zaisa mu hadu na fison in ganta awani wurin yayinda ita bata ganina . Iya
tsawon wannan lokacin ban kirata ko sau daya bah aka nan itama garama ni
Ana gobe sati zai cika na tura mata text don tunatarwa da ranar tayi kuwa har
qaguwa nayi dare yayi don inkira inji ansa amma da daren yayi sai kuma na
kasa kira sai juya wayar nake ahannuna sai na dauka kamar zan kira amma sai
inji tsoro in fasa dakyar dai misalin sha daya da mintuna na daure na kira, tana
dauka kuwa ta fara gaisheni bayan mun gaisa na gaya mata ga abinda yasa na
kira , abin mamaki sai ta nuna kamar bata san maganar ba said a taji nadage
sannan sai ta fara yi min wasu tambayoyi wanda acikinsu daya kawai na rike
don ji nayi kamar a mafarki wait a tambayeni “KAI WANE YARE NE?” . Mun
dauki kusan minti ashirin da biyar amma bata sanar min hkuncin da ta yankeba ,
sai ma daga baya tace min tana bukatar Karin lokaci ni kuma sai na maida mata
da martini “in dai likacine na baki daga zuwa koma yaushene zan jiraki, amma
kawai kibi ra’ayin zuciyarki don kuwa zuciya keda dammar yanke hukunci akan
abinda takeso ko abinda bata so” daga nan mukayi sallama na tafi na kwanta
amma azuciyata na riga na sadaqar cewa kawai nauyina takeji shiyasa bazata
iya gayamin cewa bata sonaba don haka na fara bawa zuciyata hakurinda sam
Lokaci lokaci nakan kirata mugaisa amma maganar wani campaign duk
na aje gefe don nasan ajin yafi karfina . Awannan tsakanin haka mukayita
artabu da abokaina kan su yarda cewa ba Aisha bace ta sace zuciyata amma sun
doge don sun fuskanci abubuwa awurina da dama amma sai na nuna musu cewa
ita Aisharce kadai tasan yarinyar shiyasa kusancinmu da ita yakaru, don
acikinsu ma akwai wadanda suka ringa fadimin Magana afakaice don dai inji
haushi wasu kuma har kiranta sukayi a waya don su tambayeta amma sai Allah
yasa bata biye ta harkarsu sai ta nuna musu bata san zancenba , ahaka har lokaci
yayi nisa.
Kwatsam sai wani abu mai matuqar firgitarwa ya sameni duk da cewa
nasan Aisha tafi qarfina amma saida naji mugun kishi ya motsa akanta wannan
abin kuwa shine ganin wasu messages da nayi cikin wayar wani course mate
dina mai suna Abdulkadir wadanda ya turawa ita Aishar yana neman soyayyarta
amma kuma bai taba gayamin ba koda dai cewa shima baisan tsakanina da itaba
, yadai san kawai combination daya muke da ita, adaidai lokacin na tuna da
sa’adda yace in bashi numberta amma na ki harsai day a takura sannan na tura
masa, banyi masa Magana ba ganin wadannan messages din sai dai kawai da
nashi na fita barshi da sunan zanje indawo dawowar da banyi ba kenan aranar,
bayan yan kwanaki kuma an bamu wani Assignment based on combinations sai
ita Aishar ta nemi mu tafi library don mu duba answer tare na kuma yarda muka
Bayan mun fito na dan taka mata kadan zuwa kusa da AUDITORIUM
BLOCK wato AU sai nayi m ata said a safe na nufi hostel dinmu, ina gab da
shiga sai naji kira a waya nayi mamaki da naga itace ke kira don ganin yanzu
muka rabu amma kuma saigashi ta kirani, alokacin babu cikakken kudin da zan
kirata ta wayata hakan yasa na cire kunya na daga wayar nayi allama, tun kafin
ta amsa na tambayeta “ya akayi?” na tambayeta kamar a uzurce sai tace “kasan
meh?” “a a sai kin fadi” cikin yar dariya take cewa “nifa na dauka cewa
assignment din special target zamuyi” ni kuwa sai na amsa mata da “hmm, ai ni
kuma tsammanina na mama kike batu akai” sai ta sakeyin dariya kana tace “ai
na fadi hakan cike da mamaki daga nan mukayi sallama nace saida safe. Har
recharging dana kirata bayan ta daga wayar sai na tambayi ya akayi sai tace min
cewa “dama akan maganar ………” bata karasa ba sai tayi shiru tace “kaih..
kawai ka barshi ba saina fadaba” take sai naji gabana ya fadi cikin rashin
fahimtar me take nufi nace “ban ganeba meyasa bazaki fadi ba?” “kawai ka
barshi bazan iya fadi ba” haka ta mayarmin wanda ni kuma alokacin raina yai
matukar baci amma kawai sai na dake nace “ok shikenan tunda bakison nayi
barci sai da safe” da kawowata nan sai na yanke wayar, ko cikakken minti day
aba ayiba sai ta sake kirana, dagawa kawai nayi ba tare da nace komai ba sai da
tace “naji ka kashe” “eh mana in ban kashe ba ya zanyi tunda kince bazaki
fadimin ba?” shiru tayi na dan lokaci wanda har hakan yasa nace “kinyi shiru
me yafaru?” “naji kace bazakai barci bane shine nakeson nace kar ka dami
kanka kayi barcinka ba bu komai” haka ta fadi kamar irin ta damu dani dinnan
ni kuwa sai nace “wannan kuma bai kamata ya dameki ba tunda bazaki gaya
min ba kawai abar maganar anan” jin alamun na damu da gaske yasa ta sake
bani hakuri ni kuma na nuna ban sanshiba, daga karshe ma kawai kasha wayar
nayi na zuba tagumi kamar wanda aka aikawa da sakon mutuwa, ban ankaraba
sai naji karar shigar message awayata , dubawa ta kuwa sai naga “dama akan
maganar Rabi’u musa ne da kuma wannan da yace kabashi number nan a group
dinmu na research” take sai naji cikina yayi wani kara don jin abinda ban taba
tsammaniba, saboda shi wanda take Magana akai din abokina ne don dama
shine na taba gaya muku cewa naga messages a wayarsa wanda keda alak a da
hakan
bayan ta daga sai na farad a cewa “naga text din da k ika tura m in yanxu”
Sai tad an yi shiru na lokaci kafin daga baya tace “eh dama shine abinda yake
damuna” ni kuwa cikin karfin hali sai nace “toh ai wannan mai saukine tunda
abu ne da yashafi zuciyarki don haka kawai tunani zakiyi ki kuma yi shawar da
zuciyarki akan wanda yafi dacewa da ita hakanan kuma duk sa adda kika yanke
hukunci ki sanar da su duka cewa wani ya riga wani daga cikinsu hakanan
wanda kika zaba din kuma sai kisanar masa domi n dukkansu su sami
kwanciyar hankali” tunda na fara Magana shiru tayi batace komai ba har sai da
na rufe baki sannan tace “toh shikenan na gode mukayi sallama na sake zuba
tagumi awurin batare da na tashi ba bare in kwanta na jima ahaka kafin daga
baya na dauki wayata na tura mata text mai dauke da “Ina mai kara jadda da
miki cewa don Allah duk wanda yayi nasarar samun zuciyarki to ki sanar masa
ki kuma sanar da wadanda suaka rasaki don su san a wane hali suke ciki, kada
kuma kiyi la’akari da yadda kuke da mutum komai kusanci don wannan abune
day a shafi zuciya ba gangar jiki zalla ba.” Na tura mata sannan na tashi na tafi
Karfe shida saura yan mintuna na safe sai naji wayata tayi qara ina
dubawa sai naga itace ta turo abinda aka rubuta a text din kuwa shine “ akwai
wani abu da nake son sanar dakai wanda baka sani ba, na taba yin aure kuma
ina da da shin zaka iya tarayya da matar aure? Bazan cuceka ba” iyakacin
abinda message din ya kunsa kenan. Hmm babbar Magana nayi matukar girgiza
da ganin wannan sako don na tabbata da atsaye nake sai na sami abin jingina
don akwai yiwuwar in fadi ban sani ba, akwance nake am ma sai da n a rintse
idona na tsawon lokaci kafin daga baya na dawo cikin hayyacina na sake
karanta meassage din sannan na nayi reply kamar haka “toh nana Aisha kinyi
Magana daya mai ma’ana biyu wanda na kasa fahimta da farko kince kintaba
yin aure , daga baya kuma kina tambayata ko za iya tarayya da matar aure, shin
har yan zu kina da aurenne ko kuwa ada kike da auren yanzu baki dashi?” ina
kawowa nan na tura mata na cigab a da kwanciya ina jiran amsa , cikin ikon
Alllah kafin minti biyu sai ta yi reply da “ina nufin zaka iya tarayya da wacce ta
taba yin aure?” hmm abu kamar almara sai naji lokaci daya hankalina ya fara
kwanciya naja doguwar ajiyar zuciya sannan na mayar mata da reply cewa
gaskiya da tayi don kuwa hakan kara miki matsayi yayi azuciyata haka kuma a
iya sanina addini bai haramta mana auren macen da ta taba yin aureba matukar
50% Na quality da suka dace ko wace mace ta mallaka sai gashi ke kin mallaki
90% Na wadannan qualities din don haka haryanzu ina kan bakana in har
zuciyarki ta aminta dani ki sanarmin don in sami natsuwa araina" ina kawowa
nan na tura mata na sake kwanciya na tsunduma cikin tunani, sai can bayan
wani lokaci misalin karfe bakwai da rabi sai naji kira ina bi sai ta fara dariya
cike da mamaki sai na tambayi dalilin dariyar sai tace "da wasa nake" cikin
rshin fahinta nace "me kike nufi" sai tace"abinda na gaya maka da wasa nakeyi"
hmm lokaci daya na dauke wuta har saida na rufe ido sannan naja doguwar
ajiyar zuciya sannan na bude ido nace"alhamdulillah amma fa wallahi kin firgita
bazata buga ba , shiru nayi na dan lokaci sannan nace "to shikenan Allah ya
Karfe shabiyu muka hadu awurin lecture na Gse 122 sai na hadu da Abdulkadir
sai yake ban labari cewa wai Aisha bazawarace sai naji abin ya bani dariya na
sake tanbayarsa wa yagaya masa sai yace wai ita ta gaya masa ni kuwa don
bugun ciki sai nace sai na tambayeta a tsorace ya ce don Allah jar and inje na
ce sai naje na kama hanya na tafi inda take na zauna kusa da ita muka fara hira
amma har aka gama lecture ban gaya mata ba don dama tsokanarsa nake.
ranta game daniba, ita bata fito fili ta gaya min cewa bata sona inyi hakuri ba
haka nan bata kuma amsa tana sona ba, kawai dai abinda nasani shine sakin
Bazan manta wata laraba ba bayan mun gama lecture ta mat 212 wato problem
solving in mathematics muna zaune cikin aji da ita da wasu daga cikin yan ajin
namu ita tana kwafar rubutu daga wani text book zuwa littafinta wanda
yakasance assignment ne da aka bamu a chemistry department, alokacin tsaye
nake jikin bango daga gaban kujerar datake zaune, sai ga wani abokina yashigo
wand azan iya cewa shine aboki mafi kusanci da nake dashi aduk fadin
makarantar yana kuma daya daga cikin masu zargin akwai wani abu tsakanina
da ita Aishar, da shigowarsa ya fara min ba’a ni kuma sai na basar dashi don
kuwa banason ake tashin maganar saboda raina yana baci adalilin haka
kasantuwar nakan tuna da cewa na nemi soyayyarta amma ban sami karbuwa ba
har wannan lokacin kuma bana sa rai cewa zan sami karbuwar, ganin na basar
dashi yasa bai sake ba sai kawai da yaje gurin ita Aishar suka gaisa yake
tambayarta abinda take, ai kuwa kamar dama ajirace take sai tace “daman na
gaji amshi ka taya ni” shikuwa sai yace “a’a ga wanda zai tayaki nan a tsaye
baki bashi ba sai ni?” .. hmm abinda yaso bani mamaki shine sai ta kale ni
sannan tace “nmh ni in bazaka tayani ba bani” tafadi hakan tare da kai hannu
don ta karba, shima sai ya kalleni kamar masu hadin baki sannan yace “a a
barshi to zanyi ko layi ukku nayi miki ai na tayaki” ya fadi hakan tare da karbar
biron hannunta ya fara. Ni kuwa ina tsaye agefe ina dan murmushin dole don
kuwa zuciyata ni kadai nasan abinda takeji, bai dade yanayi ba sai yace “nagaji
gaskiya kai anshi kayi mata ai dama kai yakamata kayi bani ba” ya fadi haka
tare da miko min ita kuwa sai ta bishi da kallo yayinda na karba sai ta kalleni
muka hada ido sai ta yi kasa da idonta, nikuma kawai saina fara rubutu tana
dandali
Ina rubutu ina satar kallonta ayayinda ita ko aka bata kawoni ayadda na
fuskanta, ahaka har computer students suka shigo zasuyi lecture a wurin muka
fita muka basu wuri yayinda muka shiga ajin da yake opposite to wanda muka
fita muka zauna seat daya da ita ina rubutu tana wasa da wayarta yayinda wayar
yayanta(wanta) wato bishir ke rike hannunta, ina cikin rubtu ban Ankara ba sai
naji tace “kaga hoton baba” saurin waigawa nayi don inga me take nunamin sai
kuwa na tsinkayi mutum zaune cikin mota cikin shiga ta mutunci tare da
mai kamala duba da yanayin suturar dake jikinsa. Murmushi nayi kawai wanda
ya kasance iyakarsa kan fuskata don atake gaba nay a fadi don hakan ma wata
alamace dake nuna cewa Aisha ba class dita bace sai nace “na gani hoton yayi
kyau” kawai na cigaba da rubutu na yayi n da rabin hankalina baya jikina har na
tsaya ban ma saniba sai naji muryarta tace “ka gaji kaima?” dan guntun tsaki na
saki na cigaba tareda cewa “a a wani abu kawai na tuna , a haka dai har lokacin
lecture mu yayi na wani course one of the two elective courses we offered in
n ake offering din Gaseous state ita kuma take offering din nuclear chemistry
Allah dai ya kyauta aikin qaddara bayan mun tashi daga lecture muma
mun tafi hostel can misalign karfe biyar na yamma sai na kirata bayan mun dan
gaisa sai na ke tambayarta ya take sai tace min bata lafiya tana fama da ciwon
ciki, hankalina yayi matuqar tashi jin cewa bata da lafiya har ma na rasa me zan
ce da ita bayan istirja’I da nayi sai kace wanda ya fadawa wata masifa kana na
bita da sannu ta amsa yawwa “yaya jikin naki yanzu” ta amsamin cewa “da
sauki” “to Allah ya baki lafiya ya kuma kiyaye gaba” mukayi sallama take sai
na tashi na bazama yawo don kuwa jinayi zaman hostel din ya gundureni kawai
saboda jin cewa bata da lafiya ina tafiya ina saqar zuci wanda azuwa yanzu ban
iya tuna ina da ina naje alokain da na fita yawon nan nasandai na fita agalawa
zuwa gidansu Kailani bayan na fita na shiga wurin Adam shi kuma alokacin
daya dameni da ba’a saina tashi na fice na kama hanyar komawa makaramta
wanda ina kan hanya aka kira sallar magrib dpn haka sai na zarce masallaci
Bayan na tashi daga shago wanda n a saba zama lokaci lokaci bayan
sallar isha’I zuwa abin day a sauwaka sai na kuma kiranta don in tambayeta
yanayin jikin sai take cewa dani “hmm jiki Alhamdulillahi na warke” ni kuwa
sai nace Alhamdulillah naji dadi sosai Allah ya kara lafiya ta amsa amin kafin in
kaiga yin Magana sai ta fara bani labarin abinda ya haddasa mata ciwon cikin,
abin kamar wasan kwaikwayo tana fadi tana dariya yayinda tace “kasan me?
Dazu da rana bayan kun shiga lecture ni kuma na kama hanya zantafi hostel
kawai sai naji ina sha’awar garri harda zan wuce ta wurin masu saida gyada
nake cewa da ban cinye gyadata da na siya dazuba da nasa aciki , ahaka na
qarasa ina zuwa kuwa na jika na sa sugar da madara na sha nagama kenan
cikina ya fara ciwo saboda dama ban yi breakfast ban a fita….” Haka ta cigaba
da labarta min abinda ya faru tanayi tana dariya ni kuwa tsitttt nayi tausayinta
ya kamani har saida taji shirun yayi yawa sai tace “hello” na amsa da “hello
inajin ki” “naji kayi shiru.” “hmm kawai tausayi kika bani, amma meyasa ma
kika fita baki yin break fast ba ? dama ancemin baki cin abinci sosai gashi kuma
kika cusawa cikinki abinda be saba dashi ba.” Duk abinda na fadi shiru tayi tana
jina wanda har dariyar da take dan yi shiru tayi ta dena ban kuma san daliliba
wanda hakan yasa na tsargu nace “kinyi shiru bakice komai ba dagaskene kenan
baki ci n abinci sosai” sai ta amsa da “Nhm ai ba koda yaushe bane kuma ni
bawai cine banayi ba kawai irin ikina kenan bana cin abinci da yawa”…..
Kar dai in cikaku da surutan iska, abu kamar wasa ciwon ciki yaki ci yaki
cinyewa har takaiga an samata drip dag a karshema har saida ta koma gida,
domin bata gaya min zata tafi ba saida ta tafi tukunnan na tambayi kawarta
Raihana take gayamin ai ta tafi. Sai daga baya na kirata nake mata ya jiki
sannan naked an tambayarta ya akayi ta tafi bata sanar dani ba take cemin wai
tayi la akari da cewa Raihana ta gaya min, shiru kawai don kar inja abin da
tsawo har akaiga ta fadi wani abinda zai iya sawa inji ba dadi nabi ra’ayinta
nayi mata allah ya sauwake mukayi sallama satinta guda cif agida ta dawo
school wanda wannan sati dayan da tayi babu wanda bai shaida hakan ba
sakamakon canji da bayyan atare dani ana gobe za afara azumi ta shigo
makaranta, aranar ji nayi kamar anyi min wani albishir duk da dai ban sami
ganinta aranar ba domin ko aranar da zata dawo saida nace in ta shigo ta gaya
min amma sam bata juyo ta kaina ba sai misali n karfe tara na dare sannan ta
kira tana tambayata wai me yayi zafi ta dawo ban yi mata sannu da zuwa ba, ni
kuwa sai na kafa hujja da cewa ai ban san ta dawo ba saboda nace in ta shigo ta
sanar dani kuma bata gaya min ba don haka nake tsammanin ko bata dawo ba
ne nan dai muka dan zanta mukayi sallama abayan na tambayeta ya nayin jikin
nata.
Rana daya takk wacce na tabbatar bazan taba mantawa da ita arayiwata
ba itace ranar 15-05-2019 wannan rana kuwa itace ranar da ko a mafarki ban
taba tsammani zata zo min ba, kar dai in cika ku da surutu ainihin abin daya
faru shine ranar da muka dauki azumi na goma misalign kkarfe shida na safe ina
kwance kawai sai na ji karar shigar saqo a cikin wayata da sauri kuwa na duba
sai na tsinkayi sako daga wata number da sanyawa suna Nana Ayeesha, cikin
sauri na bude ina tsammanin zanga rubutu cikin screen sai nag a wani dan
kankanen rubutu wanda ko layi daya bai cika ba amma tasirinsa yafi karfin
I Luv you
Iyakacin abin da sakon yake nunawa kenan, na sake dubawa da kyau har saida
na tashi na zauna na share idona sannan na sake dubawa amma dai banga canji
ba abinda na gani da farko shi nasake gani cik, zuciyata ta tsaya tunaniya ya
tsaya na koma kamar itace saida na kwashi kusan minti goma ahaka sannan na
farfado nasake duban rubutun naga bai canja ba sai na fara tunanin “wai anya
ma tasan wanda ta turawa kuwa?”, ban sami tabbacin cewa tasan da zuwan
sakonba said a nag anta da nikab aranar haka kuma duk in ta zo wucewa ta inda
nake ko waye awurin bata yarda ta waiga koda inda muke ballantana tayi mana
cewar an bashi auren wacce yakeso, zuwa dare kuma abinda ya faru na barwa
09032287375 don aranar kawai dai don ban ganin iyayena ne yasa bazance
sannan muka tafi gida kasantuwar an daga exam sai zuwa baya salla.
Bayan salla tazo ta wuce muka koma makaranta domin yin exam, Tunda muka
fara exam har muka gama bamuyi haduwar da ta kaiwa minti goma cikakkiya
ba karewa ma ranar da zamu bar school bayan mun fito daga exam hall saida na
jirata ta fito amma abin mamaki tana fitowa kawai saita wuce kamar bata
ganniba, abin yayi min ciwo amma tunda ni kesonta yasa na bi bayanta
alokacin kuwa suna tafe ne tare da wani course mate dinmu mai suna jibril
sulaiman said a naje gani gata amma sai ta sake nuna ko in kula akaina ta cigaba
labari kawai take bashi ba wata Magana bace mai muhimmanci daza ace wai ya
dauke hankalinta, saboda zuciyata alokacin babu 80% daga ciki yasa na cigaba
da binsu kamar wanda aka daurawa igiya har muka kai gate din super market
din school din sukayi sallama har na dan tsaya na tsammaci zata waiwayeni
amma sai naga kawai tasa kai tayi gaba kamar batasan ina wurin ba, hakanan
nima na wuce hostel da niyyar in karasa yan shirye shiryena in karawa motata
mai,
Bayaan na gama tattarayan tsummokina sai na fita neman ani gaye da aka turo
min kuind mota ta account dinsa tun kwana guda da ya wuce amma wai bai
basushiga ba Daga karshe ya gaya min cewa har ballance ya duba amma babu
alamar shigowarsu don haka nazo na saba tsohuwr jakata na kira ita Aishar a
waya na sanar mata cewa na fece, ina fita kuwa na biya ta gidan yayata wacce
nake kira da yaya Nafi, na nemi ta bani 500 naira na cemata cikon kudin mota
zanyi snnaan nasa kai na nufi kano. Nasauka kenan a yan kura sai naji wayata
tana kara cikin sauri na uba sai naga number Aisha sai na kyal ban dauka ba da
niyyar sai na sami wuri na tsaya kafin na kirata, na sawa mai napep hannu ya
tsaya nace ya karasa dani unity road dayake nan nake shiga motar Pambegua na
shiga kenan sai na sake ganin kira har sau ukku wanda hakan yasa na kirata tun
kafin nayi magana sai take tambayata "nace ba... ka tafi ne ?" na ansa mata da
cewa "eh na tafi ya akayi?" sai ji nayi tace "kaih gaskiya in bakai nisa ba ka
dawo saboda an fara issueing din Teaching practice foarm kuma sunce in
mutum ya dade bai ansa ba akwa fine due" sai nagaya mata cewa ai harna shiga
kano amma zan dawo kawai in karaba muka yi sallama sai nace da me napep
din ya tsaya in sauka na biyashi ya kara gaba, daga nan sai na sake shiga bus
don inje Gidan wani wan mamana da yake a daurawa wurin mahaifiyar
mamarmu wato kakata kenan don in karbo kudin udin motar komawa Bichi
saboda ko dama niyyata itace innashigo kano kawai zan shiga motar pambegua
in naga an kusa sai in kira a biyoni da kudin motar tasha amma tasowar wannan
maagana ta T.P yasa na canja don haka nayi amfani da naira darin da tarage a
fita kenan na shiga aka ce dani ta tafi gaisuwar mutuwa , duk nauyin bakina
haka na daure na labartawa aunty wato matar wan mamartawa duk halinda ake
ciki, sai dai kuskure daya da nayi shine da nace nazo wurin hajiyane in ansa
kudin motar komawa sai kuma gashi ba ta nan to inajin da wata kila bata
fahimceni bane sai ta masa min da to kawai, ni kuwa sai na kwashi jikna na
wuce dakin ita hajiyar na zauna, ban dade ba sai aka kawo min abinci naci sama
sama don kuwa na dai cine kawai amma ba dadin sa nak jiba kasantuwar
yanayina don kuwa aduk lokacinda aka ce yau akwai wani abu da na sanya
shiga daga cikin dakinta na kwanta kan yar doguwr seat dake ciki kafin yan
mintuna kuwa sai bari yya kwasheni, afirgice na tashi don jin wayata na kara
domin dama kiris nake jira ina dubawa sai naga number mamata na dauka tare
da yin sallama cikin muryar barci sai take cewa ya akayi ban tambayi aunty ba
ta bani kudin ? sai na mayar mata cewa kawai dai na gaya mata nazoo ne in
hajiya nanan in karbi kui awurinta sai aka ce dani bata on haka nace bari
injirata daga sai tace inje in karbi kudin wurin aunty, kafin ma in fita inje
dakinata ma sai gata tashigo dakin ta tamabayeni abin da zai isheni zuwa da
komowa nan na fadimata ta dauko ta bani na dauki hanya kafin in karasa school
din ita kuma Aisha ta tafi gida, haka nan na karasa na koma dakin da na zauna
saidai haka na tarardashi kamar anyi yaki aciki na dan tattara abinda zan iya
kuwa Arzikin bichi ya fara addabata wato sauro dolece tasa na tashi na fita ina
dan takawa don dai kawai kar in zauna saboda matukar zan zauna tofa sauro ya
ringa ragargazata kenan kamar Aminu ya sami sweet potato.... indai takaita
zancen haka nan na kwana cikin matuqar takura babu katifa sai katako hakanan
babu abin rufa bare matshin kai da gari ya waye na je na karbi form din na sake
Nayi kewar Aishatu ciin hutunnan duk da cewa muna waya da ita almost
every night a haka har hutun ya kare sakkamakon dama formally hutun sati biyu
ne kacal, hutun ya karene ana saura sati kamar hudu babbar salla don haka yasa
kai tsaye ita Aishar tace bazata koma ba sai bayan sallar ni kuwa jincewa an
fara karatu yasa na tattara na koma school ana saura sati biyu salla,haka nan
school din takasancemin very lonely boring and the rest of some unfavorability
a haka har sallla tazo ina school don A garin bichi nayi sallar idi kafin daga
baya na shiga kano nayi kwana uku sannan na sake dawowa school.
ranar litinin bamuyi wata kyakkyawa ganwa da itaa ba har kusan karfe sha daya
bayan mun fito daga micro teacjhing practicum sai na sameta zaune kan waiters
dake karkashin s.l.t kamar abin arziki sai na kaimata wani note nace ta kwafa
terms akace arubuto kuma ni a wayata babu dictionary sai nace tayi amfani da
dictionary na wayarta tayi nima zanje inyi nawa daganan in karasa assignment
na chemistry da aka bayar, hmm abin mamaki sai kawai ta basar dani, ga page
din danake mata bayani daban amma sai ta bude wani wanda nikaina atake ban
iya fadin meke ciki sai na duba sai take tambayata game dashi , abin ya bata
min rai amma sai na barshi amatsayin wasa na ske cewa “hnm-nmh waike da na
buda miki wurin da zaki kwafa kuma kin bude wani wuri” na fadi haka tare da
ansan littafin na sake bude mata wurin amma sai tace “eh naji ni nan nakeson
gani” alokacin sauri nake inj hostel in dauko foolscap don inyi assignment din
amma sai kuma ga abinda taje fadimin duk da haka sai nace “wai ke zaki kwafa
ko in wuce da abina?” hmm Allah day ya kyauta abin mamaki sai kawai ta ciro
paper daga littafin kailani ta miko min wai “gashi kayimin” babban abinda ya
bani haushi shine yadda kailani ya fashe da dariya yanayimin hannunka mai
sanda harda fadin “a lallai yarinya kin san solution , kai kuma ai sai ka karba
muje” abin ya ban haushi matuka amma sai na basar na nuna kamar ba komai
nace da kailani “rabuda ita dani take” na fadi hakan tare da mikewa tsaye nace
yaxo mutafi abu kamar wacce akayiwa allura kawai sai tayi zumbur ta mik tare
da daukar Jakarta ta ajemin littafin awurin kawai ta dauki hanya kamar ta bace
don ayanayin takunta na gani ga kuma fuskarta kamar zata sa kuka, alokacin sai
nayi dariya nikuma sannan muka tashi muma muka bi bayanta doon tafiya
hostel, shi kuwa kailani tsabar neman Magana wai sai ya bita wait a bashi aron
notebook zai kwafi note, ko waige batayi bat a kai hannu cikin Jakarta dake
rataye akafadarta zata dauko sai nace dashi “kai mujje inashi zan baka” jin haka
yasa ta fasa ta cigaba da tafiya yana zuwa wurina nace masa bani dashi harta
Bayan misalign sha biyu da kusan rabi n agama nawa assignment sannan
na sami foolscap nayi mata nata amma sai nayi ta kiran wayarta bata dauka wai
tayi fushi dani , hakanan n agama assignment din muka koma school, karfe biyu
muka shiga lecture da shigowarsa kuwa yace a tattara mas assignment na hada
duka na bayar snnan na cigaba da kiran wayarta amma duk abanz daga baya ma
sai ta kasha wayar , iya damuwa na damu ganin ko lcture bata zo ba kuma tun
safe na gaya mata abubuwan da za ayi ranar amma tunda ta koma hostel bata
fitoba kum nasan bai wuce akan maganar safe bace , iyadamuwa na damu
kasancwar na ria nayi nisa cikin sonta ko kadan benison dmuwar tta don haka
yasa banyi zuciyaba naciga bad a kiran numberta amma duk ga banza sai can
misalign karfe goma na dare sannan na kira ta dauka shima ahaka tana dai
maganane amma daji kasan ranta abace yake, duk da nasan kwanan zancen
amma sai na tambayeta “baiwar Allah ba fada me yakawao gaba?” hmm abin
mamaki sai naji tace “akwai mana…” tayi shiru daganan ni kuma sai na sake
tambayar ta “fadar? Yaushe aka fara kuma me yafaru?” akule tace dani
“kamanta da safe?” “oh am sorry kiyi hakuri ni wallahi nama manta na dauka
wasace ai” haka na fadi yayinda na nuna kamar ban san maganarba, ita kuwa
shiru kawai batace komai ba sai na sake cewa “nace kiyi hakuri bakice komai
ba” cikin shagwababbiyar murya tace “to kai shikenan kullum sai dai karinga
batamin rai sannan kace inyi hakuri gaskiya nib azan yarda ba” alokacin wani
abu yazo min wuya na rasa me zance mata don maganar tata dauremin kai tayi
said a ga baya nace “ban gane bazaki yarda ba, baki hakura ba kenan?” sai bat
ace dani komai ba sai na sake cewa “to misali in kince baki hakura ba ya kike
son ayi kenan?” “nima ban saniba” haka ta mayarmin muryarta aciki ciki, nima
shiru nayi sai daga baya nayi ajiyar numfashi nace “baki sani ba?” sai batace
komai ba cikin wata defeating voice nace “to shikenan..” wanda nayi niyyar
daga haka kawai kasha wayar zanyi in hakura da sulhun donnanga alamar bamai
yiwuwa bane, amma kafin in kaiga rufe baki sai ta datseni da “to aikaine ko da
yaushe sai karinga yimin wulakanci, kuma gashi yanzu daga dawowata jiya ka
fara bata min rai” shiru nayi ina mamakin yanayin yadda take Magana kamar
zatai kuka said a ta gama sannan nace “toh yanzudai ai na baki hakuri kuma kin
nuna bazaki hakura bay a kikeson nayi dake?” alokacin sai tace “to amma
gasjkiya sai dai wannan yazama na karhe” nikuwa da abin ya kule ni sai nace
“ok shikenan yanzu sai ki fadimin sharudanki tunda nidai gaskiya ban san wani
abu da na taba yimiki don ya bata miki rai ba don haka kinga in na san sharudan
naki nan dai muka sasanta kamar abin arziki amma daga karshe sai tace wai
“amma gaskiya daga yanzu yakamata kasan lokacin wasa sannan kuma kasan
lokacin daba na wasa ba” jjin haka sai naji taaa bani haushi domin kuwa gani
nayi ita ta fara sako wasa alokacin amma sai gashi tana gaya min cewa wai
maganin kar ayi kar afara don haka na sawa raina cewa zan kiyayeta kawai don
kar ma watarana in saki jiki muna Magana tace na wulakantata domin ni nasani
cewa kowaye kuma ko yaushe muka hau da mutum zan iya yi masaa wasa
Tun da mukayi haka da ita kuwa sai yakasance ko zan kirata bazan kirata haka
kawai ba sai da kwakwaran dalili haka kuma da zaran na isar da sakona sai in
kashe kawai in jure duk wani yanayi na kewarta dazanyi, haka zalika in muka
hadu sai dai tace dani sannu in amsa da yawawa sannu kawai ta wuce in wuce
sai in ta wuce in waigeta kasancewar bazan iya jurar dogon lokaci batareda na
ganta ba amma ya zama dole in sakaya damuwata akanta ahaka har kusan sati
guda domin tun ranar monday da dare da abin ya faru har sai ranar asabar
kasancewar na saba kusan duk lecture nakan kirata 5 minutes before the time
idan naga ban ganta ba, amma kuma ranar kaewwai sainaji bani da ra\ayin
kiranta don haka ban ko shiryaba sai miisalin karfe tara da rabi dana gama
shirina sai na fito daga block din na zauna kawai a tushen bishiya ina jina kamar
mara lafiya don wallahi kwata kwata bana jin dadin jikina, ina zaune anan
wiurin sai ga kiranta na kashe na kirata sai take cewa "wai baxaka fito bane?"
nikuwa sainace "zan fito mana, ya zone?" "a a bai zoba tukunna amma naga
kowa ya hallarane kuma ban ganka ba uakamata ka taho" haka ta fadi cikin wata
murya ta nuna alamun damuwa (concern) sai nace "to shikenan ganinan zuwa"
na sake shantakewa don ni nafi son inje intadda ya shiga ko kuma ina zuwa ya
shiigo don in har na riga malamin zuwa to fa lallai dole in ringa kallon inda
takke kuma lallai zata gane ni, ba afi mintina biyara ba sai ta sake kira ba kamar
yadda na saba ba sai na daga kawai na kara akunne sai naji tana cewa "ya shigo
fa" ta fadi hakan cikin fada ni kuma sai kawai nayi saurin kashe wayar sannan
na tashi na nufi school din cikin sa a kuwa na shiga bai fara ba, abinda na sani
kawai shine yayi min worning kan kar in sake zuwa masa aji late. sakamakon
yanayin da nake ciki alokacin yasa na kalleshi kawai na wuce naje na zauna,
kazalika tun da na zauna ban yiwa kowa magana ba hasalima ji nayi kawai
kwancitya tafiye min wannan zaman sai na dan kwantar da kaina kan desk din
dake gaba na ina yi ina dan tashi don nkara malamin ya gane cewa ina kwance
ne
Haka dai aka gama lecture babu ko dadi awurina donma dai mafiya
wani damu ba, malamin na fita sai na tashi zan fita sai na tuna da maganar
micro teaching practical domin kuwa mun forming na group wanda ya kunshi
head na group din sai na suggesting cewa ya kamata mu zauna don mutattauna ,
to gashi kuma banason yiwa Aisha Magana don karta dauki abin wani iri sai na
atattauna kan issue na micro teaching practicum amma in zata iya zuwa” kamar
ajirac take sai tace “zama ta iya zuwa kuma in kun gama nima inason Magana
dakai muje ma yanzu” haka ta fadi yayinda ta tafi takirawo ita Aishar muka
sami wani empty class muka shiga saboda kawai bana jin dadin jikina yasa
Bayan mun fito ne muka kama hanyar komawa hostel sai ita Raihanar tak
tambayata kan wasu abubuwa marasa kai bare tushe, amma babban abida ataek
tambaya kai bai wuce akan maganar Ita Aishar ba, ni kuma tun da naji haka na
fahimci me take son fadi, atakaice naso inyimata bayani amm sai naga ta bukaci
dogon zance saina fasa mata komai tun daga farko har karshe domin naga da
farko laifina kawai take gani. Zuwa can dare misalign tara sai ga kiranta muka
Tun daga annan lokacin bamu sake samun wani sabani ba sai ma naga kamar
babu mai jinmu dukda dai ko ada din ma babu mai jinmu illah kawai da na sani
cewa daga ni sai ita muke sanin ko akwai matsala ko babu donkuwa nidai ba za
lokutanma har assignment take attempting zata yimin amma ni nake nuna bana
son ta wahal da kanta. Kwatsam sai wata safiya ta monday tazomin wanda nayi
agammeda Aisha wanda da farko ni dakaina na san bai kamata zuciyata tayi
wannan tunaninba tunda har abinda yasani wannan danyen aikin bai tabbata
ahannun Rabiu Musa wanda na tabbatarwa da idona cewa baifi kwana biyu
rabona da ganin zoben a hannun ita Aishar ba bayaga cewa ta fadimin cewa
azuciyata duk da cewa ban tabbaatar ba, zuciyata tana bani cewa akwai
yiwuwar asami zoben ya zama iri daya ne bawai natanbane ahannunsa wanda
awannan gabar nake samun sauki araina amma daga lokacin da na sake duban
zoben naga babu wata maraba tsakaninsa da na Aisha sai inji kamar in hadiyi
raina kawai in tafi kowa ya huta don har zuwa nayi muka sake gaisawa na sake
duban zoben sosai don har tabashi da hannuna nayi Amma dduk da haka sai
kawai na sake share lammarin na barshi araina cewa kila guda biyu ne , har ina
fadi araina cewa indai kuwa daban daban ne to lallai zan yi kokari insa ta cireshi
ahannunta don tsananin kishi a haka har suka gama shiga mota suka fita zuwa
faru, don ni ban ma ganta ba saboda munyi waya da safe cewa ba za ayi lecture
da safe ba,
Da gari ya waye ranar talata muka sake fita wurin lecture ranarma saboda babu
wasu qwararan lectures da z ayi aranar yasa bata fito ba. ,misalin qarfe goma na
safen na kirata bayan mungaisa sai na fara bugun cikinta cikin dabara amma
sam sai na lura bata fahimceni ba don hirace muke kamar haka
Ni: sonake in tambyeki amma sai kinyi alkawarin xaki bani amsa dai dai da
Ni: (cikin qaramar dariya) a a ina nufin wani abu kamar agogo ko awarwaro ko
makamancin haka
Alokacinda ta fadi haka sai naji kamar ta mareni don jinayi kamar tadan
raina tunanina don ganin na santa da zoben tunda dadewa amma yanxu tace wai
dama babu. Daga nan kawai sai nace “ok shikenan na gode..” kafin in kashe
wayar sai tayi saurin cewa “amma duk me yakawo wannan tambayar?” sai na
mayarmata da “hm babu komai kawai naso inji ko akwai wani abu a hannunne”
“hmm to banyarda ba kawai ka gaya min dalili” haka ta fadi cikin rah anima
cikin raha nace “to shikenan project nake rubutawa shine nake miki interview”
sai duk mukayi dariya sannan tace “to wane irin project ne agayamin inji” “a a
ki bari in nagama rubutawa zan kawo miki ki karanta” nan dai mukayi ta
musayar zance cikin raha daaga karshe mukayi sallama na kasha wayar, daga
AWURINTA ? ina cikin haka sai na tuno wata shawara take sai na kirata sai
nace ta fito alokacin sai tace wai zatayi wanka sannan ta fito sai nace to
shikenan ya wuce domin dama alokacin nakeda bukatar ganinta sai tace inyi
Daga lokacinne na fara tunanin ko kila ta fahimta ne sai naji abin ba dadi har
matsanancin kishina ya sake motsawa wani abu ya taso ya tokaremin kirjina don
har jinake kamar zan fadi idan na mike, ahaka har kusan karfe biyu sannan na
wacce za’ayi karfe 2:00 pm na fita da wuri na isa science complex amma babu
kowa don haka muka fito nida wani cours mate dina Umar Idris don muje GSE
mu duba result mun fito kenan sai mukahadu da ita da kuma kawarta Raihana
sama sama muka gaisa domin har zuciyata ban wani yi fari cinki da ganinta
kamar yadda na saba ba suka tambayeni venue na gaya musu muka wuce suma
Zuwa mukayi bamu tarar da mutumin da ke duba result din ba don haka
sai muka dawo zuwa wurin lecture muka taras matar bata ma zoba , zuwa nayi
na sami wurin na zauna bayan na gaisaw da wanda nake ganin zan iya gaisawa
dasu acikin mate din nawa bamu dadeba sai suka tashi zasu fita wai zasu je
wani wuri acikin gari sun fita kenan sai kuma suka dawo tare da lecturer day a
kamata tayi lecture alokacin, nan ma bsu jim ba sai naga sun tashi sunfita koda
dai kafin fitarsu sai da na tura mata takarda mai dauke da “where is your ring?”
alokacin sai naji sunyi dariya dukansu bankuma ji respond ba abin yayi min
ciwo amma sai na share wai sai can da za su tafi sai tace wai agayamin idan za
A haka dai yinin yakare inajina kamar an zare min farin cikina don kuwa
ko aiki banyi niyyr yi ba da dare kawai zuwa nayi na sami wuri silent na zauna
donkuwa bana bukatar jinmotsin wani akusa dani, ina cikin haka sai ga kira
kamar daga sama daga dubawa sai naga kirran Raihana wato kawar ita Aishar
na daga sai suke cewa wai don Allah in fito suna on suyi practice na Mat 221
wato Dynamics cikin kuna rai dai na maa musu da cewa to in sunnfita sai su
kirani na kuma zaunawa raina nayimin daci misalin takwas da rabi nafit na
iskesu cikin room a ACL wato area classes, muka fara dubawa a hankali sai na
lura ita Aishar hankalinta na wani wurin sometime ma sai inga ta hda kai da
lafiy sai tace min wai lafiya lau, shiru kawai nayi mukacigaba da duba takarda
har kusan karfe goma da rabi sannan sai nake cewa da ita "na tambayeki ina
abin hannunki yake baki bani amsa ba" sai tace "ka bari zan gaya maka"
"yaushe?" "in mun tashi" na amsa da to shikenan muaka cigaba har sai da goma
takai da minti talatin da biyar sannan nace dare yayi muka tashi don tafiya
hostels, nidai ban tambayeta ba ita kuma bata tada maganarba muka yi sallama
na nufi block dinmu suma suka wuce nasu hostel din, aranar sai bankirataba
kamar yadda na saba sai da kamar sha daya tayi sai ta kirani, kasamntuwarba
kudi awayar sai na picking tare da sallama ta amsa sai bata sake magana ba
nima sai nayi shiru don kuwa ni bani da ta cewa alokacin sai daga baya tayimin
wasu tambayoyi wadanda a tunanina bawai sune silar kiran ba kawai dai ta
tambayoyinta sai tace min ta gode sannan ta kasha waya bayan kamar minti
biyar sai ta sake kira na sake amsawa awannan karon sai ta sake mai mai tamin
tambayar farko da tayi min da sunan bata fahimci amsar da na bata ba bayan na
sake yi mata bayanine sai muka sake sallama ta kasha wayar, ni kuma sai na
sake hayewa gado na kwanta zaman jiran tsammani don kuwa sai dai ince jiran
tsammani don na tabbata komai so na da barci aranar nasan bazai zo ba sai dai
wani ikon Allah kuma, Nayi zurfi cikin kogin tunani wanda yakai extent din da
banma san me nake tunawa ba alokacin sai vibration din wayata dake bisa
kirjina ya dawo dani cikin hayyacina cikin sanyin jiki na dauki wayar na duba
sai nag a sako aka turo da na duba sai naga text kamar haka : “yana gun Rabiu
musa zoben”. Iyaka abinda sakon ya kunsa kenan wani irin abu naji a qirjina
wanda ban ma san y azan kwatanta shiba don har idona sai da naga duhu nay an
sakanni sannan ganina ya dawo normal zuciyata kuwa haka take bugu kamar an
harboni da bindiga na kuskure bullet din nan na saki wayar akan gado na rufe
idona ina jiran ikon Allah ban san sa’ar da nayi barciba nasandai na farka dai
dai lokacin da aka bude kofar dakinmu alokacin kuma karfe biyar tayi,
dafarkawata kuwa wannan sakon dana karanta da dare ya sake dawowa zuciya
ta tacigaba da maimaita shi har nayi sallah na dawo daki na kwanta amma sai
naji zuciyata kamar ana hura min wuta na fara jin haushi ba gaira ba dalili
domin kuwa Magana ma ban son yi, da naji abin na neman wuce gona da iri sai
na tashi na dauki Qur’ani na fara karantawa sai asannan na fara jin dama dama
yakasance zuciyata ta fara rauni don ji nake da nikadai ke adakin kuka zan fasa
ahaka har sai da bakwai tayi sannan na tashin don inje inyi wanka
Bayan na gama shiri tsaf na fita don zuwa lecture sai na sake jin bana son
kowa ya dameni awannan yinin hakan yasa nakoma na dauko wani kyalle na
daure fuskata dashi yakasance iyakar idanuwanane kawai awaje nasake fita
hakan ma sai naji bai gamsheni ba nasake koma na karbo wani bakin Radar (eye
glasses) nasaka wa idanuna sannan na fita awannan shigar na nufi lecture hall
aranar English zamuyi da safe da na isa sai na taradda lecturer bata zo bah aka
nan muka zauna jikin wani dakali dake gefen A.U muna jiran tsammani can sai
na hangi Aisha sun taho itada wasu yammata guda biyu wadanda ban ma san ko
suwaye ba lokacin da suka kusato inda muke sai naga kamar ta gane ni domin
alokacin na fuskanci idonta akaina yake don haka saina ce da Abdulkadir wanda
alokacin ke zaune kusa dani “yakamata mu tashi fa don kasan Karin maganar
kifi ance Zama wuri daya tsautsayi ne” daga nan sai muka tashi muka koma
kusa da central mosque na makarantar muka zauna bamu jima ba sai na sake
hangen ita Aishar sun isa tushen wata bishiyar cashew sun zauna, alokacin sai
naji gabana ya fadi don atunanina ta ganeni yasa ta biyo don ta tabbatar cewa ni
dinne ko bani ba. Atakaice dai haka ranar muka yini bamu hadu wuri daya ba
don ko da muka shiga wata lakcar ta department zan iya cewa ban sata a idona
ba sai dai kawai da muka fita sai na hadu da ita a bakin kofa don ni daman a
barine sai ta fita ta kama gabanta tukunna sannan ni in fita, Awannan lokacin da
mukayi wa juna Magana bayan mun gaisa ne sai nace da ita inba wani abu za
tayi ba inason muyi Magana, kai tsaye tace “to muje dama hostel zan koma” ta
wuce gaba na bita abaya kamar igiya har wani class dake sashen ISC classes
akasan science complex muka shiga ciki muka zauna, na dauki tsawon lokaci in
ataraddadin abinda zan fadi mata sai daga baya na cire bakin tabarau din dake
idona nayi ajiyar numfashi, ita kuwa alokacin ko kallo ban isheta ba biro ne
ahannunta tana zane ajikin bangon littafinta sai dai na tabbata hankalinta da
kunnuwanta suna tare dani tana jiran taji nayi Magana, Ajiyar zuciya na sake yi
sannan nace “jiya na tambayeki game da zobenki baki bani amsa ba” da suri ta
kalleni tace “nabaka amsa mana” … “dayaushe kenan kika bani amsa” “da
daddare na tura maka ta text, ko be shigo ba” alokacin da ta fiurta haka sai da
na sake tuno abin da ya faru sa’arda message din nata ya shigo wayata, daga
baya sai nace “ya shigo amma ban gane me kike nufi ba” kai tsaye kuuwa tace
“cewa nayi yana wurin Rabi’u Musa” adai dai lokacin da tayi wannan furuci sai
naji kamar ta mareni a tsakiyar kasuwa, shiru nayi nadan lokaci kana na kalleta
shima na dan lokaci wanda hakan yasa ta cewa “me ya faru?” sai nace da it aba
komai kana daga baya na sake cewa “ke kuma haka kawai sai kikaji ya dace ki
bashi zobe?” sai tace dani “a a shi yagani yace yanaso inbashi ni kuma na
bashi” awannan karonma sai da naji zuciyata kamar ta fashe don bakin ciki
kawai basar wa nayi nace “to shikenan tunda ra’ayimkine” awannan karon
batace komai ba sai dai kawai da taga na tsare ta idona yasa tace “meyafaru?”
ajiyar zuciya kawai nayi nace “a! ba komai” saboda yadda take azuciyata yasa
bantashi na bata wuri ba don har ga Allah ji nake babu abinda zata yimin da
zaisa son da nake mata ya ragu acikin zuciyata. Duk kokarina alokacin in tausa
tsinci kaina ina ajiyar zuciya duk bayan second biyar sai dakyar da dauriya nace
“amma ina fata kin san matsayin kyautar zobe a al’adar bahaushe ko?” hhhhh
abin dariyar da ya faru alokacin wai sai tace “a’a ban sani ba” a madadin abin
yabani haushi sai ya bani dariya wanda hakan yasa ta kallona cikin mamaki tace
“lafiya?” dariyar nasake yi kana nace “hmm lallaine bamma dai kinsan ke ba
yarinya bace haka nan nima kin san ba qaramin yaro bane da za’a fadi Magana
wacce koda kwakwalwarsa bata gamsu ba zai basar da tunanin kila iliminsa ne
bai kaiba” fuskarta cike da mamaki sai tace “,me yafaru nifa da gaske nakeyi
wallahi ban sani ba” fadin hakan da tayi yasa nayi da nasanin taso da
maganar ,ma don ji nayi aduniya ta gama rainamin wayo, ace kamar ta kuma
bahaushiyab tace wai bata san ma’anar kyautar zobe ba, kallonta kawai nayi na
kau da kaina taree da furta wata maganar da ni kaina ban san me na fadi ba
ganin haka da nayi yasa ta ce “tunda ban sani ba kamata yayi ka gaya min sai in
sani daga yau” “a’a ni bazakiji abakina don komai na fadi zaki iya daukarshi
amatsayin son rai” haka na fadi ba tare da na kalleta ba don alokacinma ji nake
kamar in tashi in bata wuri. Sai tace “wallahi bazan dauka haka ba” “kin ga
manta kawai ya wuce in Allah ya kaimu lokacin da kika sani da kanki sai ki
fahimci yadda nake ji” ina rufe baki naja kyallen fuska ta sama kallo na tayi
tace “to in karbo?” “a’a ba da yawuna ba babu ruwana, ki bashi kyautar abin
sannan kicee zaki karba, kinyi me kenan?” “a a wai tunda bakaso sai in karbo”
“to ni bance ba in kuma neman izini kike ban amince ba” cikin fada fada na
furta hakan don raina ya fara baci. Cikin wani yanayi kamar na damuwa ta
kalleni kana ta kauda kanta sannan tace “don Allah ka fadamin” “ki bari ki
tambayi Raihana zata gaya miki” da jin haka sai tace “dama ita nake jira kawo
wayarka in kirata sai tazo yanzu ta fada min” ban ko kalli fuskarta ba sai kawai
na tura mata wayar ta dauka ta kira number Raihana sukayi Magana ko kadan ni
ban kai hankalina wurin ba, bamu jima ba sai gata ta iso bayan mun gaisa sai ita
Aishar take tambayar ta game da abinda muka tattauna da ita da buda bakin
Raihana sai tace “ya danganta da yadda kyautar takasance don ka bawa mutum
kyutar zobe ba wani abu bane, kawai mutumci ma zai iya sawa” “hmm daman
nasan za’aayi haka don nasan bakinku daya” “iya abinda na furta kenan nayi
shiru sai kuwa Raihanar tace “a a wallahi bah aka bane ai ita gaskiya duk inda
take fadin ta ake…” kafin ta rufe bakinta sai nayi hanzarin katseta da cewa “ok
dama gaskiyar haka take ? na tambayeki ainihin ma’anar kyautar zobe kina
cemin mutuncine kawai?” “a’a nace mutumci ma yanasa ayi kyautar zobe” inji
ita Raihanar jin haka ni kuma yasa nace “atsakanin mace da mace kenan ko?”
ringa yin adalci aduk lamuranku, ke tsakanin ki da Allah abinda kika fada haka
yake,?” abin mamaki kawai sai ta fara dariya wanda acikin dariyar sai take cewa
“agaskiya in namiji ya bawa mace zobe ko mace ta bawa namiji zobe yana
nufin so ne , ko da dai akan samu amincin da zai sa hakan ta faru koda ba son
bane” tana zuwa nan sai tayi shiru wanda ni kuma hakan yasa nace “kamar
misalign yaya kenan?” “kanar wa da kanwa mana” tana fadin haka sai nayi
ajiyar zuciya nace araina Allah ya kama min ita ta fadi ainihi gaskiya sannan
nace to Alhamdulillahi tunda Allah yasa kin fadi gaskiya yanzu,” ko kallon
Aisha banyi ba nasake kasa da kaina, sai asannan sai Raihanar tace “wai ma
tayiwa tambayar ba wanda ni kuma adalilin haka ysa ban furta komai ba ban
kuma kallesu ba, Kallona Aisha tayi ganin ban nuna damuwata akansu ba kuma
bana da niyyar yin Magana sai ita Aishar tace “waifa akan zoben da na bawa
dan antine ya gani shiyasa yake wannan maganar”, sanda tazo nan sai tayi shiru
ta kalleni ni kuma sannan kunnena kawai na basu don in na kallesu raina baci
yake, Awannan karon sai Raihana tace “to wai yanzu meyake nufi?” “oho nima
ban san me yake nufi ba, to ko yana ganin kamar ina sonshine?,” da tazo nan sia
tace “Raihana don Allah ina son shi?” danaji abin na neman zama fooling sai
nace “kunga ni duk ba wannan ba dama tambayace nayi mata kuma tace bataa
sani ba don haka maganar ta wuce” cikin wata dariya kamar ta tsiwa sai Aisha
take cewa “to yanzudai in karbo kenan tunda nasani” “a a babu ruwa na ba
kuma zan umurceki da aikata wani abu da ya sabawa turbar gaskiya ba don haka
kawai na bar maganar tunda nasan ajin da nake” lokacinda nazo nan amaganata
sai suka kalli junansu sukayi dariya aciki sannan Raihana ta kauda kai ta fara
sakin zance kamar haka “sufa halin maza kenan basu wa mata adalci su da
sunga abu bazasuyi binchike ba sais u fara maganganu shiyasa fan a tsani
soyayya aschool dinnan..” ta karasa magnar aciki wanda nasan ita kadai ce zata
Raina yayi ,matukar dugunzuma yadda naga ga gaskiya kiri kiri amma sai
nine ma nazama mara gaskiya laifin ma gaba daya akaina aka dorashi wanda
hakan yasa na maida kyallen fuskata kana nasanya bakin tabarau din dake
gareni alokacin, kallona kawai sukayi sannan suka kalli junansu Raihana ta kebe
baki sannan tace “Aisha tashi muje hostel yunwa nakeji wallahi” ba tare da mai
da mata martini ba sai kawai ta waigo inda nake sannan tace “tashi muje”
tsamm! Na tashi kamar dama ajirace nake na kama hanya har sai da na kai
bakin kofa basu taso ba, nadan jira su kadan naga kamar tafiyar tasu basu shirya
yenta ba sai nace dasu “naga kamar bakujin tafiyane donn haka sai anjima” ban
ko jira sun bani amsa ba nasa kai na wuce aranar dai bamu sake haduwa ba.
A haka dai rayuwa ta cigaba wani lokacin sai inji kamar ban san
damuwaba amma wani lokaci sai inji kamar ban taba jin farinciki ba, saboda ni
mutum ne mai tsananin kishi wanda na tabbatar da wuya in sami wacce zamu
jitu sosai matukar inada wannan kishin, Akwai wani lokaci ma nakanji indai
ason raina ne ban so ko Magana tayiwa wani namiji in bani ba, ko kuma in ma
yazama dole sai tayi maganar to banso ta cika yawan dariya kamar yadda ta
saba yiwa kowa, amma sai gashi kiri kiri sai ingga tashiga aji ta zauna kusa da
maza, abin yana matuqar qona min rai sosai domin nikaina da sanina nake kin
zama kusa da ita alokacin lecture saboda ban san wani irin kallo za ayi mat aba
in aka ga namiji akusa da ita domin kuwa ita macece mai kamun kai wanda
kowa yasani she is very decent ga addini sannan da kokarin karatu, sannan ni
asanina zan iya cewa ko makarantar za a tara gaba daya babu wanda zai iya
bada shedar cewa gashi yau anji kanta da wata ko wani, tasan mutumcin kanta
yadda ya kamata, hakan ne yasa ban san zama kusa da ita saboda ina ganin
kamar zai iya zubar mata da mutiumcinta kasancewarta kowa yasan tana da
kamun kai sannan zai iya zubar mata da kima saboda kowa ya ganni ya ganta
yasan ta wuce ajina koda kuwa ba a binciki asali ba don haka yasa koda yaushe
nake jin kawai dai ta amsa tana sonane don kar tace bata sona yazama cin zarafi
a gareni, ina matukar shiga qunci alokacinda na tsinkayi wani namiji zaune kusa
da ita saboda koda ace ita ta kame to fa sai ka samu masu takalarta da zance
koda kuwa baza ta maida martani ba ballantana kuma ace ta mayarda martanin,
Nakan zauna nayi ta mazari akan meyasa kusan kowane namiji haka yake
muddin zai zauna kusa da ita saikaga yana kokarin takalarta da zance ko meyasa
haka oho shin sunayi don inji haushine ko don me? In kuma ba haka bane
halinsu ne ahaka meyasa ni ban jin ra’ayin yiwa mace maggana koda kuwa yar
wace ce domin wani lokaci ko dama ace yar uwa ta ce natujar bamu saba soai
bay i mata magna yana matuqar yimin wahala ko kuima halittace hakan oho, to
takaiga nakanyi kwanaki sama da biyu batare da mun sami sabani da wani ba
saboda na koyi shanye damuwa koda kuwa wace irice, dalili dayane kuma
saboda aduk lokacin da tayi min wani abu wanda ya bata min rai wanda
batayi dai daio da ra’ayina ba, tofa dole zan shanye saboda ina matukar jinta
azuciyata bana kuma bukatar wani abu da zaisa taji ba dadi akaina, domin ji
nake kamar zata daina kulani in na fadi maganar da ta bata ranta, wanda ni
Kwanci tashi rayiwa ta cigaba wata rana mun fito daga lecture Real
analysis under maths department wato mat 223 sai muka jero Da ni da kailani
da Raihana da Kuma Aisha, da farko mai da Magana muke kan abubuwan suka
faru alokacin lecture wanda kuma bayan mungama wannan sai muka cigaba da
tafiya muna wasu indistinct Magana ni da raihana muna gaba sai ita kuma Aisha
suna tare da kailani daga bayan mu kenan sai da muka zo har kusan shagon
agallawa mai chaji sai na ga Raihana ta dan dakata sai asannan ne na waiga
naga me ke faruwa sai asannan ne naga ashe mun barosu Aishar abayane
hasalima shi kailani ya tsaya suna gaisawa da wani gaye wanda ni ban ma san
kowaye ba don kuwa ban sanshi ba, ganin haka sai nace da Raihana “Ni nayi
nan sai anjima” ita ma ta amsa min da cewa “to shikenan Malam Aminu sai
anjima” daga nan sai na nufi hostel din mu don nasan Balallai bane kailani ya
gama abinda yake da wuri saboda sanin halinsa da nayi wajen surutu.
Da zuwa na daki kuwa saina fara kici kicin dafa abinci, ganin har naje na
debo ruwa na dawo na dora abincin ban ga kailani ya iso ba yasa na fita naje
super market don in diba shi ama da naje sai ban ganshi ba nan nasan ya ware
gidansu ne abin ya bata min rai matuqa don haka ne ma yasa ranar ban ko kawo
ra’ayin zuwa gidansu araina ba bayan sallar isha’I kuwa sai kawai na wuce
shago don kuwa ina da kwantain aiki da banyiba, haka kawai bansan me ke
damuna ba sai nake jina ranar rai abace kuma ban fara jin haka ba sai da na fara
typing din wani project wanda erro sukayi yawa aciki na farko spelling mistake
na biyu kuma rubutun duk a cukurkude sai na kura ido nake ganewa gashi kuma
Biology ne ba normal English terms bane aciki balle in ringa rubutawa dai dai
yadda nasan Kalmar nan fa naji raina yayi mugun baci wanda hakan yasa na
saki kida a cikin wasu kananun speakers dake shagon nasanya wasun waqqoki
guda biyu da suke ta maimaita kansu wanda ko kadan hankalina baya gunsu
nidai kawai banason jin wani abu daga ko ma waye, inban manta ba waqar
LOYAL ce ta chris brown tyga da lil wayne sai kuma waqar Ayo ta chris brown
da tyga, ina cikin haka sai nake jin kamar ana sallama sai na waiga sai na iske
Adam yusuf Adam ya gaji da sallama har ya shigo, ko kadan ban rage volume
na wakar ba ban kuma kashe ba haka muka gaisa sama sama sannan yace in
bashi charger yasa chaji, alokacin wayatce ajiki ko 30% bata kai bah aka na cire
na mika masa don kawai banason dogon surutu, yadan zauna na dan lokaci yaji
kara ya dameshi ya tashi yayi gaba aranar dai babu wanda ya jure iya zama
ashagon har kusan karfe goma sai ga Bashir wani room mate dina dan asalin
jihar kano ne shi daga Karamar hukumar takai acikin garin Faruruwa wanda
nake ganin aduk room dinmu babu mai shekarunsa don haka ya zama kamar wa
garemu sai dai shima yana da barkwanci sosai ina zaune yazo yayin sallama
shiru ba amsa don banma san yazo ba sai da yazo ya dafani sannan nasan yazo,
yafara Magana yaji kamar rada yake saboda shi kanshi bajin kansa yake ba
hakan yasa yadan dake ni yace kai da Allah karage wannan karar banzar ko ka
kashe, ban ko kawoshi aka ba alokacin kuwa kokarinake in gano wata kalma da
na kasa ganewa tun shigowarsa, ganin naki kulashi yasa ya dauke takardar
yarike yace ko in kashe ko ya tafi da ita dole tasa na rage, sannan ya fara jana da
surutu in maidamasa atakaice don dai kawai ya rabu dani daga baya sai ya sami
kujera yace in kunna masa film ya kalla don shi ba kallona yazo yi ba, saboda
sanin halin sa sai na kunna masa film din na projecting masa a wani separate
monitor dake shagon ni kuma na cigba da aikina da main screen din dan dole na
kashe waqar gaba daya abin ma bai tsaya iya nan ba sai ya ringa takalata da
Magana domin duk scene da akayi wani abu increadible sai yayi comment akai
kuma sai ya sani ciki wani lokaci in tanka masa wani lokacin kuma sai dai in yi
kamar ban jiba ahaka wasu yara daga kauyen dake kusa da makarantar suka
karu sai muka zama mu hudu ashagon, muna haka har wajen goma da rabi sai
ga kailani yana zuwa yace in bashi ruwa yasha , alokacin banyi niyyar kulashiba
amma danaji abinda yaxo dashi hajace da bata shallake kowa ba sai na dauki
fifty naira na bashi nace gashinan tafi ka kawon canji, ganin haka yasa shi kuma
yace “lallai ne P.G wato yau ni kake bawa hamsin kake gayan mara dadi ko?”
alokacin ya ban dariya amma sai na share nace kaga malam tai kaje kasha ruwa
in ka dawo koma meye ka hidi, dariya kawai yayi ya fita yana cewa ina dawowa
akwai Magana, ban tanka masa ban a cigaba da aikina duk na gaji da zaman da
nake ma har na kosa 11:00 pm yayi saboda akashe gen din makaranta intai in
kwanta, baifi saura minti bakwai a kashe gen din ba sai ga kailani ya dawo da
zuwansa sai ya fara cewa “kai zo nan kaji wani batu” sai nace bari in karasa
aikinnan da yaji haka sai yace “karfe nawa yanxu?” nuna masa agogo kawai
nayi ba tare da fadin wani abu bas hi kuma sai yace “ok an ma kusa kashe gen
bari in ka tashi munyi magnar” shima sai yabi sahun masu kallo,
Ana kashe Gen kuwa ko cikakken mintuna uku banyi cikin shagon
nan ban a tattara na fito na kulle sannan nace da kailani “to uban rashin
mutumci ina kaje dazu bayan mun fito lecture nayi ta jiran ka shiru”
alokacin wata shegiyar dariya yai yace “ka riga kasan halina, bama
wannan ba wata tambaya zanyi maka” “ina jinka” iya abinda na furta
budar bakinsa sai yace “dama Aisha ta gaya maka tana da wani saurayine
na daban?” ji nayi kamar an harbeni akirji kaina yayi min wani irin nauyi
nake jin kamar ba da hausa yayi Magana ba sai da ga baya na dan basar
kana nace “kai ban gane ba me kake nuhi?” shikuwa sai sake cewa yai ina
nufin Aisha nada wani saurayine daban bayan kai?” iya fadin maganar
ma kawai ta tayar min da hankali matuka dukda cewa nasan tana iya
yiwuwa yanayine don ya kada min ciki, dan tsaki na saki nace “kai
malam banson tsiyarka don Allah” shikuwa ganin haka yasa yayi dariya
sai na maze na sakeyin dariyar yake don kuwa sai dai yake don alokacin
kirjina in banda dukan uku uku baa bin da yake “to naji koma dai meye
“to ya isa haka wa ka gani?” “small mana wannan me cafe” yana fadin
haka sai na tuno lokacin da muke waya da ita nake cewa nib azan yi
Kafila Yususf sai kuma Bellon Hasan Gazara ina tuno hakan araina saina
karajin ba dadi amma daga baya da na tuna cewa dama tun farko nasan
tafi karfin ajina sai na dan sauko sai abin ya koma damuwa daga jin
haushi, ajiyar zuciya nayi alokacin sannan nace “to koma dai meye Allah
yafimu sanin gaskiyar lamari” daga karshe na sake yin dariya nace “to
waima inma saurayin nata ne ai niba wai abin damuwa bane awurima
sosai saboda dama nasan ba ajina bace bare ince dole saini kadai zata so”
kailani kuwa kwafa yayi sannan ya ciji baki yace “lallaima kai.. bai
katraasaba yai shiru yace “amma dai mai daki shiyasan inda ruwa yake
masa zuba” nima dai dariyar kawai nayi ta yake sannan mukayi sallama
yayi hanyar gidasu nikuma na nufi hostel dinmu kaina wani girim kawai
nakeji, haka naje na kwanta ko alwala banyi ba, nan fan a zurma ramin
tunani narasa abinda kemin ciwo, na kasa rarrabe wane hukunci zan
don kar yazama ta wulakanta dan adam, to amma kuma aduk lokacin da
na tuna cewa in harfa na rasa ta to tabbas wanine zai sameta hakan sai
yasa inji wani bakin ciki, har infara wani sakaran tunani wanda in nayi
wasa tauhidina zai sami rauni saboda har jinake me yasa ni nakasance
bantaba jin son wata araina ba, gashi kuma bias ga alamu bazan sameta
karfe sha daya da yan mintuna sai na kira number Raihana domin wayar
Aishar ta sami matsala sai nai sa’a kuwa batayi barciba mun dan gaisa
sama sama sai take cewa dani Aishar tayi barci, to daman ni bba Aishar
nakeson Magana da it aba ita Raihnar ce, sai na fara Magana kamar haka
kuma?” sai nace “eh kedin amma don Allah ina rokonki duk maganr da
akaina bayan mun tattauna” haka na fadi mata abinda yasa na fadi haka
kuwa shine banason taji magnar daga wani harr anta y abaci dominkuwa
na tabbata bazata ji dadi ba shiyasa, take kuwa tace kar ka damu insha
Allah bazataji abakkina ba” “to nagode.. am dama sonake inji ko kinsan
meke tsakanin small da Aisha?” “small mai CAFÉ wai?” “eh shifa”
amaimakon ta bani amsa sai naji tayi wata tambaya wanda da farko saida
gaba nay a fadi cewa tayi “ban gnae ba me yafaru ?” sai naji hakan kamar
yana nuna alamun ta sani ne,sainace a a ba komai wallahi kawai jita jitace
naji yasa nake son inji kar inyi abinda ba daidai ba” ajiyar zuciya tayi
kawai tana kai masa photocopy kuma baya amsar kudinta amma nidai
nagode dama wallahi magna ce tayi yawa kan wai shi saurayin Aisha ne
shiyasa tun ina share wa har abin yafara damuna saboda rashin tabbaci
akai” haka na fadi kana ita kuma daha baya tace “gaskiyane dole abin
zaio dame ka, amma ka tambayeta mana kaji daga bakinta” “a a basai na
gaskiya bane” haka na fadi cikin sauri don karma tace ita xata gayamata
in shiga uku domin ji nake muddin labara ya isketa zan iya shiga matsala
“to shikenan Al-ameen insha Allahu ma bagaskiya bane” “to Allah yasa
haka, nagode sai dasafe” “to sai da safe Allah ya tashemu lafiya” nan
tunani domin jinake tunda har Raihana bata saniba to lallai jita jitace
kawai, nan nayi barci na harda dan guntun mafarkina wanda kafin safe
lecturw farko da akayi da safe ban ganta ba nayi ta jira duk da dai na dan
tsorata da zancen da kailani ya gaya min amma sai nayi ta duban kofa
kozan ganta ta shigo amma shiru har lecture ta kare kafin mu fita wani
lecturer ya shigo muka dora da wata lecture daban, harm un kusa kare
lecture sai ga kira daga number Aisha dayake raina ya far abaci saboda
rashin ganinta da banyi ba kuma nayi ta kiran wayarta bata shiga sai nayi
kamar bazan dauka ba sai daga baya sai na dauka na kara a kunne sai
kuwa naji sallamar Raihana nan fa sai naji gabana ya fadi na fara
muka gaisa sannan sai tace “wallahi Aishace dama bata da lafiya tunda
safe muna asibiti da ita” wani rin sarawa kaina yayi naji kamar an buga
min wani abu saida na dauki yan sakanni ina istirja’i sannan nace “a wane
asibitn kenan?” sai tace dani clinic din makaranta, har na yunkura zan
mike sai na tuna cewa a cikin class nake sai na koma na zaun nace da
Raihana “ok in sha Allahu ganinan zuwa yanzu ina lecture ne zan nemi
excuse in fita” dan basarwa nayi kadan naga abin fa bazai yiwu ba don
class din dsauri nayi asibitin makarantara don inje inganta don inga halin
da btake ciki domin dagaske hankalina yayi matukar tashi bias ga rashin
lafiyar tata nidai kawai fatana shine inje intarar cewa jikin yayi sauki
saboda a mafiya yawn lokuta in naji wani abu ya sami Aisha jinake
kamar ana cizona in kuma naganta acikin wani hali sai’inji kamar an zare
lakar jikina yadda tafiya ma adole nake yinta cikin hanzari na isa asibitin,
ina shiga kuwa na isketa kwance cikin wani irin yanayi don ni aganina
ma kamar bata san nazo ba muka dan gaisa da wadanda ke tare da ita
Aishar cikin tausaywa nace “sannu ko” tayi min alamun taji kuma ta
amsa tahanyar motsa kanta kadan duk da cewa akwance take, ji nayi
kamar inyi kuka alokacin sai da na daure nace da ita ya jikin ta sake yin
alama wanda ni azuciyata naji kamar tace “da sauki domin kuwa
kunnuwana basu jiba kasa sakeyi mata Magana nayi har sai da Raihana ta
iso daga inda take domin alokacin da na shiga bata ward din muka dan
gaisa da ita sama sama sannan na tambayeta ya jikin Aishar tace min da
sauki. Har da wani iyayi nawa don kuwa nasan a matsayin iyayi zasu
dauke shi dukda cewa ni har cikin rainana fadi yadda na ce “amma an
dubata kenan ahaka?” “eh sun dubata kenan gama maganin da suka bata”
“oh God” haka na tsinkayi kaina ina fadi sai daga baya nasake duban
Aishar ina ji araina kamar in cire mata abinda ke damunta kawai ta tashi
mubar wurin da ita sai da na sake yin ajiyar zuciya sannan nace to
charges fa nawa suka chaje ku?” sai kace irin ina jin karfi dinnan dominfa
a sannan ko cikakkiyar five hundreds babu ajikina amamakina sai naji
tace “ai tana da file anan kuma kasan in mutum yana da file kyautane”
“ok..” iya abinda nasake iya fadi kenan nayi shiru “wai kinga nifa ina
ganin kamar gara akaita cikin gari don a running over all test a kanta
domin naga abinnne yaki ci yaki cinyewa” haka na furta bayan na dau
tsawon lokaci ina tauna maganar araina don gudun kar suga kamar na
raina musu abinda sukai ita kuwa Raihanar sai cewa tayi “eh haka ne
nima nayi wannan tunanin amma yanzu tunda sun bata magani mu gwada
mu gani tukunna in yaso in abin yan cigaba sai akaita cikin garin, duk da
dai muna sa rai zata sami sauki” “toh Allah yasa hakan don munfi sonn
hakan dama” na furta hakan cikin wani yanayi dani kaina ban san yazan
kwatantashiba nan dai na dan zauna shiru kafin daga baya na fita atsarge
nace bari in dawo, abinda yasani tsarguwa kuwa shine ganin yadda na
taradda ita Aishar cikin wannan hali sannan babu abindama yafi bani
takaici ma sai yadda na tuna cewa asannan babu wasu cikakkun kudade
ajikina ballantana in dan yi mata saye saye wanda suka kamata, haka na
nufi super market kamar wanda babu laka ajikinsa shiga kasuwar nayi
nadan sai wani abu wanda kunya zata hanani furta muku shi sannan na
sake nada kwana na koma clinic na sake zama kamar wani mai gadin
wani abu sai dai in dan duba inda ita Aishar take in sadda kaina kasa
kamar wani munafiki saboda ni kadaine namiji awurin har sai da na duba
agogo naga na kusa share mintuna talatin zanne sai na tashi nayi musu
sallama sannan na fice na nufi hostel na kwanta duk da cewa lokacion sha
biyun rana tayi kuma akwai lecture da yakamata in halarta amma sai naji
bazan iya zuwa ba don nasan ko naje ba abinda zan fahimta, na kusa
mintuna sha biyar ahaka sai wata zuciyar ta ce dani gara in tashi in yaso
Muna tasowa kuwa na yiwa Raihana waya ina tambayar yanayin jikin
sauki, Raihanar ta amsa da amen kana tace “munga abu mun gode” fadin
hakan da tayi sai da gabana ya fadi don nasan kwanan zancen domin ance
mara gaskiya ko acikin ruwa jibi yake sai na dan basar nace bangane ba
“eh nace ne munga abu mungode” haka tasake mai maitawa nikuma sai
nace to shikenan tunda an fara haka sai anjima banma jira tayi Magana
Aranar jumua’ah kuwa bayan mun fita sallar jumu’ah sai muka dawo
muka taradda anyi mana shashanci a hostel din mu domin acikin dakin
arasawa, hakan yasa muka raka wadanda abin ya shafa security division
don suyi report don gudun tashin maganar wata rana, muna kan hanyar
mu ta tafiya sai na hangi Aisha zaune kan gabar wata gada gab da school
clinic tun daga nesa na gane cewa itace don haka na kasa dauke ganina
daga gareta don da ganinta kaga marar lafiya hankalina dai bai kwanta ba
amma saboda tunanin kada mutanen da muke tare dau suyi wani abinda
bai dace ba yasa sai banyi wa Aishar Magana ba illa iyaka da mukayi wa
juna murmushi sannan a daga mata hannu afakaice itama alama tayi min
da kanta muka wuce, bayan mun bar security division din sai sauran suka
fice daga makarantar don shiga gari ni kuma sai nayo kwana na dawo har
da gudu gudu don saurin inzo inga switch din duk wani mood da nakan
iya shiga azuciyata wato wacce ako yaushe nake daukar kaina kasa da ita
don ganin matsayinta da nake, nake jin cewa alfarma ce kawai tayimin da
har take iya kulani don kuwa ban cancanci koda gaisuwa ba ma bare har
wani batu soyayya ji nakeyi koda ace zatace dani ta jingine ni gefe bazan
taba ganin laifinta ba hakanan bazan taba daina wani abu gareta ban a
daga kyautatawa don kuwa na riga nayiwa kaiana alkawalin cewa ko tana
sona ko bata sona baza ta taba neman wani danake da ikon yi matra shi in
babu shakka zan bauta mata, ko da acikin kawayenta naga suna Magana
koda kuwa kuwa tarahace na tsani inga anyi mata wani abu wand aba
daidaiba ballantana kuma ace daga bangaren maza, wanda da farko wanta
Cikin rashin sa’a sai ban insketa awurin ba nan danan sai n adage
waya na kirata nayi sa’a kuwa ta daga bayan mun gaisa sai na tambayeta
abinda take awurin da na tarar da ita sai tace dani sun fito daga clinic ne
sai sauran suka fita main gate don suyi siyayya ita kuma sai ta tsaya
hutawa da nasake tambayarta “yanzu kin koma kenan?” sai tace “a’a ina
nan in ashan iska a kusa multi purpose hall(church)” “ok to yayi kyau, ke
haka sai da naji kaina yayi kato cikin zumdi kuwa nace “in dai kin bani
daman zuwa me zai hana?” “to kazo mana ain i kadaice kuma ba wani
abu nake ba kawai hutawa nake” haka tafadi wanda sannan na mayar
mata da cewa “to ba ki ganin in nazo zan dameki?” “hmm kai dai kawai
in akwai inda zakaje shikenan amma ni bance zaka dameni ba” abinka da
mai neman kuka da aka jefa da kashin awaki ban ko jira ta rufe bakiba
nace “to shikenan ganinan ahanya” na fadi hakan gami da kashe wayata
na kara sauri.
Da isata sai na taradda ita zaune kan yar kujerar karfe daketushen
isa wurin, sallama nayi wacce ta fargar da ita har ta waigo don taga ko
waye sannan ta amsa, ganin na coge a tsaye sai tace “ka zauna man aka
tsaya atsaye?” alokacin yar kunyace ta kama ni don dari dari nake da ita
shiyasa na coge ganin kujerar ba wani girma gareta ba sai kuma gashi ta
cedani wai in zauna, jikina har wani bari yake slightly ayayin da na dan
matsa kadan na zauna kusa da ita tazarar dake taskanina da ita baifi 1feet
ba wato 12 inches, kwatan kwacin 30cm kenan, muka dan gaisa
samasama na sake yi mata ya jiki ta amsa cewa da sauki kafin daga baya
muka dan fara hira sama sama dai mun kai kusann mintuna 40 har ta
turamin wasu pics dinta, sai can da na fara rasa abin fadi sai nace da ita
“akwai wani abu da yake raina na kasa mantawa dashi duk da cewa ban
kira amma ban sami mafita ba” bata ko kalleni bat ace “to mekenan haka”
sai da nayi ajiyar zuciya sannan nasami damar sake budar baki nace
“wani labarine mara tushe ya isheni cewa wai usman small saurayinkine,
saboda kore tanttama,” sa adda na fadi haka sai tayi shiru bat ace komai
ba sannan ta juya kanta wani wurin kamar ba da ita nake ba, wanda hakan
ya dan sa gaba nay a fadi na dan kalleta na tsawon lokaci sannan nima na
kauda kaina na koma kallon wayata araina nace bazan sake tambayarta ba
don naga alamar ranta ya baci kuma gashi dam aba cikakkiyar lafiya take
da itaba har na fara tunani fara bata hakuri sai naji tayi ajiyar zuciya
yanzu ba” wani abu naji azuciyata kamar an dokeni akirji dakyar na
hadiye yawu sannan nace “hmm ok amma ni abin tsoro ya bani domin
naga bantaba sani ba” kafin in sake furta wani abu sai tace “gani nayi ai
sannan nace ita ma Raihana da na tambayeta cewa dani tayi bata sani ba”
“ai alokacin bama tare da Raihana shiyasa bazata sani ba domin kasan
NCE I lokacin bamu san juna da raihana ba” da fadi haka sai tayi shiru ta
dan kalleni har muka hada ido kafin ta kauda idonta, nima alokacin sai
nayi shiru na dan lokaci sannan nace “kar kice na dame ki da tambaya,
amma meye silar rabuwar ku dashi?” bata ko jira ba sai naji tace
“halinssa yasa muka rabu” daga nan ban sake tambayarta wani abu ba har
aka fara kiran sallar la’asar mukayi sallama na tashi na nufi masallaci ita
ma sai ta nufo masallacin domin tayi sallah kafin ta koma hostel, amma
rshin lafiya don har ajikin a jinake yi kamar nine bani da lafiya, domin
har ga Allah ban taba jin son wata ya mace da gaske da zuciya daya ba
kamar yadda nake son Aisha ba haka kuma bana tunanin akwai wacce
zata kuma samun wannan damar domin kuwa zuciya ta gaba daya na bata
kuma nasan bazaiyiwu ta dawo gaba daya ba babban abin bakin cikin ma
shine duk kokarin da nake wajen ganin na faranta mata sam sai kaga
kamar bata san inayi ba wani lokacima sai in ringa mamaki araina “me
yake kawo haka? Saurayi gareta daban ni kuma irin kumfar kogi nake
emotionless?”
A haka muka kasance rayuwa dai gata nan sai daikawai ayi
alabarce