100% found this document useful (2 votes)
1K views206 pages

Abdus Samad 1

Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
100% found this document useful (2 votes)
1K views206 pages

Abdus Samad 1

Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
You are on page 1/ 206

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)

*Heart you so much*

*labari ne ƙirƙirarre,banyi dan cin zarafin wani ko wata ba,idan yayi dai-dai da
rayuwar ki to an samu daidaito ne amma ba wai niyar tozarci ko wani abin ba*.

*Masoyana wa'inda na sani da wa'inda ban sani ba ina miƙo godiya ta a gare
ku,sannan ina fatan zaku bani haɗin kai a wannan kamar yadda kuka bani a
ƙareenateey,sai dai ina me baku haƙuri domin kuwa wannan zai fi ƙareenateey tsayi
sosai duk da wancan ɗin ma yankewa nayi amma wannan babu wannan maganar dan haka
ina fatan zaku bani haɗin kai sannan kuma zakuyi jimirin bibiyar shi har izuwa
ƙarshe nagode sosai*.

Bismillahir-rahmanir-rahim.

📖📖01-02📖📖

Jejin dake hanyar Abuja idan ka baro kaduna,tafiyar mita ashirin daga ƙauyen
banguwa,wani madaidaicin gida wanda yake kusan ginin ba'a ƙarasa shi ba.
Manya-manyan Bishiyoyi sune suka yiwa gidan ƙawanya inda baka hangen komai daya
shafi gidan,ƙaton get ne irin na da wanda keda nauyi da kuma daɗewa.

Daga cikin gidan kuwa,wata irin farfajiya ce me girman gaske wanda ciyayi da
kuma rairayi suka rufe wajen ba zaka iya gane yanayin ƙasar wajen ba.

Ƙofar da zata sadaka da ciki kuwa ƙofa ce ta ƙarfe me matuƙar nauyi,daka shiga
wani falo ne ƙarami me duhun gaske wanda idan baka yi da gaske ba zaka iya
bugewa,babu wani tarkace a falon banda kujeru da kuma tum-tum wanda suke ajiye a
ƙasan carpet ɗin ɗakin.

Ta ƙaramin corridor kuwa doguwar hanyace wacce ke ɗauke da ƙofofin ɗakuna jere
masu yawan gaske,daga ƙarshen corridor ɗin kuwa wani falon ne wanda yake babu kyan
gani,saboda komai na ciki kalar ja ne,sannan ga wani irin tururin hayaƙi da yake
fita me matuƙar ban tsoro da tashin hankali.

A ƙalla mutanen dake jere tsaye sanye da zani babba kalar ja jikin su babu
riga,fuskar kowanne na nuna damuwa da ɓacin rai,sama dasu ishirin,kowanne kanshi
babu koda ɗigon gashi.

Wani mutum duka suke kallo wanda yake zaune saman wata ƙatuwar kujera wacce
gefen ta kuwa gunkin zakuna ne hannun dama dana hagu,gaban shi kuma ƙwarya ce babba
wacce ke saman wuta tana ci sosai da sosai.

Tsayin minti biyar babu wanda yayi magana kafin can wani dake gefe yace cikin
fusata da damuwa.

"haba Tuge wai wayo kake son ka gwada mana ko kuwa ɗan naka so yake yafi ƙarfin
ka,yau shekara ashirin da biyar kenan da yiwa *oregbu* alƙawarin bashi jinin matar
ka da ɗanka amma babu ɗaya daya samu".

Wannan dake zaune saman kujerar ya ɗago idanun shi da suka kaɗa suka yi ja ya
zubawa wani mutumi wanda yake durƙushe gaban wannan ƙwaryar,cikin fusata yace;
"bakaji tambayar da akeyi maka bane ko kuwa baka da amsar da zaka bayar ne?".

Cikin matsananciyar damuwa yace; "nayi iya yina *Appu* amma abu ya gagara matar
nan ko gidan ta bata bari na kusanta kuma kun san hakan sannan dai-dai da rana ɗaya
bata taɓa barin jikin su babu kariya ba shi kan shi yaron nawa ba sani na yayi
ba,kuma fa kun riga da kun san hakan kuma tunda na yiwa Oregbu alƙwarin jinin sa
aikuwa babu makawa jinin nashi ne".

Wannan daya kira da Appu ne ya miƙe tsaye sannan ya ɗauko wata sanda doguwa daga
saman ta kuma tsini gare shi kamar kibiya ya ɗaga ta sama sannan yace; "har yanzu
Tuge da sauranka,baka cika aƙawarin daka ɗauka ba dan haka sandar zama magaji tana
nan a ajiye sai lokacin daka cika sannan Oregbu ya fara gajiya idan har baka kawo
jinin ɗaya daga cikin su ba nan da lokaci kaɗan ba zaka fuskanci fushin shi".

Tuge ya buɗe baki zai yi magana Appu cikin tsananin tsawa yace; "maganar Oregbu
itace magana baya buƙatar martani ko kuwa gardama,a fara gabatar da wankan
tsari",dole yaja bakin shi yayi shiru.

Wani me ƙaton ciki ya taho cikin sauri ya ciri wannan ƙatuwar ƙwaryar dake saman
wuta ya ɗaga ya miƙawa Appu shi ya fara sha sannan ya kwarara jinin a jikin shi
wanda bana da tabbacin jinin na meye sannan aka miƙawa Tuge shima yayi yadda Appu
yayi sannan sauran mutanen dake wajen.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸
*HAYIN RIGASA,KADUNA*.
ƴan mata guda biyu ne suka sauka daga Keke Napep a bakin titi,dukan su suna sanye
da pink din hijab wanda ya saukar musu dan har ya wuce gwiwa,ɗayar fuskar ta tasha
make-up ɗaya kuwa babu wani kwaliyya a fuskar ta sai dai duk da haka kyawun ta ya
bayyana,dukkan su kama ɗaya gare su wanda hakan ya tabbatar mini da cewa ƴan biyu
ne kenan.

Wacce tayi make-up ɗin ta ya mutsa fuska tace; "Ramluv,wallahi na gaji


sosai",wacce aka kira da Ramluv ɗin tayi murmushi kawai tana buɗe purse ɗin dake
hannun ta,ta ciro ɗari biyu ta miƙawa me Keken tace; "malam bamu canjin mu".

Me Keke Napep ɗin ya leƙo da kan shi yace; "haba Hajiyoyi ai bakuda canji,tun
daga Tudun nufawa sannan ku nemi canji haba mana".

Wacce tayi make-up ɗin da yawa ta kalle shi ta wurga mishi harara tace"wallahi
baka isaba sai ka bamu canjin mu ai dama ɗari da hamsin muka yi da kai sannan koda
ka kawo mu baka shigar damu cikin unguwa ba mun kuma ƙyale ka shine zaka ce ba zaka
bamu canji ba wallahi sai ka bayar".

Shima ɗan Keke Napep ɗin ya fito ya tsaya cikin faɗa da fitsarar ƴan zamani
yace; "idan kuma na hana me zaki yi mini?",ta kalle shi taja tsaki tace; "au
tambaya kake ma to wallahi zaka sha mamaki kaɗan daga aiki na wallahi na saka ayi
maka dukan tsiya ƙaryar rashin mutunci kake".

Ɗayar ta kalli wajen sannan ta kalle su yadda kowanne keji da ɗanyan kai ga kuma
waje ya fara cika cikin murya me rauni tace; "Rimluv dan Allah kiyi haƙuri kizo mu
tafi",ta juyo ta balla mata harara sannan ta cigaba da masifar ta.

Yadda suke kamar zasu yi dabbe ga jama'a a wajen,gashi taƙi ta dena ya saka ƴar
uwar ta fara hawaye wanda ita bama ta lura da ita ba,ita kuwa daman ƙoƙarin ta taja
ƴar uwar tata su bar wajen.

"banza ɗan iska mara mutunci",Rimluv ɗin ta faɗa cikin fusata,hannu ya ɗaga
domin sauke mata mari ya sauke akan ƴar uwar ta wacce ke ƙoƙarin raba su,Rimluv ta
kalli ƴar uwar tata tace; "ka mare ta wallahi ba zaka ci bulus ba",itama ta ɗaga
hannu ta kwashe shi da mari,wanda hakan yayi dai-dai da zuwan wani dattijo.

Cikin sauri yace; Nusreen kece da dambe da maza a titi harda mare-mare?",ganin
wanda yayi maganar yasa ta saukar da kanta ƙasa tana cuno baki.

Cikin daka tsawa yace; "kin wuce gida ko sai na ɗauke ki da mari shegiya me
baƙin hali",ta ɗago da zummar yin magana ƴar uwar tata tayi saurin matse hannun
ta,shiru tayi tana ƙwafa sannan ta kalli me Keke Napep ɗin ta harare shi,hamsin ɗin
da yake miƙo mata ta fuzge sannan ta juya tayi gaba tana faɗin"matsiyaci kawai".

Kowa a wajen da abinda yake faɗa,ita kuwa gaba tayi tana tafe tana
masifa,dattijon nan yace; "ki rufe mini baki ko kuma nayi miki duka a wajen nan me
mugun hali irin na uwar ta",shiru tayi tana jin wani tuƙuƙi a cikin ranta wanda
hakan ba ƙaramin takurata yayi ba na rashin bata damar maida mishi da martani da ta
hanata yi.

Can ƙarshen layin wani gida na rufin asiri za'a ce dan kana gani ka san talakawa
ne,duk da dai ya sha sumunti sannan da ƙofa irin ta zamani a jiki,gaban gidan kuwa
siminti ne a shinfiɗe wanda ya ƙara fito da gidan.

Tana shiga ta banko ƙofar wanda saura kaɗan wannan Dattijon ya buge,aikuwa ya
fara ɗebe mata albarka yana banbamin faɗa,ita dai hannun ƴar uwar ta taja suka
shige ciki.
Tsakar gidan kuwa yana nan yadda suka zata,duk tarkace alamun tun safe ba'a yi
shara ba kenan,gefen famfo wata matace ƙatuwa tana zaune tana faman tace ƙullun
wara wanda hakan ke nuni da kayan sana'ar tane.

Nusreen taja tsaki bayan sunyi sallama bata amsa ba,tace; "mutum dai wuta zai
shiga idan yayi wasa domin kuwa rayuwar yanzu bata da tabbas kayi aiki nagari ma
yaka cika balle kowa ya san da cewa Sallah da salati bata dami mutum ba ai ba abin
mamaki bane idan mutum yaƙi amsa sallama".

Wannan matar ta taso cikin masifa tace; "ke mara kunya fitsararriya wallahi idan
baki dena shiga harkata ba a gidan zan jibge ki naga wanda ya tsaya miki".

Nusreen ta wulla mata harara tace; "gwara ni Allah ne ya tsaya mini ba boka
ba",wannan maganar caraf a kunnen Dattijon nan wanda ya shigo yana nashi masifar.

Kanta yayi da gudu,ita kuma ta zuba da gudu tayi wani ɗaki wanda yake daga can
lungu tana faɗawa ɗakin ta rufo ƙofar.

Cikin haki yace; "wallahi zaki zo ki same ni ne shegiya me zubin mayu,matar tawa
kike faɗawa haka shegiya da haihuwar ki gwara ɓarin ki,zan kuma zo kan uwar taki ne
wacce ke ƙara zuga ki",yana faɗin haka ya juya.

Dai-dai ƴar uwar tata ya tsaya wacce ke faman zare idanu domin tasan akan ta abin
zai ƙare aikuwa kamar yadda ta zata yana zuwa ya zuba mata rankwashi sannan ya kama
kunnen ta ya murɗa yace; "ƴar iska munafika kina zare idanu kamar ƙwan nufawa",ta
girgiza kai hawayen azaba yana zubowa daga idanun ta.

Sai da ya gaji dan kan shi sannan ya saki kunnen,ya fice yana bambami,wannan
matar me ƙiba ta kalle ta cikin huci,da sauri ta nufi ɗakin da ƴar uwar ta ta shige
amma kan ta kai taji saukar kwano a kanta wanda yasa ta ƙwalla ƙara saboda azabar
zafi.

Nusreen na daga ɗaki tana jin ihun ƴar uwar ta ta yunƙura zata tashi mahaifiyar
su dake zaune ta wurga mata harara,bata son ɓacin ran mahaifiyar tasu hakan yasa ta
koma ta zauna tana wuci.

Ita kuwa Nusram ganin babu sarki sai Allah yasa ta miƙe ta ƙaraso bakin ƙofar ta
ƙwanƙwasa,Nusreen tayi sauri taje ta buɗe mata sannan ta riƙo ta suka shigo tare
cikin ɗakin.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

*UNGUWAR SARKI,KADUNA*.

wani katafaren gida wanda kana ganin shi ka san ƴan gidan sunci kuma sun tada
kai,wanda zaka iya cewa basu ma san talauci ba,ko'ina ka duba a bakin gida
securities ne ke kaikawo domin tsare lafiyar ahalin gidan.

Daga cikin gidan kuwa a ƙaton falon wanda yaji kayan more rayuwa,samari guda
biyu na hango zaune saman kujera,sai mace ɗaya dake zaune a ƙasa rungume da filo
tana danna waya,daga gefe kuma wata yar budurwar ce gefen ta yaro wanda ba zai wuce
shekara goma sha biyu ba hannun shi riƙe da littafi da alamu karatu take koya
mishi.

Jin taku da kuma wani fitinannen ƙamshi yasa dukan su ɗaga kai suka kalli
Upstairs ɗin suna jiran ɓullowar me wannan ƙamshin,wata matashiyar macece wacce a
ƙalla zata kai shekaru arba'in zuwa arba'in da biyar,fara me ɗan ƙiba,tana da tsayi
wanda shiya ƙara ɓoye ƙibar tata,jikin ta sanye da wani danƙareren lace wanda a
ƙalla zai kai dubu tamanin zuwa tamanin da biyar,ɗinkin borno wanda yake plain zani
ne da kuma rigar iya gwiwa wacce taji aikin wuta,kafaɗar ta kuwa ta yafa wani gyale
milk shima me tsadan gaske ƙafar ta sanye da takalmi high hill hannun ta na hagu
saɓe da riga baƙa irin ta lawyers,wanda take sanye da wani siririn agogon azurfa
wuyan ta sanye da siririyar sarƙar zinare,hannun ta na dama riƙe da jakar ta ƴar
ƙarama kalar ruwan madara da kuma key tana kuma rike da wayar ta wacce kuma kunnen
ta ke sanye da eye piece da alamu ma ya nuna waya take amsawa,sai dai yadda take
murmushi zai tabbatar maka da cewa wanda take wayar dashi mutum ne me matuƙar
mahimmaci a rayuwar ta.

"Baby,maganar ƙarshe da zanyi shine dole ka dawo gida a cikin satin nan idan ba
haka ba zaka sha mamaki na",ta ɗan yi shiru alamun na can ɓangaren magana yake yi.

Cikin damuwa tace; "Baby ba zan canza magana na fara gajiya da halin ka,kodan
kaga na damu da kai zan kira Daddyn ku Allah na faɗa mishi wannan halin naka,and
maganar ƙarshe shine ka biyo jirgi gobe ka dawo gida ko kuma ka ganni a England ɗin
na dai faɗa maka",bata jira cewar shi ba ta kashe wayar sannan ta kalli yaran nata
da suka zubo mata idanu tace;

"zan tafi wajen aiki fatan baku da wata matsala",ɗaya daga cikin wa'innan
samarin yace; "Mum,maganar canza mini motar fa,kinga......".

"Tameer,ya isa haka! Ina mun gama wannan maganar ka jira Daddyn ku nan da sati
biyu",ta faɗa,cikin sauri ya buɗe baki zai yi magana tace; ya isa haka! Sai na
dawo",daga haka ta fice.

Wanda ta kira da Tameer yayi ƙwafa yace; "wallahi na gaji da halin Mummy me yasa
bata damu da halin da muke ciki ba amma ta damu da wancan wawan?".

Ɗayan saurayin wanda suke kama sosai daka gansu ka san ƴan biyu ne yace; "Tameer
ka dinga ƙoƙarin ɓoye fushin ka mana,Abdul fa ɗan uwan mu ne".

Cikin fushi Tameer yace; "Abdul! Na tsani wannan yaron kamar yadda na tsani
mutuwa ta",wannan budurwar dake zaune tana danna waya tayi tsaki tace; "nifa Yaya
Tameer wallahi ina bayan ka kuma ko ni na tsane shi dan dai bani da yadda zan yi
dashi ne".

Ɗayar dake koyawa yaron nan karatu tace; "Kai Aunty Surayya ki dena faɗin haka
Yaya Abdul fa ɗan uwan ku ne ya kama ta ku dinga sassauta tsanar da kuka yi
mishi",cikin fushi Surayya tace"dallah rufe mana baki,keda Yaya Sameer ai naga
bakwa kishin kanku kuma wallahi ko ku canza ko kuma kuna gani zaku mutu babu yadda
zaku yi mu dai zamu san yadda zamu yi".

Sameer yayi murmushi yace; "Surayya Sumayya fa ta fiki gaskiya,koma meye dai ɗan
uwan mu ne",Tameer ya juyo yace; "eh ɗan uwan mu ne amma kuma Mummy bata ɗaukar
hakan kana gani abinda ya faru da ace Abdul ne ya nemi ta canza mishi mota data
canza amma da yake ni ne sai dai na jira Daddy".

Sumayya tayi murmushi tace; "Yaya Tameer kaifa kana da kuɗin da zaka canza motar
ka me zai sa ka jira Mummy?",suka yi shiru duka,ita kuma ta kalli yaron tace;
"Fahad tashi muje kayi wanka",tana faɗin haka ta ja hannun shi suka shige ɗaki ta
bar su nan tsaye.

Surayya na ganin haka tayi ƙwafa ta wuce itama ta barsu,Tameer shima yayi tsaki
yace; "Sameer duk kuɗi na ya kama ta ace tunda na tambaya Mummy ta siya mini,kada
ka ɗauka iya kaina hakan zai tsaya wata rana zai tsallako kanka",daga haka shima ya
wuce ya bar Sameer a tsaye.

Sameer yayi ƙwafa yace; "mahaukata waye yace musu ana fito da ƙiyayya oho! Abdul
ka ƙwace mana komai taya kuwa zan so ka???".

#LIKE
#SHARE
#COMMENT

* Babyn Abdul,Maman Meenal,Elham da kuma Farouk*

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖3-4📖📖

Nusram ke zaune bakin famfo tana wanke-wanke, tana ta sauri domin tayi ta gama
gudun kada tayi lattin zuwa makaranta, Mama Jummai ta fito da tarkacen kayan
kwanukan ta ta zube gaban Nusram tace, "gashi nan tunda ba za'a fito da miji ayi
aure ba sai a zauna ayi mana bauta", Nusram ta saukar da kanta ƙasa kawai tana me
jin zafin magan-ganun na Mama Jummai.

Nan ta zube su ta juya tana mita; "to dama meye amfanin ku a gidan yara tun
nonowa suna kirji har sun faɗi amma kun ƙi ku fitar da mazaje,ai wallahi dani daku
ne a gidan ga uwar can tsohuwar munafika kullum tana ɗaki a kile kamar kayan wanki
Musa a baki Fir'auna a zuci", Nusram ta ƙara kallon hanyar bayin inda ta tabbatar
da cewa Nusreen na jiyowa fatan ta dai ace bata jiyo duka ba,sai dai ta makaro
domin kuwa duka magan-ganun Mama Jumman a kunnen ta suke kuma Allah-Allah take ta
gama ta fito domin bata amsa.

Tana fitowa Nusram tayi sauri ta miƙe, idanun ta cike da hawaye tace; "Pls Rim
kada kice mata komai dan Allah", Nusreen ta galla ma ƙofar ɗakin Mama Jumman harara
sannan tayi ƙwafa ta wuce, Nusram kuwa ganin hakan yasa tayi ajiyar zuciya sannan
ta cigaba da wanke-wanken ta, Kan wani lokaci ta gama sannan ta kwashe nasu ta kai
ɗaki ta ɗauki na Mama Jumman ta kai mata itama ƙofar ɗaki sannan ta juye nata ruwan
ta shiga wanka.

Bata jima ba ta fito inda ta shiga ɗaki ta tarar da Ummi na zaune tanawa Kubra
tsifa yayin da Nusreen ke faman sheƙa kwalliyya, Nusram ta kalle ta tayi murmushi
kawai sannan itama ta hau shiryawa.

Atamfa ta saka me kalar pink da ash sai ratsin fari da baƙi kalar ta jikin
Nusreen ɗin sai dai banbancin shine ɗinkin domin kuwa Nusreen tata fitted gown ne
ita kuma Nusram tata me buɗewa ce daga ƙasa, bata tsaya kwalliyya ba kamar ƴar uwar
ta mai da hoda kawai ta shafa sai kwalli data zizara ta ɗauki hijab ta saka kalar
ash wanda ya kasance kalar uniform ɗin makarantar kenan ta tada sallah, haka itama
Nusreen ɗin sai da ta gama tata ƙyale-ƙyalen sannan tayi sallah suka fice cikin
sauri suna yiwa Ummi sallama akan sun tafi islamiyyar.

Ummi tayi musu addu'a da fatan nasara sannan ta ɗaga Kubra domin ta gama yi mata
tsifar saura wanke kan.

Suna fitowa suka iske yaran Mama Jumman Atika da Ameera sun dawo daga tallan
shinkafa da waken data ɗora musu, Nusreen ta kalle su tayi tsaki tace; "mutum bashi
da aiki sai yawon tallace-tallace wata rana garin jarabar son kuɗi a kwasowa mutum
abinda zai jefa shi a masifa", Mama Jumman ta fara balbalin masifa ita dai Nusram
taja hannun ta kawai suka fice.

Kan hanya ma sai faman masifa take ita dai Nusram bata kula ta ba har suka iso
bakin makarantar, ana ta taron latti amma da yake Nusreen ɗin akwai rigima haka ta
wuce cike da taƙama tana taku ɗai-ɗai.

Nusram kuwa da sauran ɗaliban suka tsaya suna kallon ta, Malam Abbas shima ya
bita da idanu da sauran malaman dake bakin wajen, ganin da gaske take yasa shi daka
mata tsawa yace; "Nusreen Abdullahi Dabai ki dawo nan", ta juyo cike da ƙasaita
tace; "sunan haka yake malamin addini babu kuskure", duka wa'inda ke wajen sai da
suka kwashe da dariya wanda hakan ya kuma tunzura Malam Abbas ɗin yayo kanta da
bulala.

Tsayawa tayi ƙyam tana kallon shi harya kawo kusa da ita kafin yaja dan kan shi
ya tsaya, tana ganin ya tsaya ta saki murmushin ƙasaita tace; "ya ka fasa ai da ka
zuba mini a jiki kawai", ta ƙarasa tana mishi wani kallo.

Duk abinda yake faruwa akan idanun shi kuma yana kallon meke faruwa ganin idan
beje ba za'a yi abinda be kamata ba yasa ya taho wajen da sauri.
"meke faruwa ne?", ya tambaya, Malam Abbas yace; "latti tayi amma tazo ta wuce
kamar zata shiga ɗakin su", Malam Saleem yayi murmushi sannan yace; "Malam Abbas ai
kun riga da kun san halin wannan domin samun maslaha ka ƙyaleta kawai ta wuce",
haka dole yasa Malam Abbas ya barta ta wuce ya koma kan sauran yana jibgar su, koda
yazo kan Nusram sai da ya sauke haushin Nusreen akan ta tsaf sannan ya ƙyaleta gaba
ɗaya ya farfasa mata hannu, haka ta tafi aji tana kuka.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

Ta ɗagawa ƴar matashiyar data kawo mata Coffee ɗin hannu tana me cigaba da amsa
wayar ta hankali kwance.

"Baby ban san wannan ƙorafe-ƙorafe,dole fa ka dawo gida gobe na ƙara jadadda
maka, shiru tayi alamun magana yake har zuwa lokaci me tsayi kafin tayi murmushi
tace; "yauwa ko kaifa", ra ƙara sakin murmushi tana fadin; "Mummy loves you more,
bye", daga haka ta ƙatse wayar.

Cikin isa da ƙasaita ta hau kiran; "Aziza! Aziza!!", kan tayi kira na uku ta iso
gare ta, cikin isa da bada umarni tace; "kije ki faɗawa sauran ma'aikatan gidan kan
cewa Baby yana kan hanya gobe sannan ki tura Salma ta buɗe ɓangaren shi gani nan
zuwa na gyara mishi", jiki yana rawa Aziza ta amsa da"to", haka ta tafi cikin murna
da farin ciki domin kuwa sun san cewa hanyar ƙofar samun su ta kusa dan akwaishi da
kyauta sannan ko ita kanta uwargidan tasu bataso yin abu ba indai kayi kamun ƙafa
dashi tofa aikin ya gama cika,koda ta sanar da ma'aikatan gidan nan suka hau murna
suna sam barka da dawowar tashi.

Babu jimawa ta miƙe ƙafafunta sanye da slippers ta fice daga ɗakin nata zuwa
part ɗin shi, a falon ƙasa ta tarar dasu kamar koda yaushe, Surayya ta danna waya,
Sumayya kuma littafi ke hannun ta da alamu karatu take, Sameer kuma yana operating
system ne yayin da Tameer ke kwance idanun shi a lumshe kamar me barci, duka suka
yi mata sannu da fitowa ta ɗaga musu hannu sannan ta kalli Surayya tace; "kije kan
drower a ɗaki na zaki ga box saƙon sarƙar ki ne da kika ce".

Cikin farinciki ta hau godiya, kallonta ta mayar kan Tameer kamar zata ce wani
abu sai kuma ta fasa ta kalli Sumayya tace; "ina Auta na?", tayi murmushi tace;
"Mummy Auta yayi barci", ta nufi hanyar fita kan tace; "kije ki tashe shi yamma
tayi", ta amsa da to sannan tace; "Mummy ina zaki je?", sai da ta juyo ta kalle ta
sannan tace; "Baby zai dawo gobe zanje na gyara mishi part ɗin shi ne".

Sumayya tayi tsallen murna sannan tace; "Mummy nazo na raka ki", tayi gaba tana
faɗin; "ki fara tashin Fahad daga barci tukunna", Sumayya cikin murna tayi hanyar
ɗaki domin tashin Fahad ɗin.

Tameer ya buɗe idanu sannan yaja tsaki yana faɗin; "aikin banza kawai", Sameer
ya kalle shi ya girgiza kai kan ya cigaba da abinda yake yi.

Babu jimawa Sumayya ta tashi Fahad, sai da tasa Salma tayi mishi wanka sannan
ta fito cikin gaggawa, tana zuwa falon Tameer yace; "banza mara tausayin kanta", ko
kallon shi bata yi ba ta wuce.

A buɗe ta tarar da part ɗin da kuma alamu Mummy ta riga da ta fara aikin ta,
aikuwa kamar yadda ta zata tana shiga ta tarar falon ƙyal-ƙyal ko'ina tsaf-tsaf,
tayi hanyar bedroom ɗin, Mummy na tsaye tana gyara kan madubi ta ɗago ta kalle ta,
Sumayya tayi murmushi tace; "Mummy na gama", ta ɗaga mata kai tana me cigaba da
abinda take yi.

Sumayya na tsaye tana kallo har ta gama gyaran bedroom ɗin ta canza bedsheet
saman gadon sannan ta shiga bathroom ta wanke tass, Sumayya tayi murmushi tana me
jinjina soyayyar dake tsakanin ɗa da uwar, ta san cewa idan zata kwana tana
tambayar ta akan ta bari ta taya ta ba zata bari ba shiyasa taja baki tayi gum.

Tana gama wankewa ta ɗauko turare ta zuba a burner ta kunna sannan ta hau fesa
Room freshner sai da ta tabbatar da ko'ina ya ɗauki ƙamshi sannan ta fito daga
bedroom ɗin Sumayya tana bin bayan ta.

Ɗakin dake kallon wannan ta shiga, shima bedroom ne sai dai a maimakon gado sai
aka saka ƙatuwar katifa babu wasu tarkace a nan, wardrobe ne sai dressing mirror
shikenan, sai dai jikin bangon dake ɗauke da manya-manyan hotunan ƴan ƙwallo.

Shima ta gyara shi tsaf ta saka mishi turare ta wanke bayin sannan ta rufo ɗakin
ta fito Sumayya ma na bayan ta, haka ta rufe part ɗin ta fice.

Suna isowa parking space ta ɗaga kai ta kalli motocin dake wajen, "Bala!
Bala!!", cikin sauri ya ƙaraso, ta dube shi tace; "banga ka gyara motocin da za'a
ɗauko Baby bane".

Ya shafa kanshi yace; "Hajiya walllahi Tameer ne yace na wanke tashi na bar
wa'inn..", kan ya ƙarasa ta dakatar dashi ta hanyar cewa; "dakata mini, Bala ban
san cewa Tameer ka fara yiwa aiki ba sai yau", jiki na rawa ya fara bata haƙuri,
bata kalle shi ba tace; "kasan bana iya haƙuri da abinda ya shafi Baby a gidan nan
amma kake neman ka maidani abokiyar wasan ka".

"Hajiya dan Allah kiyi haƙuri", ta girgiza kai tace; "magana ta ƙare kaje wajen
Aziza ta baka dubu hamsin ka kama gaban ka bana buƙatar ƙara ganin ka", jiki na
rawa ya tsuguna yana bata haƙuri haka tayi wucewar ta.

Nan sauran ƴan aikin suka fara bashi haƙuri shi kuma yana kuka, yaje ya tattara
kayan shi sannan yaje wajen Aziza ya amshi kuɗin.

Aziza tace; "ka bari gobe idan ƙaramin oga ya dawo sai ka dawo ka roƙe shi", ya
yarda da shawarar ta sannan yayi godiya ya tafi.

"waye nake magana yake canza mini ita a gidan nan", ta tambaya bayan ta shigo ta
sami Tameer da Surayya a zaune, ganin yadda fuskar ta ke ɗaure yasa duka suka sauke
kan su ƙasa.

"ina tambayar ku, wane ishashshe ne wannan?", ta faɗa cikin daka tsawa, a
sanyaye duka suka hau bata haƙuri, ta ɗaga hannu ta nuna su tace; "har yanzu dai
nice Brr Farida suna na be canza ba, kuma nima ban canza ba", tana faɗin haka ta
kalli Tameer tace; "kaje ka cewa Ali ya mayi aikin Bala a fito da motocin da za'a
je ɗauko Baby a wanke su", tana faɗin haka ta wuce sama ta barsu cike da baƙin
ciki.

Tameer na ganin ta wuce ya buga tsaki cikin ƙuluwa yace; "wallahi idan na cigaba
da zama a gidan nan wata rana mutuwa zan yi", Surayya tace; "to Yaya ka fito da
mata mana kayi aure", yace; "ai dole ma idan ba haka ba baƙin ciki sai ya kashe
ni", haka dole ya tafi inda ta aike shi cike da jin haushin wannan so da Mummy ke
yiwa ƙanin shi.

Haka ya basu umarni daga nan ya wuce part ɗin su dan haushin halin Mummy yake
ji, gashi basu da yadda zata yi, ita komai Baby.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸
🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸
🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

Koda aka taso su daga makarantar a hanya Nusram keta bata baki akan abinda take yi,
"haba Rim kinga fa rashin jin magana da kuma yiwa babba rashin kunya baya haifar da
komai face ci baya, dan Allah ki dena".

Nusreen tace; "Allah ko! Yau kuma wa'azi kika koma, to bari kiji ni ba zan iya
rayuwa kalar taki ba ina kallo ana cuta ta nayi shiru ko kuma na koma ina kuka
wannan ba zai taɓa yiwuwa ba".

Nusram tace; "ai na sani amma dan Allah ki rage tsiwar nan ko zamu sami wanda
zai kalle mu, muma mu wuce gori", Nusreen ta kwashe da dariya tace; "kice ga inda
maganar ki ta dosa ta ki sani wannan kuma daga Allah ne ba daga ni bane kuma ki
faɗa mini shekarar mu nawa ne just 24yrs da ƙuruciyar mu fa".

Nusram tace; "Nusreen ki duba fa kiga ƙannen mu nawa aka yiwa aure, uku fa
sannan ki duba ƴaƴan Auntyn Tudu, itama ta aurar da yara biyu Safeena da Halima
kuma duka mun girme su, dan Allah ki maida hankali".

Nusreen ta kalli ƴar uwar ta na wani lokaci sannan tace; "Ram ba zan taɓa yin
aure na barki ba kema kin sani kuma alƙwari ne na ɗauka kan cewa sai kin sami naki
mijin sannan nima zan tsayar beside ma duk wa'inda ke zuwa waje na babu wanda yayi
mini".

"Rim ki manta da ni kiyi auren ki wataƙila tawa ƙaddarar kenan, bazan taɓa samin
miji ba ke kuwa fa ko jiya fa wani yazo kan yana son ki kika ƙi fita".

Nusreen ta taɓe baki tace; "ai sai kiyi tayi wallahi ba zan yi aure na barki a
wajen wannan matar mara tausayi ba ta dinga muzguna miki a hakan ma wai duk da tana
tsoro na ya aka cika ina ga na tafi na barki, kuma maganar wai ke taki ƙaddarar
kenan ashe kema zaki iya yanke ƙauna daga rahamar Ubangiji?, to bari kiji Allah
yana sane dake kuma na san addu'ar da mahaifiyar mu take mana ba zata taɓa faɗuwa
ƙasa banz.....", bata ƙarasa ba saboda ruwa da wata mota ta shiga ya fallatso mata
duk ya ɓata mata jiki.

Nusram na ganin yadda ta haɗe rai yasa tayi saurin riƙo ta tace; "dan Allah Rim
mu tafi kada kice komai", Nusreen ta ɓalla mata harara tana kallon motar da ta rage
gudu a hankali kuma motar ta fara dawowa baya.

Nusreen na ganin motar tayi parking ta fincike hannun ta daga na ƴar uwar ta
tayi kan motar cikin sauri kuma ɗauke da fushi.

Tana zuwa yana fitowa ta galla mishi harara kafin tace; "kai ɗin waye da har
zaka zubawa mutum ruwa kuma ka cigaba da tafiya, kodan kana taƙama da cewa mahaifin
ka nada kuɗi shikenan dama haka halin ku yake kallon talaka kuke a banza a wofi to
wallahi ni ba irin sauran bace banda haƙuri mutum nayi mini zan yi mishi, mutum ya
hayo titi kamar na ubanshi to kaji ka sani ba ɗauka zanyi", ya tsaya yana kallon ta
cike da mamaki.

Ta ɗaga hannu ta nuna kanta tace; "kalle ni da kyau na wuce raini kuma idan
taƙamar ka kuɗi ni kuma ina da Allah domin shiya tsaya mini......", kafin ta ƙarasa
abinda zata faɗa aka buɗe ɗayar ƙofar aka fito.

Wata dattijuwar mata ce fara sosai, tana ɗingisa ƙafa ta ƙaraso gaban ta, tayi
murmushi sannan tace; "Ƴan mata kiyi haƙuri bada sani bane, sauri yake ya kaini
airport domin zan tafi syria inda za'a mini aikin ƙafa da take damuna".

Nusreen ta kalle shi, shima dai itan yake kallo yana murmushi ta galla mishi
harara tace; "Allah ya taimake ka da wallahi saina ɗauke ka da mari", tana gama
faɗin haka ta juya ta bar wajen.

Nusram ta saukar da kai ƙasa tace; "dan Allah kuyi haƙuri kuna sauri mun tsayar
daku", ta maida kallon ta kan shi wanda shima ita yake kallo cike da mamakin kamar
ta da waccen har muryar su sai dai ita wannan muryar ta sanyi-sanyi take; "kayi
haƙuri ba haka take ba ranta ne ya ɓaci, Mama Allah ya baki lafiya yasa ayi aikin a
sa'a", tana gama faɗin haka ta juya tabi bayan ƴar uwar ta.

Duka suka bita da kallo wanda kowa da irin nashi ma'anar, shi yana mata kallon
girmamawa yayin da mahaifiyar shi ke mata kallon sha'awa da birgewa tana fatan
inama ƴar ta ce.

Ta maida kallon ta kan ɗan nata sannan tace; "Shureim muje ko", yayi ajiyar
zuciya sannan ya shiga motar ya jata suka tafi.

Nusram duk iya saurin data yi bata tarar da ƴar uwar tata ba har ta isa gida,
tun kan ta shiga gidan ta jiyo muryar ta tana faɗin; "wallahi mutum yayi mini na
mishi dukan mutuwa".

Tana ƙarasa shiga, Mama Jummai na fitowa tana faɗin; "to shegiya fitsararriya
sai kizo ki dake tan a gaba na, anƙi aure anzo an ishi ƴaƴan masu gida", Nusreen
tace; "to mu ai sai a sheganta mu, yadda yake gidan uban su haka yake gidan uban
mu, maganar aure kuma naga wata ma tsabar daɗewa sai da ta shekara talatin da biyar
sannan tayi auren fari, aka kuma tafi da me daka gidan mijin gwara mu ma muna da
kyan jiki, mtsew abu kamar guzuma", saukar mari taji wanda ya hanata ƙarasawa ta
juyo ta kalli Ummi, Ummi kuwa cikin ɓacin rai tace; "wuce ɗaki", babu musu ta wuce
tana faɗin; "wallahi sai na dake ta sai dai ta dena fita".

Mama jummai kuwa sanin da ita Nusreen take yasa tana huci tana faɗin; "bari uban
naki ya dawo sai na tambaye shi idan shi ya zauna ya kitsa miki, shegiyar ƴar
tasha".

Nusram ta fara zubar da hawaye tana me baƙin ciki da halin da gidan nasu yake,
Allah yayi ta da rauni shiyasa hayaniya koya take bata iya jure ta.

Ummi ta kallo ta cikin tausayawa kasancewar ta mahaifiya gare su ta san halin su


ya bambamta duk da kamar da suke, tace; "Nusram jeki cire hijab ɗin mana kizo ki
share gidan", ta amsa da to sannan ta wuce.

Tana shiga ɗakin ta tarar da Nusreen har ta fara gyara ɗakin, ta wuce ta ta
ajiye hijab ɗin sannan ta fito ta ɗauki tsintsiya ta share gidan tas.

Ummi kuwa kan lokacin ta gama girki dan haka ta tattara kayan da Ummin tayi
amfani dashi ta wanke sannan ta wuce tayi alwala ta shiga ɗakin nasu domin yin
sallah.

Koda suka idar nan suka zauna kowa yana nashi karatun har aka yi kiran isha'i
sannan suka tashi suka yi sallar.

Sun fara cin abinci kenan suka jiyo Mama Jummai na kasawa yaranta tallan kunun
aya da kuma ƙwai, Nusram cike da baƙin cikin halin Mama Jumman ta kauda kai kawai.

Nusreen kuwa bata ce komai ba banda zama data gyarawa Kubra suna cigaba da cin
abincin su, babu jimawa Baban nasu yayi sallama ya shiga, gaban Nusram ya yanke ya
faɗi.

Suna gama cin abincin Nusreen ta kwashe kwanukan ta gyara wajen sannan ta koma
kusa da ƴar uwar ta suka yi zaman fira.

Babu zato babu tsammani ya banko ɗakin ya shigo, yana hango su yayi kan su ya
hau dukan su, yana faɗin; "marasa mutunci kawai".
Nusreen ta miƙe domin guduwa yasa ƙafa ya taɗiyo ta ta faɗi a wajen yayi kanta
yana duka, daman ita yake so ya daka rashin gane wacece a ciki yasa ya haɗa su duka
amma da ƙoƙarin gudun da tayi ya gano itace wacce yake nema dan haka ya rabu da
Nusram yayi kanta.

Nusram kuwa tana kuka tana bashi haƙuri amma yaƙi haƙura, Ummi kuwa tunda ta
saukar da kanta ƙasa bata kuma ɗagowa ta kalle shi ba, ganin hakan yasa Nusram
faɗawa jikin ƴar uwar tata tana tare mata dukan.

Haka ya haɗa yayi musu duka sannan ya ƙyale su ya fice, ganin fitar shi yasa
Nusram janye jikin ta cikin wahala domin ita fatar ta bata jure duka ko yaya yake,
ita koda wanki ne ya cika yawa sai ya fasa mata hannu balle duka gashi kuma dama
ɗazu tasha na Malam Abbas yanzu kuma tasha na Yayan su Isa.

Da ƙyar itama Nusreen ɗin ta miƙe ta zauna tana dafe da gefen cikin ta inda
tasha ƙasa ɗazu, sai dai abin baƙin ciki kan su gama jimamin wannan duka suka jiyo
hargagin mahaifin nasu ya nufo ɗakin nasu.

Nusreen haka taja jiki ta gudu ɗaki yayin da baƙin ciki ya hana Nusram tashi
daga wajen, yana shigowa ya fara zuba mata wayar wutan dake hannun shi, tun tana
zaune har sai da ta kwanta a wajen haka ya bita ya cigaba da duka sai da ya
tabbatar da ko yatsa ba zata iya ɗagawa sannan ya ƙyale ta.

"kuma wallahi ko ku fito da mijin aure ko nayi ta azabtar daku a cikin gidan nan
shegu masu baƙin jini irin na mahaifiyar su", ya cillar da ragowar wayar yayi waje
yana bambami.

Sai da suka dena jiyo hargagin shi sannan Nusreen ta fito da sauri tazo ta kama
ƴar uwar ta, Ummi kuwa tsabar ɓacin rai numfashin ta har sarkewa yake yi.

Duk yaji mata ciwo a fuska da jikin ta, Nusreen tace; "Ram ki dinga guduwar wa
dukan Baba dana Yaya Isa", yadda tayi da fuska ya tabbatarwa da Nusreen cewa ranta
ya ɓace.

Ummi ta miƙe ta juye mata ruwan data ɗora saman murhu bayan ta sauke abinci,
kaɗan ta sirka mata sannan tace; "Nusreen kai mata bayi, ke kuma ki tashi ki cire
kayan kije ki gaggasa jikin ki", babu musu duka suka miƙe suka hau aikata abinda
Ummi ta umarce su.

Mama Jummai tayi shewa tace; "ai dama ni na wuce tunanin mutum gobe ma ki kuma
turo su suyi mini rashin kunya ni kuma na kuma sa su gashi ahayye sai ni Jummala ƴa
ga Habu sarkin wanzamai", babu wanda ya kula ta har tayi ta gama.

Nusram kuwa taji daɗin jikin ta data gasa tana fitowa Nusreen ta shiga tayi nata
wankan.

Koda Nusram ta shigo ɗaki Ummi ta miƙo mata mansileta tace; "amshi wannan ki
shafa", ta amsa ta shafa inda hannun ta ba zai kai ba Ummi ta taya ta ta shafa
sannan ta miƙo mata wata doguwar riga mara nauyi hannun vest gare ta tace ta saka
ta ansa ta saka sannan ta kwanta.

Nusreen ma koda tayi wanka kayan barci kawai ta saka riga da wando,rigar iya
gwiwa sai wando dogo tana gama shiryawa ta haye bayan ƴar uwar ta ta kwanta.

Ummi ta kalle su cike da tausayawa tana me tausayin su, gasu duka mata Allah ya
basu sai dai Allah ya bata ɗaya wacce ita ke ɗan ƙwato musu ƴancin, ta share
hawayen ta tace; "Allah kana kallon wannan zalunci".

*WACECE NUSRAM DA NUSREEN*.


#LIKE
#SHARE
#COMMENT

*babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖5-6📖📖

Malam Abdullahi haifaffen ƙauyen dabai ne, mahaifin shi tun yana ƙarami Allah
yayi mishi rasuwa sai mahaifiyar shi ta auri me garin Dabai.

Me garin Dabai kamar yadda yake tura ƴaƴan shi suyi karatu haka ya tura
Abdullahi shima Zaria domin yin karatun, da yake me ƙwazo ne ya samu ya gama
secondry yana dawowa me gari ya haɗa shi aure da Maimuna ƴar wazirin shi.
Sun zauna a garin dabai tsayin shekara ɗaya cikin so da kulawa daga nan sai ya
sami aikin messenger na wani company a kaduna hakan shine silar dawowar su Kaduna,
Tudun Nufawa

Anan Allah ya azurta su da yara guda biyu duka mata, shine aka saka musu Nusram
da Nusreen, Malam Abdullahi ƴaƴa maza yaso amma Allah be bashi ba haka dole ya
haƙura ya barwa Allah.

Anan inda suke suka haɗu da Hajiya Kaltume wacce ke zaune tare da mijin ta itama
sai dai su suna da rufin asiri babu laifi.

Kamar ƴan uwan juna haka suke ita da Maimuna, ita ta raini Nusram kasancewar
tafi Nusreen haƙuri tun suna ƙanana, babu ƙyashi ba komai duk abinda ta samu zata
basu.

Har su Nusram suka kai shekaru bakwai amma Maimuna bata kuma samin ciki ba
wannan fa ya soma kawo matsala a tsakanin zaman Abdullahi da kuma Maimuna.

Ita dai sai dai idan abin ya ishe ta tayi kukan ta godewa Allah, haka suke zaune
cikin rufin asiri.

Nusram yarinya ce data biyo halin mahaifiyar ta na haƙuri da rashin son tashin
hankali, yayin da Nusreen ta kasance me tsiwa da faɗa ga saurin fushi, sha yanzu
magana yanzu.

Haka rayuwar su take gangarawa har lokacin da Abdullahi ya samu aikin zama a
plaza wanda shine silar tashin su suka koma Hayin Rigasa domin can zai fi mishi
sauƙi.

Maimuna da Kaltume sun ji zafin rabuwa da juna sai dai basu da yadda zasu yi,
ita Kaltumen a lokacin tana da yara guda shida, Sulaiman shine babba sai Halima,mai
bi mata Safeena sai Sadiya, Musa sai ƙaramin su Adam.

Shi kanshi Sulaiman ɗin shekara ɗaya kacal ya bawa su Nusram yayin da sauran
ƙannen nashi duka su Nusram sun girme su da shekara biyu saboda shekara uku ke
tsakanin ƴaƴan Kaltumen.

Anan wajen aiki anan Abdullahi ya haɗu da Jamila wacce ake kira da Jummai, ta
kan kawo abinci ɗan gaban wajen kaɗan inda su kuma ƙananan ma'aikata su kan fita su
siya.

Nan soyayya ta ƙullu a tsakanin su, har ta kaisu ga yin aure, Jummai macece da
take ganin ta kai ta isa wacce taƙi aure da wuri tana ganin ai yawancin masu
jinkirin nan sun fi samun mazaje masu kuɗi, sai da ta shekara ashirin da takwas
sannan ta fara neman ya zata yi ta auru, nan fa mazaje suka ce basu san wannan ba.

Ana haka wani yaro wanda ba zai wuce shekara ashirin da biyar ba ya fito a kan
yana son ta, nan fa ta hau tsalle tana murna ita da mahaifiyar ta Iya Nafi, ganin
su zaman alkhairi ne.

Yayan ta Adamu ya kira ta yayi mata faɗa ya kuma yiwa yaron tatas domin ya san
yaron zai yi wuya ya aure ta, aikuwa ta miƙe ta ci mishi mutunci ita da mahaifiyar
ta ganin haka sai kowa ya saka musu idanu.

Aikuwa ta kira yaro suka cigaba da soyewa kan ta ankara ya ɗirka mata ciki ya
gudu, koda suka farga sun ji takaici da haushi yayin da sauran ƴan uba suka shiga
farin ciki da murna.
Babu abinda ba'a ɗurawa cikin ba amma da yake Allah ya raya kayan shi babu
abinda ya sami cikin wannan ya ƙara ɗaga hankalin su, suna ji suna gani ta haifi
yaron nata aka saka mishi suna Isa.

Daga nan mahaifiyar ta ta cigaba da rainon yaron inda ita kuma ta cigaba da
ɗaukar tallar duk da ranta baya so tana ganin ta wuce talla haka mahaifiyarta ta
lallaɓa ta domin kuwa idan tayi a gida babu me zuwa ya siya sai dai a barta dashi.

Lokacin da Abdullahi ya nuna yana son ta, sunyi matuƙar farin ciki da hakan, jin
tsoron kada ya fasa idan yaji tana ɗa a waje yasa suka je aka rufe bakin shi ruf.

Lokacin da labarin auren yaje kunnen Maimuna bata wani tada hankalin ta ba domin
kuwa babu rashin ci ko rashin sha, ƴaƴan ta suna zuwa makaranta dan suna primary
five islamiyya ma sukan je kuma yana biya dai-dai gwargwado.

Ana auro Jummai komai ya fara taɓarɓarewa, amma duk da haka Maimuna ta cigaba da
zaman haƙuri da Abdullahi.

Haka ta ɗauko ɗan shegen ta tazo dashi kuma Mal Abdullahi ya nuna yafi son shi
sama da ƴaƴan daya haifa, tun yana ƙarami dan ya girmi su Nusram da shekara huɗu
suka taso da ƙiyayyar juna, haka Jummai zata saka yayi musu dukan tsiya amma duk da
hakan sai Nusreen ta san yadda tayi itama ta rama.

Sai da Jummai ta shekara guda sannan ta sami ciki, murna wajen Mal Abdullahi
ba'a magana inda yake ganin zai sami ɗa namiji ta ɓangaren ta wannan ya bata
lasisin shuka rashin mutuncin ta yadda take so.

Bayan wata tara sai gashi ta santalo ƴar ta mace aka saka mata Habiba, wannan
shine abinda yaso ya kawo matsala tsakanin su sai dai da yake da asiri hakan be
wani tasiri ba.

Kafin Habiba ta cika shekara ɗaya Jummai ta sake samun wani cikin nan fa sabuwar
murna ta tashi, a lokacin kuma Nusram suka gama primary suka shiga aji ɗaya a
secondry yayin da Isa ke aji uku a secondry.

Nan ma ta sake haifo mace inda murnar Malam Abdullahi ta koma ciki, ranar suna
aka saka mata suna Sahura, sai da Sahura ta shekara Uku sannan ta sami wani cikin
ta haifi mace aka saka mata Sakeena, to daga nan fa sai haihuwar ta ɗan tsaya mata.

Bata kuma samun ciki ba sai da su Nusram suka shiga aji huɗu a secondry shi kuma
Isa yana aji shida a secondry sannan ta kuma samun ciki ta haifi ƴar ta mace aka
saka mata suna Atika bata kuma cika shekara ba ta sami wata ƴar inda taci sunan
mahaifiyar shi Kareema ake ce mata Ameera daga nan bata kuma samin wani cikin ba.

Nusram kuwa suna aji na shida a Secondry sannan maman su ta sami ciki, babu
kunya ba tsoron Allah Malam Abdullahi ya fara murna akan zai sami ɗa namiji, nan
kuma bakin Jummai ya mutu.

Su dai suka zubawa ikon Allah idanu, babu inda Jummai bata je ba don asiri amma
kuma ciki yaƙi zubewa hakan ne ya ƙara tada hankalin ta.

Ciki na shiga watan haihuwa ta haifi ƴar ta mace, ranar Jummai har party sai da
ta haɗa a gidan, su Habiba suna gama jss 3 ta cire su daga makaranta ta fara ɗora
musu talla.

Haka Malam Abdullahi na kallo amma bashi da yadda zai yi da ita dole ya ƙyale
ta, Kubra nada shekara ɗaya aka fara gane cewa aljanu sun taɓa ta wannan dalilin
yasa Malam Abdullahi ya dena kwana a ɗakin Maimunar wai tsoron ta yake ji.
Ummi kuwa magani ta shiga nemawa ƴar ta, ta manta dashi, Nusreen kuwa ta buga
tsalle tace Mama Jummai ce tayi mata asiri, sai da Ummi ta tsawatar mata sannan ta
bari.

Tun daga lokacin da faɗa ya taɓa haɗa su da Nusreen ta kama ta zata dake ta
Nusram taji haushi ta shiga.

Dama ance faɗan me haƙuri be iya ba, haka ta jibgi Mama Jummai da itace a kai
dalilin kuwa Habiba ta fara tsayawa da saurayi sai takewa Nusreen ɗin habaici shine
ita kuma ta gaza haƙuri har ta tsinkawa Habibar mari a lokacin Mama Jumman bata ce
komai ba.

Sai da ta bari Nusreen ta saka guga a rijiya taje ta rufe ta da duka, Ummi tana
zaune tana kallo bata ce komai ba, Nusram kuma na riƙe da Kubra tana shafa mata
maganin da Auntyn Tudu (Hajiya Kaltume) ta amso ta kawo mata.

Wani haushi da zuciya ya taso mata, dama Maman ta ɗora abincin siyarwa tana
dafawa ta saki ta tafi duka, wajen murhun ta nufa tana zuwa ta ɗauki itace ɗaya
tayi kan Maman.

Tasa hannu ta janyo ta ta haɗa da bango, ta sa itacen ta dinga rafka mata a kai
tun tana faɗin ta sake ta har ta gaji ta fara ihu, da kan ta Nusram ɗin ta sake ta
Ummi bata ce komai ba.

Tunda ta sake ta, Maman tayi ɗaki bata fito ba a ranar girkin ma Habiba da
Sahura suka ƙarasa suma a tsorace suke da Nusram ɗin domin sun san ba halin ta
bane.

Baban na dawo ta faɗa mishi aikuwa har ɗaki ya bisu yayi musu shegen duka, wanda
har ya jiwa Nusram ɗin ciwo a goshi wannan tabon shike bambace Nusram ɗin da
Nusreen ɗin dan be ɓace ba sai dai ya disashe yadda sai ka ƙura idanu zaka ganshi.

Haka da Isa ya dawo ta sake faɗa mishi, shima ya kuma yi musu duka amma tun daga
wannan lokacin ta tsorata bata kuma kai hannu ta daki Nusreen ɗin ba duk iya abinda
zata yi mata in dai ta san Nusram ɗin tana nan sai dai suyi ta fatar baki, sai dai
cewa da tayi tunda haka ne su da aure sai dai suga anayi.

Wannan be dame su ba domin sun san ta Allah ba tata ba, sun gama karatun su na
secondry amma babu wanda ya taɓa zuwa sallama dasu.

Nan fa Baban ya kuma takura su da masifa ga Maman tana nata habaicin, Ana haka
Habiba da Atika suka sami nasu tsayayyun nan fa gori da masifa ya sake tashi.

Babu me tanka musu sai Nusreen, haka abu yayi ta tafiya har aka zo aka yi biki
ƴan dabai sun zo nan suka dinga shan surutu dan ma Nusreen ɗin tana mai da musu.

Bayan biki ne Auntyn Tudu ta bawa Ummi shawara maimakon zaman da zasu yi haka me
zai hana su cigaba da karatu wannan dalilin yasa suka fara fafutukar shiga jami'a.

Lokacin da labari ya isa kunnen Baba cewa yayi ba saka hannun shi haka Ummin kan
yi wankau da sana'ar ƙulle-ƙulle domin samun na rufin asiri.

Daga haka ma wata rana yace; "shifa ya gaji da ciyar da ƙatti dan haka zai dena
bata kuɗin cefane", bata ce komai ba haka taje Dabai tasa aka siyar da shanun da
take kiwo guda biyu.

Wanda wannan ne ya saka ta sami kuɗin dasu Nusram suka yi registration sauran
kuma ta siyo shinkafa da taliya,macaronic,siga,gishiri,magi wake da sauransu ta
fara siyarwa a gida.
Ita kuma dama Nusram ta iya kitso da lalle dashi suke samun rufin asiri, da
taimakon Abba( mijin Kaltume) suka sami addmission a nan KASU inda Nusram ke
karantar Business administration Nusreen kuma ke karantar Mass com.

Isa kuwa dama diploma yayi akan inter sci ya sami koyarwa a wata makaranta dake
kusa dasu nan yake gangara rayuwar shi.

Duk da makaranta hakan besa su Nusram ɗin zama haka ba sukan je wajen Auntyn
Tudu su amshi kayan ƙamshi, wato turaren tsinke dana wuta,humra,kwalakca, detol da
air freshner su shiga dashi makaranta su siyar.

Abban ya buɗewa Sulaiman plaza inda yake siyar da takalma kayan sawa da sauran
su wannan yasa har Takalma da sarƙoƙi sukan amsa su shiga dashi makaranta su siyar.

Suna aji ɗaya a jami'a Sakeena ta sami miji itama aka yi mata aure, wannan karon
har duka sai da Baban yayi musu dan haushi.

Rufin asiri dai-dai gwargwado suna samu, Nusram kuwa idan ta sami lokaci har
amarya ta kan shirya kwaliyya da komai-komai tana yi sai dai ita ɗin ba ma'abociyar
yin kwalliyar bace a fuska sai dai takan yiwa wasu.

Nusreen dai ita tafi son karatun sama da sana'ar hannu wannan dalilin yasa bata
cika maida hankali akan komai ba sai dai ta kan taya Nusram ɗin wajen kwalliya.

Wannan shine taƙaitaccen labarin su inda yanzu suke da shekara Ashirin da huɗu a
duniya kuma har lokacin basu da tsayayyen saurayi gwara ma Nusreen ta kan samu sai
dai tace bata so sai lokacin da ƴar uwar ta ta samu nata mijin.

*CIGABAN LABARI*.

Sai da Nusram tayi jinya na kwana uku sannan ta warke inda Allah ya taimake ta
ƙarshen mako ne babu makaranta, Nusreen kuwa haushi ta dinga ji kamar me gashi Ummi
ta hanata magana washe gari.

Yau litinin zasu shiga makaranta da wuri hakan yasa suka tashi suka fara aikace-
aikace, sai da suka yi wanka suka shirya Nusram tayi wanke-wanke ta share gidan
tsaf, Nusreen kuwa ta ɗora musu abin kari, kunu da dankali soyayye.

Nusreen ta fara shiga tayi wanka sannan itama Nusram ta shiga, kamar kullum sai
da Nusreen ta fante fuskar ta ita kuwa Nusram bata wani tsananta ba, wani material
ligaht blue da ɗigon fari da pink a jiki suka saka, hijab kalar light blue suka
saka haka takalmin su.

Shaf-shaf suka karya sannan suka kwashi littattafan su domin tafiya makaranta,
Ummi ta miƙo musu ɗari biyar tace; "gashi Allah ya kiyaye hanya", suka amsa da
ameen sannan suka fito.

Mama Jummai na gaban murhu tana kwashe koko cikin ƙatuwar roba gefen ta Atika ce
ke ɗauraye robobin zuba kokon, Ameera kuma na ƙoƙarin fifita wutar da samanta aka
ɗora kaskon suya da mai a ciki wanda hakan ke nuni da cewa na suya ne.

Nusreen ta taɓe baki sannan tace; "ayi dai mu gani aikin banza", Nusram ta balla
mata harara sannan tace; "ina kwana Mama?", haɗiye amsar da tayi niyar bawa Nusreen
tayi sannan ta amsa gaisuwar Nusram ɗin shima a ɗan ɗage.

Nusram taja hannun Nusreen ɗin suka fice yayin da Mama take cewa; "an tafi yawon
ta zubar ɗin ne", suna daf da shiga zauren gidan Nusreen ta juyo tace; "gwara mu
fita muke muna yi wasu kuwa har zauren gidan uban su ake biyo su ana dannewa", basu
jira me zata bada amsa ba domin kuwa Nusram jan hannun ta tayi suka fice kawai.

A ƙofar gida kan dakali suka sami Baba zaune gefen shi Isa ne, da alamu lissafi
suke yi domin ga kuɗi ne ajiye a saman dakalin, Baba na ganin su ya haɗe rai,
Nusram tace; "Baba ina kwana?", sai da ya ɗan ja tsaki sannan ya amsa da lafiya, ta
juya wajen Isa tace; "ina kwana Yaya isa?", shi kuwa juyar da kai kawai yayi yana
wullawa Nusreen harara.

Nusreen ta taɓe baki sannan tace; "Allah ya ƙara wai ke uwar biyayya ni Uwar
mutum ma bata ishe ni kallo ba balle shi", daga Baba har Isan suka miƙe suka yo
kanta, cikin sauri tayi gaba abinta.

Cikin tsananin jin haushin abinda ta faɗa Isah ya juyo ya kife Nusram da mari,
Nusram ta saukar da kai ƙasa sannan tace; "kayi haƙuri Yaya Isa", tana faɗin haka
ta juya tabi bayan ƴar uwar ta.

Har ta kusa bakin titi sannan ta tarar da ita, Nusram tayi yaƙe tace; "kai Rim
gaki da tsokana ga tsoro, da haka kawai ne da sai na ta haɗaki da Allah akan ki
ɗago ƙafa amma da yake kin san kinyi tsokana ai gashi har kin kusa titi", Nusreen
tayi dariya tana faɗin; "ai wallahi ba zan tsaya aci zalina ba", haka suka ƙarasa
bakin titi suka tari mota suka wuce makaranta.

Koda suka sauka kowa faculty ɗin shi ya nufa, sai wajen ɗaya sannan Nusram ta
gama nata don haka tana fitowa ta fara bin wa'inda ta san ta basu kaya suka haɗa
mata kuɗaɗen ta sannan ta nufi faculty ɗin su Nusreen.

Taje ta same su suna daf da shiga wata lecture ɗin hakan yasa ta sami garden
gefen masallaci ta zauna ta ɗauki litattafan ta tana karantawa.

Basu suka gama ba sai uku, tunda suka fito take jiyo hayaniyar ta, cike da
mamakin halin ƴar uwar tata, ta ɗago tana kallon saman steps ɗin da suke tunda hall
ɗin a sama yake.

Bata bar surutun ba har suka sauko ƙasa, ita da wata budurwa ne suka bi bayan
wata mata wacce daga gani ita sukewa hayaniyar, Nusram ta tashi ta ƙarasa kusa dasu
sannan ta kalli ɗayar tace; "wallahi kema Yasmeen kina bani mamaki in banda haka
meye na biyewa wannan".

Wacce ta kira da Yasmeen ɗin ta juya idanu tace; "kai Ram ashe haka zaki ce kin
san me tayi ne takalmi da sarƙa ta amsa amma har yau bata biya ba kuma sati biyu
kenan".

Nusreen ta wullawa matar harara, Nusram ta juya ta kalli matar tace; "kiyi
haƙuri Maman Waleed wa'innan sai shiriyar Ubangiji kawai, kada ki damu duk lokacin
da kika samu sai ki bada", Nusreen tace; "Ram kin san......", cikin sauri Nusram ta
tari numfashin ta tace; "dakata ya isa haka ki dinga yiwa mutane uzuri mana haba".

Maman waleed ɗin ta kalle su ta watsar tace; "ai wallahi kun bani mamaki ashe
ƙoƙarin tona mini asiri kuke yi to Allah ya fiku, kuma idan banda ƴar uwar ki
wallahi da na bar ɗaukan kayan ki har abada, banza mara mutunci".

Nusreen abin nema ya samu dan haka tace; "tab ashe yau zan naɗawa mata duka nice
mara mutuncin", Nusram ta kai mata duka tace; "wai ke me yasa kina girma ne kina
hauka matar auren zaki daka??", Yasmeen tace; "koma wacece", Nusram tace; "Dalla ku
rufe mana baki ku wuce muje", sai da Nusreen ta doka mata harara sannan ta bi bayan
ƴar uwar ta yayin da Yasmeen itama ta bita.

Har suka fita bakin titi Nusram bata kula su ba, haka suka sami mota suka shiga,
a Anguwar Mu'azu suka sauke Yasmeen sannan suka wuce.
🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

Surayya ta fito cikin shiri, jikin ta sanye da doguwar riga ƴar kanti wacce
taji stones ƙanana masu kyau, rigar kalar light blue, ta ɗauki kwalliya sosai
sannan duka komai to match ta saka.

Cikin sauri ta sauko ƙasa, Mommy ta kalle ta sannan ta wulla mata harara tace;
"kin raina ni ko? tun ɗazu muke zaman jiran ki".

Surayya ta sunkuyar da kai ƙasa tace; "Mum kiyi haƙuri", Brr Farida ta ɗaga mata
hannu tace; "ya isa haka, ku wuce muje".

Sai da ta juya ta fara tafiya sannan na lura da kayan dake jikin ta, wata ƴar
ubansun shadda ce me tsadar gaske, kalar blue dark, kanta kuwa head ne wanda aka
mata ɗaurin steps gashi ya buɗe sosai wuyan ta kuwa murjani ta saka me tsada sosai,
ƙaramin space ne sanye a fuskar ɗan ƙarami, jikin shaddar kuwa aikin hannu ne wanda
ya fita sosai, mayafi ta yafa a kafaɗa kalar ruwan madara me haske haka takalmin
dake ƙafar ta, agogon azurfa ne ke sanye a hannun ta fuskar ta kuwa tasha kwalliya
ga wani annuri dake fita duk da irin girma da mulkin ta hakan be hana bayyanar
farin cikin ta ba, wayar dake hannun ta take cillawa a hankali kuma kaɗan-kaɗan,
cike take da nishaɗi da farin ciki.

Gefen ta kuwa, Fahad ne dake sanye da riga ja da wando blue jeans sai takalmi
cover shoe baƙi me kyau, fuskar shi sanye da ƙaton glass.

Daga gefen daman ta kuwa Tameer ne shima sanye yake da ƙananan kaya irin na
jikin Fahad ɗin wanda hakan ke nuna kenan anko suka yi, daga shi har Surayya fuskar
nan tasu babu wani fara'a.

Tafiya suka yi me tsayi kan su ƙaraso harabar gidan inda take cike da securities
maza da mata kowannen su sanye da suit, suna zuwa aka buɗe musu manya-manyan
motocin dake jere suka shiga kafin sauran securities ɗin suka shiga sauran motocin,
a haka motocin suka fara ficewa daga gidan.

*CANCANGI AIRLINE, KADUNA*, inda suka nufa kenan, koda suka isa wajen basu wani
sha wuya ba domin kuwa ana ganin su ake kauche musu daga hanya dan kowa ya san
familyn *NAGIMI* cikin Kaduna da kewaye balle kuma wannan da sun san ko wacece wato
*Brr Farida Mus'ab Alƙali* ɗaya daga cikin member na *ALƘALI'S FAMILY*.

Ƙasa-ƙasa Tameer yaja tsaki yana me kallon agogon dake ɗaure a hannun shi, kusan
da ragowar minti goma sha biyar kafin jirgin nasu yayi landing, cike da jin haushi
ya ɗago ya ƙara kallon wajen, kusan kowa idan yazo sai ya kalle su kasancewar burin
jama'a kenan ganin wannan ishashshen familyn domin kuwa family ne guda biyu masu ji
da kuɗi da izza da taƙama da mulki kowanne ba baya ba wajen iya mulki da kuma
ƙasaita sai ya kasance sunyi autayya sun haihu aikuwa abin kallo naga wannan
wa'inda jini biyu ya gauraye a jikin su.

Ƙara jan tsaki yayi sannan ya kuma kallon jama'ar dake wajen wanda suka zubo
musu idanu, maida kallon shi yayi kan Mummy wacce ke faman murna da farin ciki,
cike da jin haushi yace; "ji yadda take murna sai kace Dad ne zai dawo", Surayya ta
ɗago ta kalle shi fuska a ɗaure sannan ta nuna mishi hannun ta alamun lokaci.

Ya ɗan tura kan shi inda Mum ɗin take yana mata nuni da tayi mata magana, zaro
idanu tayi sannan ta girgiza kai, Mum ta juyo ta kalle ta hakan yasa dole suka ɗan
yi yaƙe gudun kada ta zargi komai.

Fuskar tace ta cika da farin ciki jin an fara sanarwa da isowar jirgin, ji take
kamar ta ruga da gudu taje ta taro shi, Surayya da Tameer kuwa banda taɓe baki babu
abinda suke yi.

Haka mutanen suka fara fitowa ɗai-ɗai da ɗai-ɗai, yayinda Brr Farida ta ƙara
zuba idanu tana jiran ganin ta ina ɗan lelen nata zai ɓullo.

#LIKE
#SHARE
#COMMENT

*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da farouk*.

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*


*Heart you so much*

*ban san wane irin haƙuri zan baku ba, Kuyi haƙuri insha Allahu zamu shiga cikin
novel ɗin sosai domin ina fatan komai ya dai-daita zaku dinga ganin shi kullum
insha Allahu atleast sau huɗu a sati ko biyar, nagode*

📖📖7-8📖📖

Saukar mari kake ji tasss, kasancewar inda suke kamar hall haka wajen yake, inda
aka ƙawata shi da jan labulaye, gashi kuma dare yayi sosai hakan yasa marin ya amsa
a ko'ina.

Cikin tsananin fushi da ɓacin rai yake kallon shi, shi kuwa ya saukar da kanshi
ƙasa, Appu ya nuna shi cikin karaɗi da gargaɗi yace; "ka kiyayi fushin Oregbu idan
ka bari ya fusata zai tsine maka ya kuma cire duk wata alfarma da yayi maka".

kanshi a ƙasa yace; "ina neman afuwar Oregbu sannan kuma fatan hucewar zuciyar ka
data Oregbu, nayi iya ƙoƙari na akan ganin na kawo shi nan amma wannan shegiyar
matar ta hana gaba ɗaya taƙi bamu dama, amma yanzu tunda zai dawo ina ganin wannan
wata damace a gare mu".

Cikin tsananin fushi Appu yace; "baka iya yi mishi komai ba yana can shine zaka
wani ce ya kusa dawowa idan ma ya dawo ba zaka iya ba", Tuge ya buɗe baki zai yi
magana Appu ya dakatar dashi sannan yace; "a fara gabatar da kwankwale".

Dole Tuge ya dakatar da maganar da yake so yayi ya koma baya, nan suka fara ɗaga
hannaye suna wasu irin magan-ganu marasa kan gado, can wani jibgege ya shigo hakan
yasa duka suka saukar da kan su ƙasa.

Nan ya fara zuba sassan jikin mutane cikin madaidaicin plate ɗin yana miƙa
musu, haka suka hau ci gwanin ban ƙyama da tashin zuciya, su kuwa babu ruwan su
daka gani sun riga da sun saba.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

Cikin ƙasaita yake takowa, saurayi ɗan shekara ashirin da biyar kenan me jini a
jika wanda yake da kyau da kwarjini ga kuma cikar zati da haiba.

Dogo ne yana da haske dai-dai gwargwado yana da zubin ƙarfafa, jikin shi sanye
da riga kalar Ash da wando jeans blue-black ƙafar shi yana sanye da takalmi cover
shoe me ruwan ash, fuskar shi me ɗan faɗi wacce take cike da haiba da kwarjini, me
ɗauke da ɗan mitsitsin bakin shi wanda ƙananan haƙoran sa farare tas ke ciki, ɗan
sajen shi irin na samarin yanzu wanda yasha gyara shiya ƙara ƙawata fuskar shi,
Hannun shi na dama ya ɗago wanda yake da hsske saman fatar cike da gargasa baƙa
wacce ta kwanta sai agogon Rolex dake maƙale a hannun ya shafa sumar kanshi wacce
take kwance luf baƙa wuluk daga gani tana samun kula ta musamman ya shaƙi iska yana
lumshe idanun shi wa'inda suke dama can kamar a rufen domin dogayen lashes da Allah
yayi mishi, murmushi ya saki wanda har sai da gefen kumatunshi dama da hagu suka
lotsa, haka ƙananan haƙoran shi farare suka bayyana.

Idanun shi ya buɗe a hankali sannan ya fara bin mutanen wajen da kallo a ƙoƙarin
shi na gano ina abar ƙaunar shi take, wani ƙayataccen murmushin ya kuma saki sannan
ya nufi inda take cikin sauri.

Brr Farida kuwa daman kamar ta kwasa da gudu ta tari ɗan lelen nata haka take
ji, cikin tsananin kewa da ƙaunar juna suka rungume juna suna masu tsananin murna.
Tameer da Surayya suka taɓe baki suna juyar da kai cike da baƙin ciki, wanda su
kuwa basu san ma suna yi ba.

Brr Farida ta ɗago ta shafa fuskar shi tace; "Welcome back, son", murmushi ya
saki sannan yayi peck ɗin ta a goshi.

Hannun su sarƙe da juna suka juyo kowa ya kalle su sai sun birge shi ganin yadda
kowanne ke ji da ƙasaita, Brr Farida ta kalli Tameer tace; "ka saka securities su
ɗauko kayan", daga haka ta juya suka tafi.

Tameer kuwa kamar ya ɗora hannu a kai ya ƙwala ihu haka yake ji, wannan wane
irin masifa ce, idan banda yana shakkar mahaifiyar tashi da ba zai taɓa aikata
abinda aka saka shi ba, cike da jin haushi ya fizgi akwatin da kuma ɗaya jakar
kamar su suka bashi haushi.

Kan ya ƙaraso har sun shiga mota hakan yasa ya ajiyewa securities kayan sannan
ya buɗe motar ya shiga, su kan su securities ɗin sun fahimci akwai abinda yake
damun shi dan haka suka kauce suka bashi hanya.

Cikin sauri suka saka kayan duka sannan suka buɗe motocin su suka shiga don zuwa
gida, a cikin motar da aka ɗauko shi kuwa, kan shi na saman kafaɗar mahaifiyar
tashi, yayin da ita kuma take ta sakin murmushi cike da farin ciki.

Surayya ta kalle su ta taɓe baki sannan tace; "barka da dawowa", kamar ba zai
amsa ba tsayin daƙiƙa takwas sannan ya ɗaga mata kai ya maida idanun shi ya lumshe.

Surayya kuwa wani baƙin ciki yazo mata wuya ya tokare idan da ace babu Mommy a
wajen babu abinda zai saka ta kalle shi balle har magana ta haɗa su.

Tsaki taja ƙasa-ƙasa gudun kada mahaifiyar tata taji tace; "mutum ba ɗan sarki
ba ba kowa ba amma sai iya mulki da wulaƙanci", Tameer dake zaune kusa da ita yayi
ƙwafa.

Brr Farida ta maida kallon nata kan Tameer tace; "kai baka ga ɗan uwan naka
bane?", shafa kai yayi yace; "Mum tsakanin nida shi waye gab......", cikin daka
tsawa tace; "shut up my friend, ina tambayar ka kana tambaya ta", ya saukar da kai
ƙasa sannan yace; "kiyi haƙuri", ya ɗan kalli Abdul ɗin da idanun shi ke rufe yace;
"Barka da dawowa".

Be buɗe idanu ba balle ya saka ran zai samu amsa sai dai ɗaga mishi hannu kawai
yayi, Surayya duk da ɓacin ran da take ciki sai da abin yaso bata dariya, aikuwa ta
hau tarin ƙarya dan ta san yadda Tameer ya kai matuƙa wajen ɓacin rai tana yin
dariyar zai sauke akan ta.

Tameer kuwa ya maida kallon shi kan Brr Farida yace; "Mum ki ganni yadda yayi
mini fa? Amma baki ce komai ba", Brr Farida dake danna waya ta ɗago tace; "ya gaji
ne ka bari idan ya huta zai maka magana ne ai", daga haka motar tayi shiru kuma aka
cigaba da tafiya.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

*HAYIN RIGASA, KADUNA*

Koda suka isa gida Nusram ƙin kula Nusreen tayi, har zuwa lokacin da suka shirya
domin tafiya makarantar islamiyya.

Ummi ma dai bata bi ta kan su ba, Nusram data fito daga wanka ta kalli Kubra
tace; "Autar mu kina hutawar ki Ummi na ji dake", yarinyar ta ɓangale baki tana
dariya.

A ɗan fizge ta kalli Nusreen wacce keta faman kwalliya, jikin ta sanye da shadda
kalar orange doguwar riga, Nusram ta taɓe baki sannan ta hau nata shirin.

Kusan a tare suka gama sai dai kallon farko da Nusreen ta yiwa Nusram jikin ta
yayi sanyi ganin ita sanye take da Atamfa me ruwan toka da ɗigon baƙi wanda ba haka
sabon su yake ba, kasancewar Nusreen ɗin ke fara wanka dan tana daɗewa a shiri
sannan duk kayan data saka yana nufin shi Nusram zata saka kenan, duk ranar data
canza to tana fushi da ita kenan.

Nusram nada haƙuri sosai da kau da kai sai dai akwai kafiya sannan idan tayi
fushi tana jimawa bata sauka ba, yayinda Nusreen take sha yanzu magani yanzu amma
fa da angama ya wuce kenan.

Haka suka fito domin tafiya, Nusram ta buɗe jaka ta ɗauko sweet guda biyu ta
miƙawa Kubra a hannu tana faɗin; "Ummi sai mun dawo", ta amsa tana bin yaran nata
da kallo domin daga ganin banbancin kaya a jikin su ta san sun yi faɗa kenan.

Suna fita tsakar gida Ameera tana wanke-wanken kayan da suka siyar na rana, Mama
Jummai kuma na kusa da ɗakin ta a zaune da ɗaurin ƙirji tana faman lissafa kuɗi.

Tana ganin sun fito tayi shewa tace; "kaga irin haihuwar da ake so ba irin wacce
za'a dinga yawo kwararo-kwararo ba da sunan karatu dan an rasa mashinshini", yau
dai tayi sa'a domin kuwa Nusreen ko kallon ta bata yi ba.

Kamar kurame haka suka tafi har izuwa makarantar, basu yi latti ba hakan yasa
kawai suka shiga aji, har aka tashi babu wanda yayi wa juna magana.

Haka har suka iso gida, a ƙofar gida suka tarar da Baba a zaune a dakali yana
jin labarai, suka mishi sannu da hutawa amma ko kallo basu ishe shi ba.

Suna shiga suka tarar da Mama Jummai gaban murhu tana ta faman iza huta, gefen
ta kuma Ameera ce take shirya jarkunan kunun aya dana zoɓo.

"ba dole mutum kullum yayi ta baƙi ba, koda yaushe yana gaban murhu", faɗan
Nusreen kenan, Mama Jummai ta wullo mata harara tace; "tunda jikin na Uban ki ne ba
sai ki hana ni zama gaban murhun ba".

"ai dama nashin ne sanin dai ne da ba'a yi saboda ba'aje makaranta bane an san
haƙƙin miji", ta bata amsa ba tare da shakka ba.

Mama Jummai ta ɗaga hannu ta nuna Ummi dake ƙofar ɗaki tana wanke shinkafa tace;
"kin ga wacce bata yi makaranta ba kuma bata san haƙƙin miji ba", ta buɗe baki zata
bata amsa Isa yayi sallama ya shigo.

Ta kalle shi ta kauda kai sannan tace; "ai naga saboda tsabar sanin haƙƙin mijin
ne yasa aka taho da ɗan gaban fatiha", tana ƙarasa ta zuba da gudu tayi ɗaki.

Nusram data ɗauko tsintsiya domin share gidan ta girgiza kai kawai cike da
takaici ta tsugunna ta cigaba da sharar ta, Isa kuwa cikin tsananin takaici yace;
"shegiya ƴar isa ai da kin tsaya da yau sai na ɓalla ki a gida nan", cikin salon
mugun ta ya sakarwa Nusram dundu a gadon baya wanda ta jishi har saman kanta.

Ƴar ƙaramar ƙara ta saki sannan ta durƙushe a wajen, yaja tsaki ya fice ya bar
maman shi tana zuba masifar ta a tsakar gida.

Ummi bata ko ɗago kai ta kalle su ba, Nusram kuwa sai da tafi minti biyar sannan
ta iya miƙewa ta cigaba da sharar ta tana yi tana share hawaye.
Koda ta gama sharar sannan ta ɗaura alwala tana kallon Nusreen tana leƙowa domin
tabbatar da fitar Isa, sallah ta tayar ta ƙyale ta.

Bayan sun idar da sallah nan suka zauna har kiran isha sannan suka yi sallar,
suna idarwa suka dawo falo suka zauna domin cin abinci.

Kasancewar garin da zafi yasa Nusram ɗaukar tabarma ta shinfiɗa musu ƙofar ɗaki
sannan suka fita duka.

Suna cikin cin abinci Nusreen ta maida kallon ta zuwa ga Nusram tace; "wai Ram
meye nayi miki ne da tun ɗazu kike share ni".

Jin hakan yasa Nusram tsame hannun ta daga abincin tace; "Rim magana kike fa
akan dukan matar aure, wallahi Rim bana son wannan halayyar taki, kiga fa yadda
kika dinga ɗaga murya kina faman faɗa akan abinda be taka kara ba balle ya karya
haba Nusreen kina girma kina cin ƙasa, ki sani ba ko da yaushe ba ake faɗan abinda
kaga dama ba, kwata-kwata Nusreen baki da haƙuri gaba ɗaya kin lalata rayuwar ki da
tsiwa".

Nusreen tayi shiru tana sauraren ƴar uwar ta kamar da gaske, kafin tace; "tunda
bakya so insha Allahu zan dena", Nusram ta saki murmushi tace; "yauwa ko kefa",
haka suka cigaba da firar su gwanin ban sha'awa, Ummi kuwa murmushi kawai take yi
domin taji abinda ƴar tata ta faɗawa ƴar uwar ta kuma hakan ya birge ta.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

*UNGUWAR RIMI, KADUNA*.

Shureim ne kwance saman sofa wacce take ɗakin shi, idanun shi a lumshe babu
abinda yake dawo mishi banda magan-ganun yarinyar yadda take juya idanu da yadda
take tsiwar tata.

Ya saki murmushi a karo na babu adadi, ya ƙara gyara kwanciyar shi cike yake da
muradin ƙara ganin ta, sai dai yana shakkar yadda zata tarbe shi dan da gani
yarinyar babu raini a tattare da ita.

Abokin shi Naufal ya ƙaraso ya zauna kusa dashi sannan ya bubbugi gefen sofa
ɗin, cikin sauri Shureim ya buɗe idanun shi sannan ya kalli abokin shi yace; "ya
akayi ne kake tashin mutane suna barci?".

Naufal yayi murmushi yace; "ka dena magana irin haka mana, bafa barci kake ba
idanun ka biyu don yadda kake murmushi wallahi yadda ka san sabon bazawari", tare
suka hau dariya.

Sai da suka tsagaita sannan Shureim yace; "tsiwa ta", Naufal yayi tagumi yace;
"yau kuma me tsiwar taka tayi?, kun kuma haɗuwa ne?", Shureim ya girgiza kai yace;
"ina fa sai dai yau ina so ka shirya muje binciken gidan su na gaji wallahi".

Naufal ya ɗan haɗe fuska yace; "gaskiya ka bari ba yau ba dan nima ina da wajen
zuwa", Shureim ya miƙe zaune yace; "lallai Naufal ni kake faɗawa haka ko saboda na
gama yi maka amfani amma kada ka manta lokacin da kake neman auren Futuha na tsaya
maka sosai".

Naufal ya girgiza kai yace; "gaskiya ka san Futuha tana da kishi sosai wallahi
taji zan raka ka taɗi to abin ba zai ƙare mini da kyau ba".

Shureim yace; "banza matsoraci dan Allah wallahi ba zan bari mu daɗe ba", Naufal
ya saukar da numfashi yace; "shikenan angon tsiwa", suka sake yin dariya.
Shureim yace; "yadda Mamie ta ƙosa nayi aure ne shiyasa bana so ta dawo ta samu
magana ba tayi nisa a tsakanin mu ba, na kuma san zata ji daɗi".

Naufal yace; "ni ba wannan ba kada fa taje tayi ta mana tsiwa ne", Shureim yayi
murmushi yace; "ai wallahi abinda nafi so tayi kenan", haka firar tasu ta cigaba
cike da annashuwa.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

*UNGUWAR SARKI, KADUNA*.

motar na yin parking Sumayya ta kwaso da gudu, shima cikin farin ciki ya buɗe
mata hannu ta faɗa jikin shi tana faɗin; "Oyoyo Yaya na".

Ya riƙo hannun ta sannan yace; "fatan na same ku lafiya", cikin fara'a tace;
"lafiya lau sai dai kewar ka da muka yi kawai".

Haka ya riƙe hannun ta suka shige cikin gidan, Fahad na zaune yana kallon
cartoon ganin shigowar su yasa ya miƙe ya nufi inda suke.

Abdul ya tsugunna dai-dai tsayin shi yace; "little angel ya school", Fahad yace;
"lafiya lau Yaya", Abdul yayi murmushi fahad ya ɗora hannun shi dai dai dimple ɗin
shi yace; "Yaya na daina ganin wannan".

Ɗauke shi yayi cak ya ɗaga sama yace; "to ai yanzu na dawo zaka cigaba da gani",
Brr Farida tace; "yanzu kaje ka huta anjima sai kazo kaci abinci".

Cikin shagwaɓa yace; "gaskiya ba zan iya haƙuri da cin abincin ki ba First love
har sai anjima", Sumayya tace; "Yaya kamar ka san yayi daɗi kuwa".

Ya kama hannun Sumayya suka nufi dinning tana zuba mishi surutu shi kuma yana
murmushi bayan shi kuma Brr Farida ce ita da Adnan.

Sai lokacin na juya na kalli falon babu kowa alamu ya nuna Surayya da Tameer sun
bar falon kenan🤔.

Brr Farida da kanta tayi serving ɗin shi, haka ya dinga ci yana santi su kuma
suna dariya, sai da ya gama sannan Brr Farida ta bari su Sumayya suka ci.

Shi dai yana gamawa ya miƙe ya nufi part ɗin shi domin hutawa, a hanya suka haɗu
da Surayya, ta kalle shi ya kalle ta, cike da takaici ta nufi part ɗin su Sameer.

Ya taɓe baki yana me shigewa nashi part ɗin, lumshe idanu yayi jin irin ƙamshin
dake tashi a ɗakin ya san aikin mahaifiyar shi ne shi yasa yake matuƙar ƙaunar ta.

Sai da yayi wanka sannan ya saka singlet da three quater ya kwanta, be wani jima
ba barci ya ɗauke shi.

#LIKE
#SHARE
#COMMENT

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*


♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖9-10📖📖

Surayya cikin kuka ta shiga falon, Sameer dake kwance saman kujera ya tashi da
sauri, wajen shi ta nufa tana zuwa ta faɗa jikin shi tana sakin kuka.

"wai meya faru ne?", ya tambaya, cikin sheshsheƙar kuka tace; "Yaya wallahi na
kusa haɗiyar zuciya na mutu saboda baƙin cikin Yah Abdul da Mummy".

Cikin sauri Sameer ya miƙe yace; "wai me yasa kuke haka ne komai Abdul! Abdul!!
Haba ya kamata ace kun canza wata maganar ok mutuwa zaki yi to kuwa sai ki shirya
mutuwar domin kuwa Mummy ba zata taɓa dena son Abdul ba dan wannan kam daga Allah
ne", yana gama faɗin haka ya kwashi wayoyin shi yayi waje.

Part ɗin Brr Farida ya nufa yana tafe yana tunani; "tabbas abinda ƴan uwan shi
suke complain shima yana damun shi sai dai kuma shi ba zai yi wauta irin tasu ba".
Yana daf da shiga itama tana fitowa, jikin ta sanye da doguwar riga baƙa ƙirar
Saudia, tayi rolling da gyale kalar peach, hannun ta riƙe da wani ƙaton littafi
kamar diary.

Da sauri ya ƙarasa wajen ta yace; "sorry Mummy banzo yiwa ɗan lelen ki sannu da
zuwa ba barci ne ya kwashe ni".

Ba tare da komai ba tace; "kada ka damu amma gaskiya banji daɗi ba", ya kwantar
da kanshi saman kafaɗar ta yace; "sorry Mum", ta shafa kanshi tana faɗin; "ya wuce
ai bari nayi sauri na tafi zan kaiwa Brr Isma'il wannan documents ɗin ne yanzu", ya
kamo hannun ta yace; "muje na raka ki bakin get", babu musu yaja hannun ta suka
tafi.

Suna tafe suna fira har suka iso bakin get ɗin, Securities cikin sauri suka buɗe
mata ƙofa domin ta shiga, Brr Farida kuwa lokacin da ta saka ƙafa domin shiga cikin
motar gaban ta ya yanke ya faɗi, cikin sauri ta juya ta kalli hanyar part ɗin shi.

Sameer yace; "Mummy lafiya kuwa?", da sauri tace; "Sameer Abdul", cike da
takaici amma ya danne yace; "Mummy me zai same shi kuwa? Kawai ki tafi kada ki ɓata
lokacin ki".

Ta kalle shi sannan ta girgiza kai tace; "bari dai naje na dubo shi na dawo", da
sauri Sameer ya riƙo hannun ta yace; "kije Mum zan je na binciko shi I promise
you", bata saurare shi ba ta nufi hanyar part ɗin nashi.

Shi kuwa da yake barci wanda yake cike da mafarkai marasa daɗin gani, wai gashi
a ƙulle jikin wata ƙatuwar tukunya ƙasa kuma wuta ke ci ga wasu mutane dake sanye
da jajayen kaya babu abinda suke kira sai *Murad*.

So suke su riƙe shi amma wutar taƙi ta basu dama, a duk lokacin da suka kawo
hannu domin riƙe shi sai wutar tayo sama kaman zata taɓa su, wanda shi kuma yo
saman da wutar take ba ƙaramin ƙona shi take ba.

A dai-dai wannan lokacin kuwa Appu ne gaban ƙatuwar ƙwaryar tsafin su, wacce take
cike da jini da kuma wasu irin ganyayyaki kalar ja da shuɗi.

Sunan *Murad* yake ƙwala kira cikin ƙaraji da kuwwa, tar fuskar Abdul ta fito
cikin wannan ƙwaryar yana kwance yana barci.

Wata mahaukaciyar dariya yayi sannan ya kira Tuge akan yazo ya gani, cikin sauri
ya matso gaban katuwar ƙwaryar, tabbas shine wanda suke nema ruwa a jallo amma
ƙaƙababbiyar matar nan ta hana taƙi basu dama su nufe shi da sharri.

Wani magani Appu ya ɗauko me kalar baƙi ya fara wasu surutai yana watsawa cikin
ruwan, ya jima yana watsawa sannan ya cigaba da ƙwala mishi kira, a cikin ruwan ya
buɗe idanu sannan ya fara yunƙurin tasowa zuwa gare su.

Sosai duka wajen suke murna ganin aikin su na tsayin shekaru ashirin da biyar
zai cika, ta ruwan Appu yake ƙoƙarin janyo shi.

Sai dai shigowar Brr Farida yasa wajen ya dauki wata irin ƙara Ƙwaryar kuma ta
kama da wuta wanda yayi sanadiyar matsawar su baya cike da tashin hankali gudun
kada fuskokin su su ƙone.

Brr Farida kuwa ganin yadda Abdul ke haɗa zufa ga wata irin jijjiga da yake yi
yasa tayi saurin jijjiga shi tana kiran sunan shi cike da tashin hankali.

A matuƙar razane ya buɗe idanun shi wa'inda tsabar masifa da tashin hankali suka
canza kala da grey colour suka koma ja da yellow-yellow a haɗe, cikin matukar tsoro
da tashin hankali ya faɗa jikin ta ya rungume yana sakin ajiyar zuciya.

Ta fara shafa bayan shi tana karanto addu'o'i tana tofa mishi, tun jikin shi na
rawa har ya dena a hankali kuma ya numfashin shi ya fara dai-dai ta.

Sai da nutsuwar shi ya dawo sannan ya zame daga jikin ta ya kwanta saman gadon,
Brr Farida kuwa ganin hakan yasa tace; "ai dama na faɗa maka indai ba zaka dena
kwanciya barci baka yi addu'a ba hakan ba zai dena faruwa da kai ba, yanzu da ban
shigo ba fa? Abdul ka dinga addu'a amma abu ya gagara".

Ya juyo ya riƙe hannun ta sannan yace; "First love kiyi haƙuri barcin ne yazo
mini ban shirya ba, amma ba zan kuma ba", tayi peck ɗin shi a goshi tace; "yauwa
Baby na, kada ka kuma kaji".

Ya ɗaga kai kawai, sai da ta kuma yi mishi addu'ar tsari da kariya sannan tace;
"ka cigaba da barcin ka yanzu zanje na kaiwa Brr Isma'il wannan takardun na dawo".

Cikin sauri ya miƙe yace; "First love bari na shirya mu tafi tare", yana gama
faɗin haka ya shige bayi domin wanka, be jima sosai ba ya fito inda ya samu har Brr
Farida ta fito mishi da kayan da zai saka.

Haka ya shirya cikin riga peach da kuma baƙin wando, takalmi ya zura ya fito yana
ƙoƙarin ɗaura agogon hannun shi.

Brr Farida dake tsaye tana kallon shi, gaban ta sai da ya faɗi ganin irin kyawun
da yayi gashi yana tsananin kama da mahaifin shi.

Ya hura mata iska a ido, ta lumshe idanun sannan tace; "kayi kyau ɗana", ya riƙo
hannun ta yace; "duk kyau na ai ban kai ki ba", haka suka jera gwanin ban sha'awa
har waje.

Sai da ya buɗe mata ƙofa ta shiga sannan ya zagaya securities suka buɗe mishi
shima ya shiga ya zauna, cikin natsuwa driver ɗin yaja motar sauran motocin suka
rufa musu baya.

*FEDERAL HIGH COURT, KADUNA* bakin wajen Brr Farida suka yi parking, ta kalli
Abdul da idanun shi ke ƙasa tace; "Baby ka jira ni bari na shiga na fito yanzu",
kamar wani ƙaramin yaro haka ya maƙe kafaɗa, Brr Farida ta saki murmushi sannan
suka fito duka, hannun su sarƙe dana juna suka nufi ciki.

A wani office suka sami Brr Isma'il ɗin yana zaune yana rubuce-rubuce, ta miƙa
mishi documents ɗin sannan suka fito.

Sun ɗauki hanyar komawa gida Abdul ya kalli mahaifiyar shi yace; "First love in
tambaye ki, wai waye *Murad*?".

Cak ta dakatar da tapping ɗin laptop ɗin da take yi tana zuba mishi idanu na
tsayin minti biyu, har gaban shi ya fara faɗuwa, "a ina kaji wannan sunan?".

Abdul ya sunkuyar da kai yace; "mafarkin da nayi ne ɗaz....", tayi saurin


dakatar dashi tace; "ya isa haka Abdul mafarki ne kawai kuma mafarki shirme ne".

Daga haka ta ɗauki waya tana dialing number ɗin mijin ta wato *DR ABUBAKAR YUNUSA
NAGIMI*, tace; "Daddyn ku yace baka kira shi kace ka sauka lafiya ba".

Ya shafa kai yana faɗin; "ganin ki ya mantar dani shi", ta saki murmushi sannan
ta kara wayar a kunnen ta, tana faɗin; "Assalamu alaykum hasken ruhina farin cikin
Farida angon brr", a tare suka yi dariya yayin da Abdul ya kauda kan shi yana sakin
murmushi, soyayyar mahaifiyar shi da mahaifin shi tana matuƙar birge shi sosai sam
basa gajiya da juna sannan babu ruwan su da yaran su kullum cikin bege da ƙaunar
juna suke.

Miƙo mishi wayar da tayi shiya katse tunanin da ya tafi, sai da yayi ɗan jim
sannan ya amsa, cikin ladabi ya gaishe dashi, shi kuma ya amsa cike da so da
kulawa.

"na san Mummyn ka tana ƙoƙari da kai sosai, babu wata matsala ko?", kamar yana
gaban shi sai da ya ɗaga kai sannan yace; "eh babu", Dr yace; "to masha Allahu na
yi muku order ɗin motocin ku kai da ƴan uwan ku nan da next week zasu iso".

"Daddy yaushe zaka dawo?", tambayar daya jefa mishi kenan, sai da yayi shiru
sannan yace; "nan da lokaci kaɗan Insha Allah, kaje Hayin Rigasa?", shima ya jefa
mishi tambayar.

" a'a, amma insha Allah zan je zuwa gobe", ya bashi amsa,Dr yayi murmushi yace;
"to Allah ya kaimu, ka ƙara kulawa kaji", yace; "to", haka suka yi sallama sannan
ya miƙawa Mummyn shi wayar wacce ta zuba mishi idanu.

Kauda kai yayi yana sakin murmushi, can ya kuma ɗagowa idanun nata yana kanshi,
ya kwaɓe fuska yace; "First love, me kuma nayi?".

"ina zakaje kake faɗawa Daddyn ku nan da gobe?", ta tambaye shi, ya riƙo hannun
ta sannan yace; "Mum muna magana ne akan zuwa na Hayin Rigasa", kauda kai tayi
kamar bata ji me yake cewa ba shima kuma yayi murmushi ya kwantar da kanshi saman
kujera.

Be san meke tsakanin Mummyn shi da dangin mahaifin nashi ba sai dai ya lura basa
wata mu'amala sosai, shine ma me ƙoƙarin zuwa amma sauran basa zuwa sosai kuma
itama bata tilasta musu suje kuma shima Daddy haka be wani damu da suje ba sai dai
abinda ke bashi mamaki yadda Daddyn ke tilasta mishi shi yaje duk da Mummy bata so,
to shi kanshi yaje sai ran shi ya ɓace wani lokacin sai dai duk da haka yana ƙaunar
gidan.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

*HAYIN RIGASA, KADUNA.*

Shureim ya kalli Naufal yace; "yauwa kaga wa'incan masu hijab ɗin ruwan toka to
ɗaya daga cikin su ce, sannan suna wucewa zamu bisu a baya", Naufal dake ƙunshe
dariya ya ɗaga kai duk da suna daga nesa ba zai gane yanayin su ba.

Idanu ya zuba musu har suka matso, duka kyawawa ne, masu haske sannan marasa
ƙiba sosai, suna da idanu manya wa'inda suke farare hanci su dogo ne sai bakin su
daya kasance ɗan madai-daici duka suna sanye da hijab me ruwan toka wanda ya ƙara
fito da ainihin kyawun su, sannan kuma daga gani shine Uniform ɗin islamiyar tasu.

Ɗayar ya kalla, yadda take buɗe ƙananan haƙoran ta farare tas take faman zuba
magana yayin da ɗayar ke sakin murmushi inda gefen kumatun ta ke lotsawa duka biyu
tana kuma lumshe idanu da har yadda zarazaran gashin idanun ta ke rufe idanun ruf.

Iya kallo na ƙurilla yayi musu amma ya kasa gane makusar su sannan kuma ya kasa
banbance su, duka kamar su ɗaya baya jin ko mahaifiyar su zata iya banbance su, ya
sauke ajiyar zuciya sannan ya maida kallon shi kan abokin nashi wanda shima su ya
zubawa idanu yana kallo.

" to anan waccece tsiwar taka?", ya jefa mishi tambaya, Shureim yayi murmushi
yace; "kaima daga gani ai ya kama ta ka bambamce mana, kalle su da kyau ka gani
ƙwaƙwalwar ka ta hasaso maka", ya ƙarasa yana kai duba gare su tare da sakin
murmushi kamar wani ɗan can haka 🙄.

Naufal ya ƙara kallon su, izuwa yanzu kuwa sun matso sosai kusa dashi kuma yana
iya ganin su tarr da suna daf da gifta su, shi dai har yanzu ba zai banbance su ba
domin kuwa ko agogon dake maƙale a hannun su me ruwan toka kala ɗaya ne haka zobe
dake yatsun su na hannun hagu, sannan atamfar da suka saka me Blue da light yellow
duka kala ɗaya ne haka flat ɗin takalmin dake ƙafar su shima kala ɗaya ne wanda ya
kasance blue.

Shi dai bashi da wani abu da zai bambamce su, ya maida kallon shi kan abokin
nashi daya zuba musu idanu kamar zai cinye abin ban dariyar shine yana ganin sun yi
murmushi shima zai, Naufal ya kalle shi ya kuma kalle su ya kwashe da dariya yana
faɗin;

"Allah Shureim kana daf da ka zare", Shureim ya kwaɗa mishi harara yace; "so
kenan ake faɗa maka malam".

Naufal ya kuma juyawa ya kalle su dan har sun gifta su yace; "nifa bana jin ko
mahaifiyar su zata banbance su", Shureim dake tada motar yace; "me zai hana ta
bambamce su tunda ita tayi naƙudar su ko kai kayi mata?", ya girgiza kai yana taɓe
baki.

Bin su suka yi a baya har zuwa lungun da gidan nasu yake,daga bakin lungun suka
yi parking sannan suka fito suna kallon gidan da suka shiga, gida na uku a cikin
jerin gidajen dake lungun.

Nusreen da Nusram kuwa suna shiga gida suka tarar da Sahura da uban jibgin kaya
a gaba sai kuka take sha, Mama Jummai kuma na gefe tana kallon ta.

Nusram tace; "sannun ku da gida Mama", Mama Jummai tace; "yauwa sannu", sosai
hakan ya basu mamaki saboda zagi ne ke biyo baya amma yau ta amsa jiki a sanyaye.

Nusram ta kai dubanta ga ƴar uwar ta tace; "lafiya kuwa ke kuma?", Mama Jumman
ta taɓe baki tace; "ina fa lafiya Nusram Nura ne ya sake ta saki ɗaya mahaifiyar
shi tace idan be sake ta Allah ya isa shine ya sako ta".

Sosai Nusram ta tsorata, ta tsugunna kusa da Sahurar tana bata haƙuri, Sahura
dake zubar da hawaye ta galla mata harara tana jan tsaki.

Nusreen haushi ya cika ta itama kuwa ta ja tsaki tace; "ai ga shi nan garin
neman gindin zama kin jawa kanki raini a wajen ƙanwar ƙanwar ki, dama ai duk abinda
mutum ya shuka shi zai girba kuma taya zaka kasance mowa a gidan mijin ka ƴaƴan ka
ma kace dole sai sun zama wannan ƙaryane yadda kake gasa ƴaƴan wasu haka za'a gasa
naka".

Mama Jummai ta miƙe tana wuci tace; "wallahi ki fita hanya ta Shegiyar ƴar Allah
bani", Nusreen tayi shewa tace; "ga ƴaƴan Allah bani nan ana korowa gidan Mama, ai
duk wanda yace tukunyar wani ba zata tafasa ba nashi ko ɗumi ba zata yi ba".

Mama jummai cikin hayagaga tace; "ai gwara su an shaida dan har aure sun yi kufa
babu wacce keda mashinshini,ai ko yanzu kasuwa ta tashi ɗan koli yaci riba", ta
ƙarasa tana cewa.

"ai da aure irin na ƴaƴan ki wallahi gwara na zauna har abada babu aure, auren
jeka nayi ka ita kanta wannan ɗin da take kamar muciya saki biyu ke akanta, waccan
😂 saki ɗaya ƴar baƙa ma(😂 Habiba) itama saki ɗaya gaskiya ki
kamar turmin( Sakeena)
canza boka wannan inaji batirin shi yayi sanyi😮.
Ba Mama jummai ba har Ummi dake ƙofar ɗaki tana girki sai da ta ɗago ta kalli
yarinyar tata balle Nusram da har kusa faɗuwa sai da tayi, duka kallon Nusreen ɗin
suke yi ita kuma ta maze kamar babu abinda tayi.

Sahura ta taso cikin rashin kunya tace; "malama ya ishe ki haka, ai naga aiki da
bokan ba ita kaɗai ta fara ba wata ma abinda take yi kenan, banza wacce taƙi
auruwa".

Mari ta kai mata da sauri Nusram ta tare tace; "kada ki fara ai ke kika janyo ma
kanki", Nusreen ta gallawa Nusram harara tace; "ai wallahi sai na mare ta, sai na
nuna mata niba sa'ar yin ta bace sa'ar yin uwar ta ce".

Sahurar itama cikin haki da masifa tace; "kamar yadda nake ba sa'ar yin ki ba
sa'ar yin taki Uwar ce ba", ai kuwa tana rufe baki Nusreen na sauke mata tafi a
fuska.

Jijjiga ta tayi ta wullar ƙasa ta hau kai ta fara duka, Nusram kuwa ta tsaya
tana kallon ikon Allah, Mama Jummai ta ɗauki roba ta fara ƙwalawa Nusreen ɗin tana
faɗin; "au baƙin ciki yasa zaki kashe mini ƴa ne?",.

Ummi ta kalli Nusram tace; "zo ki wuce ciki", babu musu ta ƙyale su ta wuce ta
ɗauki buta domin yin sallar magrib, Nusreen kuwa sai da ta gama kirɓar Sahurar
sannan ta ɗaga ta dan kanta tayi ɗaki.

Mama Jumman ta dinga jero mata zagi, yayin da Sahura ke zabga ihu domin ta daku
sosai, haka taja jikin ta tayi ɗaki domin dai ta jibgu sosai da sosai.

Nusreen na idar da sallah ta kalli ƴar uwar ta, Nusram taja tsaki tana miƙewa ta
bar wajen, Nusreen tayi murmushi tana shafa fuska ta san cewa sai da ta ƙara yin
ladabi kafin su shirya da ƴar uwar tata.

Ta kalli Ummi, Ummi kuwa ta zuba mata harara hakan yasa ta saukar da kai tace;
"Ummi kiyi haƙuri", shiru ne ya biyo baya domin sallamar wani yaro.

Mama Jummai dake waje ita ta amsa tana faɗin ya akayi me zaka siya?", yace; "yan
biyu aka ce na kira", Mama Jummai taja tsaki cike da takaici da kuma mamaki wanda
ya bayyana ƙarara a kan fuskar ta.

Nusram dake yanka latas ta ɗago ta saci kallon ƴar uwar tata, ita kuwa Nusreen
dama neman hanyar yiwa ƴar uwar tata magana take dan haka tace; "Ram baki ji ba ana
kiran ki".

Nusram ta juyar da kai tace; "kada Allah yasa ki tashi kije ki zauna neman
magana har Baba ya dawo kinga koda ace kuturu ne ya nemi ɗaura muku aure", ai kan
ta ƙarasa ta miƙe ɗauki hijab ɗin ta.

Koda ta fita Mama Jummai ce kawai a waje hakan yasa tayi waje kawai, Mama Jumman
tace; "Allah yasa gurgu ne", Nusreen ta saki dariya tana ƙarasa ficewa.

Suna tsaye suna kallon ƙofar gidan, kallon su take ƙasa zuwa sama, ita dai ba
zata tuna kosu waye ba domin bata san su ba, amma kuma daga ganin su kaga wa'inda
hutu ya samu waje ya zauna a jikin su.

Suna sanye da shadda bugaggiya kalar ruwan madara wacce tasha aikin wuta sosai a
jiki, ɗayan kan shi da hula ɗayan kuma babu hula, duka har agogon su kala ɗaya ne
haka takalmin su.

Ɗaya baƙi ne ɗayan kuma yana da haske kuma yana da ƴar ƙiba kaɗan yayin da ɗayan
yake dogo, dogon baƙin wanda ya zuba mata idanu itama haka ta zuba mishi idanu.
A hankali ta fara takowa zuwa wajen su, Shureim kuwa ji yake kamar ya ɗauke ta su
gudu tsabar son da yake mata, Nusreen kuwa sai da ta matso kusa dasu sannan ta gane
shi.

Wani irin ɗaure fuska tayi tana mishi kallon uku saura kwata, tana sakin musu
harara ganin yadda ya raina mata wayo wato har ma ƙofar gidan su yazo kenan?, da
alamu sai ta nuna mishi ita ba sa'ar shi bace.

" marin kazo nayi maka ko kuwa waccan wankin dana yi maka yayi kaɗan ne? Ko dai
kazo ƙara zuba mini datti ne? Ko ƴan sanda ka kwaso mini? Ko kazo ganin ni ƴar
wacece?", duka ta jero mishi tambayar idanun ta na kanshi.

Shureim da Naufal suka kalli juna cike da mamaki, Naufal kam da ƙyar ya iya riƙe
dariyar dake cin shi ganin yadda abokin nashi ke zare idanu, gashi ita kuma ta
ɗaure fuska yadda kasan uwa ta titsiye ɗan ta yayi mata laifi, shi kuma sai zare
idanu yake kamar yayi wa sarki ƙarya.

#LIKE
#SHARE
#COMMENT

*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖11-12📖📖

Tsit wajen yayi Shureim dai kallon ta kawai yake yi cike da birgewa yayin da
gaban shi ke dukan uku, Nusreen ta kuma balla mishi harara tace; "baka da baki
ne?".

Cikin sauri Shureim ya girgiza kai yace; "abinda ya kawo ni daban".

"me kenan? Ko kana bina bashi ne?", ta ƙara jefo mishi tambaya, wacce tasa Naufal
ya kasa riƙe dariyar shi.

Ta juya ta kalle shi ta taɓe baki tace; "kai kuma ka sami taɓin hankali ne, ko
kuwa sabon wulaƙanci ne da kuka samo ku ƴaƴan masu kuɗi", Naufal ya kauda kai yana
mamakin ƙarfin halin yarinyar da kwata-kwata ta hana su maganar.

"ya wani je ya kwaso ka, kai kuma ka wani biyo shi dunƙul-dunƙul, to ko zaka
tare mishi, wai yanzu zamani yazo da rashin mutunci ma har ƙofar gidan ku ake zuwa
ayi maka, to wallahi ku tattara komatsen ku kubar nan kafin nasa ayi muku rashin
mutunci na ƙarshe wanda ko hanyar nan ba zaku kuma kallo ba", tana gama faɗar haka
ta shige gida ta bar su a tsaye.

Shureim ya dafe kai da sauri, shi kuwa Naufal banda dariya babu abinda yake yi,
lallai wannan yarinyar ta wuce yadda yake tunani, cikin masifa Shureim ya kalle shi
yace;

"nifa ba na kira ka nan bane ka ƙara mini matsala, matsala ta nazo ka warware
mini amma ji yadda kazo ka lalata komai", Naufal ya kuma tuntsirewa da dariya.

Shureim kamar zai yi kuka yace; "na gode da irin sakamakon da kayi mini", nan ya
shige motar ya barshi, shima Naufal ɗin haka ya gaji ya shigo sannan yaja suka bar
unguwar.

Nusreen na shiga gida ta nemi waje kusa da Nusram ta zauna, Nusram dake cin
abinci ta kalle ta, ta kauda kai.

Nusreen ta janye abincin dake gaban Nusram din ta hau ci, Nusram kuwa bata ce
mata komai ba sai tashi da tayi ta wanko hannun ta.

Ummi ta dube ta tace; "wai waye yazo ne?", Nusreen ta taɓe baki tace; "nima ban
san shi ba wai ashe kwatancen da akayi mishi ne ba dai-dai ba", Ummi ta bita da
kallon tuhuma, ita kuma ta fuske tana me cigaba da cin abincin ta.

Tana gama cin abincin Baban su yayi sallama ya shigo, duka suka amsa mishi,
ɗakin Mama Jummai ya nufa suma kuma basu wani damu ba.
Ita kuwa sai dai tayi wata ƴar shewa sannan ta bishi ɗakin nata, Nusreen ta taɓe
baki tana jan tsaki.

Ummi ta dube su tace; "tashi ku shiga daga ciki aje a kwanta", babu wanda ya
musa haka suka tashi suka shige cikin ɗakin.

Sun kwanta babu jimawa Baban yayi kiran Nusreen, ta amsa tana ƙunƙunai, "shi
baban nan ya iya kiran mutane idan tashi ce ta haɗo ku amma hakan nan ba zai tsaya
yaji matsalar ku ba", haka ta fice tana mita, ita kuwa Nusram tana jin ta murmushi
tayi tana me yiwa ƴar uwar tata fatan shiriya.

Baban ya kalle ta yace; "ance wani yazo wajen ki", ta ɗago ta kalli Baban sannan
ta juya ta kalli wacce ke bayan shi Mama Jummai, ta ɗan ja tsaki ƙasa-ƙasa tace;
"nifa wallahi gulma ce bana so".

Baba yace; "me kika ce?", ta girgiza kai tana faɗin; "babu komai, ni babu wanda
yazo waje na".

Mama Jummai ta sako baki tace; "waye zai miki ƙarya, ina zaune aka aiko kiran
naki zaki ce babu wanda yazo ko dadiron naki ne, yara basu son aure sun fi so su
zauna suyi ta iskancin su a gidan uban su".

Baba ya ɗaga mata hannu sannan yace; "ya isa haka! Kince babu wanda yazo ko?",
Nusreen ta ɗaga kai, yace; "tashi kije zan saka a bincika mini idan na samu akasin
abinda kika faɗa sai na ɓata ranki kuma, tashi ki bani waje".

Babu musu ta miƙe kamar mutuniyar arziƙi tayi ɗakin su, Mama Jummai baƙin ciki ya
ishe ta hakan yasa ta tashi fuu tayi nata ɗakin.

Baban ya kalli Sahura yace; "ke kuma sai ki faɗa mini lafiya kika dawo gida",
cikin sauri tace; "Baba Nura ya sake ni", sai da Baba ya zage Nuran tas sannan yace
ta tashi taje zai nemi nuran.

Nusreen na shiga ɗaki ta tuntsire da dariya, jin hakan yasa hankalin Nusram ɗin
kwantawa don tayi tunanin ko wani abu ne ya faru.

Nusreen ta zauna gefen katifar su tace; "Ram kinji Mama Jummai da gulma wai har
ta kaiwa Baba gulmar wani yazo nema na?", Nusram ta juya kwanciyar ta tana ƙara
runtse idanu.

Nusreen taja tsaki tace; "dama na san ba zaki kula ni ba tunda yanzu kin dena
ƴar uwar dani", har lokacin Nusram bata motsa ba hakan yasa Nusreen ɗin taɓa ta
tace; "Ram ki tashi kiji me nake cewa mana".

Ta turo baki tace; "ai dai nace kiyi haƙuri ba zan kuma ba", saura kadan Nusram
da Ummi su kwashe da dariya amma suka dake, Nusram ta tashi ta zauna sannan tace;

"Nusreen kin cika ladabin ƴan Jos 🙄 ne, yanzu zaki tuba anjima ki sake komawa ki
aikata kalar wannan aikin, wannan ba hali bane me kyau".

Nusreen tace; "kiyi haƙuri na dena", Nusram ta girgiza kai tace; "ai wannan abin
da kike shine ladabin ƴan Jos ɗin, ba dai kince kin dena ba to gobe ma kuma yi zaki
yi nafa san halin ki".

Nusreen ta riƙo hannun ƴar uwar ta tace; "Nusram tunda nace na dena na dena ne
ba zan kuma ba ki yarda dani", Nusram tace;

"shikenan zamu gani idan da gaske ne, ni nafi so ki fahimci wani abu Mama
mahaifiya take a wajen mu dan tana auren mahaifin mu atleast u deserves our
respect, amma ke bakya ganewa yanzu kiwon mutum ake ba dabba ba sannan ki sani babu
alkhairi a barin wa ƴaƴan ka tarihi ko tabon rashin kunya, ki fahimta wasu abubuwan
kauda kai ake yi kada ki manta daba dan haƙurin manzon mu ba da yanzu addinin
musulunci be kawo mana ba amma da yayi haƙuri fa ba gashi yayi nasara ba, wallahi
haƙuri akwai nasara da dacewa a cikin shi ba komai ake maka kace sai ka rama ba ki
dinga sanyawa zuciyar ki haƙuri da salama mana ko zaki dace wajen koyo da ma'aiki".

Kamar da gaske Nusreen tayi shiru tana saurara d most funny part ɗin ma yadda ta
maida fuskar ta kai kace da gaske maganar na shigar ta, cikin sanyin murya tace;
"nayi nadama sosai ƴar uwata kuma insha Allahu zan yi koyi da Annabin mu(SAW),
nasan kina ƙauna ta shi yasa kike faɗa mini gaskiya na gode sosai".

Nusram tace; "yauwa ƴar ƙanwa ta yanzu mu kwanta ko sai da safe", babu musu
Nusreen ta zame ta kwanta, Ummi ta girgiza kai tana me yin murmushi.

Sau nawa ana yin irin hakan amma babu abinda ya canza yanzun ma bata jin zata
canza zani.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

*UNGUWAR SARKI, KADUNA*.

Brr Farida dake zaune ta zuba tagumi tana kallon gefen ɗaya wanda alamu ya nuna
cikin damuwa take, gefen ta Surayya ce ke danna waya sai Adnan dake game a tab dake
hannun shi.

Wani irin ƙamshi ne ya ziyarci falon kafin ya sako kai ciki bakin shi ɗauke da
sallama, cikin sauri Brr Farida ta ɗago tana kallon shi.

Riga ce a jikin shi kalar Blue sai wando fari, sosai kayan suka yi mishi kyau,
dan duk kayan da zai saka to suna amsar shi sosai, Surayya kallo ɗaya tayi mishi ta
kauda kai, Adnan kuwa wajen shi ya nufa da gudu.

Abdul ya riƙo hannun shi yace: "yauwa boy", Adnan yayi dariya sannan yace; "Ya
Abdul zaka je dani wajen Farha?", Abdul yayi murmushi har kumatun shi ya lotsa
sannan yace; "me zai hana kuwa?", Brr Farida ta ɗaure fuska tana me kallon gefe.

Kusa da ita yazo ya tsaya, ta juyo ta kalle shi yana rataye da ƙamar jaka wacce
ya zuba kayan amfanin shi a ciki, fuskar ta ɗauke da damuwa tace; "fatan ba zaka
jima ba a can ko?".

Riƙo hannun ta yayi yace; "eh bana jin zan wuce sati ɗaya", wani kallo ta wurga
mishi sannan tace; "sati ɗaya shine baka jima ba?, ko dai kafi son zaman can ne?",
ya girgiza kai yace; "haba first love taya zan so zaman wajen da babu ke".

"to kayi kwana biyu kawai ka dawo", ta faɗa tana kallon shi, yayi murmushi yace;
"shikenan First love to amma bakya ganin Daddy zai ce ban cika umarnin daya bani ba
munyi dashi one week fa?".

"kaga Allah ya kiyaye hanya", tana gama faɗin haka tana fara ƙoƙarin barin
wajen, cikin sauri ya sha gaban ta fuska ɗauke da damuwa yace; "bana so muyi irin
wannan rabuwar Mum, dan Allah kada kiyi fushi dani, idan hakan ya ɓata ranki, to
kiyi haƙuri", ya ƙarasa muryar shi na rawa.

Ita kanta bata san wane kalar so take wa ɗan nata ba, tana ji dashi sosai kuma
bata son ganin shi a damuwa, amma kuma zuwan shi Hayin Rigasa ta san ba wani kula
zai samu a can ba.
"shikenan zan haƙura amma da sharaɗi", cikin sauri ya tambaya; "meye sharaɗin?",
ta riƙo hannun shi sannan tace; "zaka yarda securities su raka ka har can.

Yayi ajiyar zuciya dama ya san sharaɗin ba zai wuce wannan ba to shi kuma ba wani
birge shi hakan yake yi ba balle hakan ya ɗaɗa shi da ƙasa sannan kuma shi baya son
hayaniya amma ya zai yi tunda shiri yake nema.

Yace; "shikenan, na yarda", tayi murmushi tana me amsar jakar hannun shi tace;
"muje na raka ka", haka suka jera har zuwa inda motocin suke sannan suka shiga a ka
jasu, yayin da baya da gaba take cike da motocin securities.

Duk inda suka gifta kallon su ake wanda hakan shine abinda Abdul ɗin baya so
amma babu yadda ya iya.

Cikin mintina kaɗan suka iso Unguwar, haka suka fara shiga cikin ta, shi dai ba
zai ce ga yanayin da yake ciki ba amma ya san cewa gaban shi yana faɗuwa.

Ya kwantar da kan shi saman kafaɗar Brr Farida yana me lumshe idanu, bakin shi
ɗauke da addu'a.

A bakin ƙaton estate ɗin suka dakata, sai da securities ɗin suka duba su sannan
suka bar su domin su shiga.

Gida ne me apartment daban-daban gasu nan jere sama da ashirin da biyar kowanne
kalar shi ɗaya da ɗan uwan shi, gefe da gefen titin da aka shinfiɗa kuwa flowers ne
aka jera wanda suka ƙara ƙawata wajen.

Daga saman get na biyu naga an rubuta *NAGIMI'S ESTATE*, nan ma sai dai aka duba
aka ga ko su waye sannan aka basu hanyar wucewa.

Nan fa suka fara wuce gidaje dake jere wa'inda duka kalar su ɗaya, kuma kowanne
da get ɗin shi, babu kowa a waje sai masu aiki suma jefi-jefi sun yi tafiya me
tsayi kafin su iso ƙarshen wannan titin inda wani get ɗin ke kallon su.

Sai da suka yi horn sannan aka buɗe musu get ɗin suka shiga, gida ne madai-
daici me cike da ƙawa da kayan alatu kai daga gani ka san me gidan yana da dukiya
sosai.

Haka suka jera parking a harabar wajen, Abdul ya kalli Brr Farida yayi murmushi
sannan yace; "First Love muje ko?", wani shegen kallo ta wurga mishi sannan taja
tsaki tana kauda kai.

Ɗan langwaɓar da kai yayi sannan yace; "Mum pls ki shiga ki gaida Malama dan na
san tana nan ga kuma Hajja itama", cikin haɗe rai tace; "amma ai bance maka ina da
buƙatar gaishe dasu ba ko sannan suma basu gaya maka cewa suna buƙatar tawa
gaisuwar ba ko?".

"Mum sufa ɗin Ƴan uwan Daddy ne sannan surukai suke a wajen ki dan Allah ki
shigo", ba dan ranta yaso ba tace; "sauka muje".

Cikin jin daɗi ya sauko suka fito tare, haka suka jera har cikin gidan, koda
suka shiga falon farko babu kowa a ciki dole haka suka shiga falo na biyu wanda
wata yar ƙaramar varender ce ta raba tsakani.

Ƙarami ne wannan falon don kujeru set biyu ne kawai a ciki sai wajen dinning a
gefe sai ƙofofi guda biyu nan ma babu kowa sai dai hayaniyar su da ake jiyowa daga
ciki.

Ya janyo hannun ta yana faɗin; "Mummy mu shiga daka ciki ina jin suna falon
ciki", babu musu suka ƙara kutsa kai ƙofar dake ɓangaren daman su.

Shima falon babu tarkace sosai a ciki dan shi be kai falon tsakiya girma ba,
suka yi sallama matar dake zaune saman kujera gaban ta ƙaramin table ne tana rubutu
a sama ta ɗago tana kallon su.

Da mamaki take bin su da kallo tana me ƙara duba zuwa gare su, wacce ke zaune
saman dinning ce ta amsa sallamar tasu tana me cigaba da cin abincin ta.

Sun tsaya sama da minti biyar kafin Brr Farida ta haɗe fuska ta ƙarasa cikin
falon ta sami kujera ta zauna, ganin hakan yasa Abdul wucewa ya shiga ƙofar dake
can corridor.

Da sallama ya shiga ɗakin, Ƴar tsohuwar dake zaune saman dardumar da alqur'ani
gaban ta, ta ɗago tana me kallon shi.

Kusa da ita yaje ya zauna ya ɗora kan shi saman ƙafar ta, ta saki murmushi tana
me shafa kanshi, ya lumshe idanu yana ajiyar zuciya.

A hankali yace; "First love na falo tana jiran ki", ya ɗago yana kallon ta,
fuskar ta babu yabo babu fallasa don haka ba zai tantance yanayin da take ciki ba.

Sai da tayi jimm sannan tace; "tashi muje", babu musu ya miƙe haka itama ta
miƙe, sai lokacin naga irin tsahon da matar take dashi gata fara sosai.

Cikin taƙama da ƙasaita take takun nata, na dafe baki ina faɗin; "Lallai Abdul
baka yardar a ƙasa ba ashe abin naku gado ne?".

Yadda ya shiga ya barsu haka ya dawo ya ssme su, baya jin magana ta haɗasu a
tsakani, shi kam wannan abu yana bashi mamaki.

Har sai da suka zauna sannan Brr Farida ta ɗago daga danna wayar da take yi ta
kuma sauke ƙafar ta ƙasa tace; "Ina wuni?", sai da tsohuwar tayi daƙiƙu kafin ta
amsa da ; "fatan kuna lafiya".

Brr Farida tace; "lafiya lau", daga haka babu wanda ya kuma magana a tsakanin
su, fin minti biyar sannan aka buɗe ƙofar falon aka shigo da sallama.

Taɓ 😂
! Kallo ya koma sama shaho ya ɗauko giwa 😂.

Wata ƴar ƙwalisar tsohuwa ce baƙa ta shigo falon tana taku ɗai-ɗai, ko kayan
jikin ta ka kalla kasan cewa ba ƙamar mace bace dan ita mayafi ta yafo saman
atamfar da ta saka Holland, ɗinkin doguwar riga wanda ya zauna a jikin ta sosai
babu abinda take sai tashin ƙamshi me shegen daɗi.

Kallo ɗaya ta yiwa Brr Farida ta ɗauke kanta, itama kuma Brr Farida bata kalle
ta ba, sama da minti biyar shiru sannan Brr Farida tace; "ina wuni".

Taja tsayin lokaci me nisa kafin ta iya cewa; "lafiya lau, ƴar mulki", Brr Farida
ta saki wani murmushi na ƙasaita.

Wacce ke saman dinning ɗin ta gama cin abincin ta sannan ta sauko itama kujerar
tazo ta zauna ta ɗauki remote ta kunna plasma ɗin dake maƙale a jikin bango.

Ɗan juyowa tayi ba tare da ta kalli ɓangaren Brr Farida ba tace; "ina wuni Brr?",
Brr farida ta amsa da ; "lafiya lau Fatima".

Babu wanda ya kuma magana hakan ya bawa Abdul damar gaishe da kakanin nashi guda
biyu duka sun amsa babu yabo ba fallasa sai dai wannan ƙasaitar tana nan.
; "Ina wuni Aunty?", Fatimar ta kalle shi tace; "lafiya lau, fatan ka dawo
lafiya", ya amsa da lafiya, wacce dai ke rubutu ce har yau bata ɗago ba balle ma
naga ya fuskar ta take.

Abdul yace; "Ina wuni Brr", cak ta tsaya da zana biron da take saman takardar
sai da taja lokaci kaɗan sannan ta ɗago.

Kyakkyawa ce ajin farko dan sai nace ta kusa kamo Brr Farida a kyau, fara ce
sosai wanda farin ta har ɗaukar idanu yake yi kana ganin ta ka san ƴar hutu ce gaba
da baya.

Cikin hausa irin ta ƴan boko da kuma zamanin yanzu wacce take cike da ƙaƙale
tace; "brr!? Ashe haka kake kiran uwar ka kenan?".

Brr Farida ta saki wata irin dariya me cike da nishaɗi da annashuwa kafin ta
janyo ɗaurin ɗankwalin ta ya dawo gaba tace; "wallahi idan kina ƙoƙarin haɗa kanki
dani Brr Hauwa dariya kike bani sosai, kema fa cewa ki kayi Uwar shi ai kin san
tsakanin mu da bambamci".

Brr Hauwa cikin fushi tace; "ai a juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe ne Brr
Farida", aikuwa babu sanya tace; "nifa na riga da na zama ƙadangaren bakin tulu
zama dani ya zama dole".

Brr Hauwa tace; "kada ki manta kayan aro har abada na aro ne, kuma wata rana
gaskiya zata yi halin ta".

"ko a yanzu kasuwa ta faɗi ɗan koli yaci riba sannan ki sani ni ɗin ruwan jakara
ce idan baki sha ni a kauye ba zaki sha ni a birni".

Cikin sauri kafin Brr Hauwa tayi magana Fatima ta dakatar dasu ta hanyar cewa;
"wai meye hakane kuke abu kamar yara ƙanana ku baku haɗuwa waje ɗaya ne sai kun
nuna halin ku".

Brr Hauwa tace; "wane kalar hali ai wallahi ko yanzu na san sama tayiwa yaro
nisa sai dai ya ɗaga kai ya kalla, domin kuwa idan na raina kasuwa ko sautu bana
bayarwa".

Brr Farida ta miƙe tsaye ta taka har gaban Brr Hauwa tace; "nafi ƙarfin ki kira
ni da ƙarama domin kuwa ke kanki kin sani hangen dala ba shiga birni bane kuma ba
girigirin ba tayi mai, irin ku masu cika baki suna bani mamaki sosai ki sani ni ɗin
ce Brr Farida Alƙali har yanzu sunan a haka yake be canza ke in banda ruwa ya daki
babban zakara da idan aka ce ki kalle ni ki faɗa mini wata maganar da ba zaki yi ba
wallahi koda kuwa kuɗi aka baki kada ki manta nifa itace kabari ce na danne uban
kowa dakalin majina a hauni a zame na hau mutum na zauna dai-dai, murucin kan dutse
ban fito ba sai da na shirya, kainuwa dashen Allah ba dashe na mutum ba.

"da bamu san asalin ungulu ba sai muce daga misra take, dama dangin ku ai dangin
taƙama ne da taka haye", amsar brr Hauwa kenan wacce ke tsaye gaban Brr Farida.

"kada ki manta tunkan a haifi uwar me sabulu balbela take da hasken ta kuma dama
ɗawisu ai kowa da zanen ta ya ganta, ke ƙaramar yarinya ce Hauwa ki bini a sannu
idan ba haka ba zan koyar dake darasin da ba'a taɓa yi miki ba", daga haka Brr
Farida ta ɗauki jakar ta sannan ta juya wajen tsofaffin biyu dake kallon su tace;

"zan tafi Malama, Hajja sai anjiman ku", tana gama faɗin hakan ko Abdul ɗin bata
yi zaman jira ba tayi waje kawai.

*tofa abu ya fara fin ƙarfin jin Deeje ƴar gidan Ahmadu jikan inusa, ni kaina a
dunƙule suka bani shiyasa nima na baku a haka amma zan ajiye biro na haka har sai
naje na tambayo fassarar wa'innan maganganun dan kada inje ko bindige ni suke nufi
ayi*.

*kuyi haƙuri da abinda kuke samu daga gare ni kunji na san ina yin delay ɗin
posting ɗin amma ku ƙara haƙuri saboda ina da uzururruka a gaba na sosai*.

#LIKE
#SHARE
#COMMENT
#VOTE

*Babyn Abdul, Maman Meenal Elham da Farouk*.

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

*godiya gare ku*.

*Aishatu Babayo*.
*Salamatu( kaka ta)*.
*Hafsat A garkuwa*
*Aunty Ummee*
*Kamal no love*
*Rukayyat Imam (Mama na)*
*Ibanatu*

Na gode sosai da sosai ku ɗin aminan ƙwarai ne kuma mutanen kirki ina ji daku
sosai da sosai.

*ina cigayar Khairat aminullah, da Hajjaju dan Allah wanda ya gane mini su ya
taimaka yace One Love na neman su*.

📖📖13-14📖📖

Hajja tace; "lallai wuyan ki ya isa yanka Farida har gida kizo ki zage mu tas",
ita dai Brr Farida bata san suna yi ba dan tayi nisa da tafiya.

Brr Hauwa tace; "yaushe dama take da wata tarbiya irin tarbiyar gidan su kenan,
kuma irin ta take bawa yaran dakta tunda shi yaji ya gani".

Fatima tace; "dan Allah ya isa haka, ku bar naganar mana", Hajja tace; "ba zamu
bari ba Uwar mu sai munji duka".

Abdul kuwa a hankali ya sulale ya bar musu ɗakin domin ya san idan sun gama kan
shi zasu dawo nan aka barsu da cece kuce ɗin su wanda baya ƙarewa.

Ɗakin ya tura ya shiga a hankali yana nan yadda yake, komai a tsaftace, ya saki
murmushi sannan yace: "Fadil kenan akwai tsafta", gefe ya ajiye jakar shi sannan ya
faɗa saman gadon.

Ya jima yana tunani wanda shi kanshi be san na meye ba, sannan ya miƙe ya nufi
bayi yayi wanka, cikin riga shirt mara nauyi fara da kuma wando jeans fari ya
shirya.

Koda ya fito falon dai ya nufo babu kowa a ciki sai yara guda biyu da suke wasa,
suna ganin shi suka nufo shi, ɗai-ɗai ya dinga ɗaga su sama yana ajiyewa.

Namijin yace; "Uncle A baka zo da Adnan ba?", ya ɗaga mishi kai yace; "ai yana
gida saboda makaranta", Yaron yace; "da kazo dashi da ba sai mu dinga tafiya daga
nan ba".

"au hakane kuma fa! To yanzu dai kayi haƙuri sai idan na sake dawowa", yaron yayi
murmushi, maccen kuwa ita daga gani bakin ta ma be buɗe ba dan haka ya riƙo hannun
su zuwa falon ya zaunar dasu.
Ɗakin dai wannan tsohuwar ya nufa, tana zaune tana linke kaya, tunda ya shigo
take kallon shi tana murmushi har yaja ya zauna kusa da ita.

Shi dai be san me yasa yake son matar ba kuma yake ganin tsananin ƙaunar shi
daga idanun ta a iya sanin shi kishiyar mahaifiyar baban shi ce.

Wayar shi ya zaro ya nemo number ɗin Mum ɗin shi, sai da tayi ringing sosai
sannan ta ɗaga.

"Baby sai yanzu ka tuna dani kenan?", ta faɗa tana dariya wacce dariyar tana
zuwar mishi har cikin kunnen shi.

Ya shafa sumar kanshi kamar yana gaban ta yace; "First Love barci ne ya kwashe
ni", sai da tayi jim sannan tace; "fatan dai kayi addu'a", ya ɗaga kai yace; "eh
sosai ma".

Haka suka cigaba da firar su gwanin ban sha'awa, har take fada mishi ashe Daddyn
su yayi musu oder na motoci?" yace; "eh amma ni nafi so ya dawo ne".

Ta ɗan yi dariya sannan tace; "ai zai dawo ne yace ƙarshen watan nan in Allah ya
yarda yana hanya, yauwa na san mota ɗaya tayi maka kaɗan shi yasa nake jin zan ƙara
maka koda biyu ne su zama uku kenan".

Yayi shiru na wani lokaci kafin yace; "Mum ki bar ɗayar kawai ta ishe ni
rayuwa", tace; "ba zai yiwu ba dole ka ƙara tunda kaga baka da wata motar a yanzu,
gobe idan kazo office ɗina za'a turo mini da hotuna sai ka zaɓa kawai, maganar fara
aikin ka fa?".

Ya shafa gefen fuskar shi yace; "Mum ni ina so na fara idan Daddy ya dawo saboda
komai yana buƙatar tsari sannan kinga ban san ina su Yaya Tameer suka tsaya ba".

"hakane shikenan mu bari idan ya dawo ɗin, I love you", yace; "love you too",
sannan ya katse wayar.

Malama taja dogon ajiyar zuciya tana ɗauke idanun ta daka barin kallon shi domin
kuwa duk tsayin wayar da suka yi tana kallon shi ne har ya gama, haka kuma wani abu
yana taso mata daga ƙasan zuciyar ta.

Abdul yace; "Malama wai ina Fadila ne da Fadil?", tace; Fadil na wajen aiki
Fadeela ma haka", shiru ya biyo baya kafin kuma ya dube ta yace; "nifa yunwa nake
ji".

Bata kalle shi ba tace; "kaje wajen Hajja mana nasan ba zaka rasa abinda zaka ci
ba ko kuma ka tafi part ɗin Abban ku".

Girgiza kai yayi yace; "bari dai naje Part ɗin Abban amma wajen Hajja ɗin nan da
sauƙi dan na san su Husna basa nan suna makaranta ba lallai a samu abinci ba", daga
haka ya fice.

Shiru ƴar tsohuwar tayi tana me bin inda ya fice da kallo, sosai ta kasa daurewa
ta saki kuka me cin rai wanda ni dai ban san dalilin kukan nata ba.

Tunda ya fita yake haɗuwa da matasa da ƴan matan gidan wa'inda wasu sun dawo
aiki wasu kuma sun dawo makaranta, haka suke gaisawa cikin mutunci duk da dai halin
nan nasu na shariya da taƙama da wasu suka ɗebo.

Shifa tsarin gidan su yana bashi mamaki, sai mace ta kai shekara ashirin da biyar
bata yi aure ba wata talatin duk wai da sunan boko don dole ne sai kin gama
university kuma sai kin fara aiki shi yasa dan kuɗi fa akwai su haka ilimi.

Wani gidan dake ɓangaren daman shi jeri na huɗu gida na biyu nan ya ƙwanƙwasa me
gadi ya buɗe mishi suka gaisa cike da girmama juna sannan ya shiga ciki.

A garden ya jiyo hayaniyar su wanda hakan ya nuna mishi suna can kenan, a can
kuwa ya tarar dasu.

Ƴan mata guda uku da samari guda huɗu sai mahaifiyar su dake zaune a gefe da
laptop a gaban ta alamu ya nuna aiki ma take yi.

"Lallai muna da manyan baƙi ga baƙon India a gidan mu", ɗaya daga samarin ya
faɗa, Abdul ya harare shi yace; "bana son yawan surutu fa Kabeer har ka dawo
kenan?".

Ya miƙa mishi hannu suka gaisa sannan yace; "ban daɗe da dawowa ba dan ma na
biya na ɗauko Aunty Khaleesat ne a office daba dan haka ba da tun Uku zan dawo".

Sauran ya miƙawa hannu suka gaisa duk suna tsokanar shi, shi dai kawai murmushi
yake yi, ɗaya daga cikin matan data kafe shi da idanuwa.

Ya kalle ta ya zaro idanun nashi yace; "ya akayi ne Saleema", Murmushi tayi tana
kauda kai, biyun suka kalli juna suka kwashe da dariya.

"Wallahi Abdul ina ji gaba ma cewa zaka yi ka girmi har su Abba jifa wai Salima
babu ko ɗan Sister ma a jiki".

"to ai ba wai ta girme ni bane da yawa", Maman nasu ta riƙe haɓa tace; "kai
Abdul lallai na shaida son girman ka to ba Saleema ba ko Hafeeza ta girme ka, kaifa
sa'an su Fadil ne da Fadeela kaga kuwa tsirar ka da Muhibba wata biyu ne Muhibba
kuma su Fadeel wata ɗaya suka bata, ai daga Kabeer sai Kamal sune ƙannan ka amma
duka sauran sun girme ka".

Ya juyar da kai yana murmushi, Hafeeza tayi dariya sannan tace; "Mummy ta tona
maka asiri dai", ya ɗan juyo ya harare ta kaɗan sannan yace; "nifa yunwa nake ji".

Cikin sauri Saleema ta miƙe tana faɗin bari nayi maka setting ɗin table sai kazo
kaci", babu wanda yayi magana sai fira da suka cigaba a tsakanin su.

Gidan Ambassador Ibraheem Yunusa Nagimi kenan, Jakadan Nigeria a ƙasar Italy,
shi mahaifin Abdus-samad yake bi, yana can ƙasar Italy ɗin sai dai lokaci zuwa
lokaci yake kawo ziyara ƙasar ta nigeria.

Yana da mata guda biyu amaryar ita ke can inda sukan yi wata shida-shida ne sai
ɗaya ta canji ɗaya, doka ce ta familyn basa fita waje suyi gida hakan yasa dole ya
ajiye yaran nashi a nan.

Ƴaƴan shi takwas biyu ne kacal suka yi aure yanzu haka shida suna nan basu yi
aure ba, cikin wa'inda suka yi auren akwai Muhsina da Maryam, Muhsina ita ke aiki a
bank Maryam kuma lecture ce a nan KASU dake kaduna.

Sai Adam wanda yake aiki da companyn NNPC yana da shekara talatin har da biyu
sai Saleema dake cikakkiyar likita me shekaru talatin, sai Hafeeza me ashirin da
takwas ita kuma tana aiki a ɗaya daga company na gidan ne sai Muhibba me shekaru
ashirin da shida sai Kabeer me ashirin da biyar sai Kamal me ashirin da uku daga
kan Muhibba zuwa ƙasa su karatu suke yi.

Saleema ta ƙaraso inda yake tace; "na gama zaka iya tasowa", babu musu ya miƙe
ita kuma ta biyo bayan shi.
Ta wata ƙofa ƙarama suka biyo sai gasu a ƙaton falon gidan, inda yake cike da
kayan mire rayuwa dinning area suka nufa wanda nan ɗin ma wani sabon kallo ne a
wajen.

Da kanta tayi serving ɗin shi sannan ta koma gefe ta zauna tana kallon yadda
yake cin abincin, cikin natsuwa sosai babu wata hayaniya ko tashin hankali.

Sai da ya gama sannan ya juyo ya kalle ta yace; wannan kallon fa ya kusa yayi
yawa", tayi murmushi tana kauda kai gefe shima murmushin yayi yana miƙewa tsaye.

Da sauri ta miƙe tsaye ta matso kusa dashi cikin sauri ta riƙo hannun shi tace;
"Abdul kayi kyau", ya sakar mata murmushi yace; "na gode sosai", daga haka ya zame
hannun nashi ya fice.

Tana tsaye tana kallon shi har ya fice daga falon, ajiyar numfashi tayi tana me
dafe kumatun nata da hannuwa biyu.

Ita tun ba yanzu ba Allah ya jarabce ta da tsananin son ƙanin nata wanda ta kan
rasa ina zata saka kanta.

Shi kuwa Abdul yana fita suka haɗu da Muhibba tayi ihu tana yo kanshi, cikin
sauri ya kauce ya balla mata harara yace; kefa matsala ta dake rashin hankali".

"au dan ma na nuna farin ciki da ganin ka", Kabeer dake kwasar dariya yace;
"Allah na rasa ina ƙasaitar ta take tafiya idan ta ganka", Muhibba ta cilla mishi
harara.

Juyowa tayi tana kallon Abdul ɗin wanda shi kuma yake ƙoƙarin ficewa daga gidan,
"ina zaka je ne?".

Be juyo ba ya bata amsa da zan tafi part ɗin su Hajja ne", da sauri ta biyo shi
tana faɗin; "muje na raka ka", ya dafe kai shi dan dai yana jin yunwa ne yazo gidan
nan amma hayaniyar su ta dame shi sosai.

Suna tafe tana mishi surutu shi dai kawai kallon ta yake yi sai murmushi lokaci
zuwa lokaci, haka har part ɗin Hajja.

Suna shiga Fadila dake zaune a saman kujera ta tashi da sauri tana ihun murna,
ya girgiza kai yana me yin murmushi ƙarfin hali.

Kujera ya samu ya zauna yana faɗin; "bismillah", Muhibba ta zauna a gefe Fadila
a ɗayan gefen, haka suka saka shi a tsakiya kafin su hau fira.

Firar da suke ma ba wata me hayaniya bace sai dariyar su kaɗa-kaɗan da zaka


dinga ji lokaci zuwa lokaci.

A haka har Fadil ya fito, ɗan saurayi dashi wanda suke kusan sa'anni da Abdul
ɗin, sai dai abinda zai baka mamaki yadda duk Abdul ɗin ya ɗarasu kyau kasancewar
yanayin shi daban.

Fadil yace; "kaga Sarki ka taso mu wuce ka rabu da wa'innan", babu musu ya
miƙe, yayin da Muhibba ta turo baki tana faɗin; "kai Yaya Fadil sai kazo ka wani
janye shi, kai baka zauna anyi firar zumunci da kai ba shima sai ka wani hana ayi
dashi".

Kafin ya basu amsa Abdul ɗin ya fito sanye da kayan ƙwallo kalar na jikin Fadil
ɗin, yana zuwa suka fice.
Bayan sun fita Abdul yace; "nifa bana son na wannan Estate ɗin mu ɗan je na
gamji mana", Fadil yace; "to shikenan ai Abban Nihal baya nan zamu iya tafiya",
haka suka fice daga cikin gidan.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

*HAYIN RIGASA, KADUNA*.

Nusram ta harari Nusreen tace; "wallahi kiyi sauri mu tafi dan na gaji gashi
kuma ina buƙatar hutawa", Nusreen ta yamutsa fuska tace; "to a haƙura da zuwa Tudun
Nufawan mana".

"sai kunje shi na san duk kece kike so ki janyo salalan tsiya to wallahi baki
isa ba kin san gobe akwai bikin Wasila ƴar gidan Malam Hassan kuma ta riga tazo ta
tambaya akan Nusram take so tayi mata kitso da kwalliya ko amma shine kike so ki
janyo abinda zai hana ku zuwa gobe bata da lokaci idan kuma kika sake kuka fasa
zuwa yau to gobe zaki je ke kaɗai kenan?".

Nusram ta girgiza kai tana faɗin; "Ummi zamu tafi yanzu Rim dan Allah kiyi ki
ƙarasa", Ummi tace; "ku dai kuka sani", ta cigaba da ƙulla sigar ta.

Nusreen ta miƙe tsaye, tana sanye da atamfa kalar blue da ratsin ja da kuma
ruwan toka sosai atamfar ta haska kalar fatar ta, fuskar nan ta ɗauki kwalliya
sosai.

Hijab ta ɗauko kalar ash ta saka takalmi da jaka ƴar ƙarama swagger kalar ja ta
saka sosai tayi kyau wanda itama Nusram ɗin shigar da tayi kenan sai dai ita fuskar
ta babu wata kwalliya sosai.

Ummi ta irgo kuɗi ta miƙa musu tace; "gashi nan ku kai mata kuce zamu yi waya
anjima, sannan ta ƙaro muku Curry da thyme harda citta duka domin ta waje na ta
ƙare saura ku daɗe".

"insha Allah da wuri zamu dawo", faɗar Nusram kenan tana ƙoƙarin saka kuɗin
cikin jakar ta.

Kamar koda yaushe Mama Jummai ta tsakar gida tana faman ɗora manyan tukwane
domin girkin siyarwa, Ameera da Sahura suna taya ta.

Haka suka fice ba tare da sunyi mata magana ba wanda ina ganin dalilin Nusreen
da bata so su kuma ɓatawa da ƴar uwar tane.

Koda suka isa bakin titi basu jima ba suka sami abin hawa inda suka hau zuwa
Tudun Nufawa.

Har ƙofar gidan me Keke Napep ɗin ya kaisu, Nusram ta ciro kuɗin shi ta miƙa
mishi, gidan babu laifi ya haɗu domin kuwa harda get a jiki.

A hankali suka tura suna masu jero sallama, daga can cikin gidan aka amsa sannan
suka shiga, ɗakin dake gefen hannun hagu suka ga takalma wanda ya nuna musu Auntyn
tasu tana cikin ɗakin.

Ɗaki ne wanda take sana'ar ta a ciki komai na kayan ta to a ciki yake haka ma
idan masu siye sun zo nan take kaisu.

Suna shiga suka tarar da Ƴan mata uku da kuma wata ƴar matashiyar mace wacce ba
za'a kira ta da tsohuwa ba, Matar tana ganin su ta sakin murmushi tace; "yauwa
Allah ya kawo mini ku, kamar kun san aiki yayi mini yawa".
Nusreen ta yamutsa fuska tana cuno baki, Nusram kuwa zama tayi sannan tace;
"meya faru Aunty?",

Wacce ta kira da Auntyn tace; "dama wa'innan da kike gani muke gyara dasu yau
kwanan mu goma sha takwas kenan, to yau kinga aiki yayi mini yawa ga kaya zan je
amsowa domin ɗazu an aka kira ni akan kaya sun iso ina so naje na zaɓo kada a riga
ni ga kuma jakunkuna da zan haɗa guda hamsin da biyar wa'inda ƙanwata Kaltume zata
wuce dasu Borno to aikin duk ya caɓe mini tunda kunzo sai ku taya ni".

Nusram tace; "babu komai Aunty, ga wannan ma inji Ummi tace a kawo miki wai zaku
yi waya ga kuma wannan kuɗin kayan mu ne dubu talatin da biyar ga na Yaya Sulaiman
shima dubu arba'in sai ki ajiye mishi, naso muje can ɗin da kanmu amma tunda kina
da aiki zamu hakura kawai sai ki ce mishi ya sake haɗo mana wasu kayan zuwa gobe na
rigunan kuma da turarruruka idan kin dawo sai ki bamu ko?".

Auntyn tace; "yauwa ƴa ta yanzu wanne zaki yi", Nusram tace; "bari na fara yiwa
amaren dilka idan yaso Rim kuma sai ki bata sample ɗin jakar sai ta fara yi miki
kafin na gama".

Auntyn ta gallawa Nusreen harara sannan tace; "ai banga alamar zata yi mini ba
ganin yadda take yatsina fuska", Nusreen tayi dariya tana fadin; "haba dai Aunty
zan yi miki mana sai dai kin cika saka aiki ne idan mutum yazo".

Aunty ta riƙe baki tana faɗin; "Nusreen ni ɗin lallai wuyan ki ya isa yanka",
Nusreen ɗin tace; "wasa nake miki ina Adam fa?".

"yana gidan Halima sai gobe zai dawo", Nusram tace; "Aunty kije ki manta da
wannan kawai", aikuwa", Auntyn ta faɗa kawai tana miƙewa domin zuwa ta shirya.

Ita kuma Nusram ɗin ta cire hijab sannan ta kwaso kayan da zata fara nata
aikin, nan ta shiga haɗawa, su kuwa amaren babu abinda suke sai mamakin yadda
wannan matashiyar zata musu gyara.

Haka dai suka fara gyaran inda nan suka cika da mamaki ganin yadda take gyara su
cike da bai, Nusreen kuma tana gefe tana haɗa jakun-kuna dama su kan taya ta hakan
yasa suka iya domin duk wanda zai zauna da ita tofa ba zai yi zaman banza ba.

Kan wani lokaci ta gama gyaran sannan ta koma kusa da Nusreen ɗin tana taya ta
haɗa jakun kunan, suna fira tsakanin su sama sama.

Yayin da suma amaren suke nasu firar lokaci zuwa lokaci, haka har magriba ta
kusanto, tashi Nusram tayi ta sirka musu ruwan da zasu yi wanka wanda ruwan ma da
wasu itatuwa da sinadarai masu ƙamshi.

Sai da suka fito sannan ta ɗauko wani ƙaramin roba me cike da wani mai me shegen
ƙamshi ta basu suka bi jikin su suka shafa.

Ɗayar ta kalli Nusram tace; "gaskiya kin huta da kika koyi sana'a ba ruwanki da
zama haka bayan kin yi aure", Nusram tayi murmushi kawai, haka suka yi sallama cike
da birgewa da mutuntawa.

Nusreen ta ajiye ta hannun ta tace; "gashi Aunty har yanzu shiru ko lafiya?",
kan suce wani abu tayi sallama ta shigo.

"kuyi haƙuri na jima sosai ban dawo ba", ta faɗa tana ajiye uban kayan dake
hannun ta, Nusram tace; "babu komai, na manta ince miki Ummi tace ki bata wasu
cittan da curry da thyme na hannun ta sun ƙare".
Auntyn tace; "bari na haɗo muku", ta faɗa tana ƙarasa miƙewa domin haɗo musu
yayinda su kuma suka hau zaɓar kayan domin tafiya da nasu.

Sai da suka haɗa komai sannan suka yi mata sallama, ta ciro ɗari biyar da ta
basu haka suka yi mata godiya suka fice daga gidan cikin sauri akan zuwa jibi zasu
dawo domin amsar ragowar kayan.

Haka suka fice daga gidan da kaya niƙi-niƙi Allah yasa babu nisa ma zuwa bakin
titi,sun ɗan jima kafin su samu abin hawa kasancewar magriba ta gabato.

Ana kaisu suka sauka, haka Nusreen ta bashi kuɗin shi sannan ta ɗauki nata
kayan itama Nusram haka, da ƙyar suke tafiya da kayan dan suna da yawa sosai.

Nusreen wacce ke gaba da kaya a hannun ta, su biyu suka taho a jere Fadil na
riƙe da kwallo yayin da Abdul ke gefen shi a iya saurin su shine kada magriba ta
iske su akan hanya.

Ɗan bangajar hannun Nusreen yayi wanda yasa kayan dake hannun ta faɗuwa, ita
kanta sai da ta kusa faduwa saboda gajiyar da tayi sosai Allah ya taimake ta Nusram
ta riƙo ta da sauri.

Abdul kuwa cikin sauri ya tsuguna ya ɗago jakar dake cike da kayan, Nusreen kuwa
wani irin haushi yazo mata wuya.

Da sauri ta tsuguna ta fizge jakar tana faɗin; "Malam dallah bani jaka ta mutum
yana tafiya kamar wani makaho ai ba kowa kafi sauri ba kuma yadda kake da uzuri
haka kowa ma yake da uzuri na rasa me yasa irin ku basu san darajar mata
b..........".

Kasa ƙarasa tayi saboda ɗagowar da yayi domin ganin wacece wannan, ita kuwa
Nusreen maganar taji ta tsaya mata a maƙogoro saboda wani kwarjini da yayi mata ga
idanun shi masu kama dana mage daya kafe ta dasu wanda ya haddasa mata daburcewa.

Ba ita ba ita kanta Nusram babu abinda ƙirjin ta yake sai dukan uku-uku, tunda
take bata taɓa haɗuwa da mutumin daya firgitata kalar wannan ba a zahirin gaskiya
ba uta yake kallo ba amma ji take kamar a gaban kotu take, jikin ta har rawa yake
yi tsabar ruɗewa.

Ya miƙe tsaye sosai sannan ya matso kusa da Nusreen yace; "ina gain tunda har na
baki haƙuri ai ya kama ta ki haƙura ko, *MENE NE RIBA TA??* (littafin zaratan
marubutan Golden pen, wanda mutum biyar ke aikin rubuta shi domin kawowa masoyan
su) dan naci zarafin mace wacce bata da ƙarfi kuma take da rauni, ya kamata ace kin
kula da martabar ki da darajarki ki dena ɗaga murya a titi duk kuwa da irin abinda
aka yi miki", daga haka ya juya ya tafi Fadil yabi bayan shi.

A tare suka sauke ajiyar zuciya kafin Nusreen taja tsaki jiki a sanyaye ta ɗauki
kayan nata suka wuce gida.

Koda suka isa gidan sun tarar da mutanen gidan na cikin ɗaki domin yin sallah
hakan yasa kayan kawai suka ajiye suma suka fara ƙoƙarin yin sallah.

Har lokacin jikin Nusram a sanyaye yake domin har zuwa yanzu sautin muryar shi
be bar kunnuwan ta ba, haka tayi sallah sannan suka zauna lissafi.

Sai da suka fitar da komai sannan wani yaro ya shigo yana faɗin ana sallama da
ƴan biyu, Nusram tace; "Rim tashi kije kina jin abinda yaron nan ya faɗa".

Dole tasa Nusreen wacce har yanzu bakin ta ya gagara buɗewa kamar da ta miƙe
tana jan tsaki ta ɗauki hijab tayi waje.
Kamar yadda ta zata kuwa sune dai a tsaye cike da jin haushi ta ƙarasa wajen su,
Shureim kuwa babu abinda yake yi banda kallon ta yana jin wani farin ciki a cikin
zuciyar shi.

Naufal kuwa dama drama ɗin su yasa ya biyo abokin nashi dan haka tun fitowar ta
ya fara kunshe dariya dan yadda ta fito kawai zai tabbatar maka da babu wasa.

Ɓangaren Abdul kuwa yarinyar ta bashi mamaki sosai ga wanu haushin ta da yake ji
a rayuwar shi ya tsani mace me tsiwa da hayaniya ko rawar kai, dalilin da yasa
kenan yaji abin ya ɓata mishi rai sosai.

Fadil yace; "kai amma gaskiya sun haɗu wallahi daga gani ƴan biyu ne", Abdul
yace; "suwa kenan?.

Fadil cikin mamaki yace; "kai wai baka lura dasu biyu bane?", Abdul cikin jin
haushi dan yanzu ya fahimci dawa yake ko ince wacce yake nufi dan haka yaja bakin
shi yayi shiru.

Haka Fadil ya cigaba da wani zuzuta kyawun su yayin da Abdul yake ji kamar ya
kwashe shi da mari.

"wai kai me yasa kake mini hakane yarinyar da babu abinda ta iya sai tsiwa shine
zaka wani dame mu da maganar ta idan son ta kake ai sai kaje ka aure ta, mtseww
yarinyar ƙarama sai rainin wayo".

Fadil yace; "ai kai kayi mata laifi ya kamata ace ka ɗauki duk wani abu da yazo
daga gare ta wai kai baka lura da tsananin kyawun da take dashi ba, ai wallahi da
ace zan sami kalar ta na auro ta a nan familyn to da sai na ɗinga ɗaga kai domin
kuwa na san na sami mace me kyau".

Abdul yaja wani tsakin sannan yace; da alamu ka samu taɓin hankali, ai wannan ba
wata me kyau bace abu mummuna da ita ka wani dage sai koɗata kake yi ai wallahi ka
cuci familyn mu daka haɗa su da ita".

Fadil yace; "ai kuwa kaf familyn mu babu me nuna mata kyau bayan kai dan dai baka
tsaya ka kalle ta da kyau bane".

Cikin sauri Abdul yace: "dan Allah na gaji da jin wa'innan shirmen kazo muje
muyi alwala mu wuce muyi sallah", haka dole Fadil yaja bakin shi ya tsuke.

Nusreen kuwa sai da ta bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya tana yatsina fuska, dama ga
haushin waccen daya gama raina mata wayo ya kuma hana ta fitar da abinda ke ranta
ga kuma wannan ɗan anacen da yake neman takurawa rayuwar ta.

#LIKE
#SHARE
#COMMENT
#VOTE

@ wattpad_ 13 deeja.

*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.


♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖15-16📖📖

shureim yace; "barka da wannan lokacin gimbiyar mata", Nusreen tayi mishi wani
kallo sannan tace; "wai kai meye matsalar ka ne dani?".

Yayi murmushi sannan yace; "ni kuwa nake da matsala dake, tun daga lokacin da
muka yi wannan haɗuwar har yanzu ban kuma samin kwanciyar hankali ba kullum da
tunanin ki nake kwana nake tashi ki taimaki bawan Allah ki amshe shi hannu biyu dan
Allah".

Mamaki ya hana Nusreen magana, lallai ma wannan ya raina ta cab, cikin masifa
tace; "au sakar maka fuskar da nake yi har yasa ka fara tunanin tara ta da wannan
maganar lallai ma dole na ɗauki mataki akan ka".
Shureim ya kalli Naufal dake faman ƙunshe dariya yace; "Naufal ka dena irin haka
ma ya ana maganar rayuwa ta kai kuma kana faman dariya".

Naufal yace; "yi haƙuri, amm ƴan mata ki daure ki bashi dama akan laifin da yayi
miki ya samu damar gyarawa, dan Allah ki amsa mishi kada hakan ya zama matsala a
rayuwar shi".

Nusreen tace; "ai rayuwar shi ba'a hannu na take ba dan da a hannu na take da
sai na bashi idan yaso ya dauwama a duniyar".

Naufal yace; "yanzu dai ba wannan maganar ba yayi miki laifi kiyi haƙuri kinji,
ki amshi ƙoƙon barar shi ko ya samu sauƙi na abinda yake damun shi".

Nusreen ta yamutsa fuska tace; "sai nayi tunani akai", sosai Shureim yaji daɗin
hakan.

"to yanzu ya sunan ƙanwar tawa?", Naufal ya tambaya, sai da Nusreen ta harare shi
ta ƙasan ido sannan tace; "Nusreen".

Cike da shauƙi Shureim ya sake maimaita sunan; "Nusreen! Nice name", Nusreen
tace; "bari na tafi kawai gida kada Baba na yazo ya same ni a nan".

Tana faɗin haka tayi shigewar ta gida, Shureim kuwa kamar ya ɗaga Naufal sama
haka ya dinga ji.

Naufal yace; "ka bari mana har sai ta amsa", Shureim yace; "wallahi naji daɗi
sosai", haka suka tafi cike da farin ciki.

Tana shiga ta tarar da Nusram na harhaɗa kayan da suka amso daga Tudun Nufawar,
Nusram tace; "har kin dawo kenan?".

Nusreen ta bata amsa tana me zama gefen katifar su tace; "eh har na dawo ban
daɗe ba ko".

Bata bata amsa ba sai da mai da komai inda yake sannan tazo ta zauna kusa da ita
tace; "Rim faɗa mini gaskiya waye yazo".

Nusreen tace; "ina wannan wanda ya taɓa watsa mini ruwa har yace maman shi zai
kai Airport", Nusram ta ɗaga kai alamar ta gane.

Nusreen ta cigaba da cewa; "to shine yazo wai yana so na", Nusram farin ciki ya
lulluɓe ta tace; "Alhamdulillahi ashe dai kema kina da rabon yin aure, Rim dan
Allah kada ki dakatar da wannan domin kuwa tun lokacin da muka haɗu na lura yana da
tarbiya sosai".

Nusreen tayi murmushi sannan tace; "amma kin san duk son da nakewa ɗa namiji ba
zan taɓa aminta dashi ba har sai kema kin samu naki ko?".

Jikin Nusram a sanyaye tace; "Rim kada muyi haka dake idan kuma Alƙah ya ƙaddara
ba zan taɓa yin aure ba fa?".

Nusreen tace; "nima shikenan ba zan yi ba", Nusram ta riƙo hannun ta cikin alamar
lallashi tace; "dan Allah ki daure ki janye wannan maganar taki domin kuwa zaki
ɗaura mini laifin da bazan iya kare kaina ba a wajen Allah, kiyi haƙuri ki tsaida
miji kiyi aure".

Nusreen ta taɓe baki tana me miƙewa tace; "ba zan taɓa canzawa ba Ram, kuma ina
nan akan baka ta har sai ranar da kika sami miji sannan nima zan tsaida mijin aure
na", tana gama faɗin haka ta fice daga ɗakin.

Nusram ta buga uban tagumi tana me tunanin halin ta da halin da ta tsinci kanta,
Ummi dake tsaye saman kanta, ta dafa ta tace; "Nusram ki dena damuwa kowa da kika
gani da tashi ƙaddarar".

Nusram cikin jimami tace; "Ummi da ace ina da wanda ya taɓa cewa yana sona yau
dana fito dashi a matsayin miji ko dan Nusreen, Ummi ko Nusreen bata faɗa mink ba
na san cewa ba zata taɓa canzawa ba akan abinda ta faɗa, sannan bana so tayi asarar
wannan mutumin domin kuwa daga ganin shi yana da nagarta kuma zai iya jurewa halin
ta, sai dai kash babu wanda ya taɓa furta kalmar so a gare ni".

Ummi cikin tausayin ƴar tata tace; "kada ki damu ki miƙawa Allah lamuran ki shine
kawai wanda zai iya share miki hawayen ki".

Ranar haka Nusram ta kwana cike da zullumi da tunanin mafita, yayin da Ummi ta
kwana tausayin ƴar tata ganin halin da take ciki.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

Yana zaune ya tasa laptop a gaba sai faman shagwaɓa yake zubawa da alamu dai waya
yake yi shida Brr Farida domin yadda yake yi kaɗai zai nunar maka da hakan, Fadil
kuwa in banda dariya babu abinda yake yi.

Abdul ya ɗago ya dalla mishi harara sannan ya cigaba da amsa wayar shi, "First
Love ki bari dan Allah su fara zaɓa idan yaso wacce suka bar mini ina son ta a
haka".

Brr Farida tace; "shikenan tunda haka kace amma ka sani ko bata yi maka ba tunda
kai kaso haka zaka amsa".

Ya ɗaga kai alamar ya yarda, Brr Farida tace; "nayi kewar ka sosai yaushe zaka
dawo ne?", ya shafa sumar kan shi yana murmushi yace; "nan da kwana uku".

Sosai Brr Farida ta ɓata rai sannan tace; "wai kai me kake samu daga wannan gidan
ne da ka nace shi kake son zaman cikin shi duk irin yadda ƴan gidan suke nuna maka
ƙiyayya".

"yaushe Daddy zai dawo ne, yace mini gobe amma kuma banga alamun hakan ba", ya
faɗa cikin son kaudar da waccen maganar.

Sanin halin ɗan nata yasa tace; "eh yace sai nan da sati me zuwa idan Alƙah ya
kaimu, nima ina so naje Dubai saboda kayan hannu na ya ƙare".

"kai First Love yanzu sai kiyi tafiya ki barni gaskiya zan biki", ya faɗa cikin
shagwaɓe fuska, tayi murmushi tace; "idan ka dawo daga nan ɗin ba idan kuma baka
dawo ba yaro sai dai kaji na wuce".

Ya noƙe kafaɗa yace; "idan kika tafi ni kuma sai inyi zama na a nan gidan in ƙi
dawowa", Brr Farida tayi dariya tace; "in dai Rigasa ne ai gaka ga ta nan da ƙafar
ka zaka gudu domin yanzun ma dan Abban Husna baya ƙasar ne".

Shiru yayi shi yana mamakin yadda Maman shi ke sanin wasu abubuwan da yake faruwa
a gidan koda ace bata nan, ya ɗan dafe kan shi yace; "bye Mum zan kwanta".

Tace; "ok shikenan sai da safe kada ka manta kayi addu'a kaji I love you", ya
bata amsa da "love you too", ya katse kiran.

Ta baya ya faɗa saman gadon kanshi na kallon sama, tunanin rayuwar su yake yi
yana kuma mamakin wasu abubuwan gashi idan zai kwana yana tambayar Maman shi ba
zata bashi amsar da yake so ba kuma shi ya san tabbas akwai wani abin.

"Kana tunani akanta kamar yadda nake yi?", muryar Fadil kenan yayinda ya katse
mishi tunanin shi.

Abdul yace; "waye kenan?", Fadil yace; "wacce muka haɗu ɗazu mana, gaskiya
yarinyar ta haɗu wallahi".

"just shut up", ya faɗa cikin fushi, ina cikin farin ciki zaka lalata mini da
wani zancen banza".

Fadil yayi murmushi yace; "Allah ka sake tunani, wallahi yarinyar zaku dace sosai
barin ma ɗayar dan naga ita tana da hankali sosai kuma itama wannan ɗin banga wani
aibunta ba", jin shiru ya tabbatar masa da idan zai kwana yana magana ba zai amsa
mishi ba hakan yasa yaja bakin shi yayi shiru.

Abdul kuwa sai da ya tabbatar da yayi addu'a sosai sannan ya gyara kwanciyar shi
domin yin barci wanda kuwa be jima ba barcin ya ɗauke shi.

Washe gari da wuri suka tashi domin zuwa ƙwallo ta ƙaddara, sai dai sauƙin ta a
cikin estate ɗin suka buga.

Suna ƙoƙarin shiga Brr Hauwa na ƙoƙarin fitowa, dan haka cikin sauri ya kauce
ya bata hanya, ta mishi wani kallo sannan taja tsaki ta wuce.

Hakan be wani dame shi ba domin ya riga ya saba da halin na ƙanwar mahaifin
nashi, wacce yake mamakin abinda yasa bata ƙaunar shi.

A kan dinning suka tarar da sauran, dan haka suma zama kawai suka yi, Husna ta
jefa mishi wani kallo sannan tace; "Ina kwana".

Ko kallon inda take beyi ba hakan ba ƙaramin bata haushi yayi ba amma haka ta
daure ta miƙe a ƙoƙarin ta na haɗa mishi abin kari.

"am ok", abinda ya faɗa kenan yana ƙoƙarin miƙewa, Hajja tace; "kai bana son
iskanci koma ka zauna kaci abinci".

"Hajja nifa ba yanzu zanyi break fast ba", ya bata amsa, cikin ƙasaita ta kuma
cewa; "ba wannan na tambaye ka ba, umarni na baka".

"haba Hajja tunda yace ba zai ci ba ki ƙyaƙe shi man........", cikin ƙaraji Hajja
tace; "ke kuma waye ya saka bakin ki a ciki ƙaramar alhaki, ki sani idan ina
sha'anin ƴaƴa na bana buƙatar bare ya saka mini baki".

Fadila ta kalli Malama wacce fuskar ta ke ɗauke da damuwa tace; "kiyi haƙuri
bada wata manufa na faɗa ba", tana gama faɗin haka ta miƙe ta bar wajen.

Abdul kuwa dan dole ya koma ya zauna, sai da ya harari Husna sannan yace; "serve
me", jikin ta har rawa yake wajen zuba mishi.

Sai da Hajja taga ya fara cin abincin sannan ta bar wajen, yana ganin ta shige
ɓangaren ta yaja tsaki yana kauda abincin.

Husna tace; "Yaya ai baka ci komai ba", ya balla mata harara sannan yace; "duk
ranar da kika kuma gigin shiga rayuwa ta sai na kusan sumar dake banza mara
hankali".

Husna ta cuno baki, Saleema tayi sallama ta shigo, jikin ta sanye da riga da
wando pakistan sai hannun dake riƙe da rigar lapcoat ɗayar kuma tana riƙe da kula.

Tayi kyau sosai ga kuma murmushin daya kuma ƙawata fuskar tata, tunda ta shigo
idanun ta ke kanshi tana me ƙara washe baki.

Yayi mata kyau sosai dan yana sanye da wando fari ne da riga blue kanshi kuwa
yayi combing ɗin shi hakan yasa gashin ya kwanta sosai.

Shima kuwa da murmushin ya bita, har kusa dashi ta ƙaraso, Fadil da Fadila
suka gaishe da ita, ita kuma ta gaishe da Malama.

Malama ta amsa tana me tashi ta bar musu wajen, Sayyada ma ta gaishe da ita ita
kuwa Husna gefe ta kalla tana me sakin tsaki ƙasa-ƙasa.

Murmushi suka kuma sakarwa juna sannan tace; "ina kwana", ya ɗan sosa kai yace;
"lafiya lau, har kin shirya".

Sai da ta juya idanu sannan tace; "eh har na fito na jira kazo breakfast baka zo
ba shine na biyo ka dashi".

"am ok na riga naci abinci anan", sai da murmushin dake fuskar ta ya ɗauke cikin
damuwa tace; "nifa da kaina na shiga kitchen na haɗa maka amma babu komai nasan
maybe dan baka san zan maka bane".

Wani irin murmushi yayi wanda ya tafiyar da imanin su gaba ɗaya, shi kanshi yana
jinjinawa haƙurin Auntyn tashi wannan kuma ke janyowa take matuƙar birge shi yana
son mace me sanyin hali.

Saleema da take ji kamar ana ƙarawa zuciyar ta wutar son shi ta juya tace; "bari
na wuce wajen aiki", tana faɗin haka ta fara tafiya.

Cikin sauri ya miƙe ya biyo bayan ta yana faɗin; "bari na raka ki", ya ƙarasa
yana amsar jakar hannun ta.

Sosai Saleema taji daɗin hakan kuma ta san cewa yayi ne dan ya sanyaya mata rai
na rashin cin abincin ta da beyi ba.

Husna kuwa kamar ta ɗora hannu a kai tayi ihu haka take ji yayin dasu Fadil suka
kasa riƙe dariyar su sai da suka dara sosai.

Husna kuwa abin ya ƙara baƙanta ranta dan haka ta nufi ɗakin Hajja tana kuka, su
kuwa suka cigaba da dariyar su.

Suna fita harabar gidan motar Abban su Fadil na shigowa, da sauri Saleema ta
buɗe motar ta shiga yayin da shi kuma Abdul ɗin ya mika maya jakar tata.

Abba daya fito daga cikin tashi motar yabi motar ta da kallo yana girgiza kai,
Abdul ya shafa kai sannan ya gaishe da Abban.

Cikin fara'a Abban ya amsa, hakan ba karamin daɗi Abdul ɗin yaji ba ganin yadda
ɗan uwan mahaifin nashi ya sakar mishi fuska.

Haka ya riƙo hannun Abdul ɗin har cikin gidan, da gudu Fadil da Fadila suka yi
wajen mahaifin su nan suka gaishe dashi ya amsa yana tambayar su ina wajen aikin
ba, nan suka bashi amsa da yanzu zasu tafi.

"to ayi sauri a tafi bana son wasa da aiki", dole suka ƙarasa shiryawa da wuri
suka fice, hannun shi cikin na Abdul suka shiga ɗakin Hajja.
Hajja tace" na rasa me dangin Malama suka baka da kake naniƙe muku kabi duk ka
wani manne dasu, to ka sani su ɗin rabin ƴan uwan mahaifin ka ne".

Abdul ya saukar da kai ƙasa cike da kunya ga Abban su Fadil amma bata ji kunyar
faɗin haka ba.

Abban Fadil kuwa yayi murmushi kawai idan da sabo yaci su saba da halin Hajjar;
"ina kwana Hajja".

"mun tashi lafiya?", amsar data bashi kenan, beyi fushi ba yace; "lafiya lau",
daga haka bata kuma cewa komai ba.

"bari na ƙarasa na gaishe da Malama, ga wannan a sa mana albarka", ya ciro ƴan


dubu-duɓu ɗauri biyu ya ajiye a gaban ta.

Da ƙyar ta iya cewa; "an gode Allah yayi albarka", Abban Fadil ya amsa da Ameen
yana me jinjina mulki irin na Hajja.

Yana miƙewa Abdul shima ya miƙe, Hajja tace; "to ɗan annace ina kuma zaka je?",
kamar ba zai amsa ba sai kuma yace; "gidan Abba".

"wane Abban?", ta ƙara jefa mishi tambaya shifa ya fara gajiya dan haka a ɗan
ƙarage yace; "Abban Kabeer", wani ɗan murmushi tayi sannan tace; "a dawo lafiya".

Har ya juya sai kuma ta kira shi, ba dan yaso ba ya juyo ya dawo, " yauwa ɗazu
meya haɗa ka da ƴar uwar ka Husna".

Sai da yayi jim sannan yace; "meta ce miki?", Hajja cikin hasala tace; "ina
tambayar ka kana tambaya ta?".

Yayi shiru be tanka ba, sanin cewa ba zai faɗa mata bane yasa itama bata kuma
magana ba haka suka zauna tsayin minti goma sha biyar kowa yana ji da nashi
miskilancin, dan kanshi ya miƙe ya fice, ita ma kuma bata ko kalli inda yake ba.

Yana fita ma ya fasa zuwa can ɗin dan haka ya nufi ɗakin Malama, har Abban
Fadil ɗin ya fita.

Da kyar ya iya yin sallama ya shiga, ganin hakan itama Malamar tunda ta amsa
mishi bata kuma cewa komai ba sai ma sallah data tayar.

Kan gadon ta kawai ya faɗa wanda yake tsaf-tsaf ya san aikin Fadila ne domin
tare suke kwana da Malamar yana kwanciya babu jimawa barci yayi awon gaba dashi.

Malama tana idar da Sallah ta juyo tana kallon shi, cikin idanun ta babu abinda
kake gani sai Ƙauna, tausayi da kuma bege, a hankali ta ƙarasa gaban shi tana
kallon shi.

Hannu ta kai wanda har rawa yake yi ta shafa fuskar shi hawayen da ban san kona
meye ba ya zubo daga idanun ta.

Baki take motsawa alamar addu'a take yi, sai da ta gama sannan ta shafa mishi
tana cigaba da zubar da hawayen ta, tana gamawa ta tashi ta koma kan sallayar ta
tana me ɗaga hannu sama tana addu'o'i hawaye na kuma zubowa wanda hakan zai nunar
maka da tana cikin baƙin ciki.

Sai bayan azahar sannan ya farka, babu kowa a ɗakin hakan ya nuna mishi kenan
Malama ta fita.

Ya sauko daga saman gadon ya shiga bayin ta yayi Alwala sannan ya fito, yana
fitowa daga ɗakin Hajja na fitowa daga nata ɗakin.

Ta kalle shi cikin masifa tace; "ina raba ka da Malama da abinda ta haifa kana
ƙara maƙale mata ko?, kana sane da cewa ba ita ta haifi Uban ka ba amma kabi duk ka
shige mata, so kake yadda ta cinye ƴar ta kaima ta cinye ka?".

Ya juya cike da jin kunya domin kuwa Malama dake tsaye a wajen ya kuma san taji
abinda Hajjar ta faɗa.

Malama cikin rawar murya tace; "Hajja me yasa kike faɗin haka ne taya uwa zata
lashe kuruwar ƴar ta?, meyasa kike so ki raba ƴan uwan taka ne ki sani da Fiddausi
da Baban Abdul Uban su ɗaya fa".

Hajja tace; "ai Uba kika ce ba Uwa da Uba ba sannan Baban Abdul ɗana ne Fiddausi
kuwa ƴar ki ce wacce tsabar maita kike lashe kuwar ta dan haka ki tattara ki ƙyale
mun jika dan yafi karfin ki".

Malama kasa cewa komai tayi dan haka ta shige ɗakin ta yayinda Abdul ya juya ya
bar wajen da sauri.

*Fiddausi* shi kuwa ya jima yana jin wannan sunan, domin kuwa sunan Muhibba
kenan, sannan Nihal ma sunan ta kenan sunan wata ne suka ci?.

Shi tunda yake be taɓa jin wannan sunan a wajen Mummyn shi ba, amma ya kan ɗan
ji shi cikin Estate idan ya shigo wanda alama ya nuna ƴace ga Malama kuma ta rasu
ne shekaru masu yawa.

Sai yamma sannan su Fadil suka dawo nan ya manta duk sauran damuwar shi ya dawo
dai-dai.

Suna fitowa sanye da riga baƙa yayin da Abdul yasa wando fari, shi kuma Fadil ya
saka baƙi sunyi kyau sosai idan ka gansu.

Sai dai duk da haka Abdul ya ɗara Fadil ɗin kyau, Saleema tayi sallama ta shigo
jikin ta sanye da abaya baƙa tayi rolling da farin gyale.

Murmushi ɗauke a fuskar ta, Fadila da Husna da suka fito, suka kalli juna Fadila
ta kwashe da dariya yayin da Husna ta ja tsaki.

"Yaya Abdul dan Allah mu tafi kawai", faɗar husna kenan cike da kishin ƴar uwar
tata kuma yayar ta.

Saleema ta dubi Abdul tace; "fita zaku yi ne?", gira kawai ya ɗaga mata tayi
murmushi tace; "da naga babu abinda zan yi ne shine nace bari nazo muyi fira amma
tunda fita zaku yi shikenan bazan dakatar daku ba Allah ya kikaye hanya".

Abdul ya ɗan yi jim sannan yace; "ko dai zakije ne kinga sai muyi having fun
tare?", Saleema ta ɗan yi dariya tace; "anya kuwa naga tafiyar ta yara ce amma
tunda anyi mini tayi bana ƙi ba", da fadil da fadila suka kwashe da dariya saleemar
na taya su.

Abdul kuwa kallon shi ya kai kan Husna yana sakin wani murmushi na rainin wayo,
Husna kamar tayi kuka ta juya.

Fadil yace; "ya haka Husna kizo muje mana", cike da jin haushi tace; "ba zani ba
na fasa", kan su ce wani abu ta shiga ɗakin Hajja.

Basu ƙara bi ta kanta ba suka yi waje, Abdul ke tuƙi a motar Saleemar yayin da
Saleema ke gefen shi sai Fadil da Fadila a baya.
Ba wani fira suke ba dan Abdul ya maida hankalin shi kan tuƙi ne, ita kuma
Saleema kacokan ta maida hankalin ta kan kallon shi, tana jin wani irin wuta ta
ƙaunar shi kuma tane me fatan zamowa mata agare shi duk da tarin kunya da matsalar
data hangowa a game da hakan.

Sun ɗan taɓa tafiya sannan ya juyo ya kalle ta yace; "Gamji get ko Peach palace?,
wani irin abu taji daga kanta har zuwa ƙafafunta wanda yasa ta koma ta jingina da
kujerar tana me lumshe idanu.

Tsinkayar muryar Fadila suka yi tana faɗin; "Abdul B mall Pls", ya juyo ya kalle
ta sannan yace; "shikenan muje can ɗin kawai".

Yana tada motar ita kuma tana tsallako titin zata shiga unguwar su hakan yasa ya
ɗan bangaje ta, da yake bangazar mota ne da mutum dan haka sai da ta faɗi kayan
hannun ta suka zube.

Cikin sauri ya fito yana jan Innalillahi, suma su Fadil duk suka fito, kusa da
ita ya ƙarasa yana taimaka mata wajen miƙewa.

Sai da ta miƙe tsaye sannan ya tsuguna yana tattaro mata kayan da suka zube sai
dai abin ban haushi duk wasu sun fashe don taje kasuwa ne ta siyo, Flask, glass cup
dinner set sai kuma plates na roba wanda Ummi ta bata kuɗi akan ta siyo mata.

Anyi sa'a dai dinner set ɗin da kayan robobin basu fashe ba amma flask da glass
cup duk sun fashe.

Ya ɗauko dinner set ɗin da robobin ya zuba mata a ledar, ta ɗan ƙuje saman
goshin ta sai kuma gwiwar hannun ta.

Sai da ya fara miƙa mata kayan sannan ya ga fuskar ta, gaban shi ya faɗi ganin
yarinyar rannan wacce ya buge har ta nemi ta zage shi.

Itama Nusram gaban ta sai da ya faɗi sannan jikin ta ya ɗau rawa, ita kuwa bata
son idanun wannan mutumin a kanta, ta kauda kai.

Abdul ya taɓe baki sannan yace; "kiyi haƙuri kuskure ne, ga wa'innan sauran kuma
sun fashe".

"babu komai ai tsautsayi ne, na gode", ta faɗa in cool voice tana amsar kayan,
mutanen dake wajen dai cece kuce suke yi.

Ya juya wajen Fadil yace; "akwai kuɗi a hannun ka?",Fadil ya girgiza kai yace;
"babu wallahi Atm ne kawai".

Saleema da tausayin yarinyar ya kamata tayi saurin zaro kuɗi cikin jakarta dubu
goma sha biyar ta miƙa ma Abdul akan ya bata.

Yayi murmushi yace; "thanks", sannan ya amsa ya miƙawa Nusram.

Nusram ta girgiza kai tace; "ba sai kun biyani ba tunda Allah yayi saiya fashe
koba ta sanadiyar ku ba zai fashe ɗin".

Abdul ya damƙo hannun ta, wani yar suka ji gaba ɗaya hakan yasa ya kuma riƙe
hannun, ita kuma da sauri ta ɗago ta kalle shi, kuɗin ya saka mata a tafin hannu
sannan yace; "ba wai biyanki muka yi ba kya rage asara kiyi hakuri", daga haka ya
saki hannun ta ya juya ya bar wajen.

Har suka tada motar suka tafi tana tsaye a wajen kamar statue sai da taga
ɓacewar su sannan taja numfashi ta damƙe kuɗin ta juya ta fara tafiya itama jiki a
sanyaye, mutanen wajen suna ta faɗin Allah ya kyauta amma ko samun damar amsa musu
bata yi ba.

#LIKE
#SHARE
#COMMENT
#FOLLOW @ WATTPAD 13DEEJA
#VOTE

*ga tambaya yau dai ku amsa mini naga masu bibiyar buk ɗin nan*.

-waye yafi birge ki a cikin su kuma ki kawo dalilin da yasa yafi birge ki?.

-wacece a cikin ukun nan kike tunanin itace jarumar littafin *Saleema,Nusreen ko
Nusram* sannan ki kawo dalilin ki?.

-shin ko zaki iya cankar meke saka Malama kuka? Kuma menene dalilin da yasa Brr
Farida tafi son Abdul kan sauran yaranta?.

-wai meke tsakanin Brr Farida da Brr Hauwa da yasa basa zama waje ɗaya, kuma meke
tsakanin Brr Farida da surukanta wanda yasa bata son yayan ta suje gidan musamman
ma Abdul?.

-Wai waye a tunanin ki su Tuge suke son kaiwa gaban matsafin su domin su bada jinin
shi?.

-zuwa yanzu wane darasi kika koya daga wannan littafin? Idan babu ko ɗaya shin kina
ganin a nan gaba zaki dauki wani darasi a ciki?.

-ya kika ɗauki littafin a ranki?

*bari muga wa'inda ke bibiyar littafin, idan kun amsa mini a dadinku ya kai na
cigaba da idan baku bani amsa ba na dakata da littafin*

*Babyn Abdul, Maman Elham, Farouk da Meenal*.

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*


*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

*Zulaihat isma'il kamar yadda na alƙawaranta ga page ɗin ki ke ɗaya na gode sosai*

*Aunty oum deedat ina godiya sosai keda Aunty Ummee*.

*My Aunty Fatima mazadu barka da dawowa Allah ya kawo twins next time ya kuma raya
mana baby*.

*ibnatu Baballe kinfi kowa son littafin nan kema na gode da kulawa*

📖📖17-18📖📖

Abin ya haɗe mata biyu ga yanayin da take ciki ga kuma dama sanyin da take dashi
dan haka sai taga kamar an ƙarawa gidan nasu tsawo.

Tana shan kwanar lungun gidan su ta haɗu da Isa zai fito hannun shi riƙe da jaka,
yana ganin ta ya washe baki, ita kuwa ta saukar da kanta ƙasa tana ƙoƙarin wucewa.

Ganin bata tanka ba ya gane Nusram ce dan haka ya ƙara washe baki sosai yana
faɗin; "ƴar ƙanwa ta har an dawo", sosai mamaki ya kashe Nusram ganin ba haka suka
saba ba a duk lokacin da suka haɗu hantara ce da tsana ke biyo baya.

"dama ina so muyi magana dake anjima fatan zaki tsaya ki saurare ni", ya katse
mata tunani.

Kai kawai ta ɗaga mishi domin har yanzu tana jin hannun wannan mutumin a jikin ta
ga yanayin daya saukar mata a jiki.

"yauwa ki same ni anjima bayan isha'i anan waje", nan ma dai ɗaga kai kawai tayi,
daga haka ya wuce itama kuwa ta wuce.

Tana shiga ta tarar da Aziza da Ameera suna wanke-wanken kwanukan da suka yi


talla yau gefe kuma sahura keta rizgar kuka.

Nusram ta matsa kusa da ita tace; "Sahura lafiya kuwa?", Sahura cikin zubar da
hawaye tace; "Nusram har yanzu Idris be zo ba biko ni kuma na gaji da zaman gidan
nan wallahi ina so na koma ɗaki na".

Sai da Nusram ta waiga taga babu kowa sannan taja Sahurar suka yi wajen famfo,
ƙasa-ƙasa gudun kada a jiyo su tace; "Sahura ki faɗa mini ainihin abinda ya haɗaki
da mijin ki".

Sahura ta ɗanyi shiru sannan tace; "Wallahi Nusram komai yana kawo mini ya ajiye
to wani lokacin bana da kuɗin adashi shine sai na ɗauka na siyar ko kuma idan ina
so na canza wani abin kamar shinkafa ko taliya tofa shine mamar shi ta faɗa mishi
wai satar abinci nake mishi shine ya mini faɗa ni kuma naja tsaki shine ya tsinka
mini mari ya koro ni gida".

Nusram ta ɗan yi jim sannan tace; "kinga Sahura ki yiwa kanki karatun ta natsu
ki tsaya ki gyara gidan auren ki, ki san yadda rayuwar gidan nan take idan kuma ba
tallan kike so ki sake komawa cikin shi ba to shikenan, kina ganin yadda har yanzu
muke fama da rayuwa gashi nan Allah be kawo mana masoya ba da wuri dan haka ki
tsaya ki yiwa mijin ki biyayya, ki bani number ɗin Idris ɗin zan neme shi gobe duk
yadda muka yi zaki ji".

Sahura ta washe baki tana faɗin; "wallahi kinfi Nusreen hankali ke har Baba
kinfi shi hankali, gashi nan ina so na koma ina tsoron na tunkare shi".

Nusram tayi murmushi har dimple ɗinta ya lotsa tace; "kai Sahura kece ai tun
farko baki fada mishi gaskiya ba, ki bani zuwa gobe sai na neme shi kawai".

Sahura tace; "yanzu kuwa ƴar uwa Allah ya baki miji wanda yafi ɗan gote kuɗi muzo
mu kwashi arziƙi", Nusram ta kwashe da dariya tace; "kada kiyi mini wannan fatan ai
kuma sai abin ya shafe ku, kuna son gani na abu ya gagara ke dai bani kawai kada
wani yazo ya gan mu tare, idan zakiyi mini addu'a kice ne Allah ya bani nagari".

Sahura ta janyo wayar ta Techno T345 ta nemo number ɗin shi da ƙyar sannan ta
bata, ita kuma Nusram ta kwafe Number ɗin.

Tana miƙawa Sahura wayar ta Mama Jummai na fitowa daga ɗaki, ta kama baki tace;
"au yanzu kuma abinda aka koma kenan? Kai ni Jummala ina ganin abu a gidan nan, ke
kuma uwar me kike tare da wannan uwar matan?".

Sahura ta zumɓuro baki tace; "kai Mama wannan ai tsakanin mu ne ba sai kinji ba",
Mama Jummai tace; "ni kike faɗawa haka wallahi idan baki baro wajen nan ba sai na
kusa karya ki".

Ta ƙara zumɓurar baki tace; "ai shiyasa nake so na koma gidan miji na kona huta
da matsalar ki, kinji Nusram sai gobe kawai duk yadda kuka yi ki neme ni".

Mama Jummai ta buga salati tana tafa hannu; "Sahura ba dai mijin ki kika bawa
wannan ba? Sahura yaushe zakiyi hankali ki fahimci me sanki ne da wanda basu son
ki, shikenan ta fitar mini da ƴa ita kuma tana so ta shiga gidan wallahi bari uban
ku ya dawo sai na faɗa mishi".

Nusreen dake tsaye a ƙofar ɗaki dan hayaniyar Mama ta fito da ita taja tsaki
tana faɗin; "me za'a yi da wannan me zubin ƴan daudun".

Nan Mama Jummai tayi kanta dama kamar jira take yi, ita dai Nusram ɗaki kawai ta
shige domin bata da lokacin tsayawa shirmen su dsn yanzu abin ya dena bata tsoro ya
koma bata dariya suyi ta abu kamar ƙananan yara.
Ummi dake tsaye bakin ƙofa Nusram tace; "Ummi dan Allah kizo ki zauna ki ƙyale
wa'innan da suka koma kamar Annabi da kafiri".

Ummi ta shigo ɗakin ta tsaya kusa da ita tace; "Nusram faɗa mini gaskiya meya
haɗa ki da Sahura kuma meta baki a wayar ta".

Nan Nusram ta kwashe komai ta faɗa mata, Ummi ta ɗan yi jim sannan tace; "eh to
hakan ma abu ne me kyau amma baki tunanin wata matsalar ta biyo baya?".

"insha Allahu babu abinda zai biyo baya sai alkhairi", abinda Nusram ta faɗa
kenan tana maida kallon ta kan Nusreen ɗin data shigo tana faman haki.

Ummi tace; "ke wai yaushe zakiyi hankali ne, wannan fa matsayin mu ɗaya da ita a
wajen ku amma ke kullum baki da abokiyar faɗa sai ita".

Waje ta nema ta zauna tana faɗin; "zan dena ne Ummi, Ramluv muga kayan?", Nusram
ɗin tayi banza da ita.

Nusreen ta taɓe baki, "nifa na shiga uku na manta nayi alƙawarin denawa yanzu sai
na sake ladabi kenan", ta faɗa cikin ranta.

"wallahi Ramluv na manta da munyi alƙawarin na dena kuma ai kinga itace ta fara
nema na da faɗa, kiyi haƙuri ba zan sake ba na miki alƙawari".

Nusram ta mata wani kallo sannan tace; "alƙawarin ki na banza Nusreen anjima nan
karya shi zaki yi dan haka ki hutar da bakin ki kawai bana buƙata", daga hakan ta
juya ta maida kallon ta kan Ummi sannan ta fara bata labarin abinda ya faru amma ce
mata tayi kawai tazo tsallaka titi suka bugeta ta kuma ɗauko kuɗin ta nuna ma
Ummin.

Ummi tace; "Allah sarki an gode sosai amma kuɗin yafi na kayan da kin sani ma
baki amsa ba".

Nusram tace; "wallahi Ummi naso naƙi amsa amma yadda suka bani tasa dole na
amsa", Ummi tayi ajiyar zuciya tace; "shikenan ai".

Nusreen tace; "yauwa Rimluv sai mu siyo cooler kawai dashi", Nusram tayi kamar
bata ji ta ba, Ummi tace; "eh hakan yayi idan yaso gaba sai ku siyo flask ɗin".

Nusram tace; "shikenan Ummi yadda kika ce haka za'a yi", Ummi tace; "yauwa Allah
yayi muku albarka amma cooler ɗin ki siyo ku biyu".

Nusram tayi murmushi tace; "Ummi cooler ta nawa-nawa kenan ki bari dai gaba idan
na sami kuɗi na sayi tawa".

Haka Nusram ta ƙara yinin ta tana me share Nusreen ɗin, ita kuma Nusreen ɗin
abin duk ya dame ta hakan yasa ta dinga aunawa Mama Jummai harara a ganin ta itace
silar ɓatawar ta da ƴar uwar ta.

Da daddare suna zaune suna cin abinci, Baban nasu ya shigo kamar ko wane lokaci
be amsa sannu da zuwan da Ummi da Nusram suke mishi ba.

Suna jiyo lokacin da Mama ke faɗa mishi ƙarya da gaskiya akan wai Nusram tana so
ta ƙwacewa Sahurar miji.

Nan ya fara bambami tun daga ƙofar ɗakin nasu, yana faɗin; "ba'a nan gidan ba
kina babbar banza har yanzu kin kasa fitar da miji yanzu kuma muguntar da zaku koma
kenan?".
Nusreen ta cuno baki, yana ƙarasowa kusa dasu ya rarumi itace yayi kansu, Nusreen
dai Allah ya taimake ta tayi ɗaki da gudu dan haka dukan akan Nusram aka sauke shi.

Babu wanda yace yayi haƙuri sai Sahura dake ƙoƙarin fahimtar da Baban ba haka
bane, amma ina bema bi ta kanta ba, Isa ne daya shigo yayi kan Baban ya samu ya
ƙwace itacen yana bashi haƙuri.

Tunda yaga Baban na duka ita kuma bata motsa ba ya tabbatar mishi da Nusreen ce,
dan haka yaje ƙwatar ta.

Allah yasa beji mata ciwo ba sai dai duk jikin ta ya tashi, kuma ko ɗigon hawaye
domin kuwa idan da sabo yanzu ta saba da dukan baban nasu.

Isa yace; "Baba kayi.mata haƙuri ba zata kuma ba, ke Nusram ki sako hijabi ki
same ni a waje", bata amsa ba domin baƙin cikin dake cikin ranta.

Yana fita itama ta miƙe ta shige ɗaki domin zuwa lokacin Nusreen ɗin ta buɗe
ƙofar tabbatar da cewa Baban ya fita zuwa lokacin.

Nusreen na ganin Nusram tace; "Ramluv ki dena tsayawa Baba na dukan ki", wata
irin tsawa ta daka mata sosai Nusreen ta tsorata dan haka ta ja baya.

"idan ma ya kashe ni ina ruwan ki, ko kina da asara ne?", Nusreen kam ta kasa
magana sai dai binta da idanu dan ta san tana misbehave zata iya jibguwa a hannun
ta dan idan tayi zuciya babu kyau.

Nusram taja tsaki sannan ta ɗauki hijab ta fice, Mama Jummai na zaune tana guɗa
tana kuma sakin habaici.

Nusram ta matsa kusa da Ummi tace; "Ummi zan je kiran Isa ba zan daɗe ba zan
dawo", Ummi ta ɗaga mata kai kawai, ita kuma ta juya ta fice.

A saman dakali ta same shi zaune, jiki na rawa ya miƙe yana bata wuri ta zauna,
Nusram dai abin har mamaki yake bata.

Sun ɗan jima a haka yana kame-kame kafin yace; "abinda yasa na kira ki shine,
kinga wannan dukan da Baba yake miki bana jin daɗin shi kwata-kwata shi yasa na
yanke wani hukunci akan mu ni da ke, kinga dama banyi aure ba kema kuma kina zaune
bakiyi aure ba shine nace me zai hana mu auri juna kawai".

Wani irin bugawa zuciyar ta tayi bata taɓa kawo haka ba idan tayi la'akari da
yadda yake ɗaya daga cikin maƙiyan su na cikin gidan, cikin kiɗima da tashin
hankali tace; "me kace Isa ban fahimta ba?".

Yace; "ina nufin mu dai-dai ta kanmu kawai ki amince mini naje da maganar gaban
Baba akan cewa mun dai-daita juna a ɗaura mana aure hankali kwance na san Baba ma
zai yi farin ciki sosai domin hakan kamar taimakon juna ne".

Wani irin gumi ne ya karyo mata tasa hannu ta share, miyan da zata haɗiya ma.ya
gagare ta, gaba ɗaya ƙwaƙwalwar ta bata aiki hakan yasa kawai ta lumshe idanu tana
me karanto duk addu'ar da tazo ranta.

Can wata dabara ta faɗo mata rai dan haka ta kalle shi tace; "Isa ka bari naje
nayi tunani a kai", ya jinjina kai yace; "shikenan na baki wannan damar amma ki
sani idan har kika sake kika ƙi amince mini wallahi sai na faɗawa Baba cewa mun
amince da juna sannan kuma in aure ki in gallazawa rayuwar ki sai kin gwammaci
zaman ki a nan gidan dan haka kada ki sake ki ƙauracewa magana ta".
Nusram ta girgiza kai hawaye ya zubo mata tace; "dan Allah Isa ka bari na san
abinda zan yi akai", Isa ya ɗaga kafaɗa yace; wannan kuma ruwan ki ne?", yana gama
faɗin hakan ya wuce ya barta a wajen.

Ta saka hannu ta share hawayen daya zubo mata sannan ta juya domin shiga gida.

Cikin sauri Naufal yace; "Nusreen", jin sunan yasa taja tsaya, juyowa tayi tana
kallon su, mutane biyu ne a tsaye kasancewar da hasken farin wata kuma suna cikin
hasken yasa ta hango su sai dai basa kusa hakan yasa bata gane ko wasu waye ba.

Jiki a sanyaye ta ƙarasa kusa dasu, ta bisu da kallo Nuafal yace; "sannun ki
ko?", ta kalle shi sannan ta kalli wanda ke gefen shi gani take kamar ta taɓa ganin
fuskar amma ta manta waye.

"yauwa sannu", Naufal ya kuma cewa; "dama muna neman wanda zai kira ki ne ashe
kece ma a nan waje".

Cikin tsananin kisha Shureim yace; "fisabilillahi haka muka yi dake? ni ina can
na kasa samun sukuni saboda zullumin amsar da zaki bani amma ke kina nan kina
rayuwar ki tare da wani na wai ya kike so nayi ne?".

Naufal ya galla mishi harara domin tunda suka fahimci itace Shureim ɗin yaso
yaje ya yiwa saurayin nata rashin mutunci ya hanashi kuma ko yanzu sai da yace;
"idan tazo kada yayi mata maganar".

Nusram tayi murmushi domin sai yanzu ta fahimci waye domin kuwa Nusreen ta faɗa
mata yadda suka yi, tace; "ya jikin Mama fatan anyi aikin cikin nasara?".

Shureim yace; "kinga ni ba wannan na tambaye ki ba waye wancan daya tafi


yanzu?", Nusram ta koma yin dariya sannan tace; "baka gane ni ba ko? To ni ba
Nusreen bace ƴar uwar Nusreen ɗin ce dai Nusram".

Wayyo! Ji yayi kamar ƙasa ta tsage ya shige, shifa tsabar kishi ya manta cewa su
ƴan biyu ne, ya shafa kai yace; "ayya! Wallahi na ɗauka itace, aikin kam anyi shi
sai dai mu jira sakamako kawai".

Tace; "to Allah yasa muji alkhairi bari na kira maka Nusreen ɗin", tana faɗin
haka ta juya ta tafi.

Naufal ya kalli Shureim yace; "wallahi yau Allah ya taimake ka amma daba haka ba
yau da babu me kwatar ka sai Allah kai da ba'a gama amicewa da kai ba amma har ka
sami bakin tuhuma Allah ya soka".

Shureim yayi murmushi yace; "Allah sarki baiwar Allah, me kyawun hali ga
hankali", cikin tsokana Naufal yace; "to kodai ita zaka komawa ne?", Shureim ya
harare shi.

Nusram kuwa ganin saurayin ƴar uwar nata ya ɗan rage mata damuwa kaɗan don haka
da ƴar ƙarfin gwiwar ta ta shiga gidan.

Nusreen na zaune Kubra na saman ƙafar ta yayin da take shafa mata magani Ummi
kuma na gefe suna fira.

Da sallama ta shiga kafin ta zauna kusa da ƴar uwar tata cikin farin ciki ta
kalle ta tace; "yauwa Rim kawo Kubrar na ƙarasa shafa mata maganin kije waje kina
da baƙo".

Nusreen ta washe baki domin kuwa ta san Alƙah ne ya taimake ta har Nusram ɗin ta
sauko ta san zuwan mutum ɗaya ne zai dawo da walwalar ƴar uwar tata amma duk da
haka cikin salon tsokana tace; "waye kuma?".

Nusram tace; "waye kuwa banda Shureim yana nan a waje dan Allah tashi kije kada
ya gaji da jira", Nusreen ta taɓe baki ita ta rasa me yasa ƴar uwar tata ke sonta
da Shureim ɗin.

Nusram ta miƙo mata hijab wanda yake a linke tace; "amsa ki saka tashi maza
kije", to ya zata yi da naciyar Nusram ɗin gashi tunda ta lura Nusram ɗin na son ta
dashi take ganin zata iya amsa mishi.

Amsa tayi ta saka sannan ta yiwa Ummi sallama ta fita, Nusram tace; "yauwa Rim a
dawo lafiya", Nusreen ta girgiza kai tana dariya kawai.

Tana fita ta hango su yanzu sun dawo inda su Nusram suka zauna ɗazu domin nan
babu hasken wata sai dai ta san su biyu ne kamar koda yaushe dan haka ta hade fuska
domin janyowa kanta girma ta fara takawa zuwa inda suke.

Tunda ta fito Shureim ya zuba mata idanu kamar ya maida ta ciki haka yake ji, da
sallama ta ƙaraso suka amsa mata sai da suka gaisa sannan Naufal yace; "munzo jin
amsar mu ne me aka yanke?".

Nusreen ta dan yi jim sannan tace; "akwai alƙawari da na yiwa ƴar uwata zan jira
ta har zuwa ta sami mijin aure dan haka idan kaima zaka iya haƙura zuwa lokacin
shikenan".

Naufal yayi murmushi yace; "kafin ayi maganar aure ai za'a yi ta soyayya ko
yanzu ita ta kawo mu", Nusreen tace; "tunda ƴar uwata tana sona dashi nima na
amince ko dan farin cikin ta".

Naufal yace; "ah lallai mun gode sosai sai ki miƙa mana gaisuwa gare ta, lallai
na jinjina mata kuma tayi mana ƙokari", Shureim yayi ajiyar zuciya yace;
"Alhamdulillahi na gode sosai".

Naufal yace; "yanzu shikenan zamu sami Baba mu nemi izinin shi dan ya san da
zaman mu", Nusreen tace; "shikenan", nan dai suka ɗan taɓa fira.

Suna daf da yin sallama Baban ya iso, da torch light ya haska su, ganin Nusreen
yasa yace; "to ƴar banza yau kuma iskancin har ƙofar gida na?", Nusreen ta zumɓuro
baki cike da jin haushi.

Su Shureim suka gaishe da Baban ya amsa sannan ya maida kallon shi kan Nusreen
yace; "kin wuce kin bani waje ko kuwa?", ba dan ranta yaso ba tayi cikin gida.

Baba ya kalli Shureim yace; "ku kuke lalata mini yara ko?", Shureim ya girgiza
kai yace; "a'a Baba", Naufal ya ɗora da cewa; "dama munzo neman amincewar tane
kafin muzo neman izini wajen ka".

Baba yace; "su har wani neman izinin ta kuke yi?, waye yake sonta a cikin ku?",
Naufal ya nuna Shureim.

Baba ya kalli shureim yace; "yaro ya sunan ka? Kuma wacce kake so a cikin su?",
Shureim ya shafa kai yace; "Nusreen nake so kuma sunana Shureim".

Baba yayi murmushi yace; "Shureim in dai Nusreen ce na baka ita kaje ka turo
magabanta ka kawai a tsaida rana bana so ta kai wata me zuwa a gida na".

Shureim da Naufal suka kalli juna, su dai tunda suke basu taɓa jin anyi aure
haka ba, Naufal yace; "to shikenan Baba mun gode sai dai wani hanzari ba gudu ba,
Mahaifin shi ya rasu sai Mahaifiyar shi, Mahaifiyar shi kuma bata ƙasar tana can
ƙasar Syria za'a mata aikin ƙafa to muna neman alfarma a bamu dama har zuwa lokacin
da zata dawo".

Baba yayi jim sannan yace; "shikenan Allah ya kaimu, kai fa idan har kana so zan
iya baka ƴar uwar ta", Naufal ya girgiza kai yana faɗin; "a'a Baba ina da mata".

Baba yace; "to shikenan amma ƙofa a buɗe take idan har da wanda kake ganin zai
iya auren ta to kawai ka turo mini shi koda babu akwati sadaki kawai ya isa kaima
kuma kada ka takurawa kanka", Shureim ya amsa da to.

Naufal ne ya matsa kusa da motar shi ya ɗauko rafas ɗin ƴan ɗari biyar-biyar ya
haɗo da ƴar takarda, biron dake jikin aljihun rigar Shureim ya zara sannan yayi
rubutu ya haɗa ya miƙawa Baba yace; "Baba ga wannan a saka mana albarka wannan kuma
Number ɗin abokina ne dan Allah a bawa Nusreen ɗin ace ta kira shi dan Allah".

Baba ya washe baki yana faɗin; "ah lallai za'a je daku na gode sosai Allah yayi
albarka insha Allahu ina shiga zan bata", ya amshe yana saka musu albarka, nan suka
yi sallama ya shige gida su kuma suka tafi.

Ɓangaren Nusram kuwa tana gama shafawa Kubra magani ta ɗauketa ta kaita kan
shinfiɗar ta, sannan itama taje tayo alwala tazo ta kwanta.

Abubuwan da suka faru yau su suka dawo mata cikin kai, haka harta gangaro kan
zuwan ta kasuwa da bigeta da wannan bawan Allah yayi, dawowar ta gida zuwa ga
matsalar Sahura, dukan da Baba yayi mata da magan-ganun da suka yi da Isa.

Tasa hannu ta share hawayen daya zubo mata, yanzu ina zata saka kanta?, gaskiya
ko aure zata yi ba zata auri Isa ba sanin cewa ba wai zai iya riƙeta bane.

Ta miƙe ta zauna taja ajiyar zuciya tana ganin kawai gobe zata kai tallan kanta
ne masallaci wanda ta yiwa sai yazo ya rufa mata asiri, to kina da tabbacin shi
yana da hali me kyau?, abinda zuciyarta ta faɗa nata kenan.

Sai dai duk halin da take ciki bata so Nusreen ta rasa wannan saurayin domin
tana ji a jikinta zai zamewa ƴar uwarta alkhairi.

Faɗuwar ƴar uwarta jikin ta ya katse mata tunani, Nusreen ta rungume ta tana
dariya, Nusram ma cikin dabara ta goge hawayen fuskar ta.

Ta ɗago Nusreen tace; "Rimluv ban labari na sha meya faru", Nusreen tayi dariya
tace; "Ram na amince da Shureim domin shima ya amince da sharadi na".

Nusram tace; "bangane ba? Wane sharaɗi?", Nusreen tayi fari tace; "sharaɗina
mana na ba zai nemi aure na ba sai kin sami naki mijin".

Shiru Nusram tayi na ɗan lokaci kafin tace; " haba Rimluv wannan wane irin
sharaɗi ne?, gaskiya ki janye", Nusreen ta miƙe tana taɓe baki tace; "babu abinda
zan canza".

Har suka kwanta kowa da tunanin da yake yi, ita Nusram tunanin ta shine yadda
zata nemo mafita akan abu biyu na farko shine matsalar ta da Isa na biyu kuma
matsalar ta da Nusreen.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

Haka suka isa Mall ɗin cike da nishaɗi domin kuwa Abdul tunda suka rabu be kuma
tuna abin ba, hakan yasa ya washe suka cigaba da farin cikin su.

Sai da suka yi siyayya sosai duk inda suka gifta kallon su ake cike da sha'awa,
Saleema kuwa yau ji take komai ya warware mata kamar damuwarta ta ƙare gata ga
abinda zuciyar ta ke muradi.

Shi yaja mata weelbasket ɗin ita kuma tana zaɓar abinda take so a haka har suka
gama siyayyar sannan suka wuce park.

Ƙayataccen waje suka samu suka zauna inda masoya kan zauna domin fira da kuma
jin daɗin soyayyar tasu.

Saleema tace; "Abdul ban san dalili ba amma yau naji kamar nafi kowa sa'a", yayi
murmushi yana kashe ido ɗaya yace; "da gaske ko?".

Ta ɗaga kai tana ƙara jin son shi har cikin ranta, wayar shi ya zaro sannan ya
danna kiran mahaifiyar tashi.

"Baby sai yau ka tuna dani ko?", ta faɗa tana dariya, Abdul ya shafa kai yace;
"First love da safe ma munyi waya fa".

"baka san yadda nake ji bane da ko awa ɗaya ba zaka yi ba sai munyi waya, ina
kewar ka sosai", ta ƙarasa da alamar damuwa.

Abdul yace; "nima nayi kewar ki Mom jibi zan dawo", Brr Farida tace; "taɓ ai
kuwa gobe zan wuce Dubai", ya ƙwalalo idanu yace; "da gaske to gaskiya sai kin dawo
zan dawo nima".

Brr Farida ta kalli Sumayya dake gefen ta tace; "to ai ga ƙanwar ka nan duk ta
damu ka dawo", cikin sauri Sumayya ta amshi wayar daga hannun mahaifiyar ta.

"Yaya Abdul dan Allah ka dawo", ta faɗa cike da shagwaɓa, Abdul yayi murmushi
yace; "sai idan Mum ta dawo kinji zan dawo kada ki damu nima nayi kewar ku sosai".

Sumayya ta noƙe kafaɗa tace; "ni dai ka yiwa Mummy magana gobe ta barni nazo
wajen ka".

"shikenan zanyi mata magana nasan zata barki", Sumayya tayi ihun murna tace;
"that's my lovely bro, bari na bata", ta faɗa tana miƙawa Brr Farida wacce ke faman
hararar ta tunda taji ta ambaci zuwa wajen shi ta haɗe rai.

Tana amsa tace; "kada ma ka fara dan ba zan bari ba", Abdul ya shafa kai yana
murmushi wanda Saleema ke ƙara ɗimaucewa duk da waya yake yi yayinda ita kuma ta
zuba mishi idanu.

"Kai First love please ki barta dan Allah wallahi zan kula da ita", Brr Farida
tace; "kaima ka san son da nake maka ba zaka taɓa neman abu na hanaka ba".

Yayi murmushi yace; "nagode my Mum", Brr Farida tace; "babu komai gobe driver zai
kawota and please ka kula da ita soaai dan bana so wani abu ya sameta dan zaman ta
kusa da Brr Hauwa barazana ne gare ni".

Abdul yace; "insha Allahu babu abinda zai same ta", nan suka yi sallama cike da
ƙaunar juna.

Ya kalli Saleema yace; "Aunty muje gida ko?", tayi murmushi tace; "yadda kace
Abdul", yace; "to taso muje", babu musu ta tashi suka tafi.

Abdul ya dubi Fadil da Fadila yace; "to ku kuma idan kun gama sai kuzo mu wuce",
Fadil yayi dariya sannan suka miƙe.

Haka suka dawo gida cike farin ciki, sai da suka ajiye Saleema a gidan su sannan
suka wuce.

Duka ɗakin Malama suka nufa, tana zaune saman sallaya dattijuwar akwai ibada
koda yaushe cikin bautawa ubangiji take.

Fadila taje ta kwanta a jikin ta, Abdul ya kalle ta ya taɓe baki yace; "katuwar
banza kawai", Fadil yayi dariya.

Abdul ya shiga bayi yayi Alwala sai da ya fito sannan Fadil shima ya shiga yayo
tashi alwalar sannan suka tafi masallaci.

Basu shigo gida ba sai bayan isha'i dan haka direct dinning area suka nufa inda
dama duk mutanen ɓangaren na zaune a wajen.

Suna zama Husna ta miƙe ta fara serving ɗinsu bece mata komai sai dai harara daya
dalla mata.

Ita kuwa batama san yana yi ba, dan haka abincin kawai ta zuba ta turo mishi
gaban shi yaja ya fara ci.

Koda ya gama tashi kawai yayi ya shige ɗakin Malama, Hajja tace; "wallahi ka
fito daga ɗakin nan domin ba ita ta haifa mini Abubakar ba" kota kanta bebi ba.

Kan gadon Malama ya faɗa kawai ya gaji sosai hutawa yake buƙata, ya gyara
kwanciyar shi yana me jan tsaki, gaskiya idan Daddy ya dawo aiki zai fara ya gaji".

Ya lumshe idanu fuskarta ta dawo mishi da sauri ya buɗe idanu, me kenan?


Yarinyar da kwanaki ya ganta harta nemi tayi mishi tsiwa amma yau kuma ta canza
hali koda yake dama mata ai canzawa suke kamar hawainiya".

Ƙara gyara kwanciya yayi kawai yana kawar da tunanin ta, a haka barci ya kwashe
shi me cike da abubuwan mamaki.

#LIKE
#SHARE

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*


*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖19-20📖📖

*MURAD* shine sunan dake mishi yawo a ƙwaƙwalwa, cikin tsakiyar daji yake masu
dogayen bishiyoyo, babu abinda ke tashi a wajen sai wasu irin muryoyi cikin ɓacin
rai da hargitsi suke ƙwala wannan kiran.

Yasa hannu biyu ya toshe kunnuwan sa yana me tsugunawa a wajen, jikin shi
sharkaf da zufa cikin ƙanƙanin lokaci numfashin shi ya fara sama-sama wanda a dai-
dai wannan lokacin Malama ta ɗago shi a tsorace tana kiran sunan shi.

Kamar wanda aka jefa rami ko rijiya me zurfi haka numfashin shi ya dawo, cikin
tashin hankali da kiɗima ya buɗe idanun shi, Malama ke zaune tana tofa mishi
addu'o'i gefen ta kuwa Fadila ce da Fadil duka idanun su na kanshi.

A hankali numfashin shi ya dai-daita sannan idanun shi suka buɗe gaba ɗaya,
kamar wanda aka watsawa ruwa haka jikin shi ya jiƙe sharkaf da zufa.

Ganin ya dawo hayyacin shi yasa Malama cewa; "ka dena wasa da addu'a, ya zaka zo
ka kwanta barci ba tare da kayi addu'a ba idan wani abu ya same ka fa ina kake so
na saka rayuwa ta".

Duka suka bita da idanu suna mamakin furucin ta, ganin kallon da suke mata ne ya
tunatar da ita meta faɗa dan haka cikin sauri ta riƙo hannun Abdul tace; "bana da
abinda zan faɗawa Kakarka da mahaifiyar ka don haka ka kiyaye", jinjina kai kawai
yayi sannan ya fara ƙoƙarin miƙewa.

Fadil yazo ya taimaka mishi har ya dai-daita a tsaye sannan suka yi musu sai da
safe suka fice.

Koda suka koma nasu ɗakin sai da yayi alwala sannan ya kwanta, yana kwanciya
wayar shi nayin ƙara.

Ganin wake kiran shi kuma baya son ɗaga mata hankali dan ya san har yanzu ba wai
ya gama dawowa dai-dai bane dan haka ya maida wayar silent kawai ya koma barcin
shi.
Washe gari, da safe sai da suka shirya tukunna suka fito zuwa falo, akan dinning
kamar kowanne lokaci suka same su, sanin halin Hajja yasa bema nufi kan dinning ɗin
ba.

Daga saman kujera ya gaishe dasu ɗaya bayan ɗaya suka amsa mishi, Husna da tunda
ya fito take kallon shi don yayi mata kyau sosai.

Jikin shi ƙananan kaya ne as usual, wando fari da riga blue gashin kanshi yasha
gyara sosai, ƙafar shi sanye da slipper irin na maza shima kalar blue, babu abinda
yake tashi a jikin shi banda ƙamshi.

"Ina kwana Yah Abdul", be ɗago ya kalle ta ba yace; "lafiya", sosai amsa gaisuwar
ya ƙular da ita amma sai ta share kawai.

Sayyada kam babu ruwan ta hakan yasa gaisuwa sosai ke shiga tsakanin su har ya
kan tsokane ta ma.

Bayan sun gama karin nasu kowa ya kama gaban shi, Fadil da Fadila suka wuce
wajen aiki, Husna da Sayyada suka wuce makaranta, Hajja da Malama kuma falo suka
dawo suka zauna saman kujeru.

Hajja ta saka glass ta ɗauki jarida ta fara karantawa yayinda malama kuma ke
riƙe da husnul muslim tana karanta addu'o'i.

Abdul kuwa yana kwance ne idanun shi a lumshe, a haka zaka zata barci yake yi
amma kuma idanun shi biyu.

Fuskar yarinyar jiya kawai yake gani, koda yayi ƙoƙarin kauda fuskar sai ya kasa
hakan yasa ya ƙara gyara kwanciya kawai.

Babu jimawa sosai Brr Hauwa ta fito cikin riga ja iya gwiwa da wando baƙi jeans,
kanta kuwa tayi rolling da ɓaƙin gyale yayinda ta sako ƙaton shade.

Dan kyau tana dashi kuma jikin ta baya nuna tsufanta domin macece me kwalliya,
kan kujera ta ajiye jakar sannan ta zauna itama tana gaishe da Iyayen nata.

Wayar Abdul tayi ƙara hakan yasa ya buɗe idanun shi sannan ya buɗe idanu, a
hankali ya zaro wayar ganin me kiran ya sashi sakin murmushi kafin ya ɗaga.

"Morning mom", daga can ɓangaren tace; "morning Baby ya ka tashi?", ya ɗan shafa
kanshi sannan yace; "yadda kika tashi haka na tashi mama na".

Tayi murmushi tace; "jiya na kira ka but u didn't pick d call hope kana lafiya
dai ko?", lafiya ta lau kawai at dat time nayi barci ne kuma ban duba call logs
ɗina ba yau da safe sorry".

"Never mind, yanzu zan wuce airport ga Sumayya nan yanzu driver zai kawo ta ita
da Adnan sannan idan na fita zan maka transfer na kuɗi domin bana so kan na dawo
kuɗin hannun ka su ƙare kazo kana complain".

"ba zan yi complain ba Mom kawai ki bari akwai enough kuɗi a waje na", cikin
basarwa tace; "mun canza shawara inaji idan na gama abinda nake yi zan wuce England
wajen Daddyn ku kawai sai mu taho tare dashi on monday".

Abdul yace; "hakan ma yayi, zamu baro rigasa ranar lahadi kenan?", Brr Farida
tace; "duk yadda kuka yi ma ya rage naku", yayi dariya kawai.

Itama dariyar tayi kafin tace; "bari na wuce sai ka sauka idan na saka sim zan
nema ka bye bye I love you".
'Love you too, take care", ta amsa da insha Allah", daga haka suka katse wayar,
yana me jin daɗi.

Brr Hauwa taja tsaki, Hajja da Malama dai babu abinda suka ce, Abdul yace; "Ina
kwana?", kamar ba zata amsa ba sai kuma tace; "lafiya lau", daga haka ta miƙe ta
fice.

Shima Abdul ya taɓe baki kafin ya miƙe ya fice, Gidan su Saleema ya nufa, kamar
yadda ya zata duk sun fice daga gidan sai Muhibba itama tana shirin fita.

"ina zaki je?", tace; "zanje gidan su Nihal ne dan kaga nan babu kowa", ya ɗan
shafa kanshi sannan yace; "fara taimaka mini da abinci tukunna", babu musu ta ajiye
gyalen hannun ta tayi hanyar kitchen shi kuma ya zauna saman Sofa wacce take falon.

Babu jimawa ta fito hannun ta ɗauke da tray, yam balls da kunun gyada sai Fried
egg da tea da kuma bread.

Sai da yayi bismillah sannan ya fara ci yayinda ita kuma Muhibba ta zauna tana
zuba mishi idanu domin yanayin cin abinci ma abin kallo ne cike da natsuwa.

Sai da ya gama ta maida kayan sannan ta fito, yana gaba tana bin shi a baya
ganin ya nufi hanyar fita daga Estate ɗin yasa tayi saurin tsayar dashi.

"Ya Abdul ina zaka ne?", sai da ya ɗan ja tsaki sai kuma yace; "akwai inda nake
son zuwa ne", ta langaɓar da kai tace; "ko nazo na rakaka ne?".

"jeki inda zaki je kawai", yana faɗin haka ya cigaba da tafiyar shi, ganin hakan
yasa Muhibba biyo shi da gudu, koda ta ƙarasa inda yake be kalle ta ba kawai ya
cigaba da tafiya a haka har suka fice daga gidan.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

Nusram ta gama shirin ta hankali kwance, ganin tana da sauran lokaci dan yau sai
bayan an sakko sallar juma'a zasu shiga makaranta.

Ta kalli Nusreen wacce ke kwance tana malelekuwa saman katifa kunnenta kare da
waya tana amsawa cike da farin ciki.

Nusram ta taɓe baki tace; "kinibabbiya ana so ana kaiwa kasuwa", Nusreen tayi
dariya tana juya idanu.

Nusram ta ɗora da cewa; "zan je in dawo yanzu ba zama zanyi ba munyi waya da
Idris yace mu haɗu a Juny Caft, ko zaki je ne", Nusreen ta girgiza kai kawai.

Nusram ta juya ta fice tana faɗawa Ummi sai ta dawo, Ummi ta bita da adawo
lafiya, kamar yadda suka shirya da Sahura akan zata fara yin gaba haka kuwa akayi.

A can saman layin nasu ta iske ta, Sahura ta bita da kallo itace ƙanwar su a
ƙalla shekara biyar zuwa huɗu tsakanin su amma ba zata nunawa Nusram ɗin ƙuruciya
ba.

Doguwar riga ta saka ta yadin rariya wacce aka yiwa ɗinkin gown ta buɗe sosai
fari ne yadin da ɗige-ɗigen ruwan goro,hijab ɗin data saka kalar goro ne hakan ya
ƙara haskaka kalar fatar ta.

Fuskar ta babu kwalliya sosai dan haka a washe take, sai lips ɗin ta data sakawa
man baki kalar orange me ɗan turuwa sosai tayi kyau.
"muje mana idan kuma kallo na zaki tsaya yi to bismillah", Sahura tayi dariya
kawai, me Keke Napep suka tare inda ya ɗauke su har can Sardauna crescent.

Sanda suka shiga caft ɗin yana zaune yana jiran su, koda ya gansu cikin farin
ciki ya miƙe tsaye.

Baƙi ne amma kuma babu laifi yana da kyau, idan ka ganshi yaro ne ba wani babba
ba, ga tsafta komai tsaf-tsaf hakan yasa Nusreen ke cewa ɗan daudu domin kuwa komai
nashi a tsaftace yake harma yaso yafi wata macen ƙyale-ƙyale.

A mutunce suka gaisa, sannan Nusram tace; "Idris kayi haƙuri naji duk abinda ya
faru daga bakin ta kuma nayi mata faɗa dan haka insha Allahu ba zata sake ba, kaga
zaman a gida bashi da wani amfani ka daure ka maida matarka kawai".

Idris cikin girmamawa yace; "shikenan babu komai Aunty amma idan wani abu ya taso
daga baya to gaskiya zan haƙura kawai".

Nusram tace; "insha Allahu babu abinda zai faru, zata kiyaye na gode sosai dan
Allah anjima kazo sai ka ɗauke ta".

Idris yace; "shikenan ta shirya ɗin idan na dawo daga kasuwa saina biyo mu tafi
amma ta sani wallahi mahaifiyar ta, idan ta faɗa mini mara daɗi tafiya ta zan yi".

Sahura tace; "ai bama sai ka shigo ba kana zuwa ka kira waya ta kawai zan fito",
Idris ya gamsu da hakan dan ya san wacece Mama Jummai.

"to yanzu me za'a kawo muku?", Nusram ta girgiza kai tace; "Alhamdulillahi a
ƙoshe nake sai dai ko matar taka".

Sahura ta riƙe haɓa tace; "ni ba zan iya cin wani abu a nan ba kawai dai na
gode", duka sai da suka yiwa maganar ta dariya, Nusram kam murmushi ɗauke a fuskar
ta, koda ta ɗago caraf idanun ta a cikin nashi.

Gabanta ne ya faɗi cikin sauri ta kauda kanta ƙirjinta na cigaba da dukan uku-
uku, ta kalli Sahura da suke faman fira tace; "to ni dai zan wuce idan kun gama ki
wuce gida kawai".

Sahura tace; "ina zaki je?", Nusram da duk ta gama tsorata da yanayin kallon da
yake mata tace; "zanje shagon Yaya Sulaiman ne ba zan jima ba zan dawo,sai anjiman
ku", tana faɗin haka ta bar wajen cikin sauri.

Abdul na ganin ta fita ya kalli Muhibba yace; "ina zuwa?", da sauri ta miƙe
tana faɗin; "ina kuma zaka je wanda muke jiran fa br ƙaraso ba", be kalle ta ba sai
ma key ɗin dake ajiye saman table ɗin ya ɗauka cikin sauri ya fice.

Koda ya fito nan ya fara dube-duben inda zai hango ta, can ya hange ta harta tare
abin hawa, dan haka cikin sauri ya nufi tashi motar.

Ganin hakan yasa Nusram ɗin tace da Me Keke Napep ɗin su tafi kawai ko gama dai-
daitawa basu yi ba.

"shi kuma wannan me tayi mishi da zai dami rayuwar ta haka?, oh na shiga uku ni
Nusram ko dai Aljani ne?", ita kaɗai take maganar ta.

Leƙowa tayi aikuwa ita yake bi domin motar shi na bayan tasu, kaɗan ya rage bata
yi suman zaune ba "idan kuma ɗan garkuwa da mutane ne fa?, to me nake dashi da har
zan damu kaina", haka dai take da wasi-wasi a ranta har suka ƙaraso inda zata
sauka.
Ji take kamar kada ta sauka, "Hajiya.mun ƙaraso fa", me Keken ya sake
maimaitawa, bata da yadda zata yi haka tayi shahada ta sauko daga ciki.

Ta miƙa mishi ɗari biyar ta ƙara gaba cikin sauri kamar wacce ake hankaɗawa, Me
keken na ta tsaya ta amshi canji amma ita bata wannan take ba.

Abdul dake hangen duk abinda yake faruwa dan haka ya fito ya jingina da jikin
motar yana kallon ƙofar shagon data shiga.

Me keke kuwa ganin bata kulashi ba yasa yaja keken shi yayi gaba abin shi.

Tana shiga tayi ajiyar zuciya tana me neman waje ta zauna tana maida numfashi,
kamar wacce tayi gudun fanfalaƙi haka take jin ta.

Sulaiman dake cikin ɗan ɗakin dake shagon yana hango ta dan haka yayi murmushi a
ranshi yana faɗin; "Nusram kenan sarkin tsoro", ganin ba zata ƙaraso bane yasa ya
miƙe ya nufo inda take.

"kamo ta nan", abinda ya faɗa kenan wanda yasa Nusram ɗin zabura tana neman
ficewa, Sulaiman ya kasa riƙe dariyar shi aikuwa ya dara.

Nusram ta sauke ajiyar zuciya ganin wanda ya tsorata ta sannan tace; "Kai Ya
Sulaiman dan Allah", shima cikin kwaikwaiyar yadda tayi yace; "Kai Nusram dan
Allah".

Ta shagwaɓe fuska kamar me shirin yin kuka, ya kauda kai yana dafe baki yace;
"Lalala babu ruwa na", yadda yayi ba ƙaramin dariya ya bata ba, tana dariya tana
tafiya zuwa inda table ɗin shi yake.

Har ta wani manta da ɗan garkuwar ta, wanda ya kusa sace ta🤣, Ya Sulaiman kuwa
cikin shagon ya shiga ya fara haɗo mata kayan da zata tafi dashi.

Sai da ya haɗa tas sannan yazo inda take, cike da wasa da dariya suka gaisa yana
yi yana tsokanar ta, wani tayi dariya wani kuma ta ƙyale shi.

"wai ina waccen me tsiwar ne?", ta san wacce yake nufi dan haka tace; "me tsiwa
yanzu tsuntsun so ke shawagi da ita a sama", ya ɗaga gira ɗaya ta jinjina mishi
kai.

Nan take bashi labarin yadda akayi da abinda Baba ya faɗa na ya bashi ita,
Sulaiman ya zaro idanu yace; "Babu bincike?".

Nusram cikin jimami tace; "kaima kamar ka manta halin Baba kenan?", Sulaiman
yayi ajiyar zuciya sannan yace; "zan so haɗuwa dashi kuwa inajin gobe na shigo
layin naku idan yaso duk abinda muka yi zan je na sami Abba shi zai san abin yi
akai amma ya za'a yi a ɗauki ƴa kamar wata kaza a bashi haka kawai to ko kaza ce ai
a bincika a gani ba ɓarawo bane", Nan dai yayi ta faɗan shi ita dai Nusram bata ce
komai ba.

"To ke kuma fa?, har yanzu?", Nusram cikin jimami ta bashi labarin abinda Isa ya
faɗa, a zuciye ya miƙe tsaye sannan yace; wallahi yayi ƙarya a ɗauki ƴa me asali a
bawa shege".

Nusram dama ta san hali, cikin zuciyar ta tace; "aifa abin nema ya samu", cikin
lallashi ta miƙe tace; "Ya Sulaiman nifa abinda nake so shine mu rabu lafiya ka san
yadda Baba ke son shi yana faɗa mishi Baba yarda zai yi".

Sulaiman yayi huci yace; "naga uban daya isa ya aura miki wannan ɗan iskan me
kama da mata-maza", Nusram kamar tayi dariya amma tana tsoro yanzu abin ya ƙare
akanta dan haka taja bakin ta tayi gum.

"to yanzu dai mu ajiye maganar Isa a gefe, ayi ta Shureim tunda zaka shigo gobe
zan faɗawa Nusreen ɗin sai tace yazo goben sai ku haɗu, yanzu bani kayan na wuce".

Ya galla mata harara, Nusram tayi murmushi tace; "haba Angon Aisha", shi kanshi
sai da ya murmusa sannan ya miƙe ya biyo ta.

Yana gaba riƙe da kayan tana bayan shi haka har suka fito waje, tana ɗaga idanu
ta sauke a kanshi aikuwa saura kaɗan ta faɗi saboda tsorata.

Wannan wane irin mutum ne ace duk wannan daɗewar yana tsaye yana jiranta, shi
kuwa Sulaiman bema lura dashi ba dan haka nesa dashi kaɗan suka tsaya.

Abin hawa ya fara wuya idan akayi la'akari da lokacin Sallah daya matso, sun
jima a tsaye kafin Sulaiman yace; "to kodai zaki koma shago ne ki zauna idan yaso
in mun sauko daga masallacin sai na kaiki ko kuma lokacin zaki sami abin hawa?".

Ta girgiza kai tana fadin; "a'a Yah Sulaiman kawai kaje masallacin ni zan tsaya
Allaha zai kawo kaga ana saukowa zamu wuce makaranta kuma bana so waccen tayi ta
jira na ka santa da ƙorafi".

Ya ajiye kayan sannan ya ciro dubu ɗaya ya miƙo mata yace; "shikenan sai anjima
idan kuma har an sauko kina nan to", ta amsa tayi godiya yayin da shikuma ya koma
shagon domin shiryawa.

Abdul da duk yana tsaye yana jin me suke cewa domin tazarar dake tsakanin su bata
yi nisa sosai ba sannan kuma hankalin shi gaba ɗaya yana kansu.

Nusram kuwa tsaye take amma kaɗan-kaɗan takan ɗago ta kalle shi, sai dai a yadda
yake zaka ɗauka wayar dake hannun shi yafi bawa mahimmanci.

Tayi ajiyar zuciya ganin ko kallon ta beyi ba sai dai ta makaro domin kuwa yana
kallon yadda duk ta wani tsargi kanta kamar mara gaskiya, minti biyar suna tsaye a
haka kafin ya ɗago sosai ya kalle ta shi take kallo amma ganin yana ɗago yasa tayi
saurin kauda kanta.

Kamar ta koma haka take ji, tana kallon shi ta gefen ido harya maida wayar shi
cikin aljihu sannan ya fara takowa zuwa inda take.

Ta kalle shi ganin ya nufo ta gadan-gadan yasa tayi saurin juyawa amma sai dai
kan tayi wani taku ya ƙaraso inda take.

Kayan hannun ta ya riƙo ganin taƙi saki yasa ya kalle ta, cikin sauri kuwa ta
saki, yayi murmushi sannan ya fara takawa zuwa wajen motar tashi.

Sai da ya kai kayan ya buɗe booth ya saka sannan ya juyo ya dawo, hannun ta riƙo
ta cije ganin hakan yasa ya fizge ta da ƙarfi, ko tayi ihu bashi da amfani domin
kuwa babu mutane sosai kasancewar duk sun tafi masallaci.

Shagon Sulaiman ɗin ma ya rufe domin kuwa ta ƙofar baya suke bi su tafi
masallacin tana ji tana gani ya buɗe motar ya saka ta sannan ya maida ya rufe ya
zagaya ya shiga.

Ita dai sai idanu babu baki ga kuma kirjinta dake dukan tara-tara,😂, haka har ya
tada motar bata iya ce mishi komai ba.

Ganin da gaske tafiyar zai yi cikin rawar murya tace; "dan Allah kayi haƙuri mu
bamu da wasu kuɗin da zamu baka Baba na talaka ne Mama na itama talaka ce dan Allah
ka kayi haƙuri ka sauke ni na tafi gida Mama na hankalin ta zai tashi haka ma ƴar
uwa ta, wallahi bamu da wani kuɗi rufin asiri kawai muke dashi".

Magan-ganun ta yake juyawa cikin ranshi, wato ita kallon me garkuwa da mutane
take mishi kenan?, be san lokacin da murmushi ya ƙwace mishi ba.

Ita kuwa ganin yayi murmushi yasa idanun ta kawo hawaye cikin sheshsheƙar kuka
tace; "idan kuma masu yin fyaɗe ne kayi haƙuri ka maida ni gida Baba na zai iya
kashe ni idan hakan ta faru Mama na kuma zata shiga damuwa sannan maganar idan ta
fita za'a iya fasa auren ƴar uwata dan Allah kada ka lalata mini rayuwa ka bata
sunan gidan mu kasa Mama ta sami abin yiwa Ummi gori",.

Ga abin dariya amma babu halin yi hakan yasa kawai ya maida hankalin shi kan
titi, ganin hakan yasa Nusram ta fara addu'a domin ta san yau tata ta ƙare cikin
uku za'a yi ɗaya ko dai yayi mata fyaɗe ko kuma ɗan garkuwa da mutane ne ko ɗan
yankan kai.

Ta ciro wayar ta a hankali ta kalla, Number din Nusreen ta nemo ta tsurawa


number ɗin idanu haka kawai taji wani kukan yazo mata shikenan ita kuma tata ta
ƙare.

Nima kaina nace; "Allah sarki Nusram RIP 😭.

#LIKE
#SHARE
#COMMENT
#VOTE
#FOLLOW @13deeja

*Babyn Abdul,Maman meenal, Elham da Farouk*.

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖21-22📖📖

Wayar dake gefen shi tayi ƙara ganin Muhibba ce me kiran wannan yasa ya dannan
amsawa, "Haba Abdul kana ina ne?", abinda ta faɗa kenan?.

"Abdul!", Nusram ta sake maimaita sunan a cikin ranta, inbox ta shiga ta rubuta
summary ɗin abinda ya faru harda sunan data ki wata ta kira shi.

Wayar na hannun ta tana juyawa tana me fatan koda ace ya kashe ta ne to wani ya
tsinta domin kuwa bata ga alamun wasa ba a fuskar shi.

"Nifa gani a hanyar gida kawai ki nemi abin hawa ki wuto gida", amsar daya bawa
Muhibba kenan.

Cikin jin haushi Muhibba tace; "haba Abdul amma dai ai hakan ba adalci
ban.......", kafin ta ƙarasa ya katse wayar.

Nusram data zuba mishi idanu, ta kauda kanta ganin sun ɗau titin da zai kai su
Hayin Rigasa yasa ta saki ajiyar zuciya har sai da ya juya ya kalle ta.

Dai-dai kwanar hanyar gidan nasu yaja ya tsaya wato inda ya bige ta, bece mata
komai ba itama ganin hakan yasa tayi shiru tana saƙe-saƙe a ranta.

Cikin ɗan ƙarfin hali ta kai hannu ta fara ƙoƙarin buɗe motar sai dai abin ban
haushi taƙi buɗewa hakan yasa kawai ta koma yadda take ta zauna.

Ta kalle shi, ba ita yake kallo ba kuma yaƙi ce mata komai, hakan yasa ta fara
murza zoben hannun ta.

Abdul dake kallon ta amma idan baka sani ba sai kace idanun nashi a lumshe suke
saboda yadda yayi, shi jira yake ta nuna mishi hanyar da zasu bi ita kuma ta kasa
fahimta.

Nusram ganin zaman yayi yawa yasa ta kada baki tace; "dan Allah ka buɗe mini na
fita", jin yayi shiru yasa ta sake kallon fuskar shi.

"so cute", abinda ta faɗa kenan ganin idanun shi a rufe, sai kuma tace; "very
arrogant", be san lokacin da murmushi ya suɓuce mishi ba wanda hakan ba ƙaramin
kyau yayi mishi ba.

Nusram kuwa idanu ta zaro tana me dafe ƙirji, ya buɗe idanun shi gaba ɗaya a
kanta, sosai ta daburce har jikin ta ya fara rawa.

"wai baki gaji da gani na bane da kika barni a nan?", abinda ya faɗa kenan,
yadda yayi maganar idan ba kana kusa ba, ba lallai kaji ba.

Nusram cikin in-ina tace; "to ai......to ai......to....ai kaine baka buɗe mini
ba", shima cikin kwaikwayar ta yace; "to ai......to ai.....to....ai kece baki faɗa
mini hanyar da zan bi ba".

Hannu ta ɗaga sannan ta nuna mishi hanyar shi kuma ya tada motar ya shiga, haka
tayi ta nuna mishi hanya har zuwa ƙofar gidan nasu wato lungu daga shi kana hango
gidan su.

Sai da ta fita sannan shima ya buɗe motar ya fito, boot ya buɗe ya ɗauko mata
jakar kayan sannan ya ƙaraso inda take tsaye.

Ita kuwa kallon shi kawai take yi tana yaba kyawun da Allah yayi mishi, mutum
kamar balarabe, yaran dake wasa a wajen su kansu duk shi suke kallo don ganin
balarabe a layin su.

Ya miƙo mata jakar kafin yace; "nifa bana son yawan kallo", cikin sauri ta amsa
sannan ta juya ta fara tafiya, Abdul kuwa yabi bayan ta da kallo, har tayi nisa
sannan ta tsaya.

Ta juyo ta kalle shi sannan tace; "na gode", ya jinjina kai kawai ita kuma ta
juya sai dai idanun ta yayi mata mugun gani domin kuwa Isa ne a tsaye a gaban ta.

Cikin masifa yace; "uban waye wancan daya ajiye ki", Nusram ta kauda kai gefe,
cikin takaici yace; "wallahi baki isaba domin baki da mijin da ya wuce ni", ya nuna
ta yace; "wato dan iskanci har yanzu baki bar bin maza ba kenan, kuma wai abin ban
haushi balarabe kika komawa to wallahi tun kan ki bar mana abin faɗa yau zanje na
sami Baba na faɗa mishi meke tsakanin mu".

Nusram cikin sauri tace; "amma Isa ai ban riga na amince ba ko", shima cikin
sauri yace; "wannan kuwa ke ta shafa", ya wuce ya barta a tsaye.

Ta juya a hankali ta kalli inda yake tsaye sai dai babu shi, wato ya tafi tun
ɗazu kenan?, taja ajiyar zuciya sannan ta shige gida.

Abdul kuwa yana ganin suna magana da wani mutumi yaja motar shi ya tafi, yana
tafe yana mamakin yadda har ya taimaki wannan yarinyar.

Koda ya isa gida har an sauko masallaci hakan yasa kawai ya wuce ɗakin Malama,
bayin ta ya shiga yayi alwala.

Yana fitowa ta kalle shi tace; "lafiya baka sami sallah ba?", ya ɗan sosa kai
sannan yace; "wallahi wani abu ne ya ɗauke mini hankali, kuma kan na iso an sauko".

Cikin haɗa rai tace; "ka maida hankali akan addinin ka, ka dena wasa dashi",
yace; "to Malama".

Da kanta ta shinfiɗa mishi abin sallah ya hau ya fara, Malama ta kalle shi tayi
murmushi.

Bayan ya idar da sallar ya juyo ya kalli Malamar yace; "Sumayya tazo ko?", tace;
"eh kana fita ɗazu ɓaka jima ba ta iso ina jin tana ɗakin Hajja ko kuma tana gidan
Mukhtar(Abban Nihal).

Ya jinjina kai kawai ba tare da yace komai ba ya haye saman gadon ta ya kwanta,
baya son zuwa gidan Abban Nihal Allah ya sani har cikin ranshi, a haka har barci
yayi awon gaba dashi.

Malama ta matsa kusa dashi tayi mishi addu'a, tana kallon shi cike da tsananin
ƙauna.

Har su Fadil suka dawo tana zaune kusa dashi ta kasa tashi ta barshi, Fadil da
Fadila suka kalli juna suna mamakin abinda Malama take yi akan Abdul kwata-kwata
bata son abinda zai taɓa shi tun suna ƙanana haka rayuwar take.

Fadil yayi gyaran murya da sauri Malama ta tashi daga kusa da Abdul, Fadila ta
nemi waje ta zauna saman center carpet din dake shinfiɗe tana faɗin; "wash wallahi
na gaji".

Fadil ya harare ta sannan yace; "kamar wani aiki tayi a office ɗin ina kallo fa
Hafeez ne yayi aikin kina gefe", tayi murmushi tana kauda kai gefe.

Sumayya ta shigo da sallama sannan ta ruga da gudu tana ihu, Fadil ya buɗe hannu
ta faɗa jikin shi.

Firgigit Abdul ya farka, cikin sauri ya dafe kai sannan ya kalle su yadda suke
ihu yaja tsaki.

Su kam bama su san yana yi ba, Fadil kuwa ya koma kamar wani yaro sai biye mata
yake yi, Abdul cikin jin haushin tashin shi da suka yi ya ɗauki filo ya cilla musu.

Sumayya ta kalle shi ta shagwaɓe fuska, ya cilla mata harara kan yaja tsaki ya
miƙe, Fadil kuwa dariya kawai yake yi dan ya san sun gama bawa Abdul haushi dan ya
tsani yana barci a tashe shi.

Bayin Malama ya shige, su kuwa bama ta shi suke ba dan haka suka cigaba da
hayaniya a ɗakin, inda Sumayya ke basu labari su kuma suna dariya.

Fadila tace; "ai ni kam naso zuwan Surayya ko dan na kwashi dariya", Sumayya
tace; "taɓ kema kin san Aunty Surayya ba zata zo ba sai dai Daddy idan ya dawo".

Fadila tace; "ai da yake Family meeting ya kusa zuwa nan da two months fa",
Sumayya tayi ihu tana faɗin; "yes gaskiya naji daɗi".

Abdul daya fito daga bayi yana nemi waje ya zauna ya dafe kanshi, Malama ta dafa
shi tana tambayar lafiya.

Yayi murmushi yace; "kawai hayaniyar wa'innan ne take damuna", Malama ta miƙe
tana murmushi kawai.

Sai da suka gama shirmen su sannan suka fice waje, Fadila ta kalli Abdul tace;
"wallahi har ɗakin yayi shiru", bece mata komai ba sai wata harara daya jefa mata.

Ya jima a zaune kafin ya miƙe ya fice, ɗakin su yaje yayi wanka sannan ya fito
falo inda su Sumayya suke a zaune.

****** ******* ******

Ɓangaren Nusram kuwa tana shiga gida kamar yadda tayi zato, Nusreen keta surfawa
Mama Jummai rashin kunya yayin da Mama Jumman take surfa mata zagi.

Nusram tayi ajiyar zuciya kan tayi sallama ta shiga gidan, Nusreen na ganin
Nusram tayi shiru sannan ta shige ɗaki.

Mama Jummai kuwa cikin hargagi tace; "shegiya mara kunya ai da kin fito kin
cigaba daga inda kika tsaya kuma ni nan na faɗa kuda aure wallahi sai dai kuga ana
yi", Nusram dake daf da shiga ɗaki ta juyo ta kalli Maman kan ta juya ta shige
ɗakin.

"kya juyo ki kalle ni mana shegu masu yawon ta zubar", Maman Jummai kenan wacce
ke sake cigaba da bambami.

Nusram na shiga ɗakin ta sami Ummi na zaune tana ƙulla man ja da man gyaɗa yayin
da Kubra ke gefen ta, tana wasa domin kuwa yanzu ta kan zauna har ma ta dinga wasa
da abinda aka bata.

Sannu ta yiwa Ummi sannan ta shige uwar ɗaki anan ta tarar da Nusreen tana ƙara
gyara fuskar ta, domin su tafi makaranta.

Jakar hannun ta ta ajiye sannan ta juya ta fice, alwala ta ɗoro tazo ta data
sallah sai da ta idar sannan ta kwashi litattafan ta sannan suka tafi.

Bata faɗawa Nusreen abinda ya faru tsakanin ta da Isa ba domin sanin hali yafi
sanin kama, hakan yasa taja bakin ta tayi shiru.

Basu baro makaranta ba sai yamma, Nusreen na rataye da jaka inda Nusram ke
rungume da littattafai haka suka jero.

Suna karyo kwanar lungun su suka hango Mahaifin nasu tare da wani mutumi wanda
yake tsaye jikin motar shi.

Nusreen da Nusram haka suka gaishe da baƙon baban nasu, hakan Baban nasu yayi ta
washe baki shi kuwa baƙon bin su yayi da idanu kamar wani maye har lashe baki yake
yi.

Suna shigewa gidan ya haɗiye yawu sannan ya kalli Baban su Nusreen ɗin, Baban
yace; "kayi haƙuri Alhaji Baballe insha Allahu nan da ƙarshen wata zan haɗo maka
kuɗin ka".

Alhaji Baballe ya girgiza kai yace; "a'a Malam Abdullahi dan dai dubu ɗari ai ba
zai gagara na bar maka ba dan haka ni yanzu wata magana nake so muyi da kai".

Malam Abdullahi yace; "ina jin ka Alhaji", Alhajin yace; "wa'innan ƴan shilan
ƴaƴan waye ne?", Baba yace; "wai Nusreen da Nusram ƴaƴa na ne ka gansu nan sai dai
garari a gari babu wanda yazo domin auren su na rasa yadda zanyi dasu".

Alhaji Baballe ya washe baki yace; "to ai ni dai in dai ba'a musu miji ba sai ka
aura mini ɗaya daga cikin su kawai", Baba ya washe baki yace; "aikuwa na gode da
wannan alfarmar da zaka yi mini, sai dai Nusram da ita Nusreen wani yazo kwanaki
duk da akwai yarjajeniya a tsakanin mu".

Alhaji Baballe yace; "koma wacece ni dai a cikin su ina son ɗaya", Baba yace;
"in dai Nusram ce na baka sai dai mu jira lokaci kawai".

Alhajin yace; "ka tambayi yarinyar kada yazo bata amince ba dan itama tana da
haƙƙi a kai", Baba ya ja tsaki yace; "ba dai kana son ta ba ai magana ta ƙare".

Alhaji Baballe yace; "a'a fa kada a takura mata dan ka san yaran yanzu ka dai
tambaye ta idan ta amince sai ka sanar mini ina jira".

Baba ba dan son ranshi ba yace; "shikenan zan tuntuɓe ta ɗin", haka suka yi
sallama da Alhajin sannan Baban ya wuce masallaci jin an fara kiraye-kirayen
sallah.

Cikin gidan kuwa suna shiga Nusreen ta ja tsaki tace; "banza maye kawai", Nusram
dai bata ce mata komai ba.

A bakin ƙofa suka sami Ummi tana kwashe abincin data gama nan suka yi mata sannu
da zuwa.

Ummi cikin farin ciki tace; "yauwa sannun ku ƴan mata na, yau da alamu anyi
ciniki kenan naga babu ko ɗaya da kuka dawo dashi".

Nusreen ta miƙawa Ummi kuɗin tana faɗin; "gashi ki ajiye wallahi kaya yau sunyi
kasuwa gaskiya yau Yaya Sulaiman ya bamu kaya designer".

Nusram kuwa tsintsiya ta ɗauka ta hau shara, sai da ta gama sannan ta ɗauki buta
domin yin alwala.

A bakin famfo ta sami Sahura, Nusram tace; "ke ina Idris ɗin?", Sahura tayi
dariya tace; "yana nan mana amma mun canza shawara sai gobe zai zo domin yace yana
so na ɗan gyara kafin na koma".

Nusram tayi dariya tace; "ah lallai kace sababbin ango da amarya kuke kenan?",
duka suka kuma yin dariya.

Sahura tace; "dan Allah gobe idan baki da ayyuka masu yawa sai ki yi mini ƙunshi
da kitson ko?", Nusram tace; "shikenan Allah ya kaimu amma kuɗin dubu biyar",
Sahura ta riƙe haɓa tace; "ai wannan tsakanin ke da ƙanin ki", Nusram ta harare ta
tace; "kinji wani daɗin baki".

Nusram ta kuma cewa; "amma ya kamata a yau ki faɗawa Baba da Mama kada su ga
kawai kin bi mijin ki gobe", Sahura tace; "shikenan sai yadda kika ce haka za'a
yi", daga haka Sahurar ta bar wajen.

Nusram tana idar da sallah kiran mahaifin nasu ya iso kunnen su, Nusreen ta
taɓe baki tana faɗin; "wallahi matsalar gidan nan yawa yake dashi".

Duka suka miƙe suka fice, ɗakin Mama Jummai zasu je kuma harda Ummi, tun daga
ƙofar ɗaki suke jiyo bambamin Maman.

Haka suka yi sallama suka shiga, Mama tace; "yauwa ku shigo ina kinibabbiyar
take har ta san ta sasanta tsakanin miji da mata".

Gaban Nusram ya yanke ya faɗi, ko daga ji ta san da ita take, suna zama Baba
yace; "Ina Nusram?", Nusram tace; "gani Baba".

Baban yace; me yasa kika haɗu da Idris har kike neman juyar mishi da tunani?",
Sahura ta yi tsagal tace; "Baba wallahi ba haka aka yi ba nina same ta nace ina son
na koma gidan miji na shine taje ta bashi haƙuri ni kuma tayi mini faɗa".

Baba yace; "oh har kin kai girman da zaki sasanta aure kenan?", Nusram ta
girgiza kai tana faɗin; "kayi haƙuri Baba ita ta same ni da maganar".

Baba yace; "shikenan kin hutar dani ne kuma dama zaman nata ya ishe ni, magana
ta gaba da nake so muyi shine akan ku", ya faɗa yana nuna Nusram da Nusreen.
"ɗazu kun wuce ni da Alhaji Baballe, kun dai san shine manager a inda nake aiki
to ya nuna yana son na bashi ɗaya daga cikin ku, na dai faɗa mishi Nusreen akwai
wanda na bawa ita to ke Nusram tunda baki da kowa ke na bashi dan haka sai ki
shirya ina ganin gobe ko jibi zai zo sai ku ƙara fahimtar juna, kuma na faɗa musu
duka su biyun bana so bikin naku ya wuce wata ɗaya to amma dalilin shi Shureim wato
manemin Nusreen ya bada uzurin mahaifiyar shi da bata ƙasar to hakan yasa na ɗaga
ƙafa amma duk da haka bana so ya ɗara wata biyu nan gaba".

Mama Jummai tace; taɓɗijam yanzu Abdullahi auren su Nusreen ɗin za'a yi lallai
da sake", Baba yace; "me za'a sake ɗin, ai.magana ta ƙare nine mahaifin su kuma na
tsayar musu da miji dan haka nan da ɗan lokaci kaɗan wallahi zasu bar gaba na haba
na gaji kullum ni kenan ana zagi na babu dama na saka sabon kaya sai kaji ana cewa
dama na bar yara a gaba na sunki aure ai dole na dinga shiga ina fita to wallahi ya
isa haka dan haka aurar dasu babu fashi kai koda da almajirai ne sai na aurar
dasu".

#LIKE
#SHARE
#COMMENT

*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

🎶🎶🎶
*Idanu na tsimin su ganka, Abdul kana ina*🎶🎶🎶

🎶🎶🎶
*Baki ya yawaita ambatan ka, hannu ya jinjina*🎶🎶🎶

🎶🎶🎶
*sanya mini shinfiɗa ta fuska, bango na jingina*🎶🎶🎶

🎶🎶🎶
*Abdul in zaka zo ka wulga, nima ba zan ƙi waiwaye ba*🎶🎶🎶

📖📖23-24📖📖

Nusreen ta zunɓuro baki sannan tace; "haba Baba muna ƴaƴan ka amma ka gaji damu,
ai wannan babu adalci a ciki, gaskiya ni wallahi ba zan yarda ba aure kamar wasu
kaji......", Baba ya kai mata duka cikin sauri ta kauche.

Yace; "wallahi Nusreen tsakanin ni da ke zanga wanda ya isa da wani", bayan Ummi
ta shige tana ƙunƙunai.

Mama Jummai ta taɓe baki tana faɗin; "zan san abin yi don ba zai yiwu ba", babu
wanda yabi ta kanta, Baba ya miƙe yana faɗin; "na riga da na gama magana".

Ummi ta miƙe haka Nusreen, Nusram kuwa ta daɗe zaune ko kanta bata ɗago ba tana
tunano halin da zata shiga, cikin dabara ta goge hawayen idanun ta domin bata so
Aziza da Ameera su gani.

A bakin ƙofa taci karo da Mama Jummai ta kalle ta tace; "ai wallahi da sake,
zaman gida be ƙare muku ba tukunna dai", Nusram cikin jin haushi tace; "ai bake
bace Allah" faɗar haka ta wuce ta bar Mama Jummai a tsaye.

Mama Jummai kuwa bata kuma cewa komai ba domin Allah ya sani tana tsoron Nusram
idan har tayi zuciya dan bata da sauƙi.

Tana shiga ɗaki ta tarar da kowa na harkar shi dan haka itama zama kawai tayi,
Nusreen ta dawo kusa da ita tace; "Ramluv ki kwantar da hankalin ki babu wanda zaki
aura sai wanda kike so kinji".

Nusram ta kalleta tace; "to yanzu waye yace miki bana son shi?", wani kallo
Nusreen ɗin ta yiwa Nusram sannan tace; "Ramluv kada ki cuci kanki, na san
cew......" da sauri Nusram ta ɗagawa Nusreen hannu sannan tace;

"Rim dan Allah ki rabu dani barci nake ji haka", sanin halin Nusram ɗin yasa
Nusreen miƙewa ta koma kusa da Ummi ta zauna.

Nusram kuwa ganin haka yasa ta miƙe ta shige uwar ɗaka, kan katifar su ta faɗa
sannan ta saki ajiyar zuciya, ita bata taɓa ganin rashin adalci irin wannan ba taya
za'ace anyi aure kalar wannan?, hawaye suka gangaro daga idanun ta.

Tana ji lokacin da Nusreen ɗin ke waya da Shureim baya ta shigo ɗakin ta kwanta,
har suka gama Nusram bata bar zubar da hawaye ba domin kuwa abin yayi mata yawa, ji
take kamar ta gudu ta bar gidan.

Nusreen tana gama wayar ta juyo tana me haska bayan Nusram ɗin sannan a hankali
tace; "Ram!", haka ta kuma kiran sunan amma shiru Nusram bata amsa ba, ganin haka
yasa ta ja bakin ta tayi shiru domin ta sani yanzu tana misbehave sai ta daku a
hannun ƴar uwar tata.

Nusram kuwa tana jin Nusreen ɗin amma tayi banza da ita domin bata so Nusreen
ɗin.ta gane halin da take ciki wannan zata barwa cikin ta ne don wata dama ce da
Allah ya bata domin ƙubucewa daga hannun Isa sannan kuma domin bawa Nusreen ɗin
damar yin aure.

Duk yadda barci ya iya sata a daren nan sai da ya bar Nusram ta kuma sha kuka har
ta ƙoshi sannan ta kaiwa ubangiji kukan ta domin shi kaɗai zai iya share mata
hawaye.

Ummi kuwa duk abinda Nusram keyi tana sane dashi, wannan yasa ta ƙudurce a ranta
idan har Nusram ɗin bata son wannnan Alhajin to dole ne tayi fito na fito da Baban
nasu akan wannan hukuncin domin ba zata so ƴaƴan ta su fuskanci irin abinda take
fuskanta ba a gidan auren ta barin ma Nusram wacce take da zurfin ciki da kuma
haƙuri.

Nusram koda tayi sallar asuba komawa tayi ta kwanta domin kuwa barcin dama ba'a
cin bashin shi a zauna lafiya.

Nusreen shigowar ta uku kenan domin ta tashi Nusram ɗin ta karya amma abu ya
gagara, zama tayi gefen katifar tasu sannan tace; "Ram dan Alƙah ki tashi", kamar
ma bada ita take ba.

Nusreen ta bubbuga filon da Nusreen ɗin ta ɗora kanta a kai, a matuƙar kasala
Nusram ɗin ta buɗe idanu sannan tace; "Pls ki ƙyale ni haka ma Nusreen", Nusreen ta
cuno baki tace; "Ummi tace ki tashi fa, ga abin karin ki har yayi sanyi".

Nusram ta kuma maida idanun ta ta rufe kawai ta cigaba da kwasar barcin ta,
ganin hakan yasa Nusreen miƙewa.

Nusreen ɗin na cikin shiryawa Sahura tayi sallama ta shigo, Nusreen ta amsa tana
me cigaba da abinda take yi, Sahura tace; "Nusreen ko Nusram", Nusreen taja tsaki
hakan ya alamtawa Sahurar ko wacece.

"Ina Nusram take?", cikin masifa Nusreen tace; "kin bani ajiyar tane?", Sahura ta
ja tsaki ta juya wajen Ummi tace; "Ummi Nusram fa?", Ummi tace; "tana ciki tana
barci ko tashi bata yi ba har yanzu".

Sahura tayi hanyar uwar ɗakin, tana shiga ta fara tashin Nusram ɗin, haka dole
tasa ta miƙe sannan ta kalli Sahura tace; "me kuma ya faru", Sahura ta washe baki
tace; "lallai da kitso mana".
Nusram ta dafe kai tace; "wallahi na manta gashi barci nake ji sosai", Sahura
tace; "dan Allah kizo kiyi mini", Nusram tace; "to bari na karya", haka Sahura ta
miƙe ta baro ɗakin.

Babu jimawa itama Nusram ɗin ta fito tana zabga hamma, nan ta gaishe da Ummin
sannan ta fita tayo brush ta dawo, Nusreen tace; "to ni dai na tafi".

Nusram dake ƙoƙarin kai kunun bakin ta tace; "ina zaki je?", Nusreen tace;
"zanje Tudun Nufawa Yaya Sulaiman yana nema na", Nusram ta sauke kofin daga bakin
ta tace; "a dawo lafiya", Nusreen ɗin ta amsa da ameen tana me ficewa daga ɗakin.

Sai da Nusram ta gama karyawa sannan ta miƙe ta cewa Ummi; "bari naje na siyo
Lallen da zan yiwa Sahura", Ummi tace; "a dawo lafiya", doguwar riga ce a jikin ta
kalar ruwan ƙasa ta ɗora hijab ruwan madara a sama ta fice.

******** *********

Kamar yadda suka saba a saman dinning suka tarar da ƴan gidan, haka suka bi su
ɗai-ɗai suka gaishe dasu, kowa ya amsa musu amma banda Brr Hauwa.

"lallai Farida ta samu sake idan banda haka mu data guje mu meye na turo mana
yaran ta suzo su zauna damu?".

Fatima tace; "wai meye haka ne Brr abinda kuke yi sam be dace ba", da sauri
Hajja ta katse ta sannan tace; "faɗa mini abinda be dace ɗin ba?", Fatima ta juyar
da kai sannan tace; "ni na tafi", Hajja taja dogon tsaki.

Babu wanda ya kuma magana tsakanin su banda cin abinci da suke yi, Abdul kuwa
wayar shi ce a hannun shi yake dannawa.

Hajja ta kalle shi tace; "kai kuma ba zaka ci abincin bane", ya miƙe cikin sauri
domin abinda Brr Hauwa ta faɗa ya bashi haushi yace; "Idan zan ci zanje gidan Abban
Fadil naci".

Ai kamar ya ƙara zuga ta ne nan ta hau sababi, "tunda shi Jabeer ɗin uban ka ne
ai dole kaje gidan shi", Abdul kam hannun Sumayya ya riƙe ya fincike ta dole ta
tashi ko gama cin abincin bata yi ba.

"to sake ta ta dawo taci abinci", abinda Brr Hauwa ta faɗa kenan, kamar be ji ta
ba haka ya cigaba da tafiya, taɓ ai ji tayi ya gama raina mata hankali tana magana
yayi banza da ita a gaban yara ƙanana kan ta buɗe baki ta kuma magana ya fice hakan
yasa itama ta miƙe cikin fushi ta kwashi kayan ta.

Suna tafe yana tunanin halin gidan su ya rasa meke tsanin su da Mom ne haka da
yayi zafi har haka?.

Koda suka shiga gidan kusan kamar ko wane lokaci babu kowa ya zaunar da Sumayya
saman kujera sannan ya nufi sama.

Yana ƙoƙarin shiga tana ƙoƙarin fita, da sauri suka ja suka tsaya, a tare suka
saki murmushi me ƙayatarwa, Abdul ya bita da kallo tun daga sama har ƙasa.

Tana sanye da doguwar riga, Dubai abaya kalar ruwan kasa me haske, kanta kuwa
blue ɗin mayafi ne wanda tayi rolling dashi, ƙaramin gilashi ne maƙale a idanun ta
wanda yawancin likitoci suke sakawa.

Hannun daman ta saƙale da riga ta aikin su, sai kuma hagun ta inda take riƙe da
ƙaramar jakar ta da kuma wayar ta babu abinda ke tashi a jikin ta banda ƙamshi.
Ya langaɓar da kai, Saleema ta zuba mishi idanu fuskar ta cike da annuri na
ganin ƙanin nata kuma masoyin ta abin ƙaunar ta.

"yau kam zan iya cewa nafi kowa sa'a", ta faɗa cikin sanyin murya wanda kusan
halin ta kenan, ya saki ƙayataccen murmushi kan yace; "ni kuma gashi yunwa nake ji
balle ma na tantace na tashi a sa'a ko akasin hakan".

Ta ɗan zaro idanun ta sannan tace; "me yasa baka kira ni ba da yanzu na haɗa maka
ai", ya kauda kai sannan yace; "gashi kuma naga kin gama shiri da alama direct sai
wajen aiki, bari kawai insa Hanne ko Muhibba su dafa mini", ya ƙarasa yana ƙoƙarin
juyawa.

Cikin sauri ta riƙo hannun shi tana faɗin; "ayya ba za'a yi haka ba gaskiya bari
na shiga kitchen ɗin na sama maka abinda zaka ci", tana gama faɗar haka ta nufi
downstairs da sauri, Abdul yabi bayan ta yana me jinjina irin soyayyar da take yi
mishi.

Saleema ta ƙara washe baki ganin Sumayya a zaune, Sumayyar ma cikin farin ciki
ta gaishe da yayar tata, nan Saleemar ta barsu ta wuce kitchen domin sama musu
abinci.

Sumayya ta matso kusa da ɗan uwan nata sannan ta miƙa mishi wayar tana faɗin;
"Ya Abdul kalli motar da Daddy ya siya muku".

Amsa yayi yana kallo, motoci ne guda uku masu kyau sosai, ɗaya baƙa ɗaya ruwan
ƙasa ɗaya ja, ya miƙa mata yana faɗin; "na san dai baƙar suka bar mini ko?".

Sumayya cikin alhini tace; "babu yadda Mummy bata ba akan Ya Tameer ya bar maka
wannan amma ƙememe yaƙi bar maka wai ita yake amma naji Mummy tace zata maka order
ɗin wasu guda biyu", ya jinjina mata kai kawai ba tare da yace komai ba.

Wato ya san da biyu Ya Tameer ya zaɓi baƙar ya bar mishi ja domin ya san yadda ya
tsani mota ja, haka kuma kowa a gidan ya san Tameer ɗin ke son mota ja har ma su
kan tsokane shi da kalar mata ce, amma shine ya zaɓi baƙa kawai dan ganin ya ɓata
mishi rai.

"Ya amma gobe ba da wuri zamu tafi ba ko?", Sumayya ta katse mishi tunanin da ya
tafi, ya ɗaga kai kawai, sun cigaba da fira inda yawanci kawai ɗaga mata kai Abdul
ɗin yake yi domin tunanin shi baya kanta yana kan wannan yarinyar ta jiya.

Saleema ta fito hannun ta ɗauke da tray, da sauri Sumayya ta tashi ta amso ta,
Sumayya tace; "sannu Aunty Saleema da aiki ai da kin saka Hanne".

Saleema tace; "kada ki damu ƴar ƙanwata kun wuce kuci abincin Hanne a waje na
bayan ina gidan", ta ƙarasa tana kallon Abdul ɗin wanda shima idanun shi yana kanta
domin ya san akan shi take maganar ba wai dan Sumayya ba.

Yayi murmushi sannan yace; "aikuwa mun gode da wannan karramawar, kuma munji
daɗi sosai, abinda zamu ce kuma shine adawo lafiya", ta saki murmushi tana ɗaga
musu hannu ta fice.

Tare suka ci abincin kamar suna gida suna yi suna fira wacce bata da hayaniya
sosai, a haka Mummyn ta fito ta tarar dasu nan suka gaishe ta, da yake itama da
shirin office ta fito hakan yasa ta wuce su kawai.

Ya miƙe tsaye itama Sumayya haka ya kalle ta yace; "ni zan fita kije wajen Nihal
na san tana nan", daga haka ya juya ya fice.

Motar Fadil yaje ya ɗauka sannan ya fice daga Estate ɗin gaba ɗaya, wajen Akram
yake so yaje wanda zasu haɗu a jiya amma saboda Nusram basu samu damar haɗuwa ba.

Har ya gifta ya hango kamar ita a tsaye a bakin titi, sai fama duba waya take
wanda alamu ya nuna sauri take kuma bata samu mota ba, a hankali ya fara dawowa da
baya da baya har yazo kusa da inda take.

Yana sauke glass ɗin suka haɗa idanu, Nusreen ta ja ƙaramin tsaki tana me kauda
kai, Abdul kuwa abin ya bashi mamaki, a jiya tsoron shi yake gani a idanun ta amma
a yau kuma yaga masifa da tsiwa kawai ke cin ta.

Ya jima a haka ita bata waigo ba shi kuma be wuce ba, Abdul ya kuma juyawa ya
kalle ta, Atamfa ta saka me ruwan ganye da ratsin ja da fari haka Hijab ɗin jikin
ta fari ne, tayi kyau sosai domin kuwa fuskar nan ta ɗauki kwalliya.

Abdul ya taɓe baki domin ganin shi jiya tafi kyau don jiya babu kwalliya a fuskar
ta, ya duba agogon hannun shi sannan ya buɗe motar ya fito.

Gaban ta ya je ya tsaya, Nusreen kuwa kamar bata san dashi a wajen ba duk da
yadda gaban ta ke faɗuwa dan yana yi mata kwarjini sosai.

Abdul kuwa cikin bada umarni yace; "shiga muje", wani shegen kallo Nusreen ta
wulla mishi kan tace; "sannu Malam Abdullahi🙊".

Abdul ya kafe ta da ido yayin da Nusreen ɗin taƙi yarda su haɗa idanu, hannu ya
kai zai riƙo nata da sauri taja baya sannan tace; "wallahi ka sake ka ɗora hannun
ka saman jiki na sai nayi maka ihun kwarto", sosai hakan ya bashi mamaki kan yace
wani abu motar Shureim ta tsaya kusa dasu.

Shureim ya fito cikin sauri yace; "afuwan Sarauniyar mata wallahi na ɗan tsaya
amsar saƙo ne", Nusreen ta cilla mishi harara sannan tace; "ka kyauta daka shanye
ni a nan har wasu marasa ilimi da hankali suke tunanin ko ni ɗin ina da araha har
haka", ta ƙarasa tana kallon inda Abdul ke tsaye wanda tun lokacin da Shureim ya
ambaci Sarautar mata yaji wani abu ya daki zuciyar shi.

Shureim ya kai kallon shi inda Abdul yake, cikin sauri ya ƙarasa yana miƙa mishi
hannu; "barka da hutawa yallaɓai", Abdul yayi murmushi yace; "Shureim dama kana nan
shine ko ziyara babu".

Shureim ya shafa kai yace; "kayi haƙuri yallaɓai wallahi abubuwa ne sun yi yawa
sannan ban jima da dawowa najeriyar ba don ina Egypt karatu".

"ina Ammie? Fatan tana lafiya", Abdul ɗin ya tambaya, Shureim yace; "Ammie tana
Syria wallahi ciwon ƙafa ne ya matsa mata".

"ayya amma ya ƙafar yanzu", Abdul ɗin ya tambaya, Shureim yace; "eh to wai
likitan da ake saka ran zaiyi mata aiki ne sai nan da kwana uku zai dawo Dr John
Burlin".

"John Burlin ai na san shi ka bari zan kira shi sai a san yadda za'a yi aikin",
nan fa Shureim ya fara godiya.

Nusreen ta baje hanci da baki tana kallon su bata yi tunanin sun san juna ba,
ganin abin bana ƙare bane yasa tace; "wai Habibi a waje zaka barni ne ko kuwa zaka
wuce muje?", da sauri Shureim yace; "Afuwan Sahiba shiga muje", ya faɗa yana me
buɗe mata ƙofa sai da ta harari Abdul ta ƙasan ido sannan ta shige.

Shureim ya kalli Abdul yace; "yallaɓai mun gode sosai Allah ya saka da
alkhairi", babu abinda Abdul ya iya samun dama banda ɗaga mishi kai da yayi, yana
kallo Shureim yaja motar ya tafi.
Abdul ya buɗe motar shi ya shiga sannan ya kifa kanshi saman sitiyarin motar,
babu abinda ke mishi yawo a idanu banda meye haɗin Shureim da wannan yarinyar?.

"ai amsar a fili take saurayinta ne", zuciyar shi ta bashi amsa, da sauri ya
furta; "Impossible!", sai kuma wata zuciyar tace; ina ruwan ka ne?", ya ɗaga kafaɗa
alamun babu haka yaja motar shi ya bar wajen.

Nusreen bayan sunyi nisa ta kalli Shureim tace; "meye haɗin ka da wancan?",
Shureim yace; "lokacin da mahaifina yake da rai a ƙarƙashin mahaifin shi yake aiki,
ke kuma meye haɗin ki dashi", ya dawo mata da tambaya.

Nusreen ta taɓe fuska tace; "babu komai ni ban ma taɓa ganin shi ba sai yau",
Shureim yayi murmushi kawai domin sanin halin Nusreen ɗin.

Abdul kuwa koda ya ƙarasa wajen abokin shi Akram ɗin kasa zama yayi dan haka ya
miƙe yana faɗin; "ina ji gida zan koma kawai".

Akram ɗin ya miƙe yana faɗin; "haba Abdul yaushe kazo da har zaka koma?, gashi ko
maganar da zamu yi ma bamu gama ba", Abdul ya ɗan ja tsaki sannan yace; "kada ka
damu idan na dawo next time zamu yi maganar".

Dole haka Akram din ya rako shi har wajen masana'antar, tuƙi kawai yake yi amma
hankalin shi naga Shureim da kuma wannan yarinyar ya rasa me yasa abin ya tsaya
mishi a rai.

Yana zuwa dai dai layin kamar ance ya kalli hanyar ya hango ta sanye da doguwar
riga me ruwan ƙasa da kuma hijab kalar ruwan madara.

Cike da mamaki yake binta da kallo to ko dai aljana ce amma abin da mamaki a
yadda yaga tafiyar su ya tabbatar inda zasu je ma da wuya idan sun kai balle har su
dawo.

A hankali ya fara bin bayan ta har zuwa ƙofar gidan nasu wato lungun da zaka iya
hango gidan su, Nusram da bata san ana bin ta ba ta shige gidan hannun ta riƙe da
ledar data siyo kayan lalle wanda ta san zata buƙata wajen yiwa Sahura.

#LIKE
#SHARE
#COMMENT

*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖25-26📖📖

Abdul na ganin ta shige gida ya juya da kan motar shi ya fita a layin, lallai
akwai wani abu a tattare da yarinyar amma ko meye zai yi ƙoƙari ya gano shi.

Nusram kuwa tana shiga gidan ta tarar Sahurar na jiran ta, dan haka ruwan dake
saman murhun su ta juyo, yayin da Nusram ta shiga ɗaki ta ɗauko haɗin man da take
wanke kai.

Sai da ta fara shafa mata haɗin Kanumfari da Kaltufah, ta saka leda ta rufe
sannan ta ɗauko abin lallen ta fara kwaɓawa, sai da kan yayi tsayin minti goma sha
biyar sannan ta buɗe kan, ta ƙara tajewa kafin suka je bakin famfo ta wanke mata.

Kan yayi kyau sosai dan babu laifi Sahurar ta ɗan kwaso dangin mahaifin nasu,
Ameera ta Kalli Aziza ganin yadda kan yayi kyau yake kuma sheƙi.

Sai da ta tsane kan gaba ɗaya sannan ta ɗauko haɗin mayukan musulunci, Man
zaitun, man hulba, man habbatus-saudaa, man maciji da kuma ɗigon man ayu, ta ware
mata kan tana shafawa tana tajewa haka tayi har kan ya saki sannan ta naɗe mata
gashin inda take so ko'ina man ya shiga, idan kaga gashin Sahura a lokacin zaka
ɗauka taje wajen masu wanke kai ne.

Ita kanta sai da ta kasa yin shiru tace; "Nusram Allah kuwa da zaki buɗe wajen
gyaran kai da jiki ko ba ƙaramin ciniki zaki yi ba", Nusram tayi murmushi kawai ba
tare da tace komai ba.
Jan lalle ta fara tsantsara mata, sannan ta ɗora mata baƙi a sama, kan wani
lokaci ta gama zana mata lallen, sannan ta ɗauko kibiya ta hau yi mata kitson.

Mama Jummai dai sunyi sa'a dan ko kallon inda suke bata yi ba, aikin gaban ta
take yi wato ƙoƙarin ɗora abincin siyarwar ta kenan take yi domin rana ta fara yi.

Ƙananan kitso Nusram ɗin ta yarfawa Sahurar wanda yayi kyau sosai, kan wani
lokaci sun gama domin kuwa Nusram ɗin tana da sauri akan ayyukan nata.

Tashi tayi taje tayi Alwala sannan ta shige ɗaki inda ta bar Sahura a zaune
domin barin ƙunshin nata ya ƙara ja, koda Nusram ta idar da sallah sannan ta ɗebi
abinci.

Tana ci tana yiwa Kubra wasa wacce itama kwanon abincin ke gaban ta, duk ta
watsa shinkafar a ƙasa.

Ummi ta kalli Nusram sannan tace; "ina so ki faɗa mini gaskiya Nusram shin kina
son wannan auren da mahaifinku zai muku?".

Nusram tayi murmushi tace; "Ummi me kika gani?, nifa wannan be dame ni ba kuma
ina farin ciki ko babu komai zan bar gidan nan sannan ƴar uwa ta ma Allah ya cika
mata burin ta wato zamu yi aure lokaci ɗaya".

Ummi ta kuma cewa; "amma ai ya kamata ki tabbatar da cewa kina son shi kafin
auren bana so kiyi abinda zaki yi nadama sannan bana so ki fuskanci matsala a gidan
auren ki".

"Insha Allah Ummi ba zan fuskanci wannan matsalar ba, zan yi farin ciki kamar
yadda kike mini burin yi", abinda Nusram ɗin ta bawa Ummi amsa kenan.

Ummi tace; "shikenan tunda haka kika ce Allah ya baku zaman lafiya, amma ki sani
shi aure ba abin wasa bane idan har kun haɗu kinji bakya son shi to ki sanar dani
ni kuma zan yi iya ƙoƙari na wajen ganin ba'a ɗaura wannan auren ba".

Nusram ta riƙo hannun Ummi tace; "kada ki damu kanki Ummi, Insha Allahu zan so
shi kamar yadda kowacce mata ke son mijin ta", ba don Ummi ta yarda da abinda
Nusram ta faɗa ba ta ƙyale ta.

Sai wajen biyu sannan Nusram ɗin taja ruwa a rijiya inda ita kuma Sahura ta
miƙe taje wajen ta, Nusram da kanta ta wankewa Sahurar lallen sannan ta shafa mata
muhallabiyya aikuwa yayi kyau sai shinning yake yi.

Sahura sai washe baki take yi ganin yadda tayi kyau sosai ga wani ƙamshi da
tafin hannun nata yake yi, domin dai kowa ya san ƙamshin muhallabiyya akwai daɗi
sosai.

Koda ta shiga ɗakin su da murnar ta ta nunawa Mama Jummai, Mama Jummai tace;
"na fani yayi kyau sai dai ki cirewa ranki komawa gidan Idris".

Sahura ta turo baki gaba kafin tace; "amma ai Baba ya yarda ko?", Mama Jummai
taja tsaki tace; "ai ya yarda ne saboda kada ya dinga cefane dake, yau Alhajin da
zai auri Nusram zai zo don haka ina so ki san yadda zaki yi ki ɗauke hankalin shi
daga kanta".

Sahura ta kalli Mama Jumman sheƙeƙe sannan tace; "Mama ke kina ganin muna da
kyawun da zan iya karawa da Nusram ɗin?, to wallahi bana dashi sannan kuma ba zan
taɓa aikata mata haka ba kuma ni Mama miji na ya maida ni dan haka ba zan yi aure
kan aure ba, gidan miji na zan koma yau ko ki so ko kada kiso".
Mama Jummai cikin hargagi tace; "Sahura ni kike faɗawa haka, to wallahi kinyi
kaɗan kuma baki isaba zanga ta yadda zaki fita kibi mijin naki", ba tare da damuwa
ba Sahurar tace; "za kuwa ki gani".

Mama Jummai cikin ranta tace; "ina dole na sake dabara idan ba haka ba wanki
hula zai kaini dare", tana gama faɗar haka ta ɗauki hijab ta fice.

Nusram tana ƙoƙarin ɗora girki Nusreen tayi sallama ta shigo hannun ta ɗauke da
kaya, Nusram ɗin da kanta ta miƙe ta taro ƴar uwar tata.

Ɗaki suka shiga dashi, Nusram cikin farin ciki tace; "wa'innan fa daga ina?",
Nusreen tace; "wallahi Auntyn Tudu tace na taho dashi zata zo sati me zuwa kin san
bikin Ya Sulaiman wai sati uku suka saka".

Nusram ta ƙara washe baki tana faɗin; "ah lallai kace Yaya Sulaiman ɗin ango
yake, ya akayi to?", Nusreen ta tabe baki sannan tace; "ashe ma wai ya san Shureim
ɗin baki ga yadda suka dinga fira ba, amma duk da haka yace zai ƙara bincike akan
shi, wai daman Maman Shureim ɗin a wajen Ya Sulaiman ɗin ma take siyayya".

Nusram tace; "shikenan ma ashe abin yazo da sauƙi", Nusreen ta cire hijab ɗin
jikin ta sannan tace; "na bashi labarin naki angon baki ga yadda ya dinga faɗa ba,
yace ma zai zo koda zuwa sati me zuwa ne ko kuma gobe".

Nusram ta harari Nusreen ɗin tace; "to waye yace ki ɗin ki faɗa mishi?", Nusreen
tayi dariya sannan ta juya wajen Ummi tace; "gashi nan inji Aunty tace zuwa gobe ko
kuma sati me zuwa zata zo wai sai kuyi magana".

Ummi tace; "Allah ya kaimu", suka amsa da ameen, Nusreen ta kwanta yayin da
Nusram ta koma wajen girkin ta don so take taci ƙarfin girkin kafin lokacin da zasu
tafi makarantar.

Ƙarfe huɗu sun idar da sallah inda suka saka atamfa duka a jikin su riga da zani
sannan suka ɗora hijab wanda ya kasance na makaranta sannan suka yiwa Ummi sallama
suka tafi.

Nusreen ta kalli ƴar uwar tata sannan tace; "Ramluv kin san me?, yanzu tunani na
shine anya kuwa Baba zai yi mana kayan ɗaki masu kyau?".

Nusram tace; "ke kuma abinda ya dame ki kenan kai Rim Allah ya shirye ki, abinda
nake so ki gane shine duk abinda Allah ya hore mishi wannan zai yi mana dan haka
kada ki damu ga kuma kuɗin da muka tara a wajen Auntyn Tudu na san sati me zuwa
zata zo dasu a shiga kasuwa sai a siyo koda kayan kitchen ne tunda a ƙalla zai kai
dubu ɗari da saba'in sannan akwai wa'inda muke tarawa a gida kinga duk Allah zai
rufa asiri dai, ni dai burina yanzu shine na bar gidan kawai".

Nusreen tace; "hakane kuma, kai amma sana'a tana da rufin asiri yanzu fa kinga da
bamu yi da shikenan", Nusram ta harare ta tace; "kamar wata gwanar sana'ar ai zan
bawa Shureim shawara kawai ya buɗe miki boutique ne kada ya tsaya ɓata kuɗin shi".

Nusreen tace; "nifa gidan radio zan yi aiki na", Nusram tace; "da auren naki
ko?", eh mana me za'a fasa", Nusram tace; "Allah ya baki sa'a to", ta amsa da
ameen, haka suka cigaba da firar tasu har suka isa makarantar.

Koda suka taso, sauri kawai suke tayi domin su ƙaraso gida dan basa so ayi
kiran sallar Magrib suna kan hanya.

A.ƙofar gida suka tarar da Idris, cikin girmamawa ya gaishe dasu, suma suka amsa
sannan suka shiga ciki.
"ni Sahura ban isa na faɗa miki magana kiji ba kenan?, Sahura dani kike ja ko, ki
koma babu inda zaki je", maganar Mama Jummai kenan wacce ta iso kunnen su.

Su ka kai duba, zuwa inda take ta kama Sahurar ta cukuikuye ita kuma Sahurar
tana ƙoƙarin fizgewa, idan kaga yadda suke sai abin ya baka dariya.

Nusreen data kasa riƙe dariyar ta nan ta hau yin ta babu ƙauƙƙautawa, Mama
Jummai ta jefo musu harara tace; "shegu mayu, wallahi Allah ya isa tsakani na
daku".

Nusreen ta ƙara kwashewa da dariya harda shewa, wanda hakan ba ƙaramumin ƙular
da Mama Jummai ɗin yayi ba, itacen dake cikin wuta ta ɗauko ta nufo Nusreen ɗin
gadan-gadan sai dai ganin yadda Nusram ta haɗe rai take kuma kallon ta yasa ta kasa
ƙarasawa kusa da Nusreen ɗin, tana haki ta nuna Nusreen ɗin tace; "zamu haɗu ne
shegu sunƙi aure".

Baba yayi sallama ya shigo, inda ya samu Mama Jumman ta sake cukuikuye Sahurar
tana ƙoƙarin tura ta ɗaki, Baba yace; "yanzu dan Allah meye haka?".

Mama Jummai tace; "yauwa gwara daka zo, nice nan nace babu inda zata je, wai
amma yarinyar nan sai ƙoƙarin ja dani take yi a gidan nan tana tona mini asiri,
kuma wa'incan ƴaƴan mayun sune suke ƙara zugata".

Baba yace; "to ke meye na hana ta tafiya ki barta taje mana, bafa na son rigima",
cikin hayagaga tace; "au haka ma zaka ce Abdullahi?, to wallahi ba zai saɓu ba".

Baba yasa hannu ya rabata da Sahurar sannan yace; "ke wuce kibi mijin ki",
Sahurar kuwa ta nufi hanyar fita tana murna inda take ɗagawa Nusram hannu, Nusram
ta mayar mata sannan ta wuce nasu ɗakin.

Suna idar da sallah Ummi tace; "Nusreen ke ba zaki dena ɗauko mini magana ba a
gidan nan ko?", Nusreen ta cuno baki tace; "yanzu me nayi ko dariya ma ta zama
rigima a gidan nan kenan bamu da ƴancin muyi dariya kenan?", Ummi ta kai mata duka
Nusreen ta fice da gudu.

Nusram kuwa tabarma ta shinfiɗa musu a ƙofar ɗaki sannan ta zubo musu abinci,
Nusreen ta ɗauko Kubra ta fito da ita, Nusram kuma ta ɗauko babbar roba sannan ta
saka hijab tace; "bari naje na siyo mana ƙanƙara", daga haka ta fice.

Kasancewar gidan babu nisa da nasu yasa bata wani jima ba ta siyo sannan ta nufo
hanyar gida, a ɗan lungun kusa da gidan su ta hangi mota, bata kawo komai ba ta
shiga lungun.

Ganin shi sai da gaban ta ya faɗi, Babban mutum ne sanye da fararen kaya, hannun
shi riƙe da waya yana dannawa, hasken wayar shiya haska mata fuskar shi ina da a
take a lokacin ta gane ko waye.

Tana daf da shiga gida ya ɗago sannan yace: "amm ji mana", cak Nusram ta tsaya
gabanta na faɗuwa, "idan kin shiga kice ana sallama da Nusram dan Allah", ji tayi
kamar ta dawo ta kwaɗa mishi mari amma haka ta daure ta shige gidan kawai.

Koda ta shiga bata kuma bi ta kanshi ba, wajen randar su ta nufa ta ciko jug da
ruwa ta buɗe tiyara ta zazzage a ciki ta juya sannan ta sassaka ƙanƙarar ta kawo ta
ajiye musu.

Kusa da Nusreen ta je ta zauna amma ta kasa cin abincin har sai da Nusreen tace:
"Ramluv, kin ƙi cin abincin?", da sauri ta jefa hannun ta sai dai tana kai lomar
bakin ta yaro yana rangaɗa sallama.
Mama jummai dake nata ƙofar ɗakin ta amsa mishi domin yawanci su kan shigo domin
yaranta ko kuma siyayya, yaro yace; "wai ana sallama da Nusram", Mama Jummai taja
tsaki.

Nusram kuwa abincin da bata kai ga haɗiyewa ba shine ya dawo ya shaƙe ta inda
gaba ɗaya ya haddasa mata tari me ƙarfi, Nusreen ta miƙo mata ruwa ta sha.

Yaron ya kuma maimaitawa, Mama Jummai cikin fushi tace; "dallah fita ka bawa
mutane waje ai mun ji ko?", Nusreen tace; "kaje kace tana zuwa".

Tana zaune tana ƙoƙarin dai-daita nutsuwar ta taji sallamar Baba inda ya hau
surfa mata faɗa akan ta bar mutum a tsaye, dole hakan tasa ta miƙe tayi cikin ɗaki.

"au ɗaki kika shige ba zaki fito ba sai na biyo ki ciki?", Ummi tace; "amma ai
ka bari ta shirya ko?", rufe mini baki ɓammbaƙar munafika duk waye ya ɓata yaran
idan bake ba", hakan yasa Ummi taja baki tayi shiru.

Nusram dake ɗaki ta fashe da matsanancin kuka, ita tunda take bata taɓa ganin
uban da yake yiwa ƴaƴan shi abinda Baban nasu yake yi musu ba, haka bata taɓa ganin
mijin da yake yiwa matar shi abinda Baban nasu yake yiwa maman nasu ba.

#LIKE
#SHARE
#COMMENT

*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

*Note:-* masu cewa basu gane rayuwar waye ake so a nuna ba an ce rayuwar Abdus-
samad amma kuma ana kawo rayuwar Nusram, kada ku dama idan har kuka ƙara haƙuri
zaku fahimci ina littafin ya dosa amma be kamata tun a yanzu ku yanke hukunci ba ya
kamata ku haƙura har zuwa lokacin da littafin yayi zurfi sosai kada ku manta fa ko
pages talatin ba'a yi ba kuma tun farko na faɗa muku littafin nada tsayi why d
eager??.

Sannan ga masu son shiga whatsapp group na Rayuwar Abdus-samad kuyi searching
Aishatu Babayo sai ku tura mata da number ɗin ku ta pc zata saka ku a ciki amma dan
Allah iya mata kawai banda maza, Na gode sosai ga masu complain suna duba whattpad
amma basa gani kuyi haƙuri wallahi ko ƙareenateey na kasa ƙarasa balle na fara saka
wannan amma zan dage kan azumi na saka su duka acan ɗin tnxs for ur love😘.

📖📖27-28📖📖

Jiyo muryar Baba yana ƙara wage baki yana ƙwala mata kira yasa Nusram saurin goge
hawayen fuskar ta, sai da ta ɗan gyara fuskar dan bata so kowa ya gane halin da
take ciki.

Tana fitowa Baba ya kai mata ranƙwashi tsakiyar kai yace; "shegiya me baƙin hali
irin na uwar ta, ko kare be taɓa zuwa ƙofar gidan nan da sunan yana son ki ba shine
kinyi sa'a yanzu Alhaji Baballe zai rufa mana asiri ya rufa miki kema shine kika
tsaya nurƙufanci ko?", Nusram bata iya cewa komai ba ta gifta mahaifin nata cikin
baƙin ciki da damuwa.

A inda ta bar shi a nan ta dawo ta same shi, yana hango ta ya hau washe baki,
Nusram kuwa cikin mutunci ta gaishe dashi.

Ya amsa yana ƙara washe bakin shi, "kinga dai yadda Allah yake ikon shi ko, wato
dalilin da yasa kenan ko Sauro be taɓa zuwa ƙofar gidan nan da sunan yazo wajen ki
ba ashe ke ɗin rabona ce".

Nusram ta haɗiye wani abu me ɗaci daya tsaya mata a maƙogoro, wato har labari ma
Baba ya bashi kenan, bata iya cewa komai ba banda "Um ko u'um", yayin da shi kuma
ya dinga yi mata surutu.

"abu na gaba da ya kamata ki sanu shine mata na guda biyu, yarana Ashirin da ɗaya
cif, amarya nada goma uwargida nada sha ɗaya, kinga ke idan kika zo sai kiyo
dozin".
Nusram ta kalle shi ta kauda kai, wai dozin lallai ma, suna nan tsaye Isa ya
dawo, fuska a murtuke ya kalli Alhajin sannan ya shige gida.

Nusram ta ajiye ɓoyayyiyar ajiyar zuciya, shi kuwa Alhajin da yake be san me
take ciki ba be wani damu ba, sai ƙarfe tara da rabi da ƴan mintuna sannan yayi
mata sallama ya tafi.

Nusram kuwa har wata iska me daɗi taji tana kaɗata domin dai Allah ya gani ji
take da atakure take, tana shiga zaure ta tarar da Isa a tsaye yana jiran shigowar
ta.

Yana ganin ta ya nufo ta sannan ya ɗaga hannu hannu ya sharara mata mari, cikin
masifa yace; "ni ina can na shanya baki ina jiran ki ashe ke kina nan kina taɗi da
wani ƙato ko, to wallahi ko kina sona ko bakya so na baki da miji sai ni", yana
ajiye aya Nusram ta raɓa ta wuce.

Ya fizgo ta ya haɗa da jikin bango sannan yace; "wallahi kina wasa dani da yawa
ko, matuƙar naga zaki kuɓuce mini sai na raba ki da budurcin naki naga uban me
mijin naki zai samu".

Gaban Nusram ya yanke ya faɗi, cikin sanyi tace; "Dan Allah ka sake ni na tafi
mana", ya ture ta har sai da ta kusa faɗuwa sannan ya fice ya barta.

Nusram ta tsuguna a wajen ta saka kanta tsakanin ƙafafun ta sannan ta fashe da


kuka, ita kaɗai ta san ya take ji a cikin zuciyar ta.

Ta daɗe a wajen dan sai da taji alamun Baba zai shigo sannan ta miƙe cikin sauri
ta shige gida, a bakin ƙofa ta tsaya ta gyara kwalliyar ta sannan ta shiga.

Nusreen dake tsaye da hijab a hannu da Ummi dake kan abin sallah suka bita da
kallo, Nusram tace; "ke kuma lafiya na ganki tsaye da hijab?", Nusreen tace; "Allah
dama naga kin daɗe ne shine wai zan biki naga ina kika tsaya ne ko lafiya", Nusram
tayi murmushi sannan ta juya tace da Ummi; "har ya tafi bari naje na kwanta, Rim
muje ciki na san dai Shureim ba zai zo ba tunda tara ta wuce", Nusreen kam kai
kawai ta ɗaga.

Sai da suka gama shirin barcin su sannan Ummi ta shigo, ta kalli Nusram tace;
"Nusram ki faɗa mini tsakanin ki da Allah kina son wannan alhajin?", Nusram babu ko
ɗar ta ɗagawa Ummi kai, Ummi tayi ajiyar zuciya sannan tace; "shikenan tunda haka
kika ce, ku kwanta kawai amma ki sani matuƙar bakya son shi to ki sanar dani domin
rayuwar aure ba ɗaya take data gida ba", tana faɗin haka ta fice.

Nusram ta saki ajiyar zuciya sannan ta kwanta, Nusreen ma haka sai data jima
sannan ta sami damar cewa; "wai Ramlove da gaske ne kina son Alhaji Baballe?".

Nusram tace; "sosai ma kuwa, mutumin nan babu ruwan shi gashi da sauƙin hali ga
barkwanci baki ga yadda ya dinga saka ni ina dariya ba, ni dai gaskiya yana birge
ni sannan ina jin daɗin mu'amalata tare dashi", Nusreen tace; "amma fa kin sani
Nusram Alhaji Baballe tsoho ne sannan baya da mutunci akan kuɗi a gaban ki fa Baba
yake zagin shi akan baya da mutunci yanzun ma idan kika bibiya kuɗi ne ya haɗa su
ake so a saka ki a tsakiya".

Nusram tace; "bana jin abinda Baba yake faɗa akan shi gaskiya ne kin dai san
halin baba, sannan maganar kuɗi kuma zato kike yi dan haka kada ki tada hankalin ki
akan hakan", Nusreen tace; "amma dai ni ƴar uwar ki ce ko, dan haka ba zan taɓa so
wani abu ya cutar dake ba kamar yarda kike ƙoƙari wajen ganin kin bani farin ciki
kin kuma kare ni daga duk wani abun cutarwa Nusram kece fa kawai wacce nake da ita,
ƴar uwa ta rabin jiki".
Nusram ta balla mata hararar wasa sannan tace; "ina kika bar Kubra, Sahura dasu
Ameera kiji mini yarinya".

Nusreen tayi dariya tace; "Allah da gaske basu kai mini ke ba, Nusram tare fa
muka kwanta a cikin mahaifiyar mu tsayin wata tara abincin da zamu ci yana haɗe
dana juna, muka fito tsayin shekara biyu mahaifiyar mu na ciyar damu da abinci kala
ɗaya wanda har kika sha ki saki na kama kema kuma na kan sha na saki ki kama tun
lokacin da muka fara wayo har tana Pant kala ɗaya muke sakawa kuma bamu taɓa raba
wajen kwana ba, taya zan haɗaki da wasu, ke ɗin *Bloody*😭 na ce".

Ummi ta katse zancen ta hanyar cewa; "tabbas abinda Nusreen ta faɗa gaskiya ne,
kunfi kusanci da juna sama da duk sauran ƴan uwanku Kamar yadda bakya son wani abu
ya same ta haka itama bata so wani abu ya same ki, dukkanku kuna son junan ku sai
dai ba zai taɓa kaiwa koda rabin son da nake yi muku ba, nice mahaifiyar ku na
ɗauki wahalar ku tun daga lokacin da kuke ciki na, a cikin abincin da naci a ciki
kuke samu kuma kuci, lokacin da cikin ku ya kai wata takwas bana iya barci kwata
kwata sai da rana da ranan ma a zaune, nazo naƙudar ku haka nasha wahala kamar zan
mutu, bayan na haifo ku nayi tunanin wahala ta ƙare ashe yanzu wata sabuwa zan ɗora
domin kuwa da ɗaya ta fara kuka ɗayar zata ɗauka, haka zan ta rarrashin ku, kuyi
barci da rana ni kuma da daddare ku hana ni yin barcin amma duk da haka banji a
raina cewa wai bana son ku ba, naci fitsarin ku naci kashin ku, naci tunɓuɗin ku
amma duk da haka ban gaza, daga baya nauyin kula daku ya dawo kaina haka kuma nake
ta haƙuri, ki sani Nusram shekarun dana ɗauka ina wahala dake ba zai saka nace na
gaji dake idan ma kina tunanin dan ki kauce mini da wahalar da nake ba to ki sani
koda zaki ƙara shekara ashirin ko sama da haka matuƙar ina da rai ba zan taɓa
gajiya dake ba", Nusram cikin kuka ta haɗa su duka ta rungume.

"tawa ƙaddarar kenan ba zan taɓa samun farin ciki ba a rayuwa ta, kuma tabbas
aure ya zamar mini dole ko dan gudun samun matsala da kuma ɗaukewar farin ciki a
rayuwar ku", abinda take faɗa kenan a cikin ranta.

Sun ɗan taɓa fira a tsakanin su kafin su kwanta barci, sai lokacin Nusram ta ɗan
sami sauƙin abinda yake ranta don ko babu komai firar da suka ɗan yi ta rage mata
damuwa ba kaɗan ba.

******** **********

Jikin shi sanye da Wando jeans fari da kuma rigar polo t shirt kalar blue da ratsin
fari, ƴar ƙaramar jakar shi ce riƙe a hannun shi, Fadil kuma yana bayan shi haka
suka shigo da sallama.

Kamar koda yaushe suna saman dinning table inda zasu yi breakfast, Sumayya dake
cin abinci ta gaishe dashi, ya amsa fuska a sake sannan ya gaishe dasu, kowa ya
amsa kamar kowanne lokaci amma banda Brr Hauwa.

"idan kin gama tashi mu tafi", Sumayya tace; "to Yaya", sannan ta miƙe, cikin
rawar jiki Husna tace; "Ya Abdul kai ba zaka ci abincin bane?", be kalle ta ba
balle ta saka ran samun amsa daga gare shi.

Hajja tace; "baka ji ana yi maka magana bane?, ni ina mamakin halin ka domin iya
sani na uban ka ba halin shi ba kenan, anya kuwa kai ɗan shi ne?".

Wata irin ɗagowa Abdul yayi sannan ya kalli Hajja, itama Malama kamar zata zubar
da hawaye take bin Hajjan da kallo.

Ganin yadda ranshi ya ɓace yasa Hauwa cewa; "waye ya sani ko a yawon neman
shaidu aka samo shi aka zo aka ƙaƙabawa ɗan uwa na, ni dama na jima ina tunanin
haka dan ko kama baya yi da ƴaƴan Doctor".

Hajja ta girgiza kai tace; "tabbas hakan zata iya kasancewa bari Abubakar ɗin ya
dawo dole azo ayi bincike kada a lalata mana zuria da bara gurbi".

Wannan karan kam da Sumayya da Malama kasa daurewa suka yi dan haka Sumayya ta
saki kuka, Malama kuwa hawaye ta hau sharewa, Fadil kan shi na ƙasa sai dai yadda
ya tsuke baki zai tabbatar maka da cewa yaji haushin abin.

Fadila kuwa kasa bari tayi dan haka ta miƙe tace; "yo Hajja dan Abdul yayi
nurƙufanci ai ba abin mamaki bane idan aka yi duba da halin Brr Hauwa shima haka
yake kinga kenan ita ya ɗauko, taƙama da ƙasaita kuwa kowa ya san halin ki ne ko
ince a jinin ki yake, dan wani dalili naku kuke son haramta ɗan sunnah anya abinda
kuke yi kuwa dai-dai ne, in dai a neman yawon shari'ah ake samo ɗa ai ya kamata
kema Brr a bincike ki gudun ɓata zuria nan gaba", sanin halin Brr Hauwa yasa tana
gama faɗar haka taja ƙafar ta, ta bar wajen ɗakin Malama ta shige ta dannan key.

Brr Hauwa kuwa kan ta gama haɗa magan-ganun Fadila, Fadila ta ɓace a wajen,
Fadil kuwa jin ɓaranɓaramar da Fadila tayi yasa ya kama hannun Sumayya suka fice
daga gidan.

Hajja cikin masifa tace; "ai wallahi zaki zo ki same ni yaushe yaran gidan nan
suka ɓace har haka, bari Abban Nihal ya dawo ni Fadila take zagi kuma Malama kina
kallon ta?".

Malama har lokacin hawaye take zubar wa, Hajja ta fashe da kukan munafirci tana
faɗin; "Brr kaini wajen Ahmad", jin hakan yasa Brr Hauwa miƙewa ta ja hannun Hajja
domin tafiya.

Malama na ganin sun fita ta miƙe da sauri taje ƙofar ɗakin ta, sai da ta
ƙwanƙwasa tana ƙwalawa Fadila kira sannan ta buɗe, cikin sauri Malama ta janyo
hannun ta sannan tace; "zo ki bi su Abdul Hajja ta yafi wajen Ahmad kuma kin san
sauran idan har labarin yaje kunnen shi, babu inda kike da mafaka sai wajen Farida
dan haka fito maza".

Ita kanta Farida jin sunan wanda aka ambata yasa jikin ta ya hau rawa, Ahmad
shine babban ɗan Hajja tsohon sojane, yana ji da Hajja kuma duk abinda ta faɗa dai-
dai ne yana taka duk wanda ya taka ta.

Malama ta kamo hannun ta sannan ta haɗa dana Abdul tace; "maza ku tafi tare idan
lokaci yayi da zata dawo zan kira ka sai ta dawo kaji", Abdul da har lokacin
damuwar fuskar shi bata kauce ba ya ɗaga kai kawai yana me jan hannun Fadilar.

A waje suka sami Fadil da kuma Sumayya, inda kana gani ka san haƙuri yake bata
Abdul yayi murmushi yace; "kuzo mu tafi ko?", ba tare da sun ce komai ba suka bishi
a baya.

Fadil ke tuƙa su yayin da Sumayya ke gefe, baya kuma Abdul ne da Fadila, babu
wanda yayi magana tsayin lokaci kafin Fadil yace; "Sumayya kuyi haƙuri kun riga da
kun san halin Hajja tun ba yanzu ba be kamata hakan ya dame ku ba".

Sumayya ta share hawayen ta tace; "Yaya Fadil da na san abinda zan zo naji kenan
a bakin Aunty Hauwa da Hajja da ban matsa sai nazo ba".

Fadila ta saka hannu ta dafa Sumayya tace; "kada ki damu kanki Sumayya baku
kaɗai take wa haka ba har mu duk tabi ta dame mu".

Fadil yace; "hali ne kowa da kalar nashi gashi ban san me yasa duk tabi ta tsani
Abdus-samad ba, kamar ba jinin ta ba".
Sumayya tace; "amma abinda take yi be dace ba kuma ni ba zan kuma zuwa gidan nan
ba", Fadila tace; "aikuwa dole kizo domin kuwa nan shine asalin ki".

Sumayya ta taɓe baki tace; "asali na kuma? Bayan basa kauna ta", Fadil yace;
"amma ai muna sanki mu ko?".

Abdul kuwa yana jin su amma be ce komai ba domin kuwa kwata kwata baya son
hayaniyar ta dinga damun shi sanin cewa sai dai yayi ta jin ƙunar abin kuma haka
shine su Hajjan suke so.

Ya fahimci abu ɗaya shine Brr Hauwa shine tafi tsana yayinda Hajja kuma jinin
First love ne bata so.

Yana buɗe idanu yabi kwanar hanyar da kallo, ba zai ce ga abinda yake tunani
akan yarinyar ba amma tabbas ya san akwai wani al'amari a rayuwar ta, ya sauke
ajiyar zuciya yana me maida kanshi ya kwantar saman kujera.

Sun jima suna tafiya kafin suka iso unguwar tasu, wato *Unguwar Sarki* unguwar
da kowa ke rayuwar shi ba ruwan wani da wani, wannan yana ɗaya daga cikin abinda
yasa yake son unguwar tasu.

A bakin get aka tsayar dasu, ganin sun tsaya yasa Abdul ɗago kai yana kallon
wanda ya tsayar dasu ɗin, mutumin kuwa sai faman washe baki yake yi.

Sumayya ta juyo tace; "Yaya kai fa Bala yake yiwa magana", Abdul ya sauke glass
ɗin ɓangaren shi sannan suka gaisa.

Bala cikin durƙusar da kai yace; "dama ƙaramin oga wallahi tun wancan satin nake
zuwa neman ka amma aka ce mini kana Rigasa".

Abdul yace; "ya akayi ne Bala?", Bala ya shafa kai sannan yace; "alfarma nake
nema a wajen ka da kayi haƙuri na dawo bakin aiki na, Hajiya ta sallame ni akan
kuskuren dana aikata kuma gashi yanzu gari babu aiki na nema wani ban samu ba, ga
yarinyata da aka kwantar a asibiti shine da naji cewa ka dawo nace bari nazo
to.kuma sai na taki rashin sa'a bakanan shine da nazo jiya ake ce mini yau zaka
dawo to Allah da ikon shi tun safe nake zaman jiran ka".

Abdul ya dafe kai, wannan wane kalar dogon bayani ne haka, ya ilahi! Sai kuma ya
ɗago yace; "ka shiga ciki bari mu shigo mu ma", da sauri Bala ya shige har yana ɗan
haɗawa da gudu.

Fadil ya kwashe da dariya domin ya san dogon bayanin Bala ya ɓatawa Abdul ran
shi, Abdus-samad kuwa kauda kai gefe yayi.

Ko kan su ƙarasa parking space ɗin har Balan yaje can yana jira, Abdus-samad
yace da Sumayya; "menene aikin shi", Sumayya ta bashi amsa da; "wankin motoci yake
yi".

Suna gama parking ɗin da kanshi yazo ya buɗewa Abdus-samad ɗin ƙofa, Abdul kuwa
ya haɗe rai yaƙi fitowa, Fadil da ya san hali ya dubi Bala yace; "ka maida ƙofar ka
rufe baya so ana buɗe mishi", cikin sauri Bala ya maida ƙofar ya rufe.

Abdul yayi murmushi sannan ya buɗe ya fito, masu aikin ya kira sannan yace;
"waye ke aikin Bala a gidan nan", Idris yace; "nine nan".

"a da meye aikin ka?", Abdul ya kuma jefa mishi tambaya, Idris yace; "gyaran
fulawa", Abdul ya kalli Bala yace; "ka koma bakin aikin ka kawai", yana faɗar haka
yayi hanyar part ɗin shi.
Su Fadil kuwa mamaki ne ya cika su, na ganin direct ya bada umarni, Sumayya kuwa
murmushi tayi kawai sannan tace: "kuzo muje, idan har kuna gidan nan sai kun dena
mamakin ikon da Ya Abdul yake dashi".

Haka suka bi bayan Sumayya, duk ƴan gidan suna falo dan haka Adnan ya nufo su da
gudu yana murna, Fadil ne ya ɗaga shi sama yana faɗin; "Oyoyo autan gidan".

Fadil ya ƙarasa kusa da Sameer da Tameer ya basu hannu suka gaisa, Fadila kuma
ta gaishe dasu daga inda take.

Surayya tace; "yau kunzo mana gidan kenan? Ko kuwa dai kuma ɗan lelen kuka
rako?", Fadil yace; "bangane ɗan lele ba?", ta miƙe tsaye tana me kwashe
littattafan ta sannan ta juyo tace; "waye ɗan lele banda Ya Abdul", tana faɗar
hakan ta nufi hanyar ɗakin ta.

Fadil da Fadila suka kalli juna cike da mamaki, sun san akwai ƙiyayya tsakanin
ƴan gidan da Abdus-samad amma basu ɗauka tayi zafi haka ba.

Sumayya ta fara ƙwalawa Aziza kira, jima kaɗan ta ƙaraso Sumayya tace; "ki kawo
wa baƙi ruwa mana", Aziza ta amsa da to sannan ta miƙe ta tafi.

Sameer yace; "ina Abdul ɗin yake?", Sumayya tace; "yana part ɗin shi", Sameer
yace; "be san cewa munyi kewar shi bane shine zai wani tafi nashi wajen", ya ƙarasa
yana miƙewa domin tafiya, Tameer yaja tsaki yana gyara kwanciyar shi.

"ya Allah! Wannan wane kalar gida ne babu daɗi", abinda Fadil ya faɗa kenan a
ranshi, Sumayya ta.miƙe sannan tace; "Aunty Fadila zo muje ɗaki na", Fadila ta miƙe
tabi bayan Sumayyar.

Fadil shima ganin yadda gidan yake yasa ya miƙe ya fice kawai, Part ɗin Abdul
ɗin ya nufa, ƙofar a buɗe take dan haka ya shiga kawai.

Baya bedroom ɗin amma yana jiyo ƙarar ruwa hakan ya tabbatar mishi da wanka
yake yi kenan?, Fadil ya zauna saman bed ɗin yana me bin ɗakin da kallo, kai kace
ɗakin wani hamshaƙin me kuɗi ne komai kuma yana inda ya dace.

Abdul ɗin ya fito ɗaure da towel sai ƙarami kuma da yake goge kanshi dashi, ba
tare da ya cewa Fadil ɗin komai ba, Fadil kuwa ya bishi da idanu.

Gaban dressing mirror yaje ya tsaya yana shafa mai, har ya gama yayi combing
kanshi Fadil kallon shi yake yi, Wardrobe ya bude ya ɗauko kayan da zai saka.

Riga ƙarama baƙa da wando fari jeans three quarter ya saka sannan ya fito daga
wajen canza kayan, tuararruka ya hau fesawa nan fa ɗakin ya buɗe da ƙamshi, ya
ɗauki zoben shi ya maida yatsan shi yana cikin ɗaura agogo ya ɗago ya kalli Fadil
ɗin ta madubi, ganin yadda yake binshi da kallo yasa ya ɗaga mishi gira ɗaya alamar
lafiya.

Fadil ya girgiza kai yana murmushi, shima Abdus-samad ɗin murmushi kawai yayi
yana me juya kanshi zuwa gefe.

Wayoyin shi ya kwasa sannan yace da Fadil ɗin; "muje ko?", tare suka fito
daga bangaren, a harabar gidan suka tarar da sauran duk sun fito.

Kusa da Tameer da Sameer yaje sannan yace; "barkan ku da hutawa", Sameer yayi
murmushi yace; "barka da fitowa ɗan lelen Mommy ai na shiga amma kana bayi
lokacin".
Ba tare da Abdul ɗin yace komai ba ya lumshe idanun shi, Tameer yaja tsaki yana
kauda kanshi gefe, hannun Abdus-samad Sameer yaja ya kai shi har gaban motar tashi
sannan yace; "ga gift ɗin Daddy daya turo.mana da ita", murmushi kawai yayi kafin
yace; "thanks" yana faɗar hakan ya juya ya koma inda yake ya zauna.

Shi kanshi Sameer yaji haushin abinda Abdul ɗin yayi.mishi haka ma su Fadil
ɗin, Tameer kuwa murmushi yayi yana yin ƙwafa.

Sumayya ta zauna kusa da Abdus-samad ɗin ta riƙo hannun shi, ta buɗe baki zata
yi magana ya buɗe idanun shi gaba ɗaya a kanta.

Wani irin abu taji wanda gaba ɗaya kamar ya janye duka miyau na bakin ta, maida
bakin tayi ta rufe, a hankali yace; "pls kaina ciwo yake yi i need some space".

Tashi tayi ta bar wajen dan ta san tunda ya faɗi hakan to hakan yake nufi wato
baya son damuwa.

Fadil da Fadila kuwa kallon su kawai suke yi, Surayya waya ce a hannun ta take
latsawa Tameer ma haka, Sameer kuwa yana zaune ne yana kallon wani wajen.

Fadila cikin raɗa tace; "anya kuwa zan.iya zaman gidan nan?", Fadil yace; "zaki
iya mana, meya faru?", tace; "kalli kaga fa basa fira tsakanin su ni da har ina
cewa na baro kurkuku na dawo waje me ƴanci ashe gwara can da nan?".

Fadil ya girgiza kai yace; "taɓ gaskiya na tausaya miki to ko zamu tafi tare
ne?", Fadila ta ƙwalalo idanu tana faɗin; "Abba Major fa?".

Fadil ya ɗaga kafaɗa, Fadila ta girgiza kai tana faɗin ka barni kawai a nan",
Fadil yace; "to shikenan".

Ɓangaren Abdul kuwa wannan mafarkin daya saba shi yayi, sai dai wannan karon
fuska ce wacce babu nama ko ɗaya a jiki take tsaye a gaban shi, iya fuskar kawai
sannan tana ƙwala wannan kiran na *MURAD* a gigice ya farka duk ya haɗa zufa, duka
suka bishi da kallo.

Ya sauke ƙafafun shi daga saman kujerar yana me dafe kanshi, Fadil ya ƙarasa
inda yake ya dafa shi, Abdul ya ɗago ya kalle shi.

"lafiya kake kuwa?", abinda Fadil ɗin ya tambaya kenan, Abdul yayi murmushin dole
yace; "lafiya ta lau", Fadil yace; "shikenan to bari nazo na tafi gida", Abdus-
samad ya miƙe domin rakashi.

Sai da Fadil ɗin yayi musu sallama sannan suka ƙarasa kusa da motar shi, Abdul
ya buɗe mishi ya shiga inda shi kuma Abdul ɗin ya juyo ya dawo ciki.

Fadila kam zaman gidan duk babu daɗi take ji amma bata da yadda zata yi dole
hakan nan ta zauna a gidan dan shine rufin asirin ta kawai.

Wajen Sumayya ta koma inda nan suka fara fira domin ita kanta ta lura kamar
zamar gidan ya ishe Fadilar hakan yasa tayi ƙoƙarin ɗauke mata hankali.

Abdul kuwa yana zaune a wajen ne amma kuma sanyi-sanyi yake ji hakan yasa dole
ya miƙe ya koma part ɗin shi ya kwanta sai dai yana kwanciya zazzaɓi ya rufe shi.

Sai wajen Magrib sannan zazzaɓin ya sake shi, bayi ya shiga yayi wanka tare da
ɗoro alwala yazo ya tada kabbarar sallar la'asar yana idarwa ya janyo waya domin
kiran Fadil yaji ya yaje gida.

Ganin missed calls na Mommyn shi yasa yayi murmushi, tun safe daya kira ta akan
zasu taho be sake kiran ta ba, number ɗin Fadil ya kira inda nan ya mishi ya yaje
gida.

Fadil yace; "lafiya ƙau, ya jikin?", Abdul ya ɗan basar sannan yace; "na sami
sauƙi, ni kuwa in tambaye ka mana?", Fadil yace; "ina ji".

Shiru yayi na ɗan lokaci kafin yace; "barshi ma kawai, sai anjima ka gaishe da
Malama", Fadil yayi dariya yace; "shikenan ni.kuma ka gaida mini ƴan biyu ta", daga
haka suka rabu.

Number ɗin Mummyn shi ya kira nan ya dasa mata shagwaɓa ita kuma tana ta yi
mishi dariya, "Allah Mummy gidan babu daɗi da bakya nan har zazzaɓi sai da nayi
baki ga yadda na rame ba".

Brr Farida tayi dariya tana faɗin; "asha yaron nawa rago ne ban sani ba, to idan
na mutu fa", ya ƙara turo baki gaba kaman tana kallon shi yace; "nima mutuwa zan yi
balle ma sai na riga ki mutuwa", cikin sauri Brr Farida tace; "ya isa haka, ina ƴan
uwan ka?".

"nifa ina ɗaki na tun kan la'asar", Brr Farida tace; "kada kace mini a ɗaki kayi
sallah", yace; "barci ne fa ya kwashe ni kuma da gaske nayi zazzaɓi yanzu ne na
sami sauƙi".

Brr Farida tayi ɗan jimm sannan tace; "shikenan, Allah ya sauƙe, tahowar wuri
zamu yi gashi ma ina ta haɗa kayan mu ka san mu yanzu dare yayi sosai".

Ya ɗan shafa kai yace; "hakane fa, bari naje nayi sallah bye", tace; "bye take
care", yace; "sure love you", sannan ya katse wayar ya miƙe ya fice domin amsa
kiran ubangiji.

Sai bayan isha'i sannan ya shigo gidan, a saman dinning ya tarar dasu, shima nan
ya zauna suka ci abincin tare.

Firar dai sama-sama ce dan ji da kansu ba bari yake suyi wata fira ba, sai bayan
sun gama ne ma ya ɗan taya su Fadila firar kafin ya nufi part ɗin shi domin
kwanciya.

Laptop ɗin shi ya janyo inda ya kira Mummyn shi, bata yi barci ba dan haka kuwa
suka shiga fira, duk da su can daren yayi nisa sosai, sun jima suna fira har barci
ya ɗauke shi.

Brr Farida tabi ɗan nata da idanu tana murmushi, soyayyar shi daban take a
zuciyar ta wacce ta san Allah ne ya saka mata shi, ko yaya zai ji a ranar da duk ya
san gaskiyar rayuwar shi.

"kada ki damu zai ɗauki haƙuri", Daddy ya faɗa, ta juyo ta kalli mijin ta cikin
karaya tace; "ina tausayawa halin da zai shiga Abban Adnan".

Dr Abubakar ya rungumo matar tashi yace; "kada ki damu komai zai zo da sauƙi,
sannan ma bana jin zai san gaskiyar al'amari tunda kin riƙe amana sannan ba duka
mutane bane suka san ainihin waye shi ba".

"amma kuma Malama ta sani, sannan shi kanshi ya fara mini tambayoyi akan waye
Murad ga Alhaji Mustapha dake raye kuma na san har yanzu yana bibiyar rayuwar
Abdus-samad ɗin".

Dr Abubakar yace; "kada ki damu hakan ba zai zama wata barazana ba domin kuwa
Allah zai mana tsari dashi", haka ya dinga lallashin ta har ya samu hankalin ta ya
kwanta.
#LIKE
#SHARE
#COMMENT

*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

*Sannan ga masu son shiga whatsapp group na Rayuwar Abdus-samad kuyi searching
Aishatu Babayo sai ku tura mata da number ɗin ku ta pc zata saka ku a ciki amma dan
Allah iya mata kawai banda maza, Na gode sosai*

📖📖29-30📖📖

Fadila tana gyara ɗaurin ɗan kwalin ta Abdul ya turo ƙofar ya shigo, koda ta
kalle shi sai da numfashin ta ya kusa ɗaukewa ganin irin kyawun da yayi.

Sumayya dake ƙoƙarin ɗaure gashin ta, ta juyo tace; "wow Ya Abdul ka haɗu kamar
yau ne ɗaurin auren ka", ya gyara links ɗin shi sannan yace; "ku fito fa, dan bana
so First love tayi zaman jiran mu".

Fadila ta ɗaga kai alamun to, tana ƙara kallon ɗan uwan nata, cikin shigar
manyan kaya wato shadda kalar sararin samaniya wacce taji aikin hannu.

Kanshi babu hula sai dai kwantacciyar sumar shi wacce ke ƙara mishi kyau, ya
juya cikin ƙasaita ya fice daga ɗakin.

Fadila ta saki wata irin ajiyar zuciya har sai da Sumayya ta kalle ta, cikin
sauri Fadilar ta basar tana me zama gefen gadon Sumayya.

Yana tsaye ya juya baya yana amsa waya suka fito dukan su, ganin waya yake yi
yasa duka suka tsaya Surayya ita ma ta fito sanye da riga da skirt na atamfa.

Abdul tace; " ka bari later kawai yanzu zamu je ɗauko Mummy ne a airport", yana
faɗar haka ya katse wayar.

Ya juyo ya kalle su, Surayya ita kanta sai da taga kyawun Yayan nata don haka
cikin sauri ta kauda kai, ita fa abinda ke hanata tafiya tare dashi kenan sai tayi
wanka na ƙasaita yana yin nashi sai ya shafe nata.

Suna gaba yana baya haka suka fito harabar gidan, anan suka tarar da Tameer da
Sameer, kowannen su cikin shirin ɗauko iyayen nasu.

Abdul yayi murmushi yace; "to muje", yana ƙoƙarin buɗe mota, Tameer yace; "amma
dai ya kamata ace mun hau motar da Daddy ya siya mana ko?".

Sai da Abdul yayi ɗan jimm sannan yace; "to shikenan", Tameer yace; "idan ma
baka son jar ne, ga makullin tawa", Abdul ya kalli yayan nashi da mamaki sai kuma
ya kauda kai cikin sauri yace; "nop bari naje a tawa kawai".

Tameer ɗin ya taɓe baki yana me nufar tashi motar, shima Abdul ya nufi tashi,
Abdul da Sumayya sai Adnan a baya, sai Sameer da Fadila dan tace ba zata shiga jar
mota ba kamar ta ƴan shan jini, Surayya kuwa ta Tameer ta shiga domin tafiyar su
zata fi dai-dai.

Haka suka fice daga gidan cikin farin ciki domin zuwa ɗauko iyayen nasu babu ma
kamar Abdus-samad wanda yake jin kamar ya shekara ne bega mahaifiyar tashi ba.

********* **********

Nusreen ta kalli Nusram wacce ta zuba ubam tagumi, itama cikin damuwa ta ajiye
zanin gadon dake hannun ta, ta zubawa ƴar uwar tata idanu.

Ummi da Auntyn Tudu suka shigo tare wanda hakan shiya dawo da Nusram daga
duniyar tunanin data tafi, cikin sauri ita da Nusreen suka amshi kayan dake hannun
su.

Sai da suka zauna Aunty tace; "Wash wallahi na gaji, Allah yasa ma wancan yaron
ya amso ragowar", Ummi tace; "tunda har kin faɗa mishi zai amso ne kada ki damu".

Kaya ne na kitchen sai kuma sauran kayan da zasu yi amfani dashi na bikin, nan
aka baje ana gani, ita dai Nusram nata idanu ne babu abinda take tunani sai auren
da zata yi.

Nusreen ta juyo ta kalli ƴar uwar tata sannan tace; "Ram koba haka ba?", Nusram
ba tare da ta san me Nusreen ɗin ke magana akai ba ta ɗaga mata kai kawai tana
miƙewa ta bar wajen.

Duka suka bita da kallo, Aunty tace; "Allah sarki ni dama na san Nusram ba zata
taɓa farin ciki da wannan auren ba kawai dai zata yi shi ne".

Ummi tace; "nima na lura da bata wani farin ciki da bikin amma ko meye addu'a
zamu taya ta dashi sai dai har yanzu ina kan baka ta matuƙar tace bata son shi to
kuwa sai dai a fasa auren".

Nusram kuwa kan katifar su ta faɗa hawaye na zubo mata, ita ta san ba zata ce ga
wani zaɓi da take dashi na wanda zata aura ba amma tabbas bata son auren me yara
irin wa'innan yaƴa ashirin da ɗaya!".

Haka ta dinga zubar da hawaye cikin baƙin ciki da zafin abinda ke faruwa a
kanta, cikin ƙarfin hali ta miƙe a zuciyar ta tana maimaita addu'ar da mutum keyi
idan musiba ta same shi tana kuma me neman zaɓin Allah.

Haka ranar Auntyn wuni tayi a gidan suna ta shirye-shirye domin kuwa gobe ake
saka ran dawowar mahaifiyar Shureim ɗin.

Kuma tabbas Baba ba zai ɗaga auren ba dan yace tana dawowa da sati biyu ko sati
uku, Shureim kam dole ya amsa a hakan har yaje ya sanar da dangin mahaifin shi.

Su kansu sai da suka ce; "wannan wane kalar aure ne kamar an gaji dasu ai a bari
mu muyi bincike idan su ba zasu yi ba ko", shi dai Shureim beda abin cewa nan suka
gama maganganun su kafin wan baban nashi ya saka ƴaƴan shi guda biyu akan su zo
suyi bincike.

Alhamdulillahi koda suka zo suka yi bincike basu sami wata tangarɗa ba domin
kuwa an basu amsoshi me kyau sosai, dan an sheda musu ma ko ƙawa basu da ita
mahaifiyar su ma basu taɓa ganin tana yawon gidan maƙwabta ba.

Sun komawa da mahaifin su da sakamako me kyau inda ya kira Shureim ya sheda


mishi, aikuwa Shureim yayi murna sosai da sosai wannan shine abinda ya kira Abdus-
samad ɗin yana faɗa mishi.

Sai dare sannan Yaya Sulaiman yazo ɗaukar Aunty, duka suka fito domin rakata
Auntyn tace; yanzu sai ku fara zuwa gyaran jiki ko?", Nusreen ta amsa da to
shikenan.

Yaya Sulaiman yace; "ke kuma meye ya ramar dake haka?, ko duk fargabar auren
ne?", Nusram tayi yaƙe kawai.

Auntyn tace; "to ni dai kunji abinda na faɗa muku dan haka zanyi zaman jiran ku
idan har kun dawo daga makaranta sai ku dinga wucewa can.

Yaya Sulaiman ya kalli Nusram bayan sun matsa gefe yace; "ƴar ƙanwata faɗa mini
matsalarki mana", Nusram ta sauke ajiyar zuciya sannan tace; "babu komai, yauwa
kayi bincike akan Shureim ɗin".

Yayi murmushi yace; "bashi da wata matsala, hakama mahaifiyar shi da mahaifin
shi kan ya rasu, gidan su gidan mutunci ne, yanzu abinda ya rage shine wannan
alhajin naki Baballe".

Nusram tayi saurin girgiza kai tace; "a'a kada kayi Yaya domin koda kayi ko baka
yi aurena dashi babu fashi", Yaya Sulaiman cikin tsokana yace; "duk soyayyar ce
haka?", Nusram ta saukar da kai ƙasa.

Haka suka yi sallama cike da ƙaunar juna kamar ƴan uwa na jini sosai, suna
ƙoƙarin shiga Isa ya ƙaraso, Nusram taja hannun Nusreen dan su shige ya tare
hanyar.

Ta gefe ta koma nan ma ya sake tarewa, ita dai Nusreen kallon ikon Allah take
yi, Nusram ganin hakan yasa tace; "Rim shiga ciki gani nan zuwa", Nusreen ta taɓe
baki sannan ta wuce.

Isa ya matso kusa da Nusram ɗin ta ja baya, ya kuma matsawa ta kuma jan baya,
har sai da ta kai jikin bango, hannu ya kai kan saman fuskar ta, Nusram ta runtse
idanu tana faɗin; wai Isa meye haka ne an faɗa maka ni ƴar iskace ko me?".

Yace; "ok nine ɗan iskan kenan? To ki ajiye a cikin ranki kema sai na maida ke
ƴar iskar, sannan ki sani wallahi matuƙar baki janye auren da kike so kiyi ba nima
ba zan janye ba nayi miki alƙawarin sai kinzo kina roƙo na akan na aure ki", yana
gama faɗar haka ya fice ya barta a wajen.

Nusram taja dogon numfashi sannan ta shige cikin gida, Mama Jummai ta kalle ta
tayi tsaki tace; "ayi dai mu gani".

Ita dai Nusram bata wani kula ta ba, koda ta shiga ɗaki ta samu an kawar da
kayan nasu hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba domin bata ƙaunar ganin kayan daya
danganci bikin kwata-kwata.

Da yamma zasu tafi makaranta Nusreen tace; "baki faɗa mini meye tsakanin ki da
Isa ba", Nusram ta kwashe komai ta faɗawa Nusreen ɗin nan fa Nusreen ta hau masifa.

Ita dai Nusram ɗin sai toshe kunne tayi dan yanzu hayaniya damunta yake yi, haka
har suka isa makarantar Nusreen bata bar mita ba.

Ƙarshe dai Nusram ɗin ta bar mata bencin, koda aka tashi haka ta dasa daga inda
ta tsaya faɗi take; "wallahi ke kika bashi dama idan banda haka taya zai iya buɗe
baki ya faɗa miki cewa wai yana son ki ko an gaya mishi bamu san asalin shi bane?,
yaushe zai haɗa ɗan sunnah da ɗan zina".

Nusram cikin takaici tace; "wai ke Nusreen kin manta a kan titi muke ne",
Nusreen ta dalla mata harara tace; "ina ruwa na ko filin arfa muke", jin hakan yasa
Nusram ɗin ƙyale ta.

********** *************

Cikin farin ciki take saukowa daga matattakalar jirgin babu abinda idanun ta ke
son gani kamar ɗan nata.

Dr Abubakar ya riƙo hannun ta ganin tana ƙoƙarin barin shi, cikin kunnen ta
yace; "haba mana rabin raina ya zaki tafi ki barni", Brr Farida ta saki murmushi.

Abdul dake tsaye a can wajen da ake jiran ƴan tafiyar ya saki murmushi ganin
yadda iyayen nashi suka yi, sai da ya ɗauke su hoto.
Dole Brr Farida ta jira mijin nata suka jero tare, Abdul ya saki hannun Adnan
ɗin ya nufi wajen Mummyn tashi, ta buɗe hannayen ta ya shige ciki suka rungume juna
cike da ƙauna da so.

Daddy kuwa wajen ƴaƴan nashi ya ƙarasa inda ya bisu ɗai-ɗai yana rungume su,
suma cikin farin ciki suke.

Brr Farida ta shafa kan Abdus-samad tace;"nayi kewar ka sosai", shima cikin
shagwaɓa yace; "nima ai kika tafi ki barni", taja kumatun shi tana faɗin; "kai ai
ka fara tafiya ka barni", suka yi dariya duka.

Hannun su sarke dana juna suka ƙaraso inda sauran suke, Abdus-samad ya saki
hannun Brr Faridar ya ƙarasa wajen mahaifin nashi suka rungume juna.

Dr Abubakar ya shafa kan Abdul ɗin yace; "Allah yayi maka albarka", Abdus-samad
ya amsa da ameen, itama Brr Farida haka tabi yaran nata duka ta rungume su har da
Fadila har tana tsokanar ta, Fadila kam murmushi kawai tayi.

Abdus-samad ya haɗa rai ganin sun nufi motar Tameer, Brr Farida tayi dariya
tace; "sarkin kishi to muje na shiga taka", Dr Abubakar ya riƙo hannun ta yace;
"gaskiya ban yarda ba, nifa kin ga kishi nake yi dashi", duka akayi dariya.

Abdus-samad ya shafa sumar kanshi yace; "shikenan kuje a tashi kawai", Brr Farida
tace; "Surayya kije motar Abdus-samad ɗin".

Surayya ta zunɓuro baki tace; "ni wallahi ba zan shiga jar mota ba kamar wata
ƴar shan jini", Brr Farida zata kuma magana Fadila tace; "Mummy ki ƙyale ta zo ki
shiga ta Yaya Sameer ni bari naje ta Abdul ɗin".

Surayya ta shiga ta Sameer ɗin, Adnan kuwa yana wajen Mummyn shi, dan haka
Sumayya da Fadila sune suka shiga motar Abdul ɗin.

Motar Sameer ɗin ke gaba sai motar Tameer sai ta Abdul, suna cikin tafiya Fadila
ta kalli Abdul ɗin tace; "gaskiya yau kun birge ni".

Ya saki murmushi yace; "meya birge ki", ta ɗan kaɗa idanu tace; "yadda kuke son
junan ku mana", Sumayya dake baya tace; "ai dama muna son iyayen mu sosai", Fadila
ta jinjina kai tana faɗin; "na tabbatar da hakan".

Sumayya ta buɗe baki zata yi magana Babbar mota ta nufo inda suke, kan Abdul
yayi wani yunƙurin kaucewa motar ta buge su.

Dr Abubakar ya kalli matar tashi, hannun ta ya riƙe yace; "na lura gangar jikin
ki ke nan amma zuciyar ki na wajen Abdul".

Brr Farida ta ƙara kai kallon ta jikin madubin a karo na babu adadi tayi
murmushi tace; "ka dena haɗa kanka da ɗana fa", kan ta rufe baki ta hangi abinda ya
faru, cikin sauri tace; "innalillahi wa'inna ilaihir-rajiiuun.

Cikin sauri suka tsayar da motocin nasu, sai ga Brr Farida na gudu zuwa wajen
motar tasu yau babu ƙasaita ba mulki ba gayu.

Duka su Daddy suma suka nufi wajen, can gefen titi motar ta faɗa kusa da wata
bishiya, gashi wajen babu mutane kasancewar bayan gari ne basu riga sun shiga cikin
gari ba suna kallo me motar ya gudu.

Da ƙyar aka iya zaro Fadila da Sumayya daga ciki, Abdus-samad kuwa sai da aka
juya motar duk ta komatse, haka aka zaro shi kamar gawa.
Brr Farida ta faɗi a wajen sumammiya, Tameer ya kira abokin shi wanda ya kasance
likita ne aka turo musu da ambulance, Sumayya kuwa dama ɗan kujewa tayi, Fadila
kuwa hankalin ta na nan amma kuma gefen fuskar ta da hannun ta na dama duka jini
ne, Abdul ne ko numfashi babu tare dashi.

#LIKE
#SHARE
#COMMENT

*Babyn Abdul, Maman Meenal Elham da Farouk*.

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*


*Heart you so much*

*Sannan ga masu son shiga whatsapp group na Rayuwar Abdus-samad kuyi searching
Aishatu Babayo sai ku tura mata da number ɗin ku ta pc zata saka ku a ciki amma dan
Allah iya mata kawai banda maza, Na gode sosai*

📖📖29-30📖📖

Babu wanda hankalin shi ke jikin shi, koda suka isa asibitin cikin sauri aka wuce
dasu *A&E* aka fara basu taimakon gaggawa. Daddy kuwa duk da kasancewar shi likita
ya kasa taimakawa da komai.

Sumayya da Fadila aka yiwa dressing ɗin inda suka ji ciwo, har ita Fadilan aka
ce ta ɗan kwanta domin ta huta.

Likitan ya fito yana cire handgloves ɗin hannun shi, da sauri suka bishi suna
tambayar lafiya??.

Likitan yace; "Dr ka biyo ni Office", haka Daddy ya bishi, sauran kuwa ji suke
kamar suyi tsuntsuwa su ji abinda ke faruwa.

Tameer ya zauna yana dafe kanshi, Sameer ya dafa shi yace; "ka dena damuwa Allah
zai basu lafiya", Tameer yayi ajiyar zuciya yace; "yanzu wani sai yayi tunanin nina
turo a kashe shi alhalin ba ni bane", Sameer ya girgiza mishi kai yace; "ka dena
faɗin haka".

Cikin tashin hankali Tameer yace; "Sameer ko ma meye Abdul ɗan uwana ne kuma ba
zan iya cutar dashi ba", ganin yadda hankalin Tameer ɗin ya tashi Sameer ɗin ya
fara kwantar mishi da hankali.

"haba Tameer ai kowa ya san ba zaka taɓa iya aikata hakan a gare shi ba, domin
kuwa ɗan uwa ya wuce wasa", Tameer dai babu abinda yake fata da buri banda Allah ya
basu lafiya musamman ma Abdul ɗin wanda yake gani kamar shike da alhakin ciwon
nashi.

Likitan yayi gyaran murya yace; "Dr ku kwantar da hankalin ku be wani ji mugun
rauni ba, ya tafi doguwar suma ne saboda tsoratar da yayi, mun duba babu internal
injuries a jikin shi, sai matar ka ita kam munyi mata allura domin ta samu ta huta
kuma shima ɗin muna saka ran nan bada jimawa zai farka, Allah ya kiyaye gaba",
Daddy ya miƙa mishi hannu suka yi musabaha yace; "ameen yana me fita daga ɗakin".

Koda ya shiga ɗakin, suna kwance zaka iya tunanin barci ma suke, sai dai shi
Abdus-samad ɗin hannun shi ɗaure da drip.

Sameer da Adnan suna jikin gadon mahaifiyar su, Tameer kuwa yana can zaune a
gefe ne jikin window ɗin ɗakin tana kallon waje yanzu ya gama waya da Surayya yana
faɗa mata abinda ya faru.

Daddy ya koma jikin gadon Abdus-samad ɗin ya tsaya, yana me tausayawa yaron
wannan wane irin abu ne rayuwar yaron tana cike da hatsarrurruka gashi be san komai
daga rayuwar shi balle ya dinga ƙoƙarin kare kanshi daga hatsarin.

Surayya ta buɗe ƙofa ta shigo hankalin ta a tashe, ta faɗa jikin mahaifiyarta


tana sakin kuka sosai. Tameer da Sameer suke rarrshin ta dan Adnan ganin Auntyn shi
tana kuka shima kukan ya fara Daddy kuwa ya kasa ce musu komai.

Ta goge hawayenta tana mata addu'ar samun sauƙi, can ta ɗago kanta; "ina
Sumayya?", kanta rufe baki Fadila ta bude ƙofa ta shigo bayan ta kuma Sumayya ce.
Itama Sumayyar wajen ƴar uwarta ta nufa suka rungume juna suna kuka, Surayya ta
sake ta sannan ta janyo Fadila itama ta rungume".

Daddy kam ikon Allah yake kallo, babu wanda ya kalli gadon da ɗan nashi yake
kwance lallai ya tabbatar da cewa har yanzu Brr Farida bata shirya kan yaran nata
ba.

Daddyn Fadila yayi sallama ya shigo tare da mahaifiyar su, cikin sauri Fadilar
tayi wajen iyayen nata ana jajantawa juna, Fadil da Salima sune suka shigo daga
ƙarshe.

Wajen gadon Abdus-samad ɗin suka nufa su direct, cikin damuwa Fadil yace; "Daddy
har yanzu be farka bane?", Daddy ya dafa kanshi yace; "zai farka insha Allahu nan
bada jimawa ba kuyi haƙuri tukunna.

Nan suka koma suka zauna jugum domin kuwa daga Brr Faridar har Abdul ɗin babu
wanda ya farka har zuwa lokacin kowa kuma a ciki fatan shi shine su tashi lafiya
lau.

Salima na riƙe da hannun shi tana zubar da hawaye domin kuwa hankalin ta ya kasa
kwanciya, bata so ta rasa abinda take so.

Fadila ta kalle ta sannan ta taɓe baki, ita fa ba wannan bane ya dameta, kuma
ta san suna son abinda ba zasu taɓa samu bane daga Husnar har Salimar.

Fadila ta dubi Fadil tace; "ina su Hajja banga sun zo ba?", Fadil ya taɓe baki
yace; "kema kin san halin ƙasaitar matar nan waye zai iya zaman jiran ta, Malama
tana so ta biyo mu amma matar nan ta hana wai sai dai ta jira ta su taho tare, baki
ga yadda hankalin Malama ya tashi ba ina jin har kuka sai da tayi amma wai Hajja
taƙi bari a taho da ita......". Daddyn shi ya kai mishi duka a ƙeya yace; "Fadil
baka da hankali ko uwar tamu kake faɗawa haka muna wajen", be kuma cewa komai ba
sai shafa wajen da yayi yana turo baki.

*********** ************
*UNGUWAR RIMI, KADUNA*

Shureim ya zauna kusa da mahaifiyar shi wacce ke zaune cikin kayayyaki, tunda
taji labarin bikin nan hankalin ta ya koma kai.

Tace; "ya akayi fatan an gama komai, ka san bana so azo a sami matsala ga
Sharifa har yanzu bata iso ba", Shureim yace; "me kuma Aunty Sharifar zata yi?",
Mama tayi mishi daƙuwa tace; "zaku je a ƙaro abubuwan da babu ne, Usman ma munyi
waya akan sarƙoƙi da zai ƙaro ya dai ce yana tunanin a satin nan kayan zasu iso".

Shureim ya kwantar da kanshi jikin mahaifiyar tashi yace; "Mama lallai kina ji
dani", ta shafa kanshi tace; "wa nake dashi banda kai, Shureim kai nake gani na
tuna da mahaifinka, dole na fito na nuna bajinta akan aurenka, ɗana guda ɗaya tilo.
Sharifa tayi dariya tana karasa shigowa gidan tace; "Aunty kenan, kullum firar ku
kenan".

Mama tace; "to idan bashi ba ɗin da waye zanyi", Sharifa ta zauna kusa ɗa ƴar
uwar tata sannan ta tura mata ledar gaban ta tace; "gashi mun riga da mun siyo da
naga mun biyo ta wajen Mall ɗin tare da Baban Naufal shine nace mu ƙarasa kawai mu
siyo".

Mama ta fara ɓuɗewa tana faɗin; "yauwa gaskiya na gode sun kuma yi kyau sosai",
ta ƙarasa tana ɗaga ɗogunayen rigunan".
Aunty Sharifa tace; "nima sun birge ni shi yasa na ɗauko su", Shureim ya miƙe
yana faɗin; "bari na tafi wajen aiki".

Mama tace; "yanzu ƴar tawa sai bayan biki zan ganta kenan?", Shureim yace; "Mama
kinfa santa ina wacce ranar da zan kai ki Airport.....".

Kafin ya ƙarasa ta miƙe tana washe baki tace; "madallah kamar ka san yarinyar
tana cikin raina, saboda hankalin ta nayi maka sha'awar ta gaskiya naji daɗi na san
zan ji daɗin zama da ita ba kamar ƴar uwar ta ba, yarinya sai tsiwa". Gaban Shureim
ya faɗi kada dai Mama tace bata son Nusreen.

Aunty Sharifa tace; "wai wacece kuke magana akai", nan Mama ta shiga bata
labarin ƴan biyun da suka haɗu a hanya da yadda ɗaya tayi musu rashin kunya ɗayar
kuma ta basu haƙuri. Sharifa ta washe baki tana faɗin; "lallai kam tana da hankali
sosai kuma ta cancanci ta shigo cikin wannan familyn".

Shi dai Shureim a jiki a sanyaye ya bar falon domin kuwa abun yana so ya caɓe
masa dole ya san yadda zai yi, ya kira Naufal a waya nan ya shiga faɗa mishi abinda
ke faruwa.

Naufal yace; "yanzu meye abin yi tunda dai biki ya matso ni ina ganin kawai ka
faɗa mata gaskiya, dan koda baka faɗa mata ba wata rana zata gane idan kayi
la'akari da yadda Nusreen take da tsiwa ba iya ɓoyewa zata yi ba".

Shureim yace; "nima abinda nake tsoro kenan kada fa garin son zuciyana na nemo
abinda zai zo ya ɓatawa Mama ya kuma janyo matsala tsakani na da ita, banda kowa a
yanzu sai ita".

Naufal yace; "hakane amma duk da haka baka sani ba ko meye dalilin da abubuwan
suke faruwa a haka ba ta yiwu alkhairi ne auren ku".

Shureim yace; "hakane", Naufal yace; "ni ina ganin ka faɗa mata kawai", Shureim
yace; "shikenan zan gwada ɗin", daga nan kuma Naufal ya koma tsokanar Shureim ɗin
har sai da Naufal ɗin yaga Shureim ya saki jikin shi sannan suka rabu a wayar.

******** ***********

*HAYIN RIGASA, KADUNA*

Ummi ta zauna kusa da Nusram wacce ta zuba uban tagumi kamar anyi mata mutuwa,
ta dafa ta tace; "Nusram na faɗa miki tƴmun farko idan har bakya son wannan auren
to ki faɗa mini ni kuma zan saka a hana".

Nusram ta ɗago idanun ta wanda yake cike da hawaye tace; "Ummi kada ki damu da
wannan insha Allahu zan yiwa Baba biyayya koda kuwa me zai faru".

Ummi tace; "ban tambaye ki biyayya ga mahaifinki ba ko akasin hakan, tambayar da


nayi miki shine kina son shi ko bakya son shi?".

Nusram tayi murmushi me ciwo tana saukar da kai ƙasa, sanin cewa ba zata yi
magana ba yasa Ummi miƙewa tana faɗin; "ke kika sani tunda ba zaki iya buɗe baki
kiyi magana ba".

Nusreen dake ƙoƙarin shigowa hannun ta riƙe da babbar leda don ta dawo ne daga
Tudun Nufawa tace; "Ummi meya faru".

Ummi tace; "meye kuwa be faru ba ni da ƴar uwar ki ne gata can taƙi ta faɗi
abinda ke ranta game da auren nan".
"ni wallahi abin na damuna Ummi, Nusram duk tabi ta lalace ta ƙare, gashi wajen
gyaran jikin ma ta dena zuwa kana yi mata magana sai kuka Ummi ina tsoron kada
damuwar da take ciki ya kaita ga halaka", Nusreen ta ƙarasa cikin damuwa.

Ummi taja tsaki tace; "to ba ita taso ba, Nusreen ta fito ta cewa Baban ku bata
son auren ta kasa sai dai ta zauna a cutar da ita".

Nusreen tace; "bari naje wajen ta naji meke faruwa", tana faɗin hakan ta wuce
Ummi zuwa cikin ɗakin.

A zaune kamar yadda Ummi ta barta haka ta zo ta same ta, Nusreen tace; "Nusram
ki yiwa Allah ki faɗa mana menene damuwar ki".

"auren ne Nusreen bana so, kuma ba zan iya faɗawa Baba ba", wannan shine abinda
zuciyar ta ta faɗa amma sai tace; "Nusreen ki taya ni da Addua kawai".

Koda Nusreen ta takura mata kuka ta sakar mata kawai, cike da tausayi Nusreen
ɗin ta biye mata suka dinga rera kukan tare sai da Ummi ta shigo tayi musu tatas
sannan suka yi shiru.

********* **********

*UNGUWAR SARKI, KADUNA*.

Tameer ya kalli agogo sannan ya kalli Daddy yace; "Daddy har yanzu shiru basu
farka ba kome ke faruwa kuwa".

Daddy shima cikin damuwa yace; "ku cigaba da addu'a zasu farka ne", haka suka
yarda da shawarar mahaifin nasu.

tana tsugunne tana kuka cikin tashin hankali, taji an dafa kafaɗarta, cikin
sauri ta waigo fuskar da ba zata taɓa mantawa bace take kallon ta.

Itama ta tsaya tana kallon ta, waccen matar tace; "Bestyy kin yi sanyi dole ki
ƙara gudun tafiyar ki idan ba haka ba Mustafa yana daf da cin miki".

Cikin yanayi na rashin madogara da kuma karyewar zuciya Brr Farida tace; " taya
zan aikata hakan bayan ban san inda Abdul yake ba, ji nake kamar ya tafi ya bar ni,
Abdus-samad shine ƙarfi na yanzu kuma babu shi".

Matar tayi murmushi tace; "kada ki damu ɗanki na nan be tafi ba, zo muje ki
ganshi", ta kama hannun Brr Farida zuwa wani kyakykyawa Lambu ta ɗaga hannu ta nuna
mata inda Abdus-samad yake zaune fuskar shi ɗauke da murmushi yana kallon ta.

Cikin jin daɗi ta nufi inda yake sai dai kafin ta kai wani irin jibgegen Shaho
da jajayen kaya yazo ya sungume Abdul ɗin yayi sama dashi, nan fa Brr Farida ta
fara Kuka tana ƙwalawa Abdul ɗin kira.

Daddy ya riƙo ta yana tofa mata addu'a, ita kuwa da bata san yanayi ba kukan ta
kawai take sha tana kiran sunan Abdul ɗin.

A hankali kuma idanun ta ya fara buɗewa har ta buɗe shi tas, shiru tayi tana
kallon su ɗai-ɗai sai taji ranta yayi sanyi sanin cewa mafarki take yi.

Tayi murmushi tace: "kaga ashe mafarki ma nake yi, ja ɗauka gaske ne ina Abdul
ɗin?", Dr Abubakar yace; "calm down My Brr ɗanki yana lafiya", jin hakan ya tuno
mata da mafarkin ta.
Sai tayi murmushi tace; "ina yake My Dr ina son ganin shi, na san duk inda nake
zai kasance a wajen?", Sumayya ta ƙaraso kusa da ita tace; "Mummy Abdul barci yake
yi yanzu ko kina so a tashe shi ne?".

Ta girgiza kai da sauri tana lumshe idanu sai dai cikin sauri ta buɗe su sannan
ta sauke kan Fadila wacce kanta ke manne da plaster, a hankali kuma komai ya fara
dawo mata cikin kai.

Cikin sauri Brr Farida ta fara yunƙurin miƙewa amma Dr Abubakar ya hanata, gaba
ɗaya ta ruɗe tana faɗin; "shikenan sun kashe mishi shi".

"yanzu meya faru dashi ya mutu ko?, na dena ganin shi?", magan-ganu dai kala-
kala, ganin bata hayyacin ta yasa Dr Abubakar riƙo ta jikin shi ya rungume ta saki
kuka me ƙarfi.

Kowa yana tausaya mata, Abban Fadil sai da jikin shi yayi sanyi sanin irin
ƙaunar da take yiwa ɗan nata, ya kalli gadon da Abdul ɗin ke kwance kamar gawa.

Malama da Saleema kuwa duk idanu ya kumbura tsabar kuka, Hajja ce ma dai ta dai
yi hawayen amma ba kamar su ba dan itama yadda tazo ta same su abin ya bata mamaki.

#LIKE
#SHARE
#COMMENT

*babyn abdul maman meenal elham da farouk*

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

*Ga masu cewa ina jan littafin ne dan na samu kuɗi, Wallahi ba haka bane domin kuwa
da ina son siyar da littafi da tuni nayi sai dai ina so ku sani kuɗin ku bashi ne a
gaba na, duk wanda ya ɗauki wani abu ya bani ya bani dan raɗin kanshi ne ba wai dan
na tambaye shi ba, hasalima kyautatawa ce tsakani na dasu, rubutun novel buri na ne
dan haka bana fatan ko gaba nayi novel ɗin siyarwa, na gode sosai to ai hikenan😉*.

*Godiya ta musamman ga Zuciya ta, da kuma Matar so ina miki son so sannan ina jin
daɗin sharhin ki sosai Shabihaty fans club kuna ƙarƙashin zuciyar One Love*

*Sannan ga masu son shiga whatsapp group na Rayuwar Abdus-samad kuyi searching
Aishatu Babayo sai ku tura mata da number ɗin ku ta pc zata saka ku a ciki amma dan
Allah iya mata kawai banda maza, Na gode sosai*

📖📖31-32📖📖

*UNGUWAR SARKI,KADUNA*

Cikin sauri ya buɗe idanun shi yana faɗin; "innalillahi wa'inna ilaihir-
raji'uun", ƙoƙarin miƙewa yake yi Brr Farida ta riƙo shi cikin sauri.

ya rungumeta yana sakin ajiyar zuciya, Brr Farida kuwa harda ƙara ƙaƙumeshi
hawaye yana saukowa daga idanun ta.

Tameer ya shigo tare da likitan da yaje kira, sai a lokacin suka saki juna
allurar barci ya kuma yi mishi babu ɓata lokaci barcin ya kuma kwashe shi.

Hajja tace; "tunda yayi barci bari muzo mu tafi Allah ya ƙara sauƙi,
Mus'ab(Abban Fadil) ka tashi muje ka sauke mu a gida".

Haka ba dan sun so ba suka miƙe dukkan su, bayan sun tafi Brr Farida ta kalli
Surayya tace; "kuma ku wuce gida, na san zuwa anjima zasu sallame mu", haka suma
suka tafi cikin jimami Sameer ya tafi kai su.

Ya rage saura Tameer da Brr Farida da Dr Abubakar, hakan yasa wajen yayi shiru,
ita dai Brr Farida tana riƙe da hannun Abdul ƙam-ƙam kamar za'a ƙwace mata shi.

Lokaci zuwa lokaci take sauke ajiyar zuciya, kallon shi take cikin tausayawa
tabbas da saka hannun wani a wannan lamarin to waye kenan?.

Amsar da ta kasa samu kenan, bata da tabbacin wanda take zargi domin kuwa bata
da wata hujja.

Kamar ance ta ɗaga ido ta kalli saitin window idanun ta ya hasko mata dattijon
dake tsaye jikin window.

Ƙara zaro idanu tayi gabanta yana dukan uku-uku, shima kuwa ganin ta hango shi
yasa yayi saurin barin wajen.

Brr Farida ta miƙe a kiɗime, Dr Abubakar da be san meke faruwa ba yace; "My Brr
ina zuwa kuma?", ta bashi amsa yayin da take ficewa daga ɗakin; "ina zuwa".

Sauri take yi kamar ƙafarta zata tsinke ta fice ta zagaya bayan window ɗin, sai
dai kash baya wajen nan ta hau jefa idanu tana neman ina zata ganshi.

Har bakin get taje neman shi sai dai Allah be bata sa'ar ganin wanda taje nema ba
haka ta gama zagayen asibitin ta dawo.

Tana daf da shiga ɗakin idanun ta ya sauka a kanshi, da sauri ta ƙarasa kusa
dashi, shima kuma ita yake kallo fuska gwanin tausayi.

*MUSTAPHA ABUBAKAR TUGE* sunan data ambata kenan a bayan ta iso kusa dashi, ya
kalli mutanen wajen sannan ya maida idanun shi kanta itama ta kalle shi ta ɗaga
gira ɗaya.

"ko nace Mustapha Sulaiman harɗo, wanne yafi dai-dai? Yadda kake da fuska biyu
hakama sunan ka yake".

Alhaji Mustapha ya kalli kanshi ya ƙara kallon jama'ar wajen yana da tabbacin
dan basu gane ko waye shi bane da yanzu sun cika wajen dan kowa ya san shi a faɗin
garin kaduna kai kaf Nigeria yana ɗaya daga cikin masu kuɗi na farko-farko, gashi
kuma da taimakon jama'a sosai wannan ya ƙara mishi farin jini.

Cikin kwantar da murya yace; "Brr dan Allah kizo muje garden ina so muyi magana
dake".

Brr Farida tace; "babu magana tsakani na da kai domin babu abinda ya haɗa ni da
kai", ta ƙarasa cikin ɓacin rai.

Ya sauke ajiyar zuciya sannan yace; "naji ance Murad yayi hatsari ne shine nazo
duba shi, naga jikin nashi ma da sauƙi hankali na ya tashi sosai ina ƙasar Mali
labarin yazo mini", ya ƙarasa fuskar shi ɗauke da damuwa.

Brr Farida ta taɓe baki sannan tace; "kamar da gaske yadda ka maida fuskarka sai
kace na Allah, to bari kaji kana ɗaya daga cikin prime suspect ɗina kuma zan yi
bincike matuƙar da saka hannun ka akan abinda ya sami Abdul bar ganin kana da kuɗi
zan tarwatsa farin cikin ka ne".

"haba Farida ya kike magana haka, kada ki manta nine mahaifin Murad ba zan taɓa
iya cutar dashi ba, waccen ma baki fahimta bane kuma Fiddausi ma..........".

"dakata ya ishe ni haka! Ka tabbatar ka bar wajen nan domin dai ka sani koda
wasa ba zan taɓa bari kaje kusa da ɗana ba ko?, Sannan nayi maka gargaɗi ba sau
ɗaya ba, ba sau biyu ba akan ka fita harkata nida ɗana kaƙi ji ko? To wallahi zan
ɗauki babban mataki akan ka", tana gama faɗar haka ta shige ta barshi a tsaye.

Alhaji Mustapha ya tsaya cike da takaici gashi yana so ya ga lafiyar ɗan shi
amma babu dama, ya kalli kayan dake jikin shi riga daban wando daban sai hula irin
taɓani kaji hadisin nan, wannan duk yayi ne dan yazo yaga lafiyar yaron nashi amma
abu be yiwu ba haka ya tafi.

Brr Farida kuwa tana shiga ta sauke ajiyar zuciya sannan ta dai-daita natsuwar
ta kafin ta ƙarasa inda yake.

Abdul daya farka yana tambayar ina Mummyn shi ganin ta yasa ya danyi murmushi
amma be samu martani ba zama kawai tayi gefen gadon.

Ya ɗora kanshi saman kafaɗar ta, ita kuma ta lumshe idanu har yanzu ƙirjin ta be
bar bugawa ba, Dr Abubakar ya zuba mata idanu kawai ganin yadda fuskar ta tayi ya
san akwai abinda yake damun ta.

Sun jima a haka sannan likitan ya shigo, yayi murmushi yace; "da alamu dai
wannan jinyar ta ƙare ganin yadda majinyacin ya zama ɗan lele", duka suka yi
murmushi banda Brr Farida.

Nan ya bashi magunguna sannan ya fice, da ƙyar aka samu ya sha maganin sai
shagwaɓe fuska yake yiwa Mummyn nashi ganin yadda fuskar Brr Faridan yake yasa ya
koma serious.

Sai da ta gama bashi sannan yace; "First love lafiya? Meke damun ki?", ta riƙo
hannun shi sannan tayi yaƙe tace; "kada ka damu babu komai me zai dame ni bayan
ɗana ya buɗe idanun shi bayan doguwar sumar da yayi".

Yinin ranar haka Brr Farida tayi shi sukuku domin kuwa motsi kaɗan sai taga
kamar Alhaji Mustaphan zai dawo inda suke yazo ya cutar mata da ɗa.

******** ***********

*HAYIN RIGASA, KADUNA*

Kwanci tashi babu wuya gashi Allah ya nuna mana lokaci domin kuwa yau saura sati
ɗaya bikin su Nusreen, duk ɓangaren uku shirye-shirye suke babu kama hannun yaro.

Nusreen a lokacin idan ka ganta kamar ka sace ta ka gudu tsabar kyawun da tayi
saboda ta tsaya sosai Aunty ta gyara ta kuma yadda ya kamata jikin ta har wani
sulbi yake yi ga wani yelo-yelo da tayi tsabar haske da dilka data sha.

Saɓanin Nusram da tayi baƙi ta rame sai idanu zuru-zuru, irin farin cikin nan da
amarya take yi kam to banda Nusram domin kuwa tunda satin bikin ya kama ta tabbatar
da cewa auren za'a yi mata da Alhaji Baballe ta kwanta zazzaɓi ya rufe ta.

Yanzun ma tana kwance jikin ta yayi zafi rau, sai rawar sanyi take yi Nusreen ta
shigo ita da Yasmin ƙawarta, sun dawo daga rabon kati duk wani wanda ya kamata su
kaiwa to suna ta ƙoƙarin kai mishi.

Gaba ɗaya hidimar daya kamata ayi ta da Nusram sai Yasmin ce ta wakilce ta,
Halima ma tazo duk da ba sa'ar su bace amma takan taimaka musu wajen yin hidimar
bikin.

"wallahi na gaji sosai gashi gobe ma sai mun sake fita", Nusreen ta faɗa tana
ƙoƙarin zama gefen katifar da Nusram ke kwance.
Yasmin tace; "ai gobe kinga Hayin banki zamu shiga sai kuma Shaheeda da take
Unguwar Sarki shikenan sai mu dawo".

Nusreen ta yamutsa fuska tana faɗin; "nifa dan dai kin matsa ne amma da bazan
wani kaiwa Shaheeda ba", Yasmin tace; "aikuwa ya kamata, dan Shaheeda tana da
ƙoƙari kuma ta gayyace ki bikin yayan ta, dan dai kin ƙi zuwa ne".

Nusreen bata ce komai ba sai hannu data kai kan jikin Nusram; "kai Ram jikin ki
zafi fa baki da lafiya ne?".

Nusram ta ɗaga kai kawai hawaye na zubo mata, Nusreen tace; "to kin sha magani",
nan ma Nusram ta ɗaga mata kai kawai, "Allah ya baki lafiya to", Yasmin tace;
"ameen dai".

Nusreen ta miƙe taje ta zubo musu abinci ta kawo nan suka fara ci, ita dai
Nusram zazzaɓin banda ƙara rufe ta da yayi ga wahala, shaƙar ƙamshin abincin da
taji amai ya taso mata.

Tayi ƙoƙarin miƙewa ta fice daga ɗakin tana ƙarasawa bakin famfo ta fara sheƙa
amai me wahala domin kuwa babu komai a cikin ta wanda zata fitar dan rabon data kai
abinci bakin ta tun jiya da rana shima sai da Nusreen tayi kuka a gabanta sannan ta
yarda ta ci da dare kuwa tun kan Nusreen ɗin ta fara kuka ita ta fara domin bata
son cin komai dan ɗaci yake yi mata sosai.

Aunty dake tsaye a ƙofar ɗaki suna lissafin kuɗi da alama matar da zata yi musu
dubulan da cin-cin ne tayi saurin ƙarasowa kusa da Nusram ɗin tana yi mata sannu.

Ita ta taimaka mata har ta gyara jikin ta sannan ta wanke wajen tas, ta ƙwalawa
Nusreen kira babu ɓata lokaci ta fito.

"kamata kuje ɗaki", Nusreen tace; "to Aunty aman tayi ne?", Aunty tace; "eh
wallahi ai inajin Yayan ku yana zuwa zasu tafi asibiti tare".

Mama Jummai dake kusa da murhu kamar koda yaushe tayi shewa tace; "ai amai yanzu
ta fara shi kuma muddin ina raye bata ba aure", babu wanda yabi ta kanta.

Da yamma Yaya Sulaiman ya tasa Nusram a gaba suka je wani ƙaramin asibiti nan aka
dubata aka bata magun-guna suka dawo gida.

********* ***********

*MAƘARFI ROAD, KADUNA*.

ya zauna yana me ajiyar zuciya, meke faruwa ne, shi kanshi baya da tabbas ɗin
abinda yake faruwa yanxu".

Ɗayan mutumin dake zaune kusa dashi yace; "ka kira ni tun ɗazu amma baka ce
mini komai ba, meke damun ka ne Tuge?".

Alhaji Mustapha ya sauke tagumin da yayi sannan yace; "Brr Jibril ina cikin
tashin hankali, ɗana baya da lafiya yana asibiti".

Saura kaɗan tray ɗin da matar ta shigo dashi a hannu ya faɗi, yar kyakkyawa da
ita baƙa mara tsayi, kana ganin ta zaka tabbatar da cewa itace matar gidan.

Sai da ta dai-dai ta natsuwar ta sannan tayi sallama ta shiga, kusa da Brr Jibril
taje ta ajiye tray ɗin sannan ta matsa kusa da mijin nata tana miƙa mishi hannu,
yayi kissing hannun.
"Abban Khausar zan koma wajen aiki domin yanzu muka yi waya da Md yace nazo da
sauri", matar ta faɗa.

Alhaji Mustapha yace; "a dawo lafiya", daga haka ta fice cikin sauri.

Brr Jibril yace; "ya jikin nashi fatan da sauƙi dai ko?", Alhaji Mustapha ya
ɗaga kai yace; "da sauki sosai sai dai Brr Farida bata barni na ganshi sosai ba".

Brr Jibril yace; "kada ka damu Alhaji wata rana komai zai zamo me sauƙi insha
Allahu ka dage da addu'a kawai".

"Brr Jibril tana zargina da yunƙurin kashe ɗan dana haifa", Alhaji Mustafa ya
faɗa cike da damuwa, Brr Jibril yace; "kada ka damu just pray", yayi mishi sallama
sannan ya fice.

Cikin tashin hankali take tuƙi, bata ma jira masu tsaron lafiyar nata ba, sai da
ta gangara can wajen Kaduna by pass sannan ta gangara zuwa wani gidan gona.

Tayi horn me gadi yazo ya buɗe mata sannan ta shiga, tana yin parking sannan ta
fito daga motar kamar zata tashi sama tana shiga ciki ta sami kujera irin ta
shaƙatawa ta zauna.

Mutumin dake cikin ruwan tare da wata mace suka fito a tare, duka kallon ta suke
yi cikin alamun tambaya.

"Abdus-samad be mutu ba", ta faɗa cikin takaici, ɗayar tayi murmushi tace; "na
san da hakan ai tun jiya dan har su Malama da Hajja sun je dubo shi".

Mutumin yayi dariyar mugunta sannan yace; "aikin Razor beyi ba, dan haka na tura
Scorpion da saƙo zuwa gare shi".

Dukkan su sun san saƙon kona meye dan haka suka yi murmushi, Mutumin yaja kujera
kusa da Matar ya zauna sannan ya riƙo hannun ta yace; "Salma kada wannan abin ya
ɗaga miki hankali, Abdus-samad zai mutu dole ne wannan koya so ko be so ba domin
babu wanda ya isa ya hanani kauda shi daga bayan ƙasa".

A'a bawan Allah akwai Allah fa, kuma dama idan kwanan mutum ya ƙare ai dole ya
mutu😏.

Hajiya Salma ta saki ajiyar zuciya sannan tace; "tabbas hakane amma Alhaji
Sa'eed ina tsoron abinda zai biyo baya, bana so mustafa ya mutu ace bani zan gaji
dukiyar shi ba ni da yarana kawai nake so su gaji ɗumbin dukiyar shi".

Alhaji Sa'eed yayi murmushi yace; "kada ki damu ke da ƴaƴan ki kawai zasu
gaji dukiyar Tuge sai dai zaki san mana nida Baby na", ya ƙarasa yana kanne ido
ɗaya.

Salma ta kalli Brr Hauwa suka yi murmushi tare, Alhaji Mustafa yace; "yanzu zan
sami biyan buƙata ko?".

Salma tace; "me zai hana sai dai kayi da sauri dan bana so Alhaji ya fahimci
daɗewar da nayi gashi ban fito da Securities ba".

"ba matsala just one hour ma yayi", ya faɗa yana riƙo ta daga nan suka shige
ciki inda suka bar Brr Hauwa zaune a wajen tana shan iska.

Alhaji Mustafa kuwa ya jima kafin ya tashi ya fito, a falo ya sami yaran nashi
guda biyu da Khausar babbar kenan wacce a satin nan ta dawo daga ƙasar Singapore
inda take karatun likitan mata, sai mai bi mata Khaleesat wacce take NIGERIAN
TURKISH INT ABUJA, tana secondry.

"Yauwa Daddy dama maganar shopping ɗin da muka yi", Khaleesat ta faɗa cikin
shagwaɓar yaran masu kuɗi.

"yanzu duk kuɗin dake account ɗin ki Khaleesat sai kin tambaye ni?, kije wajen
Habu ya kaiki zan miki tranfer yanzu".

"yauwa amm.......", yayi saurin dakatar da Khausar dake ƙoƙarin yin magana
yace; "ina buƙatar hutu", daga haka ya wuce kawai.

Khausar ta taɓe baki, Khaleesat kuwa murna sosai tayi sannan ta haye sama inda
ta hau shiryawa domin tafiya siyayya ɗin.

Sai bayan magrib sannan Hajiya Salma ta dawo, sai da ta shiga nata ɗakin tayi
wanka ta sake shiryawa cikin riga da skirt ɗin material me kyau da tsada sannan ta
fito.

Kitchen ta shiga ta haɗa Coffee sannan ta nufi sama inda ɗakin me gidan nata
yake.

Ta shiga da sallama, yana yin waya ne dan haka koda ta ajiye sai ta nemi waje
ta zauna, Alhaji Mustafa ya kalle ta sannan ya miƙe ya fice daga ɗakin, Hajiya
Salma ta taɓe baki.

"Alhaji Mustafa ka bani mamaki yanzu har kaine zaka iya zuwa dubo ɗan ka ba tare
da sani na ba".

Alhaji Mustafa yayi jim sannan yace; "amma dai Alhaji Sa'eed ka san da cewa
yaron nan shi kaɗai ne ɗana namiji ko, sannan kuma dole sai na shiga jikin su sosai
kafin na iya aiwatar da umarni Oregbu a kanshi".

Alhaji Sa'eed yayi murmushi sannan yace; "hakane kuma tabbas, yanzu ya jikin
nashi", Alhaji mustafa ya sauke ajiyar zuciya yace; "Brr Farida bata barni na shiga
ba".

"toh! amma dai ina so na ƙara tuna maka da cewa saɓawa umarnin Oregbu dai-dai
yake da ɗaukewar numfashin ka dan haka kada son ɗanka ya saka ka saɓa mishi".

Alhaji Mustafa kamar zai zubar da hawaye yace; "na sani kuma zan aikata hakan
insha Allah", daga haka ya katse wayar.

Ya jingina da jikin steps ɗin yana sauke ajiyar zuciya, ya zai yi ne?, ɗan shi
ƙwara ɗaya tal wanda yake tsananin ƙauna shi zai bawa Dodo ya sha jinin shi, meya
saka tun farko ma.yayi wannan alƙawarin".

Oho maka dai kai ka sani😏 Me kan gwanda.

Aishatu Babayo ta ranƙwashe ni tace; "idan kika kushe shi ai kamar kin kushe
Abdul ne baki ganin kamar su ɗaya".

Na taɓe baki ina me ƙare mishi kallo, tabbas abinda Zuciya ta(Aishatu Babayo) ta
faɗa gaskiya ne kamar su ɗaya da Abdul bambamcin su kawai girman jiki dan Alhaji
Mustafa ya ɗan manyan ta.

*Na san wasu zasu ce yau kuma ina One love ta tafi, naji sabbabin suna to ai dama
sabbabin suna ba xasu ƙare a buk ɗin nan ba har sai mun kai tsakiya ko ince kusa da
ƙarshe sannan ba lallai ku fahimci littafin ba sai munje ƙarshe shima ko.ince
tsakiya, fatana dai kuyi haƙuri ku cigaba da bina duk da dai na san ina muku ƴar
zilliya amma kamawa tayi ina kuma ƙara baku haƙuri domin kuwa na san cewa kuna
haƙuri sosai*.

#LIKE
#SHARE
#COMMENTS

*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖33-34📖📖
*UNGUWAR SARKI, KADUNA*.

Sai da Abdul ya ƙara kwana biyar a asibiti sannan aka sallame shi, kuma
Alhamdulillahi jikin shi yayi sauƙi sosai da sosai.

Sameer ya kaisu har gida inda ya tarar da su Suraiya suna mishi barka da
dawowa, yaji daɗi sosai hakama Brr Farida ita da Dr Abubakar duka sun ji daɗi.

Ɗakin shi ya wuce yayi wanka sannan ya kwanta domin ya huta, sai dai kanshi da
yaji yana sara mishi wanda hakan yasa barcin yaƙi zuwa.

Ya jima a kwance kafin wayar shi ta hau ƙara, ya ɗauko ya kara a kunne,
"yallaɓai y gida ya aiki?", dama cewa nayi bari na tuna maka ɗaurin aure na 28th
Feb 2020, nan da jibi kenan".

Abdus-samad yace; "insha Allahu ba zan manta ba zan zo kuma", Shureim yace;
"yauwa nagode sosai na bawa Fahad IV zai baka".

Yace; "shikenan, sai anjima", daga haka suka yi sallama, be jima ba barci ya
kwashe shi.

Sai wajen la'asar ya farka, yayi alwala ya rama sallar dake kanshi sannan yayi
wanka ya fito, a falo ya sami Fadila da Surayya suna fira.

Duka suka yi mishi sannu da jiki ya amsa shima, waje ya fita kawai inda ya tarar
da Sumayya da Tameer a zaune.

"barka da fitowa Yah Abdul ɗazu ai naje wajen ka amma kana barci sai na ƙyale
ka", cewar Sumayya, Abdus-samad yayi murmushi yace; "hakane, Yaya Tameer barka da
hutawa".

"barka ya jikin", ya tambaya, sai da ya shafa gashin kanshi sannan yace; "da
sauki", daga haka babu wanda ya kuma magana a tsakanin su.

Abdul yana zuba musu idanu da alama fira suke yi akan wani abu me mahimmanci,
"Yaya ni ina ganin kawai ka sami Daddy da maganar".

"kin san halin Mummy shiyasa nake so ki fara sanarwa da Daddy ke da kanki idan
yaso sai ni nayi mata magana daga baya", Sumayya tayi dariya tace; "to Yaya na".

"tunda kina son a fita dake anjima ba", ta kuma yin dariya tace; "Yaya ai
kaima buƙatar kanka ta tashi", yace; "to ya isa haka".

Motoci suka fara shigowa gidan dan haka duka suka maida hankalin su kan
motocin, sai da suka gyara parking sannan Brr Farida ta fito ita da mijin ta.

Abdus-samad ya miƙe da farin ciki ya tare ta, ta mishi peck a goshi sannan tace;
"ka gama barcin kenan?, na shiga wajen ka ai Daddyn ku na raka wajen wani tsohon
abokin shi wanda ya kusa aure".

Duka suka yi dariya, Brr Farida ta harare su duk suka yi shiru banda Abdus-
samad, tace; "kai kuma ba zaka dena ba kenan?".

Ya ɗora yatsun shi biyu saman leɓen shi, Tameer yace; "saboda Allah me sa'an
Daddy zai yi da mata?", Brr Farida tace; "sai kaje ka tambaye shi".

Abdus-samad ya kauda kai gefe yace; "ni tsorona ma ace tare da Daddy zasu
angwance, dan maza ba abin yarda bane".
Brr Farida ta kalli Dr Abubakar da sauri, cikin sauri ya girgiza mata kai yana
faɗin; "me zan yi da wata amarya a yanzu ai ke kin ishe ni".

Brr Farida tace; "kai dai ka sani wallahi ka sake ka ƙara aure kai da matar sai
na maka ku kotu", suka kwashe da dariya, cikin jin haushi ta shige cikin gidan ta
barsu.

Dr Abubakar ya gallawa Abdus-samad harara yace; "kana neman janyo mini tashin
hankali ko", ya saukar da kanshi ƙasa yace; "yi haƙuri Daddy", ya rasa me yasa duk
soyayyar da mahaifin nashi yake nuna mishi baya iya sakewa dashi kamar yadda yake
sakewa da Mahaifiyar shi, sai ya dinga jin nauyin shi sosai.

Nan ya zame yayi part ɗin shi ya barsu suna cigaba da yiwa Daddy dariya dan
haƙiƙanin gaskiya ya kasa shiga gidan.

******** *************

Baba ya gyaɗa kai bayan ya gama sauraren bayanan Ummi sannan yace; "Maman Kubra
wa'innan yaran ƴaƴa na ne dan haka ki fita daga cikin wannan maganar".

Ummi tace; "ni dama ba wani abu nace ba gani nayi ita waccen ba lafiya ta cika
ba.......", be bari ta ƙarasa ba ya katseta.

Cikin tsawa yace; "sai akayi me kuma? Nawa ake kaisu gidan miji basu da
lafiya?", Ummi ta girgiza kai sannan tace; "maganar gaskiya fa ba son auren nan
take yi ba kawai ina gani a fasa shi, don gaskiya bana so tayi irin wannan auren".

Baba ya ɗauke ta da mari hagu da dama, hakan ya janyo hankalin dangin ta da


dangin shi wanda suka zo daga Dabai, sun ɗauka shawara suke yi a tsakaninsu amma
zuwa yanzu sun fahimci cewa faɗa ne suke yi.

Inna Gaje( Ƴa ga me gari wacce take kamar ƙanwa a wajen Abdullahi), ta ƙaraso da
sauri tana faɗin; "ashsha meya kawo faɗa kuma yanzu".

Baba ya nuna Ummi yace; "wallahi kar ki ɓata mini rai idan ba haka ba zaki sha
mamaki na, kuma ki sani aure babu fashi matuƙar baki goyi bayan shi ba to zaki bar
garin nan ki koma Dabai kuma ba'a matsayin matata ba a matsayin bazawara dan
wallahi duk wanda ke adawa da wannan auren zan iya rabuwa dashi ko waye, kuma itama
munafikar ki fada mata matuƙar ba zata mini biyayya ba to ta tattara kayanta ta bar
mini gida kuma ta nemi wani uban dan babu ni babu ita".

Nusram ta fashe da kuka bayan sauraren bayanin Baban, Ummi ta share hawayenta
tace; "kiyi haƙuri kinji", Nusram ta ɗaga mata kai kawai domin bata da bakin magana
a lokacin.

Nusreen kuwa jikin ta yayi sanyi sosai ganin yadda mahaifiyar tasu take zubar da
hawaye, wannan wane kalar cin mutunci ne ace a bainar jama'a sai Mahaifin nasu ya
nuna basu da galihu.

Aunty ke aikin rarrashin Ummin, tana kuma ƙoƙarin kwantar mata da hankali. Ba
jimawa wayar Nusram ta ɗauki ƙara ganin Yaya Sulaiman yasa ta ɗauka.

"fito waje ina jiran ki", abinda ya faɗa kenan ya kashe wayar, Nusram ta miƙe
duk da jikin ta babu ƙwari, Nusreen ta miƙe da sauri tana so ta taimaka mata amma
Nusram ta dakatar da ita.

"kada ki damu Ya Sulaiman ke nema na a waje", abinda ta bata amsa dashi kenan
sannan ta saka hijab ta fita.
A tsakar gida ta sami Mama Jummai da Babbar ƴar ta Habiba sai ƙaramar wacce
bata yi aure ba Atika a tsaye suna magana amma suna ganin ta suka dena.

Nusram ta kauda kai domin ita Habiba dai ƙanwar tace amma bata wani birge ta dan
yarinyar akwai shige-shigen boka, kwanaki ma garin hakan ne wani ɗan damfara ya
damfare ta dubu ɗari uku.

Idan kaje ɗakin ta babu komai ko leda babu amma kuma ta san inda take fito da
kuɗin zuwa wajen boka, shi yasa sam basa shiri da Nusram kwata-kwata.

Atika kuwa ta cika girman kai da gani-gani hakan yasa Nusram ko kulata bata yi
dama dai waccen ƴar neman rigimar ce amma ita kam ko kallon inda take bata yi.

Dama cikin su masu sauƙin biyu ne Sahura da Ameera sune kuma wa'inda Nusram ke
kula su.

Su kuwa duka biyun shakkar Nusram ɗin suke yi hakan yasa basa shiga sha'anin ta,
ko kwanaki sai da Nusram ɗin ta kama Atikar ita da wani ɗan iskan yaro suna taɓe-
taɓen su, hakan ya tsorata Atikar amma taga koda ta dawo gida Nusram ɗin ko kallon
ta bata yi ba haka duk ƴan gidan babu wanda yayi mata magana hakan yasa take ƙara
shakkar ta( rashin kula ɗan iska da mara kunya ya kan ƙara maka kwarjini).

Habiba tabi bayan ta da harara tana me jan tsaki, Mama Jummai tace; "barta duk
ta gama iyayin ai na yau ne".

Habiba tayi dariya tace; "ina fa wani iyayi mutum ya kuma kamar tsinke", Atika
tace; "ina jin iskancin da take yi ne acan ta samu HIV", suka kwashe da dariya.

Habiba ta ciro ƙullin magani guda ɗaya da turare da kuma laya guda ɗai-ɗai, ta
ɗaga maganin tace; "wannan yace duk yadda za'ayi a tabbatar Baba yaci a cikin
abinci yau da daddare".

Ta miƙawa Atika turaren tace; "wannan kuma ke ce zaki shafa shi yanzu idan
Alhaji Baballe yazo kije ki gifta ta gaban shi abinda ake buƙata kawai yaji
ƙamshin, sai wannan layar ita kuma ki sami kusa da rijiya anjima bayan kowa yayi
barci ki haƙa ki saka ta a wajen shikenan aikin".

"yace da zarar Baba yaci abincin nan to zai ƙara tsanar ta ne sannan duk abinda
kika ce zai aikata, shi kuma Alhaji Baballe da zarar yaji ƙamshin wannan turaren to
duk abinda Baba yace mishi zai aikata, yadda layar nan take a binne haka bakin
shegiyar zai ɗaure ba zata iya ƙaryata komai ba haka kota ga Bangis ba zata mishi
ihu ba", suna gama jin bayanan Habibar suka shewa.

"wato na lura Habiba kin fini tsanar wa'innan yaran, shi yasa kika fi waccen
soloɓiyon".

"ai dole nayi kishi dasu kinga akwatin ɗazu da ina ganin saura kaɗan jini na ya
hau, barin ma na Nusram goma sha biyu fa kai dole ma su koma na Atika".

Mama Jummai ta kuma washe baki tana faɗin; "yauwa ƴar albarka haka nake son ji
daga bakin ki", Atika kuwa sai faman murna take yi jin duk wa'innan uba uban kayan
zasu koma nata.

A saman sabuwar motar shi ta same shi, shima dai Yaya Sulaiman ɗin saura kwana
ashirin da biyar nashi bikin shi, tayi sallama ya amsa mata yana binta da kallon
tausayawa.

"Nusram wai me yasa ba zaki rungumi ƙaddarar ki ba kiyi haƙuri ko Allah zai baki
lada, haba Nusram kamar ba musulma ba".

Hawaye ya zubo mata, cikin sheshsheƙar kuka tace; "Ya Sulaman nifa na haƙura
kuma na yarda da duk abinda ya same ni daga ubangiji ne sannan ina neman lada a
wajen shi, sai dai wasu abubuwan ne dole naji takaicin faruwar su".

Yace; "ya isa haka, be kamata ace har yanzu kina zubar da hawayen ki ba, ki zama
jaruma mana", ta jinjina kai tana goge hawayen fuskarta.

Yace; "yauwa ko kefa, yanzu amshi wannan ɗinkin ku ne wanda zaku saka gobe akwai
shadda a ciki kalar brown ita zaku sa da rana anko ne gaba ɗayan mu", ta amsa da to
tana mishi godiya.

Ya ɗan ja ta da fira har ta sake tana maida mishi da fara'ar ta, kan wani lokaci
ma har ta soma kwasar dariya, tabbas Sulaiman ya taka muhimmiyar rawa a rayuwar ta
Nusram.

Koda su Shureim suka zo Nusreen ta fito wajen su, tayi mamakin hangen ƴar uwar
tata tana fira da dariya, tunawa da cewa a gidan su Sulaiman ɗin ta taso kuma tare
suka taso yasa ta taɓe baki ta wuce.

Nusram kuwa da yake ƙofar gidan da jama'a hakan yasa bata ma lura dasu Shureim
ɗin ba, sun jima suna tsaye sannan motar Alhaji Baballe ta karyo kwanar layin.

Duk ƴan wajen sai da suka bi motar da kallo don ta haɗu sosai daka gani ka san
mamallakin ta ya ci ya sha ya tada kai.

Shi kuwa Alhaji Baballe hasko Nusram da yayi tana kwasar dariya ba ƙaramin ɓata
mishi rai hakan yayi ba, wato dalilin da ya saka tace mishi ta yafe zuwan da zai
dinga yi wajen ta kenan.

Cikin jin haushi ya fito daga motar, Nusram ta kalli Ya Sulaiman tace; "bari
naje wajen Alhaji na dawo", yana tsokanar ta tana dariya haka ta bar wajen.

"waye wancan ɗin", ya tambaya cikin fushi da kuma yatsinar fuska, Nusram ta
kuma kai kallon ta kan Ya Sulaiman daya ke danna wayar ta da alama wani abu yake
kallo ganin yadda ya ɓata fuska kuma ya natsu.

Ta juyo ta kalli Alhaji Baballe rai ɓace bata taɓa jin haushin titsiya ba sai yau
bata sani ba dan ko babu ɗigon son Alhajin a ranta bane oho, tace; "Yaya na ne".

Alhaji Baballe yace; "shine kuma sai ku fito titi kuna fira kamar wasu saurayi
da budurwa", tsabar haushi da takaici Nusram kasa cewa komai tayi.

Sallamar Atika yasa ta ɗago tana kallon ta, taci kwalliya cikin atamfa doguwar
riga da wani siririn mayafi saman kafaɗar ta, fuskar ta kuwa taci kwalliya sosai ga
wani uban turare da ta saka wanda saura kaɗan kan Nusram ya juya.

Cikin kissa ta tsugunna tace; "ina wuni Alhaji", ya amsa yana kallon fuskar ta,
ta saki murmushi ta maida kallon ta zuwa Nusram tace; "Aunty Nusram waccen ne ya
aiko ni".

Nusram tabi inda Atikar ta nuna da kallo wani gajere ta hango sai dai bata gane
ko waye ba kasancewar wajen babu haske dan haka bata ganin fuskar shi.

Atikar tayi murmushin mugun ta tace; "gashi yace in baki", ta ƙarasa tana miƙo
takardar hannun ta wacce take linke.

Nusram ta saka hannu ta amsa ta dube ta tace; "Atika waye wancan ɗin", cikin
salon munfinci tace; "Aunty wannan saurayin naki ne fa wanda kuke yawan fita tare
dashi wanda kwanaki Baba ya mishi gargadi akan ya dena zuwa ƙofar gidan nan saboda
ya kamaku tare a zaure kuna aikata abinda be kamata ba, bayan anyi haka kika gudu
wajen shi har kika kwana biyu har Baba yasa aka je aka kama shi da ƴan sanda to ya
ce mini ɗazu aka sako shi shine ya sami labarin za'ayi auren ki, shine yazo".

Kan Nusram ta gama fahimtar me Atika take nufi Atikar tayi gaba da sauri, Alhaji
Baballe kuwa jin abinda Atika ta faɗa yasa yayi saurin fizge takardar daga hannun
Nusram ɗin.

Cikin fushi ya ɗago bayan ya karanta wasiƙar yace; "lallai kin cika ƴar iska
amma duk da haka bari kiji abinda zan faɗa miki auren ki dai ba zan fasa ba kuma ki
kuka da kanki idan kika shigo hannu na, kada ma kiyi ƙoƙarin cewa kin fasa domin
kuwa kuɗin da mahaifin ki ya ci mini ba zai taɓa iya biya ba har ƙashen rayuwar shi
dan haka auren mu babu fashi". Yana faɗar haka ya ciro bandir ɗin ɗari biyar-biyar
guda uku ya cilla mata yace; "gashi nan kuɗin da zaki yi amfani dashi ne gobe tunda
kince bakya buƙatar komai na biki", yana gama faɗar haka ya wuce ya barta.

Har ya shiga motar shi ya rufe ƙofa sai kuma ya buɗe ya cillo mata takardar
sannan ya maida ƙofar ya rufe ya figi motar tashi ya bar wajen.

Nusram ta saki kuka tana tsugunnawa a wajen, ga mutane duk a wajen har sun fara
cece kuce, Ya Sulaiman yazo ya ɗagota sannan ya tsugunna ya kwaso mata kuɗin da
takardar.

"Nusram kiyi haƙuri, kada wa'innan abubuwan dake faruwa su dame ki, ki sani
bayan wuya sai daɗi kuma a dukkan tsanani akwai sauƙi na faɗa miki wata rana sai
komai ya wuce kamar ba'a yi ba", Nusram ta gyaɗa kai kawai.

Kuɗin ya zuba a aljihu sannan yace; "zan je na ajiye wa'innan kuɗin ba zaki taɓa
ko biyar ba, duk abinda kike buƙata kiyi mini magana zan kawo miki amma bana so
kiyi amfani da komai na Alhaji Baballe".

Takardar ya linke bayan ya gama karantawa sannan yace; "zan ajiye takardar itama
kada kuma ki faɗawa su Ummi wannan abin kinji", ta ɗaga kai.

Hannu ta kai tace; "dan Allah ka bani na karanta", ya miƙa mata takardar:-

*Assalamu Alaykum, zuwa ga masoyiyata Nusram, ki sani na fito ɗazu daga cell
kuma naji yadda tsohon ki yake son rabani dake, dan haka na yanke shawarar gobe zan
zo mu gudu da daddare dan haka ki shirya komai naki zan zo sai mu gudu kawai.*

*daga Bangis(ur love)*

Nusram ta miƙawa Yaya Sulaiman takardar kawai domin kuwa ta san ba zata fahimci
komai a ciki ba dan bata san inda maganar ta dosa ba.

Shureim kuwa ganin abinda ya faru yasa suka sallami Nusreen da sauri ganin yadda
hankalin ta ya koma kan ƴar uwarta.

"Ram meya faru ne tsakanin ki da wancan ƙaton?", Nusreen ta tambaya bayan ta


ƙaraso kusa dasu.

Yaya Sulaiman ya galla mata harara sannan yace; "wuce ki bar nan wajen", ta wuce
tana ƙunƙunai har ta shige gida.

Yaya Sulaiman ganin ta tafi ya ƙara jawa Nusram kunne akan kada ta sake ta
faɗaws ƴan gidan abinda ya faru sannan yace taje ta kwanta domin dare ya fara ja.
Tana shiga zaure taji an fincikota, kanta ya bugu da jikin bango ta saki ihun
wahala, sai dai be fita ba domin an toshe mata baki.

Ɗakin Isa dake zaure nan aka hankaɗa ta, ta faɗi ƙasa cikin kiɗima ta juyo tana
bin inuwar mutumin da kallo, ɗakin babu haske sosai dan haka bata ganin ko fuskar
waye.

Cike da tsoro tace; "waye dan Allah", ba'ayi magana ba sai dai janta da aka yi
zuwa ciki kan katifar ɗakin aka cillata sannan mutumin yayo kanta yanzu kam ta gane
meke shirin faruwa da ita dan haka suka shiga dambe.

Sun jima a haka yana ƙoƙarin kaita ƙasa amma abu ya faskara, shi kanshi Isan
yayi mamakin ƙarfin ta be taɓa tunanin haka take da ƙarfi ba, ƙara ƙaimi yayi inda
Allah ya bashi sa'ar cire hijab ɗin dake jikin ta, ya kuma yaga rigar jikin ta.

Ya ɗaga ta ya buga a katifar sannan ya saka ƙafa ya danne ta, haiƙam yake son
rabata da kayan jikin ta, Nusram kuwa zuwa yanzu ƙarfin ta yayi ƙasa gashi dama ba
wata lafiya ta cika ba wanda dole ta saduda.

Shi kuwa ganin ya sami dama a kanta yasa ya saki jiki sosai yana ƙoƙarin aikata
mata abinda zuciyar shi ke raya mishi.

Hannu Nusram ta miƙa Allah ya taimake ta taji ta riƙo wani abu wanda ba zata
bambamce kwalbace, ƙarfe ne ko kuma roba bace duk da haka tana fatan ya kasance
abinda zai taimake ta ne.

Ragowar ƙarfinta ta tattaro ta hankaɗe shi, ganin hakan ga ƙoshi ga kwanan yunwa
ya ƙara harzuƙa Isa dan haka ya ɗauke ta da mari wanda sai da ta kifa, wannan abin
ta ɗaga ta kwaɗa mishi a kai iya ƙarfin ta.

Ya saki wata irin ƙara me ƙarfi wacce ta ratsa duka gidan, Nusram kuwa jin hakan
yasa tayi saurin dirowa tayi hanyar waje.

Sai dai kanta kai ga fita yasa ƙafa ya taɗiyo ta, ta faɗi a wajen hakan kuma
yayi dai-dai da ƙarasowar mutane.

Ɗaki ya gauraye da haske, nan fa Mama Jummai ta saki ihu tayi kan Isa tana riƙo
shi tana tambayar shi abinda ya faru.

Babu abinda yake faɗi sai " Nusram zata kashe ni", jin abinda ya faɗa yasa Mama
Jummai saka salati.

Tayi kukan kura ta faɗa kan Nusram wacce ke kwance tana sake ƙudundune jikin ta
da hijab ɗin ta wanda ta ɗauka bata kai ga sakawa ba.

Aunty taje ta bangaje Mama Jummai sannan ta ɗago Nusram tace; "haba Jummai a sai
ki tsaya kiji meya faru".

"wane kalar meya faru? Kina ganin Kaltume zata kashe mini ɗa", Aunty ta taɓe
baki tace; "to sai ki bibiyi meya faru tukunna", Mama Jummai zata kuma magana Baba
yace; "duka a tafi ɗakin Jummai domin ayi maganar".

"dakata Jummai ba ita bace babba dan haka ɗakin Maimuna za'a je", cewar Baba
Sailuba yar Malam Abdullahi.

Haka aka ɗunguma zuwa ɗakin Ummi, aikuwa ɗaki ya cika maƙil dan harda ƴan Dabai
wa'inda suka zo biki.

"meya haɗa ka da ƴar uwar ka?", Baba ya tambaya, Baba Sailuba tayi saurin cewa;
"a ina ta zama ƴar uwar tashi? Ban sani ba Abdullahi ko kai kayi mata cikin shi a
waje?".

Cikin sauri Baba yace; "a'a Yaya wallahi da ɗanta na ganta", Baba Sailuba tace;
"yauwa yanzu naji batu ka tambaye shi meye haɗin shi da ƴar sunnah bayan shi shege
ne bashi da uba", Mama Jummai ta wulla mata harara.

Isa ya saukar da kai yace; "dama ina kwance ne kawai sai na ga mutum a tsaye a
kaina kan nayi wani motsi ta faɗo jiki na tana faɗin wai sai na biya mata buƙata".

Nusram ta girgiza kai hawaye yana zubo mata jin irin sharrin da Isa yake mata,
Baba yace; "ni kam na shiga uku yanzu iskancin naki gida ya dawo kenan?, wallahi
idan kika cigaba da ɗauko mini magana zan tsine miki kibi duniya".

Nusram hankali tashe ta rarrafo zuwa gaban Mahaifin nata cikin kuka tace; "dan
Allah Baba kayi haƙuri wallahi ba haka bane nazo shigowa gida ne shine ya jani
ɗakin shi don yayi mini fyaɗe har ya yaga mini riga amma wallahi bani naje ɗakin
ba".

Mama Jummai tayi salati tana tafa hannu tace; "yanzu Nusram waye zai miki ƙarya
Isa ko waye", Baba yace; "bar shegiya me baƙin hali".

Baba Sailuba tace; "shegantata zaka yi Abdullahi yanzu ɗan shege yafi ɗan sunna a
wajenka, lallai ba banza aka barka ba".

Baba yace; "Yaya ki duba wannan lamarin fa", ta ɗaga mishi hannu tace; "ya isa
haka Abdullahi maganar yarinyar nan abin dubawa ne be kamata ka goyi bayan ɗaya
daga cikin su ba zaka yi dana sani fa".

Nan dai Baba ya tafi yana bambamin shi, Baba Sailuba ta ɗago Nusram tace;
"kinji kiyi ta addu'a Allah yana sane da ke", Nusreen ta amshi Nusram ɗin suka
shige ɗaki suna kuka.

Ummi kuwa banda hawaye babu abinda takw gogewa Aunty na ƙara kwantar mata da
hankali, to dai magana ta shiga unguwa domin kuwa jama'a duka sun ji, wasu sun
yarda da abinda Nusram ta faɗa wasu kuma sun ƙarya ta jin abinda ya faru tsakanin
ta da Alhaji Baballe ɗazu.

Ranar dai kam gidan ba kowa yayi barci ba wasu hidimar biki wasu kuma ɓacin rai
ya hanasu barci ciki kuwa harda Nusram wacce tasha kuka ta godewa Allah.

Washe gari da safe kuwa da ƙyar take buɗe idanun ta saboda kumbura da yayi,
Nusreen ma dai idanun ta yayi ja sosai dan itama kwana tayi tana kuka don taya ƴar
uwar ta jimami.

Koda Aunty tazo ta same su a kwance nan ta rufe su da faɗa, haka dole Nusreen ta
tashi tayi wanka ta shirya don an kusa ɗaurin aure.

Nusram kuwa magani tasha sannan ta koma ta kwanta, ta ɗaga hannu ta kalli
lallen dake zane a hannun ta wanda da ƙyar ta bari akayi mata shi sai da Ummi tayi
mata kuka sannan ta bari aka yi shi.

A yanzu kam babu abinda ta tsana kalar auren nan nata, ta ɗaga kai ta kalli
yadda jama'a ke hada-hada.

Nusreen ake sheƙawa kwalliya me kyau da kuma ɗaukar hankali, Aunty ta shigo
ganin Nusram ɗin a kwance yasa tace; "au yanzu baki tashi ba kenan? haba Nusram
tashi dan Allah mana", ta ƙarasa tana kamo Nusram ɗin don ta miƙe.
A haka jikin ta babu wani ƙarfi ta miƙe ta ɗauke sosa da sabulu tayi bayi, ta
tarar Aunty ta haɗa mata ruwa me kyau da ƙamshi nan tayi wankan sannan ta fito.

A wajen famfo suka haɗu da Atika wani lace ne me tsada ta saka a jikin ta, sosai
taci kwalliya zaka iya tunanin ma itace amaryar.

Nusram ta kauda kai gefe batare da tace mata komai ba, Atika kuwa ta saki
murmushi na izgilanci tana sakin shewa.

Tana shiga Aunty ta jata zuwa uwar ɗaka nan suka tarar da Safeena tana zaman
jiran su dan haka tana shigowa ta fara aikin ta wato kwalliya.

Sadiya ta buɗe ledar kayan da Yaya Sulaiman ɗin ya bata jiya ta ɗauko mata
shaddar, doguwar riga ce wacce taji stone work har zuwa ƙasa tayi kyau sosai.

Babu yadda Safeena bata yi da ita akan ta tsaya ta ɗaura mata ɗan kwalin ba amma
taƙi, dan haka gyale fari ta yane kanta dashi zuwa kafaɗar ta kawai.

Tana zaune tana kallon Nusreen yadda take ta sakin murmushi cikin farin ciki da
annashuwa.

Nusram ta miƙe tsaye sannan ta ɗauki ɗan ƙaramin memo wanda ke ajiye saman
cabinet ɗin su, ta zame ta fice.

Jan gyalen tayi ta rufe rabin fuskar ta hakan yasa har ta gifta Ummi da Aunty
wainda ke tsaye suma sanye da shaddar duka kala ɗaya da tasu basu lura da ita ba.

Koda ta fito ƙofar gida babu kowa domin kuwa duk suna masallacin dake gaban
gidan kaɗan inda anan ne za'a ɗaura auren.

Haka kawai zuciyar ta ke zafi dan haka ta yanke shawarar fitowa ta dan miƙe
ƙafa domin ta ɗan sha iska.

A hankali take tafiya hawaye na zubowa daga idanun ta, yanzu shikenan ta san
cewa ba zata taɓa farin ciki a rayuwar ta ba kamar mahaifiyar ta ƙila gwara Ummi ma
domin ƙila tana amarya ta ɗan ji daɗi.

Abdus-samad dake sanye da shadda kalar ruwan toka yayi kyau sosai duk da be cika
wannan shigar ba, tare suka zo da Fadil domin halartar ɗaurin auren saboda Shureim.

Jin hayaniya tayi yawa yasa ya fito daga masallacin domin ya sha iska, yana
tsaye yana danna waya ta bullo hanyar.

Jin ƙamshi me daɗi da sanyi yasa Abdus-samad ɗagowa ya kalle ta, ganin wannan
yarinyar ce yasa gaban shi faduwa, ya tsura mata idanu.

Tayi baƙi ta rame yabi ta da kallo tun daga sama har ƙasa tayi kyau sosai sai
dai kuka take kuma hankalin ta baya kan inda take tafiya.

Ba lallai ka lura da kukan da take yi ba idan ba ka lura sosai ba, tana zuwa daf
dashi ta ɗan bigi hannun shi wayar ta faɗi.

Sai lokacin hankalin ta ya dawo jikin ta, cikin sauri ta tsugunna domin ɗauƙo
wayar, a tare suka miƙa hannu domin ɗauƙo wayar. Da sauri ya janye hannun shi ta
ɗauka, tana ƙoƙarin miƙewa gyalen kanta ya zame gashin ta ya bayyana wanda yake
dogo ga baƙi ga santsi wanda kuma ya sha gyara da mayuka me kyau da ƙamshi.

Saura kaɗan Abdus-samad ya suma a wajen domin Allah yayi shi da son mace me
gashi, baya manta lokacin yana yaro haka zai zaunar da First Love ɗin shi ya saka
mata rigima akan zai mata tsifa yayi ta wasa da gashin.

Kan ya ankara har Nusram ta miƙe tana ƙoƙarin gyara gashin nata, Abdus-samad ya
kai hannu ya ɗauko ribbom ɗin ta ya miƙe domin miƙa mata wanda itama Nusram din sai
lokacin ta lura da ko waye.

Zaro idanu tayi jikin ta ya ɗauki rawa, da sauri ta fara ja da baya kafin ta
juya da sauri, Abdus-samad yayi saurin binta domin amsar wayar shi ya kuma bata
ribbom ɗin ta amma ina ko ƙeyar ta be gani ba.

Cikin sauri yake bin lungunan domin neman ta sai can ƙarshen lungun ya hango ta,
tana tafe tana waige-waige kan ya ƙaraso ta fice daga lungun.

Tana isowa ƙofar gida ta samu jama'a cike alamu dai an gama daurin aure, Sahura
ta tare ta tace; " Yaya Nusram ina kika shiga", da sauri Nusram ta juya ganin
Abdus-samad ya kusa ƙarasowa inda take yasa taja hannun Sahurar suka shige cikin
gidan.

Abdus-samad ganin ta shige gidan yasa yayi murmushi yana faɗin; "Nusram! Nice
name".

Fadil ya ƙaraso wajen shi da sauri Abdus-samad ya saka ribbom ɗin cikin aljihun
shi gudun kada Fadil ya gani.

"ina ka shiga ne ga Shureim.can da abokanan shi suna neman ka", Fadil ya faɗa,
Abdul yace; "muje wajen nasu yanzu me zasu yi?".

"zasu shiga a gaisa da ƴan uwan amarya ne", Abdul yace; "ok to.muje wajen nasu",
haka suka ɗunguma zuwa cikin gidan su Nusram ɗin.

Sun gaisa da jama'a an kuma ɗauki hotuna inda suka yi al'adar kaduna wato kiɗan
ƙwarya nan abokanan ango suka cashe da kakanin amarya akayi wasa da dariya kafin
suka bawa kakar su Nusreen ɗin kuɗin cin goro sannan suka fito ana ta sam barka.

Abdus-samad dai duk yadda ya baza idanu Allah be bashi sa'ar hango Nusram ɗin ba
haka ya haƙura suka tafi.

Nusram kuwa suna shiga gidan ta saki hannun Sahurar sannan tayi nasu ɗakin, anan
ta tarar dasu Ummi ana ta guɗa ana faɗin; "an ɗaura".

Zuciyar Nusram kamar ta faɗo ƙasa tsabar takaici, tana shiga wata cikin abokan
wasan su tazo ta turare ta hau fesa mata, Nusram ɗin ta saki kuka sannan tayi cikin
ɗaki.

Tana shiga taji ana sanar da shigowar su Shureim ɗin dan haka ta koma gefen
katifa ta zauna tana me sauke ajiyar zuciya tana kallon su Nusreen suna leƙe ta
window amma ta ita ta kasa leƙawa har suka fita.

Babu jimawa aka sanar da shigowar Alhaji Baballen tare da nashi tawagar, nan
suma aka yi wasa da dariya inda ya bawa kakannin Nusram ɗin maƙudan kuɗi na cin
goro nan fa waje ya ɗauki shewa da guɗa.

Anan wasu suka ƙara jinjina kuɗin na Alhaji Baballe inda Baba keta washe baki
shi a dole ga sirikin me kuɗi.

Abdul dake ƙoƙarin shiga mota yaji an riƙo mishi hannu, da sauri ya kalli wanda
ya riƙo shin.

Cikin tsananin mamaki yake kallon shi ya kalli inda Fadil yake yaga hankalin shi
yana kan abokan ango.

Cikin mamaki ya nuna shi, da sauri yaja hannun shi ya bar wajen dashi, sai da
suka isa inda babu mutane sannan ya sake shi, Abdus-samad yace; "waye kai".

Alhaji Mustapha yayi murmushi yace; "Ka tambayi Brr Farida kace waye Mustapha
Tuge a wajen ka?, ka sani koda baka tare dani ni ina tare da kai idan kaje ka
tambaye ta", daga haka ya bar wajen.

Abdus-samad ya daɗe be motsa daga wajen ba, ya ja ajiyar zuciya sannan ya koma
inda motar shi take har lokacin Fadil yana tare da Angon dan haka ya danna mishi
horn cikin sauri ya taho dan ya san kaɗan ga aikin shi ya tafi ya barshi.

Koda yazo sai da yaja tsaki sannan yaja motar suka tafi.

Bayan sallar isha'i aka fara cewa amare su fito nan fa idanun amaren ya fara
raina fata, Nusram da Nusreen suka rungume juna suna kuka me tsanani.

Sai da suka saka mutane da yawa a wajen kuka, kafin a samu a raba su, an kaisu
wajen Ummi inda suka yi musu nasiha sosai da sosai suna zubar da hawaye suka rabu
Ummi tana saka musu albarka da yi musu addu'ar tafiya a sa'a.

An kaisu wajen Mama Jummai wanda babu abinda ta dinga faɗa banda habaici, Baba
ma dai cewa yayi idan sun zauna kansu idan basu zauna ba to sai dai su nemi wani
uban ba dai shi ba.

Nan aka saka kowacce a mota domin tafiya dasu zuwa gidajen su, nan fa mutane
suka rabu gida biyu wasu suka tafi raka Nusreen wasu kuma Nusram.

Aunty tace; "Nusram ki shiga da ƙafar dama", haka ta shiga da kafar dama tana me
addu'a, duk da gabanta dake faɗuwa.

Gida fa ya haɗu sosai da sosai dan faɗan kyawun shi ɓata lokaci ne, kowa sai
yaba kyawun gidan yake yi.

Amma Nusram ita kyawun gida bashi ya dame ta ba, sai ma zazzaɓi daya rufe ta,
babu jimawa ƴan kawo amarya suka gama abinda zasu yi sannan suka tafi, suka bar
amarya daga ita sai halin ta.

#LIKE
#SHARE
#COMMENTS

*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

*yau kam kamar na zubar da hawaye saboda comments ɗin ku naji daɗi sosai Allah ya
bar ƙauna.

*godiya gare ku ABDUS-SAMAD FANS CLUB, naji dadin comments ɗin ku, ku sani ina
son ku sosai akan san ku zan iya shanye maltina gwangwani biyu😁*.

*Innalillahi wa'inna ilaihirraji'uun, haƙiƙa wannan jarabta ce da Allah ya


saukar miki Zulaihat Ubangiji Allah yasa ayi aikin cikin nasara ya bata lafiya yasa
ya zama kaffara, ya kuma ƙara muku juriya ya bata lada domin lallai cuta bata da
daɗi*.

*ƴan uwa muna barar addu'ar ku za'a yiwa yarinyar ƴar uwarku a musulunci
Zulaihat Isma'il aiki yanzu haka suna Asibiti a India dan tana fama da heart
attack, dan haka muke roƙon ku taya mu da addu'a Allah yasa ayi a sa'a ameen*.

📖📖35-36📖📖

*HAYIN RIGASA, KADUNA*.

Abdul ya shiga get ɗin Estate ɗin sannan ya sami waje yayi parking motar, cikin
sauri Fadil ya kalle shi yace; "me hakan ke nufi?" bece komai ba sai ma kifa
kanshi da yayi akan steering motar.

Sanin cewa ba zai tanka mishi bane yasa Fadil buɗe motar ya fice, be jima sosai
da fita ba Saleema ta ƙaraso wajen motar ta buɗe ta shiga.

A hankali ta dafa shi sannan tace; "kayi haƙuri, komai yayi zafi maganin shi
Allah ka kaiwa Allah kukan ka shi zai share maka hawaye".

Ya ɗago yana kallon ta, tayi murmushi sannan tace; "damuwa da tashin hankali
bata yiwa wannan kyakkyawar fuskar kyau, a koda yaushe murmushi da dariya sune suke
ƙara ƙawata wannan fuskar me girma da kwarjini, shin ko kasan murmushin ka yana
sanyaya zuciya nawa ne a gidan nan?, suna da yawa ciki kuwa harda tawa fatan za'a
duba tamu zuciyar a dena shiga damuwa".

Wani sanyi yaji yana ratsa zuciyar tashi, haƙiƙa iya magana ma wani abu ne
lallai kam a cikin mata Saleema ta ciri tuta.

Ya saki murmushi sannan yace; "kai Aunty na ke ɗin ta dabance", itama tayi
murmushi kan ta riƙo hannun shi tace; "kai ɗin wani ɓangare ne na rayuwata na sani
cewa zuciya ta tana girmama abinda duk ya shafe ka".

Kan wani lokaci me tsayi sai ga Abdus-samad harda dariya, sai da Saleema ta
tabbatar da bata bar Abdul cikin damuwa ko kaɗan ba sannan ta buɗe motar ta fice.

A hankali ya ja motar ya fice daga gidan, Husna taja tsaki tace; "katuwar banza
ta ɓige a wajen ɗan cikin ta", sannan ta juya cikin gida cike da kishi.

Dr Saleema kuwa da batama san Husna nayi ba ganin ya bar gidan yasa ta koma
cikin gidan su tana me jin daɗin yadda ta sami nasarar kawar wa da masoyin nata
damuwar da yake ciki.

Koda ya isa gida duka ƴan uwan nashi suna falo, Fadila da Sumayya suka hau
rige-rigen yi mishi sannu da zuwa, ya amsa musu duka yana ɗaga Adnan sama yana
cillashi yayin da shi kuma Adnan ɗin ke yin dariya.

Dr Abubakar da Brr Farida da suke saukowa daga sama suna fira da dariya, Dr
Abubakar yace; "kai lallai ma maza sauke mini autana kada ka faɗar dashi".

Brr Farida tayi dariya tace; "aikuwa dai Baby ba zai taɓa faɗar da Autan ka ba,
sai dai ya ƙara kula dashi", Abdul yayi dariya har gefen kumatun shi ya lotsa yace;
"dat's mah first love".

Dr Abubakar yace; "lallai ma wato shigar mishi kika yi kenan?", tace; "a'a fa
ni ban shigar mishi ba", nan suka cigaba da firar su gwanin ban sha'awa.

A hankali Abdul ya zame ya shige nashi ɗakin, wayar Sumayya ya kira akan yana
neman ta, babu jimawa ta ƙaraso hannun ta ɗauke da ƙaramin bowl me ɗauke da Fruit
salad.

"Ya Abdus-samad gani", ta faɗa tana gyara tsayuwar ta dan ta fara gajiya, ya
ƙara gyara ƙafar shi dake saman ƙaramin table din dake tsakiyar ɗakin.

Yana cigaba da danna laptop ɗin dake saman cinyar shi yana yi yana cin fruit
salad ɗin, kamar ba zai amsa ba dan har ta cire rai da amsawar tashi sai kuma taji
yace; "ranar nan firar me kuke yi ke da Yaya Tameer?".

Sumayya ta zaro idanu tace; "wallahi Yaya yace.....yac......yace kada na


faɗ........kada na faɗ", kallon da yayi mata yasa tayi saurin haɗiye wani yawu.

"ki bani amsata kawai", ya faɗa yana cigaba da abinda yake yi, tace; "dama cewa
yayi na shawo kan Mummy akan......akan.....aka......akan yarinyar da yake so ya
au.....aura", ta ƙarasa tana jan numfashi.
Abdus-samad ya ɗago ya mata wani kallo sannan yace; "ke zaki mata maganar aure
ko wato kin girma ko? Kema auren kike so kenan?", da sauri ta girgiza kai, cikin
daka tsawa yace; "fita ki bani waje shashasha", har tana harɗewa wajen fita.

Sai da ta ganta a waje sannan tayi ajiyar zuciya kafin ta bawa bujen ta iska,
Fadila dake kallo a falo ganin yadda Sumayyar ta shigo yasa itama ta ruɗe.

Nan ta hau tambayar ta abinda ya faru ba tare da ta bata amsa ba ta wuce ɗakin
su, Surayya tayi murmushi tana girgiza kai.

"kada ki damu da wannan mashirmanciyar wata ƙila laifi ta yiwa Ya Abdul shi
yasa ya tsoratata haka", Fadila banda ɗaga kai babu abinda take yi.

Koda aka yi kiran sallar la'asar ta ƙofar baya ya fice inda yaje yayi sallar shi
sannan ya shigo ta ƙofar gaba.

Tun daga nesa ya hango su a tsaye da alama akwai abinda suke tattaunawa, ya
ƙaraso wajen su da sallama, ya miƙawa Sameer hannu suka yi musabaha sannan ya kalli
Fadila yace; "kinyi sallah ne?".

Ta girgiza kai da sauri, ya mata wani kallo babu shiri har tana harɗewa wajen
barin wajen, Sameer na ƙwala mata kira amma ko juyowa bata yi ba, dan bata manta
yadda Sumayya ta shigo ba ɗazu.

Sameer ya ɓalla mishi harara yace; "ka kore ta ko?", Abdul ya shafa gashin
kanshi kan ya kalli Sameer ya taɓe fuska yace; "dan Allah yanzu me kuma nace ni",
Sameer yayi dariya yana dukan kafaɗar Abdul ɗin.

Tameer daya shigo ya kalle su yace; "me kuke yi kuma anan?", Abdul yace; "firar
auren ka muke yi Yaya", Tameer ya harare shi yace; "ina wasa da kai kenan?", Abdul
ya shagwaɓe fuska.

Tameer yace; "maganar gaskiya na kasa tarar Mumny da maganar, wallahi", Abdul
yace; "shikenan sai ka zauna a matsayin gauron ka", Tameer ya riƙo shi yace; "dan
Allah mana, ka faɗa mata", yace; "me zance".

Tameer ya sosa kai yace; "ka gane yarinyar da nake so ne na tabbatar Mummy ba
zata amince ba, ƴar wani ma'aikaci ne a company ɗin mu, kuma kasan halin Mummy tafi
son ƴar me kuɗi".

Abdul ya ɗaga kafaɗa yace; "taɓ ai ra'ayi ne me sunan shi da sunan ta?", Tameer
ya kuma washe baki yace; "Sunan ta Bilkisu ƴar Malam Sunusi Ladan", Abdul yace;
"shikenan zan gwada sa'a ta".

Tameer yace; "nama san zata amince dan inda kaine magana ta ƙare", Abdul yace;
"to idan ta amince meye tukuici na?", Tameer yace; "baƙar motar ka", Abdul ya shafa
kai yana murmushi.

Sameer kuwa dariya yayi ganin yadda ɗan uwan nashi ya sallama haka da wuri,
Abdul na barin wajen Sameer ya janyo Tameer yace; "anya kuwa soyayyar da kake
nunawa Abdus-samad yanzu ta gaske ce?".

Tameer yace; "har cikin raina da gaske nake a da ɗin ma ina tunanin shine
matsalar rayuwata ne sai da naga na kusa rasa shi sannan na tabbatar da ina son shi
sai dai maganar gaskiya har yanzu ina kishin shi", Sameer yayi murmushi.

"bari naje nayi sallah", daga nan Sameer ɗin ya fice shi kuma Tameer ɗin ya
shige cikin gida domin kuwa shi yayi sallar shi dama.
Fadila tana zuwa ta tarar da Sumayya ta idar da sallah, cikin sauri ta shige
bayi ta hau alwala, Sumayya ta kwashe da dariya domin ta san kome ya faru.

Ta san cewa Abdus-samad babu abinda ya tsana irin mutum me wasa da Sallah duk
shirin da kuke yi idan har kana wasa da Sallah to lallai zai ci ƙaniyar ka ne.

Fadila ta fito daga bayi, ganin Sumayya na dariya yasa ta kwaɗa mata harara
sannan ta tada kabbarar sallah sai da ta idar sannan ta bata labarin abinda ya
faru.

Nan itama Sumayya ta bata nata labarin, lokacin Surayya ta shigo haka suka haɗu
suka dinga yiwa juna dariya.

Surayya tace; "haba Aunty Fadila ina shekarun ku kusan ɗaya me yasa kike tsoron
shi", Fadila ta galla mata harara sannan tace; "ke baki san wannan bane wani
lokacin fuskar yara gare shi wani lokacin kuma babu wasa wallahi ban san lokacin
dana bar wajen ba", suka kuma kwashewa da dariya.

A falo ya same su zaune Bayan Sallar isha'i, ya kalle su yace; "kun yi sallah
ko?", duka suka amsa da eh, yace; "First love fa?", Surayya tace; "tana sama", be
kuma magana ba ya nufi saman.

Da sallama ya shiga ɗakin, Dr Abubakar na zaune saman carpet inda Brr Farida ke
gefen shi tana mishi fira, Abdus-samad yayi murmushi soyayyar dake tsakanin iyayen
shi abin yana bashi mamaki kuma yana birge shi.

Brr Farida ta tashi ta riƙo hannun shi har suka zo suka zauna, Dr Abubakar
cikin zolaya yace; "gaskiya na kusa fara kishi da kai, waye ma ya kawo ka a wannan
lokacin da nake buƙatar kulawar mata ta".

Abdus-samad yasa hannu biyu ya rufe fuskar shi, a dole nan yaji kunya, Brr
Farida ta kwantar da Abdus-samad saman ƙafar ta sannan ta harari Dr Abubakar ɗin
cikin wasa tace; "ai shi koda yaushe nake kulawa dashi kaine ma kake da ƙaiyadajjen
lokaci".

Dr Abubakar ya ciza yatsa yace; "wayyo Allah na zasu haɗe mini kai", su kam
banda dariya babu abinda suke yi.

Abdus-samad ya gyara zaman shi sannan yace; "Daddy dama magana nazo muyi", Dr
Abubakar yace; "akan me fa?".

"dama magana ce akan Yaya Sameer da Yaya Tameer sune suka samu wa'inda zasu aura
shine suka ce a sanar maka".

Ya ɗan saci kallon Brr Farida idanu kawai ta zuba mishi ya kauda kai ya maida
kan Dr Abubakar sannan yace;

"To shine nace bari a sanar da kai", Dr Abubakar yayi murmushi sannan yace; "ka
kira mini su yanzu", Abdus-samad ya ɗauki wayar shi ya kira su duka wanda babu ɓata
lokaci suka zo.

Dr Abubakar ya kalle su yace; "naji saƙon ku a wajen Abdus-samad kuma insha


Allahu zan bibiya na kuma yi bincike akan gidajen nasu yanzu sai ku mini bayanin su
waye?".

Sameer ya shafa kai sannan yace; "ni dai yarinyar da nake so ita ce Fadila", Dr
Abubakar yace; "wace Fadilar?", Sameer yace; "Fadilar nan gidan".
Brr Farida ta zaro idanu cikin sauri tace; "ba zai taɓa yiwuwa ba da raina ba
zaka janyo mini abin ɓacin rai ba wallahi tun wuri ka canza ba zan taɓa amincewa
ba".

"me yasa kike hakane Farida?", da sauri Brr Farida ta miƙe tace; "dangin ka Dr
dangin ka fa ba zai taɓa yiwuwa ba kaima ka sani ba zan taɓa amimcewa ba".

Dr Abubakar yace; "Farida ki tsaya ki duba wannan lamarin mana", ba dan ranta
yaso ba ta koma ta zauna ta wurgawa Sameer harara.

Dr Abubakar yace; "naji naka saura kai kuma", Tameer yace; "Bilkisu ce ƴar gidan
Sunusi Ladan".

Brr Farida ta miƙe cikin sauri tace; "wane Sunusin ba dai wannan talakan ba?",
Tameer ya ɗaga kai cike da tsoron kada taƙi amincewa.

Ta girgiza kai sannan tace; "ni Farida Alƙali zaka ɗaukowa ƴar talaka wanda beda
cin yau balle na gobe, ni talaka wallahi ba zai yiwu ba".

Duka suka bita da kallo cike da mamakin abinda take faɗa, duk tabi ta birkice
lokaci kaɗan.

Dr Abubakar yace; "ku tashi ku tafi Allah yayi muku albarka", suka amsa da ameen
jikin su duk a sanyaye.

Dr Abubakar ya kalli Abdus-samad yace; "kaima jeka mana", Abdus-samad cike da


damuwa ya fice daga ɗakin.

Bayan fitar shi sannan Dr Abubakar ya miƙe ya riƙo hannun ta, kusa dashi ya
zaunar da ita sannan ya cika kofi da ruwa ya miƙo mata, ta amsa ta shaye tass.

Ya matse hannun ta sannan yace; " haba My Brr ki dena irin wannan shifa komai a
rayuwa yana zuwa ne dai-dai yadda ka ɗauka, ki daure ki rage ƙiyayyar da kike yiwa
ƴan uwa na da kuma talaka".

Brr Farida ta zame hannun ta sannan tace; "Dr har kana tunanin zan manta
ƙiyayyar da ƴan uwan ka suka nuna mini?, ko kuwa na manta abinda talaka yayi mini
ya rabani da abar ƙauna ta ƙawata aminiya ta wacce nake matuƙar ƙaunar ta".

Dr Abubakar yace; "Assha! Be kamata ace kin riƙe abinda ya faru a baya ba a cikin
ranki, ki sani su ɗin yan uwa na ne kuma ba zan taɓa canza su ba shin ke ba zaki
ɗauke su a matsayin ƴan uwa ba, haba Farida ki dinga haƙuri mana babu fa abinda
yake tabbata a rayuwa komai da kika gani wucewa yake yi kada ki riƙe abinda ya faru
cikin ranki, sannan maganar talaka ina so ki fahimci wani abu a ciki talaka akwai
mutumin kirki akwai wanda yake akasin haka, haka acikin masu kuɗi akwai mutumin
kirki akwai akasin haka, sannan baki san me Allah ya shirya musu ba a rayuwa, ki
saka musu Albarka a matsayin ki na mahaifiyar su sai suga haske a rayuwar auren
nasu amma fushin da zaki yi dasu shine zai bawa maƙiyin su da kuma wanda yake
ƙoƙaerin cutar dasu dama wajen aiwatar da nufin su".

Lallai magan-ganun na Dr Abubakar ya shige ta, cikin sanyin jiki tace; "shikenan
Allah ya zaɓa abinda yafi alkhairi", Dr Abubakar yayi murmushi yace" yauwa ko ke
fa".

Zata yi magana ya dakatar da ita yayinda yace; "tashi muje muci abinci", Brr
Farida ta miƙe haka suka jero cikin farin ciki.

Akan dinning suka same su, duka uku babu wanda ya iya cin abinci, fatan Sameer
da Tameer shine Mummyn tasu ta amince da zaɓin nasu yayin da Abdus-samad kuma
tunanin halin da ya baro Mahaifiyar tashi shine yasa.

Yana ganin su yayi saurin miƙewa ya ƙara inda take ya rungume ta, Brr Farida
tayi dariya tace; "My Baby kenan?", shi ya ja mata kujera ta zauna.

Ganin yadda yaran nata suke cikin damuwa yasa ta fara jan su da fira har suka
sake da ita, nan suka ci abincin su cikin annashuwa.

Bayan sun gama suka koma saman kujeru suka zauna, Abdul ya ɗora kanshi saman
ƙafar ta yace; "First love na tambaye ki?".

Tace; "eh Baby na", ya yi murmushi sannan yace; "Waye Mustapha Abubakar Tuge",
Brr Farida taji saukar sunan kamar saukar aradu.

Cikin sauri ta ture kan nashi daga jikin ta sannan tace; "a ina kaji wannan
sunan kuma waye yace ka tambaye ni?".

"shi da kanshi ne ya faɗa mini, kuma muna kama sosai dashi, kin san na sanshi
tun a london domin kuwa yana yawan zuwa ɗaya daga cikin attajiran dake Africa".

Brr Farida tace; "to wannan shine amsar tambayar ka, shi ɗin me kuɗi ne wanda
ake ji dashi a Africa, sai kuma me kake son sani?".

Abdus-samad ya girgiza kai domin yadda Brr Faridar tayi magana ya nuna a hasale
take.

"yauwa First love ya kira ni da Murad", ya faɗa yana me kallon mahaifiyar tashi,
Brr Farida ta miƙe tsaye cikin hasala tace; "na faɗa maka Murad baya nufin komai a
wajen ka, kada kuma ka sake tara ta da wannan maganar idan ba haka ba ranka zai
ɓace", tana gama faɗar haka ta bar falon.

Abdus-samad ya kalli Dr Abubakar, cikin sauri kafin Abdus-samad ɗin yace wani
abu, ya kalli Sameer yace; "ka shirya gobe zamu je Hayin rigasa daga nan zamu wuce
Abuja", yana gama faɗar haka ya wuce ya bar falon.

Abdus-samad ya kalli Sameer, Sameer ya ɗaga mishi kafaɗa alamun i don't care,
shima Abdul ɗin ya taɓe baki kafin ya miƙe ya fice.

Kida ya shiga part ɗin shi bayi kawai ya wuce yayi wanka, a gaban mirror ya
tsaya yana ƙara kallon kanshi, so yake ya gano meye suke da bambamci da wannan
mutumin na ɗazu wato Alhaji Mustapha.

Komai nasu kala ɗaya ne gaba ɗaya kamar tasu har ta ɓace, bambamcin su kaɗan
ne wato bakin shi ƙarami ne ba kamar na wancan ba, banda wannan kuwa babu abinda
suke da bambamci da juna sai tsufa kawai.

Ya lumshe idanu, ganin fuskar ta yasa yayi saurin buɗe idanu, babu abinda yake
tunawa sai lokacin da gashin ta ya bayyana.

Cikin sauri ya ɗauko kayan daya cire ɗazu ya hau binciken ribbom ɗin nata, babu
jimawa ya ganshi a aljihun shi, ya riƙe a hannun shi yana kallo.

Tuno yadda fuskar ta ke nuna tsantsar tsoro a duk lokacin da suka haɗu yasa yayi
murmushi a hankali ya furta; "Nusraaaaaam!".

Yasin yana Abdul yana ruwa 🙄🙄🙄.

******** ***********
*MAƘARFI ROAD, KADUNA (GIDAN AMARYA)*.
Nusram ta miƙe cikin yanayi na rashin lafiya ta nufi bakin ƙofa ta fice daga
ɗakin, bata taɓa tunanin Alhajin zai kai zuwa yanzu be shigo ba.

Ta tsaya tana kallon falon nata, bata san lokacin data ja tsaki ba inama ace
wannan kuɗin da maman nata da Auntyn ta suka kashe gidan wanda take so ne.

Kanta da yake sara mata ta dafe sannan ta nufi wata ƙofa data gani, ganin ta a
inda take zato wato Kitchen yasa taji daɗi sosai.

Buɗe-buɗe ta fara tana neman abinda zata ci, babu komai wanda zata iya ci dan
haka dole ta fito, hango fridge yasa ta nufi can.

Allah ya bata sa'a domin ta sami ruwa pure water a ciki me sanyi dan haka ta
ɗauko ɗaya daga ciki ta wuce ɗakin nata.

Bincike ta fara yi har Allah yasa taga kayan dubulan ɗin ta nan kuwa ta ɗiba ta
hau ci hannu baka hannu ƙwarya, sai da ta ƙoshi sannan ta kora da ruwa.

Ta kai kallon ta kan agogon ɗakin ƙarfe sha biyu da rabi duk inda ango yake ya
kamata ace zuwa yanzu yana cikin gidan shi.

Mema zai saka ta damu bayan ba wani son shi take yi ba, ita kanta tayi mamakin
rashin tsoron data nuna, Allah sarki Nusreen ko yaya take yanzu oho, ko ta dena
kuka zuwa yanzu bata sani ba.

Nan taji hawaye yana zubo mata, Allah yasa ma Shureim yana tare da ita ta san
cewa yanzu zai rarrashe ta, ita fa bata da kowa, ta share hawayen daya zubo mata
sannan ta nufi bayi.

Alwala ta ɗoro domin tazo tayi nafila, ta ɗauki hijab ta saka, Sallama taji a
falo kafin tayi wani yunƙuri taji an nufo ɗakin ta wanda yayi dai-dai da fitowar
mutum daga cikin wardrobe ɗin ta.

Kallon shi take bakin ta ɗauke da addu'a don a tunanin ta Aljani ne, ya matso
kusa da ita yace; "yauwa masoyiyata kiyi sauri mu tafi kafin wancan ƙaton ragon ya
shigo".

Alhaji Baballe da yayi niyar shigowa jin abinda ke gudana a cikin ɗakin yasa ya
turo ƙofar cikin fushi, ya bisu da kallo yadda fuskar Nusram ya nuna tsoro da kuma
hijab ɗin dake sanye a jikin ta ya gasgata abinda yaji.

Ya nuna ta da hannu "wato sai da kike nuna ban isa ba haka Uban daya haife ki ma
be isa ba wallahi, dan haka sai na sauya miki kamanni ta yadda gobe wani namiji ba
zai ga wannan kyawun naki ba har ya janyo hankalin shi gare ki", yana gama faɗar
haka ya kulle ƙofar inda ya tafi neman abin duka.

Ganin haka yasa Bangis ɗaga window ya dira yayinda ya bar Nusram kamar statue,
bata dawo hayyacin ta ba sai da taji ana buɗe ƙofar.

Alhaji Baballe ta gani hannun shi riƙe da zabgegiyar bulala irin ta wayar wuta,
nan jikin Nusram ya fara rawa; "ka dakata kaji wallahi ba abinda kake tunani
ban.......", bata samu damar ƙarasawa ba sabida saukar bulalar da taji.

Sosai ta daku a hannun Alhaji Baballe wanda dama kamar ƴa take a wajen shi, dan
dai kawai aure ya ratsa tsakanin su ne, dama fatar Nusram fashewa take idan taji
duka dan haka dan danan ya fasa mata jiki.

Tana bashi haƙuri tana zagaye ɗakin haka yake binta yana duka, har ta faɗi a
ƙasa amma haka yasa ƙafa ya dinga takata yana huci.

Sai da ya gaji dan kanshi ya ƙyale ta, a lokacin gaba ɗaya kukan ma ya dena fita
sai dai hawaye kawai da take yi na tsabar azabar da ta sha.

Ta dafe cikin ta wanda ke mata wani irin tsananin ciwo, tana ji tana kallo ya
kira police akan suzo gidan shi, amma bata da damar yin magana.

Ya tashi ya shiga bayi ya taro ruwa ya fita be jima ba ya dawo hannun shi riƙe
da bokitin ya nufi inda take ya shara mata ruwan.

Nusram ta runtse idanu tana jujjuya kai cikin wahala da tsananin raɗaɗin da
take ji a inda ya zuba mata ruwan.

Ya kamo wuyan ta ya shaƙe yana faɗin; "ina ɗan iskan saurayin naki yake?",
Nusram babu baki wuya kam ta sha ta, idanun ta yayi ja babu abinda take jira banda
mutuwa tazo ta tafi da ita.

Ƙarar isowar motar ƴan sandan ya ƙwace ta daga hannun Alhaji Baballe, hijab
ɗin ta ya kama ya jata har zuwa waje inda ƴan sandan suke tsaye sannan ya cilla
musu ita yace; "ku tafi da ita ku rufe mini ƴar iska kada ku sake ku bada belin
ɗinta".

Ya juya cikin gida yana huci, Nusram ta daɗe kwance a wajen kafin ta iya miƙewa
tsaye jiri na iyabar ta, ta kalli ƴan sandan dake tsaye a wajen su kansu sun
tausaya mata duk da basu san laifin da tayi mishi ba.

Ɗaya daga ciki ya ɗago ankwa din hannun shi, Nusram cikin baƙin ciki ta miƙa
hannun ta kamar wata ɓarauniya ko wacce tayi wani babban laifi.

Haka suka tasa ƙeyar ta cikin motar, Nusram ta ɗaga hannu ta kalli ankwar
hannunta ta fashe da kuka tana me tausayin rayuwar ta.

Ta saka hannu ta janyo hijab ɗin ya rufe gefen fuskar ta a haka har suka isa
ofishin ƴan sandan, haka suka shiga ciki, sai sa suka tambayi sunan ta ta faɗa musu
suka ɗan yi rubuce-rubuce sannan suka ce ta cire ƴan kunnayen ta da zobunan ta haka
ta cire duka dama babu komai a hannun ta dan haka suka iza ƙeyar ta zuwa cikin cell
bayan sun saka ta cire hijab ɗin ta.

Koda suka maida suka rufe a wajen Nusram ta durkushe tana kuka me cin rai, wai
yau itace a rufe a cell abinda bata taɓa tunani ba kenan, Aunty tace wata rana zata
yi farik ciki ko sai yaushe wannan ranar zata zo??.

#LIKE
#SHARE
#COMMENT

*babyn Abdul, Maman Meenal Elham da Farouk*.

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖37-38📖📖

Ranar duk iya satar barci sai da ya ƙyale Nusram, ga sauro ya sanyi ga raɗaɗin
ciwon ta ga kuma zazzaɓin dake jikin ta ga damuwa da fargaba.

Kuka kam ta sha shi har ta bawa uku lada, tana yi tana istighfari; "Astaghfullah
Allah idan laifi nayi maka kake jarabtata da wannan masifun domin na tuba ya
Ubangiji ina me ƙanƙan da kai zuwa gare ka Allah ka amshi tuba na", abinda ta kwana
ambata kenan.

Koda safiya tayi haka ta tasa fararau-fararau ɗin koko da ƙosai ƙwara uku a gaba
tana kallo tana hawaye, duk yadda suke a gidan su basu taɓa irin wannan karin ba
abinda ke ƙara bata mamaki shine yadda yau aka kawo ta Cell gashi ma har ta kwana.

Da safen ragowar wa'inda suka kwana a gidan biki ƴan Dabai ne kawai dan jiya
tunda aka kai amare kowa ya wuce gidan shi.

Su ke ƙoƙarin haɗa abin kari babu wanda ya kula Mama Jummai wacce ke faman shewa
da murna to babu wanda ya san ma me take yiwa murnar.
Tun da asuba Bangis ya kira Habiba ya shaida mata aiki yayi kyau, wannan shine
silar murnar tata sai dai ba'a sami dama kan gidan Nusreen ba saboda lokaci ya
ƙure.

Mama Jummai tace; "babu komai ai tunda ka ƙwato mana me maiƙon waccen zan ji da
ita daga baya kada hakan ya ɗaga maka hankali".

To wannan shine ya saka su a cikin murna kuma suna jiran sakamako me kyau.

Wajen goma suna zaune sai ga Baba ya fita da sauri, Mama Jummai ta kuma aashe
baki tana murna tana fatan ace aikin su ne yaci.

Baba kuwa ganin Alhaji Baballe harda ɗan duƙawa wajen gaishe dashi, Alhaji
Baballe ya amsa a fuzge sannan ya miƙowa Baba takarda yace; "ka takardar
matsiyacoyar ƴar ka nan na sake ta saki uku, sannan na baka nan da kwana uku ka
dawo mini da duk wani kuɗi daka san na baka shi".

Baba ya ƙwalalo idanu waje, cikin rawar murya yace; "haba Alhaji me yayi zafi
haka, meta aikata maka wanda ta cancanci wannan sakamakon?".

Alhaji Baballe yace; "oho sai kaje ka tambaye ta ni dai na gama magana ka dawo
mini da kuɗi na kawai", Baba yace; "dan Allah Alhaji kayi haƙuri, kada muyi haka da
kai na san cewa Nusram yarinya ce me biyayya ga haƙuri kuma".

Alhaji Baballe yace; "ne haƙuri fa kace, yarinyar dana kama da saurayin ta zasu
gudu ranar da aka kawo ta gida na, har cikin gida na ƙato ya shigo zai tafi da
ita".

Baba ya hau salati yana tafa hannu, cikin jimami yace; "Alhaji ka dai sake
bincikawa amma ba halin ta bane, na san Nusram ciki da bai".

"oho wannan kuma kai ta shafa bani ba kaji na faɗa maka ka dawo mini da kuɗaɗe
na kawai ni ba zan iya zama da ƴar iska ba".

Baba yace; "bafa za'a yi haka ba akwai ƙanwarta idan kana so yanzu ma sai a
ɗaura muku aure", Alhaji Baballe ya girgiza kai.

Baba ya hau roƙon shi da Allah dan ya amince, sun jima a haka sannan Alhaji
Baballe yace; "na yarda shikenan zanje na dawo zuwa ɗaya sai a ɗaura, kaima ka
shiga ka faɗawa naka ƴan uwan", Baba yayi ajiyar zuciya ganin Alhaji Baballe ya
amince yace; "insha Allahu yadda kake so haka za'a yi, yanzu ina ita Nusram ɗin
take?".

Ba tare da damuwa ba yace; "tana ofishin ƴan sanda", yana faɗar haka ya shige
motar shi ya tafi, Baba kuma ya shiga gida.

Ɗakin Mama Jummai ya shiga ya zuba tagumi, cikin Kissa tazo tace; "meya faru ne
Baban Atika".

Ya ɗago ya kalle ta sannan ya bata labarin komai da yadda suka yi da Alhaji,


cikin damuwa yace; "ni yanzu ban san ko zasu amince ba gashi nayi mishi alƙawarin
wata".

Mama Jummai cikin ranta kamar tayi me dan murna amma a fili sai tace; "Ashsha
gaskiya Nusram bata kyauta ba sai dai dama shekaranjiya Atika tace mini wani ɗan
iska ya aike ta wajen Nusram ɗin amma na kwaɓe ta dan kasan surutun yara".

Baba yace; "kira mini Atikar", Mama Jummai kuwa rai fes ta ƙwalawa Atika kiea,
dama tana laɓe tana ji dan haka babu ɓata lokaci ta amsa tana shigowa ciki.
"Atika ki taimaka ki rufawa Mahaifinki asiri ki yarda ki auri Alhaji Baballe
dan Allah ki mini wannan alfarmar".

Atika ta ɗago tace; "Baba magana kake fa akan mijin ƴar uwata Nusram ai hakan ba
zai yiwu ba na aureshi bayan yana matsayin mijiɓ ƴar uwata kuma suna tare".

Baba ya ƙara saukar da kai ƙasa yace; "Atika ki tsaya ki saurare ni, yanzu haka
takardar Nusram tana hannu na ya sake ta saki uku, kuma yace sai na dawo masa da
kuɗin shi, Atika kema kin san hakan bame yiwuwa bane dan ko gidan nan na ɗaga na
siyar ba zai kai kuɗin daya bani ba Dan Allah ki rufa mini asiri kinji".

Atika ta ɗan yi shiru sannan tace; "shikenan Baba insha Allahu zan share maka
hawayenka, zan kuma yi maka biyayya Allah yasa hakan shiya fi".

Baba har ƴar ƙwalla sai da yayi jin abinda ƴar tashi ta faɗa, faɗi yake; "Atika
Allah yayi miki albarka", sannan ya miƙe ya fice.

Yana fita Atika tayi tsalle ta faɗa kan mahaifiyar ta, suka hau murna suna jin
daɗi, Sahura ma na zuwa suka bata labarin abinda ya faru nan itama ta hau taya su
murna sannan fa suka fara shirye-shiryen yadda bikin zai kasance.

Baba dake tsaye ƙofar ɗakin Ummi yace; "Maimuna! Maimuna!! Fito yau da ƴa ɗaya
na haifa da sai dai na haɗiyi zuciya na mutu to Allah yasa ina da wata".

Ummi ta ɗan yi jimm sannan tace; "Baban Nusreen meya faru ne?", cikin ɗaga murya
yace; "meye ma be faru ba Maimuna", ya zaro takardar ya miƙa mata.

Ummi ta juya takardar sannan tace; "ai baka ce komai ba ka san ba iya karantawa
zan yi ba".

Mama Jummai dake bakin ƙofa ta tuntsire da dariya tace; "matsalar ka kasance
jahili kenan", babu wanda yace mata komai.

"ƴar ki na Police Station mijin ta ya kamata *A DAREN FARKO* zata bi saurayi su


gudu shine ya kai ta caji ofis yanzu haka acan ta kwana, wannan kuma takardar
sakinta ne ya sake ta saki uku, na nemi alfarmar ɗaura mishi aure da ƴar uwar ta
kuma ya amince dan haka yau ƙarfe ɗaya za'a ɗaura auren, yanzu zan je kasuwa na
ƙara siyo abubuwan da babu sai a cigaba da biki kawai kayan ɗaki da komai da komai
kuma za'a barwa ƴar uwar ta ne".

Yana gama faɗin haka ya juya yana faɗin; "bari Hansai( ƴar uwar shi daga Dabai)
tazo muke kasuwa tare sai ta taho da abubuwan da babu", Ummi kuwa tana tsaye ne
kawai ta rasa meke mata daɗi.

Baba Sailuba ta fashe da kuka aka shiga bata haƙuri tace; "ku dena bani haƙuri
yau naga meke faruwa gidan Abdullahi, lallai ba hakanan ba Maimuna ki tattara
kayanki kawai mu tafi gida, dan ni yanzu zan bar garin nan".

Ummi ta girgiza kai sannan tace; " Baba meye amfanin tafiyata a yanzu bayan
nasan cewa babu me amso mini ƴata wajen hukuma idan har na tafi to haƙuri na na
shekaru ashirin da ɗoriya ya tashi a banza kenan dan haka Baaba kiyi haƙuri zan
zauna kawai a nan".

Baaba Sailuba tace; "shikenan na fahimci wane irin zama ake a gidan Abdullahi,
dan haka ku haɗo kayanmu, mu tafi gida kawai", ta ƙarasa tana goge hawayen daya
zubo mata.

Haka yawancin ƴan Dabai suka tafi sai ɗai-ɗai ku wa'inda ke goyon bayan
Abdullahin, Ummi kam banda zubar da hawaye babu abinda take yi.

tun daga waje suka fara jiyo faɗan Aunty, tana shigowa taja wata doguwar ajiyar
zuciya sannan ta kalli Ummi ta balla mata harara tace; "Wallahi idan kika zauna sai
baƙin cikin ɗa namiji ya kashe ki", muryarta na rawa tace; "yau wai Nusram ce tayi
kwanan Cell!?", ta fashe da kuka.

Ummi ta taso zata riƙe ta, Aunty ta dakatar da ita ta ɗora da faɗin; "kada ki
taɓa ni Maimuna, haƙurin ki a da ke yake cutarwa amma yanzu ya fara taɓa ƴaƴan ki,
abin ban haushi kamar mara gata mace da kwanan Cell, dan yana da kuɗi shikenan sai
kuma ya dinga taka duk wanda yaso haka ake rayuwa wannan ba adalci bane, wallahi ko
ki tashi ki ƙwatarwa kanki da ƴaƴan ki ƴanci ko kuma daga yau kada ki kuma nema
na".

Ummi ta koma baya ta zauna sannan tace; "shikenan Kaltume kije kawai inaji
gawata kuke so a ɗauka a gidan nan, na ɗauka ke kin fahimce ni ashe ba haka bane,
Kaltume banda yanda zanyi".

Aunty tace; "ke kuwa kike da yadda zaki yi amma idan har kika zauna kika zuba
idanu to wallahi zaki kamu da ciwon zuciya kuma ba matsalar su bane".

Tana gama faɗar haka tayi waje a zuciye, sauran ƴan ɗakin suka riƙo ta, ta kalli
ɗaya daga ciki tace; "sakeni Hadiza dole ne mu kwaso kayan mu domin kuwa babu
ƙwandalar ubanta a ciki".

Ummi tayi saurin miƙewa tace; "kiyi haƙuri Kaltume ki bar wannan maganar", ta
juyo cikin fushi tace; "ba zan bari ba", ganin abin kamar zai zama faɗa yasa Hadiza
da Karima suka riƙe Aunty suka yi waje da ita, tana kuka Ummi na kuka haka suka
rabu kowa rai babu daɗi.

Ummi ta share hawayen fuskarta tace; "Allah kana ji kuma kana gani idan har dan
inyi biyyaya ga umarnin daka bayar na cewa mata ta yiwa miji biyyaya, Allah ka duba
halin da nake ciki ka ceto mini yarinyata sannan ka shirya wa'inda suka mata wannan
sharrin Allah ka bani ikon ganin ƙarshen su", Hadiza dake tsaye tace; "ameen dai".

Aunty kuwa sai da ta tsaya a zaure ta goge hawayenta sannan ta ɗauko waya ta
kira Sulaiman ta faɗa mishi halin da ake ciki.

Cikin tashin hankali yace; "yanzu Mama zan je duk wani police station na nan
kusa domin sanin wanne aka kaita", Aunty tace; "yauwa maza kaje dan Allah yanzu zan
kira Baban ku shima domin ganin ta yadda zai taimaka mana".

Yaya Sulaiman na ajiye wayar yayi saurin fita daga shagon cikin sauri, mota ya
shiga hankali tashe yana kuma mamakin irin wannan abu dake faruwa ga wannan baiwar
Allah".

Babu inda be zaga ba amma abin haushi duk inda yaje cewa ake yi ba'a kawota nan
ba abinda be sani ba shine Alhaji Baballe ya bada umarni akan kada su sake su nuna
an kawo ta nan.

Har zuwa yamma Yaya Sulaiman be sami inda aka kai Nusram ba, duk wani Police
Station da ya sani na kusa dana nesa yaje amma be samu ba, har ya fara fita yankin
nasu wato Kaduna North, har zuwa dare babu labari.

Aunty kuwa sai yamma ta koma gidan, hankalin ta ba wani a kwance yake ba, koda
ta isa magana ta yiwa su Hansai akan su fito a tafi buɗar kai amma abin mamaki suna
fitowa Baba ya maida su.

"waye zai kai Atika ɗakin mijin ta idan har kuka kwashi jiki kuka tafi kuma",
Hadiza tace; "Haba Yaya amma a al'ada yau ake buɗar kai", Baba ya karkata kai yace;
"to ni nace a fasa ba shikenan ba, Atika ta fito ku wuce kawai".

Aunty cikin zafin zuciya ganin duk sun tsaya tayi hanyar waje, wayar Halima ta
kira da ta Safeena sai Sa'adatu da bata yi aure ba, babu jimawa suka iso nan tace;
"su shiga gidan su kwaso mata kaya zasu wuce buɗar kai".

Sun so tambayar ta abinda ya faru amma ganin yadda take ranta a ɓace yasa suka
ja bakin su, suka yi shiru koda suka fito da kayan nan suka haɗu da maƙwabta guda
biyu da kuma Hadiza wacce ta kasance ƙanwar Ummi da kuma Karima suka wuce buɗar kan
Nusreen.

Sun shiga mota sannan Sulaiman ya kira Aunty, "Mama babu inda banje ba amma
wallahi ban sami inda suka kaita ba", Aunty ta ɗanyi jim sannan tace; "na kira
baban ku yace zai kira dpon yankin amma shiru har yanzu ka kira shi kaji ya suka
yi", Sulaiman yace; "to".

Koda suka isa Unguwar Rimi gidan Amarya Nusreen, dole Aunty ta saki fuskarta
gudun zargi, sun tarar da gidan akwai sauran baƙi, nan suka yi duk abinda ya
kamata.

Sun zo tafiya Nusreen ta riƙo Aunty hakan yasa su Halima suka fice, Aunty ta
dubi Nusreen tace; "ya akayi ne Amarya", Nusreen ta saukae da kai ƙasa tana wasa da
yatsunta.

Aunty tace; "akwai abinda kike buƙata ne", Nusreen tace; "dama ɗazu ne naje
gaishe da Mamanshi, shine wasu a wajen suke ta mini habaici naga ba zan jure ba na
rama shine fa Maman shi ta kira shi ta dinga mishi faɗa wai ita bani take so ba
Nusram take so", ta ƙarasa kamar zata zubar da hawaye.

Aunty taja hannun Nusreen suka zauna bakin gado sannan tace; "Nusreen haƙuri
akeyi a komai yanzu sannan kada ki sake ki kuma faɗawa kowa abinda ke tsakanin ki
da dangin mijinki, domin idan kika faɗa mana zamu riƙe su a ranmu ki koyi riƙe
sirrinki sannan ki sani nan da gidanku da bamabanci dole ki koyi haƙuri kinji",
Nusreen ta ɗaga kai, Aunty tace; "yauwa Allah ya miki albarka", Nusreen tace;
"ameen, kunje gidan Nusram ne Aunty".

"eh ya akayi?, daga can muke muka yo nan", Nusreen ta kuma cewa; "na kira wayar
ta ba'a ɗaga ba", Aunty ta miƙe sannan tace; "idan kika cigaba da gwadawa zata
shiga ne, sai anjima", ta fice kafin Nusreen ta kuma cewa komai.

Ba tare da Aunty ta koma gidan ba, haka suma yaranta kowa gidanshi ya wuce, Yaya
Sulaiman ya dawo wajen goma amma babu sa'a domin dai kwalliya bata biya kuɗin
sabulu ba.

Nusram na can a kulle a cell banda kuka babu abinda take yi, ga tunanin halin da
ƴan uwan ta suke ciki.

Amarya kuwa bayan tafiyar su Aunty Baba yasa su Hansai suka ɗauke ta sai gidan
Alhaji Baballe, buri ya cika domin dai babu abinda aka taɓa na Nusram sai washe
baki take yi don ta san ta mori gida sama dana duk ƴan uwanta.

********* ***********

*UNGUWAR SARKI, KADUNA*.

Koda ya shigo gidan washe gari a falo ya sami Sumayya da Fadila suna fira,
ganin shi yasa suka yi shiru, yace; "ina First Love?".
Sumayya tace; "tana sama bata sauko ba", ba tare da ya kuma cewa komai ba ya
nufi saman, Fadila ta bishi da kallo.

Shigar ƙananan kaya ce kamar koda yaushe a jikin shi, blue ɗin riga anyi rubutu
da farin kala a gaba sai wando jeans fari hasken fatar shi ya fito sosai.

Da sallama ya shiga ɗakin, Brr Farida dake duba takardu wanda alamu ke nuna na
aikinta ne, ta ɗago ta kalle shi sau ɗaya ta komar da kanta ta cigaba da aikin da
take yi.

Ya ƙaraso kusa da ita, kan carpet ɗin yaja filo ya kwanta a gabanta, bata ce
komai ba har lokacin, hannu yasa ya ɗauki takarda guda ɗaya amma be gane komai a
ciki ba.

Ya taɓe baki sannan ya ajiye, yana kallonta tana aikinta shi kuma ya maida kai
kawai ya lumshe idanu.

Har lokaci me tsayi sannan ta gama ta hau tattara takardun nata, ya buɗe idanu
yana kallon ta, cikin sauri ya riƙo hannun ta sannan yace; "am sorry", ta balla
mishi harara.

Ya cuno baki cikin shagwaɓa yace; "ai na baki haƙuri", Brr Farida tace; "kai
baka ji ko? Waye yace kaje kayi magana akan wannan matsalar? Ni bance kada suyi
aure ba amma su nemo ƴar babban gida".

"inda First love kike da naƙasu kenan", ya faɗa a cikin zuciyar shi, amma a fili
yace; "nima First love ai na kusa auren nan na huta", Brr Farida tayi mishi wani
kallo ba tace komai ba ta miƙe.

" matar ka Baby har yanzu ma ba'a ƙerata ba tukunna, ni zan nemo maka matar da
zaka aura ƴar babban gida me asali da ji da kuɗi ba wai ƴar talaka ba matsiyaci",
jan bakin shi yayi shiru dan ya san idan maganar ta cigaba da tsayi to abin ba zai
yi kyau ba.

Be san dalilin da ya saka Mahaifiyar tashi ke tsananta ƙiyayya ga talaka ba, ita
dai me kuɗi in dai aka zo batun aure amma kuma sauran mu'amala zata yi da talaka.

wai matar shi ko ƙerata ba'a yi ba?, me hakan ke nufi zai sami jinkiri kenan
kamar sauran ƴan gidan kenan?, ya saki murmushi yana shafa sumar kanshi.

Tsakanin kwana biyu da maganarsu Tameer Dr Abubakar ya gama komai daya dace
sai dai kuma matsalar shine ta ɓangaren Sameer dake son Fadila.

Dr Abubakar yace a bari sai sun je Family meeting wanda zasu yi ƙarshen wata me
zuwa sai a daddale duk da yana cike da tsoron mahaifiyar tashi wato Hajja be san
yadda zata dauki maganar ba.

Brr Farida kuwa bata cewa komai game da auren nasu da anyi magana sai dai tace
Allah ya kaimu kawai kowa ya fahimci bikin be wani ɗaɗata da ƙasa ba.

#LIKE
#SHARE
#COMMENT

*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.


*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖39-40📖📖

"ina ganin Mijin Nusreen zai iya taimakawa tunda Mahaifin shi kan ya rasu babban
mutum ne shima ta yiwu ya san wasu manya", cewar Aunty.

Yaya Sulaiman ya ɗan yi shiru kafin yace; "shikenan zan mishi magana sai muji
yadda za'a yi", yana faɗan haka ya fice daga gidan.

Aunty da Ummi suka bishi da kallo kawai, a ƙa'ida bayan bikin su Nusram da sati
biyu za'a yi nashi amma har yanzu basu sami kwanciyar hankali ba, Aunty ma tana
maganar a ɗaga ne amma Ummi tace a'a.

Malam Isma'il Mahaifin Sulaiman shima dai duk iya ƙoƙarin shi a yanzu shine
Nusram ɗin ta baro hannun Police.

Da ƙyar ya samu yaga Dpo sai da ya bayar da cin hanci ma tukunna sannan ya sami
ganin shi, Nan ya bashi bayanin abinda ya kawo shi.

Sosai ran Dpo ya ɓaci, yayi faɗa sosai taya za'a bar mace a cell tsayin wannan
lokacin?, nan ya kira wani Sergent akan ya binciko mishi inda aka kai Nusram ɗin.

Ya amsa da to ya fita, Dpo yace; "kuyi haƙuri manyan ƙasan nan ke amfani da
wawayen cikin mu ana ɓatawa Police suna, yanzu zanje a fitar da ita insha Allah,
kuma duk lokacin da abu makamancin haka ya faru ga number na ka kira ni kawai".

Abba ya amsa yayi godiya sosai, babu jimawa ɗan sandan ya dawo nan ya shaida
mishi tana headquarter dake Barnawa.

Dpo ya kalli Abba yace; "tashi muje Alhaji da kaina ma zani domin a fitar da
ita", Alhaji Isma'il yace; "to".

Motar Abban suka shiga, nan Abba ya fara neman wayar Sulaiman ɗin domin ya faɗa
mishi yadda akayi.

Sulaiman kuwa sai da ya kira wayar Shureim yaji cewa yana gida sannan ya ƙarasa,
a harabar gidan ya tsaya nan Shureim ɗin yazo ya same shi, bayan sun gaisa yace;
"ba zaka shiga ba, na faɗawa ƙanwar ka cewa kana hanya".

Sulaiman yayi murmushi yace; "sai dai nace ka gaishe ta amma ni ba zan shiga ba
don akwai abinda ya kawo ni", Shureim yace; "meya faru?", Yaya Sulaiman ya bashi
labarin komai.

Hankalin Shureim ya tashi sosai, ya fara salati yana jimamin abinda ya faru,
yace; "bari na shirya sai muje gidan Kwamishinan ƴan sandan kawai".

Yaya Sulaiman yace to, Shureim ɗin ya tafi kenan wayar Sulaiman tayi ƙara, ganin
kiran mahaifinshi yasa ya ɗaga da sauri nan ya faɗa mishi yadda suka yi da Dpo ya
kuma ce mishi ya biyo su Barnawa, Sulaiman cikin farin ciki yace; "to Abba gani
nan".

Nusreen dake zaune tana jiran shigowar tasu jin an buɗe ƙofa yasa ta miƙe da
sauri sai dai ganin mijin nata shi kaɗai yasa tace; "ina Yaya Sulaiman ɗin fa".

Ya dafe goshi yace; "Sorry Nurulƙalbiy, ashe bashi bane ya iso wani abokina ne
Yaya Sulaiman ɗin ya kirani akan wai ba zai samu zuwa ba", ya ƙarasa yana wucewa
bedroom.

Babu jimawa ya fito da shirin fita, cikin sauri tace; "Hayateey ina kuma zaka
je, kayi mini alƙawarin yau babu inda zaka je fa".

Ya riƙo hannunta cikin sigar lallashi yace; "Nurulƙalbeey kiyi haƙuri ki bari na
fita wani abokina ne Custom suka riƙe mishi kaya shine yazo akan yana so na raka
shi kinji ba daɗewa zan yi ba", tace; "shikenan amma idan ka dawo zaka kaini gidan
Ramluv ko?", ya ɗan yi jimm sannan yace; "to shikenan sai na dawo ko", ta ɗaga kai,
har bakin ƙofa ta rako shi sannan ya tafi.

Ita kuma ta juya ta koma wajen Mama kawai ta wuce don bata son zama ita kaɗai,
da sallama ta shiga Mama dake yanke farce ta amsa sallamar da murmushi a fuskarta,
tun tana adawa da auren har ta haƙura yanzu.
Nusreen ta ƙarasa ta amshi Nail Cutter ɗin tana cigaba da yanke mata, suna fira
jefi-jefi har ta gama.

Yaya Sulaiman yace; "munyi waya da Abba yanzu yace mu wuce Badarawa", Shureim
yace; "to muje can ɗin", suka shiga motar Yaya Sulaiman ɗin suka tafi.

Suna zuwa ana fito da Nusram, Yaya Sulaiman sai da hawaye ya zubo mishi ganin
yadda ta koma, fuskarta tayi baƙi sosai kamar almajirar data shekara bata ga ruwa
ba, tana tafiya tana ɗingishi ga rama da tayi sai idanu Zuru-Zuru kamar ba Nusram
ɗin daya sani ba tsayin lokaci, ya tabbatar da ace a hanya suka haɗu tabbas ba zai
ganeta ba.

Shureim da Abba suma duka jikin su yayi sanyi sosai, Dpo kuwa ranshi ya ɓace
sosai ya rufe su da faɗa suna ta bashi haƙuri sai da yayi warning ɗin su sosai
sannan aka cike takardu na beli kan a basu Nusram ɗin.

Nusram da duk jikinta take ji kamar an ɗaure shi tamau ga wani irin ciwon kai
dake damunta, ƙafar ta kuwa tsabar zama waje ɗaya ne gashi dandamaryar siminti take
wuni ta kwana har kwana uku wannan shine dalilin riƙewar ƙafar.

Sulaiman ya buɗe mata ƙofa ta shiga da ƙyar sannan shida Shureim suka shiga
gaba, Nusram ta jingina kanta da kujera tana cigaba da share hawayen fuskarta.

Ita yanzu rayuwar gaba ɗaya ta sire mata, ji take dama ta mutu ta huta kawai,
wannan wane irin tozarci ne.

Tana jin lokacin da Yaya Sulaiman ya kira Aunty yake faɗa nata gasu nan sun taho
amma sun bar Abba a can.

Suna isa gida Nusram ta yunƙura ta fito, bata tsaya ba dan bata so mutane su
ganta sai dai ina ta makaro domin kuwa mutane sun riga sun san meya faru dan haka
wa'inda ke waje nan suka tsaya kallon ta.

Tana ɗingisa ƙafa ta shiga gidan, Shureim ya kira likitan su akan yazo ya duba
ta koda wata matsala, babu jimawa ya iso.

Nusram kuwa tana shiga gidan Mama Jummai ta rangaɗa guɗa, Amira kuwa ta hau
dariya, Aunty ta fito da sauri ta taho wajen ta suka rungume juna suna kuka.

Ummi tace; "ai da sai ku ƙaraso ba wai ku tsaya a nan ba", Aunty ta taimakawa
Nusram ɗin ta ƙarasa ɗaki.

Ummi da kanta ta juyewa Nusram ruwa me zafi ta kai mata bayi, Aunty ta taimakawa
Nusram ɗin ta shiga wanka tayi saɓi sama da sau biyar sannan taji iska me daɗi ta
shigar ta wannan ya tabbatar mata da ta fita kenan.

Ta ɗan ji ƙarfi a jikin ta domin kuwa da kanta ta fito har zuwa ɗaki, cikin
kayan ta wanda Ummi bata riga ta kyautar ba Aunty ta ɗauko mata doguwar riga Buba
ta saka.

Tana zama likitan da Yaya Sulaiman da kuma Shureim suka shigo, bayan sun jajanta
abinda ya faru sannan likitan ya shiga aikin shi.

Ya duba ta sosai sannan yace; "akwai allura yanzu zanyi mata guda biyu sai kuma
magunguna wanda zan rubuta muku suma guda biyu sai a siyo ta shanye insha Allahu
zata sami sauƙi stress ne kawai sai rashin barci da kuma sanyi daya shige ta.

Aunty tace; "to Allah ya kyauta gaba", duka suka amsa da ameen, Shureim da Yaya
Sulaiman suka fice daga ɗakin sannan likitan yayi mata allura daga nan ya fice
shima.

Ummi ta miƙowa Nusram ɗin liptin me zafi wanda aka sawa citta da kanunfari
tace; "ki shanye yanzu", ta amsa ta shanye tas.

Aunty ta ciko cokali da man tafarnuwa ta miƙo mata tace; "ki dinga sha kullum
cokali ɗaya da safe ɗaya da yamma", Nusram ta ɗaga kai kawai.

Ruwan zafi da ƙyalle me kyau Ummi ta miƙowa Aunty inda ita kuma ta amsa, ƙafafun
Nusram ɗin ta saka a ciki ɗaya bayan ɗaya tana gasawa har zuwa cinya.

Har lokacin Nusram ɗin bata ce komai ba, sai dai kallon su kawai da take yi, tun
tana ɗan janye ƙafar har ruwan ya fara yi mata daɗi hakan yasa ta lumshe idanu
kawai.

Aunty bayan ta gama ta kuma shafe mata ƙafafun da man tafarnuwar sannan tace;
"to kwanta", Nusram ta kwanta yayin da Aunty ta ɗauki ruwan ta fita dashi.

Aunty na bakin famfo wata mata ta shigo ɗaya daga cikin maƙwabta, suka gaisa da
Aunty sannan ta wuce, da sallama ta shigo, Nusram na jinta amma ta ƙara lumshe
idanu.

"oh ashe haka kuma abu ya faru Allah ya kyauta gaba", sai da Ummi tayi jimm
sannan tace; "ameen", hakan be ishe ta ba sai da ta kuma cewa; "ina zaune sai ga
Hassan da gudu yana faɗin Mama fito kiga Nusram ko Nusreen ɗin gidan Jummai me
abinci an dawo da ita, yana faɗin hakan nace Nusram ce domin kuwa itace take
folistashon saboda mijinta ya kamata da ƙato cikin daren da aka kai.........".

Bata ƙarasa ba Aunty dake tsaye a bakin ƙofa ta shigo tana huci a katse ta; "ya
isa haka munafikai masu zuwa lahira da ƙoƙon masaki, masu barci da ido ɗaya, wato
abinda kuke so kenan kuji inda wani abun ashsha ya faru ku yaɗa to ki sani wannan
ƙaddarace ta hau kanta kuma bata wuce kan kowa ba".

Matar ta riƙe haɓa tace; "ke baiwar Allah kada ki ɗorawa ƙaddara yaran da suke
sakaka babu mafaɗi waye be san yadda motoci ke ɗaukar su yana ajiyewa ba, ai itama
waccen aiki ne yaci mijin wannan kam daga gani ya riƙe Allah da ƙarfi ne", Aunty ta
ɗaga hannu domin kwashe ta da mari Ummi tayi saurin riƙewa tace; "a'a Maman Adam
kada ki aikata wannan kuskuren", Aunty ta fuzge hannun ta.

Matar taja tsaki ta miƙe tana faɗin; "dama ai tabarmar kunya da bori ake naɗeta
yara sun zama annoba a gari mu dai idan abin ya fara ƙarfi zamu kai ƙara ne kawai
wajen me unguwa", tana faɗin hakan ta fice.

Aunty tace cikin ɗaga murya; "ki tafi Zaria ne wajen Sarki, kada ki tsaya wajen
me Anguwa, banzaye shashashu", Mama Jummai dake zaune a waje tana ji ta tuntsire da
dariya tayi shewa tace; "sai ni Jummai ƴa ga Habu da Lantana ai duk wanda yaja dani
sai ya faɗi".

Aunty ta balla mata harara kanta ja tsaki, Mama Jummai tayi shewa tace; "wai ɗan
karo ma ya samu sake", cikin jin haushi Aunty tace; "ɗan karo ya wuce agola ya
kaiwa ƴar masu gida hari", Mama Jummai bata kuma jan maganar ba sai tayi gum.

Har yamma Nusram na kwance bata tashi ba, Sai wajen biyar sannan ta tashi ta
rama sallolin da ake bin ta, zuwa lokacin ta ɗan sami sauƙi.

Yaya Sulaiman da yazo ɗaukar Aunty ya ƙara mata sannu da jiki, murya a dashe
tace; "na gode sosai da ɗawainiya", ya ɗan ranƙwashe ta na wasa yace; "ina wasa
dake ne".
Su Ummi suka yi dariya, sunyi sallama inda Ummi ke ƙara godiya a gare su, Aunty
tace; "kada ki damu ai ɗa na kowa ne kuma Nusram idan kin tuna dama tawa ce".

Haka suka tafi suka bar su, abin mamaki har dare ƴan shigowa ganin ƙwaƙwaf basu
dena shigowa ba, Mama Jummai kuwa tafiyar Aunty sai ta bude shafin habaici, babu
wanda yace ci kanki.

Koda Isa ya dawo Nusram na jin lokacin da take faɗa mishi, yayi shiru kafin
yace; "Allah ya kyauta gaba", Mama Jummai ta balla mishi harara.

Bayan sallar isha'i Nusram na zaune saman abin sallah tana lazimi, Isa yayi
sallama ya shigo, a sanyaye ta amsa.

Kusa da ita ya tsuguna sannan yace; " ya jikin?, ta amsa da; "lafiya lau", Allah
ya kyauta gaba", tace; "ameen", ya jima tsugunne a wajen Nusram tayi banza dashi.

Da kanshi kuma ya miƙe ya fice daga ɗakin, Nusram ta sauke ajiyar zuciya hawayen
baƙin ciki yana zubo mata.

Ta koma ta kwanta tana jiyo muryar mahaifin nata a tsakar gida amma ko leƙowa
beyi ba, hasalima sai lissafe-lissafe suke yi shida Mama Jummai da alamu dai
bashinta yaci.

Cikin dare Ummi taji saukar numfashi da kuma kakari, da sauri ta miƙe ta ƙarasa
wajen Nusram ɗin, tana kwance tana murƙususu gefen ta kuwa Kubra ce ke barcinta.

Ta juyo da ita hankali tashe tace; "Nusram meke damun ki", Nusram ta nuna cikin
ta hawaye na zubo mata.

Ummi ta buga uban tagumi, yanzu me take dashi wanda zata nemawa yarinyar ta
magani duk wani kuɗi da tayi tanajin sa ta kashe shi wajen bikin nan, ta sauke
ajiyar zuciya tace; "Allah ka dube ni".

Hijab ta ɗauko ta saka sannan tazo ta kama Nusram ɗin ta miƙe, sai da ta taimaka
mata wajen saka hijab ɗin sannan ta riƙe mata hannu a ɗurkushe Nusram take tafiya
har suka fito daga ɗakin.

Ummi ta duba agogon wayar ta Sha biyu harda rabi, ta kalli Nusram tace; "Nusram
bari na faɗawa Baban ku, ko zai taimaka mana", Nusram ta ɗaga kai tana durƙusawa a
wajen dan wani irin murɗawa da cikin yayi.

Ummi kuwa ƙofar ɗakin Mama Jummai taje tana bubbugawa, sun jima sosai kafin azo
a buɗe, Mama Jummai ke baya sai Baba a gaba.

"meye kuma yanzu kika zo zaki dame ni?", Ummi ta haɗiye wani abu me ɗaci tace;
"Nusram ce bata da lafiya shine nace ko zaka taimaka a kaita asibiti", Baba yaja
tsaki zai koma ciki Ummi tayi saurin ɗurkusawa tace; "dan Allah Baban Nusreen ka
duba girman Allah ka zo mu kai yarinyar nan asibiti kada ta mutu".

Cikin fushi Baba yace; "ta mutu mana waye ya damu yarinya taje ta gama iskancin
ta, ta nuna mini ban isa ba ta kwaso abin kunyar ta shine zaki zo ki tasa ni a gaba
wai sai na kaita asibiti, to wallahi babu inda zanje, ai inda Allah ya taimake ni
ba ita kaɗai na haifa ba da sai dai a ɗauki gawata a gidan baƙin cikin ta ya kashe
ni".

Ummi cikin kuka tace; "dan Allah ka taimaka kazo a kaita asibiti duk wannan idan
ta sami lafiya ayi maganar", Baba yace; "wallahi Maimuna babu inda zanje ina
saurayin da yayi cikin yazo ya kaita mana", be bari ta kuma cewa komai ba ya maida
ƙofar ya rufe.

Nusram zuwa yanzu jikin ta har rawa yake yi, ga zafin ciwo ga kuma baƙin ciki na
magan-ganun da Mahaifinta yake faɗa akanta.

Ummi ta jima a tsaye a wajen tana share hawaye kafin ta koma wajen Nusram ɗin ta
taimaka ta ɗago ta suka fara tafiya a hankali har suka fice daga gidan.

Garin yayi tsit ga duhu, haka dai suke tafiya a hankali idan cikin ya murɗa sai
dai ta tsugunna a wajen idan yayi sauƙi sai su cigaba da tafiya.

A haka har suka ƙaraso bakin titi, babu mutane sosai sai jefi-jefi kuma yawanci
sai dai su kallesu kawai su wuce wasu ma basa ko kallon inda suke.

Duk motar da Ummi tayi ƙoƙarin tarewa bata tsayawa, ita dai Nusram na tsugunne
tana riƙe da cikinta duk addu'ar da tazo bakin ta ita take yi.

Zasu kusa rabin awa a wajen sannan wata mota da har ta wuce ta kuma dawo da baya
ta tsaya, mutumin ya leƙo da fuskar shi yace; "ina zuwa Hajiya da daddare haka".

Ummi tace; "kaga yarinya tace bata da lafiya shine nace ko zaka taimaka mana ka
kaimu asibiti, wand ake kusa duk idan dare yayi rufewa suke yi".

Ba tare da ɓata lokaci ba ya buɗe musu ƙofa suka shiga, sannan yaja suka tafi,
sun yi tafiya me ɗan nisa sannan suka iso asibitin.

Sai da ya taimaka ma Ummi suka shiga har cikin asibitin, aka bata gado har aka
shiga duba ta domin babban mutum ne, ya duba agogon hannun shi ya kalli Ummi kafin
ya ciro kuɗi a aljihun shi ya miƙo mata yace; "gashi ko zaku buƙaci wani abin,
yanzu idan zan fita zan muku clearing bill ɗin ku", Ummi tsabar murna kamar ta
tsuguna a ƙasa ta mishi godiya.

Yace; "kada ki damu ɗa na kowa ne Allah ya bata lafiya", Ummi ta amsa da ameen,
haka ta bishi da kallo har ya fice daga asibitin, ga dai shi babban mutum amma kuma
yana da sauƙin kai sosai.

Ta jima zaune a wajen kafin likitan ya fito sannan Nurses suka fito janye da
gadon da Nusram ɗin ke kai a kwance, likitan yace; "ki bisu zasu kaita ɗakin da
zata huta Alhaji Mustapha ya riga ya biya duk wani kuɗi da za'a yi muku aiki a nan,
dan haka zuwa safe zaki je Pharmacy ki amso mata magun-gunan ta, inda ta buge ne ko
kuma takata akayi dai ban sani ba to wajen ne ke mata zafi yaso ma ya taɓa
mahaifarta amma Allah ya kiyaye be taɓa ba ɗin yanzu munyi mata allura insha Allahu
nan da safiya zata sami sauƙi", Ummi tace; "to an gode sosai", tabi Nurses ɗin don
kai Nusram ɗin ɗakin hutu.

Ɗaki na musamman aka kai su, su kaɗai ne a ciki ga couch nan sai gado har da tv
wato plasma ga sanyi babu wani hayaniya, sai da suka jona mata drip sannan suka
fice daga ɗakin.

Ummi ta shiga bayi ta ɗauro alwala sannan tazo ta shinfiɗa ɗan kwalin ta, dan
bata ɗauko komai ba ta hau kai ta tada sallah.

Ta jima tana sallah kafin barci kuma ya kwashe ta wanda bata farka ba sai asuba,
tana idar da sallah Nusram itama ta farka, zuwa lokacin ruwan ya kusa ƙarewa Ummi
ta ɗauko mata roba me faɗi ta taimaka mata tayi alwala sannan tayi sallar a saman
gadon.

***********⬇️⬇️⬇️******
*MAƘARFI ROAD, KADUNA*.

Hajiya Salma ta shigo ɗakin hannun ta ɗauke da kofi, ya juyo ya kalle ta, da
sauri ta ja ɗan ƙaramin table ta ajiye a kai sannan ta nufi inda yake.

Ta taimaka mishi ya ƙarasa shirin shi, sannan ta riƙo hannun shi ta zaunar
dashi, ta ɗauki cup ɗin data ajiye ta fara bashi a baki da kanta.

Tana gama bashi ya miƙe ta bishi da kallo yace; "meya faru ne Hajiyata?", tayi
fari da idanu sannan tace; "account ɗina yayi low", yace; "zan miki transfer yanzu,
baki da matsala sai ta kuɗi", ta ɗaga kai tana murmushi.

Ya matso kusa da ita yace; "har ni ba zaki yi kewa ba?", ta riƙo hannun shi
cikin kissa tace; "shine ma kan gaba da zanyi, muje na raka ka, kada kayi missing
flight", yana gaba tana bayan shi hannun ta riƙe da jakar shi don tafiya.

Suna saukowa akan steps yace; "ki kula da Khausar kin san yanayin rawar kanta and
dan Allah ga amanar gidana nan da kuma yarana da dukiya dake kanki na damƙata a
hannun ki, ki kula kinji".

Tace; "kada ka damu yadda ka tafi ka barmu haka zaka dawo ka same mu, zan kula
da duk wata amana taka har kaje ka dawo".

Har bakin mota ta raka shi, masu tsaron lafiya suka buɗe mishi mota ya shiga,
tana ɗaga mishi hannu har ya fice.

Taja tsaki tace; "taya zan so ɗanka bayan ni baka son nawa ƴaƴan", ta juya cikin
sauri ta nufi cikin gida.

Tana shiga falon ta tarar da Khausar ta fito sanye da wando ɗan ƙarami zuwa
cinya sai kuwa riga iya cibiya.

"kin tashi Baby?", Hajiya Salma ta faɗa, Khausar ta ɗaga kai sannan ta nufi
dinning table domin karyawa yayin da Hajiya Salma kuma ta nufi ɗakin ta.

babu Jimawa Hajiya Salmar ta fito jikin ta sanye da Riga pink da ratsin fari sai
wando pink, ta ɗora after dress a sama pink me shara-shara, sai ƙaramar jaka data
rataya itama pink sai kuma makulli, ta yiwa Khausar peck a kumatu tana faɗin; "Baby
na tafi sai na dawo", Khausar tace; "to Mummy".

Tana fita masu tsaron lafiya suka taho tayi saurin ɗaga musu hannu hakan yasa
suka koma, motarta ta shiga ta tayar ta fice daga gidan cikin sauri.

Khausar na ganin fitar Mahaifiyar tata, ta ɗauki waya ta fara kira, bayan an
ɗaga tace; "Baby dan Allah kiyi sauri ina jiran ki".

Ba'a ɗau lokaci ba sai ga ƙwanƙwasa ƙofa, cikin sauri Khausar ta buɗe mata ƙofa,
suka kalli juna fuska ɗauke da murmushi kafin Khausar ta rungumo yarinyar suka yi
cikin falon.

Hajiya Salma tana fita bata zarce ko'ina ba sai guest house ɗin Alhaji Sa'eed,
kamar koda yaushe a can ta same shi sai dai wannan karon shi kaɗai ta samu babu Brr
Hauwa.

"Kamar yadda muka tsara Alhaji Mustafa ya bar ƙasar nan", cewar Hajiya Salma
kenan lokacin da take ƙoƙarin cire After Dress ɗin dake jikin ta.

Alhaji Sa'eed yayi murmushin mugun ta daga kwancen da yake yace; "kamar yadda
muka tsara komai yana tafiya dai-dai, saƙon mutuwar ɗan shi zata riske shi a can",
Hajiya Salma tayi murmushi tana kwanciya a jikin Alhaji Sa'eed.

******* ***********

*HAYIN RIGASA, KADUNA*.

sai da gari yayi haske sannan Ummi ta miƙe tace da Nusram; "bari na fita
na ɗan zagaya na san ba za'a rasa abin siyarwa nan kusa ba da zaki karya dashi",
Nusram tace; "to", dan har lokacin bata gama dawowa dai-dai ba.

Ummi kuwa ficewa tayi daga asibitin domin neman abinda zasu karya ɗin hannun ta
riƙe da wasu daga cikin kuɗin da bawan Allan da taji an kira da Alhaji Mustafa.

Bata daɗe da fita ba Nusram taji anyi sallama an turo ƙofar, ta ɗago tana me
amsa sallamar, tsayawa tayi tana kallon mutumin, tabbas fuskar shi ce, wannan dai
wanda takewa laƙabi da ɗan yankan kai sai dai wannan ya ɗan manyanta.

Duk ta ruɗe jikinta har rawa yake yi mata, tunanin ta shine kada dai canza kama
yayi yazo domin cin galaba akanta wato ya tafi da ita.

Alhaji Mustafa ya zauna saman kujerar yana satar kallon yarinyar, a ranshi yana
mamakin meye dalilin birkicewar ta lokaci ɗaya.

Sun jima a haka ɗakin shiru babu wanda yayi magana a tsakanin su, Ummi ta shigo
da sallama hannun ta ɗauke da baƙar leda me ɗan girma.

Tana ganin Alhaji Mustafan ta washe baki tana faɗin; "sannu da zuwa Alhaji", ya
shafa kanshi tare da yin murmushi har kumatun shi ya lotsa yace; "sannu da ƙoƙari
ya me jikin".

Kaɗan ya rage Nusram ta suma, lallai ma wannan wato canza kama yayi dan yazo ya
yaudare su kenan?, "tabbas shine wannan", Kallon da suke mata yasa ta gane a fili
tayi maganar.

Ummi tace; "waye kenan?", Nusram kuwa duk yadda gabanta ke faɗuwa be hana tace;
"wato kazo ka yaudare mu ne ko?, shine har da yin shigar dattijai to Allah ya tona
maka asiri", bin ta kawai suke da idanu.

Ganin hakan yasa ta cigaba da cewa; "to ai na gane ka, dan fuskarka bata canza
ba sannan ɗabi'ar ka ma haka", Ummi tazo kusa da ita ta riƙe ta.

"Nusram ki dawo hayyacin ki, wannan fa shine mutumin daya taimake mu jiya ya
kawo mu nan asibitin", Nusram ta kalli Ummi tace; "na sani mana Ummi ai ba yau ya
saba ɗauko ni ba kwanaki ma haka ya kawo ni.har ƙofar gida sai dai ba mutumin
arziƙi bane kamar yadda kike faɗa, wannan da kike gani mugu ne ɗan yankan kai ne".

Tofa! Nan zufa ta fara karyowa Alhaji Mustafa, cikin inda-inda yace; "karya take
yi ni ban taɓa ganin ta ba sai jiya daga taimako", Ummi tace; "ina jin dai bata
hayyacin ta ne bari na kira likita", ta ƙarasa tana ficewa da sauri.

Alhaji Mustafa ya kuma kallon yarinyar, Nusram ta balla mishi harara tace;
"wallahi idan ma wayar ka kake so ka amsa ba zan taɓa baka ba har sai ka bani
ribbom ɗina, me fuska biyu kawai, a wajen bikin da akayi kwana huɗu daya wuce kayi
shigar yarinta amma anan kayi shigar tsofaffi".

Kafin Alhaji Mustafa yace wani abu likita da Ummi sun shigo dan haka yaja bakin
shi yayi shiru, banda zare idanu babu abinda yake yi, likita ya dubata babu abinda
yake damunta amma gudun kada Alhaji Mustafa yace be san aikin shi ba gashi ya san
cewa babban mutum ne yasa yayi mata allurar barci.

"kada ki damu stress ne yayi mata yawa insha Allahu zata dawo dai-dai zuwa
anjima", Ummi ta sauke ajiyar zuciya tace; "to likita angode sosai".

Bayan fitar likitan Alhaji Mustafa yace; "ni zan wuce dama na biyo na duba
yadda jikinta yake ne, ga wasu kuɗin ko zaku nemi wani abin, yanzu zan bar ƙasar ne
gabaki ɗaya Allah ya ƙara mata lafiya", Ummi ta amsa da "ameen", tana kuma me amsar
kuɗin da ya miƙo mata.

"Alhaji a ƙara haƙuri dai, shirme ne irin na mara lafiya", Alhaji Mustafa yace;
"babu komai Allah ya bata lafiya", daga haka ya fice daga ɗakin.

bayan fitar Alhaji Mustafan Ummi ta kira Aunty a waya ta faɗa mata cewa suna
asibiti, Aunty tayi salati tana me faɗin gata nan zuwa yanzu Sulaiman zai kawo ta.

Ummi ta zubawa Nusram idanu lallai Allah kaɗai ya san wahalar da yarinyar nan
tasha, abu kuma harda taɓin ƙwaƙwalwa.

Koda Aunty tazo kamar ta zubar da hawaye dan tausayi bayan Ummi ta gama bata
labarin abinda ya faru, shi kanshi Sulaiman ɗin ya kai matuƙa wajen ɓacin rai.

"ki zauna dai Maman Nusreen wata rana sai kin kashe kanki da kuma yaranki, kada
ki miƙe ki ƙwaci ƴancin ki", faɗar Aunty kenan.

Ummi ta miƙe tace; "ba haka ba Maman Adam haƙuri shine kan gaba kuma shine
gimshiƙin zaman aure, bari naje gida na bar Kubra ita kaɗai babu kowa na san ba
wanda zai kula da ita a gidan", Sulaiman ya miƙe yace; "muje tare Mama sai na rage
miki hanya", tare suka fice yayinda suka bar Aunty a wajen Nusram ɗin.

Alhaji Mustafa kuwa koda ya dangana da motar shi, babu abinda yake sai sauke
ajiyar zuciya, kada dai ace yarinyar nan ta san ainihin abinda yake aikatawa.

Magan-ganun ta babu abinda ya tsinta a ciki sai shirme wai ribbom da waya?
Yaushe kuma akayi hakan?, ya kasa fahimtar inda ta dosa.

Can naga ya saki murmushi har kumatun shi ya lotsa, ya lumshe idanu yana ƙarara
gasgata abinda zuciyar shi ke raya mishi🙄.

Ya girgiza kai yana me yin dariya, a fili yace; "lallai ta haɗu da Murad ne
wajen ɗaurin auren su Alhaji Baballe".

Ya sauke ajiyar zuciya kafin yace; " *ABDUS-SAMAD ƊANA GUDA ƊAYA TILO, YAUSHE
ZAKA DAWO GARE NI NE?*.

#LIKE
#SHARE
#COMMENT

*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*


♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖41-42📖📖

Kwanan Nusram biyu a asibiti sannan aka sallameta, zuwa lokacin kuwa ta sami
sauƙi sosai sai dai har lokacin gefen cikin ya kan mata ciwo lokaci zuwa lokaci,
likitan kuwa yace kada ta damu zai dena a hankali.

Babu wanda yazo daga gida dan ya dubata, dama kuma bata saka rai ba, Aunty ce
dama ita kullum sai tazo.

Babu yadda Ummi bata yi ba akan Nusram din ta bari Yaya Sulaiman yazo sai ya
kaisu gida taƙi yarda, domin ita asibitin ya ishe ta dole hakan nan Ummi ta tattara
musu kayan su, suka taho.

Me Keke Napep suka ɗauka shata har ƙofar gida, abin ban haushi suna dawowa
maƙwabta suka fara leƙe, ita dama Nusram Kubra ta ɗauka suka shige gida.
Tana jiyo yadda mutane ke ƙananan magan-ganu suna dariya, wasu harda yiwa Ummi
ya mai jiki, ta ɗauka da zuciya ɗaya ne ko kuwa ta sani ita dai Nusram taji ta amsa
daga nan kuma ta shige bata ƙara jiyo su ba.

Ameera na zaune tayi sallama amma ko ɗago kai bata yi ta kalle ta ba, Mama
Jummai dake bayi tayi wuf ta fito, ta kalli Nusram ta riƙe haɓa tace; "eh lallai
Abdullahi yayi gaskiya ciki ne fa aka zubar gashi nan tayi haske kamar me jego".

Nusram ta bita da kallo kawai, Ummi na zuwa ta ja hannunta, ta kaita ƙofar


ɗaki sannan ta buɗe mata ƙofar tace; "shiga ciki", Nusram tabi umarnin Mahaifiyar
ta.

Kubra ta ajiye saman kujera sannan ta fara kakkabe ɗakin kafin ta ɗauko
tsintsiya ta hau shara, Ummi kuwa ruwa ta ɗora saman murhu don suyi wanka.

Yana yi zafi Nusram ta juye ta fara yi ta sawa Ummi wani, ta fito daga wankan
kenan Isa ya shigo, bata ko kalli inda yake ba.

Ya matso kusa da ita yace; "ya jiki?", ba tare da ta kalle shi ba tace; "da
sauƙi", yace; "Allah ya ƙara lafiya ya kawo me amfani", bata amsa ba sai dai cigaba
da tayi da abinda take yi wato shanya Soson wankanta a sama.

Ya kuma cewa; "Nusram ni duk abinda kika yi a hakan ina sonki, kada ki damu
tunda dai an zubar da cikin kawai ki amince muyi auren mu", ta ɗan juyo ta kalle
shi kan ta juya tayi tafiyar ta.

Isa cikin takaici ya bita da kallo, wato abinda ya faru da ita har shine take
da damar jan aji ko?, ya yi murmushi mugunta yace; "zan riƙe ki ne a hannu na",
shima ya juya ya fice.

A hankali komai ke tafiya haka ranaku ke kwaranyewa kamar ƙiftawar idanu, yau
dai bikin Nusreen keda wata ɗaya yayin da bikin Atika yake da wata ɗaya babu kwana
ɗaya.

Idan kaga Nusram a lokacin ta dawo yadda take babu wani abu dake damun ta, bata
dai fita ko'ina saboda Baba ya hanata kai koda ace ma be hanata ba zata iya fita ba
saboda tsegumin ƴan unguwa.

Bayan sunci abincin dare Nusram ta shafe Kubra da ruwan Addu'a sannan ta kwantar
da ita, daga waje ta fara jiyo muryar Baba yana faman ƙwala mata kira.

Cikin hanzari ta ɗauki hijab ta saka sannan ta fito, yana tsaye a ƙofar ɗakin
shi ya kalle ta sannan yace; "kira mini uwarki", sai da ta ɗan yi jim tukunna ta
juya zuwa ɗakin nasu.

A zaune ta tarar da Ummi da alamu taji abinda Baba ya faɗa dan tana zuwa ta
miƙe tace; "muje", Nusram ta juya kawai suka kuma ficewa.

Da sallama suka shiga ɗakin, Baba na zaune gefen shi kuma Isa ne sai Mama
Jummai itama tana zaune a wajen.

Baba yace; "kin dai san kowa ya san meke faruwa a rayuwar ku ko, kuma tarbiya
daidai gwargwado na baku amma da yake ance duk wanda ya hau motar kwaɗayi zai sauka
a tashar wulaƙanci, gashi dai abinda kika gani ko ince kike kan gani".

"babu irin abinda bana yi muku a gidan nan babu rashin ci🙄 Babu rashin sha,
amma kuka zama karuwan cikin gida kuma a gida na wannan ya ɗauka wannan ya ajiye na
yanke shawara ta ƙarshe shine aurar daku, Alhaji Baballe yazo da Allah na haɗa shi
ya amince zai aure ki ya rufa mana asiri, kowa ya sani babban mutum ne a Nigeria
gabaki ɗaya, amma kika ɗebi ƙasa kika watsa mini a idanu abin ban haushi a daren da
aka kaiki gidan mijin ki Nusram kwarto aka kamaki dashi, ya ɗirka miki ciki kuka je
zubarwa yazo da matsala shine kuka kwana biyu a asibiti, ina faɗa miki wa'innan
magan-ganun ne dan ki san cewa na san duk abinda kike aikatawa, Nusram Allah yayi
miki baƙin jini ko kare be taɓa zuwa ƙofar gidan nan da sunan yana son ki ba, ga
Ameera nan ƙanwarki ce amma ta fiki yawan samari, na kuma ƙoƙarta domin sauke
nauyin da Allah ya ɗora mini naku amma kika aikata yadda kike so saboda ban isaba,
Nusram ba zan yi miki baki ba amma kije yadda kika baƙanta mini kema zaki gani".

Izuwa yanzu kukan Nusram ya fara tsananta, jin abinda Mahaifin nata yace yasa
ta ɗagowa tana girgiza kai, cikin kuka tace; "Baba kayi haƙuri kada kayi mini baki
wallahi bana da masaniya akan duk abinda kake magana akai".

Baba yace; "ayya Nusram rayuwace fa gaki ga tanan, ni dai Allah ya gani nayi
iya ƙoƙarina a kanki na ganin na sauke haƙƙin dake kanku, sannan magana ta biyu
shine ɗazu ɗan uwanki Isa yazo mini da wani batu, yace shi ya yadda a duk yadda
kike zai aure ki dan haka na saka ranar bikin ku nan da wata biyu".

Ummi ta miƙe tace; "a matsayina na Mahaifiyar Nusram ban amince ba, maganar da
kake yi duka naji kuma bazan amince ba, kana magana akan haƙƙin yara daka sauke kai
bakaji kunyar kanka ba, wanne haƙƙi nasu ka sauke ci ko shayarwa ko kuwa tufatarwa?
Wallahi matuƙar ina numfashi ba zan taɓa bari ƴata ta auri wanda beda asali ba".

Duka ɗakin tsit yayi, abin mamaki yau Ummi da kanta take maida martani akan
abinda ake mata a gidan, Mama Jummai ta kalli Baba ganin ba zai yi magana ba yasa
tace; "au Abdullahi kana ji dan za'a rufawa ƴarta asiri shine take cewa bata amince
ba wai har karuwa tana da damar da zata zaɓi miji".

Ummi ta kalli Mama Jummai tace; "me zai hana kuwa tunda har ɗan shege ma ya sami
damar zaɓar mata ai ina ganin ba laifi bane dan karuwa ta zaɓi nata, da kike wannan
maganar naga ke har sheda kike dashi gashi nan a gabanki, kuma kike tare mishi faɗa
to wallahi babu wanda ya isa ya kuma takani ko ƴata a gidan nan".

Mama Jummai tace; "haka kika ce? To shima ya fasa auren nata", Ummi tace;
"wannan kuma matsalarku ce", ta kama hannun Nusram zasu fice Baba ya dakatar dasu.

"dawo ki zauna kun gama naku nima yanzu zanyi nawa", Ummi ta dawo kamar yadda ya
umarta ta xauna.

"na riga na gama magana aure tsakanin Isa da Nusram babu fashi, tunda ita bata
da wanda zai aure ta", Nusram ta girgiza kai tace; "Baba kayi haƙuri ni bana son
Isa dan Allah ka nemo wani amma ba Isa ba".

Baba yace; "to shikenan tunda baki son Isa sai ki kawo wanda kike so na baki nan
da sati biyu idan baki kawo wanda kike so ba zan aura miki Isa nan da sati uku".

Ummi tace; "ko bata kawo wanda take so ba, ba zan bari ta auri Isa ba", Baba
yace; "to idan kuwa har sati biyu ya cika bata kawo wanda take so ki tattara
kayanki ki tafi Dabai".

Cikin dakewa Ummi tace; "na yarda zan tafi amma ka sani ko bayan bana nan ka
aurar da Nusram wa Isa ba zan yafe ba", Baba ya juya ya kalli Nusram yace; "to
auren Mahaifiyar ki a hannun ki yake idan kin so kada ki kawo wanda kike so", ya
miƙe ya fice.

Isa cikin takaici ya miƙe yace; "ni na tabbata baki da wanda kike so, nine kika
tsana kuma ki sani aure na dake babu fashi, ƙarin gargaɗi shine matuƙar kika shigo
hannu na to wallahi sai na illata ki, ki sani sai ka fanshe duk wani wulaƙancin da
kika yi mini".

Ummi ta riƙo hannun Nusram tace; "ta Allah ba taka ba", daga haka taja hannun
Nusram suka fice.

Mama Jummai tana huci tace; "wallahi sai na wulaƙanta Maimuna da zuri'ar ta,
gobe dole mu koma wajen Malam", Isa ya ciza yatsa sannan ya fice.

Baba ya tsaya a waje yana mamakin yau yadda Maimuna ta iya maida mishi da
martani kuma a yadda ya sani tsaf zata iya rabuwa dashi, gashi suɓutar baki yasa
shi yin katoɓara.

Shi kuwa ya zaiyi da rayuwar shi🙆 Allah yasa dai Nusram ta sami miji kan
lokacin, idan ba haka ba to be san ya zai yi ba dan be shirya rabuwa da matar shi
wacce itace rufin asirin shi ba.

Ummi kuwa koda suka koma ɗaki bata nuna wata damuwa ba, sai ma sakayau da take
jin ranta da zuciyar ta tayi ashe haka mutum yake ji idan har ya maida martani na
wani abu da ake mishi lallai ƴanci yana da daɗi.

Ta kalli Nusram wacce ta zuba mata idanu cike da fargaba, tayi mata murmushi
tace; "ki kwanta mana kada wani abu ya dame ki", Nusram jiki har rawa yake yi wajen
cika umarnin Mahaifiyar ta.

Ummi ma sallah tayi sannan ta kwanta, babu ko ɗar a cikin zuciyar ta, tabbatar ko
yanzu ta koma Dabai bata da wata matsala domin kuwa tana da gatanta.

Nusram tayi shiru dama gashi dare ya tsala sosai, tunani ta faɗa na neman
mafitar abinda ya tinkaro ta, yanzu ita a ina zata sami mijin aure🙆.

Ba zata taɓa yadda ta zama sanadin rabuwar iyayen ta ba, kai bama ita ba ta san
Nusreen da Kubra ba zasu yafe mata ba idan ta zama silar gutsirewar auren nasu
musamman Kubra wacce take halin buƙatar iyayen nata, gata dai a kwance shekara
shida tana kwance babu ƙafa sai dai zama.

Ta tashi ta zauna tare da zuba uban tagumi yanzu ina zata saka ranta?, bata da
mataimaki sai Allah kullum da abinda ke tinkarota.

"ina da ɓuƙatar ganin Nusreen dole, muyi magana da ita", to wacce waya kike
dashi? Wayar ta tun ranar da aka kaita gidan Alhaji Baballe bata kuma sanin inda
take ba.

Zumbur naga ta miƙe, wata jaka dake rataye ta fara zazzagewa cikin sa'a kuwa ta
gano wayar data ajiye tun ranar bikin nasu.

Kamar wacce ke tsoron taɓawa ta ɗauko, addu'arta ɗaya Allah yasa babu password,
tana dannawa hoton shi ya bayyana.

Kyakkyawan saurayi, me zubin fulani, jersey a jikin shi blue da ratsin fari,
gashin kanshi a kwance ya jingina da kujerar da yake zaune idanun shi ya ɗan ƙara
ware su da alama wani abu ya gani ko kuma style ne na ɗaukar hoto bata sani ba,
murmushi ke kwance saman fuskar shi har sai da ƙananan haƙoranshi farare tas suka
bayyan.

Ta kai hannu daidai kumatunshi daya lotsa ta shafa, bata san ta shagala da
kallon shi ba, itama dai murmushin take yi kawai, tama manta da wata matsala dake
gaban ta.

*********⬇️⬇️⬇️********
*UNGUWAR SARKI, KADUNA*.

Ya ƙara kallon agogon dake hannun shi sannan yayi tsaki, suna tsaye suna magana,
ya kalli Sumayya sannan yace; "ba zaki wuce ki shiga ba", Sumayya ta zunɓuri baki
kafin ta buɗe motar ta shiga.

Ya ƙara kai kallon shi gare su sannan ya taɓe fuska kamar yana gaban first love
ɗin shi, ya shiga motar sannan ya danna musu horn.

Brr Farida ta kalli Fadila tayi murmushi tace; "kije idan ba haka ba wancan ɗan
ujilar zai.iya tafiya ya barki, ku tabbatar kun zaɓo kayan daya dace ki kuma saki
jiki ki zaɓi abinda kike so kinji, dalilin na san zaki fi sakewa yasa nace kuje
tare da Baby dan na san sai kunfi jin daɗin siyayyar jeki ƴata Allah yayi muku
albarka".

Fadila ta juya cike da kunya, Brr Farida ta bita da kallo tana murmushi a baya
bata wani son auren amma yadda yarinyar ta natsu yasa taji auren ya kwanta mata a
rai.

Koda ta shiga motar sai da Abdus-samad ya harare ta sannan yaja motar suka fice
yayin da masu tsaron lafiya suka biyo bayan su.

Suna tafiya kowa ya natsu babu wanda yayi magana, Fadila tace; "wai yaushe zaka
je wajen Malama ne?", yace; "kina son komawa gidane", ta ɗaga kai.

Suka kalli juna shida Sumayya sannan suka yi murmushi, yace; "yarinya ai kinzo
kenan", Fadila ta ɓata fuska, su kuwa suka sami damar tsokanarta har suka ƙarasa
Mall ɗin.

Yana gaba suna binshi a baya har ciki, kowacce taja kwando yace; "Sumayya an
sami abinda ake so ko?", tace; "Yaya Abdul ai dai ba'a kuɗin ka bane".

"duk Daddy ne ya ja mini da ya barni na fara aiki na ai da babu yarinyar da zata


raina ni", suka tafi suna mishi dariya.

Kiran wayar shi yasa ya ɗan matsa baya domin amsa kiran, "Aunty na barka da
warhaka", ta ɗan ja numfashi kan tace; "idan kace mini Aunty sai naji wani iri".

Yayi murmushi yace; "dole na baki girmanki Saleema", ta ɗanyi jim kan tace; "kai
baka iya kiran mutum ba sai dai a kira ka ko?", ya ɗan shafa gashin kanshi yace;
"afuwan zan dage na koya yanzu lafiya kuwa".

"ina zaune naji ba zan iya haƙuri ba sai na kira ka, zuciya ta ke bani kamar
wani abu ya same ka shine na kira naji ko lafiya?", Abdul yabi inda yake da kallo
yace; "lafiya ta lau yanzu ma ina Kareem Shopping Mall na kawo Sumayya da Fadila
siyayya".

Tayi murmushi tace; "hmm da ace ban gaji ba da nazo sai na taya ka fira, sannan
ka faɗa musu kada su sake su wahalar mini da kai, ka kula da kanka".

"an gama ranki shi daɗe, na kuma gode da kulawar ki, kema ki kula", daga haka ya
kashe wayar.

Idanun shi ya sauka a kan ribbom ɗin da suke jere a saman canter, yabi su ɗaya
bayan ɗaya da kallo har yazo kan wani ya tsayar da idanun shi a kai, ya jima yana
kallon shi sak kalar na Nusram wanda ya amsa a wajen ta kalar golden.

Hairat ta kalli Khausar tace; "kinga me na gani kuwa?", Khausar tace; "na gani
mana", Hairat ta runtse idanu tace; "damn Sexy, gaskiya gayen ya haɗu dole na shawo
kanshi" ta faɗa tana ƙoƙarin zuwa gare shi.

Khausar tayi saurin janyo ta baya tace; "wannan ai yafi ƙarfin ki Baby sai dai
ni, amma abinda yake bani mamaki yana kama da Daddy na", Hiarat ta ƙaro zaro idanu
tace; "tabbas hakane".

Khausar taja hannun Hairat tace; "zo muje dole na shawo kan wannan gayen", suna
isa kusa dashi Khausar ta kai hannu ta kwaso Ribboms guda biyu ta ƙaraso gaban shi
hannunta janye dana Hairat.

"amm pls dan Allah duba mana wanne kala yafi kyau", ya juyo ya kalle su, nan fa
ƙafar Khausar ta fara rawa ji tayi kamar shi kaɗai ne a cikin Mall ɗin gaba ɗaya ya
cika wajen.

Abdul ya kalle su sama da ƙasa, Khausar riga da wando ne a jikin ta daga


ƙugunta belt ta saka ta ɗaure shi, sai Hairat data saka pencil skirt baki da kuma
riga fara, babu ko mayafi a jikin su.

"kina da magana ne?", ya faɗa yana ƙara buɗe idanun shi a kansu, Khausar tace;
"am dama......dama........dam......dama.......nac......nace......ko zaka
duba.........ko zaka duba mana wanne yafi kyau".

Ya ɗan taɓe baki sannan yace; "banda sani akan kayan mata", da sauri Khausar
taja hannun Hairat tace; "shikenan muje na gode", sai lokacin Hairat ta sami damar
haɗiye miyau ɗin dake bakin ta.

Har suna harɗewa wajen fita, basu ɗauki komai ba dan haka basu tsaya wajen
cashier ba.

Abdul ya bisu da harara, kamar ance ya kalli ƙasa yaga ƴar ƙaramar purse ɗin
Khausar a ƙasa wato tsabar ruɗewa harta yarda abinda ke hannun ta.

Yana tsugunawa ya ɗauka Fadila da Sumayya suka ƙaraso, dan haka hanyar waje
kawai ya nufa, babu bata lokaci aka lissafa kayan ya miƙa Atm ɗin shi aka cira
sannan suka fice inda kuma za'a saka a kai musu kayan su mota.

Koda suka fito ya bi wajen da kallo, can ya hango su, da alamu jakar suke nema
dan buɗe motar su, ya kalli Sumayya yace; "amshi makullin nan, ki buɗe ku shiga ku
zauna ina zuwa" ya ƙarasa yana juyawa ya tafi.

Hajiya Salma ta kalli Alhaji Sa'eed suka yi murmushi, wato tun zuwan Abdul suke
wajen kuma duk suna kallon shigar shi da fitosar shi.

"yanzu ne lokacin daya kamata mu aiwatar da nufin mu", faɗar Alhaji Sa'eed kenan
yayin da yake danna wayar shi, motar yaran shi dake gaba.

Yana ɗagawa yace; "Scorpion ka aikashi lahira kawai", Scorpion yace; "an gama
ranka shi daɗe yanzu lahira zata yi baƙo", ya ajiye wayar sannan ya zaro pistol
daka aljihun motar shi ya saita ƙirjin Abdul wande ke nufar motar su Khausar ɗin
dan bata jakar ta, kasancewar motar su Khausar ɗin tana gaban ta scorpion ɗin, babu
ɓata lokaci ya harbi Abdus-samad ɗin.

#LIKE
#SHARE
#COMMENT
*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

*brr zahra Allah ya ji kanshi yasa Aljanna ce makoma ubangiji ya yafe mishi
kurakuren shi*.

Godiya ga ƙungiya ta guda ɗaya tamkar da dubu ko ince miliyan, *GOLDEN PEN WRITTERS
ASSOCIATION*, musamman jajurtattun cikin ta *UMAR ƊALHAT da kuma *SHAMSIYYA
IBRAHEEM ƊAN MUSA*.

*JINJINA GARE KU*

*Auntyna Amina Alhassan (Oum deedat)*


*Auntyna Ummee Yusuf(oum yusuf)*
*Sumayya Abdullahi Babayo(Sumiee B)*.
*Faridaty(Ƙafar yawo)*
*Harira Aliyu(ƴar fillo)*
*Ummeeteey Yusuf*
*Fatima Batula(Bloody)*
*Maryam Shahada*
*Maryam ankudi*
*Shatu*

Da duk sauran da ban ambata ba, Allah ya ƙara haɗa kanmu ya tsare mu daga sharrin
mahassada.

📖📖43-44📖📖

Cikin tashin hankali da kiɗima Sumayya da Fadila suka yi ƙasa da kai jin karar
harbi, Abdul kuwa hannu yasa ya taro Khausar dake ƙoƙarin zubewa bayan ta ƙwala
wani irin ihu na azaba da raɗaɗi.

Hajiya Salma ta zaro idanu ganin wacce aka samu, cikin sauri ta buɗe motar ta
fito ta nufi inda suke, kan wani lokaci wajen ya hargitse, ganin hakan yasa su
Scorpion jan motar su suka gudu.

Da taimakon Securities na wajen aka saka Khausar cikin mota, sannan suka rankaya
asibiti, wayar Saleema ya kira yana tambayar ta tana asibiti.

"meya faru ne? Wani abu ne ya same ku?, bana asibitin amma bari na taho yanzu",
ta faɗa duk ta gama rikicewa, Abdul kuwa ajiye wayar yayi ya dafe kanshi.

Suna isa asibitin aka amshe ta, sai da suka yi rubuce-rubuce kafin aka fara
dubata, ta zubar da jini da yawa dan ma bullet ɗin a kafaɗa ya same ta.

Hajiya Salma zuwa lokacin hawaye kawai take yi tana ihu ganin zata rasa ƴar
ta, Alhaji Sa'eed ke lallashin ta, Sumayya da Fadila ma kuka suke yi dan basu taɓa
ganin tashin hankali irin wannan ba.

Kasancewar da sanayya sai a lokacin Police suka iso, Abdul ko magana ya kasa
yi ranshi a ɓace yake ya rasa menene dalilin da yasa ake kai ƙoƙarin kashe shi.

Sun ɗauki report sannan suka ce zasu dawo zuwa lokacin da Khausar ɗin ta
farka, Dr Saleema ta fito daga ɗakin ta dube su tace; "ta rasa jini da yawa dan
haka dole sai an ƙara mata leda biyu".

Hajiya Salma ta ɗora hannu akai tace; "na shiga uku ƴata zata mutu ta barni
garin son zuciy.....", Alhaji Sa'eed be bari ta ƙarasa ba yayi saurin cewa; "haba
Hajiya Salma kada kije kiyi saɓo mana".

Abdul dai kallon su kawai yake yi amma a yadda alama ta nuna wannan ce
mahaifiyar yarinyar, yace; "kiyi haƙuri insha Allahu komai zai koma dai-dai, yanzu
zan je sai a ɗebi nawa a sa mata", Dr Saleema tace; "Abdul........".

Ya riƙe hannun ta yace; " muje kawai Aunty", bata da yadda zata yi dole suka
tafi Lab ɗin tare, ita dai Salma ba'a son ranta ya bada jinin shi ba.
"yanzu Abdul sai ka bawa stranger jinin ka wacce ma baka santa ba?", Abdul yayi
murmushi yace; "kada ki ce mini imanin ki ya gaza a nan mana, haba ina kallon ki a
matsayin me tausayi, muje a saka mata", Saleema tayi ajiyar zuciya tace; "ka koma
ka kwanta bari naje a saka mata".

tana fita ya lumshe idanu yana tunani, su waye wai ke son ganin bayan shi ne?,
ya san Mahaifiyar shi ta san wani abu daya danganci hakan amma kuma ba zata faɗa
mishi ba.

Dr Saleema tana zuwa ta same su a tsaye harda Brr Hauwa, Brr Hauwa kuwa ganin
ta sai da ta ɗan tsorata ita kuwa Dr Saleema duk da yadda zuciyar ta ke mata
kokwanto amma sai ta kauda kai kawai ta shige.

Shi kanshi Abdul lokacin da ya fito sai da abin ya bashi mamaki, amma bece mata
komai ba, ita kuwa Brr Hauwa nunawa take ai Alhaji Sa'eed ɗin ita ce lauyar shi.

Sai da komai ya dai-daita sannan Abdul yace da Fadila da Sumayya su tashi su


tafi, har wajen Hajiya Salma yaje yace; "kiyi haƙuri insha Allahu zata sami sauƙi".

Cikin ƙufula tace; "wallahi idan yarinya ta, ta mutu sai nayi shari'a da kai, an
kawo maka hari amma yanzu ƴata ce a cikin wahala", har ya fara tafiya yaja ya tsaya
ya juyo yana kallonta.

Alhaji Sa'eed da Brr Hauwa kuwa fuskar su ƙarara ta nuna rashin gaskiya, bece
komai ba ya juya ya tafi, ita kanta Dr Saleema tayi mamaki sosai, cikin sauri ta
biyo bayan su.

"dama kai aka kawowa harin?", yaji saukar tambayar, ya juyo yace; "eh amma ai
babu komai ya riga da ya wuce", dr Saleema tace; "Allah ya kyauta gaba", suka amsa
da Ameen.

Ko a mota yana jin Fadila tana tambayar Sumayya wai dama shi aka kawowa hari,
itama Sumayyar tace; "wallahi ban sani ba banda yanzu da tayi maganar".

shi dai bece komai ba har suka isa gida, Brr Farida dake zaman jiran su ta taso
da sauri, "har kun dawo?".

"eh", abinda ya faɗa kenan ya wuce part ɗin shi, Brr Farida ta bishi da kallo
kafin ta juyo ta kalli Sumayya tace; "meya faru", Sumayya ta bata labarin duk
abinda ya faru.

Hankalin Brr Farida ya tashi sosai, " ku shiga ciki ina zuwa", nan suka wuce
suka shiga falo ita kuma tayi hanyar part ɗin Abdul.

Ya shiga bayi wanka ta fito dan haka ta samu waje ta zauna tana jiran fitowar
shi, koda ya fito da sauri ta miƙe taje wajen shi ta riƙo hannun shi tace; "Baby
meya faru a wajen siyayyar".

Yace; "babu komai", ya fara goge sumar kanshi, Brr Farida ta kuma cewa; "amma
Sumayya tace an kai maka attack", be juyo ba ya cigaba da abinda yake yi.

"Abdul magana nake maka fa", ya juyo hannun shi riƙe da Comb yace; "First Love me
kike so kuma nace miki, sun baki labarin abinda ya faru ai".

Brr Farida tace; "shikenan, Allah ya kiyaye gaba", ta fice daga ɗakin, da kallo
Abdul ɗin ya bita tana fita yayi wurgi da comb ɗin hannun shi.

Kanshi ya dafe da hannu ɗaya yace; "tabbas akwai abinda kike ɓoye mini, menene
wannan?".

Be fita ba har akayi kiran sallar la'asar sannan ne ya yi Alwala ya wuce


masallaci, be dawo gidan ba sai dare.

Ganin dare yayi kawai sai ya wuce part ɗin shi, Brr Farida tana hango shigowar
shi tayi ajiyar zuciya sannan ta juya ta wuce ɗakin mijin ta.

"yanzu hankalin ki ya kwanta ko, tunda ya dawo", ya faɗa, tayi murmushi tana
ɗaga kai, "sai dai ya fara zargi na a al'amuran shi", Dr Abubakar ya riƙo hannun ta
yace; "ki kwantar da hankalin ki, na san Abdul ba zai taɓa ganin laifin ki ba koda
ace ya san tarihin shi gaba ɗaya dan haka ki kwanta kiyi barci, gobe zan fara
shirye-shirye dan ina so ya fara aiki a watan nan", Brr Farida cikin tsoro tace;
"kada kayi haka dan Allah ka bari ba yanzu ba".

"dole ne Abdus-samad ya fara aiki, kin san dai ba zai zauna a haka ba ko,
Tameer da Sameer duka aiki suke yi, ga Surayya itama sannan rashin fara aikin shi
hakan zai janyo cece kuce a cikin family", Brr Farida ta kau da kai kawai.

Bata kuma cewa komai ba ta kwanta, haka shima Dr Abubakar ɗin kowa da abinda
yake tunani.

******** ********

"yanzu irin abinda kika fuskanta kenan, Ram amma shine babu wanda ya faɗa mini",
Nusreen ta faɗa cikin kuka bayan Nusram ta gama bata labarin abinda ya faru.

Nusram ta dafata tace; "ya isa haka, ki share hawayen ki, dani da Atika duka
ɗaya ne, ni yanzu abinda yafi damu na shine yadda zan sami miji cikin sati biyu,
Rimluv bana so ta dalilina auren shekara talatin ya warware", Nusram ta ƙarasa
cikin damuwa.

Nusreen kuwa cikin fushi tace; "ya lalace mana, me auren ya tsinana mana, ko
kuma ita Ummin me Baban yake tsinana mata, nifa dama can na gaji".

"amma ban taɓa sanin baki da hankali ba sai yau, mu kuwa auren yayi mana wani
abu domin ya bamu sunan uba, martaba da daraja wacce sai wanda aka haifa ta hanyar
aure yake da ita, idan banda abin ki ko Isa ma ai sheda ne a wajen ki, sannan Ummi
da kike maganar ita ai ko babu komai tana da daraja da matsayi wacce budurwa ko
bazawara bata da shi dan haka ki dawo cikin hayyacin ki bana so na kuma jin kinyi
wannan maganar".

Nusreen ta zumɓuro baki tace; "ai ke dama ba'a yi miki abin arziƙi, daga magana
sai kiyo kan mutum da wa'azi", Nusram ta ɗauki jakar ta tace; "kinga tafiya ta
tunda ba zaki tsaya ki saurare ni ba".

Da sauri Nusreen ta janyo ta tace; "haba rabin jikina, dawo ki zauna wannan
shine zuwan ki na farko gidan nan yaushe zaki zo kuma kice zaki tafi haka".

babu yadda ta iya haka ta zauna, sun yi fira sosai duk da rabin firar dai ta
ƴan gidan su ce daga nan kuma suka yi kitchen inda suka dora abinci.

"bari dai naga meye a jakar nan da kike ta yawo dashi", Nusreen ta kai hannu ta
ɗauke jakar Nusram tana dariya.

Nusram tace; "ban son bincike dan Allah ki bani kayata", tana buɗewa ta zaro
wayar cikin mamaki take bin Nusram ɗin da kallo.

Nusram ta kauda kai, ita har ta manta da wayar ma a ciki, "wannan fa daga ina?",
Nusreen ta jefo mata tambayar.

Nusram ta taɓe baki tace; "ina tahowa ne wani a bayan me mashin ta faɗo daga
jikin shi, nayi mishi magana amma be ji ba shine na ajiye da fatan anjima ya kira".

Nusreen ta girgiza kai tace; "me wannan wayar ya wuce me hawa mashin, ki faɗa
mini gaskiya", Nusram tace; "ƙaryata ni zaki yi kenan?".

tayi dariya tace; "ba haka bane, Allah yasa ya kira da wuri", Nusram ta amsa da
Ameen, nan suka wuni tare har gaishe da Hajiya tare suka je, nan Nusram taga
tsantsar ƙauna.

Data tashi tafiya haka Hajiya ta haɗo mata kayan kwalliya da kuma atamfa Nusram
tayi godiya, Haijya cike da sha'awarta tace; "kada ki damu ƴata, ki ɗauke ni kamar
mahaifiyar ki", Nusram tayi murmushi tace; "to Hajiya".

Har bakin get Nusreen ta raka Nusram ɗin, "to.ki gaida Ummi da Kubra, wallahi
sai nake ji kamar na bi ki mu tafi", Nusram ta dalla mata harara.

"ina ji nan da one week zanje gidan Yaya Sulaiman shima naga wace wainar yake
toyawa", Nusreen ta kwashe da dariya.

Haka suka rabu cike da farin ciki, ta jima a bakin titi tana jiran abin hawa sai
dai yanayin unguwar da kuma yadda yamma ta fara yi yasa gaba ɗaya hanyar take
shiru.

Nusram ta danna wayar dake ƙanƙame a hannun ta, ƙarfe shida da minti ashirin,
nan da lokaci kaɗan za'a fara kiraye-kirayen sallar magrib, a hankali ta fara
takawa hannun ta riƙe da kayan da Hajiya ta bata ɗayan kuma riƙe da wayar sai ƙara
ƙanƙamewa take yi.

Abin haushi har aka kira sallah Nusram bata sami abin hawa ba, gashi gari ya
fara duhu nan fa ta ƙara sauri dan bata so wani abu ya same ta kan hanyar.

Ɗaya ya kalli sauran biyun dake zaune yace; "gafa wata kaya nan tana tahowa",
ɗayan ya bita da kallo, ya lashe baki yace; "gaskiya Baaba yarinyar ta gama
haɗuwa", ɗayan yace; "ai ni nama kasa cewa komai kace yau akwai sharholiya", suka
fashe da dariya.

Nusram da taji ƙarshen maganar tasu ta ƙara ƙanƙame kayan hannun ta, tana me
ƙara yin sauri, a baya suka biyo ta suna faɗin; "ƴan mata sai ina?", bata kula su
ta ƙara sauri.

Ganin sun kusa cin mata yasa ta fara gudu, suma kuwa suka rufa mata baya, gudun
su da nata ba ɗaya bane dan haka suka cimmata.

"dan Allah ku ƙyaleni na tafi", suka sheƙe da dariya, daya yace; "bari na
tambaye ki, kina jin tsananin yunwa da ƙishirwa sai kawai kiga abinci lafiyayye da
ruwa me sanyi zaki ci ko zaki bar shi?", ta girgiza kai hawaye na zubo mata tace;
"dan Allah kada ku cutar dani".

Ɗaya ya saka hannu ya finciko ta, ta faɗi ƙasa, Nusram ta saki ihu suka kwashe
da dariya, kayan ɗaya ya kalla ya tsuguna ya ɗauka yace; "kai Baaba harda abin
arziƙi take tafe dashi, amsa mun sami na zuwa canje wajen sholay gobe ya bamu
kaya", ɗayan kuwa ya ɗauki ledar kayan.

Nusram ta miƙe tsaye tace; "dan Allah ku barni na tafi to", Babu fa inda zaki
je sai mun kwashi namu rabon malama", ya ƙarasa ya yaga hijab ɗin dake jikinta.
Tasa hannu ta kare ƙirjinta, tana fashewa da kuka, ɗayan ya kalle ta yayi
dariya yace; "lallai nifa na lura Abba yawanci masu saka wannan abin sunfi kaya wai
ya hakane, kenan rowa kuke yi mana ko", ta girgiza kai.

Wanda aka kira da Abban ya kalli wayar dake hannun ta yace; "kai yasin babbar
karuwace kalli wayar dake hannun ta", jin hakan yasa ta ƙara ƙanƙame wayar.

"ke bamu wayar nan", Nusram ta matsa baya tana girgiza kai tace; "dan Allah ku
ƙyale ni haka na tafi ba tawa bace", ganin zata ɓata musu lokaci yasa ɗayan yayi
kanta dan ƙwatar wayar ita kuma ta hana, yana ƙoƙarin karɓa tana karewa ya saka
hannu ya murɗeta.

Be kai ga amsar wayar ba, mota taja ta tsaya, duka suka bi motar da kallo, na
ciki be fito ba haka be tafi ba, ganin sun shagala da kallon motar yasa ta hankaɗe
wanda ya riƙe ta, ta koma kusa da motar ta tsaya.

Fin minti biyar Abdus-samad ya bin su da kallo, yana kuma kallon yadda suke
ƙoƙarin wulaƙanta mace duk da be san wacece ba, ganin yadda yake ƙoƙarin riƙe
yarinyar ne yasa ya ƙaraso gaban su.

Sai dai zuwan shi ya fahimci wacece hakan ya kuma fusata shi, a hankali ya
ɓalle murfin ƙofar ya fito, kallon kallo suka yi da juna, cikin mamaki da firgici
suka juya a guje suka bar wajen.

Ganin hakan yasa ya juyo ba tare da ya bisu ba ya kalle ta, tana tsugune a
wajen tana kuka, ya ɗan ja tsaki cike da jin haushi kan yace; "dallah Malama tashi
ki shiga mota".

Ta ɗago fuskarta a firgice sai dai ganin ko waye ya ƙara firgitata, jikin ta ya
hau rawa, hakan da tayi ya tuna mishi da tsoron shi take ji fa dan haka ya jingina
da motar yana kallonta.

Bata bar kukan ba kuma bata tashin ba, "zan fa tafi na barki kuma idan na barki
a wajen nan ba mutum uku ba har mutum shida zasu iya kawo miki hari", jin hakan
yasa ta miƙe da sauri tana waige-waige.

Ya buɗe gaban motar, ta tsaya tana tunanin ta shiga ko karta shiga, shi dai
kallon ta kawai yake yi yana murmushi dan yanzu abin nata nishaɗin yake saka shi.

Ita kuwa tsakani da Allah take tsoron shi, dan bata mishi kallon mutumin arziƙi
sai canza kama yake yi mata, bata kai ga ƙarasa tunanin ta ba taga ya nufo inda
take, cikin sauri ta juya zata gudu, taku ɗaya ya ƙara ya cafko ta.

Janta yayi, faɗi take; "dan Allah ka ƙyale ni na tafi wallahi ina da ƙanwa da
mama, kada ka cutar dani nima ba'a son raina ranar nan na faɗa maka magan-ganun nan
ba", be saurare ta ba sai da ya tura ta cikin motar sannan ya maida ƙofar ya rufe
kafin ya zagaya ya shiga ya tada motar suka fara tafiya.

Nusram gabanta banda faɗuwa babu abinda yake yi, gani take kawai ɗaukar fansa
yake so yayi akanta na rashin kunyar da tayi mishi washe garin ranar da ya kaita
asibiti.

Shi kuwa Abdul a hankali yake tafiya, lokaci zuwa lokaci ya kan juyo ya kalle
ta, babu wanda yayi magana a tsakanin su, ita dai tana ƙanƙame da wayar shi har
suka ƙaraso wani botique.

Ya fito ba tare da yace mata komai ba, Nusram dai tana zaune tana zare idanu,
ɓangaren ta yazo ya bude sannan ya saka hannu yaa janyo ta, hannun ta ya riƙe gam
sannan ya fara tafiya, zuwa lokacin Nusram ta fara cire rai da ƙara numfashi dan
kawai ta kawo cewa gidan yankan kai ne ganin irin yadda wajen ya ƙayatu.

Yana shiga ƴan wajen suka fara gaishe dashi, Nusram na rungume da wayar shi a
ƙirjinta, idanun ta ya kawo ƙwalla, wato ma shine babba a wajen kenan, wayyo! Ummi
🙆.

Wani mutumi ɗan saurayi ya ƙaraso inda yake bayan sun gaisa sannan ya shiga gaba
suna binshi a baya har zuwa wata ƙofa, ya buɗe musu suka shiga.

Wani ɗan ƙaramin falo ne me cike da kayan alatu, ga sanyin ac, be zauna ba ya
kalli ɗan saurayin yace; "Nura hijab zaka ɗauko mata".

Wanda aka kira da Nuran yace; "yallaɓai wane kala?", Abdus-samad ya kalli
Nusram, doguwar riga ce a jikin ta, ta yadin saytin kalar blue da pink, ba tare da
ɓata lokaci ba yace; "kawo blue", Nusram ita dai banda zare idanu babu abinda take
yi.

Babu jimawa yaron ya dawo hannun shi ɗauke da leda, ya miƙowa Abdus-samad ɗin,
shi kuma ya nuna mishi Nusram dake tsaye.

Da murmushi a fuskar shi yace; "Madam ga hijab ɗin ko?", kamar wacce zata zuba
da gudu tace; "ni?", yace; "eh mana", ta kai hannu a tsorace sai kuma ta janye.

Tana tsoron kada ta taɓa taji ance masu shan jini idan suka baka abu ka taɓa
shikenan sai ka zama doya ko wani abin ko kuma ka ɓace gaba ɗaya.

Nura ya kuma cewa; "haba Madam ki amsa mana dan Allah", Nusram ta share hawayen
daya zubo mata tace; "Allah ba zan amsa ba kar naje na ɓace, su kuke ku shanye jini
na", Nura dabe fahimci me take magana akai ba ya maida kallon shi kan Abdus-samad
ɗin yace; "yallaɓai........".

Abdul dake danna waya amma jin abinda ta faɗa yasa ya tsaya, wato har yanzu bata
dena mishi kallon mugu ba kenan? Lallai zai koya mata hankali, ya miƙe ya matso
kusa da Nuran yace; "bani hijab ɗin jeka kawai".

Nura ya miƙa mishi sannan ya juya ya fice, inda take tsaye ya nufo, da sauri ta
fara ja da baya, ganin ta kai bango yasa ta fara faɗin; "dan Allah ka tsaya, nifa
ba ƴar iska bace".

Ya saka hannu ya dafa bangon yace; "to waye ɗan iskan kenan" ta runtse idanu
tace; "dan Allah kayi haƙuri ka barni na tafi", hannun shi ya kai saman kanta sai
kuma ya fasa, ya ɗan matsa baya sannan ya miƙo mata hijab ɗin yace; "saka mu tafi",
taƙi amsar hijab ɗin kuma taƙi kallon shi.

Cikin jin haushi ya finciko ta, ta dawo gaban shi sannan ya warware hijab ɗin ya
saka mata kafin ya kama hannun ta yaja suka fice.

Har sun kusa ƙofar fita sai kuma yaja ya tsaya, janta ya kuma yi suka koma ciki,
basket yaja ya fara ɗebar kaya, kayan make up na mata turarruka da kuma atamfofi da
lace.

Be jima ya kuma janta aka zuba musu kayan a leda sannan suka fice daga wajen,
sai da ya buɗe mota ya saka ta sannan ya koma ya buɗe baya aka zuba kayan, ya shiga
mota yaja suka tafi.

Babu wanda yayi magana har suka isa Hayin Rigasa, har ƙofar gida ya kaita, tana
ƙoƙarin buɗe ƙofa yace; "heys!, duk ranar da kika kuma gani na kika tsorata to
tabbas daga ranar sai na kai jinin ki wajen gunkin mu", yana faɗar haka ya buɗe
mata ƙofar.
Nusram jin abinda ya faɗa yasa ta fara yarfe hannu tana bashi haƙuri, ta miƙo
mishi wayar tace; "dan Allah in dai dan wannan ne kake bibiyar rayuwa ta kayi
haƙuri ga wayar ka".

Ya jingina da kujrerar da yake kai, ya saka hannu ya janyo ledar ɗazu ya miƙa
mata yace; "gashi kayan da wa'incan suka amsar miki, yanzu fita ki bar mini mota".

Ta share hawaye tace; "ka amshi wayar ka, kayan kuma bana so na gode ni dai dan
Allah kayi haƙuri", ya ɗaure fuska yace; "zaki amsa ki fice ko sai na canza ra'ayi
yanzu na wuce dake wajen gunkin mu", kan ya rufe baki ya wafce ledar baki na rawa
tace; "Allah ya baka haƙuri, na gode", ta fice daga motar.

Abdus-samad ya bi ta da kallo har ta shige gida, yayi murmushi wato dai duk
girman mace da wayonta a tafin hannun ɗa namiji take kenan?.

Cike da nishaɗi yaja motar shi ya tafi, babu abinda yake yi sai murmushi dama
asibiti zai je sai ya fara biyawa wajen Ƙawar Brr Farida ya kai mata saƙo, shine fa
suka haɗu dan haka kai tsaye ya wuce asibitin.

*********⬇️⬇️**********

Hajiya Salma ta kalli ƴar ta cikin ɓacin rai amma da yake Alhaji Mustafa yana
wajen sai ta daure tayi murmushi tace; "haba Khausar tunda yace zai dawo ai zai
dawo ne, ki daure kici abinci nan kinji".

Alhaji Mustafa da be daɗe da shigowa ƙasar ba ya sami wannan mummunan labarin ko


gida be jeba daga Airport ya wuto asibitin hankalin shi a tashe.

Kusa da ita yazo ya zauna sannan ya riƙo hannun ta yace; "ki daure kici abincin
kin ji zai zo yanzu", Khausar ta maƙe kafaɗa alamun bata yarda ba.

Hajiya salma ta buɗe baki zata yi magana ya turo ƙofar tare da yin sallama,
Alhaji Mustapha jikin shi har rawa yake yi ganin wanda ya shigo.

Abdus-samad shima dai da kallo ya bishi, cikin ranshi yana mamakin dama wannan
ƴar Mustapha Abubakar Tuge ce?.

Hajiya Salma kuwa kamar ta ɗora hannu akai tayi ihu haka take ji, ya gaishe dasu
sannan ya ƙarasa inda take.

Khausar ta saki murmushi tace; "ina ka tsaya tun ɗazu nake zaman jiran ka?", ya
ɗauki plate ɗin abincin ya ɗebo ya nufi bakin ta dashi.

Ta buɗe baki ta amsa, yayi murmushi har kumatunshi ya lotsa yace; "dama yunwa
kike ji kenan?", ta kai hannun kan kumatun shi tana murmushi, haka ya bata abincin
har ta cinye.

Da kanshi ya taimaka mata ya gyara mata kwanciya, ta riƙe hannun shi gam, be
hanata ba sai ma fira da suke yi sama-sama.

"ban sani ba ko jinin da ka bayar ne yasa nake gani kamar mun jima da sanin
juna", ya ɓata rai yace; "waye ya faɗa miki".

"baka san ina da ƙawa a nan asibitin ba?", ya ɗaga mata gira ɗaya tayi dariya
tace; "ai nima likita ce amma ɓangaren mata", ya ɗaga mata yatsu alamun jinjina👍.

Haka suka cigaba da fira tsayin lokaci sannan yace; "to yanzu ki kwanta sai da
safe ko?", tace; "to amma gobe zaka zo da safe?", ya girgiza mata kai "sai lokacin
dana sami dama, bye", daga haka ya fice.

Alhaji Mustapha ya miƙe da sauri ya bishi, har ya kusa parking lot, "Abdus-
samad", ya kira shi, ya ja ya tsaya.

"mun gode sosai da kulawar daka nuna mata", abinda Alhaji Mustapha ya faɗa,
Abdus-samad ya ɗan yi murmushi yace; "babu komai, Allah ya bata lafiya dai kawai".

Ya shiga motar shi yaja ya bar Alhaji Mustafa a tsaye cike da mamaki farin ciki
da kuma damuwa.

Gashi ga ɗan shi amma bashi da damar zuwa kusa dashi, hasalima ƙara matsar ɗan
nashi da zai yi hakan barazana ce ga rayuwar yaron dan a haka ma koda yaushe cikin
barazana yake da takurawa akan yadda zai kawo ɗan nashi wajen Appu domin sadaukar
da jinin shi ga oregbu.

Haka ya juya ya koma cikin asibitin cike da damuwa, Hajiya Salma dake laɓe tayi
ajiyar zuciya kafin itama tayi saurin barin wajen tana godiya ga Allah da asirin su
be tono ba.

Washe gari da safe Abdus-samad be samu damar zuwa asibitin ba, domin Brr Farida
da ta tsare shi suka tafi court tare.

Hajiya Salma ta kalli jug ɗin dake cike da haɗaɗɗen juice taja tsaki, ta maida
kallon ta kan Khausar wacce ke kwasar barci hankali kwance ta gama zaman jiran shi
be zo ba.

Ta zaro wayar ta ta kira Alhaji Sa'eed, "yau fa bezo ba gashi tun ɗazu na
haɗa mishi nake zaman jiran shi", Alhaji Sa'eed yayi dariya yace; "kada ki damu ina
ji a jikina mun kusa yin nasara".

Brr Hauwa ta amshi wayar tace; "kada ki damu zai zo ne abinda ya kamata ki maida
hankali akai shine ki tabbatar ya sha kafin ya bar asibitin.

Tace; "tabbas kuwa zai sha kafin ya bar asibitin nan, ku dai ku jira kirana
kawai dole wannan shegen yaron ya mutu".

Alhaji Sa'eed yace; "da kyau, haka nake son ji, muna zaman jiran ki", ta amsa
da to sannan ta kashe wayar.

Babu jimawa Abdul yayi sallama ya shigo, Hajiya Salma ta washe baki bayan sun
gaisa tace; "ai ta gama rigimar baka zo ba tayi barci", ya matsa kusa da Khausar
ɗin yace; "to bari na tafi kawai na dawo da yamma".

Da sauri Hajiya Salma tace; "a'a ka zauna mana ko wani abu ne ka sha tukunna sai
ka tafi ya juya yace; "kada ki damu Hajiya nagode", tace; "aikuwa ba zai yiwu ka
tafi yanzu ba", dole tasa ya koma ya zauna ta miƙo mishi.

Kiran wayar shi ya hana ya kai kofin bakin shi, sun ɗan jima suna magana kafin
ya katse wayar ya duba Hajiya Salma yace; "idan ta farka kice mata nazo na tafi
amma wata kila anjima na dawo", kamar zata yi kuka tace; "shikenan amma da ka sha
koda kaɗan ne", yayi murmushi yace; "am ok, thanks" daga haka ya fice.

Hajiya Salma kamar ta ɗora hannu a kai tayi ihu, cikin jin haushi ta kira Alhaji
Sa'eed ta bashi labarin abinda ya faru.

Shima dai ranshi ya ɓace amma yace kada ta damu komai nada lokaci idan ya
tsallake yau wata rana zai faɗa ne.
Sai da suka ƙara kwana biyu sannan aka sallame ta, zuwa lokacin ta sami sauƙi
sosai, Alhaji Mustapha kuwa kullum sai ya zo asibitin ko dan haduwa da ɗan nashi
suna haɗuwa amma ba yadda ko wanne uba Ke so ba.

zuwa lokacin kuma saura kwana sha biyu Family meeting ɗin su Abdul ɗin, dan shi
tunda aka sallami Khausar daga asibiti be kuma zuwa ba hasalima be je gidan su ba
ko sau ɗaya.

cikin kwanakin da Baba ya ɗibarwa Nusram har anci kwana bakwai, zuwa yanzu kam
hankalin Nusram ya fara tashi sosai domin kuwa bata da hanyar da zata sami mijin da
yake shirye ya aure ta cikin sati ɗaya.

Tunda kwanakin nan suka matso kullum sai Nusram tayi tsayuwar dare tana addu'ar
Allah ya fitar da ita daga wannan halin da take ƙoƙarin faɗawa.

Ummi kuwa a haka zaka ganta cikin jarumta amma da zarar ta keɓe babu abinda take
sai kaiwa ubangijinta kukan ta, Aunty ma duka abin ya dame ta sai dai bata da yadda
zata yi.

Yau ta kira Nusram ta waya tace tazo tana nemanta, duk da yamma ta fara yi haka
Nusram ta shirya, niƙaɓ ta ɗaura a fuskar ta domin kuwa sa idon na ƴan layin su ya
fara yin yawa.

Koda ta isa gidan ta sami ƴan gyaran jiki da kuma masu siyayya, Nusram ta taya
ta wajen gyaran amaren da kuma tattara kayan.

Bayan sun gama ta kalli Aunty tace; "Aunty bari na shiga wajen Aisha yanzu zan
dawo", Aunty tace; "to kada ki daɗe kinji", ta amsa da to.

Gidan dake jikin gidan Auntyn nan ne inda Yaya Sulaiman yake da amaryar shi,
lokacin bikin Nusram bata sami damar zuwa ba saboda Baba da ya hanata fita ko'ina.

Ta sami Amarya Aisha sun jima suna fira domin tana da kirki sosai, sai da ta
tsare ta har taci abinci sannan ta ƙyale ta taho.

A zaune ta sami Aunty kusa da Abba gefen shi kuma Yaya Sulaiman ne, ta yi mishi
murmushi sannan ta maida kallon ta kan Abba ta gaishe dashi cikin mutunci ya amsa
da sakin fuska har yana tsokanarta.

Sai da ya ɗan yi shiru sannan ya kira sunan Nusram, ta amsa tana me ƙara yin
ƙasa da kanta.

"kin san dai tun kina ƙarama kike gidan nan ko?, anan kika tashi har kika girma,
mun san halin ki mun san abinda zaki iya aikatawa da wanda ba zaki iya aikatawa ba,
Nusram ni da Auntyn ki kallon ƴa muke yi miki, haka Sulaiman da ƙannen shi kallon
ƴar uwa suke yi miki, abinda ya shafe ki ya shafe mu haka abinda ya shafe mu na san
ya shafe ki, in da yau zaki ganmu cikin matsala na tabbatar da cewa zaki yi duk
yadda zaki yi kiga mun fita daga wannan matsalar to dan haka dole ne muma idan muka
ganki a cikin matsala muyi ƙoƙarin fitar dake daga cikin ta, jiya Auntyn ki ta same
ni na faɗa mini halin da kike ciki keda mahaifiyar ki, na san da cewa ba zaki taɓa
so ace ta dalilin ki auren iyayen ku ya rabu ba, a gaskiya da ace tun farko mun san
da cewa hakan zai faru to tabbas da Sulaiman ba zai auri kowa ba sai ke amma da
yake Allah shine masanin komai, abin be faru ba sai bayan auren, kin san dai da
cewa samin miji a zamanin nan wuya yake yi, wanda kuka shekara kuna soyayya ma sai
yaci amanarki balle wanda kake nema cikin abinda yake ƙasa da sati ɗaya to kallon
wannan yasa muka yanke shawara shine Sulaiman dai ɗan uwan ki ke dan haka mun bashi
izini zai aure ki nan da sati ɗayan in Allah ya yarda, naso ma tun jiya naje gidan
ku na sami mahaifin naki amma Sulaiman ɗin ya roƙeni akan mu bari mu ji ta bakin ki
tukunna wannan shine dalilin da yasa muka ce to kizo, kin amince da zaɓin da muka
yi miki?".

Nusram kuwa tun lokacin da suka haɗa ta da Yaya Sulaiman numfashin ta ya fara
sama, hannu ta saka ta dafe ƙirjinta tana addu'o'i har ta samu numfashinta ya ɗan
dai-daita.

Ta kalli Aunty haƙiƙa su ɗin masoyanta ne wa'inda ba zata taɓa mantawa dasu ba,
ba zata iya kallon Aunty tace; "bata son ɗan da ya fito daga cikin ta ba, idan tayi
la'akari da yadda ta ɗauke ta kamar ƴar data haifa, tun tana ƙarama take ɗawainiya
da ita".

Abba mutumin da yake nuna mata kulawa wacce ta rasa daga mahaifin daya haife ta,
shiya tsaya mata a lokacin da take buƙatar taimako, lallai ba zata taɓa kallon shi
tace bata son abinda ya fito daga jikin shi ba.

Yaya Sulaiman wanda ya zame mata yaya guda ɗaya tamkar da dubu, taya zata kalle
shi tace ma bata son shi, wanda yayi hidima da ita tun tana ƙarama, har ta girma ko
ranar bikin su duk kayan data saka ko kuɗin da tayi amfani dashi shine ya basu ba
zai taɓa yiwuwa taƙi shi ba.

Taja ajiyar zuciya goshin ta sharkaf da zufa ta buɗe bakin ta wanda yayi nauyi
tace....................".

*ZUCIYATA WHERE ARE YOU, gafa Nusram ɗin ki cikin tasku, kizo ki taimako ta,
godiya gaba ɗaya kacokam ga *RAYUWAR ABDUS-SAMAD FANS CLUB* da kuma *ZAMA NA AMANA
2* musamman ma *ZAKARIYYA KHADIJA, AISHATU BABAYO(ZUCIYA TA), ABDUL ƘIRU, IBNATU,
MAMAN ABDUL* banda bakin yi muku godiya.

#LIKE
#SHARE
#COMMENT

*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*


*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖45-46📖📖

Tace; "nagode Aunty, kin nuna mini ƙauna wacce koda ace ke kika haife ni iya wacce
zaki bani kenan, Abba ka kula dani kulawar da ko Mahaifina be bani ita ba ban ɗauka
a komai ba face kai ɗin matsayin Uba, me zan iya ce muku da kuka bani Yaya wanda
yake kula dani a matsayin ƙanwar shi, abinda yasa kullum hankalina ke kwanciya
saboda Allah ya bani madadin duk wani abu dana rasa, da farko ya bani Uwa biyu yazo
ya bani Uba kamar ka Abba sannan ya haɗa mini da Yaya idan ban godewa Ubangiji ba
ai nayi mishi butulci".

"wallahi umarnin ku ni mai yin biyayyace, sai dai kuma kada mu duba kanmu a
kowanne lokaci mu dinga duba wasu ma wa'inda zamu iya cutar dasu suma, Aisha amarya
ce da yin auren su befi sati biyu ba nan kuma da sati ɗaya sai ayi mata kishiya
anya kuwa an mata adalci?".

"Aunty ki ɗora wannan abin a kanmu idan da ace Safeena za'a yiwa haka ko Halima
fa? Na san ba zaki taɓa jin daɗi ba, to a bar magana tasu ma idan kuma ni aka yiwa
fa?, ko Nusreen data ɗebi kwanaki a gidan ta ba zamu ji daɗi ba ace anyi mata
wannan, to yadda ba zamu ji daɗi iɗan anyiwa namu ba to muma kada mu yiwa wani, na
gode ƙwarai da wannan shawara sai dai nima ku duba nawa magan-ganun dan Allah".

ɗakin yayi shiru, kowa yana tunani daban dana ɗan uwan shi, Nusram ta kuma cewa;
"dan Allah kada mu aikata aikin da za muyi dana sani amma idan har kuna ganin
abinda kuka yanke shine dai-dai to ni meyi muku biyayya ce".

Abba yace; "tabbas abinda kika faɗa Nusram gaskiya ne, mutane zasu zage mu
sannan bamu san wane irin kallon dangin ta za suyi mana ba, dan haka zamu cigaba da
taya ki da addu'a kawai".

Nusram tayi ƙasa da kai tace; "na gode Abba, Allah ya ƙara girma", Yace; "Ameen,
Allah yayi muku albarka, Sulaiman tashi ka maida ita gida".

Ya amsa da to sannan ya miƙe daga gaban iyayen shi, itama ta miƙe tana yiwa
Aunty Sallama, Aunty tace; "Allah ya tashe mu lafiya Nusram Allah kuma ya dube ki,
ki gaishe da Maman ki", tace; "to.

Har suka isa ƙofar gidan su Nusram babu wanda yayi magana, kowa kuma abinda yake
tunani daban.

Nusram harta yunƙura zata buɗe ƙofa ta koma ta zauna, tace; "Yaya kayi haƙuri da
abinda ya faru ba wai ba zan iya auren ka bane a'a zan so ace kaima ka fahimce ni
kamar yadda suma suka fahimce ni".

Yaya Sulaiman ya numfasa yace; "kada kice komai, waye zai fahimce ki sama dani,
mun rayu tun muna yara tare kallon abu kika yi na san me kike nufi balle har ta kai
ga kin furta, kije gida kawai sai da safe nima zan taya ki da addu'a".

Tayi murmushi tace; "na gode sosai sai sa safe", yace; "Allah ya tashe mu
lafiya", tana fita ta haɗa ido da Baba wanda ke tsaye yana jiran fitowar Isa da
alamu lissafi zasu yi ko wani abin.

Yaya Sulaiman ya danna mata horn ta juya ta ɗaga mishi hannu, ya ɗago mata hannu
sannan yayi reverse ya bar wajen.

Cikin natsuwa ta fara tafiya, "barka da dare", abinda ta faɗa kenan lokacin da
tazo gifta Mahaifin nata, Baba yace; "waye ya ajiye ki a mota yanzu?".

"Yaya Sulaiman ne", cikin daka tsawa yace; "rufe mini baki gantalalliya ni zaki
rainawa wayo, wato Sulaiman ne ya kawo ki ko, kai ni kam banyi sa'ar haihuwa ba, to
bari kiji wallahi daga kwanakin dana ɗibar miki babu ƙari, nan da sati ɗaya idan
baki fito da miji ba ni da ke ne", Nusram tace; "to Baba", ta wuce gida.

Tana shiga zaure Isa na fitowa daga ɗakin shi, ya kalle ta ya kwashe da dariya
yace; "baki da miji da ya wuce ni ɗin nan".

Bata kalle shi ba ta shige cikin gida, Mama Jummai dake gaban murhu tace; "an
gama yawon ta zubar ɗin kenan?", itama dai Nusram bata kulata ba.

Ɗaki kawai ta shiga, ta yiwa Ummi sannu da gida, Ummi tace; "ya kika baro su",
tace; "suna lafiya sun ce ma a gaishe dake", Ummi tace; "masha Allah".

Har zuwa lokacin da suka kwanta Ummi bata tambaye ta ya suka yi da Aunty ba
itama kuma bata faɗa mata ba.

Ta zurfafa kanta cikin tunani ganin cewa gobe fa saura kwana shida kenan, dole
tayi wani abu a kai idan ba haka ba tana ji tana kallo matsalolin gidan su zasu fi
ƙarfin ta.

Shawarar da taji ta kwanta mata a rai ita ta fara ƙoƙarin bi, dan haka cike da
ƙwarin gwiwa tayi barcin ta.

Washe gari da safe duk wasu ayyukan da ta san zata yi duka tayi sannan tayi
wanka taci abinci.

Kayan siyarwa da Ummi take siyarwa ta tayata suka ƙulla na ƙullawa sannan ta
tashi ta wanko hannun ta.

Tana tsaye a tsakar gida, Atika tayi sallama ta shigo, Nusram ta kalle ta, itama
ɗin ita ta kalla fuska ɗauke da murmushin mugunta.

Wani rantsattsen lace ne a jikin, kalar ash da orange, yayi kyau sosai, ita
kanta Atikar tayi ƙiba tayi freah, Nusran ta kauda kai daga kallon ta.
Atika tayi shewa tayi juyi sannan ta nufi hanyar ɗakin mahaifiyar ta, bata jima
da shiga ba aka fara shigo da buhunan abinci.

Shinkafa buhu biyu, taliya kwali uku, buhun semonvita guda ɗaya, ƙaramin buhun
gishiri, sai sugar itama ƙaramin buhu, man ja da man gyaɗa duka galan ɗaya, sai
tarkacen maggi.

Nusram kuwa ɗaki ta shige dan wannan dama basu bane a gabanta, ko Ummi bata bawa
labari ba, tana daga cikin ɗaki ta jiyo sallamar Habiba, nan suka hau murna suna
shewa a tsakar gida.

Ummi ta kalli Nusram, Nusram kuwa hankalin ta naga wayar Abdus-samad tana dubawa
kamar wacce ta san kanta, Ummi tace; "bafa kiyi mini bayani akan wayar hannun ki
ba".

Nusram tace; "Hajiyar Shureim fa ta bani haɗe da kayan nan", Ummi tace; "aikuwa
an gode sosai, amma da kin sani baki amso duka ba, kayan sun yi yawa".

"nima sai da nace mata ba zan amsa ba ta tilasta, shiyasa na amsa ɗin dan kada
nayi jayayya da ita", Ummi bata kuma cewa komai ba.

Suna jiyo lokacin da suke ta hidimar su akan kayan da Atikar ta kawo, babu wanda
yace wani abu, Nusram ma cikin ɗaki kawai ta shige.

Tun ranar data dawo da kayan ta ajiye a kullum tana son ɗauka amma hakan ya
gagara saboda gani take idan ta ɗauka ɓacewa zata yi.

🤣🤣🤣🤣🤣 Nusram baki ɓace ba da kika dauki wayar shi sai kayan daya siya miki a
boutique?.

Kwanciya tayi, tana tunanin rayuwar ta har barci ya ɗauke ta, sai lokacin da
zata ɗora girkin rana sannan ta farka.

Ta fito ta haɗa wuta inda ta ɗora abinci, Sahura ta fito da sauri, Nusram ta
kalle ta tayi murmushi, suka gaisa cikin mutunci.

"ina mijin naki?", tace; "yana gida yace a gaida ke", Nusram tayi ajiyar
zuciya tace; "ina amsawa", sun ɗan taɓa fira kaɗan kafin Sahurar ta tafi.

Nusram na gama abinda zata yi ta shige ɗaki, tare da Ummi suka ci abincin, daga
nan suna juyo abubuwan dake waka na a tsakar gidan.

Nusram ta taɓe baki kawai tana cigaba da abinda yake gabanta, Ummi ma bata ce
komai ba.

"ayyiririririiiiiiiii, gaka inda aka iya haihuwa, ni Jummai waya ganni a


saudia", faɗar Mama Jummai kenan kafin kuma suka hau tiƙar rawa ita da Ameera da
Habiba, Atika na musu kiɗa.

Sai da suka gama cashewar su sannan Mama Jummai ta kuma cewa; "kai haihuwa me
daɗi, ai dama haihuwa suna ta tara mu dai tamu kam sam barka".

Duk da Nusram da Ummi suna jiyo su amma babu wanda ya tanka musu, haka suka gama
shewar su da habaice-habaucen su.

Koda yamma da Baba ya dawo, ana nuna mishi kayan da wai Alhajin ya bada a kawo
ya hau murna.
"Maimuna ina kike?", ya hau ƙwalawa Ummi kira, ta fito Nusram ma ta biyo
bayanta.

"ki kalli inda ake abin arziƙi, kin gani ko wannan shine haihuwar da ake so ba
kalar taki ba ƴaƴa sun zama kamar masu farar ƙafa babu ɗaya ƙwakkwara na kamawa".

Ummi tace; "an gode Allah ya saka da alkhairi", Baba da Mama Jummai suka ce
Ameen, inda da gaske kike", Ummi tayi murmushi kawai kafin ta juya.

"haba me ake da yaran da basu san su kyautatawa iyayen su ba, ita waccen shegiyar
har yanzu ko gidan bata leƙo ba", tsaf Ummi ta san da Nusreen yake amma bata tanka
mishi ba.

Sai bayan sun shiga ɗaki sannan ta sami damar share hawayen daya zubo mata,
Nusram ita kanta jikinta yayi sanyi, ta miƙe ta shiga ɗaki hijab kawai ta ɗauko
kafin tazo ta fice.

Ba tare da sanin inda ta nufa ba, wani lungu tabi sannan ta tsaya tana maida
numfashi, lallai ya kamata tayi wani abin kodan ragewa Ummi damuwar da take ciki,
to amma yanzu me zata yi?.

Tana nan tana saƙe-saƙe aka fara kiraye-kirayen sallah, ta miƙe sannan ta fara
takawa cikin natsuwa.

Masallacin da ta san mahaifinta baya zuwa haka ma Isa nan taje ta laɓe, tana
kallon yadda mutane ke hada-hadar su na ƙoƙarin yin alwala.

Wanda ta hango a can gefe idan zata iya canka zai kasance shine liman, tana
kallo yana alwala sai da ta tabbatar mutane sun yi alwala sun shige masallaci
sannan ta sami damar ƙarasa gaban shi.

Tayi mishi sallama ya amsa, yana cigaba da alwalar shi ta tsaya har sai da ya
ƙarasa sannan ta gaishe dashi, ya amsa yana bin ta da kallo.

Tace; "dama.......dama mijin.........dama mijin aure ......nake nema


shine ........shine nace bari ......nazo nan masallacin idan dame buƙatar ƙara mata
sai yaje ya sami......sami mahaifina", ta ƙarasa muryarta na rawa tana wasa da
yatsun hannunta.

Limamin yayi ɗan jimm kan yace; "to shikenan ki jira mu nan waje, amma kamar ƴar
gidan Malam Abdullahi", cikin ladabi tace; "eh nice", ya jinjina kai sannan yace;
"ki jira bari na shiga muyi sallah tukunna Allah yasa a dace.

Wani gida dake kusa da masallacin nan ta shiga ta rakuɓe, addu'ar da take yi
Allah yasa a dace ta sami mijin aure ko ta bar gidan nasu mahahifiyar ta, ta sami
kwanciyar hankali.

Tana jiyo lokacin da suka idar da Sallah, liman ɗin yayi sanarwa, bata da
tabbacin me suke bada amsa, amma liman ɗin ya sanar musu sannan ya faɗa musu ƴar
gidan ko waye yace; "idan dame buƙata sai ya nemi mahaifin nata", daga haka yayi
addu'a aka watse.

Daga inda Nusram take tana jiyo wasu samari suna faɗin; "kai haba dai waye zai
kai kanshi wajen yarinyar da a ranar da aka kaita gidan miji aka kamata da kwarto".

Ɗayan yace; "kai da ka gane kenan Auwalu, kwananta goma sha biyu fa a gidan
kaso", Auwalu yace; "kai Idi a dai wajen ƴan sanda ba gidan kaso ba, shima kuma
kwana takwas ne ba goma sha biyu ba".
Ɗayan yace; "ni naji ance ma wai da saurayin suka haɗa baki, suka gudu sai da ya
ɗirka mata ciki sannan ya dawo da ita, Mahaifiyar ta itace take goyan bayan duk
abinda take aikatawa, sunje zubar da cikin aka sami matsala sai aka kwantar dasu a
asibitin kwanan su shida sannan aka sallamo su".

Idi yace; "ai zasu aikata wallahi, kana ganin mahaifiyar nan tasu a haka sumimi
kasai, kamar wata mumina da gaske, ta ganku tana wani sunkuyar da kai kamar sabuwar
tunkiya, amma ita take tura yaranta karuwanci".

Auwalu yace; "kai raba kanka da irin wa'innan matan yasin, bar ganin ta a haka
da zumbulelen hijab waye ya san ita me take aikatawa, shi kanshi mijin nata ai
asiri tayi mishi to ance fa ya sake ta amma taƙi barin gidan yanzu haka ma kuɗin da
suka yi karuwanci dashi suke ciyar da kansu".

Nusram ta tsugunna a wajen ta fashe da kuka, wato kallon da ake yi musu kenan,
lallai rayuwa kenan, sai da gari yayi duhu sosai sannan ta sami damar barin wajen.

Har lokacin kuma basu bar firar su ba, taja hijab ɗin ta rufe rabin fuskar ta
sannan ta tafi.

Koda ta isa gida Ummi bata ce mata ina taje ba haka itama bata cewa Ummi ga
inda taje ba,

Koda tazo kwanciya sai da tasha kukanta ma'ishi kafin barci ya ɗauke ta

************* *************

Khausar dake kwance saman couch ɗin ɗakin ta wanda yaji kayan more rayuwa.

tana sanye da riga doguwa iya gwiwa, kwananta biyu kenan babu inda taje,
Mahaifiyar ta harta gaji da buga mata ƙofa akan ta buɗe amma taƙi.

Yanzun ma Hajiya Salma dake tsaye bakin ƙofar ta kuma bubbugawa tace; "wai
Khausar ba zaki buɗe ƙofar nan ba", shiru babu amsa.

Khausar kuwa dake ciki tayi juyi tana jan tsaki, wai me yasa ƴan gidan nan basa
ganewa ne itafa Abdus-samad kawai zasu nemo mata shine samun kwanciyar hankalin ta.

Alhaji Mustapha dake zaune saman dinning ya buga uban tagumi, lokaci zuwa
lokaci ya kan share zufar da take tsattsafo mishi.

Brr Jabeer yayi sallama ya shigo, cikin sauri Alhaji Mustafa ya miƙe ya isa
wajen shi, saman kujera duka suka zauna.

Alhaji Mustapha yayi ƙasa da murya yace; "Brr ina cikin tashin hankali, ƴata
Khausar tace babu wanda take so sai ɗan uwan ta Abdus-samad".

Brr Jabeer ya zaro idanu waje yace; "taya suka haɗu a ina kuma ta san shi, shin
ko dai ta san sirrin da kake ɓoyewa ne", Alhaji Mustapha yace; "ko Mahaifiyar ta
bata sani ba balle ita".

"tun da suka haɗu a wajen siyayya shikenan ta maƙale, yau kwanan ta biyu kenan
ta rufe kanta a ɗaki babu ci babu sha wai shi take son gani".

Brr Jabeer yayi shiru tsayin wani lokaci kafin yace; "ni ina ganin kawai abinda
za'a yi shine ka nemo shi, kga daga nan zaka sami hanyar da zaka ja sha jikin ka".

Alhaji Mustapha yace; "hakane kuma, amma kai kanka Brr kasan wacece Brr Farida
ba sai na faɗa maka komai ba, idan har na sake nayi wani motsi a kai to zata kaini
kotu kuma ka san cewa kaini kotu dai-dai yake da tonon asiri na".

Brr Jabeer yace; "kuma hakane tabbas, to amma yin shirun kana ganin shi yafi",
Alhaji Mustapha ya jinjina kai yace; "tabbas kuwa shi yafi, idan ta gaji da kanta
zata buɗe ƙofar", Brr Jabeer yace; "shikenan".

Tare suka miƙe da Alhaji Mustaphan, inda Hajiya Salma ke tsaye tana fama da
Khausar akan ta buɗe ƙofa suka je.

Brr Jabeer yace; "Khausar ki buɗe ƙofar nan ni kuma nayi miki alƙawarin baki
number ɗin shi", Khausar jin hakan yasa ta diro daga saman couch ɗin tazo ta buɗe.

Hajiya Salma da Alhaji Mustapha kuwa gaban su ya faɗi, Hajiya Salma abinda take
gudu shine alaƙa ta shiga tsakanin su bata fatan abinda zai kawo Abdus-samad ɗin
cikin rayuwar su wancan ma tsautsayi ne.

Alhaji Mustapha kuwa tsoron shi shine be san ta yadda zai kare kanshi ba idan
har asirin shi ya tonu.

Khausar ta kalli brr, shi kuma yayi mata murmushi sannan yace; "idan kika kashe
kanki a ɗaki Khausar taya zaki iya zuwa wajen Abdus-samad ɗin ko kin haƙura dashi
ne?", ta girgiza kai.

Ya riƙo hannun ta yace; "idan mutum yana son abu ba wai shiga ɗaki yake yi ya
rufe kanshi ba a'a zai iya iyakar yin shi nr ganin wannan abin yazo gare shi,
wannan shine abinda ya dace kiyi, kinji ƴar Baba".

Khausar tayi murmushi tana sauke kanta ƙasa, Brr Jabeer kuwa murmushi yayi
kafin yayi musu sallama ya fice daga gidan.

Alhaji Mustafa ya kalli ƴar tashi yace da ita; "haba Khausar yanzu kina ganin
abinda kika yi kinyi dai-dai kenan".

"kayi haƙuri Daddy ba zan kuma ba", ta faɗa cikin sanyin murya, zai kuma magana
Hajiya Salma ta dakatar dashi tace; "Khausar wuce kije kici abinci".

Sai da ta bar wajen sannan Alhaji Mustafa yace; "wai me yasa bakya son na yiwa
yaran nan faɗa ne?".

"to Alhaji wane irin faɗa kuma bayan ta riga ta fito daga ɗakin ai shikenan dai
ko, ni zan wuce wajen aiki", ta ƙarasa tana tafiya.

Alhaji Mustapha ya bita da kallo har ta fice sannan yayi ajiyar zuciya kafin ya
ciro waya ya hau kiran Alhaji Sa'eed.

"Alhaji ina cikin tashin hankali", abinda Alhaji Mustapha ya faɗa kenan bayan
Alhaji Sa'eed ya ɗaga wayar.

Alhaji Sa'eed yace; "innalillahi, ka bari anjima mu haɗu a guest house ɗin ka
dake by pass", Alhaji Mustapha yayi ajiyar zuciya yace; "to", daga haka suka katse
wayar.

Ya nemi waje ya zauna ya dafe kanshi, idan har yayi wasa tofa wanki hula zai
kaishi dare, dole ya san abinda ya kamata yayi, be shirya zuwa gidan yari yanzu ba.

******** ***********

Abdus-samad ke gaba yayin da Fadila da Brr Farida suke bayan shi, yana sanye da
ƙananan kaya, jar riga da kuma baƙin wando as usual shigar ƙananan kaya.

Brr Farida tace; "yauwa kije insha Allahu nan da sati ɗaya zamu zo kuma za'a yi
maganar auren ku, kinji ko".

Fadila ta sunne kai tana murmushi, Brr Farida itama tayi murmushi sannan ta
kalli Abdul tace; "Baby ka tafi da ita a hankali banda gudu ka san amarya tsautsayi
gare ta".

Sameer da Tameer dake tsaye a wajen parking lot ɗin suka kalli juna suka kwashe
da dariya.

Abdus-samad ya shagwaɓe fuska yace; "kai First Love ni na lura yanzu ma ba wani
sona kike yi ba ta wannan me kan gwandar kike".

Brr Farida ta riƙo hannun shi tace; "idan banda abinka, ai kai ne na gaban
goshi, ita kuma a ƙeya take", wannan yasa suka kuma dariya.

Sameer yace; "mu dai ka wuce ka kaita zamu jira ka a office idan kayi latti
kuma zaka amsa query", Abdus-samad ya murguɗa mishi baki.

Sameer zai kuma magana Brr Farida ta dakatar dashi tace; "dan Allah ka bari su
tafi kawai".

Dr Abubakar da ya fito cikin shirin tafiya wajen aiki yace; "au har yanzu baku
tafi ba kun tsaya wasa ko".

Brr Farida ta ƙarasa wajen mijinta tace; "nima abinda nake faɗa musu kenan, su
tafi kawai Baby kuje Allah ya kiyaye hanya idan Ka kaita ka wuce company zaka sami
Daddyn ku yana zaman jiran ka", Abdus-samad ya amsa da to.

Suna tsaye suna ɗaga musu hannu har suka fice daga gidan, kafin kowa kuma ya
shiga tashi motar ya bar gidan, domin tafiya wajen aiki.

Kamar yadda Mahaifiyar tashi ta umarce shi a hankali yake tuƙin, Fadila ta
kalle shi tayi murmushi.

Shima murmushin yayi sannan yace; "kin san umarnin uwa dole na cika shi",
Fadila tace; "ni ina tsoro sai nake gani kamar Hajja ba zata amince da wannan auren
ba".

Abdul cikin halin ko in kula yace; "to kada ta amince mana, ai ba ita keda iko
da ke ba", Fadila kai tsaye tace; "amma ai tana da iko da iyayen mu ko".

Bece komai ba banda hankalin shi daya mayar kan tuƙin shi, dai-dai kwanar layin
nasu yabi da kallo, tuno yadda suka yi kwanaki yasa yayi murmushi kawai.

Har ƙofar appartment ɗin su Hajjan ya kaita, Fadila ta buɗe ƙofa sannan ta
waigo tace; "na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, ga wannan dan Allah kada ka
manta ka taho mini dashi".

Ya amshi ƴar paper ɗin, rubutu ne wanda shi ba zai tantance meye a jiki ba, ya
kalle ta yace; "meye wannan", ta ɗan kauda kai tace; "abin amfani ne kai dai kawai
ka siyo mini", ya balla mata harara yace; "wato har kin fara aike na kenan".

Tayi dariya tana ficewa daga cikin motar, shi kuma ya girgiza kai kan ya ja
motar ya tafi, ya san ko yace zai shiga su gaisa ran shi ne kawai zai ɓace, gashi
zuwa yanzu ya san Fadil baya gida yana wajen aiki.
Hanyar Companyn kawai ya ɗauke, gudu yake shararawa sosai domin kuwa ya san
yayi latti gashi zuwa yanzu ya san Mahaifin nashi yana can yana zaman jiran shi.

*FARIDA AND SONS NIG LMTD*, sunan companyn nasu kenan, wanda kusan yayyin shi
ke jan ragamar companyn, yana parking ma'aikatan suka fara gaishe dashi, ya tsaya
suka gaisa cikin mutunci da girmama juna.

Kai tsaye ya wuce office ɗin CEO ɗin, inda a can ya sami Dr Abubakar na zaman
jiran shi, koda ya shiga basu wani jima ba.

Dr Abubakar ya kalli Sameer wanda ya kasance shine CEO a wajen yace; "ga ɗan
uwan ka nan zamu je yanzu mu dawo sai ka nuna mishi nashi office ɗin".

Sameer yace; "to", daga haka ya juya ya fice Abdus-samad ɗin na bin shi a baya,
motar Dr Abubakar ɗin suka shiga dukan su.

Suna tafiya ya juyo ya kalli Abdus-samad yace; "abinda yasa zaka yi aiki a
wancan companyn shine dan ka matsa kana so ka fara aiki amma yanzu zamu je inda
nake company ɗin yake ana ta aikin shine amma insha Allahu nan bada jimawa ba za'a
gama sai ka koma can", Abdul ya amsa da to.

Da ɗan tazara tsakanin wancan Companyn da wanda suka.je yanzu, a girma da faɗi
wanda suka baro yafi wannan sai dai yadda tsarin wannan yake ya bambamta da wancan.

Dr Abubakar yace; "wannan shine Compnyn ka shiga kaga yadda tsarin shi yake ni
zan wuce wajen aiki ne, idan naje zan saka driver ya kawo maka mota sai ka koma
wajen naka aikin", Abdus-samad yace; "to".

Dr Abubakar ya tafi yayin da Abdus-samad ahi kuma ya shiga ciki domin ganin
yadda tsarin companyn yake da duk yadda masu ginin ke aikin nasu.

********* ************

Nusram ke tsaye bakin titin da zai sadaka da Unguwar tasu, fuskarta tayi ja
tsabar kukan da taci, yau shine cikar kwanakin da aka ɗibar mata gashi har zuwa
lokacin bata sami wani wanda ya amsa zai aure ta ba.

akai-akai takan saka hannu ta share hawayen da yake zubo mata, kasancewar
hanyace babba wacce mutane kan gifta suna hada-hadar su kowa yazo wucewa sai ya
bita da kallo.

Ita kuwa duk ta ruɗe duk yadda ta dauki abin ya wuce haka, ta kalli samarin
dake tahowa, baya ta koma kaɗan ta jingina da ginin dake kusa da ita.

Koda suka ƙaraso gare ta, tayi musu sallama, duk suka kalle ta, cikin rawar
murya tace; "dan Allah mijin aure nake nema", wannan maganar ta basu dariya suka
kuwa dara.

Nusram ta share hawayen daya zubo mata tace; "auren mahaifiyata Babana ya ɗora
akan nawa yace idan ban fito da miji nayi aure ba a bakin auren ta, dan Allah ku
taimake ni".

Suka yi shiru suna kallon ta, dan kyau akwai kyau, hijab pink ta saka dogo har
ƙasa hakan ya hana ni ganin wane kalar kaya ne a jikin ta, ta janyo hijab ɗin ya
rufe rabin fuskar ta wanda sai ka natsu sosai zaka iya fahimtar wacece.

Ɗaya ya kalli ɗaya yace; "Bello ko zaka shiga daga ciki ne, ni dai ka san
yanzu ba zai yiwu na ɗaɗɗako aure ba ko?".
Wanda aka kira da Bello yace; "kai Aminu rabani da kyawawan matan nan, nifa
gwara na nemi dai-dai ni na aure, kaga kalar wa'innan kayi shiru kawai, waye ya san
me take aikatawa da mahaifin nata ya koro ta, ni dai kam ba zan iya ba kai dai idan
zaka aure ta to bismillah sai muje a toshe ƙofar naka ɗakin a maida shi ta cikin
gida".

Aminu yace; "bakada hankali ne yanzu ina naga kuɗin aure, sadaki akwati, waye
yace maka mace kamar wannan zata iya zama a irin gidan mu, ɗaki ciki ɗaya".

Jikin Nusram har rawa yake yi wajen durƙusawa ƙasa tace; "wallahi zan zauna,
ni dai dan Allah ku taimaka mini", suka kalli juna kafin Bellon yace; "kai anya
kuwa wannan mutum ce Aminu yau munyi gamo", da sauri suka fara tafiya.

Nusram ta bisu kamar sabuwar mahaukaciya tana kuka tana roƙon su, ganin hakan
yasa suka zuba a guje kowa na ƙoƙarin ceton ranshi.

Nusram kuwa ganin sun gudu yasa ta tsaya tana share hawayen da ya zubo mata,
bata taɓa ɗauka matsalarta zata girma ta kai hakan ba.

Duk masallatai da kuma ƴan layin su kowa gudun ta yake yi, yanzu gashi tazo
inda ba'a santa ba nan ma kallon aljana suke mata.

Tun safe take garari a hanya tana neman me auren ta amma ta rasa kowa ya
kalleta sai yace tafi ƙarfin shi, ko kuma be san me take aikatawa wasu ma kallon
zararriya suke yi mata.

Jin an fara kiran sallar Magrib yasa ta matsa can jikin wani masallaci ta zauna
dole ta sake tunani, ta jima zaune tana kuka tare da tunanin halin da zata shiga ta
kuma jefa auren mahaifiyar ta a ciki, kafin ta miƙe ta fara tafiya cikin galabaita.

Har ta ƙaraso gida babu wanda ya yarda da buƙatar ta, tana shigowa zaure Isa na
fitowa ganin yadda tayi.wujiga-wujiga yasa ya kwashe da dariya yace; "lallai na
ciri tuta ai dama na faɗa miki baki da miji sai ni", bata kula shi ba shi kuma be
fasa faɗan abinda ya ke son faɗa ba.

"ki shiga ciki Baba na zaman jiran ki ai", jin hakan yasa gaban Nusram faɗuwa,
cikin sanɗa ta leƙa tsakar gidan, Baba ne kuwa zaune saman tabarma yana faman
masifa.

Ta jima tsaye tana tararrabin ta shiga ko kada ta shiga, a ƙarshe dai haka ta
yanke shawarar shiga cikin gidan.

"eh da yake ni an raina ni.wato ke kaɗai zaki je Saudiar to naga wanda zai
barki kije ɗin" maganar da Baban keyi kenan wacce ta daki kunnuwan Nusram ɗin.

Nusram tayi sallama ta shiga, Baba yace; "yauwa an dawo daga yawon barikin, zo
nan", jikin Nusram ya kama rawa.

Ta tsuguna tace; "Baba gani", Baba yace; "ke wato dai sai kin kashe ni sannan
hankalin ki zai kwanto ko", Nusram ta girgiza kai.

"to wallahi baƙin cikinki ba zai kashe ni ba, kinfi ƙarfin kowa yanzu sai dai
mu zuba miki idanu ko?, ina ita me ɗaure miki gindin?".

Ummi dake zaune ƙofar ɗakin ta tace; "ina jinka ai faɗi abinda kake so ka
faɗa", Baba yayi ƙwafa yace; "yauwa ai ina so kiji da kunnen ki ne".

Ya kalli.Isa da Mama Jummai yace; "kuma ina so kuji abinda zan faɗa domin ina
so ku zama sheda".
Ya dawo da kallon shi kan Nusram sannan yace; "kin sami mijin auren", Nusram ta
girgiza kai tace; "dan Allah Baba kayi haƙuri".

Baba ya ɗaga mata hannu yace; "sati me zuwa ɗaurin auren ki da Isa", Ummi
tace; "wannan ne ba zai taɓa yiwuwa ba wallahi matuƙar ina da rai".

Baba ya miƙe yace; "shikenan sai ki fara shirya kayan ki na tafiya Dabai", babu
tsoro ko shakka Ummi tace; "to shikenan".

Nusram ta fashe da kuka ta riƙo ƙafar mahaifin nata tana faɗin; "dan Allah Baba
kayi haƙuri", ya zare ƙafar shi yace; "wallahi matuƙar wanda zaki aura be zo gobe
ba to sai Uwar ki ta bar gidan nan sannan kuma auren ki da Isa babu fashi", be jira
me zata ce ba yayi ficewar shi.

Nusram ta cigaba da kukanta cikin baƙin ciki, yanzu shikenan tayi sanadiyar
rabuwar iyayen nata kenan, Ummi tazo ta miƙar da ita tsaye tace; "kada ki damu muje
ɗaki".

Mama Jummai tayi shewa tace; "ahayye! Zamu gani dai idan tusa zata hura wuta ai
duk wanda yaja dani sai naga bayan shi".

Ummi ta juyo tace; "ta Allah ba taki ba, duk sharrinki akan ki zai ƙare", daga
haka taja Nusram suka shige ɗaki.

Mama Jummai tace; "ni yanzu ba zan ce miki komai ba amma ki sani ƴar ki zata
shigo hannun mu ne nan da lokaci kaɗan zaki gane ruwa shayi ne".

Nusram ta zuba tagumi tana kallon Ummi na haɗa musu kaya, Nusram tace; "Ummi
dan Allah kiyi hakuri ki bari na auri Isan kawai, in dai hakan zai saka ku cigaba
da zaman aure da Baba".

Ummi tace; "ki bar wannan maganar Nusram, ki haɗa naki kayan domin kuwa tare
zamu tafi dan wallahi ba zan taɓa bari ki auri Isa ba".

Nusram ta saka kuka tace; "ni kuma Ummi ba zan iya bari auren ku ya rabu ta
dalilina ba, Ummi me zan ce da Nusreen da kuma Kubra", Ummi tace; "ba wannan na
tambaye ki ba, ki tashi ki.haɗa kayan ki kawai".

Dole.haka Nusram ta fara haɗa kayan ta, tana yi tana kuka, Ummi kuwa ta miƙe
ta fice don ɗauro alwala tazo ta tada sallah.

Ganin.fitar Ummi yasa Nusram miƙewa, jakar ta ƙarama ta ɗauko, kuɗin da Aunty
ta bata ranar da taje gidan ta ɗauko ragowar ta saka a ciki ta ɗauki wayar wannan
da bata san ko waye ba ta saka a ciki sannan ta saka hijab ta fice.

Akan ta dai ake faɗa ko to gwara ta bar gidan, dan ita ganin ta hakan shine
maslaha kawai ba zata iya zama taga wannan ranar ba wacce zata kasance itace ta
zama silar rabuwar iyayen nata.

Sai yanzu take data sani ta amsa auren Yaya Sulaiman ɗin wata ƙila ta sami
mafita akan wannan bala'in da yake tinkaro ta, ta juya ta kalli gidan Allah sarki!
Ummi ko yaya zata ji idan ta gane cewa guduwa Nusram ɗin tayi?.

Wane hali Ƴar uwar haihuwar nata zata ji a yayin da labari ya iske mata akan
abinda Nusram ɗin tayi, yanzu ƴan layi dasu Mama Jummai zasu sami damar gorantawa
Ummin, anya kuwa abinda kike so ki aikata Nusram ba kuskure bane?"abinda zuciyar ta
ke faɗa mata kenan.
Ta girgiza kai tace; "wannan itace kawai mafita akan abinda ke damuna, dama ace
Ummi zata yarda ne na auri Isan da rabuwar auren su ai gwara auren Isan", ta ƙara
sauri a ƙoƙarin ta na ganin ta bar inda aka santa.

Haka ta iso bakin titi, lokacin ma yawanci mutane sun shiga sallar Isha'i, ta
ƙara damƙe jakar dake hannun ta, kuɗin ciki tana tabbacin zai ishe ta ta sauka wani
garin idan yaso sai ta siyar da wayar nan ta sami wajen zama da kuma jarin da zata
riƙe kanta.

#LIKE
#SHARE
#COMMENTS

*babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

📖📖47-48📖📖

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

Addu'a A Kan Abokan Gaba


‫َأ‬
‫ َالَّلُهَّم اْهِزْمُهْم َوَزْلِزَلُهْم‬،‫ اْهِزِم ْال ْحَزاَب‬،‫ َسِريَع اْلِحَساِب‬،‫َالَّلُهَّم ُمْنِزَل اْلِكَتاِب‬.

Allahumma! Munzila-l-kitabi, sar'a-l-hisabi! Ihzimi-l-ahzaba. Allahumma ihzimhum wa


alzihlum.
Ya Allah! Mai saukar da littafi, Mai gaggawan sakamako! Ka karya kungiyoyin abokan
gaba. Ya
Allah! Ka karya su, ka girgiza su.

*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖47-48📖📖

Abdus-samad yayi miƙa tare da yin hamma, agogon hannun shi ya duba ƙarfe shida
harda rabi, gaskiya ya gaji daga fara aikin shi yau.

Cikin sauri ya fara tattara kayan shi domin tafiya, Tameer ya turo ƙofar ya
shigo, ganin yadda yake haɗa kaya yasa yayi dariya yace; " duk ɗokin aikin kuma har
ka gaji".

"amma dai ka san lokacin tashi ya wuce ko, a ƙa'ida 4 ya kamata ace na bar nan",
Tameer ya buɗe baki cikeda mamaki yace; "a matsayinka na Co-ordinator".

Ya.lumshe ido yace; "as normal staff bari ka gani na gudu wajen First Love", be
jira me zai kuma cewa ba ya fice.

A harabar Companyn ya haɗu da Surayya, "yauwa wuce mini da wannan gida, ki cewa
First Love zan je Rigasa", ta amsa da to.

Ya shiga motar shi ya tafi, a hanya a ka fara kiraye-kirayen sallah wannan


dalilin yasa ya sami masallaci yayi parking sai da ya idar da sallah sannan ya
tafi.

Wani ƙaramin Mall yayi parking, ya ɗauko takardar ya juya ta a hannun shi, shi
dai gaskiya babu abinda ya fahimta game da takardar.

Ya duba cikin Mall ɗin mutane ɗai-ɗaiku ne a ciki, wata matashiyar budurwa ya
hango da sauri ya nufi inda take.

"amm dan Allah taimaka mini da wannan takardar", Yarinyar ta juyo, a tare suka
zaro idanu.

Cikin mamaki Khausar tace; "Abdus-samad", yayi murmushi yace; "dama kecce", ta
jinjina kai tana dariya.

"me kazo yi, mu ga takardar", ta faɗa tana miƙo hannu, ya saka mata takardar, ta
ɗan jima tana dubawa sannan ta ɗago tace; "na san dai ba ƙanwarka ta aiko ka ba
haka ba Mama bace, faɗa mini gaskiya budurwar ka ce ko?".

Ya shafa sumar kanshi yace; "in faɗa miki gaskiya, ƙanwata ce ta aiko ni", a
tare suka yi dariya.

Ta janyo kwando ta miƙo mishi tace; "to sai ka riƙe muje ko?", be musa ba, tana
gaba yana bayan ta haka suka dinga zagaya wajen sai da ta tabbatar da ta ɗauki duk
abinda ke list ɗin sannan suka wuce wajen biyan kuɗi.

Atm ya miƙa musu suka zare kuɗin su duka, sannan suka zuba musu a leda, duka
ya ɗauka suka fice.

Khausar ta tsaya jikin motar ta tace; "to daga barin asibiti kuma shikenan sai
naji shiru".

"wallahi abin ne ya kwanta mini sosai, amma kiyi haƙuri na miki alƙwari zan zo
insha Allahu", Khausar taja ajiyar zuciya kafin ta saka hannu cikin purse ɗin ta
sannan ta zaro wayarta ta miƙa mishi tace; "idan na baka number na gaba cewa zaka
yi ka manta amma yanzu ka saka mini taka sai ni na nemeka dan ni ba zan manta ba".

Abdus-samad yayi murmushi kafin ya amshi wayar ya rubuta mata sannan ya miƙa
mata tare da ledar siyayyar ta, yace; "na gode sosai, bye", ta ɗaga mishi hannu.

Wajen motar shi ya nufa, ya buɗe ya shiga sannan ya tada ya tafi, Khausar tayi
dariya cikin farin ciki tace; "mafarkina zai zama gaskiya🙄, cikeda murna ta shiga
motarta ta bar harabar wajen.

Koda ya isa Hayin rigasa, cikin Estate ɗin a cike yake da mutane, sai da ya
tsaya suka gaggaisa da mutane ya san dama hakan zata kasance idan yayi la'akari da
yadda family meeting ɗin su ya matso duk wani na nesa cikin wannan satin suke saka
rai da zuwan shi.

Da sallama ya shiga falon, yaron dake wasa ya nufo inda yake, Abdus-samad ya
ɗaga shi sama ya cilla sannan yace; "my Boy yaushe kuka dawo", yaron yace; "jiya
muka zo tare da Daddyna".

Ya ajiye shi ƙasa sannan ya riƙe hannun shi, Brr Hauwa ke zaune saman sofa
gabanta Laptop ne tana dannawa sai Fatima ita kuma takardu take haɗawa.

Abdus-samad ya gaishe dasu, babu laifi duka sun amsa musamman ma Fatima dan ita
basu da wata matsala a tsakanin su.

Hanyar ɗakin Malama yayi, Fatima tayi saurin kiran shi, ya juyo zuwa gare ta,
"Hajja na ciki ka shiga ka gaishe da ita tukunna", abinda ta faɗa kenan.

Ya san me take nufi don haka babu wata gardama ya nufi nata ɗakin, a kashingiɗe
take da jarida a hannun ta.

Yayi murmushi, "wato yau bokon ta tashi kenan da daddare", ya faɗa cikin ranshi
ta ɗago tana amsa mishi sallamar da yayi.

A ƙasa kusa da ƙafarta ya zauna, ta dube shi ta ɗauke kai, "barka da dare Hajja,
ina wuni", ta ɗebi sakwanni kafin ta amsa da "lafiya", daga haka be kuma cewa komai
ba itama bata kuma cewa komai ba.

Tsayin lokaci babu wanda yayi magana, ya miƙe yace; "Hajja sai da safe", har ya
fita be ji amsar abinda ta faɗa ba, ta bi bayan shi da sannan tace; "Allah ya tashe
mu lafiya".

Tun kafin ya shiga ɗakin yake jiyo muryar su wanda hakan yake tabbatar mishi da
cewa fira suke kenan.

Da sallama ya shiga ɗakin, ya zauna saman kujera yana dafe kanshi, Fadila ta
ƙaraso inda yake ta janye hannun nashi tace; "duk gajuyar ce".

Ya balla mata harara sannan ya miƙe, kusa da Malama ya koma, "ina wuni?", sai da
ta shafa fuskar shi sannan ta amsa da "lafiya lau, ina Maman ka?", yayi murmushi
yace; "tana lafiya".
Ledar daya ajiye Fadila ta ɗauka tana murmushi tace; "ah lallai matar ka ta
huta", bece mata komai ba sai ma miƙewa da yayi.

Fadil yace; "ba dai har zaka tafi ba", ya lumshe idanu yace; "Fadil na gaji da
yawa, dole ce ma ta biyo dani nan ɗin amma da gida zan wuce wallahi", Fadil ya miƙe
domin raka shi nan ya yiwa Malama sallama sannan ya fice.

Yadda ya bar su haka ya dawo ya same su, sai dai wannan karon Brr Hauwa, waya
take amsawa, sai da safe yayi musu sannan ya fice.

"to bari na bar ka a nan sai da safe", faɗar Fadil kenan bayan sun ƙaraso inda
ya ajiye motar shi, ya miƙa mishi hannu suka yi musabaha sannan ya buɗe ya shiga.

Ya kunna motar kenan, Saleema ta ƙaraso da murmushi a fuskarta ta ƙwanƙwasa


glass ɗin, sai da yayi jim sannan ya zuge glass ɗin.

"wannan wane kalar zagaye ne, ya zaka shigo ka tafi dan danan?", ya lumshe
idanu yace; "Aunty Saleema na gaji ne sosai".

Ta langwaɓar da kai tace; "amma ai ka ƙaraso ko ganin ka nayi kafin ka wuce


ko?", ya shafa gashin kanshi yace; "wallahi sauri nake yi".

"dan Allah mu ƙarasa mana, jin zuwan ka har na shiga kitchen na dafa maka abinci
yanzu kuma kace sauri kake yi", ya ɗaga kafaɗa sannan ya buɗe mata ƙofa.

Tayi murmushi sannan tace; "yauwa ko kaifa", ta shiga sannan ya tada motar suka
ɗauki hanyar Part ɗin su.

Tare suka jera har cikin gidan, duka suna zaune a falo, yana shiga suka yo
kanshi, ya dafe goshi wannan dalilin yasa baya son zuwa gidan gabaki ɗaya.

Saleema ta jera mishi abincin a gaban shi, Haɗaɗɗen spouch chicken da kuma milk
shake, be wani ci da yawa ba domin gajiyar dake tattare dashi a yanzu kawai
kwanciya yake buƙata.

Sallama yayi musu sannan ya fito inda Saleema ta biyo shi don ta rakashi,
"yausha Abba zai dawo", ta ɗan yi jimm sannan tace; "ba zai wuce sati me zuwa ba
Abban Nihal kuwa yana hanya", ya ɗan ja numfashi sannan yace; "Allah ya kawo su
lafiya", ta amsa da ameen, da haka suka yi sallama inda ya shiga motar shi itama
kuma ta juya cikin gida.

Shi ya san ba lallai a ƙare lafiya ba, a duk shekara babu ranar da yake tsoron
zuwan ta irin wannan ranar ba ta yin meeting ɗin su, ya shafa kan shi yana faɗin;
"ya Allah!".

Kamar ance ya kalli gefe ya hangota tsaye a bakin titi, kallon ta yayi sosai ya
lura kamar bata cikin hayyacin ta, har ya gifta sai kuma ya dawo a hankali ya yi
parking.

Glass ɗin ya sauke sannan ya leƙo da kanshi, Nusram dake zare idanu, tana ƙare
damƙe jakar dake hannun ta, ganin wanda ya leƙo yasa ta ɗan ja baya kaɗan.

Yayi murmushi yace; "ina zaki je?", Nusram ta haɗiye wani mugun yawu sannan ta
fara tafiya cikin sauri, ai gwara ta koma gida ko kuma ta hau titin mota ta bige ta
da wannan mugun mutumin.

Abdus-samad kuwa ganin hakan yasa yayi saurin buɗe motar ya fito, ganin tana
ƙoƙarin kwasawa da gudu yasa ya cafkota.
Ta wage baki zata yi ihu yayi saurin saka hannu ya toshe bakin, "kin manta
abinda na faɗa miki kenan ko?", da sauri ta girgiza kai.

Kasancewar kowa hada-hadar shi yake yi ya saka babu wanda ya lura da halin da
suke ciki, hannun ta ya riƙe ya jata har zuwa mota ya buɗe ya saka ta sannan shima
ya shiga ya ja suka bar wajen.

Nusram babu abinda take yi banda zare idanu, tunanin ta ɗaya shine ta gama
rayuwa ita kam tata ta ƙare.

"ina zaki je?", kamar daga sama taji tambayar, bakin ta na rawa tace; "ina so na
bar garin nan ne", ya ɗan juyo ya kalle ta kana ya sami waje ya tsaya.

Sosai yanzu yake kallon ta yayin da ita kuma take faman wasa da yatsun hannun
ta, sai da ya nazarce ta sosai kana yace; "kada dai kice mini gida kika bari".

Ta ɗaga kai tana cigaba da abinda take yi, ya girgiza kai yace; "kada ki sake ki
fara wannan kuskuren, kin san me zaki tarar a inda zaki je ko kuwa kina tunanin
matsalar da kike ciki wacce zaki tarar ba zata kaita ba, kina da tabbacin wani abu
ba zai same ki ba, kina da iyaye wane hali zasu kasance? Kina da ƴan uwa bakya
tunanin su, kin san kalar rayuwar da zaki shiga, kin san meye matsayin mace me
zaman kanta?".

Ta girgiza kai, ya ɗan ja numfashi yace; " *KARUWA*!, kin shirya amsa wannan
sunan", Nusram idanun ta ya kawo ƙwalla.

Hannu ya saka ya zaro tissue ya miƙa mata, ta amsa ta goge hawayen dake fuskarta
tace; "to ai na rasa wanda zai aure ni ne", ya ɗan yi jim sannan yace; "kamar ya
kenan?".

"Baba ne yace na fito da mijin aure kafin sati biyu, gashi sati biyun ya cika ni
kuma bana da tsayayyen saurayi wanda zai aure ni".

Ya jima sosai kafin yace; "yanzu bari na maida ke gida gobe zan zo na sami
mahaifin naki", ta ɗago da sauri ta kalle shi tace; "zaka aure ni ne?".

Shiru yayi be tanka ba, Nusram ta kuma cewa; "idan har ka san ba aure na zaka yi
ba kawai ka barni na tafi", kamar an fizgo maganar yace; "naji na amince zan aure
ki".

Daga haka babu wanda ya kuma magana, ya tada motar ya juya zuwa maida ita
gida har suka isa ƙofar gidan babu wanda ya kuma magana.

Bayan yayi parking be ce komai ba, ganin hakan yasa Nusram buɗe ƙofar, har ta
saka ƙafarta waje sai kuma ta dawo.

"ka tabbata zaka zo goben", babu wani dogon tunani ya ɗaga mata kai, tayi
murmushi tace; "ni ban damu da sai munyi zaman aure ba, koda dai sati ɗaya ne, sai
ka ƙyale ni na tafi", ya gyaɗa kai, tayi murmushi ta juya ta fice.

Abdus-samad ya bi bayanta da kallo yana tunani haka gaban shi yana faɗuwa, "wane
matsala kake ƙoƙarin jefa kanka a ciki ne?", ya faɗa yana dafe saitin zuciyar shi
dake bugawa da ƙarfi.

#LIKE
#SHARE
#COMMENT
*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖49-50📖📖

cikin natsuwa yaja motar shi ya bar ƙofar gidan, duk yadda yaso yayi tunani abin
yaci tura dole ya watsar da komai ya maida hankalin shi kan tuƙin da yake yi.

Ƙarar shigowar saƙo wayar shi yasa ya kalli wayar, be duba ba dan be kawo wani
me mahimmanci bane.

Ta ƙofar baya ya shiga gidan nasu domin baya so ya haɗu da kowa babu abinda yafi
buƙata a lokacin irin ya kwanta ya huta.

Yana shiga ɗakin shi bayi kawai ya wuce kanshi ya sakarwa shaya, ruwan na sauka
a jikin shi ya lumshe idanu, gaba ɗaya abubuwan daya faru ya fara dawo mishi.
Cikin sauri ya buɗe idanun shi yana dafe kanshi yace; "me ka janyowa kanka Abdus-
samad?", tambayar da babu amsa kenan.

"koda yake ai idan ka yiwa mahaifinta bayani zai fahimce ka domin kuwa babu
wanda zai so ƴar shi ta faɗa wannan halim", abinda zuciyar shi ta faɗa mishi kenan.

Koda ya fito ya tsane jikinshi sannan ya ciro kayan barci ya saka, jikinshi ya
feshe da turare kana ya janyo wayar shi.

*love is hard and will always be, but remember somebody loves u and that one is
me*

Abdus-samad ya taɓe baki, number ne babu suna dan haka be damu da sanin waye ba
domin kuwa irin wa'innan saƙonnin har gajiya yake da buɗe su.

Be jima sosai ba barci ya kwashe shi, Brr Farida kuwa jin shirun yayi yawa yasa
ta nufo part ɗin shi, kamar yadda ta zata ya dawo ɗin, zuwan ta na uku kenan sannan
ta tarar dashi.

Ɗakin da duhu sai dai ƴar fitilar gefen gado dake kunne, tayi murmushi sannan ta
taka zuwa kusa da gadon.

Ta jima tana yin addu'a kafin ta tofa a hannun ta kana ta shafa mishi a jiki,
yayi juyi cike da gajiya, Brr Farida tayi murmushi kawai.

Ta san dama hakan zai faru shiyasa koda ya dage akan zai fara aiki ta hana,
ranar farko kenan duk yabi ya gaji.

Cikin natsuwa ta fara mishi tausa, aikuwa malam Inusa🤣 harda ajiyar zuciya, ta
jima sosai kafin taja mishi blanket ɗin, peck tayi mishi a goshi kafin ta fice daga
ɗakin.

Nusram kuwa koda ta shiga gida bata sami kowa a tsakar gidan ba, cikin sauri ta
tura ƙofar ɗakin nasu wanda tana da tabbacin Ummi ta turo ƙofar ta shige.

Ummi dake saman abin sallah ta juyo tana kallon Nusram ɗin, Nusram ta saukar da
kai ƙasa tana wasa da hannun ta.

Ummi tace; "daga ina?", Nusram tace; "Ummi dan Allah kiyi haƙuri", Ummi ta
girgizai kai kawai, cikin sauri Nusram ta shige cikin ɗaki.

hijab ɗin jikin ta, ta cire sannan ta faɗa saman katifar su, lallai rayuwa
kenan, wayar dake cikin jakar ta ciro kamar koda yaushe hoton shi dai shine take
kallo.

"ashe dai a cikin masu shan jini akwai nagari? To kodai kema siyar dake zai yi
ko kuma ya bawa gunki jinin ki?", abinda zuciyar ta take raya mata kenan.

Zumbur ta miƙe zaune, "koda yake ma ai gwara ya bawa aljanin jini na ko na huta
da wannan rayuwar", wata zuciyar ta sake faɗa mata haka.

Addu'a tayi kafin ta kwanta, bata jima ba barci ya kwashe ta, tana me fatan gobe
ta sami mafita.

Washe gari da safe bayan sun idar da sallar asuba, Baba yazo ƙofar ɗakin nasu ya
ƙwalawa Ummi kira.

"Maimuna fito", Ummi ta miƙe ta fice, ya kalle ta ya kauda kai yace; "fatan dai
kin haɗa kayan ki na tafiya ko?", Ummi cikin dakiya tace; "eh ko korata kake ne na
tafi yanzu", ya ɗaga kafaɗa yace; "kusan hakan ai".

Ummi ta girgiza kai sannan ta juya zuwa ɗaki, Nusram dake tsaye tana jiran Ummin
domin taji duk abinda ya gudana, Ummi ta kalle ta tace; "ɗauko jakunkunan mu tafi".

Nusram hawaye ya kawo mata, ta girgiza kai, da sauri Ummi ta girgiza mata kai
tace; "kada ki soma Nusram ya kamata ace zuwa yanzu kin sami.ƙarfin zuciya, ɗauko
kinji", Ummi ta ƙarasa tana ɗaukar Kubra kasancewar bata tafiya har lokacin.

Ummi na gaba Nusram tana bayan ta suka fito, zuwa wannan lokacin Mama Jummai da
Amira harda Isa duk suna tsaye a waje.

Baba yace; "wai keda waye zaki tafi?", Ummi tace; "bangane ba, nida yarana
mana", duka wajen suka kwashe da dariya, banda Nusram dake sharar hawaye.

Baba ya harare ta yace; "to ai dana auro ki ba tare dasu aka kawo ki ba", Ummi
ta haɗe rai tace; "kamar yadda banzo na tarar dasu a nan gidan ba", daga haka ta
nufo hanyar fita.

Baba ya saka hannu ya finciko Nusram yace; "wannan dai me kama da aljanun zaki
iya tafiya da ita amma wannan kam babu inda zata je, ba zata gama ɓata yaran birni
ba ta koma ƙauye ta ɓata na can, idan naje ana mini kallo arziƙi ta zubar mini da
mutuncina ba".

Dan haushi Ummi bata ko juyo ba, jakar dake hannun Nusram ta fincike ta fice
kawai, Nusram ta fashe da kuka tana kiran Ummin, amma bata juyo ba.

Baba ya rufe Nusram ɗin da duka yana faɗin; "shegiya ƴar iska, yanzu ke har kina
da bakin ihu, ne baƙin jini kawai, ko karya takan sami karen da zai bita amma banda
ke".

Nusram kuwa banda sunan Ummi babu abinda take ambata, babu wanda ya bawa Baba
haƙuri har sai da ya gaji dan kanshi ya ƙyale ta.

bayan tafiyar shi Mama Jummai ta kwashe da dariya tace; "ai duk wanda yaja dani
dole ya yi nadama, wato tunanin ki zaki je Dabai ki huta ko, to babu inda zaki je
kina nan tare dani, aure kuma sai dai kiga anayi".

Isa ya ɓata rai yace; "kin manta Jummai nine fa zan aure ta", Mama Jummai tace;
"ai auren ku da rashin shi duk ɗaya ne domin na rantse ba zata taɓa jin daɗin auren
ta ba".

Suka kuma fashewa da dariya, Nusram kuwa hawaye kawai take yi har lokacin, ga
ƙafarta dake zafi.

har wajen sha biyu tana tsugune a wajen, babu wanda ya tanka mata, sallamar
Nusreen itace ta dawo da ita hayyacin ta.

Cikin sauri ta miƙe, Nusreen kuwa ganin halin da ƴar uwarta take yasa ta taho da
sauri, Nusram ta ƙarasa kusa da ita suka rungume juna.

"Rim Ummi ta tafi ta barmu", jikin Nusreen a sanyaye ta janye Nusram ɗin daga
jikinta tace; "me kike cewa ne?".

Nusram taja hannun Nusreen ɗin suka nufi ɗakin nasu, kan kujera ta zaunar da ita
sannan ta bata labarin abinda ya faru.

Nusreen ta fashe da kuka, Nusram ma tana sharar hawaye tana rarrashin ƴar uwar
tata.
"Ram haƙiƙa kina ganin rayuwa, kowa yana da tashi ƙaddarar ke kuma taki kenan,
Nusram waye zai tunanin mahaifin daya haife mu shike bin mu da mugun baki", ta
ƙarasa tana kuma fashewa da kuka.

Nusram tace; "kiyi haƙuri Rim kowa da yadda rayuwa take zuwar mishi, Nusreen
Ummi bata a cikin gidan nan ya zanyi da rayuwa ta".

Nusreen ta share hawayen fuskarta kafin tace; "zan yiwa Hubby magana sai mu tafi
tare dake idan yaso sai ki zauna a wajen Hajiya, kin san dama tana sonki sosai".

Nusram ta girgiza kai tace; "ba za'ayi haka ba, nifa jiya na sami wanda zai aure
ni", cikin sauri Nusreen tace; "waye kenan?".

Nusram ta janyo wayar dake jakar ta sannan ta miƙawa Nusreen tace; "kalli kiga
hoton shi", Nusreen ta zuba mishi idanu kafin tayi murmushi tace; "wannan ai Abdus-
samad Abubakar Nagimi, ɗan attajirin me kuɗi ne ina kuka haɗu dashi".

nan Nusram ta kwashe duka labarin komai ta bawa Nusreen ɗin, Nusreen baɓu abinda
take banda murmushi.

"baban shi shine ogan Hubby kafin ya rasu, mutumin kirki ne Nusram ba wai ɗan
yankan kai bane, har bikin mu yazo fa", ta ƙarasa tana kwashewa da dariya tunawa da
tayi da yadda Nusram ɗin ta dinga shirme, Nusram tayi murmushi kawai.

Sai lokacin ta lura da yadda Nusreen ɗin tayi ƴar ƙiba ga haske data ƙara,
Nusram ta girgiza kai tace; "kinga yadda kika koma kuwa?", Nusreen tayi dariya.

Suna zaune wayar Nusreen ɗin tayi ƙara, ganin Aunty ke kira yasa ta ɗaga, nan ta
bata labarin abinda ya faru.

"kada ki damu Maman ku ta kira ni ta faɗa mini komai gobe zan zo na tafi da
Nusram ɗin", Abinda Aunty ta faɗa kenan.

Nusreen tace; "Allah ya kaimu shikenan Aunty sai anjima", daga haka suka katse
wayar, nan ta bawa Nusram labarin abinda Aunty ta faɗa.

Nusram kuwa tagumi kawai tayi, tunani kala-kala shine cikin ranta, shin zai zo,
ko kuwa zata cigaba da zama da Mama Jummai ne ko kuwa Aunty zata sami nasarar
rabata da gidan?, wa'innan sune abinda ke kai kawo cikin ranta.

Abdus-samad dake zaune cikin office ɗin shi, ya dafe kai, ba zai ce ga
dalilin daya saka lokaci zuwa lokaci abin yake faɗo mishi a rai ba.

Iska ya furzar daga bakin shi, be san yadda abubuwa zasu tafiyar mishi ba, amma
dai tabbas yana ji a jikin shi wani abu zai faru dashi jin yadda gaban shi ke
faɗuwa akai-akai.

Biyar ya bar company ɗin ya ɗauki hanyar hayin rigasa, be shiga cikin gidan ba,
ɗakin Fadil kawai ya wuce.

Wanka yayi ya canza kaya kafin ya shiga ciki, babu kowa a falo hakan yasa ya
wuce ɗakin Malama kawai.

Tana zaune da alƙur'ani a gabanta, ya saki murmushi matar tana birge shi saboda
yawan bautar da take dashi.

Malama ta miƙo mishi hannu alamun ya taho, Abdul kuwa kamar dama abinda yake
jira kenan dan haka cikin sauri ya nufi inda take.
Kan ƙafar ta ta kwantar da kanshi sannan ta saka hannu tana shafa gashin kanshi,
dama ga damuwa tayi mishi yawa ga gajiya kuma dan haka babu jimawa barci ya ɗauke
shi.

Malama ta tsurawa fuskar shi idanu, hawaye ya taru a idanun ta, ta fara karanto
addu'a tana tofa mishi.

Cikin barci yaji ana jijjiga shi, ya buɗe idanu ganin Fadil yasa yaja tsaki,
Fadil yayi dariya yace; "ka tashi malam shida tayi fa", jin abinda Fadil ya faɗa
yasa yayi saurin miƙewa zaune.

"please taso muje ka rakani", abinda Abdus-samad ɗin ya faɗa kenan yana miƙewa,
Fadil yace; "ina zaka je?", Abdul yace; "kai dai muje kawai".

A motar Fadil ɗin suka fice, suna tafe duk yadda Fadil ke tambayar shi inda
zasu je be bashi amsa ba har suka ƙaraso ƙofar gidan.

Fadil ya kalli ƙofar gidan sannan ya juyo ya kalle shi yace; "har yanzu baka
bani amsata ba", Abdul ya buɗe motar kawai ya fito.

Baba da Isa dake zaune saman dakalin ƙofar gidan suka bi su da idanu, Abdus-
samad suka yi musu sallama suka amsa.

"amm dan Allah me gidan nan nake nema", Baba yace; "gani nan yaro ya akayi",
Abdus-samad yace; "dama nazo ne muyi magana dan Allah idan babu damuwa".

Baba ya tashi ya bi shi suka dan matsa gaba, Baba ya kalle shi yace; "kai nake
sauraro", Abdus-samad yace; "dama nazo akan maganar ƴar ka Nusram ne abinda ya
far.......".

Yayi saurin dakatar dashi yace; "ba dai akan maganar Nusram kazo ba?", Abdus-
samad ya jinjina kai, Baba ya kamo hannun shi yace; "muje".

Abdus-samad cike da mamaki yake bin shi, Baba ya kalli Isa yace; "tashi mu
ƙarasa masallaci", Isa ya miƙe, haka Fadil ma ya biyo bayan su.

Masallacin dake kusa dasu suka ƙarasa, kasancewar lokacin sallah ya matso hakan
yasa mutane keta alwala, dan haka Baba ma ya ɗauki buta.

Ya kalli Abdus-samad da Fadil dake tsaye yace; "bismillah mana kuyi alwala",
cikin sauri duka suka ɗauki buta domin alwala, shi dai Abdul gaba ɗaya jikin shi a
sanyaye yake.

Be gama girgiza ba sai da aka idar da sallah yaji Baba yana sanar da akwai
ɗaurin aure dan Allah, ya matsa kusa da Liman suka ɗan tattauna sannan ya kalli
Abdus-samad yace; "matso mana ɗan nan".

Abdul ya matso kusa da Baban, Liman yace; "menene sunan ka?", Abdul yace;
"Abdus-samad Abubakar", gana nan yaga Baba ya ciro kuɗi daga aljihun shi ga miƙawa
liman yace; "sadakin ma ni na biya dan Allah ɗaura kawai".

Kafin Abdul yayi dogon tunani yaji kawai Liman yana sanar da ɗaurin aure, ya
kalli Baba ya kalli Liman ɗin da kuma maƙwabcin Baban wanda shine yake wakili ga
ango, shi dai su suke kiɗan su suke rawar su.

*AN ƊAURA AUREN ABDUS-SAMAD ABUBAKAR TARE DA NUSRAM ABDULLAHI DABAI, AKAN
SADAKI NERA DUBU GOMA SHA BIYAR LAKADAN BA AJALAN BA!!!* dogon bayanin dake yawo
cikin ƙwaƙwalwar Abdus-samad kenan.

Cikin firgici da kuma razana ya ɗago yana kallon Baban yana girgiza kai, maida
kallon shi yayi kan Fadil ɗin wanda yake zaune kamar gunki dan idan banda numfashi
dake sauka babu yadda zaka fahimci akwai rai a jikin shi.

*To masu karatu, zan dakata anan saboda isowar Azumi idan Allah ya kaimu gobe da
rai da lafiya dan haka ina taya kanmu murnar zuwan wannan wata me albarka Allah ya
magance mana wannan babbar annoba da take damun mu wato Covid19, Allah yasa muga
ƙarshen watan lafiya, idan Allah ya kaimu bayan sallah da rai da lafiya zamu ɗora
daga inda muka tsaya*.

*godiya ta musamman gare ku, mabiya wannan littafin, irin su, Abdul Ƙiru, Ibnatu
Baballe Barau, Maman Abdul, Aishatu Babayo, Faɗimatu, Khadija Zakariyya da duk
sauran wa'inda ban.amabata ba na gode sosai Allah ya haɗa mu da rai da lafiya*.

*HAPPY RAMADAN IN ADVANCE*

#LIKE
#SHARE
#COMMENTS

*babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*
*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖51-52📖📖

Abdus-samad be dena zare idanu ba har aka watse daga masallacin, Liman ya ɗan
taɓo shi sannan yayi firgigit ya miƙe tsaye.

"ku taimake ni kada ku ɗaura auren nan nifa ba soyayya muke da ita ba", abinda
yake faɗa kenan.

Baba cikin fusata yace; "bangane abinda kake nufi ba ina dama kai kace maganar
ta kazo mini, ni kuwa na san idan banda maganar auren ta babu abinda zai kawo
saurayi waje na, ko kana cikin kwartayen ta ne?", Abdus-samad ya girgiza.

"amma baka fahimce ni ba, nifa maganar da nazo muyi daban taya zaku ɗaura mana
aure babu sanin iyaye na?", Abdus-samad ya faɗa cikin damuwa.

Abba ya ɗaga kafaɗa yace; "wannan kuma matsalar kuce ni dai yanzu zata bar
gidana idan yaso tunda baka sonta kaje ka kashe ta", wani abu Abdus-samad ya haɗiye
jin abinda Mahaifin nata ya faɗa.

Liman yace; "ya isa haka, ku zauna ayi maganar data dace", duka suka sami waje
suka zauna kamar yadda yace.

"kai menene ainihin abinda ya kawo ka wajen Malam Abdullahi?k, tambayar da liman
ya jefowa Abdus-samad ɗin kenan.

Labarin komai ya kwashe ya faɗa mishi na yadda ya ganta zata gudu da yadda yayi
mata magana akan gobe zai zo ya ɗora da cewa; "gani na mahaifin ta ne shi ba zai so
ƴar shi ta bar gidan shi ba dole zai janye maganar aurar da ita kota yaya ne".

Liman ya jinjina kai yace; "tabbas yaro kana da gaskiya, Malam Abdullahi wato
duk wani abu dake faruwa akan yaranka babu wanda bamu sani ba, shiru kawai muke yi
saboda gudun katsalandan domin kuwa iyayen yanzu basu so ana musu irin wannan
shisshigin Malam Abdullahi matsi da takura akan yaran yanzu daman irin abinda yake
haifarwa kenan, yanzu baka gudun ace lokacin data tafi taje ta faɗawa abinda be
kamata, gaskiya wannan abin sam be dace ba ka gyara ƴaƴa amanace Allah ya bamu kuma
idan bamu riƙe su da kyau ba zamu fuskanci fushin shi dan haka ya kamata mu gyara
tarbiyar yaran mu".

Sannan kai, ya faɗa yana juyowa ya kalli Abdus-samad; "sai dai kayi haƙuri aure
dai ya riga da ya ɗauru amma tunda iyayen ka na nan zamu je sai ayi musu bayani".

Cikin sauri Abdus-samad yace; "a'a nima zan iya yi musu bayani da kaina, amma
dan Allah ku raba auren nan".

Baba yace; "aifa sai dai duk abinda zai faru ya faru amma wallahi yau ta bar
gidan nan, bari ma ku gani", ya miƙe tsaye sannan ya fice daga masallacin.

Duka suka bi shi da idanu kafin Liman ɗin ya kalli Abdus-samad yace; "haƙuri ya
kamata kayi Abdus-samad kaga yarinyar nan tana ganin rayuwa a cikin gidan mahaifin
ta, dan a dalilin rashin auren nata yau sai da mahaifiyar ta, ta bar gidan......"
nan Liman ya bashi kaɗan daga cikin abinda ya sani wanda yarinyar take fuskanta.

Ya nuna kanshi yace; "ni nan da kaina ta kawo mini cigiyar miji kwana uku da
suka wuce tana kuka tana roƙona to abinda yasa ma dan bana da ɗa namiji ne kuma
matana huɗu amma da na tsame ta daga damuwar da take ciki, sai dai hakan be samu ba
domin kuwa babu wanda ya amince saboda waccen abinda ya faru ranar auren ta, kayi
haƙuri ka amshi auren nan domin kuwa wataƙila kai ne Allah ya turo domin ka taimake
ta ka fitar da ita daga cikin ƙangin da take ciki shekara da shekaru, yarinya ce me
haƙuri da sanyi zaka ji dadin zama da ita, dan Allah kada ka juya mata baya, laifi
dai mun riga da munyi domin ya kamata ace mun tambaye ka kafin mu ɗaura auren sai
dai ance kaddara ta riga fata, dan haka kayi haƙuri ka amshi auren nan hannu
bibbiyu ina fata da kuma buri akan ba zaka yi dana sani ba.

Shi kanshi Abdus-samad zuwa yanzu jikin shi yayi sanyi a hankali ya kai kallon
shi kan Fadil, Fadil ya jinjina mishi kai, Abdus-samad ya maida kallon shi kan
Liman yace; "shikenan Baba Allah yasa hakan shi yafi alkhairi, zan yiwa iyaye na
magana na san zasu fahimta".

Liman ya washe baki yace; "yauwa ɗana idan suka ƙi yarda ma kazo ka ɗauke ni ka
kaini ni nan da kaina zan musu bayanin komai", Abdus-samad yace; "insha Allahu".

"Allah yayi muku albarka dai yanzu tashi muje ya fito muku da matar taka sai ku
tafi ko?", duka suka miƙe suka bishi.

Yana gaba suna baya har ƙofar gidan Malam Abdullahi, Abdus-samad dai gaban shi
banda faɗuwa babu abinda yake yi, sai saƙe-saƙe yake yi.

Cikin gidan kuwa Nusram da Nusreen ke fira duk da ba wata me yawa bace yawanci
labarin abinda ya shafi rayuwar su suke yi, sai kuma jimamin abinda ya faru.

Ganin duhu ya fara yi yasa Nusram ta kalli Nusreen tace; "wai ba zaki tafi gida
bane?", Nusreen tayi murmushi tace; "ai jira nake Hubby yazo sai mu tafi".

Nusram ta buɗe baki zata yi magana taji sallamar Baba, jin yana ƙwala mata kira
yasa gabanta faɗuwa.

Ta kalli Nusreen tace; "Allah yasa lafiya", kafin Nusreen tace wani abu ya ɗago
labulen ɗakin ya shigo".

"kaga mini ƴar banza ashe kinajina kika yi shiru, to maza tashi ki shirya mijin
ki na waje yana jiran ki".

Mama Jummai dake bayan shi jin abinda ya faɗa yasa tayi shewa tare da yin guɗa,
"Lallai ma, amma dai Abdullahi wasa kake yi ko?".

"wasa! An taɓa wasa da aure ne?, kinga kada ki ɓatawa mutane rai ki shirya maza
ki fito", daga haka ya juya ya fita.

Mama Jummai ta ja tsaki tace; "wallahi da sake matuƙar angon be gamshe ni ba


dole a canza wannan abin", ta fice fuuuu.

Su dai cikin.su babu wanda yayi magana, Nusram ta fashe da kuka, Nusreen tayi
saurin riƙota tace; "dan Allah kiyi haƙuri ki dena zubar da hawayen ki haka, ina ji
a jikina wannan auren naki alkhairi ne".

Nusram ta girgiza kai hawaye yana zubo mata tace; "Nusreen komai na rayuwata ya
canza, babu farinciki babu karatun da nake matuƙar ƙauna babu mahaifiya wacce take
kula dani".
Nusreen ta dafata tace; "ki kwantar da hankalin ki ƴar uwata, kowa da yadda
rayuwa take zuwar mishi, sannan idan kuma yayi haƙuri sai ki gani wata rana kamar
ba'a yi ba".

Nusram dai tayi shiru kawai, Nusreen ta riƙo hannun ta tace; "tashi ki shirya,
ki dinga addu'a Allah yasa ƙarshen wahalar ki kenan", ba dan taso ba ta miƙe.

Ruwan da Nusram ɗin ta ɗora bayan ta gama yi musu abinci shi ta juyewa mata,
sannan ta koma ta faɗa mata.

Babu yadda ta iya haka ta nufi hanyar bayi, ita kuma Nusreen ta fara shirya mata
kayanta, ita harga Allah tana jin matsalar ƴar uwarta yazo ƙarshe kenan insha
Allahu.

Tana gamawa Shureim ya kirata a waya kan gashinan zuwa ɗaukar ta, ta amsa da to,
koda Nusram ta fito a wajen ta sami Mama Jummai da Isa harda Ameera duk sunyi
cirko-cirko.

"ni wallahi Jummai banso wannan auren ba, hakan nan sai naga samu naga rashi",
faɗar Isa kenan.

Mama Jummai tace; "kada ka damu nan babu jimawa zaka ƙara gani ta dawo gidan
nan wannan karan bama ita kaɗai ba har waccen da take firirita kamar kazar mayu".

Ameera taja tsaki tace; "ni duk haushi ya ishe ni wallahi, amma komai zai zo
ƙarshe ne", Mama Jummai tace; "insha Allahu".

Ba tare da Nusram ta kula su ba ta ajiye bokitin ta shige ɗaki inda ta tarar da


Nusreen na zaman jiranta.

Doguwar riga ta shadda ta saka kalar ruwan bula me haske, sai farin hijab, duk
yadda Nusreen tayi da ita akan ta tsaya tayi kwalliya ƙi tayi dan haka dole ta
ƙyale ta, hoda da man baki kawai ta goga kaɗan.

Ƴan kunne da sarƙa ta maƙala kafin ta juyo ta kalli Nusreen tace; "Rim gabana
sai faɗuwa yake yi", Nusreen ta riƙo hannunta tace; "ni kuwa zan so ace kin daure
kodan maƙiya da suke so suga ya zaki yi".

Ta miƙa mata ƴar ƙaramar jaka kalar kayan jikinta, ta ɗauko turare ta feshe ta
dashi sannan tayi murmushi tace; "muje Amarya", kamar me tsoron tafiyar haka ta
fara takawa.

Sai da suka fito falo kafin Nusreen ta ajiye mata takalmi me tudu ta saka,
Nusreen ta ɗaukar mata duk wani abu da ta san zata buƙata ta saka cikin ƙatuwar
Trolley bag ta ɗauka.

Suna fitowa tsakar gida Nusreen ta rangaɗa buɗa, Mama Jummai taja dogon tsaki,
Nusreen kuwa ƙara sakin wata buɗar tayi ta ciri turare tana kuma fesa mata.

Har zasu fice Baba yace; "to sarakan zumuɗi an kwana biyu ba'a sami namijin da
za'a ɓata ba shine yanzu har sauri kuke yi ko to ai sai ki dawo".

Nusreen ta juya tana zumɓurar baki, Nusram kuwa wajen Baban ta nufa, yace;
"wajen Mamanki zaki je gata can a tsaye".

Nusreen data kusa ficewa daga gidan ta juyo tace; "a'a Baba ba sai taje wajen ta
ba, ai na riga nayi mata faɗan da Uwa ke yiwa ƴarta".

Baɓa ya ɗauki takalmin dake kusa dashi ya jefa mata, da sauri tayi waje tana
janye da jakar Nusram ɗin.

Koda ta fita sai da gaban Abdus-samad ya faɗi, Shureim yayi saurin taro ta ya
amshi jakar.

ta juyo sannan tace; "ina angon yazo ya buɗe mana booth", Fadil dake tsaye yayi
saurin zuwa ya buɗe mata Booth ɗin ta saka.

"yanzu ina zaki je?", Shureim ya faɗa ganin zata koma gida, ta kalle shi tace;
"Hubby zan shiga ne ciki zan fito babu jimawa", daga haka ta shige.

"to kina dai gani da ƙyar kika samu wanda ya aure ki, shima ana bashi yana ƙin
amsa da ƙyar aka shawo kanshi dan haka kada naji kada na gani, idan kika sake kika
kashe wannan auren sai dai ki nemi wani uban ba dai ni ba", abinda Baba ya faɗa
kenan kafin ya miƙe.

Nusram kuwa hawaye kawai take yi, wai shima ana bashi yana ƙin amsa, ita kuma
haka take da baƙin jini🙆.

"tashi mana muje suna jiran ki", jin hakan yasa ta miƙe, suna zuwa zasu fita
Nusreen na shigowa, ta riƙo hannun ƴar uwar tata kafin suka fice, Mama Jummai da
Ameera da Isa suna bin su a baya.

Fadil na cikin mota a zaune, Shureim kuma yana jingine da motar yayinda nesa
kaɗan Abdus-samad ke tsaye tare da Liman suna magana.

Suna fitowa waje, Nusreen ta rangaɗa buɗa Mama Jummai ta wulla mata harara, ta
turo baki tace; "tunda ke ba zaki yi mana kara ba ai sai.muyi da kanmu", ta sake
rangaɗa wata guɗar, hakan shine ya janyo hankalin Maƙwabtan nasu.

Fadil kam ji yake kamar wasa wai Abdul da mata, gashi har yanzu basu samu damar
yin magana ba balle yaji taya akayi hakan ta kasance.

shi ya buɗe motar Nusreen ta riƙe hannun ƴar uwarta, sai lokacin Nusram ta samu
hawaye suka zubo mata, rungume ƴar uwarta tayi suka fashe da kuka.

Baba dake tsaye bayan su ya ja tsaki yace; "wannan kuma wane sabon iskanci ne,
dallah saketa su tafi kuna ta faman ɓata musu lokaci".

Nusreen ta saki Nusram tayi murmushi tace; "kada ki damu ƴar uwata ina ji a
jikina ƙarshen wahalarki kenan?", Nusram ta jinjina kai.

Abdus-samad ya dafe kai, wannan wane irin ƙaddara ce, ya kuma kallon su ya ɗan
taɓe baki sai faman ƙanƙame juna suke yi.

Baba yazo ya fincike hannun Nusram sannan ya sakata a mota, Nusreen ta zumɓuro
baki, Baba ya harare ta yace; "kema wuce ki tafi gidan mijin ki".

Daga haka Baba ya kaɗa kai yayi gida, Liman ne ma ya ɗan ƙara yiwa Abdus-
samad ɗin nasiha kafin su tafi.

Nan suka yi sallama da Shureim inda shima ya ɗauki matar shi suka wuce gida, sun
fara tafiya Fadil yace; "Abdul me kenan?".

Bece komai ba, shima ganin hakan yasa yaja bakin shi yayi shiru, har suka shiga
Estate ɗin babu wanda yace komai.

"dakata anan", cikin sauri Fadil ɗin yayi parking, Abdus-samad yayi ajiyar
zuciya yace; "fito sai muyi magana", Fadil ya amsa da to yana fita.
Kan wasu kujeru suka ƙarasa suka zauna, wajen dama daga gani irin na hutawa ne,
Abdus-samad ya dafe da kanshi.

Fadil yace; "ka kira ni kuma ba kace komai ba", Abdus samad yaja ajiyar zuciya
sannan yace; "Fadil banda abinda zance maka ne yanzu, shawarar ka nake nema kaina
gaba ɗaya ya kulle, kaga tun ɗazu First Love ke kirana amma na kasa ɗagawa saboda
tension ɗin dana shiga", ya ƙarasa yana ɗago mishi wayar shi.

Fadil ya tsaya yana kallon shi, Abdus-samad ya cigaba da cewa; "ka dai ga duk
abinda ya faru yanzu wace shawara zaka bani?".

Fadil yace; "to ni dai ban san me zance maka ba a halin yanzu, dan na san ko
giyar wake ka sha ba zaka doshi su Abba kace wai an ɗaura maka aure ba, haka ma
Mahaifiyar ka, wannan kam ba me yiwuwa bane idan kayi la'akari da tsarin gidan
nan".

Abdus-samad yayi shiru yana nazari tabbas abinda ɗan uwan shi ya faɗa gaskiya
ne, yanzu me zai yi kenan, ya dafe kanshi.

Shi ji yake ina ma ace Baba wuƙa ya samu ya caka mishi ko kuma marin shi ya
dinga yi, wannan wane irin abu ne?🙄.

Haka dama ake auren ko kuwa nashi ne yazo a haka, yanzu waye zai tunkara da
wannan auren?, Abban Nihal ko Abban Fadil?, taɓ babu ko ɗaya, First Love ya san
abinda ba zai yiwu ba kenan, me zai ce mata yaja bawa Uba haƙauri akan kada ya
aurar da ƴar shi, shi kuma ya aura mishi ko me?".

Fadil yace; "ina jin ina da shawara", da sauri Abdus-samad ya buɗe idanu, Fadil
yace; "me zai hana ka faɗawa Malama, idan yaso sai ta riƙe yarinyar a matsayin ƴar
aiki?".

Ya jima yana kallon Fadil ɗin kafin ya girgiza kai, "wannan ba zai yiwu ba, taya
kake ganin Malama zata iya ɓoye baban al'amari kamar wannan?".

Fadil yace; "hakane kuma gaskiya, sannan Hajja zata iya matsawa abin da
bincike, to ka kai ta wani gidan mana sai ka ɓoye ta".

"wannan ma bana ji hakan me yiwuwa ne, ka duba ka ga yanayin yarinyar tana


buƙatar me ɗebe mata kewa wanda zasu ɗan dinga fira, idan na kaita gida na ajiye
ita kaɗai ban yi mata adalci ba".

Fadil yace; "kai sai ka dinga zuwa", wani kallo Abdus-samad yayi mishi kafin ya
ɗauke kai, "kaima ka san Firzt Love ba zata yarda da fita ta any how ba, dole ta
dinga bincikar ina naje, ina jin tsoron ranar da zata gane cewa mace na ajiye a
gida nake kula da ita, ka nemo wata shawarar".

Fadil ya miƙe yace; "to ni gaskiya banda wata shawarar, ko kuma zaka kaita
wajen Fadila ne sai ta kasance a matsayin ƙawarta?".

Abdul yayi jim kafin yace; "Fadila da zata yi aure babu jimawa, dole idan tayi
aure na samu wajen ajiye ta", Fadil yace; "hakane kuma ka san bikin Familyn nan ba
wani jan shi suke yi ba".

Shiru ya biyo bayan haka, kowa tunanin da yake yi daban, sun jima a haka kafin
Fadil yace; "to ka kaita wajen Aunty Saleema mana".

Sai da ya tsaya yayi nazari kafin yace; "kana ganin hakan zai yiwu kuwa", Fadil
cikin ƙwarin gwiwa yace; "tabbas kuwa zai yiwu, Aunty Saleema nada sauƙin kai kaga
kenan zaka sami sauƙin kula da ita, na san soyayyar da take yi maka zai sa ta kula
da ita sosai kuma kaga bata da wata damuwa sosai", Abdul ya jinjina kai.

Wayar shi ya zaro ya kira Saleemar akan ta same shi Garden yana jiran ta, cikin
ɗoki da murna ta amsa da gata nan zuwa, shi kanshi sai da yayi murmushi saboda
yadda ta nuna murnarta a fili.

Anya ba kasada zai yi ba, idan kuma kishi yasa ta ƙi amsarta fa ko kuma ta tona
mishi asiri fa?, wannan kam anya ba ganganci bane zai aikata🙄.

#LIKE
#SHARE
#COMMENTS.

*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*


📖📖53-54📖📖

Tunda ya hangota gaban shi ya yanke ya faɗi, kada fa garin neman mafita ya jefa
kanshi a matsala idan kuma bata amince bafa ta faɗawa Abban ta.

Ƙarasowar ta shine abinda ya katse mishi tunani, cikin natsuwa tayi sallama suka
amsa mata, da murmushi taja kujera ta zauna sannan ta kalle shi tace; "lafiya
kuwa?".

Abdus-samad ya juya ya kalli Fadil wanda dama shi yake kallo, Fadil yayi saurin
girgiza mishi kai, Abdus-samad ya maida kanshi ya lumshe idanu.

Shiru ya biyo baya, ganin ba zasu yi magana bane yasa Saleema riƙo hannun shi
tace; "Abdus-samad ka faɗa mini meke faruwa mana, damuwarka ai tamu ce, kada ka
manta bakada wanda zai yaye maka damuwarka bayan Ubangijin daya halicceka sama da
mu, idan har akwai shi to bayan mu yake kada kaji komai ka faɗa mini abinda ke
faruwa nayi maka alkwari zan taimakeka kuma zan rufa maka asiri".

Ya buɗe idanu ya kalleta, gaban shi babu abinda yake yi banda dukan uku-uku ga
wasi-wasin ya faɗa mata ko kada ya faɗa mata, can ya girgiza kai baya jin wannan
mafitar zata ɓulle mishi.

Fadil yayi gyaran murya, ta juya ɓangaren shi nan ya bata labarin iya abinda ya
sani akan yadda aka ɗaura auren ɗan uwan nashi da yarinyar da haƙuri yaje bawa
Babanta.

Saleema tayi murmushi bayan ta gama jin abinda ya faru ta maida kallonta kan
Abdul wanda ita ya zubawa idanu yana so yaga yanayin yadda fuskarta zata yi.

"taɓ, yanzu me kuke so ayi?", ta tambaya, Fadil ya sosa kai yace; "dama wai
cewa muka yi ko zaki kaita appartment ɗinku, sai kice ƙawarki ce kafin komai ya
dai-daita".

Saleema taja ajiyar zuciya tace; "Abban Nihal ya dawo jiya, Abban mu kuma nan da
kwana biyar zai dawo amma zan yi ƙoƙari naga ba'a sami matsala ba, yanzu tana
ina?".

"tana mota", amsar da Fadil ya bata kenan, bata kuma cewa komai ba sai wajen
motar data nufa ta ɗan ƙwanƙwasa, Nusram da har lokaci banda kuka babu abinda take
yi ta saka hannu ta buɗe ƙofar.

Saleema ta sakar mata murmushi sannan tace; "fito ko?", babu musu ta fito a
ranta tace; "gidan yankan kai harda mace?", bata samu amsar tambayar ta ba, Saleema
ta riƙo hannun ta suka nufi inda su Abdul ke zaune.

Tunda suka taho Abdus-samad ya zuba mata idanu, gaban shi sai faɗuwa yake yi,
suna zama Nusram ta ɗago ta kalle shi yayi saurin kauda kai yana zaro wayar dake
aljihun shi wacce keta faman tsuwwa tun ɗazu, kamar yadda ya zata Brr Farida ke
kiran shi.

"Hello First Love", bata amsa ba sai cewa da tayi; "haba Baby ina ka shiga ne?,
me kake aikatawa haka ka san dai ban fiye son yawo ba jiya ma Surayya tace mini da
wuri ka bar Company amma baka taho gida ba yauma haka".

Abdul yaja numfashi yace; "First Love bafa wani waje naje ba, ina........", tayi
saurin dakatar dashi; "kaga niba wannan ba duk inda kake ka tabbatar ka iso gida
nan da minti talatin", tana faɗin haka ta katse wayar, ya bi wayar da kallo yana
sakin ajiyar zuciya.
Saleema tace; "abinda za'ayi shine ka tafi gida kawai insha Allahu babu me sani
har zuwa lokacin da zaka faɗa musu, zan yi iya ƙoƙari na mu bar wajen nan kada wani
yazo ya gan mu", duka suka miƙe itama hannun Nusram ta kama suka miƙe tare.

Ta ɗan saki hannun ta sannan ta juya ta sauka, Fadil ma fita yayi daga rumfar,
ya kalle ta ya kauda kai me kenan? Wai su nan sun bar su suyi sallama, yayi wani
miskilin murmushi.

Nusram kuwa gabanta ke faɗuwa kawai, Abdus-samad yace; "kinga zaki zauna da
wannan da tazo na san zata yi miki bayanin komai ki kwantar da hankalin ki insha
Allahu komai zai dai-daita, yanzu ba zan iya fitowa nace an ɗaura mini aure dake ba
duk abinda kike buƙata ki mata magana", be jira me zata ce ba ya fara tafiya.

Nusram ta saka hannu ta share hawayen dake zubo mata daga idanu kafin ta fito
itama daga wajen, a bakin mota ta same su, Fadil na fito mata da kayanta.

Saleema tace; "ya sunanta ne?", Abdus-samad ya ɗan kalle ta ya basar, maida
hankalin shi yayi kan Fadil yace; "zan tafi sai da safe", Fadil yace; "baka ji
abinda Aunty Saleema tace bane?".

Ya ɗan lumshe idanu shifa wannan auren har ya fara zama takura a gare shi,cike
da ƙagara yace; "Nusram", yana faɗin haka ya buɗe mota ya shiga.

Saleema na riƙe da hannun Nusram tana murmushi har suka dena hango shi, Saleema
tayi murmushi kafin ta kalli Fadil tace; "shigar mana da kayan", suna gaba yana bin
su a baya.

Da sallama suka shiga Mommy dake karatun jarida ta ɗago ta kalle su, Dr Saleema
taja Nusram suka zauna a kujera.

"wannan fa daga ina?" ta jefo mata tambaya, Dr Saleema tace; "ƙawata ce dake
karatu a KASU bata sami Hostel ba shine ta roƙe ni akan tana so ta zauna anan na
ɗan wani lokaci", Mommy ta jinjina kai tana ƙara bin Nusram da kallo.

Nusram sai sake saukar da kai ƙasa take yi, cikin dashashshiyar muryar ta gaishe
da Mommyn, ta amsa babu yabo ba fallasa.

Dr Saleema tace; "muje ciki ki ɗan huta tukunna", daga haka ta miƙe itama Nusram
ta bita a baya, kayan da Fadil ya shigar mata dashi Dr Saleema ta gyara musu wajen
zama sannan ta kalli Nusram tace; "ga bayi nan ki shiga kiyi wanka sai kizo muyi
magana", ta amsa da to.

Hijab ta cire, Dr Saleema gabanta ya faɗi ganin irin yadda Nusram take da kyau
na halitta, lallai kwanan nan Abdus-samad zai fara sonta, towel ta miƙa mata cike
da kunya Nusram ta cire kayan ta ta saka towel ɗin, ita dai Dr Saleema babu abinda
take sai binta da idanu, "fatabarakallahu Ahsanal khaliƙeen", abinda Dr Saleema ke
maimaitawa cikin ranta kenan.

Nusram ta jima a bayin tana kuka ganin yadda rayuwa take wulagegeduwa da ita,
daga nan sai nan, sai da Dr Saleema taji shirun yayi yawa sannan ta ƙwanƙwasa
bayin, cikin sauri Nusram ta fara wankan.

Koda ta fito wajen madubi ta nufa, mayuka da turarruka da kayan kwalliya duka
ta gansu masu tsada da kyau duk da kasancewar ta me yin kwalliya kuma tana yawan
binciken kayan kwalliya ta network amma sai da taga abinda bata sani ba.

Mai ta shafa da powder sai ɗan man baki, ko kwalli bata saka ba, wajen jakarta
ta nufa ta zage ta ciro riga half gown da wando blue and pink ta saka, ba tare da
ta ɗaura ɗankwalin ba ta ɗora shi saman kai kawai.

Kusa da Dr Saleema tazo ta zauna kafin tace; "na gama Aunty", Dr Saleema tayi
murmushi tace; "kinga nan shine gidan mu ni da Babana da Mama na da kishiyar ta da
kuma ƴan uwana, gidan da kike ciki gida ne me mutane da yawa saboda haka sai kinyi
taka tsantsan, kasancewar kinga mun kusa Family meeting duk wani wanda yake da
jinin gidan nan zai halarta dan haka ki ƙara kulawa, kamar yadda nace ke ƙawata ce
to zaki zauna a matsayin ƙawata, kullum idan zan tafi wajen aiki zan tafi da ke
idan na dawo ma zamu dawo tare kin fahimta".

Nusram ta ɗaga kai, Dr Saleema tayi murmushi tace; " na san zaki ce me yasa
Abdus-samad be kaiki gidan su ba ya kawo ki nan, dalili kuwa shine kinga gidan nan
gidane na ƴan boko duk wanda kika gani a ciki mace da namiji ko ɗalibi ko
ma'aikaci, sannan namiji aƙalla yakan kai shekara talatin kafin a bar shi yayi aure
mace kuma ashirin da bakwai zuwa da takwas har ma sama da haka dan haka wannan
shine dalili, ina so ki ɗauke ni ƴar uwar ki duk wani abu da kike buƙata kizo ki
tambaye ni insha Allahu zan yi ƙoƙari ganin baki zauna cikin damuwa ba, Abdus-samad
nada mahimmaci a rayuwata saboda haka duk wani abu daya dangance shi ina mahimmanta
shi kin fahimta".

Nusram ta kuma ɗaga kai, Dr Saleema ta ɗan kishingiɗa jikin couch tace; "yanzu
ki bani labarin rayuwar ki", Nusram tayi murmushi me ciwo kafin ta fara bata
labari.

Dr Saleema har da hawaye sai da ta yi, cikin shesheƙar kuka tace; "lallai duk
wanda kuka haɗu dashi akwai dalilin haɗuwar ku, kuma ko a jima ko a daɗe zaka ga
akwai wani abu wanda kuke kamanceceniya dashi, kin ganni Nusram shekaruna talatin
da huɗu na kusa shiga talatin da biyar amma babu aure".

Nusram tace; "babu wanda ya taɓa cewa yana son ki ne kamar ni", Dr Saleema ta
girgiza kai tace; " na samu samari lokacin da nake tashen ƴan matanci amma sanin
halin gidan mu yasa dole na ɗauke kaina, a cikin su akwai wanda ya nace sosai har
gidan nan sai da ya turo amma iyayena suka ci mishi mutunci dalilin haka mahaifan
sa suka yi fushi suka ce ko a hanya ya kuma kulani basu yafe ba, na damu sosai amma
haka na haƙura yanzu gashi da zama na likita shekara takwas kenan, Nusram kuɗi iya
kuɗi ina dashi babu abinda nake nema, duk wani abu da kika sani ina da kuɗin siyan
shi sai dai aure kawai".

Nusram ta kuma cewa; "toke yanzu baki da wanda kike so ne", Dr Saleema ta share
hawaye tace; "ina dashi mana sai dai na sani cewa ba zai taɓa maido mini da soyayya
ba, ni kaɗai kawai nake son shi, a da dai ina saka ran koda da idanun rahama zai
kalle ni amma zuwa yau na tabbatar da yayi mini nisa Nusram ba zan taɓa samun shi
ba".

Kafin Nusram tace wani abu Dr Saleema ta ƙwalawa Sakina ne aikin su kira, ta
shigo cikin sauri.

"ki kawo mini abinci", abinda ta faɗa kena, Sakina ta amsa da to sannan ta fita,
Dr Saleema ta miƙe ta fara cire kaya, ita dai Nusram tana ta binta da kallo har ta
shige bayi.

Nusram tayi shiru tana mamakin rayuwar wannan baiwar Allah, ta sake ɗaga kai ta
kalli ɗakin nata komai yaji dangane da alatu na rayuwar duniya, ta shafa gadon da
take zaune a kai shi kanshi royal bed ne me tsada, ƙaton wardrobe wacce ta cike
bango ɗaya, change room da kuma dressing mirror, wasu irin manya-manyan glass masu
shape ɗin duniya sai me heart a tsakiya, cikin su wasu irin ruwa ne me ƙalƙali,
ƙasa kuwa italian carpet ne me taushi da kyau, sai flower vase dake kusa da window
guda biyu manya-manya, duka kuma ash and milk ne,
Tana nan zaune Sakina ta shigo da ƙaton tray a hannun ta, ƙaramin teburin dake
jingine ta janyo ta ɗora tray ɗin sannan ta juya ta fice bayan ta yiwa Nusram
sannu.

Dr Saleema ta fito ta kalli Nusram tace; "ya baki ci abincin ba", Nusram tayi
murmushi tace; "jira nake ki fito sai muci tare", bata kuma cewa komai ba sai ma
nufar madubi da tayi.

Nan fa ta hau ƙalƙale jiki, itama ba wata kwalliya tayi sosai ba, powder ne
sai jan baki light pink da kwalli shikenan.

Ta buɗe wardrobe ta ciro rigar bacci me shegen kyau pink colour ta saka, nan ta
hau feshe jiki da turare, kan kace me ɗakin ya hau ƙamshi.

Sai da ta dawo ta zauna sannan tace; "komai ma zai zo da sauƙi tunda dama kina
karatun ki kinga da an koma makaranta sati biyu masu zuwa sai ki cigaba da karatun
ki kawai, zuwa ƙarshen satin nan zamu je muyi registration", Nusram cikin farin
ciki ta amsa da to, abinda ta cire rai akai.

Lafiyayyen tuwun shinkafa ne da biyar taushe, ba me yawa ba ta zuba musu suka


hau ci, babu sabo a tsakanin su hakan ya haifar da yin shiru, suna gamawa suka
wanke hannu.

Dr Saleema ta janyo laptop ta fara dannawa ganin hakan yasa Nusram zama ta zuba
mata idanu.

Sun jima a haka kafin Dr Saleema tace; "kiyi shirin barci mana", cikin sauri
Nusram ta miƙe, kayan barci ta ciro cikin jakar ta sannan ta hau sakawa.

Dr Saleema tayi mata kallo ɗaya ta kauda kai, wani abu ta danna sai ga plasma
yana fitowa, Nusram ta ƙwalalo idanu, Dr Saleema ta miƙa mata remote ɗin tace;
"gashi idan zaki rage dare", Nusram ta saka hannu ta amsa sannan ta koma ta zauna.

Tana zaune tana kallon kamar dole don ita ba wai ya dame ta bane, haka har barci
ya ɗauke ta wanda bata san lokacin da hakan ya faru ba.

Dr Saleema ta kalleta tayi murmushi, ta ajiye Laptop ɗin ta matso gare ta,
kallonta tayi sosai tana jinjina kyawunta waye za'a bawa mace kamar wannan yaƙi
amsa tabbas Abdus-samad ta tabbatar yanzu yafi ƙarfinta, ta share hawayen da ya
zubo mata kafin itama ta fara canza kaya zuwa na barci.

Kan couch ta kwanta har lokacin ranta a cunkushe yake, a yanzu kam tana jin cewa
wata kila harta koma ga ubangijinta bata da rabon yin aure.

******** ************

koda ya bar gidan babu abinda yake yi banda tunani, Allah ne ya taimake shi har ya
kai gida lafiya, yana yin parking suka haɗu da Sameer.

"kai kam zaka tashi office da wuri amma duk zamu riga ka isowa gida", cewar
Sameer ɗin kenan, Abdus-samad yayi murmushi kawai.

Part ɗin shi ya fara wucewa, sai da ya shiga bayi yayi wanka kafin ya fito ya
hau shiryawa, gaban madubi yaja ya tsaya hannun shi riƙe da comb, wai yau shine da
mata!?, shi Abdus-samad Abubakar Nagimi?, ya sauke nannauyar ajiyar zuciya.

Turo ƙofar da akayi itace tasa ya kalli wajen, duk da sanin wacece ta shigo,
kamar yadda ta zuba mishi idanu haka shima ya zuba mata idanu, tsoron shi ɗaya kada
ace ta gane cewa an ɗaura mishi aure.
Dr Farida ta kauda kai tace; "idan ka gama shiryawa kazo kaci abinci", be amsa
ba itama kuma bata tsaya jiran amsar tashi ba.

Tana daf da fita sai kuma ta juyo tace; "wai baka kuma magana akan yarinyar da
aka harba ba a shopping mall?".

Ya ajiye comb ɗin hannun shi ya ɗauki kwalbar turare ya hau fesawa, har ta cire
rai da zai yi magana sai kuma taji yace; "First Love komai yana faruwa saboda ɓoye
mini abubuwa da yawa da kuke yi".

Cikin sauri ta kalle shi ya kauda kai yama cigaba da abinda yake yi, ta jima
tsaye ko zai kuma cewa wani abu amma be kuma magana ba hakan yasa ta ɗaga ƙafa ta
fara tafiya, wannan murɗaɗɗen hali irin na uban shi ne", abinda ke ranta kenan ita
kanta duk da take lauya wani lokacin idan yayi magana a murɗe ta kan jima bata
fahimta ba.

"ita ɗin ƴa ce ga Alhaji Mustapha Tuge", abinda ya faɗa kenan tana dafa da fita,
Brr Farida gabanta ya yanke ya faɗi, cikin sauri ta juyo ta sake kallon shi kamar
ma bashi yayi maganar ba.

Taja ajiyar numfashi tace; "Baby ita ɗin ta faɗa maka haka?, taya akayi ka sani
ko ka sake binta asibitin ne?, kun haɗu dashi Alhaji Mustaphan?", duka ta jero
mishi tambayar babu amsa ɗaya da ya bata hakan yasa ta fice kawai.

Abdus-samad ya bi bayanta da kallo tana ficewa ya saki ajiyar zuciya, ƙarar


wayar shi itace ta dawo dashi daga duniyar tunanin daya faɗa.

Number ce babu suna hakan yasa be ɗaga ba, tana yankewa wata ta shigo itama tana
yankewa wani kiran ya sake shigowa, ya saka hannu ya ɗauka ya kai kunne.

"Hi!", shine abinda ta faɗa, a gajarce shima yace; "barka", ta ɗan yi gyaran
murya sannan tace; "ka gane me maganar".

Cikin ƙagara yace; "a'a wacece?", jin abinda ya faɗa yasa jikin ta yin sanyi,
"Khausar ce", ta faɗa cikin sauri.

"oh ya gida?, fatan komai lafiya", ya tambaye ta, murmushi tayi kana tace;
"lafiya lau, dama cewa nayi bari na kira mu gaisa", ya ɗan shafa gefen fuskar shi
yace; "na gode" kan ta kuma magana ya yanke kiran.

Sororo ta tsaya hannun ta riƙe da wayar, Hajiya Salma data ji duk abinda ya fara
ta taɓe baki tace; "wai ke qace irin wahalalliya ce?, bafa shi kaɗai bane namiji".

Khausar ta saki murmushi tace; "ni fa Mommy ina son shi kodan kama da yake yi da
Daddy", ta ƙarasa tana me juyawa ta kalli Mahaifin nata.

Alhaji Mustapha kuwa banda zufa da take karyo mishi babu abinda yake yi. be iya
cewa komai ba.

"Daddy ai ka ganshi kwanaki ko?, kana nan yazo gaishe dani a asibiti, wallahi da
badan na san cewa nida Khalee kawai Mummy ta haifa ba da sai nace ɗan kane".

"Umm", shine abinda Alhaji Mustafan ya faɗa, Hajiya Salma ta ƙunshe dariya,
Khausar zata kuma magana Hajiya Salma ta dakatar da ita.

"wai ke baki ga Mahaifin naki baya son surutu bane, gobe ƴar uwar ki zata dawo
dan haka kije ki kwanta kin san dai isowar wuri zata yi", Khausar ta miƙe tana
zumɓurar baki tayi ɗaki.
Hajiya Salma ta miƙe itama ta shige nata ɗakin, Alhaji Mustafa ya dafa kanshi da
hannu biyu yana sauke ajiyar zuciya.

"wannan wane irin masifa ce take tunkaro shi, ƴar shi ta cikin shi ke son ɗan
shi na cikin shi?, taya zai fito ya shaidawa duniya cewa Abdus-samad ɗin ɗan shi ne
na cikin shi?, akwai babban al'amarin da ko tunawa baya son yi".

Wayar shi ya zaro ya fara kiran Alhaji Sa'eed, sai dai kash ana amfani da layin,
miƙewa yayi cikin sauri kana ya fara zagaye ɗakin.

Daidai lokacin kuwa Hajiya Salma ce da Alhaji Sa'eed suke waya, "Alhaji wallahi
ban san yadda zan yi da yarinyar nan ta fahimci halin da ake ciki ba, bana ƙaunar
ganin yaron nan a raye gashi na rasa yaya zan yi".

Alhaji Sa'eed yace; "kada ki damu Hajiya Salma, zamu iya amfani da ita wajen
tunowar asirin mijin ki, na san cewa idan har abinda yake ɓoyewa ya fito fili to
tabbas yaran nashi zasu tsane shi tsana me tsanani, sannan shi kan shi Abdus-samad
ɗin zai tsane shi tsana mafi muni sannan kinsan Nagimi's Family dole zasu ɗauki
mataki, zasu maka shi kotu kuma kin san hukuncin da za'a yanke mishi ɗaurin rai da
rai ne".

Hajiya Salma tayi ajiyar zuciya tace; "Alhaji Sa'eed har yanzu baka san waye
abokin ka ba, ko tafiyar nan da yayi hannun jari yaje ya zuba a wani company dake
Hong Kong ƙimanin dala billion sha biyar, sannan yana ɗaukar kaso mafi tsoka a
babban companyn dake ƙera gwalagwalai a Dubai, dan haka bana jin kuɗin Familyn nan
zai iya da nashi, ba zasu taɓa iyawa ba ka chanza shawara".

Jim yayi yana tunani, yayin da Hajiya Salma take tunanin mafita yake nemo musu,
shi kuma a nashi ɓangaren kuɗaɗen ne suka fara girgiza shi, lallai wato Alhaji
Mustaphan ashe yana ɓoye mishi wasu abubuwan, shi dai kawai ya san cewa yana da
Companyn ƙera motoci a Dubai da kuma lagos, sai Company biyu da yake da hannun jari
a India da kuma Bangkok ashe likafa ta cigaba kuɗin nashi ya fara wuce tunanin shi
kenan?.

"Me zai hana kawai idan Khausar ta gayyace shi gidan nan mu saka mishi guba a
abinci sai ya mutu, idan yaso Baban shima daga baya sai muji dashi?".

Abinda ta faɗa ya katsewa Alhaji Sa'eed duniyar tunanin daya fara kenan, ya
girgiza kai kamar tana gaban shi yace; "hakan bame yiwuwa bane Brr Farida a sanin
da nayi mata ba zata taɓa ƙyale abin a haka ba, bana so muyi abinda zamu shiga
ciki".

Hajiya Salma taja tsaki tace; "yanzu meye abin yi?", Alhaji Sa'eed yace; "watan
gobe Brr Farida zata tafi Korea yin wani case ina ganin zamu yi amfani da wannan
damar ne kawai".

Hajiya Salma tayi murmushi tace; "shikenan Allah ya kaimu da rai da lafiya, amma
wallahi na ƙosa komai ya dawo hannu na, nima na zama ɗaya daga cikin matan da ake
lissafawa masu kuɗi a duniya".

Alhaji Sa'eed yayi wani munafikin murmushi sannan yace; "nima na ƙosa wannan
lokacin yazo ke dai kome ke akwai ki dinga sanar dani", ta amsa da to.

A haka suka rabu, Alhaji Sa'eed na katse wayar ya miƙe tsaye cikin sauri, Brr
Hauwa dake kwance jikin shi tayi saurin miƙewa tana tambayar shi lafiya.

"babu komai, dan Allah ina buƙatar yin tunani yanzu bana son damuwa ko zaki tafi
ne?", Brr Hauwa ta ɗaga gira ɗaya tace; "kuɗin da Hajiya Salma ta faɗa maka Alhaji
Mustafa na dashi shine ya tsorata ka ko me".

Jin abinda ta faɗa yasa ya ɗan saki rai yace; "ba haka bane, mafita nake nema
dole Abdus-samad da Alhaji Mustapha su mutu, kuɗi Hauwa dole ya dawo gare mu, ni
dake".

Brr Hauwa tayi murmushi tace; "ka kwantar da hankalin ka, har yanzu fa Brr
Farida bata faɗawa Abdus-samad komai ba, suna ganin sannan sirrine tsakanin ta da
Alhaji Mustafa banda su biyu babu wanda ya sani".

Alhaji Sa'eed yace; "amma shi Alhaji Mustaphan ai ya san na sani ko", ta shafa
fuskar shi tace; "amma kuma ai ya yarda da kai sosai ko".

Ya koma ya zauna kana ya girgiza kai yace; "bana tunanin hakan Brr a da Alhaji
Mustapha baya yin komai sai da sani na amma a yanzu ya canza sosai", miƙewa yayi ya
ɗauki wayar shi kana yace; "bari naje wajen Oregbu zamu haɗu gobe kawai dan yau
till down zamu yi".

Brr Hauwa ta figi jakar ta sannan tace; "muje ka ajiye ni a gida ko?", daga haka
suka fice daga gidan.

#LIKE
#COMMENT
#SHARE

*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖55-56📖📖

Alhaji Mustafa ke tsugunne jikin shi sanye da jan ƙyalle iya gwiwa, tsaye a saman
shi Appu ne shima sanye da jan ƙyalle a kwankwason shi sai dai shi ya yafa wani
saman kafaɗar shi.

Wani abu dogo ne riƙe a hannun shi, wani ƙaton mutum me ƙaton tumbi ke gefe
tsaye da ƙwarya ƙatuwa a hannun shi, Appu ke saka wannan abin cikin ƙwaryar yana
yayyafawa Alhaji Mustapha yana zagaye shi yana wasu irin surutai.

Sauran kuwa kansu na ƙasa duka a tsaye suke sanye da jan kaya riga da wando,
wajen yayi tsit sai tashin muryar Appu dake wannan surutan.

Sun jima a haka kafin wani hayaƙi ya fara cika wajen, basu motsa ba kai daga
gani kasan sun saba da yanayin, sai dai wasu ƙalilan da suke zubar da hawaye
kasancewar hayaƙin akwai zafi sosai amma babu halin rufe idanu.

Sun jima a haka wajen awa ɗaya kafin komai na wajen ya ɗauki rawa, wutar dake
kunne koda yaushe wacce take saman wata ƴar ƙaramar ƙwarya ta ɗauke, nana fa ko'ina
a wajen ya ɗauki duhu.

Minti talatin da faruwar hakan sannan hasken ya dawo, Alhaji Mustafa ya kalli
inda yake tsugunne jini ne a gaban shi malala wanda har ya gangaro ya tarar dashi,
sai yara guda biyu da suke kwance a wajen cikin su a fafe wanda yake nuna alamun
tana nan ne aka sha jinin nasu.

Appu ya fashe da dariya kafin ya matsa, wajen wata giggimemiyar kujera yaja ya
tsaya sannan ya nuno Alhaji Mustapha yace; "haƙurin Oregbu ya kusa ƙarewa Tuge,
dole ka kawo jinin ɗanka na cikin ka idan ba haka ba fushin sa zai sauka a kanka,
shekara talatin kenan da yi mishi alƙawari amma har yau ka gaza cikawa, tun ana
rarrashin shi yana amsar jinin wasu wata rana fa ba zai aminta ba", ya juya ga
sauran mutanen ya nuna mutum biyu a cikin su yace; "Oregbu yace a gaya muku ya ji
daɗin sadaukarwa da kuka yi mishi, dan haka yayi matuƙar murna shi kuma zai canza
muku da abinda kuke so".

Ya nuna wani dogo fari a cikin su yace; "yadda ka bashi ɗan ka yace a gaya maka
kaine zaka dinga juya shugaban ƙasa wanda za'a rantsar hasalima ma ƴan majalisu kai
zaka yi list ɗin su ka bayar mulkin nijeriya naka ne".

Cikin murna yayi sujjada yana godiya, ya nuna ɗayan da hannun shi yace; "kai
kuma ka bashi jini me daɗi sosai na ƴar ɗan uwanka dan haka sai ka zama babu
babban ɗan kasuwa a ƙasar Ghana wanda yake sama da kai", shima cikin murna ya
durƙusa ya hau murna.

Appu ya ɗaga mishi hannu kana ya ɗora da cewa; "abu guda zaku yi tare abu guda
kuma kowa da nashi wanda zaku yi tare shine ku baiwa almajirai guda uku sadakar
dubu goma amma jefa musu zaku yi".

Ya nuna na farkon yace; "ka samu yaro wanda bai gaza shekara goma sha takwas ba
kada ya wuce haka kayi luwaɗi dashi a masallacin ƙofar gidan ka sha biyu na daren
gobe".

Ya nuna ɗayan yace; "ka sami jariri sabuwar haihuwa ɗa namiji ka ɗauke shi ƙarfe
ukun dare kayi jefa dashi a tsakar gidan ka bayan kayi zindir idan be mutu ba ka
sake yi mishi haka har sai ya mutu, buƙatar ku ta gama biya", jinjina kai suka yi
sannan suka matsa baya.

"Alhaji Sa'eed Yahya Tsillo, da kai da Alhaji Mustafa Abubakar Tuge, Oregbu
yace a faɗa muku yana son jini daga gare ku ƙafin nan da sha bakwai ga watan gobe".

Alhaji Sa'eed yace; "ayi mini afuwa ƴaƴa biyu suka rage mini yanzu", cikin daka
tsawa Appu yace; "ka kawo ko ka haukace", Alhaji Sa'eed yace; "zan bayar".

"zaka iya bayar da na ƴar ƙanwarka Azeema domin Oregbu yace jinin ta akwai wuyar
samu", cikin murna Alhaji Sa'eed yace; "zan kuwa kawo ta".

Appu ya juya ga Alhaji Mustafa yace; "ko dai ka kawo jinin Abdus-samad ko kuma
ka kawo jarirai guda goma", Alhaji Mustafa yace; "tunda jinin Abdus-samad yaƙi
samuwa kona bayar dana Khaleesat ko Khausar mana".

Appu yayi ihu yayi kirari kafin ya girgiza kai yace; "wa'innan ba jinin ka bane,
jinin ka na asali yake so, kada ka kuma kawo zancen su", cikin sauri ya amsa da to.

Nan suka cigaba da kafurcin su da tsibbace tsibbacen su, har zuwa gabatowar
asuba kafin suka watse.

Alhaji Mustafa da Alhaji Sa'eed tare suka taho, sun shigo garin Kaduna ana
kiraye kirayen sallar asuba dan haka suka sami masallaci suka yi sallah.

Bayan an idar Alhaji Mustafa ya dubi masallacin babu kowa domin kowa ya kama
gaban shi ya kai kallon shi ga abokin shi yace; "Alhaji Sa'eed ka taimaka mini
mana, ban san ya zanyi ba".

Cikin ɗaure fuska Alhaji Sa'eed yace; "meka maidani Mustapha, nifa lura jinin
Murad ɗin ne baka son bayarwa".

Ya girgiza kai yace; "ba haka bane ka duba da kyau ka gani matsaloli sun fara
yawa tun da suka haɗu da Khausar ta liƙe shi take so, Brr Farida taƙi ko kusa ta
faɗa mishi cewa nine mahaifin shi balle na samu damar raɓar shi, sannan yaron be
cika shige-shige ba balantana na sami wata dama akan shi, ga Salma yadda take sona
take kula dani ta yarda dani ba zan iya kallon idanun ta ince mata wai ina da wani
ɗa ba".

Alhaji Sa'eed yayi murmushi yace; "hakane kuma gaskiya, to amma yanzu abinda
za'a yi shine ya kamata ace muna kula da takun Brr Farida domin na san shirun ta ba
wai yana nufin shiru ɗin bane dan haka me zai hana mu tura wata matar ta sami aiki
a gidan ta idan yaso sai ta dinga kawo mana rahoton abinda yake faruwa".

Alhaji Mustafa yace; "Alhaji Sa'eed duk abinda ya kamata kayi ni dai kayi amma
ka tabbatar da cewa asirina dana rufe shekara Ashirin da bakwai be tonu ba".

Alhaji Sa'eed yace; "kada ka damu kai dai ka bar mini komai a hannu na baka faɗa
mini meya kaika Dubai ba?".

Alhaji Mustafa yace; "hannun jari na zuba a wani company, so nake gaba kaɗan na
siye companyn gaba ɗaya haka ma Brr Jabeer ya bani shawara".

"to amma ya maganar takardun gidan gonarka dake By Pass?", Alhaji Mustafa ya ɗan
yi jim kafin yace; "suna nan, akwai matsala ne?", Alhaji Sa'eed ya girgiza kai.

Sai da gari yayi haske sannan suka fito daga masallacin kowa ya shiga motar shi
ya nufi hanyar gidan shi.

********* **************
*HAYIN RIGASA, KADUNA*.

Da asuba suka tashi tare kamar haɗin baki, Dr Saleema ta fara alwala kafin
Nusram itama ta miƙe ta shiga bayin domin alwala.

Koda Nusram da Dr Saleema suka idar da sallah babu wanda ya tashi daga inda
yake, hakan ya tabbatar da cewa dukkan su, suna da kamanceceniya ta wajen halayyar
su.

Sai bakwai kafin Dr Saleema ta miƙe ta shiga bayi, wanka tayi bayan ta fito ta
dubi Nusram tace; "ki shiga kema kiyi wankan zamu wuce asibiti", Nusram ta jinjina
kai sannan ta miƙe ta shige.

Nusram na fitowa ta sami Dr Saleema tana shiryawa itama ta hau nata shirin kafin
wani lokaci duka sun gama shiryawa.

A jere suka fito, Muhibba da Kamal ke saman dinning, yayin da Kabeer da Hafeeza
ke zaune a saman kujera suna haɗa taƙardu.

Duka idanu suka zubo musu wanda hakan yasa Nusram jin ta fara takura, bayan Dr
Saleema ta shige.

Koda suka ƙaraso saman kujera Dr Saleema taja hannun Nusram ta zaunar da ita
sannan itama ta zauna.

Kamal da Kabeer suka sauke ajiyar zuciya a tare, shiru ya ɗan biyo baya kafin
suka fara gaishe da yayar tasu.

Ta amsa cikin sakin fuska, tana miƙewa Mummy na shigowa, "ina kwana Mummy?", ta
amsa da lafiya lau, Nusram itama ta gaishe da ita kafin duka suka nufi dinning.

Muhibba tayi serving ɗin su, ita dai Nusram gabanta banda faɗuwa babu abinda
yake yi ga wani irin kallo da mazan ke binta dashi.

Ta kasa cin komai banda juya cokalin da take yi, Kabeer ya kalli ƴar uwar tashi
sannan ya kuma kallon Nusram wacce kanta ke sauke a ƙasa.

Tayi kyau sosai sanye take da atamfa me ruwan goro da ɗige-ɗigen kore, hijab ɗin
dake jinkin ta shima kore ne wanda ya ƙara haskaka fatar ta.

Hannun ta riƙe gam da wannan wayar dai ta Abdul domin kuwa barci ne kawai ke
rabata da wayar amma kusan koda yaushe tana hannun ta.

"Wai Yaya Saleema ina kika samo wannan kyakkyawar ne?", Dr Saleema ta ɗan
kalle shi kafin tace; "Ƙawata ce ta fara karatu anan Kaduna shine tazo zama anan".

"oho! Na gane sannu baƙuwa", Kabeer ɗin ya faɗa, Nusram ta ɗanyi murmushi wanda
yasa dukan su sakin baki tace; "yauwa sannun".

Zai kuma magana Mummy ta dakatar dashi don haka dole yaja bakin shi ya tsuke,
suna gamawa Dr Saleema ta miƙe inda itama Nusram ɗin ta miƙe.

"Yaya Saleema kika ce makaranta take yi da ai sai ki bari mu tafi tare da ita
ko?", cewar Muhibba wacce ta miƙe ta roƙo hannun Nusram ɗin.

Hafeeza ma ta miƙe ta kalli Kamal tace; "kai tashi mu tafi, kada mu makara",
har ya miƙe Mummy tace; "amma da dai da Kabeer kuka tafi shine fa zai je ɗauko
Daddynku a Airport".

Hafeeza ta duba agogon hannun ta kana tace; "ya dai kaini idan yaso ya dawo
daga nan ma sai yayi signing kawai", Mummy tace; "shikenan", daga haka suka juya
suka fice.

Ɓangaren su Dr Saleema kuwa ta kalli Muhibba tace; "wannan amanace a waje na ki


bari idan kuka ɗan saba sai ku cigaba da tafiya tare kinji".

Muhibba ta zumɓuro baki gaba tace; "ni wallahi Yaya Saleema ina sonta da ƙawa",
Dr Saleema tayi murmushi kana tace; "kada ki damu, Nusram muje ko".

Da Muhibba da Kabeer suka maimaita sunan cikin birgewa; "Nusram!!", Kabeer yayi
murmushi yace; "nice name", Muhibba ta kwashe da dariya.

Ita dai Dr Saleema ganin abin nasu bana ƙare bane yasa taja hannun Nusram ɗin
suka fice daga gidan.

Koda suka shiga mota babu wanda yayi magana, gaba ɗaya Dr Saleema ta maida
hankalin ta kan tuƙi yayin da Nusram kuma ta kunna wayar tana kallon hoton da ya
zamar mata jiki wajen kallon shi domin har yanzu bata san password ɗin wayar ba
hakan yasa sai dai ta kalli hoton idan ta gaji da kallo ta kashe ta ajiye.

A ɗan kaikaice Dr Saleema ta kalle ta, ta ɗan yi murmushi ganin hankalin ta ya


tafi gaba ɗaya kan wayar, bata ce da ita komai ba har suka iso babban asibitin
garin Kaduna inda Saleemar ke aiki.

Suna tafe suna gaisawa da jama'a har zuwa office ɗin Dr Saleemar, ga dai shi
asibitin gwamnati ne amma office ɗin babba ne hakan ke nunarwa da Dr Saleemar
babbace a asibitin.

Kan kushin ta nunawa Nusram ita kuma ta hau kujerar aiki inda ta fara ganin
marasa lafiya, ita dai Nusram na zaune tana kallon su haka har barci ya kwashe ta.

Bata farka ba sai daf da azahar, Dr Saleema data gama ganin marasa lafiya tana
shan coffee ta kalle ta tace; "lallai sannu da barci", Nusram ba tare da tace komai
ba ta miƙe ta zauna.

Babu jimawa wata Nurse ta shigo kiran Dr Saleemar, dan haka cikin sauri ta
miƙe, ta kalli Nusram tace; "Nusram zan shiga Theatre yanzu ga remote nan kiyi
kallo idan anyi kiran sallah ga bayi nan sai kiyi alwala kiyi sallah, idan kuma
kina jin yunwa ga wannan ki danna za'a zo sai ki faɗi abinda kike son ci, wata ƙila
na jima sosai, wata mata ce take naƙuda to kuma abin yazo da gardama bari naje
kinji", Nusram tayi mata fatan nasara kafin ta fice tana murmushi cike da yaba
hankalin Nusram ɗin.

Ta jima zaune kafin akayi kiran sallah, bayin ta shiga tayo alwala sannan tazo
tayi sallarta, koda ta idar a wajen ta zauna tana tunani.

Rayuwa kenan! Ko yaya ƴar uwarta take oho?, wane hali Ummi take shima bata sani
ba, ƙaddara duk ta raba su kowa ya kama nashi wajen.
Gashi bata da Number ɗin Nusreen balle ta kirata sai dai tana da number ɗin Ummi
da ta Auntyn Tudu dan haka zata roƙi Dr Saleema ta ara mata waya sai ta kira su ko
zata sami sauƙi.

To yanzu ma ina mijin da aka ɗaura mata aure dashi, waye ya san inda yake ma?,
tun jiya ko wane hali ta kwanta be dame shi ba.

Wata zuciyar ta ce mata; "ke Nusram shiga hankalin ki, kin manta cewa Baba ya
ɗauke ki kamar wata sanda ya bashi babu bincike ba komai, waye ya sani ma ko sadaka
ya bashi?, bata san lokacin da hawaye suka fara kwaranya a idanun ta ba.

Tun daga farkon tashinta ta fara tunani har kawo i yanzu, Baba be taɓa nuna musu
ƙauna ba ita da ƴar uwarta, ka ɗauki mutum sukutum da guda ka bawa wanda baka sani
ba.

Shin wai haka duk iyaye maza suke, basu da tausayi, imani da kuma ƙaunar akan
yaran su kodai sune basu yi dacen Uba ba?.

Ta girgiza kai, ba haka bane ai tana zuwa gidan su Auntyn Tudu tana ganin yadda
Abba ke haba haba da yaran shi har fira suke zama suyi dashi.

Kwatanta halayyar mahaifinta tayi data Abban, kwata-kwata basu da kamanceceniya,


tunda ta taso zata iya irga Albarkar da Baba ya taɓa saka musu, haka tunda take
dashi be taɓa zama sunyi fira dashi ba kuma be taɓa tambayar me suke so ba ko meye
damuwar su ba, shi dai kawai tunda ya haife su gani yake ya gama komai.

hannu taji saman fuskarta wanda hakan shine ya dawo da ita duniyar tunanin data
faɗa, ta ɗago idanun ta jajur ta zuba mishi su.

Shima ɗin ita yake kallo, tun jiya daya koma gida ko barci be yi ba saboda
tunanin halin da yake ciki.

Ya kasa yanke shawara guda ɗaya shin ya faɗawa Brr Farida ne ko kuwa yaja bakin
shi yayi shiru?, ƙarshe dai dole yaja matsaya akan kada ya faɗa mata.

Yarinyar tana bashi tausayi idan yayi duba da irin yadda aka barota daga gida
aka ɗauke ta aka damƙawa mutumin da ko sanin shi ba'a yi ba, dan ya tabbatar yanzu
da zai koma wajen mahaifinta ba gane shi zai yi ba.

Aiki ya taso dan shi a ƙa'ida huɗu yake tashi ko biyar, kamar ya wuce gida amma
sai yaga rashin dacewar hakan, dan haka ya yanke shawarar zuwa ya duba halin data
kwana.

sanin cewa Saleema na asibiti yasa ya taho kuma yana da tabbacin Dr Saleema ba
zata taɓa barin ta a gida ba.

Ya daɗe tsaye kanta amma bata sani ba saboda dogon tunanin data tafi, ya kauda
hannun shi daga fuskarta yace; "meke damun ki?".

Kanta kawai ta saukar ƙasa, ganin bata bashi amsa ba yasa ya taɓe baki sannan
ya miƙe ya koma saman kujera ya zauna.

Nusram kuwa a yanzu shi kanshi haushin shi take ji domin kuwa shima yana tuna
mata rayuwar ta da kuma zamowar shi silar barowar ta gida, duk da dai ta san cewa
taimakon ta yayi.

Jin an zare wayar hannun ta yasa ta kalle shi, wayar ya juya kafin ya kunna,
hoton shi ya bayyana yayi murmushi sannan ya maida wayar ya ajiye.
"da alamu dai ita kaɗai ta rage miki kadara ko?", ya faɗa, Nusram kuwa ko
arziƙin kallo be samu daga gare ta ba, ya ɗan jingina da kujera yana kallon fuskar
ta sosai.

Bata ɗago ta kalle shi ba har yanzu kuma bata ce dashi uffan ba, ya kuma taɓe
baki sannan ya kira Brr Farida.

Tana jin shi har ya gama wayar shi, sannan ya kuma maida kallon shi kanta yace;
"wai ke kurma ce kome?", nan ma bata yi magana ba.

Ya sunkuyo dai-dai fuskarta a ɗan hasale yace; "haka daman aka koyar dake zaman
auren?", har lokacin dai bata ce komai ba.

Zuwa yanzu fa ya fara hasala ya riƙo fuskarta yace; "ni nake miki magana kina
banza dani, baki san koni waye ba ko?".

Nusram kuwa ganin ya takura mata ga halin da take ciki na damuwa yasa ta fincike
fuskar ta, ta miƙe cikin sauri ƙafin taja tsaki ta juya domin tafiya.

Ko taku biyu bata yi ba ya damƙota, hannunta ya murɗe ta baya ya jingina jikin


ta da nashi.

"ni kike yiwa tsaki?", ya faɗa a fusace, Nusram hawayen azaba ya zubo mata, ta
runtse idanu tana me sakin kuka wanda hakan yayi dai-dai da shigowar Dr Saleema.

Sai da gabanta ya faɗi wani abu ya taso ya tokare mata maƙogoro, ta juya tana
ƙoƙarin ɗaukar laptop ɗin ta kana tace; "in tafi in barku ne ko kuwa zata zo mu
wuce?".

Babu wanda yayi magana a cikin su, sai lokacin taji shesheƙar kukan Nusram ɗin,
da sauri ta juyo ta kalle su.

Abdul kuwa kamar ma ba wani abun yake mata ba, ta kalli Dr Saleemar cikin
tsananin azaba tace; "Aunty Saleema hannu na".

Jin hakan yasa da sauri Dr Saleemar ta nufo inda suke, ganin yadda ya murɗe
mata hannu yasa tayi saurin ƙarasawa inda suke.

Hannun shi ta riƙo tace; "Abdul meye haka, dan Allah ka sake ta", kamar ba zai
sake ta ba can kuma ya hankaɗe ta kana ya juya ya fice.

Nusram ta faɗa saman carpet ɗin wajen kanta ya bugi kujera, taja numfashi
sannan ta saki kuka.

#LIKE
#SHARE
#COMMENTS

*Babyn Abdul, Maman Meenal Elham da Farouk*.

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 ✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*_daga alƙalamin ✍_*

*ƴar mutan zazzau*


*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*

*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖57-58📖📖

Dr Saleema ta jima tana

You might also like