BAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVEL NOVELS
BAKAR INUWA COMPLETE
HAUSA NOVEL
BAKAR INUWA
Kamar koda yaushe tunda suka zo garin yau ma ta
buga uban tagumi bayan kammala aikin gidan da a yanzu
ya zame musu tamkar wajibi ita da sauran ƴan uwanta.
Sai dai halinsu na rashin son moriya kesa duka aikin
ya dawo kanta sai abinda Yasmin taɗan iya tsakura a
ciki ta rage mata. Duk da azumi ne haka take dagewa
ta gyara komai tsaf, hakan ya saka gidan canjawa
cikin ƙanƙanin lokaci, da'alama dama rashin zama a
gyarashine ya sashi canja kamanni......
https://iganyabusinesshub.org/bakar-inuwa-complete-hausa-novel/9/ 17/08/2024, 04 05
Page 1 of 9
:
“Raudha!”.
Asabe ta kirayi sunanta da ɗan ƙarfi a karo na biyu. Firgigit ta
juyo ta kalleta dan sam bataji na farko ba.
Hannu Asabe ta shiga tafawa na taraddadi tana salati. “Oh ni
Asabe Raudha wai mi kike son maida kanki ne? Duka
shekarunki nawa da zaki jefa kanki cikin masifar tunane-tunane
mike damunki?”.
“Mommy babu komai fa, kawai na zaunane naɗan huta Yasmin
ta fito wanka nima na shiga”.
“Ƙarya kike Raudha, ki faɗamin gaskiyar abinda ke damunki tun
kafin mu saɓa.”
Ajiyar zuciya Raudha taja da ɗan ƙarfi tana haɗiye ƙwallar data
cika mata ido. Cikin yunƙurowar dukan damuwar dake akan
ƙirjinta ta fara magana. “Mommy so nake na koma islamiyya,
kinga dai rayuwa bazata tafi da ƙyau ba babu neman ilimi,
tunda babu tabbacin samun cikar burin yin makarantar gaba da
sakandire (secondary) inaga ya dace ace mun maida hankali
akan na addinin matuƙa, a ƙalla dai mun mori wani yanki na
arziƙin duniya dazai amfanar damu har a lahira. Amma idan na
ɓata miki rai a zancena kiyi haƙuri”.
Sosai zuciyar Asabe ta karye da tausayin ɗiyar tata. Ta sani duk
cikin ƴaƴanta babu mai nutsuwar Raudha. Yarinyace mai
hankali da sanin yakamata. Ya rinyace abar alfaharin
kowaɗanne irin iyaye. Sai dai yarinyace mai murɗaɗɗen hali da
wuyar sha’ani. Ba komai take kallo dai-dai da ra’ayin mutane
ba, ta rasa inda ta kwaso wannan bauɗaɗɗen halin nata da
taurin zuciya. A ido zakai mata kallon mai sauƙin kai, amma
sam ba haka baneba, wanda ya nutsu ga fahimtar halin Raudha
ɗinne kawai zai gane ra’ayinta yasha banban dana mutane…….
“Mommy kiyi haƙuri..”
Sassanyar muryarta ta katse tunanin Asabe. Guntun murmushi
ta saki tana kaiwa zaune kusa da ita, tare da kai hannu ta kamo
https://iganyabusinesshub.org/bakar-inuwa-complete-hausa-novel/9/ 17/08/2024, 04 05
Page 2 of 9
:
nata. “Karki damu indai islamiyya ce zan sakaku Raudha, sai
dai ki sani bazai zama dai-dai da yanda kike zuwa ta gida ba
har sau sama da uku. Saboda kinga nan zaku ringa zuwa wajen
aiki, kinga dai yanda sauran ƴan uwana ke tsaye bisa
ƙafafunsu, babu wanda ke zaune yana dogaro da Gwaggo.
Kowa neman na kansa yake yi ta yanda nima bazai yuwu na
zauna na zuba ido Gwaggo ta cigaba da ɗawainiya damu ba”.
“Hakane Mommy, sai dai ina roƙon dan ALLAH komi zamuyi ya
kasance bisa ƙyaƙyƙyawar hanyar da bazamuyi dana sani ba
watarana mu da ke. Bazan ɓoye mikiba Mommy wlhy sam
rayuwar gidan nan batamin daɗi, nafison hutawa….”
Harara Asabe ta dalla mata da ture hannayenta a cikin nata, rai
ɓace tace, “Uban hutawa kikafi so mara mutunci, Raudha bar
ganin ina lallashinki wlhy zan ɓata miki rai. Duk da buhun
wulaƙanci da tozarci da ubanku yay min har kike iya kallon cikin
idona kina faɗamin baƙya son nan kin fison Hutawa. To dan
ALLAH ga hanya nan koma Hutawar mtsoww mara mutunci
kawai”.
Hayaniyar Asabe ce ta fito da Hajiya Mama babbar yayar su
Asaben da yau bata fita ko’ina ba tana gidan tana barci.
“Asabe lafiya? Wa kikema ihu haka?”.
“Wannan mara mutuncin yarinyar Raudha mana.”
Ta faɗa a hasale tana harar Raudhan datai ƙasa da kanta
hawaye na gangaro mata bisa kumatu. Cikin ɓacin rai Asabe
taima yayar tata bayani kamar ta rufe Raudha da duka dan taji
zafin maganar datai sosai a ranta. Itama Hajiya Maman faɗa
tahau Raudhan da shi sosai har tana mata gorin ubansu bai iya
komaiba sai bin mata kamar tsohon bunsuru da busa sigari. Ba
Raudha kaɗai ba, hatta su Fatisa wannan furuci na Hajiya Mama
ya zafesu a rai matuƙa. Ana tsaka da wannan kicimilli ɗayar
yayar Asaben da suke kira Aunty Hannah ta shigo gidan. Da
alama fita tayi, dan sanye take da kaya na alfarma sai bula
ƙamshi take. Babu yanda za’ai mai kallo yace daga wannan
https://iganyabusinesshub.org/bakar-inuwa-complete-hausa-novel/9/ 17/08/2024, 04 05
Page 3 of 9
:
gidan ta fito duk da shima gidan nada ƙyau gwargwadon iko.
Sai dai shigar tata tafi kama data hamshaƙan mata da duniya
ke kan ganiyar ƙaunarsu da rungumarsu a jikinta. Ta ajiye key
ɗin motar ta bisa centre table ɗin falon tana kaiwa zaune.
“Nikam lafiya kuka rufe yarinya ƙarama da ihu tamkar wasu
kishiyoyinta?”.
Sanin halinta na rashin son ganin ana takurama yara Hajiya
mama tai saurin faɗin, “Hannah bar wannan ba abar goyon
baya baceba….” nan itama ta shiga zayyana mata abinda ya
faru da Raudha ta faɗa harya fusatasu.
Saɓanin su ita murmushi tayi tana gyara zama saboda wani abu
daya cuɗanya tunaninta da zancen Raudha ɗin cikin ƙanƙanin
lokaci, har takai ƙwaƙwalwarta ta haska mata wani nasara a
ƙananun daƙiƙu, dan yanzu haka daga government house take.
“Raudha badai islamiyya kike so ba? To zakije islamiyya”.
Ta faɗa murmushinta na sake faɗaɗa tare da shafa kan Raudha
a hankali. Su Asabe na buɗe baki da nufin yin magana ta girgiza
musu kanta tana miƙewa. Dukansu binta sukai da kallon
mamaki harta shige cikin ɗakin barcinta. Bawai amsa buƙatar
Raudha ɗin bane abin mamaki a wajensu, dan sun san itaɗin
mace ce mai son yara sosai, sannan ma tun zuwan su Asabe
gidan kowa ya fahimci irin son da take nunama Raudha, dan ko
abu zata saka ai mata kafin ta saka su Fatisa ta saka Raudha,
sannan har zama take suyi hira da Raudha ɗin. Abinda ya basu
mamaki ta shigo a yanayin damuwa sosai, amma dagajin
abinda suke ɗauka laifi ga Raudhan sai saɓanin hakan ya
bayyana a fuskarta, dan a zahiri tamkar abinda Raudhan tayi ne
ya warware dukan damuwar data shigo da shi cikin gidan………
Tofa minene a ran aunty Hannah da har yay dai-dai da burin
Raudha kuma?????
https://iganyabusinesshub.org/bakar-inuwa-complete-hausa-novel/9/ 17/08/2024, 04 05
Page 4 of 9
:
ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA????????????????????
1~ KUFAN WUTA????
Safiyya Huguma
1~ BAQAR INUWA????
Billyn Abdul
1~ RAYUWAR MACE????
Hafsat Rano
1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo
1~ NOOR ALBI ????
Mamuhgee
Guda 1????300
Guda 2??400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k
ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya????????
09032345899
KATIN MTN????????
https://iganyabusinesshub.org/bakar-inuwa-complete-hausa-novel/9/ 17/08/2024, 04 05
Page 5 of 9
:
09166221261
JAMA’AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR
kuma ta nan????????
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA
WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA????????
+227 95 16 61 77
TEAM ZAFAFABIYAR????????????????
BAƘAR INUWA…????????
https://arewabooks.com/book?
id=628103f05798291d0ecedd09
Da ɗumi-ɗuminsa????????????????????????????????
Please
Follow me
Share
Comments akan abinda ya shige maka duhu.
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages
galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka
https://iganyabusinesshub.org/bakar-inuwa-complete-hausa-novel/9/ 17/08/2024, 04 05
Page 6 of 9
:
karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following
ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara
ka bayar????????????????????????_
YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a
cike Form ɗin kamar haka: –
Enter your name: (Cikakken sunanki)
Enter your mail: (Email ɗinki)
Enter an username (Sunanki)
Enter your password: ( misali 12341234)
Confirm password: (misali 12341234)
Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a
ArewaBooks????????????.
Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka
kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account
a ArewaBooks kaitsaye.
Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
AREWABOOKS LINK kai tsaye
https://arewabooks.com/book?
id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
https://iganyabusinesshub.org/bakar-inuwa-complete-hausa-novel/9/ 17/08/2024, 04 05
Page 7 of 9
:
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba
komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma
buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan
abin alfaharine.
MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN
MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER
+234 903 177 4742
Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da
fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin
nan????????????????????????.
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
Typing????
Previous page 1 2 3 4 5 6 7
8 9 10 11 12 13 14 15 16
17 18 19 20 21 22 23 24
25 26 27 28 29 30 31 32
33 34 35 36 37 38 39 40
41 42 43 44 45 46 47 48
49 50 51 52 53 54 55 56
57 58 59 60 61 62 63 64
https://iganyabusinesshub.org/bakar-inuwa-complete-hausa-novel/9/ 17/08/2024, 04 05
Page 8 of 9
:
65 66 67 68 69 70 71 72
73 74 75 76 77 78 79 80
81 82 83 84 85 86 87 88
89 90 Next page
protected by reCAPTCHA
-
Privacy - Terms
https://iganyabusinesshub.org/bakar-inuwa-complete-hausa-novel/9/ 17/08/2024, 04 05
Page 9 of 9
: