0% found this document useful (0 votes)
39 views470 pages

Asanadin Makwabtaka 2 by Zee Laluh-1

Fatuu experiences shock and confusion upon seeing Haisam with another woman, Fanan, leading her to question their relationship. As the story unfolds, Fanan and Haisam engage in playful banter, revealing their close connection while Fatuu struggles with her feelings. The narrative explores themes of love, jealousy, and family dynamics within a vibrant social setting.

Uploaded by

Saleema Nalado
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as DOCX, PDF, TXT or read online on Scribd
0% found this document useful (0 votes)
39 views470 pages

Asanadin Makwabtaka 2 by Zee Laluh-1

Fatuu experiences shock and confusion upon seeing Haisam with another woman, Fanan, leading her to question their relationship. As the story unfolds, Fanan and Haisam engage in playful banter, revealing their close connection while Fatuu struggles with her feelings. The narrative explores themes of love, jealousy, and family dynamics within a vibrant social setting.

Uploaded by

Saleema Nalado
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as DOCX, PDF, TXT or read online on Scribd
You are on page 1/ 470

*ASM Bk2001*

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

Wani mugun bugu kirjin Fatuu ya fara yi tamkar ana mata luguden ta6are ganin abunda ke faruwa ta
cikin glass d'in hannuwanta har wani kerma suke saboda tsabar rud'ewa da razana don abune wanda
bata ta6a ganin Haisam d'in yayi ma wata Mace ba tunda take dashi, lokaci guda ta tambayi kanta
wacece wannan? Kasa jurewa tayi ta bud'e Motar ta fita ta tsaya a jikin kopar tana k'are mata kallo can
ta furta "AUNTY FANAN.....!" yadda ta furta da matukar razana, Ji tayi sam kafafunta suna niyyar kasa
daukarta saboda kermar da suke yi ga wani irin bugu da kirjinta keyi mata saboda tsabar razana,
tambayar dake ta faman kai kawo acikin zuciyarta itace, mike tsakanin Ya Handsome da Fanan da har
yake mata hakan? Ko k'annanshi da suke uwa d'aya uba d'aya bata ga yana masu hakan ba sai ita da take
Cousin d'inshi, to ko dae dama soyayya suke da ita ne? Damm! k'irjinta yay mata wani Mugun bugu yin
wannan tunanin lokaci guda kuma taji fitsari ya d'aure mata mara yana niyyar zubo mata da sauri ta nufi
gida ko kopar motar bata rufe ba ga wani duhu da take gani da kyar ta shiga gidan don har wani jiri jiri
take gani tsabar rud'ewa da kuma fargaba, toilet ta shiga tayo fitsarin tana fitowa ta nufi d'akinta ko ta
kan ta duba gwaggo bata bi ba tana shiga ta fad'a saman gadonta ta duk'unk'une wuri guda sai faman
zare ido take........

Nufar gaban Motar sukae hannunsu cikin na juna Fanan ta kalli wadda ke a mazaunin driver itama da
gani hutu ya zauna mata duk da ba fara bace irin fatar jikinta za'a iya kiranta da chocolate fuskarta lumi
tana da kyau ba laifi, da Murmushi Fanan tace "Khairat meet mah Babe" itama Murmushin take ta mik'o
mashi hannu tace "Hi Haisam it's nice meeting u" aikuwa da sauri Fanan ta ka6e hannun tace "he don't
do dat" dariya sosae khairat d'in tayi dama tsokanace kawae ba wani abu ba don tasan irin Mugun son
da take ma Haisam dole ne tai kishinshi sosae, gaisawa sukai da haisam tace "so ga heartbeat d'inka na
kawo maka sai a bani tukuici" fuskarshi da Murmushi yace ta fad'i abunda take so tace "bawani abu
babba nike so ba just babynka zaka kawo man ta kwana gidanmu don nayi ta kwanan man but she
refused" kallon Fanan d'in yay ta d'an yamutsa baki ta girgiza mashi kai alamar bazata je ba ta kwantar
da kanta a shoulder d'inshi, khairat tace "so now da babe d'inki ke gefenki shine zaki gujeni ko, it's owk
zamu koma india inda zan rama ne" k'ayataccen murmushinta mai k'ara mata kyau sosae ta saki tace
"kar ki damu Babe zai kawo ni in spending day" yar harara ta wurga mata tace bata so tana kokarin
tashin Motar Fanan na d'aga mata hannu tace sai sunyi Magana daga haka taja ta tafi, wani kallo mai
wuyar fassarawa yayi mata ta nok'e kai tana dariya har jerarrun hakoranta farare tass suka bayyana yace
"Why baki sanar dani about your coming today?" cikin muryarta ta yan gayu tace "am so eager to see u
babe shiyasa na baka huge suprise" ta k'arasa Maganar tana kashe mashi ido, hannu ya kai yaja dogon
hancinta tayi yar k'ara yace su shiga ciki har zasu juya tace mashi Zarah fa Hajiya ta gaya mata sun fita
outing tare sai lokacin ma ya tuna da Fatun na acikin Motar har ya juya ya hango kopar a bud'e ba tare
daya kawo komae ba yace yana tunanin ta shiga gida ma, still hannunsu na cikin na juna suka nufi Motar
tace ya zagaya d'ayan side d'in ita ta shiga side d'in driver tajasu suka idasa gidan bayan Officer CD ya
bud'e masu gate, bayan sun shige ya rufe gate d'in ya dawo kan bencin daya tashi ya kalli d'ayan Officer
yace "ita wanccan d'in wacece wai, ba itace naga dazun an kawo a jeep d'in nan ba?" yace mashi "eh
itama jikar Hajiyarce baka ganin kalanta na zuwa"

"Itama ta wurin Hajiya Maryam d'ince kenan?" kai ya d'aga mashi alamar eh yace "Ma sha Allah
amman duk tafi yan uwanta kyau gaskiya ni ban ta6a ganinta ba sai yau" Officer ya amsa mashi da eh ai
bata cika zuwa ba kuma yanzu tana karatu a kasar waje ne,

tana ruke da hannun Haisam suka shiga falon Hajiya lokacin tana zaune kan kujera tana kallon tv, Fanan
ce tayi sallama hajiya ta maido idonta kansu tana kallonsu da Murmushi suka nufi 2 seater suka zauna
Hajiya tace "ina ta nemo ka" yana Murmushi yace "mun dawo ne"

"Ai ce man tayi in ta raka k'awarta bazata shigo ba har sai ta nemo ka wai,nace to Allah ya bada sa'a da
yake ma akwae gidajen radio isassu maji cigiyarta in an tsinceta" d'an kallon fanan d'in yay still
murmushi take kanta a saman kafad'arshi Hajiya taci gaba "sai kawae ganinta nayi kaman daga sama fa
ni abun mamaki ma ya ban har saida na kira uwar tata nai mata korafin baza'a sanar mutum zai zo ba a
shirya masa take ce man wai ita ta hana a sanar mana tana so ne ta bamu mamaki nace aikau ta bamu
mamakin gashi tazo ma tak'i cin Abinci wai sai kazo zaka bata a baki nace ai sai taita jiranka tunda ita ba
ranar da zata girma da hakan" shidae Murmushi kawae yake can ya mik'e ya d'agata ganin zasu nufi
Dining area yasa tace mashi "but Babe u need to take bath ka dawo daga wani wuri nasan ka gaji" girgiza
mata kai yay suna nufar dining table d'in yaja kujera ya zaunar da ita yace "eat first" yaja kujeran
gabanta shima ya zauna k'in ci tayi wai sai dae ya bata a baki tayi missing hakan dole a bakin ya rink'a
bata cike da kulawa, bata wani ci mai yawa ba tace ta koshi yace bai yarda ba tace ai ta d'an ci agidansu
khairat tunda acan suka fara sauka sannan ya kyaleta, k'ara kama hannun juna sukai suka nufi cikin Falon
zasu fita yace ma Hajiya zaije yay wanka tace to,ganin zasu fita tare tace ma Fanan bazata jirashi ya
dawo ba ta mak'e mata kafad'a wai zata je ta za6ar mashi kaya ne, d'an ta6e baki Hajiyar tay tace adawo
lafiya.

Jama'a ina Fatuu???


Tunda ta kwanta bata mik'e ba sai faman sak'e sak'e take aranta ga wata irin fargaba data
mamayeta ,fitowa gwaggo tay daga dakinta idanunta suka sauka kan takalman Fatuu dake ajiye a bakin
kopa da mamaki aranta tace wannan ai takalman da Fatuu ta fita dasu ne ta dawo ne, nufar d'akin tayi
tana kwala mata kira tana jin muryar gwaggon ta rufe fuskarta da gyalenta dake yashe gefe yabar saman
kanta, d'aga labulan tayi ta hangota a kwance har lokacin da mamaki akan fuskarta ta kira sunanta
amman bata amsa ba har saida ta k'ara kiranta sannan ta amsa tace "yaushe kuka dawo ne?" daga
yadda take tace "yanzu ba dad'ewa Kawu shi6ado na gaidaki sun bada sak'on dawon Fura da Nono ma
akawo maki yana Mota" da kyar take Maganar hakan yasa gwaggon cewa "To lafiya kika wani
dukunkune saman gado?" shiru ta d'anyi tana tunanin abunda zata ce mata can tace "banjin dad'i ne
kaman zazza6i zai kamani nike ji shiyasa ma dana shigo ban maki Magana ba" shiru gwaggon tayi tana
k'are mata kallo kafin tace "ina shi yayan naki yake?"

"Muna dawowa yaga sun yi bak'i ya tsaya wurinsu shine ni kuma na shigo" jinjina kai tayi tace "halan
kinyi wasa da ruwa ne ko, nasan halinki sarai baki ganin ruwa ki k'yale" sai lokacin ta cire gyalen fuskarta
ta bayyana ta kalli gwaggon tace "a'a wllh ai Ya Handsome bazai barni ba kawae dai banjin dadin jikinne"

"To Allah ya sawake ki tashi kici Abinci sai kisha Magani" tace "na k'oshi da Abincin bari dae insha
maganin kaina ciwo yake man sosae" tana gama Maganar ta saukko daga gadon da k'yar ta tunkari kopa
gwaggo ta saki labulan ta koma d'akinta ta d'aukko mata Maganin ta fito ta bata, ganin yamma tayi
sosae yasa tace ta shiga Falo ta zauna Magriba ta kusa ba'ason kwanciya a irin wannan lokacin in tayi
Salla sai ta kwanta tace mata to.

Bayan sun shiga Parlon Haisam sosae Fanan ta yaba da tsarin parlon, Haisam yace ta zauna bari yaje yay
wanka ya juya zai nufi hanyar Bedroom kawae sai ji yay tace "should i come and help?" cak ya tsaya ya
juyo yay mata wani kallo tasa dariya daga haka ya juya yana shiga Corridor ta d'an d'aga Murya tace
"Soon i would be doing dat to u Babe" girgiza kai kawae yay ba tare daya juyo ba ya tura kopar Bedroom
din ya shige, bayan wani lokaci ta mik'e ta nufi Bedroom d'in sanin yana toilet, bin d'akin tayi da kallo
kafin ta nufi Closet d'inshi ta bud'e dan dudduba kayan tayi ta za6o mashi wanda zai sa ta d'aura su a
gefen gado ta koma gaban Dressing mirror ta jawo drawer chest ta sama ta daukko kwalin agoguna data
gani ta fiddo wadda zata hau da kayan ta daurata samansu kafin ta mayar da kwalin daga haka ta juya ta
fito falo, bai dau wani dogon lokaci ba saboda Magrib tayi ya fito sanye da bathrobe yana ganin kayan
data ajiye mashi yay wani kayataccen Murmushi, bai dau wani dogon lokaci ba ya gama shiryawa cikin
kayan ya fita tana zaune kan L-shape idanunta akan tv tana kallo jin fitowarshi yasa ta mik'e ta nufeshi
tana mashi Murmushi ya kama hannunta suka fita, saida ya rakata har bakin entrance d'in falon Hajiya
sannan ya juya ya wuce Masallaci da aka fara kiran salla itama tana shiga d'akin Hajiya ta wuce don tace
bata zama ko wane d'aki sai nan lokacin Hajiya ta kabbara salla ta wuce Toilet tayo wanka ta fito d'aure
da farin towel, trolley d'in kayanta ta d'aura gefen gado ta bud'e ta fiddo riga da wando marasa nauyi
rigar off shoulder ce blue sai wandon baki,bayan ta shirya ta d'aukko d'aya daga cikin hijjaban Hajiya
dake cikin wardrobe tasa itama ta kabbara sallar, bayan an gama sallar isha gaba d'aya suna zaune a
falon suna fira Fanan na manne jikin Haisam sai kace mage Hajiya tace "wai ni ina yar tafiya ne tunda
kuka dawo banji d'uriyarta ba sun gaisa da Auntynta Fanan kuwa ma?" Fanan d'in tace "No ban ganta ba
ta shiga gida ne bayan sun tsaya so bata zo wurina ba" Hajiya tace "aikuwa yakamata a aika masu da
abubuwancen tunda kace d'aya ledar furar tasu ce ga kuma kifi shima a d'ibar mata Dije ta ga tsarabar
Dam bari Saude ta je ta kai masu" tana rufe baki Fanan tace "ki kawo mu kai masu mana sai in gaisa da
granny d'inta" Saude ta k'wala ma kira bayan ta fito ta gaisar dasu gaba d'aya Fanan na Murmushi ta
amsa mata, umarnin ta d'ebo rabin kifin a leda sannan ta d'aukko leda d'aya ta fura da nono ta bata, ba
6ata lokaci ta kawo mata, mik'ewa Fanan tayi ta nufi Bedroom ta yafo d'an madaidaicin veil ta dawo
hannunta ruk'e da wata yar babbar leda mai handle tace ma Haisam su je yace taje ita kad'ai cike da
shagwa6a tace ita da bata san gidan ba Hajiya na dariya tace "ka rakata mana ita da ke bak'uwa" kafeta
yay da idanu yana mata wani kallo ya d'an lumshe ido kafin ya yunkura ya mik'e yace suje ta d'auki
ledojin ta bashi d'aya ya rike tace ma Hajiya sai sun dawo, lokacin da suka isa kopar gidan tsayawa yayi
yace ta shiga zai jirata amman tak'i wai ita da ba'a sani ba bashi ne zai gabatar da ita ba yace to ta shiga
tace zai shigo tace to, suna a Falo gwaggo na zaune kan kujera idonta akan tv Fatuu kuma na kwance kan
darduma dake shimfide kan Carpet tun bayan data gama salla tai kwance wurin da k'yar gwaggo ta samu
ta dan ci Abinci kad'an don duk jin bakinta take ba dad'i, da zazzak'ar muryarta ta kwad'a sallama har
saida gaban Fatuu ya fad'i, amsawa gwaggo tayi ta tashi ta nufi hanyar fita ta tsaya bakin kopa tana
kallonta har saida gabanta ya d'an fadi ganin wadda tay sallamar a d'arare tace "Maraba ki shigo"
k'arasowa tayi gaban gwaggon ta aje ledojin hannunta tace,

"Ina tare da Ya Haisam zai shigo" ta fad'a da hausarta mai dad'i gwaggo na jin hakan da sauri tace "to
to ba wani abu kice ya shigo" juyawa tayi da d'an d'aga murya tace "Babe Come in" da sallama ya shigo
gwaggo ta idasa fitowa tana amsa mashi tay masu nuni da cikin Parlon tace su shiga,cire takalmanshi yay
ya shiga Fanan ma ta daukki ledojin tabi bayanshi suka zauna tare saman 3 seater gwaggo ma ta zauna
saman 1 seater, cikin cool voice d'inshi ya gaida gwaggon ta amsa tayi mashi ya gajiyar tafiya da godiyar
ziyara Fanan ma ta gaidata da fara'a itama tana mata dariya ta amsa shiru ta d'an biyo baya sai
Murmushi suke ma juna can gwaggon tace"ban wayeki ba ko bak'in da Fatuu tace an yi ne"

"Eh nine na zo daga Lagos" gwaggo tace "to yar wajen Hajiya Maryam ce kenan, to babbar ce ko
k'aramar ni sunanku had'e man yake wllh" ta fad'a tana dariya Fanan d'in tace "Fanan ce babban",

"Ah kice Amarya ce kenan" tana dariya tace "eh nine" tana rufe baki Haisam dake latsa waya ya d'an
bugeta da hannunshi ta juya da sauri tace mashi "What?" shiru yay bai d'ago ba bai kuma ce mata
komae ba gwaggo na dariya tace "ai kwanaki can muna fira da Hajiya take gaya man anyi baikon ku tuni
amman sai kin gama karatu za'ai bikin, ko kin ma gama ne?"

"Yea but zan koma akwae wani exam da zamu yi shine final",

"To ma sha Allah, Allah ya bada sa'a" tace Amin, kokarin mikewa gwaggon tayi tana Fad'in ta barsu ko
ruwa Fanan din tace "ba wani abu granny yanzu munsha ruwa harda Abinci" gwaggo tace "amman dae
yakamata kisha na zumunci ko" tana dariya tace to abata, bayan gwaggo ta kawo mata ruwan da lemu ta
fara kokarin zuba mata a Cup tana ta barshi zata zuba tace a'a ai ita bak'uwa ce ba'a barta da aiki ba,
bayan tasha ta aje cup tace ma Gwaggo ga kayan sis Zarah gwaggo na dariya tace tsarabar tafiya tace eh
ta nuna nata tace wannan ita ta kawo mata gwaggon tayi mata godiya sosae tace Allah ya bar zumunci,
kallon inda Fatuu ke kwance tayi tace "itane ke bacci" gwaggo tace "eh tun d'azun take ta faman
kwanciya tunda ta dawo wai bata jin dad'in jikinta kuma kanta na yi mata ciwo" ta kai hannu tana
kokarin tashin Fatun Fanan na ta kyaleta gobe sun gaisa, duk abunnan da suke kaf tana jinsu jikinta ya
mutu murus a inda take ba kamar data ji Maganar aure dake tsakaninsu yanzu ta tabbatar da abunda
zuciyarta ke zargi, kenan ita ba sonta yake ba? Wannan tambayar ita ta tsaya mata har wani tuk'arta
take a k'irji kaman zata yi amai, tadata gwaggo ta shiga yi tana Fad'in bari dae ta tashi su gaisa bata
tunanin baccin yayi wani nisa tana cikin tashin nata taji wani amai ya taho mata da sauri ta tashi tsaye
hannunta dafe da bakinta tayi hanyar fita Falon da gudu,tana fita ta nufi hanyar Toilet saidae tana kaiwa
saitin kitchen ya zubo mata da k'arfi ta durkushe anan tana kwara shi sai kace yan hanjin cikinta zasu
fito, a rud'e Fanan da gwaggo suka bi bayanta suka nufeta da sauri Fanan ta duk'a ta dafata tana Fad'in
"Sannu Sis Zarah" gwaggo ma sannun take ta mata duk Fanan tabi ta rud'e, da k'yar aman ya tsaya tasa
hannu guda ta dafe gaban kanta tana nishi da karfi yayin da d'ayan hannun ke dafe da k'irjinta Fanan ta
kalli gwaggo tace "granny pls ki bamu ruwa" da sauri tace to ta nufi kitchen ta d'aukko wata yar roba taje
bakin fanfo ta taro ruwan, bayan ta kawo mata tallabo kan fatun tayi ta zuba mata a baki tace ta kuskure
bakin kafin ta wanke mata fuskar, d'agata tayi ta nufi cikin parlon da ita gwaggo kuma ta fara gyara
wurin, sauran ruwan roban data sha ta daukko ta bud'e murfin ta kafa mata abaki tace tasha, sosae
tasha ruwan don kirjinta wani irin zafi yake mata,

"Sannu sis Zarah" kai ta d'aga mata tana kokarin kwanciya, bayan ta kwanta matsawa Fanan tayi
gefenta ta zauna tana d'an tatta6a jikinta ta tambayeta ko cikinta ya lalace ne fatun ta girgiza mata kai
alamar a'a, duk wannan abun Haisam na zaune yana kallonsu ko lokacin da take yin aman yana ji,
dawowa gwaggo tayi ta zauna inda ta tashi Fanan ta tambayeta tasha Magani ne tace eh ta bata
paracetamol d'azun da tace kanta na ciwon, ta6a jikinta ta sake yi jin da d'an zafi yasa ta kalli Haisam
tace tana tunanin Malaria ce ke damunta abunda yafi ayi mata allura kawae, kai ya d'aga mata ya mik'e
yace bari ya d'aukko mota suje su siyo tace ok, bayan ya d'aukko Motar horn yayi mata ta mik'e da sauri
tace ma gwaggo bari suje su dawo tace to, komawa tayi kusa da Fatun bayan sun fita ta zauna tana mata
sannu ita dae kai kawae take d'aga mata, bayan kaman minti 30 suka dawo Fanan ce kawae ta shigo shi
Haisam yana waje cikin Mota duk ciwon da Fatun keyi ya dameshi ganin lafiya lau suka dawo da ita
amman har yayi tsanani haka, Artemether da paracetamol injection suka siyo, had'a allurar ta shiga yi
bayan ta gama tayi mata har saida gwaggon tayi mamakin yadda ta tsaya tayi mata allurar don ita in zata
yi mata wani lokacin sai tayi fama da ita da can ma da bata girma ba haka wani lokacin sai tasa Amadu ya
ruke mata ita, bayan ta gama ta tambayi inda dustbin yake gwaggo ta mik'e ta amsa taje ta yado su ta
dawo Fanan tace ma gwaggo yakamata taje d'aki ta shiga Net saboda sauro tace to, mik'ar da ita tayi
suka nufi hanyar fita gwaggo na biye dasu ta tambayi ina d'akin da zata kaita gwaggo ta nuna mata
dakinta suna shiga ta nufi gado da ita ta taimaka mata ta kwanta sai faman sannu take ce mata kai
kawae take d'aga mata ita kanta Fatun bata san mi take ji game da Fanan d'in ba ita kawae abunda ya
dameta shine Ya Handsome bai sonta ba zai Aureta ba, a hankali kwalla suka fara ziraro mata daga
kwancen ta juya masu baya yadda bazasu ga Fuskar tata ba,

"Granny ni zan tafi Ya Haisam na jirana gobe in sha Allah zanzo in yi mata second dose" godiya sosae
gwaggo ta shiga yi mata tana cewa Allah yasaka da Alkhairi ya bar zumunci ta amsa da Amin juyawa tayi
ta dafa jikin Fatuu tace "Sis Zarah Allah baki lpy kinji" kai ta d'aga mata kawae ta juya ta tafi gwaggo tayi
mata rakiya har zaure saida ta lek'a ta k'ara yi ma Haisam godiya kafin ta komo daki wurin Fatuu, a gefen
gadon ta zauna tana kallonta yayin da take ta sak'e sak'e aranta game da silar ciwon Fatun tsoronta kar
ace abunda take tunani ne sanin inda suka je ciwon na iya tasar mata, yin wannan tunanin yasa da sauri
ta girgiza kai a fili tace "in sha Allahu bama shi bane" dafata tayi tace mata sannu ta d'aga mata kai ta
tambayeta ko tana son wani abu ta girgiza mata kai alamar a'a tace "to tashi ki rage kayan jikinki bari in
je in d'aukko maki wanda zaki canza" bayan taje d'akinta ta d'aukko mata kayan bacci da taimakon
gwaggon ta tashi ta canja kafin ta koma ta kwanta gwaggo ta lullube mata rabin jikinta tasa mata Net.

Bayan sunyi parking Motar a parking space suka fito sukai ma juna irin rukon nan na turawa wato a
sak'ala hannu suka nufi part d'in Hajiya, lokacin da suka shiga ba kowa a falon hakan yasa suka wuce
bedroom dinta lokacin har ta kwanta amman bata yi bacci ba wutar d'akin ma a kunne take da alama
jiransu take, jin motsin shigowarsu yasa ta d'ago ta kallesu suka nufeta suna Murmushi suka zauna a
bakin gadon,

"Ai nayi zaton Zarah ta rik'e ki acan zaki kwana don nasan dole zatayi farinciki da zuwanki" da sauri
Fanan ta girgiza mata kai da yar damuwa tace "Sis zarah ba lpy dat's why we stayed a bit long"
yunkurawa Hajiya tayi ta tashi zaune da mamaki kan Fuskarta tace "Ba lpy kuma miya sameta" fad'i mata
abunda ya faru Fanan din tayi harda uban aman da tayi Hajiya tasa salati ta kalli Haisam dake saurarensu
tace "dama bata lpy kuka dawo" kai ya girgiza "No lafiyanta lou wai bayan ta shiga gida tace ma grandma
d'inta tana jinta abnormal and kanta na mata ciwo sosae" jinjina kai Hajiya tayi da yar damuwa akan
fuskarta tace "tohhh, Allah ya kyauta yasa ba mutanenta bane kuwa tunda anje wurin ruwa" cikin rashin
fahimta duk suka kalleta Fanan ta tambayeta suwaye mutanenta,

"Jinn nike nufi" waro ida Fanan tayi a rud'e tace "Ajanu!" yadda tayi Maganar har saida Hajiya ta d'anyi
dariya ta jinjina mata kai alamar eh,

"Dama tana dasu?" Haisam daya kasa hakuri ya tambaya, Hajiyar tace "Eh mana amman basu kada ita
yanzu saidai su sata ciwo, tama dad'e gaskiya bata yi ciwon da take irin nasu ba" jinjina kai yay taci gaba
da cewa "ai na Mahaifiyarta ne suka komo kan Fateemar amman basu cutar da ita gaskiya sai rashin ji da
suka saka mata" wani d'an guntun Murmushi haisam d'in yay ya furta "the whole things make sense
now",

"but su dama basu son aje wurin ruwa?" Fanan da duk alamun tsoro ya bayyanar mata ta tambaya
dariya hajiya tasa tace "ai kinsan su ko ina akwae su ba iya wurin ruwan ba saidae akwae inda zaki ga
sunfi zama kaman toilet to wurin ruwan ma matattararsu ce, kai bamma tunanin su ne gaskiya k'ilan dai
ta de6o sanyi ne kawae shine ya tado mata zazzabin" jinjina kai Fanan tayi tace Allah dai ya bata lafiya
hajiya ta amsa mata da Amin, mik'ewa Haisam yay yace zaije ya kwanta Hajiya tace "Allah ya bamu
Alkhairi" kokarin mikewa Fanan ta fara yi tace bari ta rakashi yace tay zamanta tace ko bakin kopa ne,
suna fitowa yace ta koma sai kawae ta jingina bayanta da bango tana mashi wani kallo mai cike da
tsantsar kauna hannu ya kai ya d'an shafi cheek d'inta da wata irin Murya ya furta mata "I luv u
Sweetheart" hannu tasa ta dafa hannun nashi tana Murmushi tace "dat's my breath babe" yar dariya
yayi ya fara kokarin wucewa ta kamo hannunshi ta baya ya juyo da narkakkun idanu tace "Gud nyt nd
Dream of me" lumshe ido yay kafin yace "Always" d'ago hannun tay tayi mashi kiss a bayan hannun kafin
ta saki ya tafi, saida ya kai bakin kopar fita ya juya ya kalleta yay mata alamar ta shiga cikin d'aki da
kanshi,blowing kiss tai mashi kafin ta d'aga hannu tay mashi bye bye ta juya ta shige..........

*ASM2002*

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

..........Washe gari da suka tashi ta d'an ji sauk'in jikin nata kawae yanzu fargaba ce tafi damunta hakan
yasa duk bata jin dad'in kirjinta bayan tayi sallar Asuba komawa tay tayi lamo kan gado sai sak'e sak'e
take aranta, yanzu shikenan ta rasa ya Haisam, tana ji tana gani zai yi auranshi ya tafi ya barta, haka dai
take ta tunane tunane tana matse k'wallan dake zubo mata ba tare da gwaggo ta ankare ba don ita duk
tunaninta bacci Fatun ta koma, Wuraren k'arfe tara saura tazo ta tashe ta tayi karin kumallo, bayan taje
tayo brush ta zauna don yin breakfast d'in saidai sam tama kasa cin komae don bata jin dad'in bakinta
gwaggo dake zaune gabanta ta lura da hakan tace mata ta daure in taci sai tafi jin dad'in jikinta ta dai
d'aga mata kai kawae, da k'yar ta d'an tuttura ta mik'e zata kwashe kayan gwaggon tace ta bassu taje ta
kwanta in ta gama zata d'auke, bayan ta gaman ta kwashe komae ta kai Kitchen bata dawo d'akin ba
saida ta had'a ma fatun ruwan wanka a toilet tace ta daure taje tayi ko ta ji k'arfi, d'akinta ta koma ta
cire kayan jikinta ta d'aura towel ta yafa mayafi kafin ta fito ta nufi toilet walking slowly don duk jikinta
ba k'arfi, bayan ta fito doguwar rigar material kawae ta zura ta haye gado taci gaba da tunane
tunanenta,
Wuraren k'arfe 11 Fanan ta farka tun bayan sallan Asuba data koma tana saukko da k'afafunta k'asa
idanunta suka sauka akan wata yar guntuwar farar takarda dake ajiye kan bedside drawer, hannu ta kai
ta d'auki takardar tana duba rubutun dake jiki kamar haka,

_Went to work_

_Luv u_

Shine rubutun dake ajiki Murmushi ta saki sanin Haisam ne ya ajiyeta, baki ta kai paper d'in ta manna
mata kiss had'i da furta Luv u too Babe,maidata tayi inda ta d'auketa ta ajiye ta wuce toilet don yin
wanka bayan ta fito ta shirya cikin skinny jeans blue da farar top bayan ta gama shiryawa ta dauki
wayarta ba tare data rufe kanta ba ta saki brown gashinta ya zuba gefe da gefen fuskarta ta nufi Parlor
ganin ba Hajiya a falon yasa ta nufi d'akin Saude tana kwance kan katifa tana huta gajiyar aikin gidan
data gama bada jimawa ba, zazzak'ar muryarta saude ta jiyo tana yi mata sallama hakan yasa ta tashi
zaune da sauri suka had'a ido ta sakar mata Murmushi itama sauden Murmushin take mata don ba
k'aramin burgeta take ba,

"Ina kwana" Saude ta gaidata ta nufo inda take ta zauna gefen katifar da Murmushi tace "kin tashi lpy
ya aiki" tace "Alhamdulillah" shiru suka d'anyi kowa Murmushi ne akan fuskarshi can Fanan d'in tace
"Hajiya ta fita?"

"Eh bata dad'e da fita ba taje wurin aiki ne" jinjina kai tayi sauden ta kuma cewa "ga breakfast can na
shirya maki a kan table",

" Owk thanks",

"Babe ya shigo kuwa yayi breakfast?" ta tambaya tana kallon sauden,shiru ta d'anyi don bata gane babe
d'in da take nufi ba gane hakan yasa fanan d'in cewa "I mean Ya Haisam" da sauri tace mata "eh ya shigo
d'azun da shirin zuwa aiki ya shiga d'akin Hajiya kafin ya fito ya tafi,

"yayi breakfast?" kai ta girgiza mata "a'a ai bai yin breakfast yake tafiya gaskiya sai dai wani lokacin in
hajiya ta matsa mashi yake dan yi shima dai kad'an" jinjina kai tayi tace "har yanzu baison cin abinci ko?"
yar dariya Saude tayi kafin tace "eh to gaskiya yana ci amman fa ba sosae ba shima dai sai Hajiya ta
matsa mashi yake d'an ci da d'an yawa" jinjina kai ta sake yi ta fara kokarin tashi Saude tace "Breakfast
d'in zakiyi inzo in zuba maki?",

"No don't worry zanyi serving kaina"

"Don Allah ki bari kar aikin yayi maki yawa" d'an waro ido tayi alamar mamaki tace "miye ne aiki ciki just
serving Myself ai kene mai yin aiki so just relax" tayi Maganar tana mata alamar ta kwanta da hannu ta
juya ta nufi kopa Saude ta bita da ido tana Murmushi aranta take ayyana kirkin yarinyar yayi yawa sam
ba halinsu d'aya da yar'uwarta ba, tana fitowa bata nufi dining don sai taji bata son yin breakfast d'in ita
kad'ai, Bedroom d'in Hajiya ta koma ta d'aura boyfriend jacket bak'a mai d'an ratsin fari ta yafa d'an
k'aramin bak'in gyale ta fito, gidansu Fatuu ta nufa wayarta ruk'e a hannunta tana zuwa bakin gate ta
tsaya suka gaisa da su Officer tana ta Murmushi suma duk suka washe mata baki bayan ta wuce ne su
kau yabonta, tana shiga gidan ta tsaya bakin kopa ta rafka sallama da zazzakar muryarta "Salamu
Aleeikum" tana niyyar k'ara yin wata gwaggo ta fito daga cikin d'akinta tana amsa mata sallamar suna
ganin juna suka saki Murmushi gwaggon ta nufeta tana Fad'in "Ah ya kika tsaya anan ki shigo mana
y'ata" nufota tayi suka had'e a tsakar gidan d'an side hug tay ma gwaggo tace "ina kwana granny" da
fara'a tace "lafiya lou y'ata ya gajiyar tafiya kuma"

"Babu shi" ta bata amsa gwaggon na niyyar ce mata su shiga falo tace "ina Sis Zarah ya jikinta fa" tace
mata da sauki sosae tana cikin d'aki "owk bari in ganta" tare suka juya suka nufi d'akin gwaggo Fatuu da
duk abunda suke tana jinsu tana jin sun nufo d'akin tayi saurin juyawa yadda baza'a ga fuskarta ba ta
runtse idanunta sosae, suna shiga d'akin Fanan ta nufi gadon ta zauna a gefe ta kai hannu tace "Sis
Zarah" shiru bata amsa ba hakan yasa ta kalli gwaggo tace ko tana bacci ne, ita kanta gwaggon ta d'anyi
mamakin ganinta haka don lokacin da Fanan d'in tayi sallama tasan ba a haka take kwance ba idonta
biyu har suna ma d'an Magana da ita, matsawa tayi gaban gadon ta kira sunanta da d'an karfi ba yadda
ta iya dole ta amsa mata sanin gwaggon tasan ba bacci ta barta tana yi ba,

"Ki tashi ku gaisa da Auntynki da tazo nasan jiya ba lalle ma in kin gane wacece ba kina cikin ciwo" d'an
jimm tayi kafin a hankali ta yunk'ura ta tashi zaune ta kalli Fanan dake ta faman yi mata Murmushi
murya can ciki tace mata "ina kwana, anzo lafiya" hannu ta kai ta dafa shoulder d'inta tace "Lafiya, ya
jikinki" amsa mata tayi da sauki tace Allah ya bata lpy, ganin yadda take ta faman yi mata Murmushi yasa
itama da kyar ta d'anyi mata na yak'e,

"How are u Feeling Now?" ta tambayeta k'asa k'asa tace mata "da sauki sosae kawae bana jin karfin
jikinne" still hannunta na asaman kafad'arta tace mata ta kwanta, komawa tayi ta kwanta dama bata so
tashin ba cike da kulawa take kallonta kafin ta maido kallon kan gwaggo dake zaune ta tambayeta tayi
breakfast tace mata eh ta d'an ci kad'an, fira suka shiga yi da gwaggon kai kace dama can sun saba tace
ko ta kawo mata wani abu taci bata kaiga d'aura abincin rana ba tace mata a'a ta barshi can gwaggon ta
mik'e tace bari taje ta d'aura girki fanan d'in tace mata ba damuwa bayan ta fita wayarta ta shiga
latsawa tana yi tana d'an d'agowa ta kalli Fatuu can ta kai hannu ta dafa kafafunta tace "Sis Zarah am
really worried about ur condition, Allah ya baki lafiya kinji" a hankali ta ware idonta kan Fanan d'in dake
kallonta cike da damuwa wani iri taji don ita kanta bata ta6a tunanin zasu kasance haka da Fanan ba
yadda suka shak'u sosae har ta k'agara ta ganta a zahiri saboda yadda take nuna mata k'auna bata ta6a
tunanin zuwanta zai jefata a matsala haka ba, a hankali wasu yan siraran hawaye suka zubo mata tana
k'okarin gogewa fanan d'in ta matsa da sauri tana Fad'in ta daina kuka zata samu lafiya bada jimawa ba
in sha Allah wai akace rashin sani yafi dare duhu, wayartace ta fara ringing takai idonta kan screen d'in
ganin mai kiran nata yasa ta saki Murmushin da tun bata d'auka ba Fatuu ta yanke wanda ya kirata, cikin
murya mai cike da tsantsar kauna bayan ta d'auka tace,

"Hlo Babe, how Work?" ta tambaya, on the other hand ya bata amsa da lafiya kafin ya tambayi tana
ina tace mashi tazo ganin Zarah ne ya tambayi ya jikinta tace da sauki,
"am on my coming back now" ya fad'a, d'an ware ido tay ta cire wayan daga kunnanta ta duba time
kafin ta maida tace mashi amman still Working hours ne ya akai zai dawo yace saboda bata yi breakfast
ba yar dariya tayi tace waye ya fad'a mashi bata yi breakfast ba yace a jikinshi ya ji, cigaba da fira sukae
cike da kauna har ta tambayeshi ya taho da gaske yace eh yana driving ma suke wayan, duk
Maganganun da turanci suke wayar fatuu na saurarensu a hankali ta juya ta kalli d'ayan bangaren d'akin
ta shiga yin kuka sosae ta rufe bakinta da hannunta guda don kar sautin ya fita, har ya kawo kopar
gidansu Fatun suna waya ta mik'e ta d'an ta6a kafafun Fatun tace zata je ta dawo, kai kawae ta d'aga
mata ta juya da sauri ta fice, tana fita kopar gida taga Motarshi ta nufi d'ayan side d'in ta bud'e ta shiga
suna had'a ido suka sakar ma juna Murmushi ya kamo hannunta ya rike yaja Motar da d'ayan suka tafi,
suna shiga Falon Hajiya Dining suka wuce da kanshi yay serving nasu don shima bai ci komae ba awurin
aiki cike da tsantsar kauna suka shiga ciyar da juna koda ya tashi komawa wurin aikin bayan sun gama
marairaice mashi tayi wai ya tafi da ita gidan is so boring yace ai Hajiya bazata dad'e ba zata dawo
amman ta k'iya dole yace taje ta shirya su tafi, bada jimawa sosae ba ta fito sanye cikin bak'ak'en Suit na
mata kafafunta sanye da ankle strap farare irin takalman nan masu tsini sosae masu rufe diddigen k'afa
da igiya sama da ake d'aure k'afa kanta ta yafa k'aramin bak'in gyale hannunta ruke da farar clutch bag
data hau da rigar cikin da kuma takalmanta yayinda kunnanta ke sanye da yan kunne fashion silver masu
matsiyacin kyau hannunta na hagu d'aure da agogon diamond sai d'aukar ido take ba k'aramin kyau tayi
ba, idanunshi akanta ya d'an lumshe su yana binta da wani kalan kallo ta nufo shi tana tafiya irin ta
wayayyun yan boko tana zuwa gabanshi ta tsaya tana Facing d'inshi tana wani kashe mashi ido yay d'an
Murmushi kafin ya kai hannu ya kama kunnanta yace dama tazo da shirin takura mashi kenan ko ta fad'a
jikinshi tana dariya a lokacin idanunshi suka sauka kan gashinta dake kwance kan gadon bayanta hannu
ya kai ya cire gyalen ya nad'e gashin yadda bazai fito ba kafin ya d'agota ya fara nad'a mata gyalen, Allah
sarki ashe ga inda Haisam ya iya nad'a gyale da Fatuu ke tambayarshi ya akai shi da yake namiji ya iya
lokacin daya ta6a nada mata har tace kumatunta sunyi kaman an tura biredi, kama hannunta yay a nutse
suka tafi.

Bayan Azahar Amadu ya shigo cikin gida daga Makaranta don yanzu a Poly yake Karatu don tuni ya
kammala Secondary d'inshi kuma Haisam ne ke d'aukar nauyin karatun nashi shi da Tk don shima ya
dasa HND bayan ya gama ND din da yake, d'akinshi ya bud'e don yanzu koparshi na a cikin gidan aka
maidota lokacin da Haisam yasa aka gyara masu gidan sai aka k'ara ma zauren girma, yana shiga d'akin
gwaggo ta fito daga cikin Kitchen ganin kopar d'akin nashi a bud'e ne yasa ta kwala mashi kira tace ya
dawo ne don bata ji shigowarshi ba, fitowa yay ya nufo inda take tsaye yace "Eh na dawo in ci abinci in
d'an huta don sai k'arfe hud'u nike da lecture" kai ta d'aga yace "ba yau zaki fara aikin rana bane naga
baki shirya ba kuma lokaci yayi" da yar damuwa tace "to na tafi aiki Fatuu ba lafiya, har yanzu fa jikinta
bai mata dadi wllh ina lura da ita har kuka take tayi" ajiyar zuciya ya sauke yace "amma ba kince jiya har
Allura an mata ba?'

"Eh anyi mata amman ai kasan ciwo ke shiga lokaci d'aya sauki sai a hankali ko, kuma ni wllh
damuwata kar ace ciwon da nike tunani ne" sanin ko wane ciwo take nufi yasa Amadun cewa "in sha
Allahu ba shi bane ma, amman ina ganin ki tafi aikin ni bari sai in fasa komawar kawae" tace "ayi haka
bazaka samu Matsala ba?"
"A'a ba wata matsala dama komawar k'ila wa k'ala ce don ba lalle ma lecturer d'in yazo ba haka yake sai
anata jiranshi ya kira waya yace bazai zo ba" jinjina kai tay tace "k'ilan uzuri ne ke masa yawa kasan
hidindimun rayuwa, bari to in mik'o maka Abincin sai inje in shirya don ya kamata inje tunda yau
Monday akwae tsare tsaren da zamuyi" tana k'arasa Maganar ta juya ta shige kicin,bayan ta mik'o mashi
abincin ta zuba ma Fatuu ta kaimata saida ta matsa mata ta d'an tsakura tace mata ta k'oshi bata jin
dad'in bakinta dole ta kyaleta ta hau shirin tafiya aiki bayan itama taci Abincin.

Lokacin da suka isa wurin aikin tun da suka fito daga cikin Mota ake ta faman binsu da ido dan duk
wanda ya kallesu sai ya k'ara wasu da suka kafesu da idanu ko kyaftawa basa yi, da suka shiga cikin wurin
wad'anda suka san Haisam da basu iya hakuri bayan sun gaisa dashi sai suce wai sabuwar Ma'aikaciya
suka yi ne anan ya gabatar masu da ita a matsayin wife to be d'inshi, fatan alkhairi aka shiga yi mashi
yayin da wasu ke fad'in perfect match har kiran Mutane aka rink'a yi suzo ga Fiancee d'in Zakee tanata
fara'a take gaisawa da mutane, bayan sun gama gaisuwar Office d'in su Nana ya wuce da ita wanda
babban Office ne don su hud'u ne aciki duk mata biyu matan aure ne sai su Nanar da wata sune marasa
aure, Nana zaune tana lallatsa Computer jikinta sanye da doguwar rigar atampa gyalenta akan kafad'a
taji an d'anyi knocking kopar kafin aka turota hakan yasa ta kai idanunta wurin, Fanan ce ta fara shigowa
ai suna yin ido biyu da Nana zumbur ta mik'e ta dafe k'irji tace "innalillahi, wa innahu min sulaimanu wa
inna hu bismillah..." tana rufe baki Haisam ya shigo tana ganinshi ta sauke nannauyar ajiyar zuciya don ta
fahimci tare suke tace "Haba Zakee irin wannan ai sai ka fara shigowa kai da muka sani, ni wllh nayi
zaton gamo nai yo kawae ana bud'e kopa sai inga Mutum irin wannan ta shigo tana man dariya" sauran
yan Office d'inne suka sa dariya taci gaba da cewa "kad'an ya rage ban saki fitsari ba" ita dai Fanan
Murmushi kawae take haka ma Haisam,

"Zakee bakuwa muka yi, daga ni dae sis d'inka ce ko?" tay tambayar tana kokarin zama ta nuna ma
Fanan kujera tace ta zauna, maida kallonta tay kan Haisam tace "Zakee na tambayeka baka ban amsa
ba" yace "Yea she's my sis and My wife to be also" waro ido Nana tayi da sauri ta kalli fanan d'in sauran
abokan aikinta ma suka kalleta ita dai sai faman sakin Murmushi take, kallon Haisam Nana tayi tace
"Haba mana shiyasa ba wata mace dake gabanka ashe ashe hurul ayn zaka aura, kace duk kallon
gwaggon birai kake mana Zakee" gaba d'aya suka saka dariya harda Fanan, taci gaba "Tubarkallah ma
sha Allah, gaskiya had'in nan yayi ba'a Magana, duk kun dace abokan rayuwa wllh Allah yasa Alkhairi ya
kaimu lokacin musha biki ya kuma maida mu damshin ku duk da dai ita Amaryar tamu bansan halinta
ba" Fanan na dariya tayi mata godiya tace ai duk halinsu d'aya Nanar tace to ta zauna anan ta tantance
in halinsu d'aya, dole anan Office d'in nasu ya barta aikuwa sun sha fira da Nana harda ma sauran yan
Office d'in sun matuk'ar yabawa da halinta na rashin ji da kai, sai gab da za'a tashi sannan Nana ta rakata
Office din Haisam wanda babban Office ne mai d'auke da duk wani abu da zaka samu a hadaddan Office
na babban ma'aikaci yana da dan falo wanda anan Secretary d'inshi yake, ana yin la'asar suka baro wurin
aikin saida Nana ta rakota har Mota tace tana jiranta tazo mata wuni gida tace in sha Allah Babe zai
kawo ta, saida suka biya shopping mall suka yi shopping yawanci duk kayan ciye ciye ne suka siya kafin
suka nufi gida.
Tun bayan da gwaggo ta tafi aiki take kwance tana ta tunane tunanen rayuwarta da Haisam, a yanzu ne
komai nashi ke bala'en burgeta a hankali take kai hannu tana goge kwallan dake zubo mata wanda sam
ta kasa tsaidasu ga wani irin kadaici da take ji don tasan da yanzu tana gidan Hajiya ba kaman da gwaggo
bata nan, da ta tuna yana tare da Fanan sai taji wani irin kunci a zuciyarta har wani zafi k'irjinta ke mata
da kyar ta yunkura tayi sallar la'asar ko Addu'a ta kasa yi don ta rasa wace Addu'a ma zatayi, mik'ewa tay
ta cire hijab d'in ta koma kan gado ta koma duniyar tunani tana ta juye juye tana goge kwalla, tana cikin
wannan halin Haulatu tazo gidan a bakin shagon Amadu daya bude bayan ya dawo daga Masallaci ta
tsaya ta gaidashi ta tambayeshi Fatuu na nan ko ta wuce islamiyya yace mata tana nan ciki kwance ai
bata Lafiya tun jiya jin haka yasa ta nufi cikin gidan da sauri har tana yin tuntu6e a bakin kopar shiga,
d'akin Fatuu ta nufa tana zuwa ta fad'a ciki da sallama ta nufi gadon Fatuu na jin sallamarta ta yunkura
da sauri ta tashi zaune fuska jage jage da hawaye ga gashinta ya kwance yay mata rumfa, a rud'e Haulat
ta nufeta tana Fad'in"Subhanallahi, wai ciwon har ya kai haka k'awata, ni wllh bansan baki Lafiya ba tun
d'azun naso zuwa to sai innarmu ta tafi unguwa tabar man kula da gidan, yanzu ma islamiyya zani inata
tunanin k'ilan ma kin tafi ina tambayar Kawu Amadu shine yake ce man wai baki lafiya tun jiya baku ma
samu zuwa Daurar ba ko?" kaman jira Fatuu take tana jin ta fad'i hakan ta fashe da kuka mai sautin
gaske ta matso ta kama hannuwan Haulat cikin kuka tace "Haulat na bani munyi kuskuren fahimta wllh"
a kid'ime ganin yadda Fatun take a hargitse tace "kuskuren mi?"

"Ya Handsome bai sona Haulat, bai ta6a sona ba wllh" zaro ido Haulat tayi murya na rawa tace
"a..amman ke ya akai kika san hakan ko kin mashi Magana ne ya fad'i maki hakan?" cikin kuka tace "a'a
ashe wai yana da wadda yake so kuma ma har ansa masu rana da ta gama karatu za'ai aurensu,yauwa ba
kinsan wannan Aunty Fanan d'in ba yar uwarsu mai karatu a india to itace, jiya muna dawowa muka iske
tazo baki ga yadda ta rungumeshi ba da suka had'u shima baki ga yadda yake farincikin ganinta ba, da
daddare suka zo tare wai kawo man tsarabar da muka yo, da tayi ma gwaggo bayanin kanta shine
gwaggon tace ko itace akai masu baiko tace mata eh ashe ita gwaggo ta sani sun ta6a yin Maganar da
Hajiya, Wllh Haulat baki ji yadda naji ba wani abu mai zafi kaman wuta naji a kirjina ga kaina da yayi wata
sarawa nan da nan amai ya taho man baki ga aman da nayi ba kaman yan hanjina zasu fito kuma su duk
sunyi tunanin ban lafiya ne har allura suka je suka siyo ita da Ya Handsome tai man" kasak'e Haulat tayi
tana sauraranta kamar gunki gabanta na fad'uwa don duk gani take itace sanadin shigar Fatun halin da
take ciki.....

Daidai gidansu Fatuu ya parker bike d'inshi Fanan dake bayanshi ta saukko jikinta sanye da workout
outfit da alama Gym zasu tafi tare, Cire Helmet din dake kanta tayi ta mik'a ma Haisam ya amsa ta juya
zata shiga gidan Amadu dake cikin shago yana ganinta ya fito da sauri don jiya da daddare bayan ya
shiga gida gwaggo ta bashi labarin zuwan nata harda allurar data yi ma Fatuu, da Fara'a ya gaidata ta
amsa yayi mata anzo lpy tana ta sakar mashi Murmushi, bayan ta wuce ya gaishe da Haisam kafin ya
koma shago, tana shiga ta kwad'a sallama da zazzakar muryarta jin ba'a amsa ba yasa ta k'ara yin
sallamar tana shiga cikin gidan a lokacin suka ji sallamar Haulat ta mik'e tana bari ta duba ita kuwa Fatuu
tana jin sallamar ta gane ko wacece hakan yasa ta kwanta da sauri ta juyama kopa baya ta lullu6e
fuskarta tana goge kwallar fuskar, d'aga labulen d'akin Haulat tayi ta lek'a kanta tana amsa sallamar
saidae a susuce ta k'arasa amsawar baki bud'e take kallon fanan dake mata Murmushi ganin tak'i ce
mata komae yasa tace mata "Sannu Gwaggo fa" a dabarbarce don bata yi tunanin zataji tayi hausa ba
cikin yar in ina tace "g..gwaggo ta... ina tunanin ta tafi aiki" tace "Ok Zarah fa" da hannu ta nuna mata
cikin d'akin alamar tana ciki ta nufo dakin har saida tace mata zata shiga kafin da sauri taja gefe ta shige,
gadon da Fatuu ke kwance ta nufa ta zauna a bakin gadon cike da kulawa tace "Sis Zarah" shiru bata
amsa mata ba ta d'aga kai ta kalli haulat tace "ko tana bacci?" da sauri tace "e..nima ban dad'e dana
shigo ba na ganta haka"

"Ok amman ina son nayi mata injection ne zamu fita bansan ko zamu dawo da wuri ba" haulat da tayi
mata k'uri tace "to bari in tada ta" matsawa tayi ta fara kwala mata kira ba yadda Fatun ta iya dole ta
yunkura ta tashi zaune a hankali ta d'an kalli Fanan din ta sakar mata Murmushi tace "Sannu sis Zarah
hope u'r feeling better" dan daga mata kai tayi kafin kaman an mata dole ta gaidata ta amsa had'i da
dafa kafadarta tace bari tai mata second dose d'inta kai kawae Fatun ta d'aga mata ba tare da 6ata
lokaci ba ta fiddo allurar da syringe daga cikin jacket din data rufe jikinta da ita ta had'ata tayi mata, cike
da kulawa tace "zamu je Gym da Babe do you need something?" wani abu fatun taji ya daki kirjinta
hakan yasa ta d'an kauda kanta ta girgiza mata Fanan din tace to ta koma ta kwanta Allah ya bata lafiya
daga haka ta juya har takai bakin kopa ta juyo ta kalli Haulat tace "U'r Haulat right?" da sauri haulat ta
d'aga mata kai kaman kadangaruwa Fanan d'in tace "I heard u'r Zara's best friend nayi farincikin ganinki"
tayi Maganar tana mik'a mata hannu a d'arare haulat ta kama hannun wani kalan taushi data ji har saida
ta had'iye miyau kutt, "zanzo gidanku in gaisa da mom naki in Zarah ta samu lpy" da sauri haulat tace
mata to ta d'an yake baki ita ala dole Murmushi take, janye hannun tayi tace mata ta tafi, ai tana fita
Haulat bata san lokacin da a zuciyarta ta furta "Bura ubannan Astagfurullah", juyawa tayi ta kalli Fatuu
suka yi ma juna k'uri da alama wutar kowa ta d'auke, a sanyaye Haulat ta koma ta zauna ganin kallon da
fatuu ke binta dashi idanunta sun cika da kwalla yasa tace " itace ko?" kai ta d'aga mata alamar eh, shuru
sukai kowa da abunda yake sak'awa can Haulat taji Fatuu tace "Yanzu Haulat ya za'ayi" a d'an firgice
Haulat tace "Uhyumm" matsowa Fatuu tayi ta kama hannuwanta kwalla suka fara zubo mata tace "Don
Allah ki bani shawara Haulat yanzu ya zanyi, wllh inason Ya Handsome in ban aureshi ba zuciyata zata iya
bugawa yanzu haka bakiji yadda nike ji ba kaman ana hura man wuta ga wani bugu da take man mara
dad'i" tana kai Maganar ta d'ago hannun Haulat d'in ta d'aura kan kirjinta kwalla naci gaba da zubowa,
wani wahalallan miyau Haulat ke had'ewa ta k'ura ma Fatuu idanu ba tare data ce mata komae ba,

"Haulat don Allah ki taimaka man kinga dama kin saba bani shawara in ina cikin mawuyacin hali kuma
duk inkika bani tana man aiki don Allah ki fad'i man abunda zanyi yanzu?" nannauyar ajiyar zuciya ta
sauke kafin tace "kin yarda in na baki shawara tana maki aiki? Da sauri ta d'aga mata kai alamar eh, taci
gaba "to zan baki shawara amman da farko ina mai baki hakuri akan halin da kike ciki don duk ni naja
maki dana yanke hukunci ba daidai ba batare da nayi la'akari da wani lokacin ko a Novel d'in muna yin
hasashe yazo bai zama gaskiya ba....." katseta Fatuu tayi "ki bar d'aura ma kanki laifi ai dama kince nima
ina sonshi kuma bazan gane ba sai naga ina niyyar rasashi to abunda ya faru yanzu kenan ni dai ki bani
shawarar kawae" wata ajiyar zuciyar Haulat ta kara yi kafin cike da k'arfin hali tace "Shawarar da zan
baki itace.................

*ASM2003*
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

"........KIYI HAKURI FATUU...." Fuzge hannunta tayi kaman wadda

Shock yaja tunkan haulat d'in ta rufe baki tana fitar da numafashi da sauri sauri tace"Hakuri! ya zaki ce in
yi hakuri bacin na gaya maki ina sonshi,ni dai bazan iya hakuri ba Haulat ki taimaka ki gaya man yadda
zanyi in ba haka ba na gaya maki zuciyata bugawa zatayi" nan da nan idanun Haulat suka ciko tabb da
kwalla ganin wai Fatuu ce a wannan halin ita da sam so bai gabanta bata da burin daya wuce tayi Karatu
amman lokaci guda komae ya canja so yayi mata mugun kamu, duk gani take laifinta ne hakan, kamo
hannun Fatun tayi cikin karewar murya tace "da inada shawarar da tafi wannan da na baki k'awata don
nima banson ganinki cikin irin wannan mawuyacin halin to amman ya zamuyi dole saidae fa hakurin
tunda dai kinga har ansa masu biki",

cikin muryar kuka tace "to ko in fad'i mashi ina sonshi don Allah ya Aure ni nima?" D'an girgiza kai Haulat
tayi jin wata Magana ta Fatuu wadda daga ji bata yi tunani wurin fad'inta ba,

Gyara zama Haulat tayi tace "duk da bansan ya kike ji acikin zuciyarki ba amman zan iya fahimta daga
yanayinki tabbas nasan kina cikin mawuyacin hali, amman fa kisani in kika ce zaki hakan to fa ba
k'aramin kuskure zaki yi ba kizo ki k'ara jefa kanki wani halin don karshe nasan ba samun biyan buk'ata
zaki ba, ke da kanki kince yayi farincikin zuwanta sosae kinga alamar yana sonta kenan sannan yanzu a
gabanki ta fad'i cewa an gaya mata ni aminiyarki ce wa kike tunanin ya fad'i mata hakan in ba Ya Haisam
d'in ba, kinga kenan duk wani abu game damu yana sanar mata ko daga kanki ma ai zaki gane yadda ta
sanki sosae tun kafin ta ganki a zahiri to baki tunanin in kin gaya mashi zai iya sanar da ita kuma in tasan
hakan mi kike tunanin zai faru? Duk fa yadda kike ganin kaman tana da kirki wllh tasan da wannan
Maganar za'a samu matsalane babba don ba yarda za'ai ace bata kishin Ya Haisam baima yuwuwa wllh
kuma tana iya sanar da Hajiya k'arshe in Maganar ta dawo kunnan gwaggo mi kike tunanin zai faru? kiyi
tunani Fatuu kowa na iya yi maki kallon mara hankali ma "

"Amman ai ba lalle in yaji irin wannan Maganar ba ya sanar da itan" k'ara girgiza kai Haulat tayi don ta
fahimci Fatuu bata cikin hayyacinta shiyasa bata ganin hakan a wani abu tace "to kina tunanin in kin fad'i
mashin Auren naki zaiyi, ni na tabbatar hakuri zai baki Ya nuna maki yana da wadda zai Aura kiyi tunani
bafa zai ta6a aurenku ba ku biyu, ai ko danginsu ma bazasu ta6a yarda ba kar fa ki manta yar'uwarshi ce
waye zai goyi bayan ayi mata kishiya a cikinsu bafa mai son kishiya Fatuu sai dole, duk da halin da kike
ciki kar ki bari tunaninki ya gushe kizo kuma ki abunda zaki danasani ki daure ki cije ki yak'i zuciyarki ta
fitar da Ya Haisam daga cikinta shine abunda yafi Alkhairi" bin ta da ido kawae Fatun keyi yayin da cikin
ranta take juya Maganar Haulat d'in lokaci guda ta tuno da Farha da Abubuwan data rink'a yi mata
lokacin data fara ganinta da kuma wani zuwa da suka k'ara yi yanzune ta gano dalilin da yasa hakanan ta
d'auki karan tsana ta d'aura mata ashe kishi take taya yar'uwarta, ganin tayi shiru yasa Haulat cigaba da
tausarta tana k'ara nuna mata had'arin dake tattare da abunda take tunanin yi na sanar mashi,

K'arshe dai saidae fasa zuwa islamiyyar Haulat tayi sai gab da Magrib ta bar gidan duk jikinta yay sanyi
lakwas, Tun bayan da Haulat d'in ta tafi tay zaune saman gado ta had'e kafafunta ta d'aura ha6arta
idonta akan bangon d'akin tana ta nazarin Maganganun Haulat tabbas tasan in har Gwaggo taji wannan
Maganar kashinta ya bushe k'arshe ma tana iya cewa zata maida ita ruga, tsorone ya kama wani 6angare
na zuciyarta yayinda wani 6angaren keta k'ara azalzala mata son Haisam tana a hakan aka kira sallar
Magrib amman ta kasa tashi taje tayi sai can bayan an gama ta daure ta saukko daga gadon ta fita don
yo alwala, bayan ta gama sallar jin jikinta sam bai mata dad'i ne yasa ta mik'e ta cire rigar jikinta ta
d'aura towel ta yafa gyale saman kanta ta nufi toilet don yin wanka, bayan ta fito tana cikin shiryawa ta
jiyo sallamar Fanan dam kirjinta yay irin bugun da yakeyi duk in taji sallamar tata, a bakin kopar d'akin ta
k'ara yin sallama a hankali Fatun ta amsa ta d'aga labulen ganinta tsaye yasa ta washe baki tana mata
dariya ta nufeta tana Fad'in"am so happy seeing u'r recovering Sis Zarah" tayi Maganar hannunta guda
kan shoulder d'in Fatuu, d'an guntun Murmushi ta daure tayi mata ta tambayeta wanka tayi ne Fatun ta
d'aga mata kai, kama hannunta tayi suka nufi gefen gado ta aje ledojin dake a d'ayan hannunta tace
gashi taci tasan bata jin dad'in bakinta, ita dae fatun shiru tayi hakan yasa Fanan ta bud'e leda d'aya ta
fiddo shawarma bayan ta warware ta kai bakin Fatuu tana Murmushi tace "ki daure kici kinji, ina son
inga kin samu lafiya kin koma normal condition naki cos am not happy seeing u like dis" d'an d'aga ido
Fatuu tayi ta kalleta ta jinjina mata kai alamar tabbatar mata da abunda ta fad'a, alamar ta bud'e bakin
tayi mata da nata bakin kaman bazata bud'e ba sai kuma ta d'an bude kad'an tasa mata ta gatsi yar
kad'an, ganin tana kokarin k'ara bata yasa ta kai hannu zata amsa amman sai ta girgiza mata kai tace "in
na baki bazaki ci sosae ba" ba yarda Fatuu ta iya haka ta rink'a bata tana ci har ce mata tayi ta k'oshi
amman tak'i k'yaleta har saida Fatuu ta ruk'e hannunta tana yamutsa fuska sannan ta k'yaleta ta bud'e
d'ayar ledar ta fiddo ice cream shima ta fara bata a bakin d'an kad'an tasha ta kauda kai tana Fad'in ruwa
take son sha, tambayarta tayi inda ruwan yake Fatun ta mik'e tace zata je tasha, a tare suka fito ta shiga
Falo ta d'aukko ruwan ita kawae so take Fanan d'in ta tafi amman saida ta rakota har Parlorn tayi mata
tsaye saida tasha ruwan, bayan sun fito tace mata tazo Ya Haisam na waje yaganta ya damu da ciwon da
take sosae, bata ce komae ba ta bita dama akwae gyale asaman kanta, lokacin da suka fita yana saman
bike zaune yana latsa wayarsa tunda suka tunkareshi gabanta ke bugawa da sauri da sauri suna zuwa
gabanshi cike da farinciki Fanan tace mashi ga Zarah ta fara samun sauk'i, idonshi akanta yana d'an
Murmushi yace mata ya karfin jikin tace da sauki yace Allah ya bata lpy ta amsa da Amin, ce mashi tayi
saida Safe yace Ok ta juya zata tafi Fanan tay saurin kama hannunta suka tafi tare saida ta kaita cikin
gidan tace mata saida safe ta juya, da hanzari ta nufi d'akinta tana shiga ta fad'a saman gado tasa wani
irin marayan kuka mai cin rai ganin Haisam din ya k'ara dagula mata lissafi, k'afartace ta ta6a ledar da
Fanan ta kawo mata aikuwa ta mik'e ta d'auki ledojin tai wurgi dasu k'asa har ice cream d'in data bata ya
zubo hakan bai isa ba ta rarumi filo shima ta wurgoshi k'asa, ita yanzu shikenan ta rasa Ya Handsome,
duk Rayuwar da take hango ma kanta zata yi dashi watace zata yi hakan, a zuciyarta take ta raya hakan,
sosae tasa kuka mai sauti tana cikin wannan halin gwaggo ta dawo don bata bari sai lokacin tashi ba
saboda Fatun na ranta, tana shigowa gidan d'akin Fatun ta nufa tun kafin ta k'arasa ta jiyo kukanta
aikuwa da sauri har tana tuntu6e baiwar Allah ta fad'a dakin, ganin halin da take ciki ba k'aramin tashi
hankalinta yay ba nufarta tayi tana tambayar mike damunta ta d'agota tana kallon fuskarta da tayi jage
jage da hawaye nan da nan itama idonta ya ciko da kwalla don ganin halin da take ciki yasa ta tabbatar
ma kanta da zargin da take yi game da ciwon Fatun, hannunta ta kamo ta d'aura kan kirjinta tana Fad'in
"Gwaggo k'irjina zafi, zai 6are ki taimaka man" nan da nan kwallan suka fara zubo mata ta hau yi mata
Addu'oi tana tofa mata, A hankali ta fara jin sauk'in k'irjin don a halin da take ciki ganin Mutum a kusa da
ita wani sauk'i ne, lamo tayi a jikin gwaggo tana maida numfashi gwaggon na cigaba da tofa mata
Addu'oin tana shafa kanta, ganin ta natsu tay shiru yasa ta d'an leka fuskarta cikin harshen fulatanci ta
tambayeta da sauk'i ta daga mata kai alamar eh sannu tayi mata taci gaba da shafa kanta tana adduoin
can ta d'ago kanta tace bari in zubo maki Abinci da sauri ta girgiza mata kai alamar a'a tace "to ayi ciwo
ba cin abinci Fatuu ki daure ki d'an ci ko ba yawa" Murya a disashe tace "naci shawarma" da d'an
mamaki ta tambayeta inda ta samu shawarmar ta d'aga yatsa ta nuna mata ledojin dake yashe a k'asa
tace "Aunty Fanan ta kawo" jinjina kai tayi tace "to amman kin ci d'in da gaske?"

"Eh itama ta bani a baki" d'an Murmushi gwaggon tayi tace "Allah sarki, wllh ban ta6a ganin mace
irinta ba Allah ya bata komae amman sam bata da girman kai bata d'auki duniya da zafi ba gashi nan tun
yanzu ta fara cin ribar hakan Allah ya bata Abokin rayuwa Nagari, gaba d'aya naji masu dad'i Allah
ubangiji ya albarkace su da zuria ta gari kaman yadda suke" k'asa k'asa Fatun tace Amin idanunta sun
ciko da kwalla amman bata bari sun zubo ba, mik'ewa gwaggo tayi ta d'aukko ledar ta dawo ta zauna
tace "to tashi ki d'an k'ara" tayi Maganar tana fiddo sauran abubuwan dake ciki wanda duk snacks ne da
sauri ta girgiza mata kai don ita ko k'amshinsu ma bata son ji ganin tak'i ci ne yasa gwaggo ta fita taje ta
d'ebo mata Abinci ta tasata gaba saida taci ba wani mai yawa ba, bayan ta gama tace mata tayi sallar
isha tunda an fara kira sai ta kwanta inta yi bacci zata k'ara samun sauki ta amsa mata da to, tana gama
sallar akan abun sallar ta kwanta tayi lamo tana ta tunane tunane itama gwaggo sallar taje tayi tana son
tayi wanka amman kuma tana son taje wani wuri hakan yasa ta bari in ta dawo tayi don kar dare yayi
sosae saida ta leka d'akin Fatun ta ganta a kwance duk a tunaninta bacci take ta juya ta nufi kopar gida
lokacin Amadu ya dawo daga Masallaci yana kokarin bud'e shago ganin gwaggon ya nufeta yace "wani
wuri zaki ne?" da yar damuwa tace "eh zanje wurin Malam tanimu ne inason gaya mashi game da halin
da Fatuu take ciki ko zai yi mata Addu'a" yace "jikin har yanzu kenan, d'azun na dubata sau biyu duk a
kwance nike isketa inna tambayeta ya jikin sai tace man da sauki"

"Eh ai kasan irin wannan ciwon dama haka yake yanzu da sauki anjima ba sauki, yanzu fa dana dawo
baka ga halin dana isketa ba da alama sun rik'e mata k'irji ne tana ta cewa zafi take ji kaman zai 6are"
girgiza kai yay yace "Allah ubangiji ya bata Lafiya mai d'orewa, muje to in raka ki"
Tace "A barta ita kadae kuwa, ko ka shiga gidan in je in dawo sai ka bud'e shagon" amsa mata yay da to
ya wuce itama ta tafi, bata k'arasa gidan bama ta had'e dashi a hanya ya dawo daga Masallaci suka tsaya
suka gaisa kafin tayi mashi bayanin halin da Fatun take ciki,sosae ya jajanta mata yace zuwa gobe da safe
a zo a amsar mata ruwan Addu'a yace da za'a samu zam zam ma da yafi tace bari taje zata sa Amadu
yaje ya siyo sai a aiko dashi ya amsa da to ta tambayi abunda za'a bada na sadaqa yace ba sai ta bada
wani abu Allah ya bata Lafiya, tayi mashi godiya sosae da Addu'a kafin ta tafi. Tana komawa gidan ta iske
Amadun a d'akin Fatuu yana zaune k'asa kusa da ita Addua ya gama yi mata yana d'an yi mata fira sama
sama take tanka mashi, sak'on yaje ya siyo zam zam d'in ta bashi tace in ya dawo ya wuce ya kaima
Malam Tanimun, wannan shi ake kira da cuta daban Magani daban don ma dai Maganin ta wani
bangaren zai taimaka don ba abunda yafi karfin Addu'a.

Bayan sun isa gida saida ya raka Fanan har d'akin Hajiya lokacin tana zaune kan Sallaya ta gama sallar
Magrib tana jiran isha suna shigowa cike da tsokana tace "Luv birds an dawo" nufarta Fanan tayi tana
dariya ta zauna kusa da ita ta kwantar da kanta kan kafad'arta, gaisawa yay da Hajiya yace zaije yay
wanka Hajiya tace ya bari yay sallar isha sai yayi yanzu ana iya kiran salla yana wanka ya amsa mata da
Ok ya nufi bakin gado ya zauna,

"Wai nikam ya jikin Fateema ne?" Hajiya ta tambaya Fanan tace "tana samun sauk'i sosae sunje yanzu"
jinjina kai Hajiya tayi kafin tace "Allah ya k'ara sauki" amsawa sukae da Amin harda Haisam d'in, bada
jimawa ba kuma aka fara kiran isha ya mik'e yace zaije Masallaci Fanan ta d'aga hannu cike da kauna
tana mashi bye bye har ya kama kopa zai bud'e tace "Babe kai man Addu'a in baka twins nine Months
after we get married" hannu Hajiya ta kai zata bugi bakinta ta fad'a jikinta tana dariya shima dariyar yay
ya fice, bayan angama sallar part d'inshi ya nufa yayi wanka ya shirya kafin ya dawo part d'in Hajiyar
lokacin itama Fanan din tayi wanka ta shirya cikin kayan bacci riga da wando milk masu santsi kanta tasa
hula itama milk ta saki brown gashinta, atare gaba d'ayansu suka nufi Dining don cin dinner, kaman
sauran lokutta suka rink'a ciyar da junansu har Hajiya nama Haisam tsiyar yadda yake cin abinci yanzu
don yaga Fanan ita daya raina sai taita fama dashi yak'i ci sosae sai ya gadama, dariya Fanan d'in tayi
tace baison 6acin ranta ne hajiya tace sai nata yake so ko, bayan sun gama falon suka koma suna kallo
Fanan dai na manne dashi lokacin da Hajiya ta mik'e tace ita dae bacci take ji shima tashi yay ya mik'ar
da Fanan d'in ya rakata har cikin dakin, saida yaga ta kwanta ya manna mata kiss a gefen fuskarta yay
masu saida Safe ya nufi hanyar fita idon Fanan akanshi yana kama handle d'in kopar ta d'aga murya tace
"I luv u nd I can't do without u Babe" juyowa yay ya sakar mata k'ayataccen murmushi kafin ya fice
Hajiya dake zaune gefen gadon ta ta6e baki tana girgiza kai Fanan taja duvet ta rufe fuskarta tana dariya.

Allah sarki gwaggo tsakar dare har tashi tayi tayi salla tayi ma Fatuu Addu'ar Allah ya yaye mata lalurar
da take fama da ita sosae tayi mata Addu'oi,Washe gari da Asuba ta tada Fatun tayi salla bayan ta gama
ta koma ta kwanta itama gwaggon komawa tayi saida gari ya waye ta tashi don ta had'a masu breakfast
lokacin da Amadun yazo amsar nashi tace mashi in ya gama yaje wurin Malam tanimu ya amso mata
sak'on yace to, a d'akin nata ta kai kayan breakfast d'in ta tashi Fatuu tace ta lalla6a taje ta wanko baki,
bayan ta dawo ta had'a mata tea mai kauri tace ta daure ta sha zata ji dadin jikinta, ba laifi taci abun
breakfast d'in sosae don ta danji dad'in jikinta ba kaman jiya ba, suna cikin yin karin kumallon Amadu ya
kawo ruwan addu'ar ya fad'i mata yace a bata tasha safe da dare sai kuma a shafe mata fuskarta da kirjin
nata daya rik'e, sosae gwaggo taji dad'i bayan ya tafi ta bud'e marfin gorar ta mik'a ma Fatuu tace "kiyi
bismilla kisha" zuru tayi tana yi mata kallon rashin Fahimtar abunda take batan ganin hakan yasa tace
"ruwan Addu'a ne ganin halin da kike ciki jiya da daddare naje na fad'a mashi shine yace zai maki Addu'a
yau da safe aje a amsa" kasa Magana tayi tana dai ta kallonta ita kuma gwaggon ganin kallon da take
matan yasa ta yin tunanin suna iya hanata sha hakan yasa ta matsa tana niyyar kwafa mata robar a baki
Fatun tasa hannu ta amsa ta kai bakinta bayan tasha ta mik'a mata ta zuba a hannunta ta shafa mata
kaman yadda aka ce,

"Yauwa in sha Allahu zaki ji kinsamu sauki ki koma ki kwanta" gwaggo ta fad'a da d'an Murmushi don
taji dadin yadda Fatuu tasha ruwan Addu'ar, mik'ewa tayi ta hau gadon tay lamo ta shiga duniyar tunani
zuciyarta na raya mata Ya Handsome na can suna shan soyayyarsu da Fanan ita tana nan tana ta fama,
runtse idonta tayi yar siririyar kwalla ta zubo mata tasa hannu ta goge batare data bud'e idon ba. Misalin
karfe sha biyu saura gwaggo na cikin Kitchen Fatuu ta fito ta tsaya a bakin Kitchen d'in tana ganinta ta
nufota tace "Sannu kin tashi" kai ta d'aga mata tace "to ya jikin?"

"Da sauki sosae" ta bata amsa a sanyaye,

"Alhamdulillah, Allah ya k'aro sauki, halan kin gaji da kwanciyar?" kai ta sake d'aga mata tace "to ki shiga
Falo ki zauna ko ki kunna kallo",

"Ki kawo in yi wanke wanke in baki yi ba" ta fad'a idonta akan gwaggon duk bata jin dad'in yadda ta
saka ta damuwa,

"Har kin samu sauk'in da zaki iya yin aiki kije ki zauna zanyi, so nike in gama amfani da abubuwan da
suka 6aci sai in had'a in wanke gaba d'aya" tace "ki kawo zan iya" gwaggon tace to don dama tafi son
taga ta dawo kamar da, tana cikin yin wanke wanken Fanan tayi sallama ta shigo jikinta sanye da
Maroon skirt babba mai tattara a sama sai rigar brown da ratsin maroon kanta ta yafa Maroon d'in veil
kafafunta sanye da flat shoe brown ta matukar yin kyau, suna had'a ido da Fatuu data d'aga kai ta kalli
kopan shigowan tana ganinta ta saki Murmushi ta nufeta tana Fad'in "am so Happy sis Zarah kinsamu lpy
ko" kai ta d'aga mata kafin a hankali tace mata ina wuni ta amsa still da fara'a, gwaggo ce ta fito daga
cikin Kitchen tana fadin"Muryar wa nike ji kaman y'ata Fan...fanna ko haka sunan yake ni shige man yake
wllh" tana dariya ta gyara mata sunan tace yauwa bazata kara mantawa ba,

"Naga Sis Zarah ta samu lpy nayi farinciki" da jin dad'in Maganarta gwaggo tace "aikuwa Alhamdulillah
sauki ya fara samuwa, ki shigo falo" ta kai maganar tana nuna mata kopar falon,

"No let me help her" tayi Maganar tana tattare hannun rigarta alamar zata taya Fatuu wanke wanken
da sauri gwaggo tace "Don Allah ki kyaleta ta idasa ita tace zata yi bama ni na bata tayi ba" tace "ba wani
abu zamu gama tare, inata so mu had'u da ita muyi fira sosae and nazo kuma bata lafiya" d'an girgiza kai
gwaggo tayi aranta tana Fad'in wace irin yarinyace wannan,ganin tana niyyar duk'awa yasa da sauri tace
bari in kawo maki kujera to tunda kin matsa sai kinyi, bayan ta kawo mata kujerar tace ta curo agogon
hannunta kar ruwa ya shiga ya lalace ta cire ta mik'a mata harda wayarta, bayan ta zauna d'auraya ta
shiga yi mata tana kifewa a cikin kwando tana d'an yi mata firar india akai akai take d'agowa ta kalleta
da Murmushi a fuskarta itama fatun sai ta d'an yi mata a haka har suka gama Fatuu tace mata ta shiga
falo tace to, bayan ta kai kayan kicin ta dawo ta wanke wurin itama ta nufi Parlon tana niyyar zama kan
kujera Fanan dake zaune kan 3 seater tace tazo ta zauna kusa da ita batare data ce komae ba taje ta
zauna, gallery d'in wayarta ta shiga ta d'an kwanto gefen Fatun tana nuna mata videos d'insu ita da
friends dinta da suke karatu tare acan india, tun dai Fatun na dar dar harta saki jiki abunda ya bata
dariya ta d'anyi wani kuma tayi Murmushi suna haka gwaggo ta shigo zama tayi kan 1 seater fuskarta da
Murmushi don taji dad'in ganin yadda Fatuu ta d'an saki jiki, d'agowa Fanan tayi tace ma gwaggon
"sannu granny kinata aiki ko inzo in tayaki?" d'an bud'a ido tay tace "ai ba wani aiki bane Abinci ne nike
yi kuma ban tunanin ma kin ta6a cin abunda nike dafawa balle har ki iya tayani" da d'an mamaki kan
fuskarta ta tambayeta miye take dafawa tace mata dambu, a hak'ik'ance tace "I know dambi mana...."
tun kan ta k'arasa gwaggo tasa dariya fatuu ma saida ta d'anyi,

"To ai y'ata Fanan tun wurin fad'in sunan nashi ma kinga ya nuna baki sanshi ba" da sauri tace "Serious
granny na ta6a cin dambin ba shine kaman cous cous ba?" kai gwaggo ta daga"tabbas shine amman ba
dambi sunanshi ba dambu ake cewa Fanan d'in tace yauwa shi to take nufi,

"Ai da har ina tunanin in sama maki wani abun kici bansan kin iya cin shi ba" girgiza mata kai tayi tace
"zanci sosae na dad'e banci shi ba Mom na mana" mik'ewa gwaggo tayi tana Fad'in to bari taje tayi sauri
ta gama ko don d'iyarta taci, Fanan d'in na Dariya jin Maganar gwaggon, kiran sallar Azahar aka fara suka
tashi ita da Fatun suka je d'akinta su kai salla bayan sun gama suka dawo falon lokacin gwaggo ta kawo
masu dambun na Masara ne yaji zogale sai kamshi ke tashi, tare ta zubo masu a babban plate don tasan
ko ta zubo masu kowa da nashi karshe Fanan din sai tace a had'a masu, sosae taji dad'in dambun duk
yadda Fatuu taso k'in ci da yawa ta hanata tace in bata cin abinci sosae koda ta samu lafiya karfin jikinta
bazai dawo ba, ba yadda ta iya haka ta rink'a turawa ba don tana wani jin dadinshi ba, koda suka cinye
gwaggo tace a k'aro masu cewa Fanan tayi eh sam bata nuna bak'unta kai kace yar 'uwarsu ce ma, k'in ci
Fatuu tayi bayan an k'aro tace ita ta koshi dole ta kyaleta taci gaba da ci ita kadae, tana cikin ci Hajiya
tayi sallama gwaggo dake zaune itama tana cin dambun ta mik'e da sauri ta fita tana Fad'in "Maraba da
Hajiya" ta amsa mata da yauwa tana nufota Saude na bayanta itama gwaggo tayi mata sannu da zuwa ta
gaisheta da fara'a ta amsa mata tace su shigo, suna shiga idon Hajiya ya sauka kan Fanan da ta tura
dambu a baki tana mata dariya Hajiya ta ruk'e ha6a tace "Oh su shanshani kafan yawo ana nan ana
kwalama ashe, to Allah ya jikanka dambu ki dai bi a hankali in ba haka ba ya shaqe ki" tayi Maganar tana
kokarin zama kan kujera gwaggo dake Dariya tace "Mutum da gidansu ai ba kwalama take ba" Fanan d'in
ta gyad'a kai alamar atoh,nuna ma Saude kujera gwaggo tayi tace ta zauna tayi tsaye ta nufi wurin ta
zauna, gaisawa suka shiga yi suka yi mata ya mai jiki tace da sauki kallon fatuu dake zaune kan carpet
gefen Fanan tayi shiru tace "Oh sannu Fateema kinji, Allah ubangiji ya yaye maki wannan lalura baki
d'aya ki huta wannan zuwa Dam bai yi dad'i ba sam" gwaggo dake d'an Murmushi tace "to ya za'ai haka
Allah ya kaddara" hajiya tace "hakane amman dae da sauki sosae ko?"
"Eh jiyane dana dawo dae na iske abun yayi tsanani har tana kirjinta zai 6are to sai nayi mata Addu'oi
na kuma je wurin Malam tanimu na fad'a mashi halin da ake ciki shine ya bukaci ruwan zam zam yayi
mata Addu'oi yau da safe aka amso tasha na shafa mata kaman yadda yace Allah cikin ikonsa ta samu
sauki sosae wllh" gaba d'ayansu duk suka girgiza kai alamar tausayawa ita dae Fatuu zuru tayi tana binsu
da ido don ta fahimci ciwon da suke tunanin yana damunta, mik'ewa gwaggo tayi tace bari a zubo masu
dambu Hajiya ta tambayeta na miye tace na Masara ne tace to a zubo masu kad'an don ta kwana biyu
bata ci shiba, wuri daban daban ta zubo masu ita da Saude Hajiya na ganin haka tace maimakon ta zubo
masu wuri guda sai sun cinye masu abinci dama ga wata acicin nan sai turawa take Fanan na jin haka
tasa dariya suma duk dariyar suke, bayan sun gama Hajiya ta tambayi gwaggo bazata aiki bane yau tace
tana son zuwa amman tana tunanin yanayin jikin Fatuu don jiya yadda ta dawo ta sameta hankalinta ba
k'aramin tashi yay ba, Fanan na jin haka tace taje aikinta zasu zauna tare Hajiya tace "to ku taho can gida
mana in ta dawo ba sai ta dawo ba" girgiza kai Fanan tayi tace "ban komawa fushi nake da Babe" Dariya
Hajiya tayi tace "Saboda yau yak'i zuwa dake aikin kika yi fushi dashi" kai ta d'aga alamar eh, tace "hum
dama dae zaki iya duk cika baki ne" gwaggo dake dariya tace "ai y'ata kishinki yake shiyasa bai je dake
ba" bayan sun gama gaba d'aya suka nufi gidan Hajiya...........

*ASM Bk2004*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

Koda suka je zama sukayi a parlor suna kallo suna fira sai dae Fatuu bata wani saki jiki sosae ba sama
sama take Magana ganin yanayinta yasa Hajiya tace taje d'akinta ta kwanta Fanan ta kama hannunta
suka tafi, kwantawa tayi saman gadon Hajiyar Fanan kuma ta wuce Toilet don tayi wanka lokacin data
fito har bacci ya kwashe Fatuu itama kayan shan iska tasa ta kwanta gefenta tana son ta kira Haisam don
taga missed call d'inshi lokacin data fito daga toilet amman sai kawae ta daure ta kyaleshi wai don yasan
tayi fushi, tana ta latsa wayarta har bacci itama ya kwasheta, sai da akayi la'asar Hajiya ta shigo yin salla
ta tashesu suma suyi sallar, da daddare bayan isha suna zaune a falo Fatuu duk ta k'agara ta koma gida
don bata son Haisam ya dawo tana gidan, har cewa tayi zata tafi Hajiya tace ta bari in Dijen ta dawo ai
zata kira ita kuma Fanan cewa tayi ta kwana anan kawae mana ita dae murmushin yak'e kawae tayi,
suna zaunen Haisam ya shigo da sallama duk suka d'aga kai suka kalleshi Hajiya ta amsa mashi yayin da
k'irjin Fatuu yay mata wani irin bugu tana yin arba da fuskarshi sai dae kuma ta kasa daina kallonshi wani
irin fresh taga yayi mata, nufosu yay Fanan ta kauda kanta yana ganin haka yaja ya tsaya Hajiya dake
kallonsu na masu Murmushi don tasan yadda sukai da Fanan d'in da safe, juyawa yay zai koma da sauri
Hajiya tace "ka rufa man asiri ban shirya yin jinya ba daga kawo man ziyara" ita kuwa Fanan d'in mik'ewa
tayi da sauri sauri gudu gudu ta nufeshi tana zuwa ta fad'a bayanshi ta k'ank'ameshi ta yadda bazai iya
cigaba da tafiya ba, ruk'e hannuwanta yay ya juyo yana kallonta ta zo6ara baki ya kai hannu ya d'an ja
lips d'inta ta saki yar k'ara sai lokacin yay Murmushi ya kama hannunta suka nufo cikin falon, wani irin
abu Fatuu taji ya tokare mata k'irji nan da nan zuciyarta ta karye taji kwalla na niyyar zubo mata da sauri
ta juyar da kanta ta kalli tv, gefen Fatuu inda ta taso ya kaita ta zauna shi kuma ya zauna saman hannun
Sofa har lokacin suna ruk'e da hannun juna kallon Hajiya yay ya gaidata ta amsa tana Murmushi a hankali
ya juya ya kalli Fatuu daidai itama ta juyo saida ta had'iye wani abu mai d'aci kafin da k'yar ta iya
gaidashi ya amsa yay mata ya jiki tace da sauki, maida kallon yay kan Fanan yace ta gama fushin Hajiya
tace "to ai ni bansan wane ma irin fushi ne wannan ba" turo baki Fanan tay ta kwantar da kanta gefen
jikinshi tace ita dama ba fushi tayi dashi ba ai, Hajiya tace to kanta dai ta k'aryata ba ita ba duk suka yi
dariya, janyeta yay ya mik'e yace zaije yay wanka baiwar Allah Fatuu daurewa kawae take ita kadae
tasan abunda take ji yanzu ta tabbatar ma kanta ba k'aramin son juna suke ba, kasa jure zaman tayi ta
mik'e tace zata je gida tasan yanzu gwaggo ta dawo Hajiya tace ta lura dae gidan take son tafiya to ta
bari taci abinci Fanan ma tace ta bari in sunci dinner sai su rakata ita da Babe Hajiya tace lokacin ma
tasan dijen ta dawo, kasa yi ma su musu tay ta koma ta zauna bada jimawa sosae ba Haisam ya shigo ya
shirya cikin jallabiya dark ash mai gajeren hannu yana shigowa Fanan ta mik'e ta kama hannun Fatuu
tace mashi suje table Zarah nason tafiya gida jinjina kai yay suka nufi dining area da tun bayan gama
sallar isha Saude ta shirya komae, kaman yadda suka saba haka suke cin abincin baiwar Allah Fatuu
daurewa kawae take idonta akan abincin gabanta da Fanan ta zuba mata ji take kaman ta rushe da kuka,
bata wani ci da yawa ba sai faman jujjuya cokali take can ta mik'e tace ta k'oshi fanan tace ta daure ta
k'ara bata ci sosae ba tace amai take ji ne hakan yasa Hajiya tace ta k'yaleta fanan d'in tace to ta jirasu a
falo su gama ta d'aga mata kai kawae, a tare suka rakota suna ta hirarsu irin ta masoya har wani d'an
fad'a mashi a jiki take, lokacin da suka k'araso kopar gidan su biyu suka shiga shi ya tsaya a waje zai
jirata, gwaggo bata dad'e da shiga gidan ba suka shigo fanan na dariya tace ta maido yar ajiya tak'i ta
kwanan mata itama gwaggon dariya take tay mata godiya sosae ta tafi, kallon Fatuu dake zaune kan
kujera tayi tace mata ya jikin ta amsa mata da sauki ta mik'e zata wuce d'akinta gwaggon tace ta tsaya ta
zubo mata Abinci sai taje ta kwanta tace taci acan daga haka ta wuce d'akinta tana shiga ta nufi gado ta
fada samanshi tayi rubda ciki sai lokacin kukan da take ta rik'ewa ya samu zubowa,wani irin son Ya
Handsome take ji acikin ranta bata da buri yanzu sai na auranshi to amman ta yaya shi da baisan ma
tana yi ba gashi yanzu tabbas ta gasgata Maganar Haulat na ba k'aramin son juna suke ba shida Fanan,
sak'e sak'e taci gaba da yi tana neman mafita har gwaggo ta lek'o ganinta haka yasa tayi tunanin tayi
bacci ne shiga tayi cikin d'akin tay mata Addu'oi duk fatun na jinta bayan ta gama ta gyara mata
kwanciya lokacin da zata fita daga d'akin ta kashe mata hasken wuta kafin ta fita.
Tun daga wannan ranar Fatuu bata k'ara yadda wani abu ya kaita gidan Hajiya ba don ta fahimci in taga
Haisam k'ara shiga mawuyacin hali take, k'iri k'iri ta hakura da ganinshin abunda bata ta6a tunani ba a
rayuwarta wato guje ma ganin Ya Handsome d'inta mutumin da ko tafiya yay a k'agare take daya dawo
don duk sai tajita ba daidai ba in bai nan, duk abunnan ba wanda ya fahimci halin da take ciki su a
tunaninsu lalurar da suke zato ke damunta ita gwaggo bata ma san cewa Fatun bata san da Maganar
baikon dake tsakaninsu ba sanin irin shak'uwar dake tsakaninta dasu duka bama kamar Haisam, itama
kuma Fanan bata san Fatun bata sani ba, Ranar Asabar ya kama kwanan Fanan shidda da zuwa Fatuu na
cikin d'akinta don yanzu ta d'aura aure da zaman d'aki ba kaman in gwaggo bata nan in tana nan ne wani
lokacin inta matsa mata take zuwa Parlor ta kunna tv saidae sunan tana yin kallonne amman hankalinta
na wani wuri tunane tunane sun zamar mata jiki duk tazama wata so silent Magana saita kama take yi,
shigowa gwaggo tayi da sallama ta d'aga kai ta kalleta kafin a hankali ta amsa mata ta nufi gefen gadon
ta zauna fatun ta yunk'ura ta mik'e zaune,

"Sannu ya karfin jikin?" amsa mata tayi da sauki, tace "Yanzu ya kike jin jikinne ina yafi damunki?"
shiru ta d'anyi idonta akanta kafin a hankali tace "ba ko ina" itama gwaggon shiru tay kaman mai
nazarinta hakan yasa Fatun duk'ar da kanta tana wasa da yatsunta,

"In ba abunda ke damunki yanzu miyasa kika k'i sakin jikin ki kaman da?" da yar damuwa tay Maganar,
damm gabanta ya d'an fad'i ta d'ago idanunta har sun canja kala a sanyaye tace "kawae banjin dad'in
jikinne kaman ba nawa ba" jinjina kai gwaggon tayi tace "a hankali zaki warware amman wannan
k'umshewar da kike cikin d'aki hada shi ke k'ara maki rashin dad'in jikin, ki daure ki rink'a sakin jikin kina
fitowa" kai ta d'aga mata tace Allah ya bata Lafiya daga haka ta mik'e zata fita sai kuma ta tsaya ta juyo
tace "ko gidan Hajiya ki daure ki rink'a zuwa kinga yarinyar nan Fanan kullum sai tazo dubaki duk ta
damu da halin da kike ciki in taga kinje zata ji dad'i, da zaki iya ma kiyi d'an wani abu ki kai mata nasan
zata ji dad'i sosae taga kema kin damu da ita kaman yadda ta damu dake" wani irin fad'uwa gabanta yay
hakanan ita bata tsani Fanan ba amman data ji muryarta ko anyi Maganarta sai gabanta ya fad'i ganin
gwaggon ta kafeta da ido ne yasa tace to mi zata yi mata, tace "yauwa to ko wainar fulawa ce akwae
komae na yi kije waje wurin Amadu sai ki amso kwai nasan ba k'aramin dad'inta zata ji ba tunda ita ba
ruwanta komae ci take" ta k'arasa Maganar tana nufar kopa, zaune tayi tay shiru bayan gwaggon ta fita,
ba wai wainar ke bata son yi mata ba kawae ita gidan Hajiyar ne bata son zuwa don karshenta zata tado
ma kanta wata matsalar ne can dai ta saukko daga kan gadon ta fita, ba tare da 6ata lokaci ba gwaggo ta
taimaka mata wurin had'a k'ullun wainar ta yi shi mai d'an yawa yadda suma zasu ci, suya Fatuu ta fara
cikin Kitchen gwaggo kuma ta yanka mata cabbage da sauran kayan ci, bayan ta soya mai d'an yawa
gwaggo tace tay sauri ta shirya ta kaimata ita bari taci gaba da yin suyar, wanka taje tayo har ta wuce
kitchen gwaggo ta kirata tazo bakin kitchen d'in ta tsaya tace "nace ko ki saka kayan data kawo maki
dinnan suna nan na saka maki acikin kayanki" kai kawae ta d'aga mata ta wuce, kayan na nan yadda suke
cikin leda tunda ta kawo su Fatun bata ta6a su ba, d'aukar ledar tayi ta koma bakin gado ta zazzagesu ta
fara d'agasu tana dubawa, sari kala ukku ne riga da wando da mayafinsu rigar iya gwuiwa ce sai kuma
doguwar riga har k'asa itama kuma tana da wando da mayafi kayan sun matukar had'uwa daka kallesu
zaka gane ainihin na india ne sun mata kyau saidae yanayin da take ciki yasa ta kasa yin murnar kayan
dama kwanaki can baya Haisam ya ta6a kawo mata irinsu kala biyu da yaje Lagos yace Fanan tace a bata
sai yanzu ta fahimci dalilin dayasa yake yawan zuwa Lagos wani lokacin harda wurin Fanan yake zuwa in
tazo,wasu sky blue ta d'auka zata sa ta mayar da sauran cikin ledar,bayan ta gama shiryawa tsaye tay
gaban mirror tana kallon kanta kayan sunyi mata kyau sosae sai salki stones din jiki ke saki ba don
yanayin da kayan suka risketa aciki ba da ba abunda zai hana har rawar india tayi,jiki a sanyaye ta yafa
mayafin kayan ta nufi kicin bayan ta sanya takalma masu d'an tudu don bata saka flat shoes shiyasa ma
bata dasu sai yan na sawa a tsakar gida, lokacin data je kicin d'in gwaggo har ta had'a wadda zata
kaimata tana ganinta ta washe bakin jin dad'in ganin yan matanta yau ta fito tsaf da ita duk da ba wata
kwalliya tayi ba iya mai kawai ta shafa sai kayan data sa sosae ta shiga yabon kayan tana sunyi mata
kyau sosae ita dae shiru tay tana bin ta da ido, d'aukko mata kwanon dinner set mai d'an girma dake a
rufe gefe tay tace gashi nan ta kaimata.

Kasancewar Weekend ne gaba d'ayansu suna zaune a falo duk kaya ba masu nauyi bane a jikinsu Haisam
da Fanan na kan 3 seater ya jingina a k'arshen kujerar Fanan kuma na kwance ta d'aura kanta kan
kafafunshi Hajiya na akan 2 seater gaba d'aya idanunsu na akan tv suna kallon wani Indian film a
Bollywood Fanan d'ince ke fassara masu abunda ake cewa don ta iya indiyanci sosae Musamman akwae
lokacin da suka ware suna koyonshi acan, da yar sallama ta shigo Falon saidai ba wanda ya jita hakan
yasa ta tsaya idonta akan Haisam wani abu take ji na bin jikinta ga zuciyarta dake bugawa da sauri da
sauri ta kasa d'aga kafarta ta idasa shiga ciki kaman ji yay idanu na yawo a kansa hakan yasa ya d'an juyo
suka had'a ido da ita shima kallon ya bita dashi from head to toe kafin ya tsaida idon cikin nata suna
kallon juna can taji cikin cool voice dinshi yace "Zaraah ki shigo mana" Maganar da yay ce tasa duk suka
juya suka kalli entrance d'in koda Fanan tayi arba da Fatuu tsaye da sauri ta yunk'ura ta mik'e ta nufeta
ganin haka yasa Fatun nufo cikin falon suka had'e gaba d'aya ita da kwanon da take ruk'e dashi ta
had'asu ta rungume tana Fad'in "am so so Happy Sis Zarah kin samu Lafiya sosae" d'agowa tay ta amshi
abunda ke hannunta ta rungume a hannunta guda d'ayan kuma ta kama hannunta suka nufi ciki, a Sofa
d'in da suke zaune ta zaunar da ita can d'ayan gefen ita kuma ta zauna tsakiya ta aje kwanon k'asa
gabanta,

"Hajiya Ina kwana" ta fad'a a sanyaye hajiya dake kallonsu tana Murmushi tace "Lafiya lou Fateema
kin yi kyau sosae, ya k'arfin jikin?" da sauki ta amsa mata kafin ta juya ta gaida Haisam da shima kallonsu
yake ya amsa fuska a sake yay mata ya jiki shima tace mashi da sauk'i,maido idon tay kan Fanan da ta
d'aura hannunta guda kan k'afafunta tana ta sakar mata Murmushi, itama gaidata tayi ta amsa tace
mata tayi kyau sosae godiya Fatun tayi mata ta kayan tace basai tayi wannan ba takai hannu ta zame
gyalen kanta ganin yadda gashin yake ba gyara tace mata tasan saboda bata lafiya ne bata gyara ba
yanzu tunda ta samu sauk'i yakamata a gyara zatafi jin dad'inshi ita dai jinjina mata kai kawae take,

"To ke an kawo man abu kin tasa a gaba ki mik'o man in ga mi na samu haka" Hajiya dake kallon fanan
ta fad'a aikuwa a hak'ik'ance tace "ba naki ne ba nawa ne" yar dariya hajiya tayi tace "hak'ilo, yanzu
yaushe kika ji ance naki ne" kallon Fatuu tayi tace ita ta kawo mawa ko kallon hajiya Fatuu tay data
kafeta da ido kaman zatayi murmushi ta sunkuyar da kanta ta d'aga ma Fanan d'in, yar k'ara tasa tace to
gashi nan Sis Zarah tace nata ne, ruk'e ha6a Hajiya tayi tace "Wato dae Fateema an rabamu ko, ada Ya
Handsome ya shiga tsakaninmu yanzu kuma ga wannan acicin ai shikenan zasu barni dake ne" yammm
taji jikinta yayi jin Maganar Hajiya ta zasu barta da ita dama k'arfin hali kawae take zama a gurin, d'aukar
kwanon Fanan tayi ta bud'e kamshin wainar ya daki hancinta har saida ta d'an lumshe ido sai dai bata
gane minene ba hakan yasa ta juya ta tambayi Fatuu sunanta tace mata wainar fulawa,

"Wasu kuma suna ce mata kalalla6a wasu suce waina gira ko alallagira wasu ma yar cana suke cewa"
suka ji Hajiya ta fad'a, bud'a ido Fanan tayi jin wasu sunaye ta fara k'okarin maimaitawa tace
"K...kal...kallalla6iya..." tunkan ta rufe baki suka sa dariya gaba d'ayansu ita dae Fatuu d'an Murmushi
kawai tay Hajiya tace "Da alama dai za'a maimaita na taliyan hausa" da sauri Fatuu ta juya ta kalli Haisam
suka had'a ido ya saki Murmushin gefe tunowa da ranar data kawo mashi taliyan hausa mai daddawa
sanin Murmushin kona miye yasa itama tayi kafin ta juyar da kan,

"Idan baki ci ki mik'o man nan k'amshinta duk ya cika man hanci" hajiya ta Fad'a idonta kan Fanan, da
sauri ta girgiza kai tace ai ko bata ci sai taci abunda Sis Zarah ta kawo mata, d'aukar kwanon tay ta nufi
dining Hajiya tace bata ci anan tace zata d'aukko fork ne,

"Shine sai kin tafi da ita wato kar ki barma kura ko" d'an d'aga murya tay tace eh cinye mata abunta
zatayi, ta sake cewa to wayace mata da fork ake ci hannu ake sawa bazata ji dad'in cinta da fork ba jin
hakan yasa ta wuce dining area ta wanko hannunta ta dawo, daga inda Hajiya take ta fara nuna mata
yadda zata ci ta nade d'aya da kayan cin acikinta ta dangwala yajin kamar yadda hajiya tace ta tura baki
ta fara taunawa, d'an bud'e ido tay lokacin da ta cinye ta yarfa yatsa tace "it's so yummy" dariya hajiya
tayi ta juya ta kai sauran ta hannunta bakin Haisam ya kalli abunda take bashin kaman bazai bud'e bakin
ba sai kuma ya bud'e ta saka mashi ya gatsa ta janye sauran ta tura baki hajiya dake kallonsu tace
"Fateema dai duk ta koya maku kwad'ayi, shima kwanaki a waya naga wainar fulawar ta burgeni nasa
Saude tayi mana ita da rana ina tunanin shi ayi mashi wani abun yaci sai ce man yayi wai zai cita nayi
mamaki don nasan ba lalle in ya ta6a ganinta ba balle ma ya iya cin dana tambayeshi dama yasanta ne
yake ce man ai da Salla da ban dawo bane ta kawo mashi ita nan ya fara cinta" dariya Fanan keyi tana
taunar wainar ita kuwa fatuu a hankali ta d'ago ta kalli Haisam da d'an Murmushi suka sake had'a idon
gaba d'ayansu Maganar Hajiya ta tuno masu da can baya sallar farko data fara yi dashi lokacin daya
dawo ta rink'a kawo mashi abinci har ya rink'a yi mata lesson lokacin ya koyi cin wainar don farko data
kawo mashi cewa yay bai iya cinshi ba saida yaga kaman bata ji dadi ba har zata tafi yace ta kawo yaci
tace mashi ita ba fushi tayi ba tunda bai iya ci ba bari taje zata kawo mashi wani Abincin amman yace
karta damu zai ci don ta gaya mashi musamman don shi ta soya dama kuma saida gwaggo tace mata ba
lalle fa in ya iya cin ta ba wannan dalilin ne yasa ya daure yaci amman kuma sai yaji dadinta musamman
data kasance ba abinci ce mai nauyi ba tun daga nan duk in ta kawo mashi yana ci, janye idonta tayi ta
maida kan tv kaman tana kallo saidae a can k'asan zuciyarta wani iri take ji tunawa da rayuwarsu ta baya
rayuwa mai cike da nishad'i daidai da rana d'aya bata ta6a tunanin komae zai sauya haka ba tsakaninta
dashi,

"To sarakan son kai sai ci kuke kun barni da shak'ar kamshi da alama cinyewa zakuyi ma ba tare da kun
bani ba ko" Hajiya tayi Maganar idonta akan su Fanan dake dariyar Maganar Hajiyar tana niyyar ba
Haisam wadda ta gutsira ya girgiza mata kai yace ta kai mata cike da tsokana ta mak'e kafad'a alamar
bazata bata ba Fatuu data juyo ta kalleta tunda hajiya tayi masu magana ganin abunda tayi yasa ta mik'e
idonta akan Hajiyar tace bari taje tayo mata wata, da sauri Fanan ta kamo hannunta tace wasa take zata
bata ba sai ta k'ara wahalar da kanta ba ta mik'e ta tunkari Hajiyar ta aje kwanon gefenta itama ta zauna
tace to gashi nan su ci yar harararta tayi tace ita da bata da masoyi ko to itama a bakin zata bata tasa
dariya tace wannan ai ba matsala bane ta d'aukko ta fara bata itama tana cigaba da ci, daga inda take
bayan ta cinye wainar bakinta tace ma Haisam "Babe we need to go 4 an outing sis Zarah zata k'ara jin
dad'in jikinta" tana rufe baki Hajiya tace "ba dai Ajiwa Dam d'in zaku je ba?" yadda tayi Maganar har
saida taba Fanan dariya ta girgiza mata kai alamar a'a, tace "ato ai naji kina ce mashi ne kina son zuwa
wurin da kika ga hotunansu nayi zaton can kike nufin kuje ince to kuje ku kad'ai banda ita a samu ma ta
idasa dawowa daidai" sunkuyar da kai Fatuu tayi cikin ranta ta ayyana koda ma ance za'a can d'in ba
zuwa zatay ba don yanzu Ajiwa Dam na d'aya daga cikin Wuraren da bata fatan k'ara zuwa fit ya fice
mata arai ya kuma shiga cikin tarihin rayuwarta ko hotunan datayi a wurin bata son gani, tana son ta tafi
gida amman tasan sai gwaggo tayi Maganar dawowarta da wuri gashi bata son taga tana sa gwaggon
damuwa, kiran sallar Azahar ta tadasu gaba d'aya suka tafi yin salla bayan sun gama ne kuma Saude ta
sanar ta shirya Table lokacin da Haisam ya dawo gaba d'aya suka nufi Dining din harda Fatuu da suka
matsa mawa duk da tace masu ta koshi taci waina amman Fanan tace taci ko kadanne ai suma sunci
wainar ba yadda ta iya, ita ta fara tashi tace ta koshi don ba k'aramin karfin halin zama take tana kallon
yadda suke ciyar da junansu ba Fanan tace ta jirata a parlor inta gama zata gyara mata gashinta ta amsa
mata da to kawae, bayan sun gaman visitor room ta kai Fatun taje dakin Hajiya ta daukko wani dan
babban kit ta dawo lokacin data bud'e ba komai ne aciki ba sai uban kayan gyaran gashi da mayuka,
nuna ma Fatuu dake zaune gefen gado stool din gaban mirror tayi tace tazo ta zauna, bayan ta zauna ta
fiddo stretcher ta fara mata stretching sosae take yaba kyaun gashin Fatuu da yake cike gashi baki wuluk
duk da na Fanan d'in yafi shi tsawo saidae baida cika, sosae ta gyara mata shi sai shek'i yake ta d'aukko
wayarta ta fara masu hotuna ta rink'a masu styles da gashin kansu iri iri, dole Fatuu ta saki ta rink'a yin
yadda duk tace mata tayi sosae hotunan su kai kyau ba kamar daya kasance ita gashinta brown na Fatuu
bak'i bayan sun gama yin hotunan ta maida komae cikin kit ta maidashi Bedroom din Hajiya ta iske
hajiyar kwance tana bacci hakan yasa data dawo tace ma Fatuu su kwanta suma su huta ba kowa a
Parlor tace mata to kawae, zuciya nason mai kyautata mata duk da halin da Fatuu take ciki sam ta kasa
jin tsanar Fanan din hakanne ma yasa wani lokacin bata iya yi mata gardama, har aka kira la'asar suna
bacci ringing d'in wayar Fanan ne ya tasheta ta duba screen din taga Haisam ne ke kira bayan ta dauka
ya tambayeta tana ina ne ya shigo har Bedroom bai ganta ba ta fadi mashi suna bacci ne a visitor room
yace su tashi suyi salla ta shirya tace to don ta gane shirin zuwa gym yake nufi, tashi tay ta koma
Bedroom d'in Hajiya within few minutes tayo wanka ta fito,shiryawa tayi cikin workout outfit riga da
wandonta Ash colour rigar tight long sleeve ce irin mai dogon hannu ta kamata sannan iyakarta tsakiyar
cikinta sai wandon shima skin tight ne dogone ya kai har kasan rigar sun matukar fiddo mata da dirinta
kuma tayi kyau sosae hijjabai guda biyu ta d'auka ta koma d'akin da Fatuu take har lokacin bacci take
dama tana fama da karancin baccin yan kwanakin nan, tashinta tay ta bud'e ido tana kallonta da
Murmushi tace mata ta tashi lokacin salla yayi ta d'aga mata kai kawae ta saukko, lokacin data fito Fanan
din ta kabbara salla don tayi Alwala a toilet hijab din data gani ajiye ta d'auka tasa itama ta kabbara
sallar, bayan ta gama saida ta jira Fatuu ta gama sannan ta sanar da ita zasu tafi Gym ne ko zata k'ara
kwanciya tace mata a'a gida zata tafi hakan yasa suka fito tare Fanan ta shiga d'akin Hajiya ta maida
hijjaban tasa takalma sneakers farare ta d'aura farar jacket kanta kuma ta rufe shi da veil Ash kalan
kayan tayi kyau har ta gaji, sallama tayi ma Hajiya tace adawo lafiya ta fito lokacin Fatuu na zaune kan
kujera a Parlor tana ganin ta fito ta mik'e ta nufeta suka fita tare suna fitowa cikin harabar gidan Haisam
ma ya fito cikin shirin gym hannunshi guda rataye da katuwar jakarshi abunda Fatuu ke ji duk ta ganshi
shi taji gashi ta kasa barin kallonshi har ya k'araso inda suke Fuskarshi a sake yana kallonta Fanan ta kai
hannu ta curo jakar ta rataya shi kuma ya nufi Parking Space don ya fiddo bike din lokacin Fatuu tace ma
Fanan ta tafi gida ta dafa Shoulder d'inta tace in ta dawo zata zo kai kawae ta d'aga mata ta nufi hanyar
gate, tana karya kwana bayan ta fito gate d'in gidan bike d'insu ya taho taja gefe don su wuce, dukkansu
sun sa helmet a kawunansu Fanan na goye da katuwar jakar suna zuwa inda take Fanan ta d'ago mata
hannu suka wuce fuuu,tsaye tayi a wurin tana bin su da kallo har suka yi nisa kafin suka 6ace ma ganinta,
kasa d'aga kafafunta tay taci gaba da tafiya, da k'yar ta matsa ta jingina da fence a cikin zuciyarta ta ke
ayyana Ya Handsome baisonta bai ta6a sonta ba yanzu ne ta k'ara gaskata hakan don ta gano dalilin
dayasa bai ta6a goyata a bike d'inshi ba tunda suke, duk in ta nuna tana son su hau shi in zasu fita sai
yace Mota zasu hau ko kuma in yaga kaman bata ji dad'i ba yace ba yanzu ba ashe duk don kar jikinsu ya
had'u ne sai yanzu ta fahimci hakan ganin da suka wuce gaba d'aya Fanan na kwance a bayanshi ta
sakala hannuwanta a cikinshi, wani 6angare ne na zuciyarta yace kawae ki cireshi a ranki tunda baison ki
yayin da wata zuciyar kuma tace yanzu shikenan sai ki hakura dashi duk irin son da kike mashi ina kike
tunanin zaki samu wani kamarshi, wasu kwalla ne masu zafi suka fara gangaro mata ta shiga yin kuka ba
tare da sauti ba don ta rufe bakinta da tafin hannunta guda,can bayan wani lokaci tasa hannu ta fara
gogewa kafin da k'yar ta d'aga k'afafunta da suka yi mata wani irin nauyi ta fara tafiya, tana karasowa
kopar gidansu har zatai kwana sai kuma ta tsaya kaman mai yin tunani can ta mik'i hanya taci gaba da
tafiya..............,

*ASM Bk2005*

_Destiny may be delayed but cannot be changed......_

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

........gidansu Haulat ta nufa tana zuwa bakin lungun ta hangota ta taho jikinta sanye da Uniform d'in
islamiyya hakan yasa taja ta tsaya suna kallon juna har ta k'araso gabanta tana kallonta ganin yanayin
fuskar Fatun yasa da yar damuwa tace "kawata ya jikin har yanzu?" gyad'a mata kai tay idanunta sun
cicciko da kwalla tace "kiyi hakuri don Allah in sha Allahu komae zai wuce ki dawo kaman da wllh Allah
ne shaidata bana jin dad'in halin da kike ciki Fatuu, dake nike kwana nike tashi kullum Addu'ata Allah
ubangiji ya yaye maki abunda yake damunki" ta k'arasa itama idanunta sun ciko, shiru Fatun tay kaman
bazata ce komae ba sai kuma Haulat taji tace "Yanzu Haulat ki fad'i man ya zanyi in daina jin son Ya
Handsome" a sanyaye tay Maganar, ajiyar zuciya Haulat ta sauke kafin ta dafa shoulder d'inta tace "shi
so matsalarshi kaman ciwo ne farat d'aya yake shiga amman sauki sai a hankali ba kaman yadda yay
maki mugun kamu,amman ba ina nufin bazai barki ba saidae a halin da kike ciki yanzu son Ya Haisam
bazai iya barinki farat d'aya ba ba kaman da yake kina ganinshi, dole sai kinyi yak'i da zuciyarki sosae duk
yadda zata rink'a azalzalarki kan sonshi ki daure ki cije kar ki biye mata in akwae abunda Ya Haisam d'in
ya ta6a maki wanda ya 6ata maki rai ki rinka tunano shi duk in ta ayyana maki wani abu game da
sonshi........" katseta Fatun tayi tace "ni bai ta6a man komae ba na 6acin rai, kawae dai abu d'aya ne
banji dadinshi ba shine yadda ya 6oye man tsakaninshi da Aunty Fanan ni nayi zaton soyayyar
yan'uwantaka ce kawae tsakaninsu kinga dana sani koda ke baki sani ba lokacin da mukayi Maganar
yana sona da zan fad'i maki yana da wadda yake so" shiru Haulat tayi yayin da cikin zuciyarta take
ayyana cewa koda ma ya ta6a yi maki abunda ya 6ata maki rai a halin da kike ciki bazaki ji haushin shi ba,
a fili tace "to ki daure kiyi kaman yadda nace maki da farko sannan ki dage da Addu'a don ba abunda yafi
karfinta in sha Allahu zaki ga komae ya wuce kaman ba ayi ba" jinjina mata kai kawae Fatun tayi, da d'an
Murmushi Haulat tace "kinyi kyau sosae" godiya tayi mata tana son tayi mata Murmushin itama amman
ta kasa ta kama hannunta tace suje kada ta makara, akan hanyarsu ne Haulat ke tambayarta sai yaushe
zata dawo islamiyyar tace mata ta kusa, a daidai kopar gidansu suka rabu Fatun ta wuce ita kuma Haulat
tay tsaye har saida taga shigewarta sannan ta girgiza kai,ba k'aramin tausayi take bata ba duk tayi sanyi
sai kace ba Fatuu ba daka kalli fuskarta zaka fahimci she's in serious grief, juyawa tay saida ta gaishe da
kawu Amadu kafin ta wuce. Lokacin data shiga gidan bata ga gwaggo ba har Parlor da d'akinta ta duba
bata ganta ba hakan yasa ta wuce d'akinta ta haye gado ta fad'a duniyar tunani,tana son ta daina jin son
Ya Handsome saidae son nashi ya rinjayi hakan acikin zuciyarta, dama don ta tabbatar ma kanta da
baisonta ne yasa take jin gara ta daina son nashi ta huta amman a yanzu bata da burin daya wuce taga ta
aureshi wani irin son shi zuciyarta ke azabta mata dashi, a hankali ta kai hannu ta goge kwallan dake
zubo mata, mik'ewa tay ta zauna tsakiyan gadon ta d'aga hannu idonta na kallon sama a fili tace "Ya
Ubangijina Allah ka yaye man damuwata ka cire man abunda nake ji acikin zuciyata na son Ya Handsome
tunda bai sona...." fashewa tay da kuka ta shafa kafin ta koma ta kwanta tana sheshsheka a haka bacci
ya kwasheta, sai gab da sallar Magrib gwaggo ta shigo gidan dama makwabta ta shiga dubiya ganin
takalman Fatuu a bakin kopa yasa ta gane ta dawo ta nufi d'akin ta d'age labule, ganinta kwance tana
bacci yasa ta shiga ta tasheta tayi salla,bayan Sallar isha saiga Fanan lokacin sun dawo daga Gym yau ma
Abubuwan ci ta kawo mata kamar rannan ta sanar da ita gobe around 12 ta shirya zasu fita gari kaman
tace bata zuwa amman kuma a gaban gwaggo ne hakan yasa ta amsa da to kawae, tare da gwaggo suka
ci abubuwan da ta kawo masu ba don tana jin dad'insu ba sai don gwaggon ta matsa mata, bayan sun
gama ta bata wanda aka d'ibar ma Amadu ta fita ta kai mashi bayan ta dawo saida ta watsa ruwa ta
canja kaya zuwa na bacci sannan ta kwanta sai faman sak'e sak'e take aranta kaman ko yaushe don sam
bata jin bacci saboda tayi na yamma koda gwaggo ta shigo yi mata Addu'a isketa tay idonta biyu tace to
in ta tashi yin baccin ta tabbatar tayi ta amsa mata da toh.
Washe gari tun bayan data yi breakfast ta tattara kayan wanke wanke tayi tana niyyar yin shara gwaggo
tace ta barshi zatayi hakan yasa ta koma tay kwanciyarta, wuraren karfe sha d'aya da wasu mintuna
gwaggo ta lek'a dakinta ganinta kwance yasa tace mata ba zasu fita bane tay kwance ta daure ta tashi ta
shirya ta amsa mata da to, bayan ta tafi ta yunkura ta mik'e zaune ta zuro kafafunta k'asa har cikin ranta
bata son fitan don tasan dole taga Ya Handsome kuma duk inta ganshi ita kad'ai tasan mi take ji, wani
dan Murmushin takaici tay wai yau itace ke gudun ganin Ya Handsome, da k'yar ta mik'e ta nufi
wardrobe d'inta ta cire kayan jikinta d'aura towel tay ta wuce Toilet, bayan ta fito mai kawae ta shafa
tasa undies ta zumbula doguwar riga ta koma gado tay kwance, K'arfe sha biyu saura mintuna kad'an
Fanan ta rafka sallama har saida Fatuu ta runtse idanunta jin muryartata, Ma sha Allah abunda na fad'a
kenan ganin shigar da tayi ta kwankwatsetsen leshi Coffee brown yana da touches din light brown an
mata wasu matsiyatan riga da skirt da suka bi shape d'inta skirt d'in daga k'asa ya bud'e sosae haka
hannun rigar ma ya d'an kumburo k'afafunta sanye da takalma masu tsini sosae brown haka hannunta
tana rike da yar madaidaiciyar jaka louis vuitton brown colour, tun daga kunnuwanta da wuyanta da
hannayenta duk zinari ne harda zobban yatsun hannunta ta kifa daurin kallabi zarah buhari da alama
tana son irin d'aurin gashin kanta ta lankwasashi ya tsaya k'asan shoulder d'inta ta d'aura d'an veil
brown color a kafadarta d'aya da bata ma sa gyalen ba saida Haisam yay mata Magana sannan ta
d'aukko tasa, tsayawa tay bakin Kitchen suna gaisawa da gwaggo data lek'o tana washe baki ta shiga
kod'a kwalliyarta tana Fad'in "Tubarkallah ma sha Allahu d'iyata kin matuk'ar yin kyau, d'ana ya barki
kikai kwalliya haka karfa a kwace mashi ke" dariya sosae Fanan ke yi jin Maganar gwaggon tace "ni tashi
ne ai ba wanda zai iya mashi snatching" gwaggo tace "tabbas wannan haka yake" tambayarta tay Fatuu
tace "tana d'aki tun da tay wanka ta shige nasan zuwa yanzu ta shirya bari in kirata" tana niyyar fitowa
Fanan tace ta barshi bari tay mata Magana ta nufi d'akin, tana d'aga labule suka had'a ido da Fatuu data
tashi zaune jin ta zata shigo, nufar ta tay ta zauna gefen gadon ta kamo hannunta tace "Zarah are u ok?"
kai ta d'aga mata alamar eh, kallon jikinta ta d'anyi tace " ya baki shirya ba?" a hankali tace mata ta
shirya,

"But u doesn't look gud in dis" tay Maganar ta d'an kamo rigar jikinta ita dae shiru tay mata hakan yasa
ta tambayeta a ina kayanta suke ta nuna mata bangaren da kayanta suke a wardrobe da hannu ta mik'e
ta nufi wardrobe d'in idon Fatuu a kanta ita kanta tayi mata kyau sosae, dudduba kayan ta shiga yi can ta
fiddo wasu riga da skirt na Red lace a sallar data wuce Haisam ya yi mata su, lokacin data juyo da kayan
har saida gabanta ya buga, aje mata su tayi gabanta tace ta sasu zasu fi yi mata kyau akan wannan rigar,
ba yadda ta iya dole ta saukko daga gadon ta d'auki kayan ta fita, bayan wani lokaci ta dawo ta saka su
Fanan na ganinta ta saki Murmushi ta hau yaba kyaun da kayan suka yi mata don itama sun kamata sun
fito mata da k'irarta saboda yanzu sun saba da Kb mai d'inki yasan irin d'inkin da take so duk da gwaggo
bata son ana mata matsattsun kaya saidae bata ma sanin an kai d'inkin saidae ta gansu an kawo taita
fad'a, kama hannunta tay ta kaita gaban Dressing Mirror yar light makeup tay mata ta tambayi inda
jewellery d'inta suke ta nuna mata drawer chest tana jawowa tay arba da sark'a mahad'in kayan silver ce
mai adon red stones harda d'an hannu da zobe ta d'aukko su ta saka mata ta sake d'aukko agogo zata
saka mata Fatun tace ta barshi d'an hannun ya isa ta amsa mata Ok, d'aurin kallabi mai kyau tayi mata
bayan ta gyara mata gashinta ta d'aure tun kafin ta tambayi takalma Fatun ta curo daga kan shoe rag
dake gefen mirror d'in ta saka, d'agowa tay tana kallon kanta a madubi yaushe rabon data yi gayu
haka,had'a ido sukai da Fanan ta cikin mirror d'in ta sakar mata Murmushi itama ta d'anyi mata suna
cikin haka gwaggo ta d'aga labule ganinsu tsaye yasa tace "kar dai 6ata maki lokaci tay bata shirya ba tun
d'azun" tana Murmushi tace "No ta shirya granny na sa ta canja kaya ne" kai gwaggon ta jinjina kafin ta
saki labule, bayan ta yafa gyalen kayan da takalma bata d'auki jaka ba suka fito, gwaggo ta fito daga cikin
kitchen sukai mata sallama kafin suka wuce idanunta akan Fatuu sosae taji dad'in ganinta tayi gayu haka,
Wata rantsattsiyar Mota ce brown fake a kopar gidan bata ma ta6a ganinta ba suka nufeta Fanan ta
bud'e mata baya ta shiga ta rufe itama ta bud'e gaba ta shige,wani masifaffen kamshine ke tashi cikin
motar hadi da ni'imtaccen kamshin ac, yana zaune jikinshi sanye da jugunannar brown shadda da akai
ma fav dinkinshi wato Sen style kanshi ba hula sumar nan tasha gyara sai salk'i take, tana shigowa ta kai
hannu ta kama hannunshi guda tace "Sorry babe we kept u waiting" jinjina mata kai yay lokacin suka
had'a ido da Fatuu ta cikin Mirror ta gaidashi a sanyaye ya amsa daga haka yaja Motar suka tafi, tunda
suka hau hanya bata ce uffan ba sai Fanan ce keta mashi hira hannunta guda ruk'e da nashi hannun yana
driving da d'aya wani lokacin kuma ya kan janye hannun kaman in zai sha round, sai Fanan d'in ta sakota
sannan take bud'e baki tay Magana, kopar Marusa lowcost ya nufa dasu gidansu Nana suna tsayawa
bakin gate d'in gidan Nanar ta fito dama tana ta dakon zuwan nasu don Haisam ya sanar da ita game da
zuwan nasu, rungume juna sukai ita da Fanan cike da farinciki take mata sannu da zuwa bayan sun saki
juna ta kai idonta kan Fatuu dake tsaye gefe da Murmushi ta kamo hannunta tana mata sannu da zuwa,
nufar Motar tay Haisam ya bud'e kopar suka gaisa tace "lallai zakee wannan too match haka kaida
Amarya kaman dae an d'aura" yana Murmushi yace mata miya rage ne, ce mashi tay yini zasuyi ko yace
zaije dae ya dawo After zuhr akwae wuraren da zasu je, lokacin data shiga dasu gidan gaba d'aya yan
gidan na a Falo don a k'agare suke da suga wadda Zakee zai aura don ba k'aramin zuzuta ta Nana tay a
wurinsu ba,suna shiga duk suka mik'e suka tarbesu da fara'a suna masu sannu da zuwa kowa idonshi na
akan Fanan dake ta masu dariya, bayan sun zauna duk suka shiga gaishe da ita tana amsa masu Fatuu
ma ta gaidasu duk suka kira sunanta suka ce tana lafiya da yake sun santa yanzu sosae don duk salla
gidan Haisam ke kawota kunshi harda kitso in tana so, wani lokacin ma hakanan in ya fito da ita kaman
da yamma in ba islamiyya sai ya kawota gidan idan ya dawo sai yaje ya dauketa yanzu Nana ta san
tsakaninta da haisam d'in don akwae lokacin data je gaida Hajiya lokacin taje gidansu Fatun suka gaisa
da gwaggo, abubuwan ci da sha aka shiga jera masu kafin a gama Abinci,Fanan ce ta fara ci ita Fatuu
cewa tay ta koshi Nana tace wai ko bata lafiya ne ita fa ta lura duk tayi sukuku ba kaman yadda ta santa
ba tana rufe baki sauranma sukace duk sun lura da hakan harda mommy d'insu, Fanan ce ta gaya masu
bata lafiya ne bata dad'e ma data fara samun sauki ba duk suka hau yi mata ya jiki tana amsa masu suka
ce Allah ya sawake,saida Nana ta matsa mata sannan ta d'an ci wani abu, fira sosae suka shiga yi da
Fanan dama ita bata da bak'unta ita dae Fatuu baka jin bakinta saida aka kira sallar Azahar Nana ta jasu
d'akinta suka yi salla Fatuu na gamawa ta kwanta kan abun sallar su kuma suka ci gaba da yin fira a
tsakaninsu har Fanan nace mata za dai tazo bikinsu ko Nanar tace ai ko a India akeyi sai taje balle Lagos
Fanan d'in tace ai a Abuja ma take tunanin za'ayi just bai wuce ay wasu programmes a Lagos sannan a
dawo Abuja a nan za'a daura aure, duk hirar da suke Fatuu na jinsu jin Maganar aurensu da Fanan ke yi
yasa ta runtse idonta sosae kirjinta yay mata wani irin nauyi, suna cikin firar kanwar Nana tazo tace ga
abinci can an shirya Fanan tace a kawo masu shi nan kawae tace to ta juya, bayan an kawo kayan
Abincin Nana tay serving nasu Fanan tace ta zuba masu gaba d'aya su ci tare tana dariya tace "an gama
Amaryarmu" kiran Fatuu ta fara yi ta tashi su ci abincin tana ji tay mata shiru har saida ta d'an bubbuga
kafafunta sannan ta amsa mata koda tace mata ta tashi suci Abinci cewa tay ta koshi zuciyarta tashi take
zata iya yin amai jin hakan yasa ta kyaleta suka fara ci su biyu har Nana na cewa gaskiya tana jin jiki
Zarah mai Magana ka ganta haka Fanan tace ai da sauk'i ma yanzu, Bayan sallar Azahar Haisam yazo ya
d'aukesu Nana da kannenta sukae masu rakiya har Mota don basu gaji da kallon Fanan d'in ba gaba
d'aya ta tafi da hankalinsu, lokacin da suka isa bakin Motar bayan sun gaida Haisam har ce mata sukae
amman dai Aunty zaki dawo ki mana wuni ko Nana tace ma Haisam ai gaskia wannan ba zuwa bane dole
ya maido masu ita wuni shi dae murmushi kawae yake Fanan d'ince tace masu zata dawo kafin ta tafi in
sha Allah Fatuu dai na tsaye gefe ta jingina da Motar duk ta k'agara su tafi ita in son samu nema su
maidata gida kawae, sallama sukai masu harda Fatun suka shige mota suna d'aga masu hannu suka tafi
sannan suka koma cikin gidan suka hau yabon Fanan. Daga nan Gra suka wuce gidansu khairat wanda
tangamemen gidane had'addan gaske don babanta dan Majalisa ne a Abuja basu cika ma zama anan
Katsina ba sunfi zama a Abuja yanzu ma don ana hutu ne,tayi murna sosae da zuwan Fanan haka Fatuu
ma hannu biyu ta kar6eta tare da sauran yan gidan har tana tambayar Fanan sis d'insu ce tace mata eh
don ranar da ta kai Fanan gidan Hajiya itama bata lura da sadda Fatun ta fito daga Mota ba ta shige gida
lokacin idonta na akan Fanan da Masoyinta, lafiyayyan Abinci da abubuwan ci da sha aka jere masu akan
c-table da khairat tace a shirya table Fanan tace ba wani ci zasuyi sosae ba don sun ci Abinci ita Fatuu ma
cewa tay ta koshi saida khairat tace ya za'ai tazo gidansu first time tace kuma bazata ci komae ba, dole ta
d'an tsakuri wasu abubuwan itama Fanan ba wani mai yawa taci ba suna cikin fira Haisam ya kirata su
fito su tafi khairat d'in tace ita gaskiya bata yarda ba cewa tay zatai spending whole day shine daga zuwa
zasu tafi saida tace mata ai zata dawo kafin ta tafi sannan ta yarda ta rakosu har waje bayan sunyi
sallama da yan gidan harda kyautar undies da turare guda ukku masu kyau da tsada taba Fatuu tay mata
godiya, suna baro gidansu khairat zagayawa yay dasu gari sai gabda la'asar suka wuce gidan Abbas suna
yin parking Abbas da dama jiransu yake ya nufi Haisam yana dariya suka gaisa ya kalli Fanan data fito
yace "Our bride u'r highly welcome" amsa mashi tayi da "thank u Abbas" tana dariya ya kai idanunshi
kan Fatuu ta d'an yi mashi Murmushi yace "Mom Zarah kwana biyu" ita dae murmushin yak'e kawae
take mashi kafin suka nufi ciki suna shiga entry din Falon Feenah ta tar6esu da fara'a tana sanye da
doguwar rigar lace hannunta ruk'e da babynta data sake haifa kusan shekara d'aya data wuce, hannu
Fanan ta mik'a mata ta amshi babyn da fara'a tace "What's her name?" tace "Nasreen" Abbas ne yace su
shiga ciki mana, jin an fara kiran salla yace bari suje suyi salla su dawo suka juya da Haisam, cikin falon
suka nufa bayan sun zauna suka gaisa da juna Fatuu ma ta gaishe da ita ta amsa tana ce mata kwana
biyu itama Murmushin tay mata kawae ta mik'e taje ta kawo masu ruwa da lemu da d'an abun ta6awa ta
koma ta zauna bayan ta zuba masu lemun a cups, hira sosae suka shiga yi da Fanan dama sun san juna ta
waya badai su ta6a ganin juna ba a zahiri ita Feenah ta ta6a ganin pic d'in Fanan wanda suka yi tare da
Haisam a wayan Abbas, bada jimawa ba su Abbas suka dawo akan 3 seater suka zauna Feenah ta gaida
Haisam ya amsa mata fuskarshi a sake Abbas yana Murmushi yace ma Fanan "Amaryarmu zuwa ba
sanarwa mu shirya maki sosae" tana dariya tace "it was a suprise" jinjina kai yay yace mata anzo lafiya ya
karatu ta amsa mashi da Alhamdulillah, kallon Fatuu yay da tay shiru gefen Fanan da yake kan sofa 2
seater suka zauna yace "Mom Zarah ya karatu?" a sanyaye tace mashi lpy lou yace "an kusa graduation
ko?" kai ta d'aga mashi alamar eh yace to Allah ya bada sa'a ta amsa da Amin ta tambayeshi ina Abdul
yace yana tahfiz daga haka ya juya kan Fanan suka cigaba da hirar india ita kuma ta d'an kwantar da
kanta tay shiru sai kace bata a falon can Abbas yace "Wai Mom Zarah kodae baki Lafiya ne?" d'ago kanta
tay ta kalleshi kafin ta bashi amsa Feenah ta rigata cewa"Wllh Dear nima am about to ask her shirun
nata yay yawa" shiru tay tana binsu da ido ta rasa mi zata ce Fanan tace masu ai bata lafiya ne almost a
week yanzu ne ta d'an samu sauk'i har suka fito tare, jinjina kai sukae gaba d'aya sukai mata Allah ya
sawake ta amsa masu da Amin suka cigaba da firarsu ita kuma ta koma ta jingina da kujera tana binsu da
ido, tun bayan da Abbas yay Maganar jefi jefi yake juyawa ya kalleta duk in ya kalleta kuma sai su had'a
ido hakan yasa tasha jinin jikinta sai yan kame kame take, wani d'an guntun Murmushi yay bayan sun
k'ara had'a ido da ita yace "Mom Zarah ko ki shiga ciki ki kwanta" kafin ta bashi amsa Feenah tace
"amman dear yamma yayi fa kuma ba'ason bacci irin wannan time en ba kaman ita da bata lafiya,

"ai dama ba ina nufin tay bacci ba ta d'an hutu looks like she isn't comfortable here" kai Feenah ta d'aga
tace "amman fa bata ci komae ba just drink tasha, kallon Fatuu yay still da Murmushi a fuskarshi yace "
Mom Zarah ana ciwo ba cin abinci ai baza'a warke da wuri ba kuwa, ki daure kici Abinci" shiru tay tana
kallonshi kafin ta kai kallon kan Haisam da tunda Abbas ya fara mata Magana yake kallonta, a hankali ta
sunkuyar da kanta jin bugun da kirjinta ya fara ga kwalla dake neman zubo mata Abbas yace in bata son
ci taje kawae aikuwa da sauri ta mik'e ba tare data yadda sun had'a ido da kowa ba ta nufi Bedroom d'in
Abdul ta shige, Abbas da ya bita da ido ya juyo ya kalli Haisam yace "miyake damunta ne?" yana daga
kishingid'en da yake ya fad'i mashi matsalar Aljanu ne da mamaki Abbas yace "Aljanu kuma, dama Mom
Zarah nada Aljanu?" kai ya d'aga mashi kafin yace mashi shima bai san tana dasu ba sai yanzu, shiru
Abbas yay kaman mai nazarin wani abu cikin ranshi ya ayyana dis is more like a heartbreak ba Aljanu
ba,can ya tambayi Haisam waye yace tana da Aljanun, farko shiru ya d'an yi mashi sai kuma yace mashi a
wurin Hajiya yaji daga haka bai k'ara cewa komai ba shima Abbas d'in bai k'ara tambayarshi wani abun
ba, misalin karfe shidda mai d'aukko Abdul ya kawo shi cike da farinciki ya ruga ya haye Haisam yana
fad'in "Baba Zakee ashe kazo" kai Haisam ya d'aga mashi yace "My Boy ka girma fa yanzu kana haye
babanka haka zaka karya shi" kyalkyacewa yay da dariya Fanan ta bisu da kallo tana murmushi don tana
son yara ba kamar yadda ta gansu haka yanzu sun burgeta shiyasa burinta suyi aure itama ta haihu,
Abbas ne yace mashi ga Momy d'inshi nan tazo yaje ya gaishe da ita da sauri yace "Aunty Zarah?" girgiza
mashi kai yay ya nuna mashi Fanan dake mashi dariya ya k'ura mata ido yana kallonta can ya juya ya kalli
Abbas yace "ba Aunty Zarah ce Mommy na ba?" Abbas dake Murmushi yace "yeah ita Mom d'in Zakee
ce ita kuma wannan Mom d'inka ce kai kadae kaman yadda Zakee yake babanka" da mamaki yace "to
Matarshi ce?" Abbas yace "eh itace zai aura" bin ta yay da kallo ganin haka yasa Abbas yace yaje ya
gaidata ya saukko daga jikin Haisam ya nufi wurinta yana zuwa ta rungume shi tana tambayarshi ya
Makaranta yace mata lpy lou tace yana dai kokari ko yace mata eh duk bai wani saki jiki ba, can ya janye
jikinshi ya koma wurin Abbas yace "Dad ina Mom Zarah ba'a zo da ita ba?"

Yace "Tana d'akin ka bata jin dad'i ne" zaro ido yay yace "bata lafiya" kai Abbas ya d'aga mashi aikuwa
da gudu ya nufi d'akin nashi suka bishi da ido da d'an Murmushi kan fuskokinsu, tun a bakin kopa ya fara
kiran sunanta yana shiga ya ganta ta dukunkune saman gado baiwar Allah da k'yar ta samu bacci ya
dauketa,hayewa yay saman gadon gefenta ya fara bubbuga jikinta yana kiran sunanta, a hankali ta bud'e
idonta da sukai ja ta kalleshi tana ganin shine ta yunk'ura ta tashi zaune da d'an Murmushin da iyakarshi
lips d'inta tace mashi ya dawo bai bata amsa ba ya kama hannuwanta da yar damuwa yace "Aunty Zarah
wai baki Lafiya" shiru ta d'anyi tana kallonshi shima kallonta yake ba komae take tunawa ba sai farkon
kawota gidan lokacin da sukai game dashi cike da nishadi da kuma sauran lokutta, ita yanzu shikenan
haka zatai ta zama da damuwa ta ayyana a ranta kawae sai ta fashe da kuka, waro ido Abdul yay a rud'e
yace "Aunty Zarah kuka kike" shiru bata ce mashi komae ba ta rufe bakinta da tafin hannunta, kokarin
sauka daga kan gadon ya fara yi yana fad'in "bari inje in gayo ma su Dad baki lafiya kina kuka azo akai ki
Hospital" da sauri ta kamo hannunshi tana girgiza mashi kai yace "kar naje na fad'i masu?" d'aga mashi
kai tay alamar eh yace "to ki daina kukan don Allah" yadda yay Maganar kaman shima zai sa kukan, a
hankali tace to ta daina ya kai hannu yana goge mata hawayen, da k'yar ta samu hawayen suka tsaya
cikin muryar wanda yay kuka tace mashi ya Makarantar yace lafiya lou tace yana dae kokari ko yace eh
sosae,shiru sukai na d'an lokaci can yace "Aunty Zarah yau bazamuyi game ba tunda baki lafiya ko?" kai
ta daga mashi alamar eh yace "Allah ya baki lafiya sai mu yi" a hankali tace Amin suna cikin haka sai ga
Abbas ya shigo d'akin Abdul na jin sallamarshi ya sauka daga gadon da sauri ya nufe shi yana fad'in
"Daddy Aunty Zarah tayi kuka a kaita Asibiti" jinjina mashi kai yay ya nufi cikin d'akin ya tsaya gabanta
yana kallonta kanta na kasa tunda taji Abdul yace tayi kuka, slowly Abbas ya kira sunanta ta amsa ba tare
data d'ago ba hakan yasa yace ta kalleshi kaman bazata d'ago ba can ta d'ago da jajayen idanunta ta
kalleshi duk ta kame kanta,

"In akwae abunda ke damunki banda ciwon da akace kar kiji komae ki fad'a man" da sauri ta girgiza
mashi kai tama kasa yi mashi Magana, d'an Murmushi yay yace "to miyasa kike kuka?" murya na rawa
tace "d...da dama jikin nawane bana jin dad'inshi..." shiru ya d'anyi kafin yace "an kai ki Asibiti ne?"

"A'a, amman Aunty Fanan tayi man Allurar zazza6i ta kwana ukku nama samu sauki sosae yanzu"

"Ko mu kaiki Asibiti to tunda kince jikin naki har yanzu bai maki dad'i" taji ya fad'a, da sauri ta girgiza
mashi kai tace "a...ai gwaggo tace ciwon bana Asibiti bane tasa anyo man Addu'a a ruwan zam zam ina
sha" shiru yay yana cigaba da kallonta hakan yasa ta sunkuyar da kanta don gabanta wani irin bugu yake
mata ita tsoronta wai kar ya gano mike damunta ya fita ya fad'i masu, sigh yay yace mata Allah ya bata
lafiya ta amsa da Amin ya kalli Abdul yace ya cire Uniform d'in jikinshi yasa kaya yazo zasu je Masallaci ya
amsa da to, wani sanyi taji bayan Abbas d'in ya fita Abdul ya nufi wardrobe d'in kayanshi don ya canja
kaya bayan ya d'aukko wanda zai sa ya juya yace ma Fatuu wai ta juya zaisa kaya bata san lokacin data
saki dariyar da rabon da tayi irinta ta manta, kifa fuskarta tay jikin pillow tace bata ganinshi yasa ya amsa
da to, bayan ya fita saiga Feenah ta shigo da Murmushi ta nufi Fatun tana tambayarta ya karfin jikin tace
mata da sauk'i tace to ta tashi tayi salla ta amsa da to ta mik'e ta nufi toilet itama ta fice dama Fanan ta
kai d'akinta tayi salla shine tazo wurin Fatun, suna dawowa daga sallar Haisam yace ma Abdul yaje ya
kira Zarah zasu tafi, tare suka fito dashi ya ruk'o hannunta idonsu akanta hakan yasa duk ta dabarbarce
ta sadda kanta k'asa har ta k'arasa cikin Falon ta zauna kusa da Fanan, Abbas ne yace ko zasu tafi sai taci
Abinci sannan, ba yadda ta iya dole ta d'an ci Abincin da Feenah ta zuba mata, har bakin Mota suka yo
masu rakiya Feenah tace ma Fanan in sha Allahu kafin ta tafi tana nan zuwa dan da suna hira tace mata
upper Monday zata tafi tace to tana jiranta, sallama suka yi masu suka k'ara yi ma Fatuu Allah ya sawak'e
Abdul ya d'aga mata hannu yana mata bye bye itama ta d'an mashi kafin ta bud'e Mota ta shige suma
duk suka shiga yaja suka bar gidan...........

*ASM Bk2006*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.......bayan sun baro gidan Abbas a wani Shopping complex ya tsaya dasu yace ma Fanan suje suyi
shopping ta amsa mashi da owk ta bud'e Motar ta fita shima bud'e kopar side d'inshi yay har zai fita ya
dakata ya juya ya kalli Fatuu dake zaune suka had'a ido,

"Ki fito zamuyi shopping" ya fad'a da cool voice d'inshi, girgiza mashi kai tay a hankali tace "ni bani
buk'atar komae" wani kallo ya bita dashi da sauri ta sunkuyar da kanta kirjinta na bugawa da sauri da
sauri,

"Let's go Zaraah" wani yamm taji a jikinta duk cikin masu kiranta da Zarah ba wanda ya kai shi iya
Fad'a gashi da wani irin sauti mai dad'i sunan ke fita, d'agowa tay suka had'a ido kawae sai ta Fara
yamutsa fuska tana ta6e baki alamar zatayi kuka dama har yanzu bata bar ta6e baki ba in zatayi kuka tun
yarinta, still yay yana bin ta da ido sai far far take da ido don kada kwallan su zubo mata kawae sai yay
wani murmushin gefen baki ya d'an girgiza kai ya fice daga Motar, zagayawa yay side d'in da Fanan take
tsaye tana amsa waya tana ganinshi tace ma wanda suke wayan zata kira daga baya tay rejecting call
d'in, ganin ba Fatuu tace mashi Zarah fa yace zuje kawae zasu d'aukar mata abunda ya dace ta amsa da
Ok, sosae sukai shopping bayan sun gama aka zuba masu a shopping bags aka biyo su dasu, jakar da
suka siya ma Fatuu kaya Fanan ta bud'e baya gefenta ta aje sauran kuma aka saka masu a boot daga
haka suka shige Motan suka tafi,suna kan hanya jin shirun Fatun yay yawa yasa Fanan ta kira sunanta
tana jinta tay mata shiru hakan yasa ta juya baya ta kalleta ganin ta langa6ar da kai gefe yasa tay tunanin
bacci take, suna k'arasowa kopar gidansu ta bud'e Motar ta fita Fanan ma ta fito ganin bata d'auki kayan
ba yasa ta tsaidata ta bud'e bayan ta d'aukko mata don tayi tunanin ko bata san nata bane har da ledan
kayan da khairat ta bata, tana tsayen kafin Fanan ta d'aukko mata glass d'in gaban ya sauka Slowly, da
sauri ta kai idonta wurin suka had'a ido dashi da yake akwae wuta globe din gaban shagon kawu Amadu
ya haske wurin, ya d'an kwantar da kanshi jikin headrest kasa jure ma kallonshi tay ta sadda kanta k'asa
lokacin Fanan ta mik'o mata jaka guda ita ta ruke mata guda tace suje, har lokacin idonshi na akanta ta
juya kawae sai taji kaman bata kyauta ba don bai ta6a yi mata abu ba ba tare data gode mashi ba kuma
hakan hud'ubar gwaggo ce, tsayawa tay Fanan ta juyo kafin tayi mata Magana tace mata zatai mashi
godiya ne ta amsa da Ok tay gaba abunta, a hankali ta nufi Motar kamar wadda kwae ya fashe mawa a
ciki ta tsaya gaban kopar tana kallonshi ba tare data ce mashi komae ba shima kuma baida niyyar tanka
mata can ta bud'e baki da k'yar tace "Nagode Allah ya saka da Alkhairi" shiru kaman bazai tanka ba sai
kuma taji yace "Ameen" k'okarin juyawa ta tafi ta fara yi taji yace "Zaraah?" wani mugun bugu k'irjinta
yai dammn ta juyo a d'arare ta kalleshi gently yace "kina da wani problem ne?" a hankali ta girgiza mashi
kai alamar a'a,

"Then why d change?" wani irin harbawa zuciyarta take ita tsoronta ma kar Fanan ta fito su tutsiyeta
tare har su gano abunda ke damunta don a yadda take ji komae zai iya faruwa, "am talking to u zaraah
why u look different?" baki na rawa kaman zatai kuka tace "b..ba..banjin dad'in jikina ne ba kasan ban
Lafiya ba" shiru yay yana nazarin Maganar calmly yace "Ok i understand, ki fad'a ma grandma d'inki
zamuje hospital tomorrow" da sauri ta d'ago ta kalleshi tace "ai ba ciwon Asibiti bane Addu'a ake man
kuma anyo man ina sha" ta kai Maganar tana sussuna kai k'asa don wani irin kuka ne ke taho mata, Sigh
yay yace mata zata iya tafiya Allah ya bata Lafiya da sauri ta amsa da Amin ta juya a harhard'e ta nufi
gidan tana shiga zaure ta lafe a jikin bango ta tura gyalenta a baki ta fashe da kuka,can zuciyarta ta raya
mata kar Fanan ta fito ta ganta haka da sauri ta goge kwallan ta d'auki ledan ta shiga cikin gidan, a bakin
kopar Parlor ta hangi takalman Fanan ta jiyo muryarta ita da gwaggo hakan yasa ta aje ledar a gefe ta
nufi hanyar toilet, jin motsi yasa daga cikin falon gwaggo ta tambayi waye tace itace zata shiga toilet ne,
koda ta shiga kukan taci gaba da yi, ita kanta yanzu tsoron fad'i ma Haisam d'in take game da son nashi
don ta yarda da Maganar Haulat ta zata jefa kanta a wata Matsalar ne,har saida taji gwaggo ta rako
Fanan suna sallama sannan bayan ta tafi ta wanke fuskarta sosae ta d'auro Alwala ta fito cikin sa'a tana
fitowa taga gwaggo ta kabbara sallar isha hakan yayi mata dad'i don bata son ta gano kukan da tay,
itama sallar taje d'aki tayi bayan ta gama sosae tayi Addu'a kan halin da take ciki daga baya ta kwanta
kan abun sallan, tana kwancen gwaggo ta d'aga labulen ta kira sunanta tace ko har ta kwanta, d'an d'ago
da kanta tay tace mata eh ta gaji ne sosae bacci take son yi tace "to bazaki ci Abinci bane?" d'aga mata
kai tay tace "eh banjin yunwa munci Abinci" jinjina kai tay tace to ta tashi ta hau gado kuma ta tabbatar
tayi Addu'a ta amsa mata da to ta juya ta tafi, mik'ewa tay ta cire kayan jikinta har zata nufi gado taji
kuma ruwa take son ta watsa ta nufi toilet bayan ta yafa mayafi a kanta, tun bayan data fito ta saka
kayan bacci ta haye gado ta dasa sana'ar tunane tunanenta, tabbas tana son ya Handsome sosae to
amman ta gane ba samunshi fa zatayi ba matuk'ar yana tare da Fanan yanzu ya zatayi, nan take ta gano
bata da wata mafita da ya wuce tay hakuri dashi tayi yak'i da zuciyarta kaman yadda Haulat tace mata,
yin wannan tunanin yasa ta saukko daga kan gado ta d'aukko Al'qurani ta fara karantawa acikin zuciyarta
bayan wani lokaci ta rufe ta d'aga hannuwa harda kwallanta ta rok'i Allah daya cire mata son Ya
Handsome, bayan ta gama ta mayar dashi cikin jakarta ta koma kan gado tay lamo tana cigaba da zubar
da kwalla a haka bacci yay awon gaba da ita.

Washe gari data tashi ba laifi ta d'an ji k'arfin jikinta bayan tayi breakfast ta fara ayyukanta gwaggo nata
jin dad'i duk in suka had'a ido sai tay mata d'an mumushi,da yake aikin safe take Fatun ta tambayeta mi
zata dafa kafin ta dawo tace ayyukan bazasu yi mata yawa ba kuwa ko ta samu wani abun taci in ta dawo
sai tayi Fatun tace ba komae zata iya, ta fad'i mata abunda zata dafa kafin ta tafi, tana ta ayyukanta tana
tunane tunane har ta gama komae tayi wanka tay kwanciyarta, rashin zuwan Fanan ba k'aramin dad'i
yay mata ba don ta fahimci duk in ta gansu su biyun k'ara mata ciwon suke,k'arfe biyu da wani abu
gwaggo ta dawo lokacin Fatuu nata bacci abunta ba laifi yau ta samu bacci sosae bata tasheta ba ta
wuce d'aki ta kimtsa kafin ta fito ta nufi Kitchen sosae taji dad'in ganin Fatun tayi Abincin lafiya lou ga
Kitchen din tsaf a cikin ranta take godiya ga Allah da ya amsa addu'arta da take ma Fatun, sai wurin karfe
ukku ta farka tayi mamakin irin baccin da tayi da har bata san gwaggo ta dawo ba, ana kiran sallar la'asar
ta watsa ruwa tay salla ta fara shirin zuwa islamiyya, bayan ta gama ta lek'a d'akin gwaggo tace mata ta
tafi islamiyya tana washe baki ta hau yi mata Addu'oi har da fitowa wai bari tayi ma yar autarta rakiya
waje ta rungumo kafad'unta Fatun tasa dariyar da yaushe rabon da gwaggon taga tayi ta, Lokacin data je
Haulat bata kai ga zuwa ba nan yan ajin suka hau yi mata ya jiki don Haulat ta sanar da rashin lafiyan
nata, lokacin da Haulat ta shigo ajin suna had'a ido da Fatun ta nufeta da yar sassarfa ta duk'a ta dafata
tana washe baki tace ta samu sauk'i kenan ta jinjina mata kai kawae, zama tay sosae taci gaba da k'arfafa
mata guiwar tayi hakuri ta cire shi daga ranta ba tare da wani ya ji maganar da suke ba a haka har
Malam ya shigo, bayan an tashi ma akan hanyarsu ta dawowa shawarwari taci gaba da bata ita dae
saidae ta d'aga mata kai kawae duk da tana son amfani da shawarwarin saidae har lokacin ba abunda ya
canja na daga son ya Handsome a cikin zuciyarta, bayan ta koma gidane gwaggo ke fad'i mata Fanan
tazo tace da daddare zata dawo tace to kawae.

Gaba d'aya satin guje ma duk wani abu da zai kaita gidan Hajiya take in gwaggo tace taje da ta fito sai ta
wuce gidansu Haulat, Fanan har Maganar rashin zuwan nata tayi don a tunaninta ta samu sauk'i tace
mata islamiyya take zuwa da yamma da safe kuma ita ke aikin gidan, sosae ta fahimceta bata sa komae a
ranta ba ita taci gaba da zuwa, ba laifi kuma Fatun ta d'an k'ara sakar mata jiki, a cikin satin Haisam ya
kaita gidansu Khairat ta wuni bata samu kara zuwa gidansu Nana ba amman ita tazo harda k'annenta
yan mata guda biyu suka kawo mata kaya harda atampopi don ranar Monday zata tafi, Feenah ma tazo
itama ta kawo mata abubuwa d'inkakkun Material masu kyau da tsada kala biyu sai kayan kamshi su
humra da kullacca har gidansu Fatuu taje ta k'ara yi mata ya jiki suka gaisa da gwaggo Abdul yaji dad'in
ganinta tana ta mashi dariya har yana cewa da yasan ta samu sauk'i da yazo da tab d'inshi sun yi game,
Feenah tace shi damuwarshi kenan game ko duk suka yi dariya gwaggo tace ina ruwan yaro, daga baya
suka yi masu sallama suka tafi Fatuu ta rako su kopar gida, Ranar Friday da safe gaba d'aya Haisam da
Fanan da Hajiya suka tafi Daura suka zaga dangi Fanan ta gaisa da su sai washe gari da yamma suka baro
daurar suka biya Ajiwa Dam sosae wurin ya burge Fanan Hajiya ma taji dad'in zuwa wurin Fanan tay
masu hotuna ba kamar ita da Haisam sai bayan Magrib suka dawo ta gaji sosae shiyasa bata je gidansu
Fatuu ba sai Washe gari lahadi bayan sun gama breakfast ta shirya ta nufi gidan Harda tsarabar Daura,
lokacin data je Fatuu bata nan tana islamiyya hira suka d'anyi da gwaggo tay mata godiyar tsaraba,
Fanan d'in tace in ta dawo ace mata tana nemanta gwaggo tace zata fad'i mata da ta dawo, bayan Fatun
ta dawo ta canja kaya gwaggo ta kirata ta sanar da ita sak'on Fanan na tana son ganinta har saida ta
d'anyi jimm don rabonta da gidan Hajiya tun wanccan satin haka haisam ma rabon data sanya shi a
idanunta tunda suka je gidan Abbas sosae take guje ma ganinshi ba kuma don bata son ganinshin ba,
bayan taci Abinci tayi sallar Azahar Gwaggo tace mata taje kar Fanan d'in taita jiranta ba yadda ta iya
dole tace to bayan ta fito zata tafi ne ta kirata ta bata wata leda dake k'ulle tace ta kai mata, tunda ta
tunkari gidan kirjinta ke bugawa hakanan ta daure ta k'arasa har Officer nace mata kwana biyu dama
tana gari ta amsa mashi da eh kawae ta shige, da zata wuce har saida ta kalli Corridor d'in shiga part d'in
Haisam ta d'an girgiza kai tunowa da baya yanzu shi kanshi mai part d'in ma gudunshi take rayuwa
kenan, lokacin data shiga Falon Hajiya gaba d'aya suna zaune harda shi Haisam d'in kamar ko yaushe dai
Fanan na manne dashi jikinta sanye da rigar shan iska wadda iyakarta guiwa santala santalan k'afafunta
dake jajur a waje kanta a bud'e tayi parking gashinta a tsakiya yayinda daga k'asa wani ke zube, shima
Haisam riga armless ce ajikinshi da wando 3 quarter, tana yin sallama duk suka juya suka kalleta Fanan ta
mik'e zaune tana mik'a mata hannu tana mata murmushi nufarta tay tana zuwa ta kama hannunta ta
zaunar da ita gefenta, gaida Hajiya dake kallonta tay tace "Oh Fateema k'iri k'iri dae kinyi mana yaji ko?"
d'an guntun Murmushi tay a sanyaye tace "a'a Hajiya na koma islamiyya ne da safe kuma dana yi ayyuka
na gama sai lokaci ya k'ure" da k'yar ta k'arasa Maganar saboda fargaba, Hajiyar tace "ai lokaci kam na
gudu wllh Allah ubangiji yasa mudace" ita da Fanan suka amsa da Amin, d'an juyawa tay ta kalli Haisam
da idonshi na akan tv ta gaidashi shiru bai amsa ba saida Fanan tace mashi Zarah na gaidashi sannan ya
d'an kalleta ya amsa kafin ya mayar da idon ta lura da yadda ya amsa mata duk sai taji dama bata zo ba
kaman ma ta mik'e ta tafi hakanan dae ta daure dama ita yarinya ce mai tsananin k'arfin hali ba k'aramin
abu ne kesata raunin zuciya ba, mik'a ma Fanan sak'on gwaggo tay ta amsa da farinciki tun kafin ma taga
miye aciki lokacin data bud'e kayan Fulani ne Navy blue riga da zani da kallabi harda mayafi sai
abubuwan ado su sark'a yan hannu harda na sawa a kai,kayan sun yi kyau sosae da ganinsu masu ingaci
ne ba tagajan tagajan ba, su kansu kayan sun sak'u sosae musamman gwaggo ta kira kawu shi6ado ta
fad'a mashi tana son kayan shi kuma yaba wani abokinshi sautu ya aiko mashi dasu jiya kawun ya bada
sak'on Mota aka kawo ma gwaggon, wata k'arar farinciki Fanan tay ta mik'e tana nuna masu abunda aka
aiko matan hajiya na dariya ta shiga yabawa cike da zumud'i ta sungumi ledar kayan tace bari taje ta
gwado Hajiya ma ta mik'e tana Fad'in bari ta biyota tana son shiga toilet, ya rage daga ita sai shi a falon
kowa yayi tsit gashi duk ta sha jinin jikinta kasancewar akan kujera d'aya suke, a hankali ta d'an juyo zata
saci kallonshi karaf suka had'a ido dashi da alama dama kallonta yake, idasa d'agowa tay tana kallonshi
tana motsa baki kaman zata ce wani abu sai kyakkyafta ido take still idonshi na akanta yana mata wani
kallo ko kyaftawa baiyi hakan yasa duk ta dabarbarce ta fara yamutsa fuska kaman zata yi kuka kawae
sai gani tay yay dariya har fararen hakoransa suka bayyana ya dan ta6e baki ya maida idonshi kan tv ita
kuma ta sadda kanta k'asa ji take kaman ta rusa ihu, fitowa Fanan tay cikin kayan Tubarkallah ma sha
Allah fad'in kyaun da tay 6ata lokaci ne Hajiya ta taimaka mata tasa komae tay kyau Over harda takalma
masu tsini ta sawo ta tunkari Haisam tana cat walk idonshi akanta yana Murmushi Fatuu ma idonta na
akanta tana kallonta da d'an Murmushi, tana isowa gaban Haisam ta wani jujjuya tana fari da ido tace
"how do i look babe?" dage gira yay slowly yace "like a bride" dariya tasa tace "yeah it's true am ur
bride" tana yin Maganar ta fad'a jikinshi tana dariya shima dariyar yake ta d'auki wayarshi ta fara yi
masu selfie duk wannan abun idon Fatuu na akan tv tun sadda ta fad'a mashi ji tay bazata iya cigaba da
zama ba tana niyyar mik'ewa Fanan ta nufota da wayar ta zauna gefenta ta d'aga alamar itama hoton
zatayi da ita, ba yadda Fatuu ta iya dole ta tsaya ganin bata murmushi fanan tace "Smile Zarah" dole
haka ta daure ta rink'a yin murmushin yak'e ta rink'a d'aukarsu, can Fatun tace mata tafiya zatayi lokacin
islamiyya ya kusa dama gwaggo ce tace tana nemanta tace eh ta mik'e hannunta cikin na Fatun ta jata
d'akin Hajiya bayan taba Haisam wayarshi, lokacin da suka shiga Hajiya na kwance akan gado Fanan ta
nuna mata stool tace ta zauna, kit d'in kayan gyaran gashinta ta d'aukko ta aje a gaban Fatun ta d'aukko
wata babbar leda itama ta aje a gabanta tace gasu nan tana tunanin kayan ciki zasu yi mata tayi amfani
dasu ta janyo k'aton trolley d'inta ta bud'e tace ta k'ara dubawa in akwae abunda take so karta ji komae
ta d'aukka, gaba d'aya Fatuu ji tay ta rasa mik'e mata dad'i kawae sai ta fashe mata da kuka, (Allah sarki
Fanan baki san Fatuu ba wannan take bukata a wurinki ba), Sosae Fanan ta rud'e ta hau lallashinta tana
cewa tayi shiru ai ba abun kuka bane Hajiya dake kwance ma tace mata tayi shiru ai ba wani abu bane
tunda ita ta bata, da kyar ta daina kukan fatun tace mata ba abunda take so suma wanda ta d'aukkar
matan ta barsu Fanan d'in tace a'a ai ita ta bata, ba yadda ta iya dole ta d'auki kayan harda kit d'in tay
mata godiya harda Hajiya, tare suka fito ta rik'e mata kit d'in har lokacin Haisam na zaune Fanan tace
mashi zata je ta dawo ya d'aga mata kai kawae, akan hanyarsu Fanan d'in ke ce mata zatai missing d'inta
sosae amman dae ai zata zo bikinsu ko fatun ta d'aga mata kai kawae,lokacin da suka isa gidan gwaggo
ta ga abubuwan data ba Fatun sosae tay mata godiya had'i da Addu'oi tay fatan Allah ya nuna masu
Aurensu lafiya, bayan wani lokaci tay mata sallama gwaggon tace zata shigo su k'ara yin sallama da
daddare, bayan sallan isha gwaggo taja Fatuu ba don taso ba suka je gidan, Washe gari da Safe misalin
karfe takwas da wasu mintuna Fanan ta rafka sallama tana sanye da skinny jeans da riga long sleeve ta
d'an saukko mata kanta ta yafa mayafi ta fito a Baturiyarta, fitowa gwaggo tay daga cikin Kitchen tana
ganinta ta nufeta tana fadin "y'ata har an fito" tace mata eh zasu tafi, gwaggo tace "to Allah ubangiji ya
tsare, mungode, mungode Allah ya k'arawa rayuwa Albarka yasa ki gama da iyayenki lafiya, ki gaida
mana da yan gidan sai munzo biki in sha Allah" d'an side hug tay ma gwaggon tana Murmushi tace "nima
nagode da kulawa granny" suna cikin haka Fatuu ta fito jikinta sanye da doguwar riga kanta ba kallabi
duk maganganun da suke tana ji kasa jurewa tay ta fito Fanan na ganinta ta saki gwaggo ta bud'a mata
hannuwa, nufarsu tay tana zuwa ta fad'a jikinta idanuwanta sun cicciko da kwalla har sun fara zubowa,
d'agota fanan tay ta shiga share mata tana Fad'in ta daina kuka ai zasu ci gaba da communicating kaman
da, horn d'in da akai a waje yasa ta saki Fatun tace babe na jiranta tare zasu tafi ta juya suka rakota
bakin kopa anan suka tsaya don ita Fatuu bata da kallabi ita kuma gwaggo ba mayafi, bud'e kopar Motar
Haisam yay shima yayi gayun k'ananan kaya ya gaida gwaggo tay mashi Allah ya tsare ita kuwa Fatuu
kasa ce mashi komae tay ta bishi da ido har ya koma Fanan na d'aga masu hannu suma suna d'aga mata
ta bud'e gaban Motar ta shige yaja suka tafi, wani irin sanyi jikin Fatuu yay gwaggo ma har ta fara jin
kewarta, juyawa sukai suka koma cikin gidan.......

Wacece Fanan? Ya akai suka fara Soyayya da Haisam?

*ASM Bk2007*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


.....Fanan jikar Hajiyace wato d'iyar Hajiya Maryam ta lagos kuma itace babbar diyarta, acan baya lokacin
da mijin Hajiya wato General Adamu zakee yay ritaya a Lagos suka fara zama acan ne kuma ita Hajiya
Maryam ta had'u da mijinta Wato Dr Mohammed Abraham wanda babban likita ne da ya kware a
aikinshi lokacin tana karatu a Jami'ar Lagos, shi kuma Senator Alee yana Katsina yana kula da harkokin
kasuwancinsu, tun lokacin da aka haifi Haisam Hajiya ta kwallafa rai akanshi k'arshe dae har tay nasarar
rabasu dashi duk da suma suna matuk'ar kaunarshi don yaro ne mai tsananin farin jini ga kyau da Allah
ya yi mashi duk wanda ya kalleshi sai ya tanka hakan yasa kullum cikin yi mashi Addu'oi suke, sosae
Senator Alee ya rarrashi matarshi Fateema ya nuna mata Mahaifiyarshi ce bazata ta6a cuta mashi ba
kuma tunda Allah yasa tana haihuwar ko shekara mai zuwa sai ta k'ara haiho wani d'an ba matsala bane,
da k'yar ya shawo kanta ta hak'ura yana shekara hud'u aka ba Hajiya shi ta saka shi a Makaranta, gatan
duniya Hajiya tayi ma Haisam saidae bata bashi gatan da zai sangarce ba duk da dama shi ba mai suffar
sangartattun bane a tsayenshi yake tun yana yaro gashi ko dariya bai cika yi ba in kaga dariyarshi to
wanda ya sani ne sosae, yana shekara bakwae lokacin yana primary 1 don saida yay nurserys Hajiya
Maryam ta haifi d'iyarta ta fari wato Fanan itama dae Tubarkallah badae kyau ba don jinin Mahaifinta ta
biyo harma ta fi shi kyau sosae, Fanan irin rigimammun yaran nan ne ga kukan banza da wofi abu kad'an
ta 6are baki gashi kuma bata son bak'in mutum hakan yasa bata cika sakin jiki da mahaifiyarta ba ko
yaushe tana manne da Mahaifinta shi kuma gashi ba mazaunin gida bane sosae saboda yanayin aikinsa
yana aiki a asibitin gwamnati kuma yana da babban private Hospital hakan yasa kullum cikin yi mashi
rigima take gashi tayi k'ank'anta bare yace ya tafi da ita koma ya tafi da ita baida lokacin kulawa da ita
saidae in barin aikin zaiyi, hakan yasa in ya barta gida tay ta yi ma Hajiya Maryam rigima data yi mata
fad'a kuma ta idasa rikice mata, duk wannan abun Mutum d'aya ne ke controlling d'inta wato Haisam
duk da shima lokacin yaro ne,duk rigimar da take da sunzo gidan tay arba dashi baka k'ara jin kukanta
tana sonshi taita shishshige mashi gashi shi ba son yara yake ba wani lokacin sai Hajiya tay mashi
Magana yake d'an sakar mata fuska har ya d'auketa kowa yasan tana shakkar Haisam hakan yasa Hajiya
Maryam watarana taje gidan Hajiya ta rok'eta ta bari Haisam ya dawo gidansu, fir ta k'i amincewa tace
itama ai don tana son zama dashi ta rabo shi da iyayenshi, wai ance tsakanin d'a da Mahaifi sai Allah
K'arshe dae saida Hajiya Maryam tay nasarar raba Hajiya da Haisam da sharad'in duk Weekend nan
wurinta zaiyi shi tace su duka ma zasu rink'a zuwa,sosae suka samu sauk'in rikicin Fanan bayan dawowar
Haisam gidan duk in zaije Makaranta sai yabar sak'on in tayi rigima daya dawo a fad'a mashi aikuwa har
ya dawo bata yin rigimar data yi niyyar farawa Hajiya Maryam zata ce daya dawo sai ta fad'a mashi sai
tace ta bari, a lokacin komae na Fanan ya dawo kan Haisam shine yi mata wanka bata Abinci data ga yayi
fushi duk sai ta rud'e ta fara bashi hakuri har sai yace mata yayi sannan zata warware da yake lokacin
girmanta yafi shekarunta tana da wayo sosae ga baki, Haisam na primary 3 lokacin shekararshi tara da
wani abu ita kuma Fanan ta kusa shekara ukku aka ba mijin Hajiya wato Adamu zakee Ministan tsaro
bayan wani lokaci suka shirya komawa Abuja dama ba wani son zama Lagos d'in yake ba yafi son ya
koma gida Arewa, Hajiya Maryam ta nuna abar Haisam nan ya k'arasa karatunshi Hajiya kuwa tace bai
yuwuwa ai iyayenshi ma sai suce wani abu don haka k'afarta k'afarshi aikuwa Fanan ta sa rikicin sai ta bi
bro haka take kiranshi sam Hajiya Maryam bata son d'iyarta tai mata nisa saida Dr Mohammed ya nuna
mata ta barta su tafi da ita kawae in ba haka ba wani sabon rikicin ne tunda ta saba dashi in ta k'ara
wayo sai ta dawo kuma in d'a take so zata iya daina planning d'in da take sai ta haihu dama so take sai
Fanan d'in tayi wayo sannan ta k'ara haihuwa, ba yarda ta iya dole ta hak'ura aka tafi da ita Abuja aka
saka su Makaranta tare da Haisam sam bata son zama class d'insu kullum tana zarya class d'insu Haisam
sai ya kamata ya maidata, da yan class d'insu sun ganta tazo sai suce Zakee ga d'iyarka nan aita dariya
shidae sai dae yay d'an Murmushi kawae, har lokacin shi ke mata wanka da sun koma gida ya bata Abinci
kullum tana lik'e dashi tun yana jin ya takura harma ya saba, bayan tafiyarta da shekara d'aya Hajiya
Maryam ta haifi Farha shima Haisam lokacin Mahaifiyarshi ta k'ara haihuwar yara biyu Laila da Nameer,
Haisam na Junior Secondary Mijin Hajiya wato Gen Adamu zakee yay Accident ya rasu lokacin ba
k'aramin tashin hankali iyalin suka shiga ba lokacin Fanan na primary 4, rasuwar mijin Hajiya yasa ta kasa
cigaba da zama a Abuja ta yanke dawowa Katsina lokacin kuma Hajiya Maryam ta buk'aci Fanan ta dawo
gida da taso ta turje aikuwa ta bude mata wuta dole ta koma Lagos shi kuma suka dawo Katsina yaci
gaba da yin Senior Secondary lokacin kuma Mahaifinshi ya zama Senator, bayan ya gama secondary ya
tafi kasar waje yin degree d'inshi na farko,akwae wani zuwa da yay Lagos lokacin yazo k'asar Fanan na
Secondary skul tana ganinshi ta rungumeshi cike da farinciki suka ci Abinci tare da daddare bayan sun
gama fira zai je ya kwanta tace mashi wai yayi mata wanka kaman yadda yake mata da d'an murmushi
yay mata yace mata ai ta girma yanzu bai kamata yay mata wanka ba tace amman ai shi yayanta ne ba
wani abu bane ganin ta turje kan hakan yasa ya zaunar da ita ya fahimtar da ita game da tsakaninsu na
shi yayanta ne amman ba muharraminta bane kuma koda ma shi muharraminta ne yanzu takai wani
mataki da bazai mata wanka ba tunda shi Namiji ne ganin ta zuba mashi ido yasa ya tambayeta ko bata
san miye muharrami ba tace ta sani wanda bazai iya auren Mutum ba yace mata hakane, da bud'ar
bakinta sai cewa tay yanzu shi zai iya aurenta kenan yana d'an Murmushi yace mata eh ai shi cousin
d'inta ne ba ta sani ba tace eh ta sani,Washe gari bayan sun gama breakfast da yake Weekend ne taje
part d'in da ya sauka ta iske shi yana kallo ta zauna kusa dashi itama tana kallon American film d'in da
yake kallo, can aka nuno jarumin film din ya duk'a kan knee d'inshi yana rok'on jarumar zata aure shi ya
mik'a mata zobe can ta amsa mashi da Yes ta mik'a mashi yatsanta yasa mata zoben ya mik'e suka
rungume juna, juyawa Fanan tay ta kalli Haisam da idonshi ke kan tv ba zato ba tsammani kawae ta
duk'a a gabanshi ya maido idonshi kanta yana kallon abunda tay murya kaman zatai kuka tace "Ya
Haisam will u marry me pls?" dan bud'a mata ido yay alamar mamaki sai kuma yay Murmushi kawae
ganin haka yasa ta fara yamutsa fuska kaman zatayi kuka tace mashi"plss answer me,will u marry me?"
d'an lumshe ido yay ya jinjina kanshi, wata k'arar murna tasa ta fita daga falon da gudu ya bita da ido
kafin ya maido kan tv yaci gaba da kallonshi, wurin Mommynta ta nufa lokacin tana d'akin Dad d'insu
saida tay masu sallama sannan tasa kai tana ta dariya ganin haka yasa Hajiya Maryam tambayarta lafiya
cike da farinciki tace Ya Haisam ne yace zai aureta yanzun nan, gaba d'aya suka bud'a idanu kafin sukai
dariya suka ce suna tayata murna ta dace miji ta juya da gudu tana dariya, bayan fitarta Hajiya Maryam
ta kira Hajiya ta sanar mata sosae tay farinciki tace ita dama tasan wannan shak'uwar inda zata kaisu
kenan, tun daga wannan ranar Fanan ta koma yima Haisam kallon wanda zata aura, Bayan ya gama
degree ya dawo Abuja ya fara aiki ita kuma Fanan ta gama Secondary tace ma Mommynta taji ana
Maganar tafiyarta karatu ita dae aure take so tunda tana da wanda zata aura in sunyi auren tayi karatun,
jin wannan Maganar yasa Hajiya Maryam ta kira Hajiya ta sanar mata game da zancen Fanan d'in ita
kuma ta kira Mahaifinshi Senator Alee, Lokacin da ya kira Haisam d'in yay mashi Maganar auren da
mamaki yace ai shi wannan lokacin wasa ne yake mata don baiyi tunanin da gaske take ba ganin ita
yarinya ce kuma ya za'ai ai mata aure ma yanzu tayi k'arama, Senator yace yanzu dae bazai aureta ba
kenan yace shidae yana mata son yan'uwantaka ne amman bana aure ba,sosae ya fahimceshi ya kira
Hajiya ya gaya mata duk da bata ji dad'i ba amman tasan bazasu yi mashi dole ba lokacin ta kira Hajiya
Maryam don ta sanar mata duk suna zaune a parlor bayan sun gaisa ne ta fara mata bayanin abunda
Haisam yace sam Hajiya Maryam ta manta ma tana tare dasu Fanan d'in take wayar saida taji su Farha
sun saka k'ara suna fad'in Sis Fanan ta fad'i sannan ta kai idonta kan Fanan dake baje k'asa kan carpet
ashe tana jin abunda suke magana ta mik'e shine ta yanke jiki ta sume wata zabura Hajiya Maryam tay ta
cillar da wayar tay kan Fanan, Hajiya nata hello hello sai Abraham ne mai sunan kakansu ya d'auka ta
tambayeshi miya faru yace sis Fanan ce ta sume data ji suna waya da Mommy d'insu, rushing dinta sukai
Hospital din Dad d'insu anan yasan abunda ke faruwa suka shiga bata agajin gaggawa koda ta farfad'o ta
ganta a Asibiti ga iyayenta akanta sai ta fashe masu da matsanancin kuka tana Fad'in"Ya Haisam will not
marry me why, why mom, Dad why? Am i ugly?....." haka ta dingi sambatu Hajiya Maryam harda kuka sai
lokacin ta amshi wayarta ta kira Hajiya dama tana ta kira ba'a d'agawa cikin muryar kuka take sanar da
ita halin da Fanan take ciki tace tana tunanin ta samu heartbreak ne gashi dama raunannar zuciya
gareta, Hajiya na jin hakan washe gari sai Abuja ta zauna da Haisam da iyayenshi tace mashi miye aibun
Fanan da bazai aureta ba ko yana da wadda yake so ne yace mata a'a shidae kawae bai mata son aure,
tace to yayi hak'uri tunda ita tana sonshi ya daure ya aureta ko don a ceci rayuwarta kar a rasata saboda
abunda bai fi k'arfin suyi mata ba yace shikenan zai aureta amman ba yanzu ba sai ya gama Masters
degree d'inshi da zai tafi bada jimawa ba Hajiya tace wannan ai ba matsala bane tunda dae ya amince
itama sai ta fara karatunta duk in suka gama sai ayi bikin in Allah ya kaimu,Washe gari Hajiya da Haisam
harda Senator suka tafi Lagos duba Fanan d'in har lokacin tana cikin mawuyacin hali a Asibiti sai faman
koke koke take, koda suka ganta gaba d'aya ta basu tausayi ba kaman Haisam da shi Mutum ne mai
tsananin tausayi hakanne ma yasa ya amince da auren nata ba tare da an kai ruwa rana ba, gaishe da ita
sukae sukai ma iyayenta ya mai jiki cike da zolaya Hajiya tace "ashe mu Laila muka haifa ba Fanan ba to
ai sai ki share hawayenki ga Majnun d'in nan na kawo maki" duk aka d'anyi Murmushi daga baya d'akin
ya rage daga ita sai Haisam dake tsaye ya goya hannuwanshi a chest d'inshi ita kuma sai kallonshi take
tana sheshsheka, can ya nufi gadon da take kwance ya zauna kan kujera tana ta6e baki tace mashi "Ya
Haisam u don't luv me, u will not marry me why?" fuskarshi a sake yakai hannu ya kamo hannunta ya
d'an matse shi Calmly yace "How can i reject a precious gift of a beautiful young lady like u" waro ido tay
da sauri tace "u accepted me to be ur wife?" lumshe mata ido yay nan take ta gane mi yake nufi ta tashi
da sauri sai kace ba mai jinya ba tanata mashi dariya tana rufe bakinta shima Murmushi yake mata, can
kuma sai yaga ta daina dariyar ta kwa6e fuska idanunta sun ciko da kwalla da sauri ya tambayi miya faru
kaman zatai kuka tace mashi tasan tausayinta ne yasa yay accepting aurenta ba don yana sonta ba tunda
da yace bazai aureta ba, mik'ewa yay ya koma gefen gadon ya k'ara kama hannunta yace mata yana
sonta sosae shiyasa ma ya yarda zai aureta kawai lokacin da sukai Maganar da farko ya d'auka tana wasa
ne amman yanzu tunda ya tabbatar tana sonshi da aure shima yaji yana sonta sosae, jin haka yasa ta
fad'a jikinshi tana dariyar farinciki, a takaice dae tun daga Wannan ranar yasa zuciyarshi ta amince da ita
matsayin wadda zai aura dama shi ba Soyayya yake ba duk da akwae mata da yawa dake mashi tayin
Soyayya anan gida Nigeria har ma da k'asar waje inda yay karatu, saida Haisam yay da gaske sannan
Fanan ta rage had'a jikinta da nashi don ta riga ta saba wata irin zazzafar soyayya take mashi, lokacin da
akai Maganar tafiyarta karatu k'asar india cewa tay Haisam zata bi inda zaije yin Masters degree tay
karatun acan Dad d'inta ya nuna yafi son taje k'asar India don shima acan yay karatunshi kuma akwae
dan'uwanshi shima likita ne acan zai taimaka mata sosae,Lokacin data kira Haisam ta gaya mashi ce
mata yay karta damu taje can d'in tace ai ita tsoro take ji yaje can shi kadae wata ta k'wace mata shi har
saida yay yar dariya dama yasan kishi ne yasa take son binshi hakan yasa ya tabbatar mata da they're
meant for each other karta damu wannan dalilin ne yasa ta tafi k'asar India karatu, da anso ay auransu
bayan ya gama karatun Dad d'inta ya nuna a bari ta gama karatun tunda Haisam d'in zai koma aiki Us ne
sai su tafi tare akwae Asibitin da zai sama mata aiki acan itama tayi, lokacin ne kuma Senator ya nuna sai
ya fara aiki anan kafin ya koma US d'in shine ya dawo wurin Sweetheart d'inshi K Hajiya, Wannan kenan
game da Soyayyar Haisam da Fanan.............

*ASM Bk2008*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

........Satin da Fanan ta tafi su Fatuu suka koma Makaranta sun cigaba da zuwa ita da Haulat har lokacin
tana cikin yanayin damuwa ga zuciyarta tay ta raya mata Ya Handsome na can suna shan soyayyarsu da
Fanan, Haulat na lura da yanayinta hakan yasa bata gajiya da bata hakuri da kuma k'arfafa mata guiwar
ta cireshi daga ranta, zubar da hawaye ya zamar mata jiki Fatuu mai zafi ta dawo Fatuu mai sanyi kowa
ya lura da canjawar da tayi yan Class d'insu da Malamai suna ta tambayarta game da hakan saidae tace
masu kawae bata lafiya ne, haka Haulat ma duk wanda ya tambayeta sai tace bata lafiya matsalar
Aljanunta ne da yake dama ansan tana dasu ba kamar wadanda sukai junior tare, ko sauran juniors ma
na section d'insu sun san SP d'insu tayi sanyi, a satin sau d'aya taje gidan Hajiya ranar Juma'a ta gaishe
da ita sanin Haisam bai nan, suna d'an yin fira a Falon Hajiya ke cewa "wai ni kam Fateema ko har yanzu
jikinne duk kinyi sanyi ba kaman da ba" saida gabanta ya fad'i jin haka cikin rawar murya tace mata
jikinne bai mata dad'i kaman ba nata ba, hajiya tace "Allah ya baki lpy ya rabaki da ciwon gaba d'aya ki
huta in sha Allahu zaki samu lpy ki dawo kaman yadda kike amman kasancewarki haka ba dad'i mutum
mai kazar kazar duk kin dawo sukuku" d'an Murmushi tay batace komae ba dai, bayan wani lokaci tay
mata sallama ta tafi, sam Hajiya bata kawo komae game da halin da Fatuu take ciki ba sanin tana da
Aljanun da gaske sannan lokacin da suka dawo daga Ajiwa ba wanda yay tunanin Fatun taga Fanan kafin
ta shiga gida don koda Hajiya ta tambayi Fanan sun ga juna ce mata tay a'a ta shiga gida kuma bayan
sunje sun dawo suka ce sun iske bata lafiya. Ranar Monday lokacin Satin Fanan d'aya da tafiya misalin
karfe bakwae da rabi Fatuu ta fito jikinta sanye da Uniform d'in boko sun sha guga bayanta goye da
k'atuwar School bag d'inta tsaf tsaf da ita tana shirin hawa hanya ta tafi galleliyar Mota dark ash ta tsaya
a gabanta har saida ta dawo baya da sauri, bin Motar tay da kallo lokaci guda k'irjinta ya fara bugu da
k'arfi da k'arfi don ko ba'a fad'a ba tasan waye a ciki, Slowly glass d'in kopar ya fara sauka k'asa nan take
tay arba da haisam cikin shirin zuwa aiki idonshi na a gaban Motar bai kalleta ba shiru tay tana bin gefen
fuskarshi da gashi ke kwance luff da kallo can ya juyo a hankali ya kalleta suka had'a ido, bin shi tay da
ido kawae shima kuma haka ganin kallon da yake mata ne yasa a sanyaye tace "Ina kwana" jinjina mata
kai yay ta sake cewa "an dawo lpy?" fuska a sake yace mata lafiya, kallon juna suka ci gaba da yi ganin
bata iya jure ma kallon nashi yasa ta sunkuyar da idonta k'asa can taji yace "in rok'e kine ki shigo?" d'an
d'agowa tay tai mashi wani kallon k'asan ido acikin zuciyarta ta ayyana sai kace ni na kirashi ni dama ka
tafi....."

"Baki kirani ba ko" bata k'arasa ba taji ya fad'i haka, a firgice ta idasa d'agowa ta zaro ido cike da
Al'ajabi jin abunda yace sai kace mai jin zancen zuci duk tay kalar rashin gaskia ta girgiza mashi kai
alamar a'a kafin ta maida kan k'asa,

"Zaraah" yarrr taji wani abu ya tsarga mata tun daga kan babban yatsanta har zuwa cikin kanta, kasa
d'agowa tay ta kalleshi don komae zai iya faruwa a wannan lokacin inta had'a ido dashi,

"Ki shiga Mota kina sani ina late in kuma baki son shiga ne let me know sai in tafi" a hankali ta daure ta
d'ago ta d'an kalleshi kafin ta kawar da idon da sauri ta nufi other side d'in Motar ta bud'e ta shiga,tana
shiga ta juyar da kanta tana kallon gefe duk yana kallonta ta Mirror bai dai tanka ta ba yaja Motar suka
tafi, daidai lungun gidansu Haulat ya tsaya ta bud'e Motar ta fita ya bita da kallo,lokacin data shiga
d'akinsu Haulatun tana kallon fuskarta ta tambayeta lafiya kaman zatai kuka tace "Ya Handsome ne..."
sai kuma tay shiru, a d'an rud'e Haulat tace "miya faru dashi?" hannu tasa tana share kwallan da suka
gangaro mata kafin tace "ya dawo yanzun nan ya ganni a kopar gida ya d'aukko ni yana waje" a k'agare
tace "to wani abu ya faru ne" girgiza mata kai tay tace "ni banson ganinshi ne haulatu zafi kirjinta ke yi
inji kaman in fad'a mashi halin da nike ciki" dafata Haulat tay ta shiga bata hakuri tana karfafa mata
guiwa, koda suka fito kafin su isa wurin Motar cigaba da lallashinta haulat tay akan ta daure karta fad'i
mashi don ba abunda zai mata saidai ya bata hakuri gwara tay hakuri komae zai wuce ita dai kai kawae
ta daga mata, bayan sun shiga Motar gaidashi Haulat tay ya amsa mata yana k'ok'arin jan Motar bayan
yaja sun fara tafiya tace "Ya haisam ya Aunty Fanan?" fuska a sake cikin cool voice d'inshi yace "ta koma
skul tace a gaidaku" da yar fara'a tace "muna amsawa" a hankali ya d'an juya side d'in Fatuu suka had'a
ido duk ta kame kanta da sauri ta juyar da kanta gefe ita kanta tasan bata kyauta ba da bata tambayi
Fanan ba, yana aje su a Makarantar ta d'an juya tace mashi an gode ba tare data jira amsawarshi ba ta
bud'e kopar tay ficewarta lokacin Haulat bata k'arasa fita ba Haisam ya kira sunanta ta tsaya kud'i ya
mik'a mata tasa hannu biyu ta amsa tay mashi godiya ya jinjina mata kai, bayan ta idasa fita yaja Motar
ya tafi, akan hanyarsu ta zuwa Class ne Haulat ke k'ara lallashinta akan ta daure ta cije taci gaba da yi ma
Ya Haisam kaman da duk da tasan abu ne mai wuya amman dai ta rink'a d'an kamantawa gudun kada shi
kuma yaga kaman ta rainashi tana wulak'antaci tunda ba haka suka saba ba, idanunta cike tabb da
kwalla tace ma Haulat "baki san ya nike ji bane Haulat wllh shiga Motar ma ba k'aramin daurewa nay ba
ji nake kaman in rusa ihu saboda takaici inna tuna na rasa shi, auranshi zay da wata...." bata k'arasa ba
tasa kuka haulat ta shiga lallashinta tana Fad'in ta Fahimceta, haka Haisam ya cigaba da kaisu
Makarantar duk da Fatuu taso ta rink'a zillewa Haulat ta nuna mata bai dace ba tunda shi ya saba kai su
tsawon shekaru ba tare daya nuna gajiyawa ba bai kamata suyi mashi haka ba,dole ta Hakuri ita kanta
wani abun ba don tana so ba take mashi don Haisam yafi karfin wulak'antawa a wurinta ita ba butulu
bace tasan Haisam shi ya mayar da ita cikakkar Mutum, akwae watarana bayan ya aje su a Makarantar
har Fatuu zata bud'e Motar ta fita yace ta tsaya jin hakan yasa Haulat ta bud'e kopar ta fita bayan tay
mashi godiya kaman ko yaushe, shiru sukae shi yana kallonta ita kuma ta sunnar da kai can taji yace
"Zaraah" amsa mashi tay ba tare data kalleshi ba yaci gaba "har yanzu baki lpy ne?" shiru tay tana d'an
mommotsa baki har saida yace ba magana yake mata bane sannan tace mashi ta samu sauki yace "then
why are u acting strangely?" shiru ta d'an yi sai kuma tace "kawae jikina ne banjin dad'inshi har yanzu"
jin baice komae yasa ta kalleshi suka had'a Ido kasa janye idon tay can yace "kina bukatar zuwa
hospital?" da sauri ta girgiza kai tace tana shan magani, gyad'a kai yay yace taje da sauri ta bud'e Motar
ta fita yaja ya tafi, bayan taje wurin Haulat sun nufi ajine jin tayi shiru yasa Haulat tambayarta lpy dae ko
kaman bazata ce komae ba sai kuma ta fad'i mata abunda ya tambayeta tace ta kyauta da bata fad'i
mashi ba amman ta daure ta d'an rink'a sakewa kar watarana a samu matsala tace mata to kawae, tun
daga wannan ranar Haisam bai k'ara tambayarta ba game da canzawar da tayi sannan shi bai canza mata
ba daga abubuwan daya saba yi mata.

Bayan Wata Biyu,

Lanar lahadi da rana Fatuu ta dawo daga islamiyya lokacin gwaggo bata nan aikin rana take amman da
wuri ta tafi saboda zata biya wata unguwa, d'akinta ta shiga ta aje jakarta wurin da take ajewa ta nufi
gado ta cire hijab d'inta ta aje tana niyyar juyawa ta nufi Kitchen don ta zubo abinci idonta ya sauka kan
wani abu dake sakin k'yalk'yali a gefen hijab d'inta da ta d'aura saman gadon, tsayawa tay idonta akan
abun ta koma gaban gadon sai lokacin ta lura da envelope ce, a hankali ta kai hannu ta d'aukko tana
k'are mata kallo ba k'aramin had'uwa tay ba sai walwali ke tashi gwanin burgewa kaman zata bud'e sai
kuma ta juya bayanta idonta ya sauka akan wani rubutu dake daga can gefe guda shima yana ta sakin
kyalli anyi shi da italic style, k'ura ido tay tana karantawa kamar haka _HAIFAN 2023_ kasa gane abunda
yake nufi tay tanata k'ara maimaitawa can dae ta bud'e cikin envelope d'in ta fiddo da wata takardar mai
kyau da salk'i dake linke ta warwareta ta fara karanta abunda ke jiki wanda katin gayyatar daurin Aure
ne na Families d'in Sen. Alee Adamu Zakee da kuma Dr. Mohammad Abraham da za'a yi ma y'ay'ansu
wato _ENGR. HAISAM ALEE ADAMU ZAKEE & DR.FANAN MOHAMMED ABRAHAM_ wanda za'ayi a
karshen watan da ake ciki wato nan da sati ukku masu zuwa kenan don satin farko ake za'a shiga na biyu,
a Central Mosque dake Abuja,mutuwar tsaye tay bayan ta gama karantawa ta sake maimaitawa har
saida ta tabbatar ma kanta lalle Ya Handsome ne nan da nan hannunta ya fara rawa cike da Al'ajabi tasa
tafin hannunta guda ta rufe bakinta, yanzu da gaske dae Ya Handsome aure zaiyi ya barta, wani irin kuka
cikinta ya fara yi da sauri ta wurga IV d'in kan gado ta nufi hanyar waje a dudduk'e take tafiyar saboda
k'ullewar da cikinta yay Allah dae ya taimaka ta k'arasa toilet d'in ba tare da abunda take ji ya zubo mata
ba,tsawon lokaci ta d'auka a ciki kafin ta fito a galabaice duk tayi sharkaf da ruwa data sakarwa kanta ta
nufi d'aki hannunta d'aya dafe da cikinta,tana shiga ta isa kan gado ta fad'a tana nishi da karfi da karfi,
wai ance in tashin hankali yay tsanani kuka kasa yinshi ake to hakan ce ta faru da Fatuu sam ta kasa yin
kuka sai zare idanu kawae take ga wata kerma da jikinta ke yi kaman wadda sanyi ya kama,duk da uwar
yunwar dake cinta ta kasa tashi taje ta zubo abincin don a halin da take ciki bata wani Abinci take bama
ko ta zubo ma ba iya ci zatai ba tana kwancen akai Azahar amman ta kasa mik'ewa taje tayi sallar sai bin
envelope d'in dake gabanta take da ido zuciyarta na wani irin bugu mara dad'i.

Bayan sallar La'asar Haisam na Masallaci Abbas ya kirashi yace gashi a part d'inshi yace mashi yana
zuwa,bada jimawa ba ya dawo ya zauna kan L-shape Abbas kuma ya zaune kan armchair, gaba d'ayansu
suka d'an kishingida kan kujerun da suke suka shiga tattaunawa kan bikin Haisam din Abbas yace "dazun
munyi Magana da Amaryar taka kan program d'in da tace ta fad'a maka zasu yi a can saboda friends
d'inta da bazasu samu zuwa Abuja d'in ba, wai Indian Night zasu yi, kenan kaga dole zamu je Lagos ni
harma na tanadi kayan indian da zansa irin masu burgujejen wandon nan ko kuma in d'aura dan zani
yadda suke" ya k'arasa yanata 6a66aka dariya haisam ma yar dariyar yay bai ce komae ba,Abbas yaci
gaba "Maganar Dinner party dinma mun gama Magana da Saleem dress code da komae sai jiran lokaci
kawae, ya kamata ma a k'ara program Dinner yayi kad'an gaskia bikin H,Zakee guda" d'age gira Haisam
yay yana mashi wani kallo can k'asa yace "for me is enough, ba zakuyi wani a Lagos ba" Abbas na dariya
yace "zamuyi dae ai kasan dae dole kaje,ko zamu je ba ango ne wannan kuma ai daban a Abuja nike
nufin Dinner kawae yay kad'an amman ko ka k'i ma su Laila suma sun shirya wasu programs d'in don
munyi Magana tace za'ai Arabian da wani can dae naku na Al'adan Ethiopia" dan ta6e baki yay kawae bai
ce mashi komae ba, gyara zama Abbas yay kafin yace "Wai nikam ina Mom Zarah ne, da ita ya kamata
ace muna preparation da tsare tsare don itama matsayin babbar k'awar Ango take" shiru haisam yaya
idonshi akan Tv kaman bai ji abunda Abbas d'in yace ba,

"Am asking u Zakee" sai lokacin ya kalleshi kaman bazaice komae sai kuma yace "nima ina nemanta" da
d'an mamaki Abbas yace "kaman ya kana nemanta bata nan ne?" "No tana nan but ta daina zuwa nan
kwata kwata" tashi Abbas yay zaune yace "to why ko kai mata wani abu ne?" d'an guntun Murmushin
gefen bakin yay kafin yace "in mata mi, she just changed completely" ya k'arasa Maganar yanayin
fuskarshi ya canja da gani ba jin dad'in hakan yake ba, Abbas yace "to amman ka ta6a tambayarta dalilin
canjawar ne?" shiru ya d'anyi kafin ya gyara zamanshi sosae yana kallon Abbas din yace "Yea,nayi hakan
i think 2 to 3 times but abu d'aya take bani shine bata jin dad'in jikinta as a result of wannan ciwon
Aljanu ne komi da tayi" wani guntun Murmushi Abbas yay kafin ya sake tambayarshi tun yaushe ta fara
ciwon Aljanun ne yay mashi bayani tun lokacin da suka dawo Outing Fanan tazo da yadda suka je da
daddare suka iske bata lpy har tay amai sosae aka tabbatar Malaria ke damunta bayan sun dawo gida
Fanan ta sanar ma Hajiya bata lpy anan suka ji tana da Aljanun, yana gama Maganar ya maida idonshi
kan tv shi kuma Abbas ya sauke nannauyar ajiyar zuciya idonshi akan Haisam sam baiyi mamakin rashin
fahimtar Haisam d'in kan abunda ke damun Fatuu ba don yasan shi ba wani sanin so yay ba sosae iya
soyayyar Fanan kadae ya sani bai tunanin daga kanta ya ta6a yin soyayya da wata, sigh yay on a serious
note yace "H,zakee Zarah has fell in love with u" Maganar Abbas ta daki dodon kunnan Haisam ba shiri
ya maido idonshi akan Abbas yana mashi wani kallo with suprise written boldly all over his face, ganin
kallon da yake mashi ne yasa Abbas d'in jinjina mashi kai cike da tabbatarwa yace "Yea am sure tana son
ka ne shiyasa ta canja maka haka don ta gane kana da wadda kake so" ido kawae Haisam ke binshi da shi
can kuma yay wani guntun Murmushi ya d'an girgiza kai kafin yace "pls Abbas don't start it,kai koda
yaushe Magananka d'aya ne soyayya mata,Zarah ne zaka ce wai sona take how possible,yarinyar da bata
da buri sai na tayi karatu ta zamo Doctor yaushe ta san wannan d'in" Abbas dake Murmushi yace "shine
kuma bazata iya canjawa ba, sanin da kai mata yanzu ta girma zata iya having feelings for man saboda
she's quite mature for her age" wani kallo haisam ke binshi dashi ya d'an ta6e baki jin Abbas yayi shiru
yasa yace "Zaraah is still immatured" da mamaki Abbas yace "amman miyasa zaka ce hakan ga abu a fili
kowa ya kalli Zarah yasan ta mallaki hankalinta ta zama cikakkiyar mace yanzu" shiru haisam yay yana
d'an Murmushi kafin yace "da sauranta don har yanzu bata fara menstruation ba" da wani kallan
expression mai nuna tsantsar mamaki Abbas yace "Zarah ce bata fara menses ba at her age? Kai ya akai
kasan hakan??" nan take Haisam ya fad'i mashi yadda suka ta6a yi da Fatun da Azumi yace "so in da ta
fara na tabbatar zata sanar dani" wani kallan Murmushi Abbas yay yace "H,Zakee Zarah zatai ta zama ne
bazata yi hankali ba,kar ka manta kana man Maganar abunda ya faru kusan 3 years back ai dole zata
k'ara hankali besides a shekarunta yanzu sun kai ace tana menstruating in kau har bata yi kaman yadda
kace to tabbas bata lafiya tana bukatar akaita asibiti ko kuma tana daga cikin matan da basu yi kwata
kwata wanda bana tunanin hakan ma gaskiya" shiru Haisam yay yanata kallonshi yayin da acikin
zuciyarshi yake nazarin Maganar tashi ta k'arshe yasan Abbas ba likita bane amman abunda yake koyawa
ya kunshi hakan wato biology,

"Kayi Nazari sosae H,zakee tsawon lokaci kana tare da Zaraah ace baka ta6a sanin tana da Aljanu ba sai
yanzu kuma basu tashi zuwa su sakar mata ciwo ba sai da Fanan tazo...." katseshi Haisam yay "amman
Hajiya ta tabbatar da haka",

"Eh dama ba ina nufin k'arya bane bata dasu sai dae koda tana dasu d'in to sun barta tun kafin kasanta
ko kuma sune ke sakata rashin ji a can baya amman basu sakata ciwo kaman yadda take yanzu kayi
tunani da kyau a gani na Zarah ta fara sonka kwatsam sai ga Fanan ranar da kuka dawo, tambayata anan
da ka ga Fanan wane reaction kay? Zai iya yuwuwa ta haka ta gane akwae wani abu tsakaninka da Fanan
saboda rikicewa ta shige gida tace bata lafiya sannan da kuka je da Fanan da daddare wane irin hira
kukai? Shin wai ma da kuka dawo da ita akan hanya tace maka bata lafiya ne dama??" shiru bakin
Haisam ya mutu yama rasa mi zaice mashi abun gaba d'aya ya gama d'aure mashi kai wai Zarah na
sonshi..........

Tana ta kwance ba um ba umum kamar wanda tay Mutuwar kwance sai ido kawae ita kanta bata san
mike faruwa da ita ba gaba d'aya jijiyoyin jikinta sun daina aiki a haka har akai la'asar ga bak'ar yunwa da
ke cinta cikinta sai kuka yake amman ta kasa tashi, tana a cikin wannan halin Haulat ta d'aga labulan
d'akin ta shiga da sallama jikinta sanye da Uniform d'in islamiyya, tunkarar gadon tay idonta akan fatuu
ta tsaya gaban gadon tace "kawata lafiya ina sallama baki amsa ni ba" k'uri tay mata da ido ko kyafta su
bata yi hakan yasa haulat kiran sunanta amman shiru da sauri tasa hannu a shoulder dinta ta jijjigata
tace "Fatuu lafiya wai? Mi ke faruwa ne?" da k'yar ta iya mik'ar da yatsanta ta nuna ma Haulat Iv d'in
dake gabanta ta kai hannu da sauri ta bud'e tana karantawa,a kid'ime ta d'ago ta kalli Fatun sai kuma ta
zauna gefen gadon a hankali ta aje iv d'in a gefe ta fara Magana "nasan dole ne ki k'ara shiga
matsananciyar damuwa yanzu amman don Allah kiyi hakuri Fatuu kaman yadda nike ta fad'i maki, ki
d'auka Allah bai kaddara Ya Haisam mijin ki bane" sai lokacin ta yunk'ura da k'yar ta tashi zaune idonta
akan Haulat da wata irin murya ta wanda ya karaya tace "amman Haulat wllh ina son ya Handsome Allah
ne shaidata...." sai lokacin kwalla suka fara zubo mata da ganin yadda take kukan zaka san ba k'aramin
ciwo take ji a cikin zuciyarta ba" dafata Haulat tay taci gaba da bata hakuri tana nuna mata kowa da irin
k'addararsa a rayuwa ta d'auka wannan ce tata ita dae kai kawae take d'aga mata can Haulat tace "da
zuwa nayi mu tafi islamiyya bazaki ma iya zuwa ba ko?" girgiza mata kai tay tace zata je,

"Da alama ma tun da kika dawo da safe kike cikin wannan halin naga ko Uniform baki cire ba, kin ci ma
Abinci kuwa?" girgiza mata kai tay alamar a'a tace "to in zubo maki zaki ki ci ko?" shiru ta d'anyi sai kuma
ta d'aga mata kai don tana jin yunwa sosae, mik'ewa Haulat tay taje Kitchen bada jimawa ba ta dawo
ruke da plate din dafa dukan taliya da wake ta mik'a mata ta sake fita taje falo ta d'aukko mata ruwa,
bayan ta dawo komawa tay ta zauna gefen gadon tana rarrashinta akan tayi hakuri ta daure taci, ba wani
mai yawa taci ba don sam bakinta bai mata dad'i tace ta k'oshi ruwan ne dae ta shanye shi duka,bayan
ta gama saukkowa tay ta nufi hanyar fita walking Slowly Haulat ta tambayeta ina zata tace alwala zatayo,
saida tay Azahar sannan tayi la'asar kafin ta mik'e ta daukko jakarta Haulat tace ta kawo ta rike mata
tace ta bashshi daga haka suka fita, Kawu Amadu na shago bai dad'e da bud'ewa ba don baccin rana ya
sha sai bayan la'asar ya bud'e Haulat ta gaidashi kafin suka wuce, tunda suka fito idonta akan gidan
Hajiya suna zuwa daidai kwanar dake jikin gidan Fatuu ta ja ta tsaya haulat ta juyo ta kalleta ganin tayi
tsaye yasa ta tambayeta lafiya ko bata iya zuwa,

"Haulat kije kawae ni zan je in fad'i ma Ya Handsome halin da nike ciki gaskiya nasan yana nan tunda
yau Lahadi" waro ido haulat tay a rud'e tace "Fatuu kar kiyi haka don Allah ki daure, wllh ko kin gaya
mashi ba abunda zai maki saidae ya baki hakuri to kinga gara ma kar ki fad'i mashi d'in don k'imarki na
iya ragewa a idonshi" kaman zatai kuka tace "naji koma mi zai faru ni ban damu ba in dai ya sani, kuma
tunda shi mai tausayi ne nasan yana iya tausaya man ya aure ni har rokonshi ma zan iya yi ko matsayin
mai aikinsu ce ya Aure ni" bud'a baki Haulat tay tasa tafin hannunta ta rufe cike da al'ajabin jin kalaman
Fatuu, ganin tana niyyar juyawa yasa ta kamo hijab d'inta a rud'e take fad'in "Fatuu kar kiyi haka don
Allah, wllh ni nasan ba zai aureki ya had'a ki da Aunty Fanan ba danginsu bazasu ta6a yarda ba....." bata
k'arasa Maganar ba sakamakon buge mata hannu da Fatun tay ta nufi gidan Hajiyar kai da gani bata cikin
hayyacinta idanunta sun rufe,tsaye Haulat tay ta rasa mi zatayi ta tsaida Fatuu, zuciyarta ta raya mata ko
taje ta fad'i ma kawu Amadu sai kuma wata zuciyar tace ko kafin ki fad'i mashi ma ai aikin gama ya riga
ya gama, sharr kwalla suka fara zubo mata ta fara fad'in "duk ni naja maki wannan halin Fatuu dana sani
ban maki Maganar nan ba" k'arshe dae data rasa mafita kawae sai ta juya ta nufi hanyar islamiyyar tana
share hawayen dake zubo mata, Fatuu na zuwa tabi ta k'aramar kopa dake bud'e tana zuwa bakin fence
door ta kutsa kai part din Haisam...............

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wannan
no 09013n804524._
*ASM Bk2009*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

........Kallon Abbas haisam yay yace "let's say abunda ka fad'a gaskiya ne amman miyasa Zaraah zatai
hakan, ban tunanin na ta6a yi mata wani abu da zai sa tay tunanin am in love wit her, so i don't believe
all what you ave said" ya k'arasa Maganar yana d'an shaking kanshi alamar rashin yarda, Abbas yace "ai
shi so ba ruwanshi da wannan H,zakee wani kallonshi kawae zakai kaji kana sonshi,kuma kai har kace ba
kai mata wani abu da zata ji son ka ba duk irin kyautatawar da kake ma yarinyar......." katseshi Haisam
yay da fad'in "ita kadae nike ma haka ne?",

girgiza kai Abbas yay "nasan ba ita kadae kake kyautata mawa ba sai dae Maganar gaskia tata is special
kana kulawa da yarinyar over ta yadda wani ma zai iya yin tunanin sonta kake, nasan ba wani abu bane
hakan a wurinka duk wanda yake tare da kai yasan kai Mutum ne mai kyautata ma mutane wanda a
zamanin nan da muke ciki da wuya asamu Wanda Allah ya bud'a mawa yake irin Alkhairin da kake, ba
kuma don ganin idonka ba kamawa tay nake fad'a nasan ba so kake ba, sai dae kasani ka sake ma Zarah
da yawa ta yadda ko siblings naka ban tunanin suna samun hakan daga gare ka hakan kuma zai iya juya
komae" shiru haisam yay yana binshi da ido har ya gama sannan cikin cool voice d'inshi yace "komae
nake ma Zaraah inada dalili Abbas, yarinyar is an Orphan marainiyane ita da Uncle d'inta and farkon
dana fara Magana da ita na fahimci tana da ambition mai kyau wanda in aka tallafa mata zatai achieving
don tana da kokari sosae, saidae kuma i found her behaviours so strange because i never came across
wani da yake behaving yadda take shiyasa na fara tabbatar da lafiyanta ta hanyar tambayarta daga baya
na fahimci haka take kuma tana buk'atar ta canja behaviours nata ta maida hankali kan karatunta
shiyasa nai amfani da daman glass da ta fasa man" jinjina kai Abbas yay sosae ya gamsu da Maganar
Haisam d'in sai yanzu ya fahimci komae dama kuma suna tallafa ma marayu sosae ta Foundation d'in
Hajiya,
"Wato ka gane H,Zakee, ita zuciya abu kad'an ke canja ta ba kamar kyautatawa don ingantaccen hadisi
na Manzo (S.A.W) yay magana akan ita zuciya an halicce tane akan son mai kyautata mata da kuma k'in
mai munana mata, nasan kasan da hakan to anan son zai iya kasancewa na soyayya ko akasin hakan to
kwata kwata ba abun mamaki bane wllh don Zaraah taji tana sonka,zata iya tunanin kuma kaima son
nata kake shiyasa kake mata hidima sosae kamar yadda nima can baya na fara zargin hakan bani kadae
bama har Najeeb yay tunanin hakan har ina cewa wannan overtaking zai man kenan ya fara da biyu" ya
k'arasa yana dariya shima Haisam dariyar yake kafin yace "da dae ba waccan sarkin kishin zan aure ba,
just don nace bazan aureta ba fa ta kwanta Medical bed yanzu taji kuma zan hadata da wata in Aurensu i
can't even imagine abunda zai faru kuma kaima kasan bani da ra'ayin mata biyu wannan sai kai da
Najeeb, nayi mamakin ma yadda akai kakai yanzu da mace d'aya i thought by now kana da 4 wives" wata
yar iskar dariya Abbas yasa shima Haisam d'in dariyar yake yace "saurin mi kake ka jira ka gani tunda
Addini ya bamu dama ni bazan cuci kaina ba kai dai kaje ka k'arata da guda d'aya kaida gwauro baku da
maraba ba kamar in ta fara aiki" d'an ta6e baki yay ya maida idonshi kan tv, duk wannan Maganganun
da suke akan kunnan Fatuu dake lafe a gefen kopar parlon Haisam sakamakon lokacin da Abbas yay
mashi waya yace yana parlonshi da ya dawo daga Masallacin shigewa kawai yay ba tare da ya rufe kopar
ba ita da kanta ta rufe saidae bata idasa datsewa ba, Lokacin data shigo part d'in nashi sai kuma ta tsaya
tana wasi wasin zuwa wurinshin can dae ta shiga cike da tsoron abunda zai biyo baya hakan yasa ta
rink'a tafiya cikin sand'a har ta haye balcony d'in ba tare data yi wani kwakkwaran motsi ba tana zuwa
bakin kopar ta jiyo muryar Abbas da yake shi yana d'aga murya in yana Magana ba kamar Haisam ba,
duk da shima Haisam d'in ya d'an d'aga murya don ba wuri d'aya suke zaune da Abbas d'in ba yana can
bangaren armchairs wannan dalilin ne yasa ta lafe ta kasa kunne tana sauraransu cike da tashin hankalin
jin akanta suke Maganar,kenan Abbas ya gano tana son Ya Handsome ta fad'a a ranta, ba komae yafi
tada mata hankali ba sai Maganar Haisam ta k'arshe da yace baida ra'ayin mata biyu da kuma zance
kwanciyar Fanan gadon Asibiti, hannu tasa ta rufe bakinta sosae gudun kada tay abunda zasu gane tana
a wurin, a hankali jiki a sa6ule ta juya har wani duhu take gani ba tare data ankare ba wurin sauka daga
stairs d'in balcony d'in kafarta ta zame ta tafi gaba d'aya ta fad'a kasa tumm k'arar faduwar har cikin
falon hakan yaja hankalinsu duk suka kalli kopar parlon Abbas ya mik'e yana fad'in bari ya duba yaga
miye, tana fad'uwar cike da k'arfin hali duk da buguwar da tay ta yunk'ura ta mik'e da sauri ta nufi
hanyar fita tana kaiwa bakin fence p door Abbas na fitowa ta fice da sauri saidae yaga bayanta kawae
lokaci guda kuma ya shaida wacece, d'an cije baki yay had'i da girgiza kanshi cike da tausayawa ya
ayyana a ranshi kenan ma tana zuwa Haisam d'inne bai sani ba,juyawa yay ya koma cikin falon ganin
Haisam na kallonshi yasa yace mashi baiga komae ba k'ilan yara ne ya d'aga mashi kai kawae, komawa
yay ya zauna idonshi akan Haisam dake kallon tv ya rasa mima zai ce mashi ya yarda abunda ya fad'i
mashi game da Zarah gaskiya ne, can dae yace "H,Zakee yanzu in da gaske Zaraah son ka take ya za'ai?"
juyowa yay ya kalleshi ya d'age gira yace "kai zan tambaya wannan ai tunda kai ka kawo issue d'in" shiru
Abbas yay shi kanshi baisan mi zai ce ba, ta ko ina abun ba mai sauk'i bane ganin Haisam ya kafe shi da
ido yasa yace "kawae na tambayane amman in ma hakanne bai wuce ka bata hak'uri ba in ace ta fad'a
maka, yanzu kuma da bata fad'i maka ba rashin sanin is the Best ka rabu da ita kawae, amman fa kasani
kayi breaking heart d'in yar Mutane wllh" d'an Murmushin gefe yay kawae ya maida idonshi kan tv don
shi jin Abbas d'in kawae yake ba don ya yarda ba.
Tafiya take saidae bata san inda take wurga k'afarta ba don wani duhu take gani Allah dae ya taimaka ta
k'arasa gida lafiya hannunta guda dafe da gaban kanta, tana shiga d'akinta ta aje jakar hannunta a tsakar
dakin tasa hannu ta cire hijab d'in jikinta ta cillar da ita can gefe ta haye can tsakiyar gadon ta zauna ta
d'age k'afafunta sama tasa hannuwanta ta k'ank'amesu tana ta zare ido yayin da zuciyarta ke tariyo
mata maganganun Haisam can ta saki k'afafun ta kama kanta da duka hannuwanta ta fashe da wani irin
matsanancin kuka cikin kukan take fad'in "Ni in baka aure ni ba Ya Handsome ba gadon Asibiti zan
kwanta ba mutuwa zanyi......" haka ta dingi maimaitawa can ta sark'e ta fara tari kan kace mi sai amai ta
saddo kanta k'asa don ta kasa saukkowa daga gadon dama kitson kalaba ne akanta gaba d'aya sun
saukko har k'asan d'akin kan carpet,tun tana aman d'an Abincin da ta ci har takai ba komae da yake
fitowa sai kumallo gaba d'aya ta gama galabaita, tana cikin wannan halin Amadu ya shigo ya shiga toilet
bayan ya fito yana niyyar fita ya jiyo kakarin aman da take yi da mamaki ya juya ya nufi d'akinta don
shidae yasan ta tafi islamiyya don data dawo baiga wucewarta ba, lokacin da ya d'aga labulen d'akin cike
da al'ajabi yake kallonta yama kasa shiga saboda tsoro, ganin halin da take ciki yasa ya kira sunanta shiru
bata amsa ba har saida ya k'ara kiran nata sannan cikin mawuyacin hali ta d'ago mashi hannu tace
"Kawu Amadu....." yana jin hakan ya kutsa kai da sauri ya nufi inda take yasa hannu ya d'agota ya
maidata saman gadon sosae kafin ya zauna yana kallonta a razane ganin yadda ta koma sai faman nishi
take yace "miya sameki ne haka, ba kin tafi makaranta ba?" fashe mashi tay da wani kukan tace "Son Ya
Handsome nike amman shi baya sona" waro ido Amadu yay baki bud'e yake kallonta jin abunda ta fada
wanda bai ta6a zaton ji daga bakinta ba, mamaki shimfid'e a kan fuskarshi yace "dama saboda shine kike
ta ciwo?" jinjina mashi kai tay alamar eh, wani d'an guntun Murmushin mamaki mai d'an sauti yay yana
kallonta cike da Al'ajabi can yace "to ke ya akai kika fara sonshi haka ina ma kika san wani soyayya da har
zaki jefa kanki cikin wannan halin?"

yunk'urawa tay da k'yar ta ja jiki ta jingina da bango tana nishi cikin jin jiki ta fara bashi labari tun farkon
yadda akai ta fara sonshi dalilin Maganar da suka yi da Haulat har zuwa yanzu data je ta iske suna fira da
Abbas, murus bakin Amadu ya mutu sai faman bin ta da ido yake sosae kuma yaji ta bashi tausayi don
yasan wacece ita sam soyayya bata gabanta don wani lokacin shida kanshi yake ce mata in bata da
saurayi taya zatai aure ta tafi ta basu wuri sai tace ai in tazama likita miji sai ta za6a,

"Na fahimci komae, kiyi hakuri kinji, naji dad'i da baki sanar dashi ba don ko kin gaya mashi ba abunda
zai maki saidae ya baki hakuri tunda kinga saura kwanaki ma bikinshi kuma dama bai kamata ma kice
mashi kina son shi ba duk yadda kike ganin kuna mutunci dashi sai wani abu ya ragu na daga mutuncin
da yake kallonki dashi don mace da kunya aka santa balle ke da kike cikakkar bafullatana wad'anda aka
sani da tantsar kunya, ba wani abu bane don mace tace tana son Namiji tunda ga misali nan akan Manzo
(S.A.W) da Nana Khadija Allah ya kara mata yarda ta furta tana sonshi saidae ita a lokacin ta girmeshi
kuma bazawara ce,shiyasa in budurwa ta furta tana son namiji sai ad'auketa mara kunya mara kamun kai
duk da ba haramun bane"

"To Kawu Amadu ya zanyi da sonshi yana damuna baka ji yadda nike ji a kirjina ba, ba irin k'ok'arin da
banyi in fitar da son nashi ko na huta amman kullum k'ara yawa yake wllh" ta k'arasa Maganar fuskarta
sha6e sha6e da hawaye harda majina, Amadu dai sai kallonta yake abun gwanin ban Al'ajabi wai Fatuu
ce so ya maida haka acikin ranshi yake fad'in nifa shiyasa ba ruwana da wata soyayya nafi gane ma in
nemi kudi tunda naga sa Mutane hauka yake ga misali nan a gabana, a fili kuma sai ya mik'a mata hannu
ta matso kusa dashi cikin sigar lallashi yace "na fahimci yadda kike ji amman ki daure ki cije ki fitar dashi
zaki iya nasan ke ba raguwa bace kar ki bari sonshi yay galaba a kanki ya rusa maki mafarkinki na
zamowa kwararriyar likita da muke burin yin Alfahari da ita bama mu kadae ba gaba d'aya k'asa zatai
alfahari dake in kika dage, lokacin sai kiga Allah ya kawo maki wanda ma yafi shi" da sauri tay mashi wani
kallo wanda ya fahimci kona miye yace "nasan Ya Haisam na dabanne samun irinshi zai matuk'ar wuya
amman fa bawai baza'a iya ba shima ai cikin Mutane aka sameshi ko to tabbas akwae wasu irinshi
wanda ma suka fishi komae, kyau, nasaba da sauransu ke dai kawae ki dage ki cimma burinki zaki ce nina
fad'a maki zaki ga yadda maza da suka amsa sunansu zasu yi rububin samunki don kema d'in sarauniyace
cikin mata Allah ya baki komae sai abunda ba'a rasa ba tunda mutum tara yake bai cika goma ba amman
dae dole sai kinyi yak'i sosae da zuciyarki, sannan in kuma kika bari tay galaba akanki to kuwa zata kaiki
ta baro ki ne, ki dage da Addu'a dare da rana nima yanzu tunda na sani zan tayaki da Addu'ar kar ma ki
bari gwaggo taji wannan Maganar don ba lalle ta fahimce ki ba tana iya yi maki fad'a ma, kuma kar kiji
haushin Haulat abunda ta fad'a maki nima kwanaki sai da nayi tunanin hakan har ina Addu'ar Allah ya
tabbatar amman daga baya tun kafin in san da akwae wadda zai Aura na fahimci kawae kyautatawa ce,
don haka mu bar ma Allah komae ki d'auka shi d'in ba rabonki bane don wata bata taba Auran mijin
wata haka wani ma bai taba Auran matar wani kowa da wanda Allah ya kaddaro mashi matsayin abokin
rayuwarshi in kuma shi d'in rabonki ne kina zaune ba tare da wata wahala ba zaki ga yazo ya aure ki har
kita mamakin yadda akai hakan, kad'an daga cikin ikon Allah ne Abunda baka taba tunanin zai yuwu yasa
ya yuwu, kiyi hak'uri kinji d'iyata kuma yar k'anwata" ya k'arasa Maganar had'i da jawota jikinshi ya
rungumeta ta gefe tay lamo tana nazarin maganganunshi acikin ranta, yayin da shima a cikin ran nashi
yake fad'in dole ya k'ara kiyayar so,

"Amman kawu Amadu inason in daina ganin Ya Handsome yanzu, don duk in na ganshi ciwon k'aruwa
yake" yaji ta fad'a cikin sanyin murya,d'agota yay yana kallonta yace "Amman baki ganin zaiyi tunanin
wani abun ace ya daina ganinki kwata kwata?"

"Eh nidae nafi son hakan kawae ai dama ya kusa tafiya ko" jinjina kai yay yace "shikenan daga yanzu
zan rink'a taimaka maki har Allah yasa ki daina jin son nashi idan yazo d'aukarki da safe zan sanar dashi
cewa Haulat tazo kun tafi nasan in akai haka sau biyu ko sau ukku zai yi tunanin ko kuna wani abunne a
Makarantar yasa kike tafiya da wuri tunda yasan kun kusa fara jarabawa k'ilan ya daina zuwa, to amman
bikin nashi fa bazaki ba?" da sauri ta d'aga mashi kai alamar eh, d'an Murmushi yay ya girgiza kai a ranshi
yace rayuwa kenan wazai yi tunanin hakan zata kasance a tsakaninsu, komawa tay ta kwantar da kanta a
kafad'arshi duk jinta take wani iri,shiru sukai na d'an wani lokacin kafin yace "nasan kina jin yunwa ko?"
kai ta d'aga a sanyaye tace "amman ban iya cin komae bakina ba dad'i" yace "daurewa zaki fa karki illata
kanki da yunwa su basu san ma kina yi ba kuma ba Abunda zasu fasa koda wani abu ya sameki, bari in
kawo maki abu ki ci" ta d'ago daga kafad'ar tashi ya mik'e ya fita, bada jimawa sosae ba ya dawo dama
saida ya kulle shagon ya shigo gidan har ya isketa a halin, k'aton biscuit da cup cake guda biyu ya d'aukko
mata da lemu ya tasata gaba bayan yasa ta wanko bakinta saida taci sosae ta rage biscuit d'in bada yawa
ba yace zaije yayo salla ta daure itama tayi tace to, saida ya gyara inda tay amai sannan ya tafi, ana idar
da sallar ya dawo lokacin tana kwance akan sallayar yace taje tayi wanka zata ji dad'in jikinta ya rakata
kar bakin toilet d'in bayan ta shiga ya shige d'akinshi, saida ya tabbatar ta gama shiryawa ya koma d'akin
ya isketa akan gado tayi lamo ya shiga ya tambayeta akwae abunda take so tace mashi bacci take son yi
amman yak'i zuwa, shiru ya d'anyi sai kuma yace mata yana zuwa ya fita, mashin d'inshi ya hau ya nufi
bakin hanya can wani babban chemist yayi ma mai shagon bayanin kanwarshi ce ke cikin damuwa tana
son yin bacci amman yaki zuwa in akwae Maganin da zata iya sha mara illa ya bashi yace mashi akwae ya
d'aukko mashi,bayan ya dawo yadda ya barta haka ya isketa sai wurga ido take ya bata Maganin yace ta
bari sai tayi sallar isha tasha tace mashi to tay mashi godiya yace ba komae shidae fatan shi ta cire
damuwar a ranta tace in sha Allahu zata cire daga haka ya juya ya nufi Masallaci don yin sallar isha da
aka fara itama ta mik'e ta fita tayo Alwala tazo ta kabbara sallar tana gamawa ta d'aukko maganin ta sha
kafin ta haye gado, lokacin da Amadu ya k'ara dawowa wurinta har tayi bacci d'an Murmushi yay a fili ya
furta "ciwon so ya kama manya,wato dae ashe ciwon nan da gaske ne, nifa na d'auka duk iskanci ne
mutum yay shame shame wai shi ciwon so yake, to Allah ka k'ara kare mu da sharrin ciwon so Amin"
daga haka ya kashe mata hasken d'akin ya tafi. Bada jimawa ba gwaggo ta dawo tana shigowa gidan
d'akin Fatuu ta nufa bayan ta kunna globe ta hangota kudundune saman gado tana ta bacci a ranta ta
ayyana yau da wuri akai bacci kenan ta juya bayan ta kashe hasken, tana fitowa tay kacibus da Amadu da
ya shigo yana k'ara mata sannu da zuwa don yayi mata a waje,tace "Fatuu Lpy dae ko naga tayi bacci da
wuri" da d'an Murmushi kan fuskarshi yace "Eh to da sauk'i tace man wai kanta na mata ciwo shine na
bata Magani ta sha"

"Bata ma je islamiyya ba kenan" yace "a'a taje" jinjina mashi kai tay tana shirin nufar d'aki shima ya
juya yaji ta tambayeshi Fatun taci Abinci kuwa yace mata eh taci daga haka ya fice itama taci Abinci

tayo wanka ta kwanta don a gajiye take.

Tun bayan da ya gama komae ya kwanta Maganar Abbas ke ta mashi kai kawo acikin ranshi, duk da bai
gasgata ba amman kuma wani sashi na Zuciyarshi yana neman takura mashi da zancen, kwance yake
jikinshi sanye da sleeping dress riga da wando farare masu laushi yana facing saman d'akin sai faman
tunane tunane yake, ba Maganar data fi damunshi sai ta Abbas da yace ya sani yay breaking heart d'in
yar Mutane, hannu ya kai ya shafi forehead d'inshi ya bar hannun ba tare da ya cire ba idanunshi a
runtse ya fara tariyo rayuwarsu da Fatuu tun farko har zuwa yanzu,wani lokacin yay d'an Murmushi wani
lokacinma yar dariya yake har hakoransa su bayyana a haka har ya gangaro zuwa girmanta gaba d'aya
rayuwarta cike take da nishadi da wuya kaga tana k'unci, ko ta d'aure fuska na d'an lokaci ne zata washe
kaga tana dariya, in bai manta ba zai iya cewa rabon da ya ga farinciki akan fuskarta tunda suka baro
Ajiwa Dam ne, a hankali ya cire hannun dake dafe da goshinshi ya bud'e idanuwanshi, yunk'urawa yay ya
tashi zaune ya jingina bayanshi da headboard ya kai hannu ya d'auki wayarshi dake kan side drawer,
bayan ya bud'eta direct images dake a gallery d'in wayar ya shiga yay scrolling har zuwa inda pictures
d'in da sukai a Ajiwa suke ya fara kallonsu da Murmushi akan fuskarshi, kai da kaganta a hotunan zaka
fahimci tana cikin tsantsar farinciki ba kamar yanzu ba duk ta canja kamar ba ita ba, a hankali ya maida
wayar inda ya d'aukko ya ajiye ya d'age kanshi sama yana jin wani iri a zuciyarshi lokaci guda ya ayyana
in dae da gaske shine silar shigar Zaraah halin data ke yanzu bai ji dad'in hakan ba...........
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wannan
no 09013804524._

*ASM Bk2010*

_Destiny may be delayed but cannot be changed....._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

........Washe gari da Asuba Amadu da kanshi ya je ya tasheta tay salla yace ta tabbatar tayi Karatun
Alqur'ani kuma tayi Addu'a sosae tace mashi to sannan ya wuce Masallaci shima, ba laifi taji dad'in
jikinta hakan yasa ta fara yin shirin zuwa Makaranta tana gama sallar, lokacin data fita gwaggo na
kitchen ta nufi can ta tsaya bakin kopa ta gaisheta don lokacin da take karatu taga gwaggon ta lek'a
dakinta da fara'a ta nufota tana amsa gaisuwar tace "ya ciwon kan jiya dana dawo kina bacci Amadu
yace man kina ciwon kai" d'an Murmushin yak'e tay tace mata ta samu sauk'i gwaggon tace "Oh ciwo
dae ya taso ki gaba kwanakin nan daga wannan sai wannan Allah ya baki lpy mai d'orewa" sadda kanta
tay ta amsa da Amin kafin ta d'ago tace mata zata tafi Makaranta da d'an mamaki gwaggon tace
"Makaranta da wuri haka, ban tunanin bakwae fa ta k'arasa in ma tayi to yanzu ne" d'an sosa gefen
kanta tay tana kallon gwaggon tace "ai zamu fara practical ne yau wanda zai fito mana a Jarabawa
shiyasa nike son zuwa da wuri mu samu gaba yadda zamu ga yanda ake yi sosae" jinjina kai gwaggo tay
cike da gamsuwa ta juya tana Fad'in bari to ta mik'o mata abun karin kumallo taci sai ta tafi,bayan ta
amshi Breakfast d'in ta koma d'aki ta fara ci, ba wani da yawa taci ba ta maida kayan Kitchen lokacin
gwaggon bata ciki ta bita d'aki tace mata zata tafi ta bata kud'i, dama koda Haisam ke kaisu tana bata
isassun kudin tara da zata iya hawa ma Bus har tay break, saida ta lek'a d'akin kawu Amadu tace mashi
ta tafi ya rakota har kopar gida yana k'ara tausarta akan ta d'age ta cire damuwa ta maida hankali kan
karatunta, saida yaga tayi nisa ya koma cikin gidan, duk da bata jin k'arfin jikinta sosae haka tay ta sauri
don kar Haisam ya isketa a kan hanya har ta k'araso lungun gidansu Haulat, lokacin da ta shiga d'akinsu
bin ta da ido Haulat d'in tay ta kasa mata Magana saboda zullumin jin yadda sukae da Haisam jiya itama
Fatun kallonta kawae take Haulat din tace mata ta zauna mana, bayan ta zauna gefen katifar itama ta
zauna a kusa da ita can dae ta daure tace "kin fad'a mashin ne?" girgiza mata kai tay alamar a'a, wani
sanyi haulat taji har saida tay d'an Murmushi kafin ta tambayeta ya akai bata fad'a mashi ba, farko shiru
Fatun tay hakanan taji bata son fad'a mata hirar da ta iske suna yi hakanne yasa tace mata kawae ta
d'auki shawararta ne shiyasa ta fasa Haulat d'in tace mata ta kyauta,

"Amman ya naga kin shiryo da wuri ko Ya Haisam dinne ya kawo ki?" girgiza mata kai tay tace" bashi
ya kawo ni ba ni na taho,ban son ina ganinshi" cikin karyayyar murya tay Maganar idonta har sun ciko da
kwalla Haulat ta dafata tace "na fahimta Allah yasa hakan yasa ki samu sassaucin abunda kike ji" a
hankali ta amsa mata da Amin, tambayarta tay ko ta kawo mata abun kalaci tace mata taci a gida haulat
d'in ta tashi ta fara shiryawa saida lokacin da suka saba tafiya yayi sannan suka tafi. Misalin k'arfe 7:30
Haisam ya parker a kopar gidan yay horn kamar yadda ya saba yi in ba kowa a waje, saida yayi sau wurin
ukku sannan Amadu ya fito ya nufi Motar Haisam d'in ya sauke glass da Murmushi Amadu ya gaidashi ya
amsa tun kafin ya tambayi Fatun Amadun yace mashi sun tafi tun d'azu, shiru Haisam d'in ya d'an yi sai
kuma yace mashi Ok, Amadu yay mashi sai ya dawo ya amsa daga haka glass d'in ya d'aga sama ya rufe
yaja Motar Amadu yabi bayan Motar da ido kafin ya d'an girgiza kai ya shige gida,

Koda suka je Makarantar Haulat na lura da ita sam bata wani saki jiki ba har gara ma lokacin da bata
kaiga ganin Iv d'in ba ta d'an fara saki amman yanzu an koma yar gidan jiya, saidae tay shiru ko ta d'aga
ma Mutum kai in yayi mata magana sai ta kama take bud'e baki tay Magana, ita kanta halin da take ciki
na matuk'ar damunta ba kuma kamar hukuncin da ta yanke na daina ganin Haisam duk sai take jin wani
irin kad'aici gashi zuciyarta sai tay ta ayyana mata fuskarshi bata da aiki sai tunane tunane,Haulat dae
bata gajiya da k'arfafa mata guiwa, A ranar da daddare bayan tayi sallar isha ta fita waje wurin kawu
Amadu yana ganinta yace "Juliet ya akai" yay Maganar yana yar dariya ita kuma ta d'an tura mashi baki
ganin tay mashi tsaye yasa yace mata ya akai ne tace "dama bacci nike son yi na kasa shine nazo ka bani
wannan Maganin na jiya" bud'a mata ido yay yace "ke kina son zama yar k'waya ne?" a sanyaye tace "a'a
ba magani bane?"

"Eh magani ne amman in kika saba bazaki iya bacci ba sai da shi don haka ki je ki kwanta kawae baccin
zai zo in sha Allah kiyi Addu'a" tana shirin k'ara yin Magana ta jiyo k'arar bike d'in Haisam ya dawo daga
Gym aikuwa da sauri ta juya gudu gudu ta shige gida ta la6e cikin zaure tana lek'enshi har yazo ya wuce,
sauke ajiyar zuciya tay ta d'an cije baki kafin ta nufi cikin gidan tana shiga d'aki ta haye gado ta kwanta
tana ta tuna rayuwarsu da Haisam kwalla na gangaro mata duk ranta bai mata dad'i sai can dare ya nisa
bacci yay awon gaba da ita. Washe gari ma sai ga Haisam yazo d'aukarta lokacin ta tafi Amadu ne ya
lek'a ya k'ara ce mashi ai basu dad'e da tafiya ba ya amsa da Owk ya tafi, abu kaman wasa Amadu na
cewa k'ilan in yazo sau biyu ko ukku ya daina zuwa sai gashi har ranar Juma'a saida yazo a wannan
lokacin kunya ta gama rufe kawu Amadu hakanan yake daurewa yana ce mashi ta tafi shi kanshi ba don
yana son hakan ba don sai yaga kaman ana wulakanta Haisam dinne wanda yafi karfin ai mashi haka,
Zaune take a aji duk ranta a jagule yake kukan zuci kawae take wanda akace yafi na fili rad'ad'i sanin yau
saura sati d'aya Haisam ya tafi kaman yadda taji a bakin gwaggo don sam bata san Fatun ma bata zuwa
gidan Hajiya ba a tunaninta in bata nan tana zuwa wani lokacin kuma tana fita da sunan zata can d'in
gudun kar gwaggo ta gano bata zuwan amman data fita sai tay tafiyarta gidansu Haulat haka in Fanan ta
kira waya tana amsa su gaisa don sosae take kiran layin gwaggo ta gaishe da ita wani lokacin ma in Fatun
na d'aki data ji suna waya sai tay baccin k'arya, Haulat har ta gaji da bata hakuri sai dae tay ta bin ta da
ido don tasan in dai Haisam ba tafiya yay ba ta tabbatar ta rasashi bazata rage damuwar da take ciki ba a
yanzu, suna zaunen Malaminsu na Chemistry ya shigo bayan yan ajin sun tashi sun gaidashi yace su same
shi a Lab ya juya ya fita duk yan ajin suka mik'e suka fara fita hannuwansu ruk'e da littattafansu da biro,
mik'ewa Haulat tay idonta akan Fatuu da ta d'aura Fuskarta kan desk, tasan ba bacci take ba don in dae
ba malami a ajin haka take yi tace "Fatuu ki tashi mu tafi Lab za'ai Practical" shiru bata tanka mata ba har
saida ta maimaita mata sannan ta d'aga mata hannu alamar taje kawae, jiki a sa6ule Haulat ta koma ta
zauna kaman zatai kuka tace "Don Allah Fatuu kiyi hakuri nasan kina yi wllh, amman karki bari damuwar
da kike ciki ta shafi karatunki wannan Practical d'in fa kinsan shine zai fito mana a ssce kaman yadda
Malam yace kuma dole ba yadda za'ai mutum yaci paper d'in Chemistry da physics ba tare daya ci
Practical ba ki yi hak'uri ki taso muje" jimm ta d'anyi kafin can ta d'ago idanunta sun yi ja cikin
disashewar murya tace "kije Haulat ko naje bazan gane komae ba damuwa tay man yawa wllh amman
daga baya sai ki koya man" tana niyyar maida kan Haulat ta kama hannunta tace "ki daure pls, sai kinfi
ganewa in a gabanki akai ni kinsan ba lalle in gane ba sosae tunda wani lokacin kece ma ke k'ara man
bayani in ban gane abu ba" zare hannunta tay ba tare data ce mata komae ba ta maida kanta kan desk,
ba yadda Haulat ta iya dole ta mik'e don kar ai biyu babu ta d'auki littafinta da biro ta fita. Sai lokacin da
aka tashi suka fito daga Laboratory d'in kasantuwar ranar Juma'a ne d'aya saura ake tashi gaba daya,
lokacin da Haulat ta shigo ajin Fatun na a yadda ta barta, d'an girgiza kai tay cike da tausayawa ta nufi
seat d'in ta maida littafinta a jaka kafin ta d'an bubbuga kafad'ar Fatun tana Fad'in ta tashi su tafi gida an
tashi, shiru kaman bazata d'ago ba can kuma ta d'ago idanunta sunyi jawur da alama kuka tasha tana
son karatunta amman damuwa ta hana ta maida hankali ji take gaba d'aya karatun ya fita a ranta
abunda zuciyarta keso ne kawae a ranta,tasan ko taje gidan ba wani samun sauk'i zatayi ba gashi bata
son kawu Amadu yaga bata d'auki shawararshi ba yaji haushi dama ba k'aramin kokari take ba a gidan
tana 6oye damuwarta sai tazo makarantane duk sai abun ya kacame mata gashi yanzu tasan gwaggo na
nan don aikin rana take sai karfe biyu zata tafi a halin da take ciki kuma tasan da taje gidan zata gano
akwae abunda ke damunta don yan kwanakin nan tana yawan tambayarta kodai wani abun ke damunta
ciwoce ciwocen sun yi yawa, tunawa da wannan yasa tace ma Haulat taje kawae ita ba yanzu zata taho
ba, cike da damuwa Haulat tace "haba Fatuu ya za'ai ki zauna a Makaranta ke kad'ai bayan an tashi ba
kowa don Allah ki taho mu tafi" da Haulat d'in ta takura mata akan ta tashi su tafi sai tace mata akwae
inda zata je ne amman sai ta d'an k'ara hutawa zata koma gidan anjima, sarai haulat tasan k'arya take ba
wani wuri da zata je amman sai tace to bari ta zauna in ta hutan sai su tafi tare, cike da tsiwa tace "to in
banson zuwa dake fa, nace ki tafi ai ba 6acewa zanyi ba ko zan dawo anjima" d'an girgiza kai Haulat tay
ta mik'e ta d'auki jakarta ta had'a data Fatun tace bari ta tafin mata da ita ba don ranta yaso ba ta tafi
tana yi tana waiwayen Fatun har ta fita ita kuma tay kwanciyarta saman seat.
Cikin sa'a Haulat ta samu Bus tana fita ta hau, daidai kwanar da aka saba aje su suka sauka da sauran yan
Unguwar, bayan ta fita lungun tana shirin hawa hanya sai ga Motar Haisam ta taho shima ya dawo daga
aiki dama duk juma'a a gida yake salla, tsayawa tay tana kallon Motar don ta gane shine yana zuwa saitin
ta ya taka burki ya tsaya a hankali kuma glass d'in Motar ya sauka fuskarshi ta bayyana, da d'an
Murmushi Haulat ta gaishe shi fuska a sake ya amsa mata yace mata an dawo tace mashi eh ya jinjina
mata kai tana ta d'ar d'ar a cikin zuciyarta kar ya tambayeta Fatuu don tasan muddin ta fad'i mashi halin
data baro ta to tabbas zai bita ne in kuma yaje ba makawa tasan Fatuu na iya fad'i mashi halin da take
ciki ita kuma bata son hakan ya faru, kawae sai taga glass d'in ya fara d'agawa sama daga haka yaja
Motar Haulat ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ta juya ta tafi, a daidai gaban shagon kawu Amadu ya
tsaya lokacin Amadun na shago yayi wankan juma'a yana jiran lokacin sallar ya idasa yi, yana ganin
Motar ta tsaya ya fito da sauri glass d'in d'ayan side d'in ya sauka Amadun ya lek'a ta nan yana gaidashi
ya amsa mashi kafin ya tambayeshi Zaraah ta dawo ne, shiru Amadu ya d'anyi alamar tunani sai kuma
yace "gaskiya dae banga wucewarta ba amman bansan koda ina cikin d'aki ba don ban dad'e da fitowa
ba bari in ga kota dawo" d'aga mashi kai yay ya juya ya nufi gidan bada jimawa ba ya dawo yace mashi
bata dawo ba ya d'anyi shiru kaman mai tunanin wani abu sai kuma yaja Motar bayan ya amsa mashi da
Ok, Yana isa gidan toilet ya shiga bayan ya rage kayan jikinshi a laundary, bada jimawa sosae ba ya fito
ya fara shirin zuwa Masallaci,sanye cikin galleliyar shadda light blue ya d'aura hula data hau da kayan sai
daukan ido take don yasan da ya je ba hular Hajiya sai tay Magana, haka ma takalman kafarshi kalar
kayan ne agogon diamond d'in hannunshi nata kyalli sai sakin fitinannan kamshi yake ya nufi part d'in
Hajiya, atare kaman ko yaushe suka tafi Masallacin bayan sun dawo suka nufi dining Area Saude tay
serving nasu suka fara cin Abinci can bayan sunyi nisa da farawa Hajiya ta dakata idonta akanshi tace
"wai nikam Fateema na zuwa wurinka,shirun yay yawa yaushe rabon da in ganta gidan nan, rannan da
muna waya da Dijen nike tambayarta kwana biyu banga Fateema ba sai take ce man ai tana ce mata
tana zuwa kilan bata iske ni ne nace to kilan dae wurin yayanta take zuwa ko kuma lokacin da take zuwa
bani nan d'in amman dae gaskiya da tana zuwan zan ganta ne tunda ai ba ko yaushe nike fita ba, gaba
d'aya tunda tay ciwon nan ta canja kwata kwata duk da dae dama mai irin ciwon nan komi yay ba abun
mamaki bane" idon Haisam a kanta bayan ta gama Maganar yace "kinsan they're about to start their
final exams k'ilan shiyasa bata da time en zuwan" jinjina kai tay sai kuma tace "amman kai d'in tana zuwa
wurinkan?" shiru ya d'anyi sai kuma yace mata eh tana zuwa ta gaidashi kuma yana kaisu skul, shi kanshi
baisan miyasa yay mata k'aryar ba abunda ba halinshi ba, gyad'a kai tay cike da gamsuwa taci gaba da
cin Abincinta, kasa cigaba da cin Abincin yay ya mik'e ganin hajiya na kallonshi yace mata zaiyi abu a part
d'inshi ne daga haka ya nufi cikin parlon ya fice, part d'in nashi ya koma yana shiga ya zauna kan kujera
yasa hannu ya dafa gaban kanshi, tun bayan da sukai Magana da Abbas abun keta damunshi a rai yana
son ya kauda tunanin amman abun ya faskara zuciyarshi na damunshi da son sanin da gaske ne abunda
Abbas ya fad'a saidae kuma wani bangare na zuciyar na gargadinshi kan rashin sanin shi yafi kaman
yadda Abbas din ya fad'a amman tabbas ya fara zargin akwae abunda ke damunta ba ciwon da yake
tunani bane kad'ai ba kamar Maganar da Hajiya tayi, yanzu ya gane tana yi ma Grandma d'inta k'aryar
tana zuwa gidan alhali kuma bata zuwa,mi zaisa tay haka? ya jefa ma kanshi tambaya, to ko dae anyi
mata wani abune don har yanzu yana shakkun Maganar Abbas saboda yasan wacece Zaraah tun bata kai
hakan ba, haka ya dingi sak'e sak'e a ranshi gashi shi sam baison damuwa duk sai yaji ya takura shiyasa
ba k'aramin abu ke tsaya mashi a rai ba, cire hannun yay ya d'auki wayarshi dake ajiye a gefe ya shiga
Contacts d'inshi bayan ya bud'e, lambar kawu Amadu ya kira bugu biyu yay picking yana gaidashi ya
amsa mashi kafin ya tambayeshi Zaraah d'in ta dawo yace mashi a'a gaskiya ba kowa ma a gidan don
gwaggo ma ta tafi aiki amman dae yana tunanin ko sun tsaya lesson ne don yanzu wasu ranakun suna
kaiwa har yamma, amsa mashi yay da Ok ya kashe wayar, tunani ya shiga yi mi zaisa ya ga Haulat ta
dawo in har lesson suka tsaya tunda tare suke class d'insu d'aya, yin wannan tunanin yasa shi mik'ewa ya
kai hannu kan c-table ya dau car key ya juya ya fice daga parlon, yana fita ya nufi Parking Space ya hau
Mota ya fice direct gidansu Haulat ya nufa bayan ya parker a kopar gidan ya sauke glass ya kira wani
yaro dake can gefe guda yace ya shiga yace Haulat tazo, bada jimawa ba sai gasu sun fito tare tay wanka
tana sanye da hijab kalan kayan jikinta, da mamaki kan fuskarta take bin Motar da kallo dama tun a ciki
tayi mamakin jin wai mai Mota yana kiranta kamar yadda yaron yace da ya shiga, zagayawa tay
bangaren da driver mota d'in yake har saida gabanta ya fad'i ganin Haisam, d'an Murmushin yak'e tay
mashi ta gaidashi ya amsa kafin yace "Zaraah fa?" wurga ido ta fara tana motsa baki a dabarbarce tace
"bata koma gida bane?" maimakon ya bata amsa sai ce mata yay "kun dawo tare ne?" hannu ta d'aga
tana d'an juya shi tace "a'a bamu dawo tare ba"

"Then where is she?" ya kafeta da kaifafan idanunsa duk tay kalar rashin gaskiya ta rasa yadda zatai
mashi bayani can tace "da..dama zamu shiga Practical ne to sai nace ta taso mu tafi lab d'in sai tace man
bata lafiya in je kawae,t..to lokacin da aka gama aka tashi da na koma class d'in sai ban ganta ba nayi
tunanin taje wani wuri ne sai na d'an jirata amman shiru bata dawo ba sai na d'an dudduba sauran
classes d'in amman bata nan sai nai tunanin ko ta taho gidane" still yay yana sauraranta har ta gama
sannan yace "amman d'azun na ganki da bag d'inta right?" damm k'irjinta ya buga da karfi tace "e...eh ai
dana koma ne naga jakar shine na d'aukko dama yanzu nike niyyar zuwa gidan in ga ko tana nan" sigh
yay ya maida idonshi gaban Motar kaman mai nazarin wani abu can ya juya yace shikenan zata iya tafiya
ta amsa da to ta juya da sauri ta shige gida shi kuma yay reverse ya fita daga lungun,tana shiga zaure ta
tsaya ta dafe kirjinta cike da fargaba,abunda yasa bata fad'a mashi gaskiya ba tasan zai iya tambayarta
miyasa Fatun tak'i biyota kuma zai iya ganin tayi rashin hankali na baro ta da tayi duk da ita tasan
wacece Fatuu in ta kafe kan abu to fa sai tayi sai wani ikon Allah ne zaisa ta fasa don ma yanzu ta d'an yi
sanyi saboda halin da take ciki, lokacin da ta lek'o wajen bata ga Motar tashi ba alamar ya tafi, tunani ta
shiga yi na Fatun bata dawo bane har yanzu yasa yazo nemanta, can dae ta juya ta koma cikin gida, yana
fita lungun ya mik'i hanyar da zata fitar dashi daga Unguwar yana hawa titi kai tsaye Makarantar tasu ya
nufa, yana shiga main gate d'in ya nufi Senior Section a bakin gate ya tsaya yay horn mai gadi ya lek'o
yana yin arba da Motar ya koma da sauri ya bud'e mashi gate d'in ya kutsa ciki a can gefe ya parker
Motar mai maigadin ya nufo shi yana washe baki don ya sanshi sosae sakamakon yawan Alkhairin da
yake masu, bud'e Motar yay ya fito bayan sun gaisa cikin cool voice d'inshi yace "Don Allah ko akwae
sauran Students a ciki?" d'an jimm maigadin yayi kafin yace "gaskiya bana tunanin da sauran dalibai don
gaba d'aya aka tashe su saboda yau juma'a har da yan aji shidda yau basu tsaya lessin d'in da ake masu
ba, Allah yasa dae lafiya" yay Maganar idonshi akan Haisam d'in,

"Akwae Sister na da nike kawo wa so bata koma gida ba har yanzu" da sauri maigadi ya ruk'e ha6a
alamar Al'ajabi yace "Hajiya dae da kake kawowa itace bata koma gida ba?" kai kawae ya d'aga mashi
maigadin yace "to kuma ba'a aiketa wani wuri ba ko tace zata biya wani wuri?" jin tambayar tashi yasa
haisam d'in yi mashi bayanin da Haulat tay mashi, da sauri yace "to ina ganin mu duba ajin nasu ko tana
can, ai ajin kimiyya take ko?" nan ma kai Haisam ya d'aga mashi alamar eh maigadin ya wuce gaba
Haisam yabi bayanshi suka nufi Science classes d'in ya tambayi haisam ajin su Fatun ya nuna mashi, koda
ya shiga wayam ya tadda ajin ba kowa sai tarkacen takardu da ledojin da aka yayyadda, juyowa yay ya
kalli Haisam dake tsaye gaban class d'in yace "Wllh Yalla6ai kaga dae ba kowa a cikin ajin" shiru haisam
yay yama rasa tunanin da zai yi, maigadin yace bari ya duba sauran ajujuwan kai kawae ya d'aga mashi,
gaba d'aya saida maigadin ya zagaye classes d'in dake wurin amman ba Fatuu ba alamarta ya dawo
wurin Haisam d'in yace mashi wllh baiga kowa ba, suna cikin hakan saiga Discipline Master na section
d'in ya shigo zai nufi Admin Block yana ganinsu ya nufesu yana tambayar maigadin lafiya kuwa ya mik'a
ma Haisam hannu suka gaisa maigadin yay mashi bayanin da Haisam d'in yayi mashi, shima da mamaki
yace "to ina taje haka, yakamata ace by now tana gida ba Sp Fateema Muhammad Ardo bace?" cikin
cool voice d'inshi yace mashi ita,

"Malam nace ko a duba clilic (clinic) ko tana can tunda ance bata lafiya" maigadi ya fad'a yana kallon
discipline d'in yace mashi "ai Baba bana tunanin tana can gaskiya don ko d'azun nabi ta wurin a rufe
yake bamma tunanin an bud'e clinic d'in yau" gaba d'aya sukai shiru kowa da abunda yake tunani a
ranshi Haisam dai yay shiru, can discipline ya kalleshi yace "Yalla6ai abunda nike tunanin za'ai shine a
d'an tattambaya inda ake tunanin zata iya zuwa ko cikin unguwa haka don zai iya yuwuwa tabi wata ne
tunda bata lafiya ni kaina kwanakin nan na fahimci ba daidai take ba mun kwana biyu ma bamu yi aiki
tare da ita ba saidae mataimakiyarta tunda duk munsan tana da lalurar jinnu" jinjina mashi kai Haisam
yay yaci gaba da cewa "nima yanzu zan fita cikin staff quarters in dan bibbincika muga, bari in baka
lambar wayata in Allah yasa ka koma ka taras ta koma sai ka sanar dani nima nan in mun ganta sai a kira
a sanar da kai in Allah ya yarda ma za'a ganta don ban tunanin tayi nisa" gaba d'aya suka amsa da Allah
yasa Haisam yace mashi wayan na Mota ya bashi tashi sai ya saka mashi lamba d'in nashi yay mashi
flashing, bayan ya saka mashi sukae sallama ya wuce suma suka dawo bakin gate saida yay ma maigadin
Alheri yana ta mashi godiya da Addu'oi da fatan Allah yasa a ga Fatuu ya bud'e mashi kopar Motar ya
shiga bayan ya juya ya fice daga cikin Makarantar Baba maigadin nata d'aga mashi hannu.........

Jama'a ina Fatuu tayi????🤔🥹

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wannan
no 09013804524._

*ASM Bk2011*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

......Tunda ya fito daga Section d'in na su ya rasa tunanin da zaiyi game da inda Zaraah ta tafi a cikin halin
ciwo,Wayarshi dake ajiye gefe ya kai hannu ya d'auka ya fara tunanin k'ara kiran Kawu Amadu ya
tambayeshi ko ta dawo daidai lokacin ya fito daga Main Gate d'in Makarantar, yana k'okarin kara wayar
a kunne kaman ance ya waiga gefe ya hango kaman wata a cikin Bus Stop dake a 6angaren hagu, cire
wayar yayi ya katse kiran kafin ya taka burki a hankali ya fara yin reverse har yazo daidai Bus Stop d'in ya
sauke glass d'in kopar, k'ura ido yay yana kallon cikin bus stop d'in, wata ce zaune ta d'age k'afafunta
sama ta kifa kanta saidae ba lalle a gane ko d'aliba bace don hijabinta ya sauka ta lullube jikinta gaba
d'aya kuma kalan hijab d'in ba irin ta sauran d'alibai bace, sanin Fatun irin hijab d'in take sawa don ita
prefect ce yasa ya bud'e Motar ya fita ba tare da ya rufe kopar ba ya nufi Bus Stop d'in saidae tun kafin
ya k'arasa ya shaida itace sakamakon takalmanta dake ajiye a gefe wanda shine ya k'ara siyo mata su
wani zuwa da yay Lagos, tsaye yay bakin wurin yana k'are mata kallo fuskarshi a yamutse sam baiji
dad'in ganinta a wurin ba don ba komae a ciki sai uban dirty,

"ZARAAH" ya kirata da wata irin murya shiru bata d'ago ba har saida ya d'an k'ara d'aga Murya ya sake
kiranta sannan ta fara kokarin fiddo kanta daga cikin hijab d'in, koda tay arba dashi a firgice ta mik'e
tsaye tana kallonshi shima kallonta yake sam fuskarshi ba walwala ganin yadda duk ta canja ga idanunta
sun yi ja sun d'an k'ank'ance, kasa jure ma kallon nashi tay ta sadda kai idanunta cike tab da kwalla
k'irjinta na bugawa da sauri da sauri,

"Follow me" ya fad'a had'i da juyawa, har ya tafi sai kuma ya tsaya ya juyo yana mata wani kallo ganin
bata motsa ba,a sanyaye ta duk'a tasa takalmanta kafin ta nufe shi da kanshi ya zagaya ya bud'e mata
kopar ta shiga ya rufe shima ya zagaya ya shige, jin bai ja Motar ba kuma taji ya shigo yasa ta d'aga kai a
hankali ta kalleshi suka had'a ido da sauri ta mayar da kanta k'asa dama tunda ta shigo haka yake, tsit
kake ji cikin Motar sai Ac dake ta aiki,

"Zaraah" bayan wani lokaci taji ya kira sunanta, a hankali ta amsa mashi,
"Look at me!" d'an cije baki tay da k'yar ta d'aga ido ta kalleshi sai kuma tasa hannu guda tana d'an
murza idanun don bata iya jure ma kallon nashi,

Gently yace "Zaraah what's ur problem??" cikin disasshiyar murya tace "ba komae" d'an ta6e baki yay
kafin yace "in ba komae mi zaisa ki zauna a skul ke kadae after closing hours and kince ma Haulat baki
lafiya bazaki attending Practical class ba ta dawo bata iske ki ba ina kika je da baki tsaya kun tafi gida tare
ba?" d'an runtse ido tay jin yadda sautin muryarshi ke fita yaushe rabon data ji Maganarshi haka,to
miyasa ma yake nemanta da har yaje wurin haulat ta ayyana a ranta, tana cikin haka taji yace ba Magana
yake mata ba, d'aga kai tay ta kalleshi kaman zata sa kuka tace "naje Clinic ne ina can aka tashi lokacin
dana dawo class kuma banga kowa ba shine na kwanta daga baya kuma na fito na zauna anan" duk da ta
d'ago bata kallon idanunshi take Maganar, sigh yay idonshi akanta ya tambayeta mi yake damunta ne
saida tay d'an jim kafin tace cikinta ke ciwo,shiru yay yana nazarinta sai faman sussune kai take,

"Why kika daina zuwa gidan Hajiya??" har saida gabanta ya fad'i jin tambayar da yay mata d'an
d'agowa tay tana yamutsa fuska tace "ai yanzu wani lokacin har yamma muke kai wa saboda lesson da
ake to wani lokacin dana koma nike tafiya islamiyya Weekend ma ina islamiyya" yace "ranar da ba
islamiyyan fa ba zaki iya zuwa ba?"

"Ai wani lokacin in na koman na gaji ne amman ko ranar nan naje Hajiyan bata nan sai Aunty Saude
kadae na iske kai kuma lokacin baka nan" tana k'arasa Maganar ta dukar da kanta don tasan k'arya ta
shirga mashi bata son ya gane kuma tasan bazai ta6a zuwa wurin Saude da sunan ya tambayeta game da
abunda ta fad'a ba shiyasa tace mashi haka,shiru yay na d'an lokaci still kallonta yake,

"About coming to skul in d morning miyasa kike tahowa, in baki so ina kawo ki ne u should tell me sai in
bari ba kisa inata zuwa kullum ba" d'an runtse ido tay ashe bai jin dad'in hakan, dama kawu Amadu
kullum sai ya gaya mata yazo ran Alhamis har yana ce mata kodae ta daure yaci gaba da kai su tunda
yak'i daina zuwa kar yaga kaman ana wulakanta shi tace ita dae a'a bata so, jin tunda yay Maganar bai
kuma cewa komae ba yasa ta d'aga idanu ta kalleshi ashe kallonta yake nan take idanunsu suka had'u
kasa saukesu tay a hankali tace "da..dama an fara yi mana lesson da wuri ne shiyasa muke tahowa
amman kayi hakuri" kawae sai taga yay d'an guntun Murmushin gefe ya jingina kanshi jikin headrest,
yana daga cikin abunda ke burgeshi da ita wato bada hakuri da ta yi mashi ba daidai ba, a da yayi
tunanin harda tsoron yarjejeniyar dake tsakaninsu yasa take saurin bashi hakurin amman daga baya ya
fahimci bashi yasa ba kawae haka take, ganin bai ce komae ba yasa tay tunanin baiyi hak'urin ba a
hankali ta k'ara cewa "kayi hakuri Ya Handsome" daga yadda yake ya k'ura mata ido itama kallon nashi
take tana d'an motsa baki,

"Ya Handsome yayi hak'urin" yay Maganar had'i da lumshe ido da sauri ta kauda fuskarta gefe ita kanta
bata ma san Ya Handsome d'in ta ambata ba tuni take son ta daina kiranshi da hakan amman ta kasa
saboda ta saba bata ta6a kiranshi da sunanshi ba tunda suke, shiru ya biyo baya kowa da abunda yake
sak'awa a ranshi haisam ya d'an d'age kanshi sama gaba d'aya ya yarda da abunda ta fad'a don yasan
bata mashi k'arya hakan yasa ya d'an ji sauk'in damuwar da yake ji game da halin da take ciki wani sashe
na zuciyarshi kuma na izashi akan ya tambayeta dangane da Maganar da Abbas yay saidae bai san ta ina
zai fara ba sai kawae yace mata ance kina sona? ya tambayi kanshi the question sound so silly, juyawa
yay ya kalleta ta juyar da kanta gefe tana kallon waje, hannu ya kai ya fara kokarin jan Motar ta juya ta
kalleshi sai kuma ta sake kauda kan gefe ta d'an ja hijab d'inta ta rufe Fuskarta, tunda suka hau hanya ba
wanda ya k'ara tanka ma wani shi idonshi na akan hanya ita kuma ta rufe fuskar, jin ya tsaya da Motar
yasa ta d'an cire hijab d'in tana kallon inda suke don taji sunyi saurin isowa in dai gida suka zo, idasa cire
hijab d'in tay tana k'are ma harabar da suke kallo lokaci guda ta fahimci inda ya kawota wato Wani
babban private Hospital ne har saida kirjinta ya buga ta juya da sauri ta kalleshi suka had'a ido yace mata
ta fito ya bud'e kopar Motar ya fita, ba yadda ta iya jiki a mace ta bud'e itama ta fita ya tunkari main
entrance na Asibitin ta bi bayanshi walking slowly, yana shiga reception inda Medical records suke ya
nufa dama suna da Family card a Asibitin nan Hajiya ke ganin likita bayan ya masu bayani an shigar da
sunan Fatun suka ce ya kaita Nurses room za'a d'auki BP nata sai a tura su wurin likita ya amsa da Ok,
juyowa yay yayi mata alamar ta biyo shi da hannu suka nufi window d'in da a samanta aka rubuta Nurses
room d'in yana tsayawa kafin yay Magana yaji daga gefenshi an ce "H,Zakee d latest ango to be" juyawa
yay ya kalli mai Magana da fara'a ya furta "Dr habeeb" yana k'araso ya mik'a mashi hannu suka gaisa da
fara'a yace "to ya shirye shirye, ai Abbas ya tura mana iv in sha Allahu damu za'a d'aura Auren" da
Murmushi kan fuskarshi ya amsa da Allah ya yarda,

"Amman miya kawo ka Asibiti ko kana fever d'in angwancewa ne" yar dariya yayi ya nuna mashi Fatuu
yace sis d'inshi ya kawo,ya kai idonshi kanta kafin ya juya kan haisam yace "an tura ta wurin Dr ne?" yace
"No yanzu za'a tura" jinjina kai yay ya lek'a ta windown yace ma Sister d'in dake zaune tay taking BP nata
ta tura mashi ita yanzu ta amsa da "Ok Dr", kallon Fatuu ya sake yi yace ta zagaya ta shiga ciki ta amsa da
to bayan ta gaidashi ta tafi sukuku da ita ta shiga shi kuma suka cigaba da Magana da Haisam yana mashi
complaining kan rashin Network mai kyau da suke fuskanta sai ana cikin aiki ya yanke Haisam d'in ya fara
suggesting abunda yakamata suyi suna cikin haka Fatuu ta fito yace ma Haisam su tafi consultation room
yace Ok, bayan sun shiga Dr d'in ya nuna ma Haisam kujeran dake gaban desk ita kuma Fatuu ta gefenshi
yace ta zauna ya fara lallatsa Computer d'in dake sama kafin ya d'ago da d'an Murmushi yace " yauwa sis
mike damunki ne?" shiru ta d'anyi sai taji dama bata ce ma Haisam ciwon ciki take ba yanzu ba daman ta
canja ciwo, a hankali tace,

"Ciwon ciki ne"

"Ok ciwon ciki wane iri, kina period ne?" damm gabanta ya d'an fad'i duk sai taji nauyin tambayar shima
Haisam dake latsa waya cak ya tsaya hakanan yaji yana son jin amsar da zata ba likitan,

"Ok yaushe kika fara ne?" saidae kawae haisam yaji wannan tambayar ta likita don da kai Fatuu ta bashi
amsar tana yi d'in,

"Shekara biyu" ta fad'a k'asa k'asa,


"To dama duk in zaki kina ciwon ciki ne?" kai ta d'aga mashi alamar eh ya sake cewa "Yanzu shine ya
saki ciwon cikin ko kuwa wani ciwon cikinne daban?" a hankali tace mashi shine duk da k'arya take ba
period d'in take ba yanzu, tambayarta yanayin yadda take jin ciwon yay ta bashi amsa ya jinjina kai kafin
yaci gaba da rubutu a Computer d'in can ya sake kallonta yace bayan wannan ba abunda ke damunta
tace eh, Jama'a ina Haisam? da alama ya k'ame a inda yake saboda tsabar mamakin jin wai Zaraah na
period for good 2 years now abunda bai ta6a zato ba duk da yasan ya ta6a yi mata fad'a kan sakin baki
tana fad'in abu irin haka amman bai yi zaton zata iya rikewa ba tsawon shekara biyu ba tare da ya sani
ba, kallonta likita yay bayan ya gama rubutun yace ta jirasu a waje don ya lura duk bata sake ba ta mik'e
sumimi sumimi ta fice, Doctor ya kalli haisam yace mashi ba wata matsala bace menstrual pain ne ai yaji
ma ya d'aga mashi kai kawae yace yanzu ya tura Magani zasu je pharmacy a amsar mata ya amsa da Ok
yana kokarin mik'ewa Doctor ya dakatar dashi ta hanyar cewa"amm H,Zakee, sis d'in nan naka ba wani
abu dake damunta banda wannan ciwon?" komawa yay ya zauna yana kallon doc d'in yace akwae
matsala ne,

"No,ba wata matsala bace babba just bp d'inta ya d'anyi high gaskiya so bansan ko wani abun na
damunta bane amman zai iya yuwuwa ciwon da take yasa shi hawan is possible" ya k'arasa yana jinjina
kai, shiru Haisam ya d'anyi doc Habib yace kar ya damu zai iya yuwuwa ciwonne amman zai iya
tambayarta yaji in wata damuwarce kar abun yay yawa ya amsa mashi da to suka mik'e tare suka fita
lokacin tana zaune kan dogon bencin dake kallon d'akin ganin likitan suna fitowa ta had'a ido da Haisam
da sauri ta juyar da kanta gefe don yanzu sai taji tana kunyar had'a ido dashi ganin yasan abunda tasan
bai sani ba, shima d'auke kan yay ya bi Doctor suka je

pharmacy d'in aka bata magungunan, lokacin da suka fito bata sani ba saida suka zo saitin inda take
zaune ta d'ago yay mata alamar su je da kanshi ta mik'e da sauri tay gaba, suna fitowa harabar Asibitin
Haisam yace ma doc ya koma shi dake cikin aiki suka yi sallama yay mashi godiya kafin kowa ya juya ai
tana ganin ya nufo Motar ta bud'e da sauri ta shige, lokacin da ya bud'e Motan ya shiga ta juyar da kanta
ta rufe face d'inta da hijab kaman yadda tay da zasu zo, idonshi akan hanya bayan sun fito yana ta
driving bai tanka mata ba saidae can k'asan zuciyarsa he was totally surprise,sai yan tunane tunane yake
lokaci bayan lokaci yake d'aga ido ya kalleta ta cikin Mirror, a daidai gaban wata babbar Super Market ya
parker Motar gefen hanya tana jin sun tsaya ta cire hijab d'in tana kallon inda suke jin ya bud'e Motar
yasa ta waiga ta kalleshi lokacin ya fita daga cikin Motar ya zagayo ta side d'in da take ya nufi cikin wurin
tana ta kallon bayanshi har ya shige ciki taci gaba da kallon wurin, bada jimawa sosae ba ya fito
hannunshi ruk'e da babbar shopping bag mai d'auke da tambarin wurin tana ganin ya taho da sauri ta
k'ara rufe fuskar, back door ya bud'e ya ajiye ledan kafin ya zagaya ya shiga ya ja suka tafi, yana driving
yana cigaba da kallonta ta mirror ba komae yafi tsaya mashi ba face hirar su da Abbas ga kuma Abunda
Doctor Habeeb yace game da BP d'inta,suna shiga layin gidansu ta bud'e fuskar tana kallon gefenta har
suka k'araso kopar gidansu a hankali ta juya ta kalleshi tace mashi ta gode yay nodding kanshi tana
niyyar bud'e Motar taji yace "da yaushe kuke zuwa skul din?" d'an kyakkyafta idanu tay ta d'an d'age
baki tace "da wuri dae muke tafiya wani lokacin k'arfe bakwae ko da yan mintuna" calmly ya furta "Ok"
ta bud'e Motar ta fita ganin tana niyyar nufar gida ya sauke glass d'in ya kirata ta juya tana kallonshi yace
ta d'auki kayan baya nata ne kai kawae ta d'aga mashi ta bud'e ta d'aukko ledar ta lek'a ta gaban tace
mashi ta gode, bin ta da ido kawae yay ta janye kan sai kuma ta kasa tafiya tana ta kallonshi ya ja Motar
ba tare da ya rufe glass d'in ba tabi bayan Motar da kallo, sai lokacin hankalinta ya kai kan wak'ar dake
tashi daga cikin shagon kawu Amadu ta Hamisu breaker wato so dangin Mutuwa,natsuwa tay tana
saurarar baitinkan wak'ar kamar haka,

_🎼🎼🎻So dangin Mutuwa ne shi don baya duba rarrashi so guba ne kama da Madara yake, shi Masoyi
yana da gaggawa buri nay ya yi wa so k'awa shi kuma so kama da kura yake🎼_

_So bai san wata kara ba,bazai ragawa kowa ba,kullum tanadin kushewa yake_🎼

_........So baza ya kyale tsoffi ba, kuma bai tsallake MAKWABCI BA nagane shi illatarwa yake🎼_

Tana jin wannan baitin ta juya da gudu ta shige gida sam shi kawu Amadu bai ma san da ita a wurin ba
yana can yana sauraren wakarshi, tana shiga d'akinta ta nufa ta haye gado tana ta6e baki kwalla suka
fara gangarowa kan cheeks d'inta don sai taji kamar don ita akai wakar can ta jawo jakar da ta shiga da
ita ta zazzago abunda ke ciki, k'amewa tay baki bud'e tana kallon uwar Pads d'in da ya siyo mata dasu
turarurruka kawae sai ta idasa fashewa da kuka, dole ma tay kuka wllh rasa Haisam matsayin Miji ba
k'aramar Asara bace yanzu da bata had'a komae dashi ba ji uwar hidimar da yake da ita ina ga kuma ace
shi Mijinta ne, Mutum ne shi da yasan yakamata wanda ba tantama zai kare hakkokin Matarshi sosae,
haka ta d'ingi riskar kuka har ta gaji don kanta ta tashi duk da kanta na mata wani irin ciwo ta cire
Uniform d'in jikinta ta d'aura towel ta nufi toilet don yin wanka, bayan ta gama shiryawa ta kabbara
sallar Azahar da bata yi ba tana gamawa tabi da La'asar da aka yi bada jimawa ba, bayan ta gama sosae
tayi Addu'oi tana zubar da kwalla ta rok'i Allah in Haisam rabonta ne Allah ya batashi matsayin miji in ba
rabonta bane kuma yasa ta hak'ura dashi,bayan ta shafa ta mik'e jin kanta nayi mata ciwo ta fita taje
d'akin gwaggo ta d'aukko Magani bayan ta sha ta koma kan gado ta kwanta ta fad'a duniyar tunane
tunane ita kanta ta san mawuyacin abu ne ta Auri Haisam ba kamar da ta ji da bakinshi yace baida
ra'ayin mata biyu kawae zuciyarta ce ke takura mata da soyayyarshi, yunk'urawa tay ta tashi zaune a
fusace ta fara buga katifa tana Fad'in "Ki daina takura man don Allah, bai sona, bai sona miyasa kike
azabtar dani da son shi ne!!!" ta k'arasa tana ta huci ta kumbura baki, a hankali kuma ta koma ta kwanta
tana cigaba da hucin da alama zuciyarta ta kaita mak'ura a haka bacci 6arawo yay awon gaba da ita.........

_Dandano Daga Next Page_


.......Da sauri ta runtse idanuwanta tana jin wani abu nayi mata yawo a duk ilahirin jikinta kafin a hankali
kuma ta ware su kan santala santalan hannuwanshi farare tas masu d'auke da zara zaran yatsu ga gashi
liya liya kwance luff,tunda take dashi tsawon lokaci bai ta6a sa hannu ya ta6a jikinta ba sai yau itace dae
ada kan ta girma sosae take ta6a shi shima bazai wuce a kirga ba kaman lokacin da su goga suka so yin
raping d'inta da ya zo ta kankameshi sai lokacin da zai masu hoto a park da kuma ranar salla shima da zai
masu hoto....tana cikin tunanin taji ya kira sunanta a sanyaye, slowly ta d'aga idanuwanta da suka
kankance ta kalleshi cikin ido kaman yadda shima yake kallonta lokaci guda kirjinta ya hau bugawa da
mugun k'arfi shi kanshi k'irjin nashi bugawar yake amman ya daure Calmly yace "tell me what's it??"
k'uri tay mashi ko kyaftawa batayi ya lumshe mata ido alamar ta fad'i mashin, A hankali ta fara motsa
baki alamar zata yi Magana tace"...........TILL MONDAY IN ALLAH YA KAI MAMU RAI.

Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wannan
no 09013804524.

*ASM Bk2012*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

2 Years Back........

Ranar wata Asabar Fatuu ta farka da Safe don yin shirin zuwa islamiyya, tana zuwa toilet don yin fitsari
kawae sai taga jini jage jage a k'asanta, a razane ta fara k'wala ma Gwaggo kira tun acikin toilet d'in
amman shiru gwaggon bata amsa ba sakamakon bacci da take, hannunta ruk'e da k'asan skirt d'inta ta
fito ta nufi dakin gwaggon tana cigaba da k'wala mata kiran, bayan ta shiga d'akin gadon da take kwance
ta nufa tana kiranta a firgice lokacin gwaggon ta farka idonta akanta cikin harshen fulatanci ta
tambayeta lafiya, da d'ayan hannunta tay mata nuni da tsakankanin cinyoyinta gwaggon ta kai idanunta
wurin ta k'ura ido tana kallo, can ta d'ago da alamun damuwa ta kalli Fatun, ganin yanayin fuskarta yasa
Fatun cewa Gwaggo ko jinin hailan ne yazo....."tsit tayi sakamakon kallon data ga gwaggon nayi mata,
can ta mik'e tace mata su je tace to tay gaba tana tafiya a gwaggwale sai kace yar shayi, toilet d'in suka
koma tace mata ta cire kayanta ta wanke wurin da kyau amman banda sabulu sai tayi wanka tace to,
komawa tayi d'akinta ta d'aukko mata towel ta kai mata kewayen tay tsaye a gefe tana jiranta har ta
gama sannan suka nufi ciki tare tace ta shiga d'akinta tana zuwa, d'akinta ta koma ta samo mata wani
yankin kallabinta mai tsabta da taushi ta koma d'akinta, lokacin da ta shiga Fatun na zaune gefen gado
sai wuwwurga ido take ta mik'a mata tace "ki amfani da wannan ki tare kafin in fita....." tun kan ta
k'arasa Fatun ta turo baki tace "kam gwaggo pad fa ake sawa ba tsumma ba",

a harzuke tace "to banda shi, baki ji nace kafin na fita ba in siyo maki tunda Amadu bai sayar da ita" tana
tura baki tace " to ko cikin taki ne ba sai ki ban ba...." tun kafin ta k'arasa gwaggon takai hannu zata
make mata baki tana Fad'in bari ta buge bakin maras kunya tunda tayi da ita tana amfani dashi, da sauri
ta goce lokacin kuma taji wani abu ya zubo mata ta d'an d'aga towel d'in ta lek'a gwaggo tay tsaye tana
kallon ikon Allah, a firgice ta d'ago tace "gwaggo gashi nan ya zubo da yawa!" tsoki ta ja ta juya ta nufi
wardrobe d'inta ta d'aukko mata pant ta dawo ta bata tace ta tashi tasaka in ta gama tasa kaya tace to
gwaggon ta juya ta fice, bayan ta gama shiryawa cikin doguwar riga ta d'auki towel d'in da hannu d'aya
cike da kyankyami ta nufi d'akin gwaggon lokacin tana zaune gefen gado da alama Al'amarin ya jefata a
damuwa,

"Gwaggo wannan yadda shi zanyi ne jinin ya 6ata shi" ta Fad'a tana d'age baki,wani kallo mai kaman
harara gwaggo ta bita dashi kaman bazata tanka mata ba sai kuma tace "tunda baki da hankali ai sai kije
ki yadda d'in",

"To ya zanyi dashi"? Ta tambaya kaman zatayi kuka,gwaggon tace " kije ki kama wurin ki wanke shi
tass ki shanya"

Tura baki tay tace "Kai gwaggo bafa jinin yankewa bane baki ga daga inda yake fitowa ba kuma sai kice
in wanke" banza tayi mata tana harararta hakan yasa ta juya tana d'an k'unk'uni taje ta wanke gwaggo
na jinta zata shiga d'aki ta kwala mata kira tazo d'akin, nuna mata k'asa tay tace ta zauna tayi zaman cin
tuwo tay mata k'uri da ido,saida ta d'an dauki lokaci suna kallon juna kafin ta fara Magana "ina son in
gargad'e ki game da wannan abun da kika fara saura kije ki bud'e baki kina shelar kin fara Al'ada don
kina yin hakan zai d'auke ya daina zuwa kwata kwata kuma mace bata haihuwa in bata yin shi don haka
in dae baki son ya d'auke to kija bakinki kiyi shiru" tana dakatawa Fatun tasa hannu ta kama lips d'inta
alamar bazata fad'i ma kowa ba sai kuma ta cire hannun da d'an murmushi tace "ashe dae shine kenan
yanzu na balaga ko?" kai kawae gwaggon ta d'aga mata,

"Wayyo, yanzu dole in rink'a yin Azumi duka kenan, amman dae ai in ana yin shi ba'a azumin da salla
ko?" ta wurga ma gwaggon tambaya nan ma kai ta d'aga mata, kafin taci gaba da cewa "sannan zan kara
gargadinki, Fatuu ba ruwanki da maza, nasan halinki sarae amman ki k'ara kiyayewa kar ki yarda wani
yay maki wayo yay maki abunda bai dace ba don yanzu tunda kin fara Al'ada to ko hannunki Namiji ya
kama zaki samu juna biyu ne"? Zaro idanu tayi a tsorace tace "cikin shege irin na d'iyar yar wajen aikin
ku?" kai nan ma ta d'aga mata a tsorace ta fara girgiza kan tace "to bazan bari ba gwaggo ai kinga dae
koda Bello na gidansu Umar ya kama man hannu can da dad'ewa har na falle shi da mari ai na gaya maki
ko?" kai ta d'aga tace "eh kin gaya man amman yanzu kar ma ta kaiga kin bari an kama hannun" da sauri
tace "toh",

"Sannan sai kin dage da yin tsafta don in Mutum bai kula da ya je kusa da Mutane za'a ji yana wari, ki
rink'a yin wanka akai akai, kina saka turare amman ba wai in zaki fita ba don ba kyau a jikinki zaki d'an
rinka fesawa ki shafa na shafawa....." katseta Fatuu tay da fad'in "harda can wurin da yake zubowar?"
girgiza kai tay a'a sai bayan kin kimtsa kin rufe sai ki shafa, kuma ba ta6a Al'qurani har sai kin samu
tsarki...."

"To harda Hadisai ba'a ta6awa?" kai ta girgiza mata alamar a'a, haka taci gaba da fad'i mata
Abubuwan da ya kamata tayi da wanda bai kamata ba, koda Haulat taje islamiyyar bata ga Fatun ba
hakan yasa da yamma ta biyo mata lokacin gwaggo bata nan tace mata ita bata lafiya bazata ba taje
kawae koda ta tambayeta miya sameta bata fad'i mata ba tace ita dae bata lafiya kawae taje haulat d'in
tay tunanin ko bata son zuwa ne kawae tay tafiyarta sai bayan Magrib gwaggon ta dawo tayo mata
siyayyar su pads da panties duk da tana da su harda turare, Washe gari kuma da ciwon ciki ta farka ta
d'ingi bullayi duk da ba wani ciwo bane na tashin hankali amman ta dingi raki har tana ce ma gwaggon
ita dae in haka zata ci gaba to gwara ya d'auke kawae ta huta gwaggon dae tay banza da ita iyakar sannu
kawae take mata da kyar bacci ya d'auketa bayan gwaggon ta bata Magani, Washe gari kuma data tashi
ba ciwon har ta tafi Makaranta, sai ga Fatuu ta zama kamar kwad'o bunu bunu sai ta tafi tayo wanka ita
don kar aji tana wari haka ta dingi 6arnar pads sai da gwaggo ta ankare ta tambayeta yadda akai tace ai
sau biyar take wanka har saida taba gwaggon dariya tace wannan ai sai sanyi ya kamata tace mata sau
ukku zata rink'a yi Safe da Rana da Dare tace to, sati d'aya tayi tana yi kafin tayi wankan tsarki don an
koya masu a islamiyya ta iya kuma gaba d'aya da tana jinin bata je islamiyyar ba, sai da ya k'ara dawo
mata ne wani watan lokacin suna Makarantar boko ta fara ciwon Haulat ta kaita Clinic anan tasan Fatun
ta fara period d'in bayan sun fito ta fara mata tsiya tana ashe su Fatuu girma yazo shiyasa aka k'ara
hankali ita dae banza ta mata tana ta kanta, ko su Hajiya sai da Azumi ya zo ne suka san ta fara Period
d'in sosae ta ja bakinta tay shiru saboda Abunda gwaggo tace mata.Wannan kenan game da yadda Fatuu
ta fara Menstruation.

*** **** *****

Ranar Monday da wuri ya fara shirin zuwa aiki before k'arfe bakawae na Safe ya shirya tsaf ya fito ko
part d'in Hajiya bai je ba don yasan ba lalle in ta tashi ba, Parking Space ya nufa ya hau Mota ya fice daga
gidan su Officer na mashi a dawo lpy, daidai gaban gidansu Fatuu ya parker motar lokacin k'arfe bakwae
tay daidai ya danna horn sai da yay kusan sau hud'u sannan saiga Amadu ya fito da alama ma daga bacci
ya taso yana isowa bakin Motar ya sauke glass da Murmushi Amadu ya gaishe dashi ya amsa yace ya kira
mashi Zaraah yace to ya juya don yasan bata tafi ba tunda bata yi mashi sallama ba, lokacin daya je
d'akinta ta gama shirinta tsaf zata tafi yace "ke kije ga Romeo d'inki can yazo" wani kallo tay mashi cikin
rashin fahimta tace waye romeo yace mata Ya Haisam yana jiranta a waje daga haka ya juya, sototo tay
ita sam bata yi tunanin daya tambayeta time d'in da suke tafiya zuwa zai yi ba, tura baki tay ta d'auki
jakarta taje tay ma Gwaggo sallama kafin ta nufi hanyar wajen kaman an mata dole, lokacin data fita ya
rufe glass d'in side d'inshi hakan yasa ta zagaya ta bud'e gaban ta shiga kafin ta rufe,d'an juyawa tay ba
yabo ba fallasa ta gaishe dashi ya amsa fuskarshi a d'an sake kafin yace mata ya jiki tace mashi da sauk'i
daga haka ya ja Motar suka tafi, lokacin da taje gidansu Haulat bayan ya tsaya fuskarta kaman zata yi
kuka Haulat ta tambayeta lafiya tace ba Ya Handsome ne bal yazo zai kaisu,

"To shine na d'aure Fuska haka keda Ya Handsome d'inki" wani kallo ta jefa mata kaman zata kai mata
bugu Haulat d'in tay yar dariya tace "yi hakuri wasa nike maki amman yakamata ki saki ranki don Allah"

"To nifa nace banson ganinshi sai ciwon yay ta k'aruwa kuma ni so nike in daina jin abunda nike ji" tay
Maganar kaman zata saka kuka,

"Kar ki damu zaki daina ji ki dawo kamar da bada jimawa ba, da kin daina ganinshi in ya tafi" shiru
kawae tay sam bata son kuma jin zancen tafiyar nashi, bayan sun koma wurinshi suna shiga Motar
Haulat ta gaidashi ya amsa kafin yaja suka tafi kaman dae kullum Fatun bata Magana sai ma juyar da
kanta da tay gefe,bayan sun isa tana shirin fita ya tambayeta lokacin da zasu tashi tace sai da la'asar ya
bata kud'i tay kaman bazata amsa ba sai kuma ta amsa tay mashi godiya ta fita lokacin Haulat ta fita tana
jiranta suka wuce aji. Da la'asar kuwa sai gashi ya dawo d'aukarsu har saida Haulat taji hakanan ya bata
tausayi, Washe gari talata ma da wuri ya shirya yaje d'aukarta yana yin horn biyu sai ga Amadu ya fito
bayan ya gaishe shi yace "aikuwa wai ta tafi" shiru yay yana kallonshi kafin yace "U mean ta tafi skul en?"
Amadu yace mashi eh yanzu da yaji horn yaje d'akinta don yayi mata Magana ya iske bata nan shine ya
tambayi gwaggo tace ta tafi,jinjina mashi kai yay yace mashi "thanks" Amadun yay mashi a dawo lpy ya
juyo ya koma gida, zaune yay baija Motar ba yasa hannu guda ya ruk'e ha6arshi yana d'an bugun
bakinshi da index finger dinshi wondering why Zaraah ta canja ne lokaci guda, nan take zuciyarshi ta
bashi amsa da she loves u dat's why,d'age kanshi yay sama ya runtse idanunshi tunanin Maganganun
Abbas ya shiga yi ga kuma Maganar Dr Habeeb na bp d'inta da ya d'anyi high hakan na nufin he's
responsible for everything, sigh yay ya bud'e idanun a hankali ya kai hannu ya ja Motar ya tafi abun nata
mashi yawo a Zuciya, lokaci guda yaji yana son ya tambayeta game da hakan saidae tunaninshi in da
gaske Zaraah son shi take ya zaiyi?? A haka har ya isa wurin aiki ba tare da ya samu solution akan hakan
ba. Da La'asar Fatuu ta dawo saida taci Abinci sannan ta shiga wanka bayan ta fito ta fara shirin islamiya
hakan yasa ta d'an Makara, sanye cikin Uniform ta fito lokacin shagon kawu Amadu a rufe yake don
shima yana Makaranta bai dawo ba, saura kad'an ta isa bakin lungun gidan Hajiya da zata karya kwana
sai ga Haisam ya taho a kan bike d'inshi zaije gym hakan yasa ta ja ta tsaya shima tsayawar yay lokacin
har ya d'an wuce ta don ma ba gudu yake sosae ba, baya yayo da bike d'in ya dawo gabanta suka fara
kallon kallo duk da fuskarshi na acikin Helmet amman tana ganin idanunshi lokaci guda taji ta tsargu da
kallon da yake mata a hankali ta kai hannu d'aya ta d'an kama gefen hijab d'inta tana d'an matsawa
yadda zata hau kan kwanar sosae nan take ya gane abunda take shirin yi wato guduwa har saida ya
d'anyi guntun Murmushin mamaki ta ciki ba tare data gani ba wato dae ita bata da ranar girma, hannu
ya kai ya cire Helmet d'in daga kanshi hakan yasa ta tsaya tana kallon fuskarshi ba ko k'yaftawa shima
kallonta yake a kausashe yace "kina ruguwa zan biki in take ki!!" zaro idanu tay da alama ba k'aramar
razana tay da jin abunda ya fad'an ba don bata ta6a tunanin zaice zai mata hakan ba, still idanunsu na
kallon juna k'irjinta na bugawa da sauri da sauri yayin da shi kuma yake nazarinta, can ta kasa jurewa ta
duk'ar da kanta ba zato kawae sai ganin kwalla yay na d'iga kan hijab d'inta hakan kuma ya k'ara
tabbatar mashi da abunda yake son ganewa hakanan ba yadda za'ai don yana kallonta ta kama yin kuka
gashi sam a can baya bata jin nauyin had'a ido dashi yarinyar dake mashi k'uri da ido,

"U can go" taji cool voice d'inshi ta fad'a,aikuwa ko kallonshi bata yi ba ta juya da sauri ta tafi saida ta
d'anyi nisa ta waigo yana nan bai tafi ba juyawa tay taci gaba da tafiya ba tare da ta sake juyowa ba har
sai da ta kai k'arshen lungun ta sake waiwayowa still he's there da sauri tasha kwana ta shige sai lokacin
ya maida Helmet d'in ya ja bike d'in ya tafi,koda taje islamiyyar tunaninshi kawae take duk in ta ganshi
sai zuciyarta ta k'ara rikice mata komae ya dawo mata sabo Haulat na lura da ita don ta rigata zuwa
saidae yanzu har ma ta saba da ganin Fatun cikin irin halin don tasan tatsuniyar gizo bata wuce ta k'ok'i.

Bayan sallar isha lokacin da Haisam ya dawo ya tsaya bakin shagon Amadu yana ganinshi ya fito yaje
wurinshi ya gaishe dashi bayan ya amsa yace yaje yace ma Zarah yana nemanta yanzu a part d'inshi ya
amsa mashi da toh ya juya da sauri, lokacin da ya shiga tana parlor ita da gwaggo ta tasa Abinci a gaba
tana d'an tsakurarshi, a bakin kopar parlon ya tsaya yace "Ke kije Ya haisam na kiranki ya wuce yace ki
iske shi a part d'inshi yanzu" daga haka ya juya ya koma, lokaci guda gabanta yay wani irin bugu ta fara
tunanin miyasa zai kirata a cikin ranta,ganin bata da niyyar tashi yasa gwaggo cewa "to ki tashi ko kyaje
ki dawo dare nayi in kin dawo kya ci Abincin ki sauri" ido tabi gwaggon dashi lokacin ta mayar da idonta
kan TV dama kallo take, a sanyaye ta mik'e ta fita hannunta ruk'e da plate d'in Abincin ta mayar kicin
kafin ta koma d'akinta ta daukko mayafi ta d'aura akanta ta tafi, tunda ta tunkari gidan zuciyarta ke
harbawa ji take kaman ta rusa ihu, lokacin data k'arasa part d'in nashi a hankali tasa hannu kan handle
din ta d'an turo kopar ta leka ganin bai ciki yasa ta idasa shiga ta tsaya bakin kopar tana kallon cikin falon
yaushe rabon da ta shigo,rasa yadda zatayi ta sanar dashi tazo tay hakan yasa tayi tsaye ta kasa
k'arasawa ciki balle taje bakin Corridor kaman yadda take mashi a da,tanata tsaye ba tare data zauna ba
can taji fitowarshi da sauri ta kai idanunta kanshi da alama wanka yayo yana sanye da jallabiya Maroon
mai gajeran hannu ganin ya nufo cikin falon yasa ta sunna kanta kasa,kan L-shape yaje ya zauna idonshi
a kanta ganin tak'i kallonshi yasa yace taje ta Zauna yana nuna mata bangaren da armchairs suke kaman
bazata ba sai kuma ta nufi ciki kaman wadda kwai ya fashe mawa a ciki, kujera ta biyu taje ta zauna ta
yadda suna da d'an nisa dashi shiru ya biyo baya kanta na k'asa tana wasa da yatsunta shi kuma ya zuba
mata ido yana kallonta ya ma rasa ta ina zai fara mata Magana don yasan ba lalle ma ta fad'i mashi
gaskiya ba kaman sauran lokutta,can ya tuna da bata ta6a yi mashi Maganar auren da zaiyi ba nan take
ya samu ta inda zai fara,
"Zaraah" taji muryarshi ta sauka a kunnanta a hankali ta amsa ba tare da ta d'ago ba, ya k'ara cewa
"Zaraah look at me" jimm ta d'anyi kafin slowly ta d'ago idanun ta sauke su akan fuskarshi,

"Dama ina son tambayanki ne baki san zanyi Aure ba?" motsa baki ta fara yanayin fuskarta ya canja
amman ta kasa cewa komae har saida yace bata ji mi yace bane sannan kaman zata yi kuka tace ta sani,

"Ok, ain't u happy for me shiyasa baki nuna man kina taya ni murna ba?" kaman zata saka kuka tace
a'a tana taya shi murna,

"k'arya kike Zaraah baki tayani farinciki zan yi Aure!" taji ya fad'a da d'an d'aga murya, girgiza kai ta fara
idanunta har sun ciko da kwalla ta fara rantsuwar tana tayashi farinciki sai kuma tasa mashi Kuka, d'an
guntun Murmushin gefe yay still kallonta yake Wannan yawan kukan kawae ya isa ya bayyana akwae
abunda take 6oyewa,

gently yace "Zaraah tell me what's ur problem mike damunki ne"? Cikin sigar lallashi yay mata Maganar,
kallonshi tay fuskarta shabe shabe da hawaye tace " ba komai Ya Ha...." bata samu damar k'arasawa ba
sakamakon buga hannun kujerar da yake zaune yace "U'r not telling me d truth Zaraah! Enough of all
these lies kinsan bana son k'arya just tell me why u been acting strange! Ba haka nasanki ba, u are not d
Zaraah i ave known!" zare ido tay tana kallonshi yana Maganar a harzuke sak kaman ranar da yayi ma
Farha fad'a da tayi mata gori yanzu ma da gani ranshi a 6ace yake yay mata Maganar,

"Am all ears Zaraah, mike damunki?" ya sake tambaya bayan ya d'an sassauta muryarshi ta rasa yadda
zatayi sai kokonto take a cikin zuciyarta na ta gaya mashi ko karta gaya mashi, ganin ya kafeta da ido
yasa ta fara motsa baki a hankali cikin Muryar kuka tace" Ba abunda ke damuna" yaraf ya maida
bayanshi ya jingina da kujerar yana cigaba da kallonta ya kankance idanu ita kuma tana ta faman
sussuna kai da gani yasan ba gaskiya ta fad'i mashi ba sigh yay calmly ya furta "u can go" aikuwa da sauri
ta mik'e ta nufi hanyar fita saidae tana kaiwa bakin kopar sai ta kasa bud'ewa ta fice sakamakon ganin
6acin rai k'arara da tayi akan fuskarshi, kamar an zare mata laka ta juya ta kalleshi ya d'age kanshi sama
idanunshi a rufe, slowly ta juyo ta dawo ta durkusa a gabanshi cikin muryar kuka tace "Don Allah YA
HAISAM kayi hakurii....." kawae sai ta fashe da matsanancin kuka ta duk'ar da kanta k'asa,yana daga
yadda yake yay wani guntun murmushi jin sunan data kirashi dashi wato HAISAM wanda tunda suke bai
ta6a jin ta kirashi da hakan ba,shiru bai dago ba still idanunshi a rufe suke yana sauraran sautin kukan da
take yi , sosae take kuka harda sheshsheka her tears trickling down, a hankali ya d'ago da kanshi yana
kallon kanta da rabinshi ke a bud'e sakamakon zamewa da gyalen yay cikin wata kalan murya da bata
sanshi da ita ba ya kira sunanta ba tare data kalleshi ba cikin kuka ta amsa yace "Look into my eyes
Zaraah" a hankali ta d'ago idanunta sunyi jawur ta kalleshi still kukan take saidae ta d'an rage sautinshi,
tunda yake bai ta6a jin zullumin a fad'a mashi wata Magana ba kamar yanzu saidae ya za6i yaji koma
miye da ganinta cikin halin damuwa haka, shi Mutum ne mai damuwa da damuwar wani ba kuma kamar
ita da yake ganin shine silar damuwartata in hasashen da suke ya tabbata,
"Ki fad'a man abunda ke damunki Zaraah, why the sudden change?" bin shi da ido kawae take tana d'an
motsa baki had'i da had'iyar yawu, yaci gaba da cewa "am not Happy seeing u like dis, am not at all" yay
Maganar yana d'an girgiza kai alamar tabbatar mata da bai jin dad'in ganinta cikin wannan halin,tsam ya
mik'e ya bi ta gefenta ya wuce, tissue box ya d'aukko ya dawo inda ya tashi tana ta dai kallonshi ya yago
mai d'an yawa ya mik'a mata ta amsa ta fara goge fuskarta ya aje box d'in a hannun kujerar kafin ya juyo
fuskarshi a sake cikin muryar lallashi yace "now tell me, kina da damuwa ko??" tsayawa tay da goge
fuskar ta d'an bud'a baki a hankali ta jinjina mashi kai alamar eh, sauke boyayyar ajiyar zuciya yay ya d'an
gyara zamanshi ya nuna mata close to him yace tazo ta zauna har saida ta kalleshi da sauri ganin wurin
da ya nuna matan ya d'an lumshe mata ido ganin hakan yasa ta mik'e ta nufi Kujerar saidae bata zauna
gab da shi d'in ba ta d'an matsa kad'an,juyowa yay ta yadda zai facing d'inta sosae ya fara bin ta da wani
kalan kallo da sauri ta sadda kanta k'asa ba zato ba tsammani kawae taga ya kawo hannuwanshi ya kama
nata hannuwan, da sauri ta runtse idanuwanta tana jin wani abu nayi mata yawo a duk ilahirin jikinta
kafin a hankali kuma ta ware su kan santala santalan hannuwanshi farare tas masu d'auke da zara zaran
yatsu ga gashi liya liya kwance luff,tunda take dashi tsawon lokaci bai ta6a sa hannu ya ta6a jikinta ba sai
yau itace dae ada kan ta girma sosae take ta6a shi shima bazai wuce a kirga ba kaman lokacin da su goga
suka so yin raping d'inta da ya zo ta kankameshi sai lokacin da zai masu hoto a park da kuma ranar salla
shima da zai masu hoto....tana cikin tunanin taji ya kira sunanta a sanyaye, slowly ta d'aga idanuwanta
da suka kankance ta kalleshi cikin ido kaman yadda shima yake kallonta lokaci guda kirjinta ya hau
bugawa da mugun k'arfi shi kanshi k'irjin nashi bugawar yake amman ya daure Calmly yace "tell me
what's it??" k'uri tay mashi ko kyaftawa batayi ya lumshe mata ido alamar ta fad'i mashin, A hankali ta
fara motsa baki alamar zata yi Magana amman ta rasa ta ina zata fara, jinjina mata kai yay idanunsu cikin
na juna ta sake bud'e baki _"Ya Haisam I luv u, I want u to Marry me pls......................._

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wannan
no 09013804524._

*ASM Bk2013*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


.........Ganin ta zuba mashi Ido tak'i cewa komae gashi kuma tana son tay Magana yasa ya d'an matsa
hannuwanta da har lokacin yake ruk'e dasu, firgit tay ta dawo daga zancen zucin da take ta d'aura
idanunta kanshi lokaci guda Maganganun su Haulat da Kawu Amadu suka fara mata yawo a kai, gaba
d'ayansu Maganganunsu iri d'aya ne kowa cewa yake Kota gaya mashi Hakuri zai bata kuma zai daina
ganin k'imarta ga kuma Maganar da ita kanta taji ya Fad'a da Bakinshi na baya ra'ayin mata biyu ga kuma
zancen kwanciyar Fanan Asibiti don yace bazai Aureta ba to ita ma kenan da take yar uwarshi yace bazai
Aureta ba inaga ita da bata had'a komae dashi ba, lokaci guda tsoron fad'i mashi gaskiya ya kamata
murya na rawa tace "da..dama banji dad'i ba zaka tafi don baka ta6a fad'a man zakai Aure ba shiyasa
duk na damu" shiru tay ta sunkuyar da kanta don kar ya gane k'arya take, sigh yay ya saki hannuwanta ta
jingina gefen jikinshi da kujera,tabbas bata yi k'arya ba bai ta6a Maganar Aurenshi da ita ba a tunaninshi
baiga Amfanin yin wannan zancen da ita ba, nisawa yay Calmly ya fara Magana "am really sorry about
dat Zaraah,u know Fanan is my sis so a hakan naci gaba da d'aukanta though we were engaged,ina ganin
bashi da wani muhimmanci in ta Maganar aure tunda lokacin bai yi ba not knowing hakan zai iya zama
matsala......" da sauri ta katseshi tace "a'a Ya Haisam ba wani abu bane kawae nayi zaton Maganar da
muka ta6a yi da kai na zamu rayu tare gaskiya ne banyi zaton zakai aure ka tafi ba kwata kwata shiyasa
banjin dad'i" zuba mata ido yay yana kallon yadda take Maganar fuskarshi a sake, nisawa yay cikin cool
voice d'inshi yace "am so sorry Zaraah i caused u worries, amman don nayi aure ai ba yana nufin zamu
rabu ba, mun zama family now ko bananan zamu kasance a tare hakan is so simple ko kin manta miye
aikin Yayanki ne?" shiru tayi tana bin shi da ido hakanan sai taji ta samu wata irin Natsuwa,

"We're leaving On Friday so ki shirya zamu tafi tare" taji ya fad'a, d'an far far tayi da idanu yanayin
fuskarta ya canja ita dae bata son zuwa bikin hakan yasa ta fara tunanin mafita ganin haka yasa yace
mata taji abunda yace ta bud'e baki cikin disasshiyar Murya tace "ai bazan samu zuwa bikin ba" wani iri
yaji Maganar har saida ya taso ya zauna daidai ya tambayeta dalili, tace "Saboda Next week zamu fara
papers d'in Practical kuma ran Friday d'in da ake Auren ranar zamu fara jarabawar gaba d'aya" da k'yar
ta samu ta gama Maganar saboda faduwar da k'irjinta yake don tasan k'arya ce take shirga mashi sai
Upper Week zasu fara jarabawar ma,shiru yay fuskarshi da experassion dake nuna baiji dad'in Maganar
tata ba don ya yarda da duk abunda ta fad'a nan take ya k'ara yin tunanin harda hakan yasa ta damu
sosae, cikin muryar lallashi yace "Ok, but banji dad'in hakan ba best friend d'in Groom bazatay attending
ba" d'an tura baki tay jin ya kirata da best friend hakan yasa ya d'anyi Murmushi kafin yace "u shouldn't
worry about dat ki maida hankali kan karatu sosae don ki passing exams and Maganar biki da komae in
kinaso zaki ga komae live koda baki je ba i can arrange dat for u" d'an bud'a ido tay alamar mamaki da
d'an Murmushi yace "ko baki so?" a sanyaye tace "amman ai hakan sai an kashe kud'i ko, ace komae na
bikin zan rink'a gani" yar dariya yay ya koma ya jingina yace "to dama ba don a kashe su ake nema ba?",

tace "to ai kaida kake da hidima"


"Wannan ai angama komae kinga sauran kud'in sai akashe kawae" d'an yamutsa fuska tay tace "to
amman ai ba iya hidiman bikinne ba kawae in aka yi Amarya ma kud'i ake kashewa sosae in kuma suka
k'are ya zaka yi" sosae yake jin dad'in yadda take mashi Magana, d'an bud'a ido yay yace "still bayan
uban kud'in dana kashe kuma in akayi auren ma sai na kashe wasu to mi kuma za'ai dasu kenan?" tura
mashi baki tay tace "Kayan dad'i ake siya su kaza....." cak ta dakata don ita kanta sai taji she sounds
foolish, ganin kallon da yake mata yasa ta yamutsa fuska kaman zata sa kuka kawae sai taga yasa dariya
har fararen hakoransa sun bayyana da sauri tasa bayan hannunta ta rufe fuskarta tana yamutsa baki
alamar zatayi kuka, a cikin ranshi ya ayyana wannan itace zaraah da ya sani a fili kuma sai cewa yay
"Zaraah ko kina son cin kaza ne?" da sauri ta bud'e fuskar kaman zata yi kuka tace "nifa bason ci nike ba,
ai haka ake yi ko in akayi aure aita cin kayan dad'i" dariyar ya k'ara yi ya d'age kanshi yana kallon sama
da alama dai ba k'aramin dadin firar yake ji ba ita kuma sai kallon fuskarshi take abubuwa na mata kai
kawo a cikin zuciya, juyowa yay suka had'a ido da Murmushi yace "kar ki damu da wannan ai itama
Amaryar tana da kud'i sai ta d'auki nauyin wannan ni kuma zanyi ma beloved sis d'ina what would make
her happy da nawa" d'an Murmushi tayi tace ba sai yayi hakan ba in su gwaggo suka dawo ta ga komae a
wayan a Kawu Amadu dan ta6e baki yay yace "Ok in hakan yayi maki, but kema yakamata by now kina
da Waya", tace "ai gwaggo bata son in ruke wayan tace sai zan cigaba da karatu sannan" shiru ya d'anyi
sai kuma yace mata to taya zasu rink'a communicating in ya tafi tace ko ta kawu Amadu ko ta gwaggo,

"No, suma suna da uzurinsu bai kamata a takura su ba, ba kaman Uncle d'inki shima yanzu yana karatu
dole yana using phone d'in sosae so i will talk to her ta bari ki rike" jinjina mashi kai tay don tana son
dama itama ta fara ruk'e wayar, can kuma sai tace "Nagode Allah ya saka da Alkhairi ya baku zaman
lafiya da zuria nagari" d'an bud'a ido yay da Murmushi ya amsa da Ameen idonshi akanta yace "kinma
tuna man kince inna yi aure matana ta haihu zaki rinka goya baby d'in ki mashi wasa right??" hannu tasa
ta rufe baki tunawa da lokacin da tayi Maganar sai kuma ta cire ta yarfa hannuwa tace "to ai ba anan
zaku zauna ba dana yi hakan?"

"To ko in tafi dake??" waro ido tay baki bud'e tace "kasar wajen?" lumshe ido yay ya jinjina mata kai
yace "sai kiyi karatun likitan acan" da sauri ta girgiza mashi kai tace "a'a so kake Aunty Fanan tace na lik'e
ma mijinta ta koro ni a wurgo ni Nigeria gwara in zauna nan in yi karatuna kuma ma ni banson in rabu
dasu gwaggo" sigh yay still da Murmushi kan fuskar tashi yace mata Fanan bazatayi mata hakan ba ta
d'an ta6e baki tace "uhmm ya haisam baka san kishin mata bane idon mutum rufewa yake kuma ita
nasan zata yi kishinka sosae" ita kanta bata san ya akai ma tayi Maganar ba ganin ya zuba mata ido yasa
ta sha jinin jikinta kamar daga sama taji yace ya akai tasan zata yi kishi sosae a dabarbarce tace "kawae
naga tana sonka ne sosae" tana kai Maganar ta sunnar da kai, jin bai k'ara cewa komae ba yasa ta saci
kallonshi kawae sai taga ita yake ta kallo hakan yasa itama ta taci gaba da kallon nashi sun d'an d'auki
lokaci haka kafin ya janye idonshi ya kai hannu ya shafi forehead d'inshi Calmly yace "last Sunday i need
help to park my stuff nace da Zaraah bata gujeni ba nasan zata man wannan" taji fada a tausashe d'an
murmushi tay tana tura baki tace "ni fa ba gudun ka nai ba" ya d'an ta6e baki taci gaba da cewa "to in
kana so sai in tattara maka ko gobe ko kuma yanzu inje in fad'i ma gwaggo sai in dawo in had'a maka"
shiru yay yana kallon yadda take Maganar har saida tace mashi "kaji" sannan yace "TK have done dat"
gyad'a kai tay still da d'an Murmushi akan fuskarta yace "sarkin kuka kawae" dariya tayi wannan karon ta
kai gefen jikinta itama jikin kujerar kaman yadda yayi,

"Pls Zaraah bana son irin damuwar nan, when u have problem just feel free to tell me" yay Maganar
yana tabbatar mata da abunda yace da kanshi ta d'aga mashi kai alamar to, kawae sai taga ya mik'o
mata dogon yatsanshi manuni bin shi tay da kallo tun kafin tace wani abu yace "Promise zamu k'ulla
bazaki k'ara shiga damuwa haka ba" nan take ta gane dalilin da yasa yayi hakan wato abunda ta ta6a yi
mashi a Mota akan rashin cin abinci data ce su kulla Alkawari in yaje wurin aiki zai ci tunawa da hakan
yasa tasa dariya sosae har gyalenta ya idasa zamewa shima dariyar yake yak'i janye hannun alamar sai
sun k'ulla cikin dariyar tace mashi ba sai sunyi hakan ba wato amsar daya bata a lokacin itama ta bashi,
sosae yaji dad'in ganin ta warware dama da biyu yayi hakan, wayarshi ya d'auka ya duba time lokaci
guda ya mik'e yace mata yana zuwa ta d'aga mashi kai ya nufi hanyar beedroom ta bishi da kallo, yana
shiga Corridor ya d'ago mata hannu ba tare daya juyo ba alamar yasan kallonshi take Murmushi kawae
tay ta maida kanta ta kwantar jikin kujerar cikin ranta take ayyana shikenan ta dae rasa Ya Handsome
saidae kuma ta wani bangaren taji dad'i sosae yadda ya damu da ita,bata yi tunanin yana ganiyar
angwancewa ba zai wani damu da damuwarta haka dan Murmushi tayi kawae, bada jimawa ba ya fito
hannuwanshi duka biyun ruk'e da manyan Akwatuna Maroon color da ratsin baki sun matuk'ar yin kyau
da gani kuma ba sai an fad'a ba masu kudi ne sosae ya nufo cikin parlon ya aje a gabanta kafin ya sake
komawa ya d'aukko wani madaidaici kaman trolley mahad'insu yana zuwa yace tayi amfani dasu tana
kallonshi tayi mashi godiya yace mata ta tashi suje ya rakata ta mik'e, manyan da ya fara kawowa ya
d'auka yace ta d'aukko k'aramin tace shi ya d'auka ya bata babba d'aya ganin abun zai zamar masu
gardama yasa ya bata na biyun ya d'auki k'aramin suka tafi.

Lokacin da suka je gidan atare suka shiga tana gaba yana biye da ita da sallama ya shiga saidae ba'a amsa
ba Fatuu tace ya shigo suka shiga Falo kowa ya aje akwatin hannunshi kafin suka zauna sai kuma ta mik'e
tace bari tayi ma gwaggon Magana ya d'aga mata kai,a daki ta isketa ta bud'e wardrobe tana shirya kaya
tace mata ga Ya Haisam yazo tace to ta dakata da abunda take tabi bayanta suka nufi falon, da fara'a ta
shiga ta zauna kan kujera ya gaishe da ita ta amsa tace mashi ya shirye shirye shima ya amsa mata da
Alhamdulillah, bayan sun gama gaisawan Fatuu ta nuna mata akwatinan dake aje gefe tace gashi nan ya
bata, hannu gwaggo tasa ganin dandatsa dandatsan akwatinan kafin ta kalleshi tace "d'ana Haisam baka
gajiya ne, haka aka cika Amadu da kaya ran lahadi Tukur ya kawo mashi" da d'an Murmushi yace mata
"ba wani abu" Addu'oi ta shiga yi mashi yana amsawa a hankali can ta mik'e tace bari ta zubo mashi
Abinci ba tare data jira cewarshi ba ta fice, bada jimawa ba ta shigo ruk'e da babban tray ta d'auro plate
d'in abincin rufe da wani ta aje Fatuu ta mik'e ta nufi Fridge ta d'aukko mashi ruwa da lemu ta aje mashi
a gefe ta koma ta zauna, ganin yak'i saukkowa yasa tayi mashi Magana ya kalleta kafin ya saukko k'asa
kan Carpet ya mik'ar da k'afafunshi ta yadda tray d'in ke gefenshi, hannu Fatuu ta kai ta bud'e mashi
Abincin wanda farar taliya da macaroni ne sai miyan alaiyahu abincin gwanin kyau a ido sai kamshi ke
tashi, hannu ya kai ya d'auki fork d'in ciki a nutse ya fara ci ita kuma tana zaune gefenshi ganin ya fara ci
yasa ta maida idonta kan Tv can ta juyo suka had'a ido tayi mashi Murmushi hakan yasa ya dakata yace
mata ita taci Abincinne tace ta fara ci ya aiko kiranta shine ta aje yace taje ta d'aukko ba musu ta mik'e
ta fita,hannunta ruk'e da plate d'in Abincin nata ta dawo ta koma inda ta tashi ta zauna kawae sai gani
tai ya mik'a hannu ya d'auki abincin nata ya k'ara mata cikin nashi ya maida mata tana dae ta kallonshi
bayan ya aje ya kalleta yace yar rigen cinyewa zasuyi tana jin haka ta waro ido alamar mamaki tana
guntse Murmushi wato abunda ta ta6a yi da Hajiya a gabanshi shine yace suyi da alama dae duk
rayuwarsu da ita bai manta ba, alama yay mata na su fara ta kai hannu ta d'auki Fork d'in ta fara ci, tun
tana ci a hankali har ta fara sauri sai gashi ta wuce shi ganin hakan yasa ya fara d'iba da yawa saidae
rashin sabo da yin lomar yasa da ya kai Abincin wurin bakinshi duk sai ya zubo Allah ma yasa riga mai
duhu ce a jikinshi daba k'aramin 6aci kayanshi zasu yi ba, Fatuu ko mi zatayi in ba Dariya ba sosae take
kyalkyata mashi dariya ba 6ata lokaci sai gashi ta cinye nata lokacin nashi da saura da d'an yawa, aje fork
d'in yay yana kallonta sai faman Dariya take mashi harda d'an kwantawa bata ta6a tunanin zaice suyi
hakan ba, baisan ko shi kadae ke ganin hakan ba amman ba k'aramin kyau dariya ke mata ba hakan yasa
sai yay ta kallonta wani lokacin in tana yi,hannu ya kai kan kujera ya d'aukko wayarsa yana dubawa can
ya d'ago yay mata alamar ta matso da hannu ta d'an matsa kusa dashi kawae sai gani tay ya d'aga wayar
ashe Camera ya shiga da d'an mamaki ta juya ta kalleshi don tasan ba ma'abocin son yan d'auke d'auken
hotuna bane, alamar ta kalli Camera d'in yay mata da ido ta juya har zai d'auka kawae tasa dariya ganin
taliya a gaban rigarshi a haka ya d'auki hoton kuma yay kyau sosae bayan ya aje wayan yace ko zata
idasa sauran Abincin nashi tay mashi wani kallo tace Allah bata yarda ba bashi yace ai yar rigen ba dole
shima ya cinye ya jinjina mata kai yaci gaba da ci har ya cinye, bayan ya sha tace lemun fa yace ya bar
mata daga haka ya mik'e alamar zai tafi itama ta mik'e suka fito daga falon tare saida taje ta sanar ma
gwaggo ta fito sukae sallama sannan suka fita tare, A daidai shagon Amadu ya tsaya yace mata ta koma
dare yayi tace to ya juya ya tafi tay tsaye tana kallonshi yayin da sautin busar sarewa na wak'ar india ke
tashi bada k'ara ba sosae daga cikin shagon Amadu lokaci guda idanunta suka d'an ciko da kwalla da
sauri ta maidasu ta juya ta shige gida. Yana isa part d'inshi wayarshi tay k'ara ya duba mai kiran yaga
Hajiya ce bayan yay picking take tambayarshi k'ara fita yay bai shigo yaci Abinci ba yace mata yaje
gidansu Zarah ne kuma yaci Abinci acan daga haka sukae ma juna saida safe ya wuce Bedroom bayan ya
rage hasken parlon, yana shiga ya aje wayar kan side drawer ya wuce cikin laundry duk da bai jima da
yayi wanka ba bayan ya dawo gym saida ya k'ara yin wani saboda Abincin daya zubar mashi a jiki, sanye
da bathrobe ya fito yana tsane gashinshi da wani farin short towel ya nufi cikin Bedroom din, shiryawa
yay cikin Sleeping dress yasa turare ba mai k'arfi ba don su kansu kayan da ya sa sakin k'amshi suke ya
goga roll-on kafin ya nufi wurin switch ya kashe hasken d'akin ya kunna bedside lamp guda daya ya haye
gadon yana kallon ceiling lokaci guda zuciyarshi ta fara tariyo mashi abunda ya faru tsakanin shi da
Fatuu, Murmushi kawae yake saki yana jin zuciyarshi Fresh can ya kai hannu ya d'aukko wayarshi,hoton
da suka yi da ita ya bud'o ya k'ura mata ido yana kallon yadda ta washe baki tayi Dariya dimples d'inta
sun lotsa sosae, murmushi kawae yake saki kafin ya maida wayan ya aje ya lumshe ido.....................
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wannan
no 09013804524._

*ASM Bk2014*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.......Tana komawa cikin gidan Falo ta nufa anan ta iske gwaggo zaune ta bud'e Akwatunan duka ta rafka
uban tagumi tana ta kallon kayan sai kace lefe koda Akwatunan basu da yawa amma kud'in su dana
kayan ciki zasuyi na wasu akwatinan lefen da suka fisu yawa itama Fatun tsaye tayi cike da Al'ajabin
ganin uban kayan don ba abunda babu na buk'atar mace da ake sakawa a lefe kama daga d'inkakkun
kaya da wanda ba'a d'inka ba,Cosmetics Undies takalma da dae sauransu, da alama dae bakin gwaggo ya
mutu ta kasa cewa komae sai jinjina kai kawae take can ta kalli Fatun tace ta kama sukai d'akinta tace to
ta matsa gwaggon ta tashi suka maida su d'akin nata, sai lokacin bayan gwaggo ta fita ta zauna ta fara
dubawa nan take ta fara ayyana ina ma ace lefen aurensu ne a hankali siraran kwalla suka fara gangaro
mata k'arshe ma sai ta kife kanta kan kayan ta shiga raira kuka ba mai sauti ba,

Washe gari da safe yazo d'aukarta don kaita Makaranta yana yin horn biyu ta fito cikin shiri ta zagaya ta
bud'e kopar ta shiga bayan ta rufe kopar ta juya suka had'a ido ya jingina kanshi da headrest, da d'an
Murmushi ta gaishe shi ya amsa fuska sake yace "How was ur nyt?" ta bashi amsa da "Alhamdulillah" ya
jinjina kai daga haka yaja Motar suka tafi saida suka biya aka d'auki Haulat kaman kullum kafin suka
wuce, ba laifi ta d'an saki jiki yau jefi jefi yake mata Magana tana bashi amsa Haulat dae nata bin su da
ido acan k'asan ranta tana ayyana Fatuu ta warware ne ko ya akai ta saki jiki haka, bayan ya aje su ya
basu kudin break tana Murmushi ta amsa tayi mashi godiya har zai ja Motar ya tsaya ya kirata bayan taje
side d'in da yake ya tambayeta karfe nawa zasu tashi ne tace sai yamma yace to zaizo ya daukesu, akan
hanyarsu ta zuwa Class ne Haulat ke tambayar Fatun game da warwarewar da taga tayi tace zata fadi
mata in sunje aji, saida akai break ne ta bata labarin yadda sukae dashi sosae taji dadi da bata fad'i
mashin ba ta kuma yaba da kirkin haisam d'in daya damu da damuwarta har haka ta tayata farincikin
kayan data ce ya siya mata saidae bata ji dad'in jin Fatun bazata bikin ba tace mata "amman Fatuu
miyasa zaki k'i zuwa bikin Ya Haisam ne fa ni kaina da za'a barni wllh ina son zuwa saidae nasan
babanmu bazai barni ba amman ke tunda nasan su gwaggo ma zasu ai da kinje kawae tunda dae kin
hakura dashi"

"Don na hakura ce maki akae na daina sonshi ne Haulat, har yanzu ba abunda ya canja kawae ba
yadda zanyi ne shiyasa gwara ma kar naje naga abunda zai k'ara tarwatsa man Zuciya" ta k'arasa
Maganar da damuwa kan fuskarta haulat tace ta fahimceta daga haka bata k'ara ce mata komae ba
game da hakan bayan La'asar Haisam ya dawo ya d'aukesu, lokacin daya ajesu ya wuce gida yana zuwa
bakin Gate Officer ya tsaidashi bayan ya tsaya ya nufo Motar lokacin ya sauke glass d'in,

"Barka da dawowa Yalla6ai" kai ya jinjina mashi yaci gaba "dama kana da bak'o ne" tambayarshi yay ina
bakon yake ya nuna mashi can gefe da hannu ya d'an lek'o kanshi ya kalli direction d'in da Officer ke
nunawa, wani dattijo ne ya manyanta sosae cikin shiga ta kamala yana tsugunne gaban mashin d'in shi
Jincheng yana ganin fuskar Haisam ya mik'e yana kallonshi da d'an Murmushi, maida kan Haisam yay
yace ace ya shigo daga haka yaja Motar ya shige, lokacin da Haisam ya fito daga cikin Motar dattijon ya
shigo yay mashi alamar ya aje mashin d'in cikin wurin, da sauri ya nufo shi bayan ya parker mashi d'in
nashi ya d'an rankwafa yana kokarin gaishe dashi ya mik'a masa hannu suka gaisa kafin yace su shiga ciki
yace to saida ya koma ya d'aukko wata leda gari yayi zafi a jikin mashin d'in kafin ya bi bayanshi suka nufi
part d'in Haisam, suna shiga ya bi parlon da kallo baki bud'e tunda yake bai ta6a shiga irin falon ba shi ko
ganin irinshi ma a tv bai ta6a ba ga ni'imtaccen sanyi had'i da daddadan kamshi da ke kaima hancinshi da
sauran sassan jikinshi ziyara, nuna mashi bangaren Armchairs yay alamar ya zauna ya nufi wurin ya
zauna a takure, shiru suka yi Haisam bai mashi Magana ba shima haka sai dae faman murmushi yake can
ya fara Magana yace "Yalla6ai baka gane ni ba ko?" Kai Haisam ya d'aga mashi alamar eh,

"Allah sarki ay dayake lokacin da tsawo sosae, Sunana Malam Garba kuma nine mutumin daka ta6a
taimako ka biya masa kud'i a caji Office shekaru kusan ukku da suka shud'e tun lokacin naso nayi maka
godiya sosae saidae ban samu halin hakan ba don baka d'aga waya dana rok'i Officer ya kiraka dama
saida ya fad'a man bazaka d'aga ba karshe ya nuna man don Allah kai man in gode ma Allah kawae" d'an
dakatawa yay Haisam dae nata kallonshi fuskarshi a sake don yanzu ya gane shi,

Malam Garban ya d'aura da fad'in "Wato Yalla6ai sanadiyyar taimakon da kayi man na samu bud'i
sosae, da yar trader na bud'e ma yarona habu Allah yasa ma abun Albarka yanzu ta Zama k'aton shago
Alhamdulillah yanzu ba matsalar Abinci a gidana sannan karatun yara ma ana kamantawa yadda ya dace
shi kanshi wanda yay silar zuwana caji Office d'in Allah ya shiryar dashi ya daina d'aukar kayan Mutane
yanzu ya natsu sosae suke Kula da shagon ni kuma naci gaba da sana'ata ta faci wadda dama injin d'inne
ya lalace na daina sakamakon taimakon kudi da kayi man na canja wani wannan dalilin ne yasa na kasa
hakuri don ban manta da abunda kayi man ba saboda ba abune da zan iya manta ba dama Officer ya
fad'a man a wurin kakarka kake da zama tun wanccan lokacin hakan yasa ban sha wata wahala ba wurin
nemo ka don ita d'in sanannace, a tak'aice dae Yalla6ai Nagode, Nagode Allah Ubangiji ya saka maka da
mafificin Alkhairinsa ya dawwamar dakai cikin Farinciki kaman yadda kake saka bayinsa Farinciki, Allah
ya jik'an Magabata ya raya maka zuria......" kasa karasawa yay sakamakon muryarshi da ta karye
idanunshi suka cicciko da kwalla",

Sigh Haisam yay Calmly yace "ai ba wani abu bane ka d'auka rabonka ne a hannuna ba sai ka damu ba"
yar dariya yayi yana kokarin mayar da k'wallan yace "duk da hakan ai ance yaba kyauta tukuici, ko don
dakon rabon da kayi ai na gode maka" d'an murmushi Haisam yay baidae cemashi komae ba can ya
mik'e ya nufi Fridge ya d'aukko lemu da glass cup ya dawo saida ya d'aukko c-table bayan ya tsiyaya ya
aje mashi yace bismilla ya sha yay godiya kafin ya daukka ya fara kur6a, bayan yasha kaman rabi ya ajiye
ya kai hannu gefenshi ya d'ago da ledar daya zo da ita yace "yalla6ai wannan daga cikin kayan shagonne
su Omo, Sabulu Tolen paper (toilet paper) da dae sauransu na kawo a ba iyali" still da murmushi kan face
d'inshi yace "Ok angode sai dae a kaima Hajiya"

"Af,af d'ana ba dae ba iyalin ba?" ya tambaya da d'an mamaki shiru kaman bazai yi Magana ba sai kuma
yace "Yea but Next week ne zanyi auren" ruke ha6a yay yace "iko sai Allah kace da sati mai zuwan nazu
dana taras ana tsaka da hidima kenan",

"Ba anan ne za'ai ba Abuja ne" idon Malam Garba a kanshi yace "Allah sarki Allah ubangiji ya kaimu ya
nuna mana, aikuwa yakamata nima inje d'aurin auren nan"

"No, ba sai kayi hakan ba" ya bashi amsa a takaice yace "d'ana ba dae baka son naje d'aurin auren
naka ba" da sauri yace mashi a'a kawae basai ya takura kanshi ba in yayi mashi Addu'a ya isa yay yar
dariya yace" shikenan tunda kace hakan amma wllh ba wata takura ai Alhamdulillah Allah ya bud'a,
Addu'a kuma kullum cikin yi ake wllh ba zancen ganin idonka ba aduk sallar da zanyi ta Farilla kota Nafila
kana cikin Addu'oi na ko bama a salla ba" sosae Haisam yaji dad'in Maganar yace mashi ya gode,

Shiru suka d'anyi can Malam Garban yace "Yalla6ai bari in barka ka huta ka dawo aiki kuma na rik'e ka,
saidae in ba damuwa ina son in gaisa da hajiyar taka,amsa mashi yay da Owk ya kai hannu gefenshi ya
d'auki wayar shi yay Sending call, Tk ya kira saida ya tambayeshi yana gida yace mashi eh yace yazo part
d'in nashi, bada jimawa ba sai gashi ya shigo da sallama ya gaida Haisam kafin ya juya ya gaida bak'on
umarnin kaishi wurin Hajiya ya bashi yace to Malam Garban ya mik'e bayan ya dau ledan yace bari akai
ma Hajiyan Haisam ya d'aga mashi kai, saida ya tsaya bakin kopa ya k'ara mashi godiya da Addu'oi
sannan ya fita,suna fita Haisam din ya kira Hajiya tunkan tay mashi Maganar ya baizo yaci Abinci ba as
usual ya rigata fad'in ga bak'o nan Tk zai kawo daga haka ya katse kiran ya mik'e ya nufi hanyar
Bedroom.

Lokacin da suka shiga parlon Hajiyar na zaune kan 2 seater idanunta sanye cikin glasses ta juyo tana
amsa masu sallamar da suka yi Tk ya nufeta yace ga bak'o nan inji Ya Haisam ta jinjina mashi kai ya juya
ya fita ta maida idonta kan Malam Garba da yay tsaye tace "ka zauna mana kayi tsaye" fuskarshi d'auke
da faffad'an murmushi ya amsa mata ya nufi one seater ya zauna Matar da yake gani a talabijin ko yajita
a Radio yau gashi gata ba k'aramin dad'i ya ji ba,bayan ya zaunan ya d'an sunkuya yana gaishe da ita ta
amsa fuskarta a sake shiru ya biyo baya can yaji tace "to bak'o daga ina don ban wayeka ba" tay
Maganar tayi mashi k'uri ta cikin gilashin, gyara zama yay ya fara mata bayanin kanshi da abunda ya
had'a shi da Haisam,

"Allah sarki da yake bamu ta6a ma yin Maganar dashi ba tunda ba fad'in abu yake ba in yayi" jinjina
kai yay yace "Allah Akbar kaji mai yi don Allah, Allah ya saka da mafificin Alkhairinsa ya k'ara sutura"
Hajiya ta amsa da Amin tana murmushi tace "ai Malam Garba da baka wahalar da kanka ba ma" da sauri
yace "wllh Hajiya taimakon da yay man ne ya tsaya man a raina har mafarkinshi nike in ban zo nayi
mashi godiyar ba bazan samu natsuwa ba" yar dariya hajiyar tayi ya fara bata labarin irin bud'in d'aya
samu sanadiyyar taimakon da Haisam d'in yayi mashi tana ta fad'in Allah sarki an gode ma Allah, can ya
mik'e ya kai ledar kayan gabanta yace ga irin kayan shagonne ayi amfani dasu ta kai idonta kan ledar
tana fad'in harda hidima haka to an gode, komawa yay ya zauna yayi mata zancen bikin Haisam daya
fad'i mashi tace eh in Allah ya kaimu juma'a mai zuwa ne da tun satin daya wuce ma zasu tafi to wai
akwae uzurorin da bai kammala dasu bane saboda ba zai dawo nan ba to yanzu sai in Allah ya kaimu jibi
zasu tafi yace ashe da rabon zai iskesu tace aikuwa, kokarin mik'ewa ya fara zai tafi da sauri Hajiyar tace
"Malam Garba ya zaka tafi ko ruwa baka sha ba mun tsaya munata Magana bansa an kawo maka ba ka
zauna sai ka sha ruwan zumunci tukunna, komawar yayi don bai iya yi mata gardama a ranshi kuwa
yanata jinjina kirkinta yadda ta sake mashi sai kace dama sun san juna, Saude ta kwala ma kira tun kafin
tazo cikin falon ta bata Umarnin kawo mashi ruwa da Abinci ta juya kitchen, bada jimawa ba ta kawo
kayan Abincin cikin babban tray saida ta kinkimo sofa table ta kawo gabanshi sannan ta d'aura tray d'in
tay Serving nashi bayan ta gaishe shi tace aci Lafiya yay mata godiya Hajiya ma ta mik'e tana fad'in bari
ta bashi wuri ya samu sakewa ya tabbatar ya ci ya koshi ya amsa mata da to yana dariya, sosae yaji
dad'in Abincin don Saude badae iya Abinci ba Musamman farfesunta in Mutum nasha kamar ya cinye da
hannunshi don dad'i da wannan ta siye hajiya, bayan ya gama Saude taje ta sanar ma Hajiya ta fito don
suyi sallama ta bashi kud'i tace ya sha mai yay mata godiya gami da Addu'oi ya tafi, Malam Garba bai
tashi shan mamaki ba saida ya je parking space don d'aukar Mashin d'inshi nan ya iske Tk ya kawo mashi
kwalin taliya da Macaroni harda yar galan d'in mai baki bud'e ya bi kayan da kallo kafin ya sauke idanun
kan Tk dake ta washe mashi baki tun kafin yace wani abu ya riga shi fad'in Hajiya ce tace a kawo mashi
kawae sai yasa ma Tk kuka yana fad'in wad'annan wane irin Mutane ne haka dama har yanzu ana samun
Mutane masu tsananin kirki haka Tk yace "Wllh haka suke ni kaina nan daga Almajiri aka mayar dani
d'an gida ba abunda ba'ai man wanda ake ma d'a Abinci,Sutura,Karatu da dai sauransu har iyayena ma
ba'a barsu ba" waro ido Malam Garba yay jin wai shi Almajiri ne wanda ba kama ba alama ba don shi ya
fad'a ba ma ba lalle ya yarda ba, cewa yay bari yaje ya k'ara yi mata godiya Tk yace ba sai yayi hakan ba
ya tafi kawae su bama su cika son yawan godiya ba nan take ya tuna zancen SP acan baya hakan yasa ya
hau mashin d'in Tk ya taimaka mashi ya d'aura komae har zai tafi ya dakata yace ma Tk don Allah in ba
damuwa ya bashi lambar wayar Haisam yaji aurenshi ya kusa yana son in an dauran ya kira yay mashi
fatan Alkhairi ya kasa tambayarshi ne d'azun yace Ok ya amshi yar wayarshi yay mashi saving lambar
kafin ya mik'a mashi yanata shi mashi Albarka yaja mashin d'inshi ya tafi Farinciki fal cikin ranshi.(Allah
ka had'a mu da Mutane irinsu Hajiyar Sanata ka bamu ikon sanya Farinciki a zukatan junanmu Amin)

Sanye cikin gym outfit ya fito daga cikin d'ayan d'akin hannunshi guda rataye da k'atuwar Sport Bag
d'inshi yana fitowa daga cikin Corridor ya d'an bud'a idanu alamar mamaki idonshi akan bakin kopar
shigowa, Fatuu ce a tsaye jikinta sanye da Uniform d'in islamiyya ya nufi wurin da murmushi don yaji
dad'in ganinta hakan ya tabbatar mashi da ta warware itama d'an Murmushin take mashi yace islamiyya
zata ta d'aga mashi kai ya nuna mata kujera taje ta zauna, mikewa yay ya aje jakar a gefe kafin ya nufi
Fridge ta bi shi da kallo babbar robar lemu Fanta ya d'aukko ya dawo ya zauna kan hannun Sofa inda ya
tashi ya mik'a mata ta kalleshi ya d'an d'age gira ya furta "u'r my guest now" tana murmushi ta amsa
tace ta gode shiru ta d'an biyo baya ta sunkuyar da kanta tana wasa da hannun jakarta can ta d'ago taga
ita yake kallo motsa baki ta fara a sanyaye tace "dama nazo in yi maka godiyar kaya tunda safe naso yi
maka,Nagode sosae Allah ya saka maka da Alkhairi ya k'ara Arziki mai Amfani" d'an bud'a ido yay with a
broad smile on his face da kaji yadda take Maganar cikin hankali zaka fahimci ta girma ba kaman da ba,
cikin cool voice nashi yace "Ameen don kin cinye ma Amarya kud'in cin kayan dad'inta su kaza da kika ce
ana ci" waro ido tay tana mashi wani kallo yasa dariya tana ganin hakan ta tura mashi baki sai kuma
itama tayi yar dariyar, mik'ewa yay yace suje yayi dropping nata kar tay late tace to bayan ta saka lemun
daya bata cikin jaka tabi bayan shi, lokacin da suka isa Parking space d'in duk a tunaninta Mota zasu hau
amman sai taga ya fiddo bike bayan ya hau ya d'aura jakar a gabanshi yace mata ta hau amman sai tayi
tsaye hakanan taji yanzu bata son hawan don tasan dole jikinsu ya hadu shi kanshi tasan ba so yake ba
kawae don ya faranta mata ne, juyowa yay ya kalleta yace ta hau mana ta d'an yamutsa fuska tace ita
tsoro take ji yace kada ta damu ba abunda zai faru ba gudu zai yi ba, ba yadda ta iya haka ta daddage ta
hau tabi ta daddafe jikin mashin d'in yaja suka tafi, gaba d'aya a tsorace take don sai taga tayi sama
sosae shi kanshi yaji a takure take hakan yasa yace ta rike shi da sauri ta kai hannu ta kama gefe da gefen
rigarshi gadagam har saida ya d'anyi dariya don ya gama fahimtarta abunda bai kai ya kawo ba shike
bata tsoro bata tsoron babban abu, a gefen gate d'in islamiyyar ya parker duk ba dalibai da alama duk an
gama zuwa, kokarin sauka ta fara yi kwatsam ta tafi gaba d'aya zata kifa cikin zafin nama ya damkota ta
dawo sama ta matuk'ar tsorata sai numfashi take fitarwa da sauri da sauri lips d'inta na d'an motsi haka
idanunta ta rufe su gam ga dogayen eyelashes d'inta sai rawa suke sakamakon idonta dake kyerma still
yay yana k'are mata kallo tunda yake da ita bai ta6a samun closeness da ita ba haka da har zai kalleta
tsaf ba, ba komae yafi d'auke mashi hankali ba irin gashin idonta dake rawa sai kace irin d'iyar roba da
ake saka ma batir, jin ta d'an samu natsuwa yasa ta fara bud'e idanun a hankali kafin ta ware su sosae
har saida ta d'an tsorata da ganin fuskarshi kusa ganin ya k'ura mata ido yasa duk taji wani iri a hankali
tace zata sauka don har lokacin yana ruke da damtsenta sigh yay kafin yace "am so sorry for dat" kai
kawae ta d'aga mashi ya taimaka mata ta sauka ta nufi cikin Makarantar, yana kokarin tashin bike d'in ya
tafi kawae sai ganinta yay ta lek'o karaf suka had'a ido tasa dariya ta juya da sauri ta koma shima dariyar
yake a fili ya furta "U'r too much Zaraah" daga haka yaja ya tafi.

Washe gari Alhamis bayan ya aje su Makaranta tana kokarin fita ya tsaidata ya tambayeta yau ma sai
yamma zasu koma tace eh, ganin ya d'an yi Jim yasa ta tambayi ko akwae wani abu yace da yana son
zasu fita ne da rana,itama shirun tayi sai kuma tace to sai ta koma da an tashi ba sai ta tsaya lesson ba
yace ba matsala tace eh ai dama past question papers ne ake fidda masu kuma duk ta iya yace Ok zai
dawo lokacin tashin ya dauketa tace to, gaba d'aya sukuku take koda taje aji sam hankalinta bai a tare da
ita sanin gobe ne Haisam d'in zai tafi ji take kaman ta bishi amman tasan tabbas hakan matsala zai k'ara
zame mata gwara ta hak'ura kawae, ana tashi k'arfe biyu saura sai gashi ya zo d'aukartata Haulat ma
tace binsu zatai ta tafi gida aka tafi da ita, bayan ya sauke Fatun tana shirin fita taji yace kada taci Abinci
sosae yasan ita acici ce zasu ci in sun fita tayi yar dariya kawae ta fice shima murmushi yake ya nufi gida,
tana shiga d'akin gwaggo ta nufa lokacin gwaggon na kwance tana bacci bata dad'e da ta kwanta ba
bayan tayi sallar Azahar hakan yasa Fatun na shiga ta bud'e ido tace mata har sun dawo da wuri haka
saida ta gaidata sannan ta sanar mata da zancen fitar da zasu yi tace to tay sauri taje ta shirya ta amsa da
to ta fita, ko Abincin ma bata ci ba ta hau shiri ba tare da 6ata lokaci ba ta gama shiryawa cikin k'ananan
kaya riga da skirt kayan roba ne hakan yasa suka kamata sosae shape d'inta ya fita sai ta d'aura After
dress tay rolling veil d'in ta fiddo takalma masu tudu ta sa ba k'aramin kyau tay ba don ma kumatunta
sun d'an fad'a, tana gamawa bada jimawa ba ta jiyo horn d'in shi saida ta lek'a don yima gwaggo sallama
ta iske tay nisa a baccinta hakan yasa ta tafi kawae, zagayawa tay d'ayan side d'in Motar ta bud'e kopar
ta shiga wani fitinannan kamshi mai tsuma zuciya ne ya bugi hancinta har saida ta d'an lumshe ido tana
kokarin rufe kopar, juyawa tay suka had'a ido ta gaishe shi yay nodding kai tana shirin juya fuskarta ta
kalli gaban Motar kaman daga sama taji ya furta "Kinyi kyau sosae" da sauri ta kalleshi with surprise ol
over her face don bata tsammaci jin hakan ba saboda tunda suke da ita bai ta6a ce mata hakan ba ko a
da saidae in ita ta tambayeshi tayi kyau in tayi gayu sannan yace eh ko in tasa kayan daya siya mata ta
nuna mashi sai yace sun mata kyau, ganin ta k'ura mashi ido yasashi d'age mata gira yace "What?" da
sauri ta girgiza mashi kai ta juyar da kanta yaja Motar suka tafi acikin ranta ta fara tunanin yadda yake
mata abubuwa wanda bai saba yi mata ba can zuciyarta ta ayyana mata don ya sakata Farinciki ne
kawae, ta juyar da fuskarta gefe tana kyakkyafta idanu don ta mayar da kwallan dake kokarin
taruwa..........
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wannan
no 09013804524._

*ASM Bk2015*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.........Wani babban Eatery mai kyau da tsari ya nufa dasu bayan ya parker Motar a wurin da aka tanada
don haka a tare suka fito suka nufi ciki Masha Allah ya dae tsaru Fatuu sai d'an bin wurin take da kallo ta
yadda baza'a ga k'auyancinta ba, wuri ya nuna mata suka zauna suna facing juna suna zama sai ga
waitress tazo tana sanye da Uniform d'in wurin bak'in skirt sai riga milk tasa yar himar bak'a dama
ma'akaitan wurin Mata da Maza ne, Haisam ta nufa cike da salo tace "Barka da zuwa Yalla6ai" ba tare da
ya kalleta ba ya d'aga mata kai Fatuu ta zuba mata ido tana kallon ikon Allah don sai faman rausaye
rausaye take, Menu ta mik'a mashi mai d'auke da lists d'in dishes dake garesu bai amsa ba yace ta kawo
mashi Fried rice d'an d'aga gira tay jin yadda yake Magana tace "with Beef or chicken yalla6ai" chicken
ya bata amsa a tak'aice sai kuma ta k'ara kanne murya tace "to yalla6ai itafa mi za'a kawo mata?" Shiru
yay mata jin wata tambaya mara kan gado gata ba sai ta tambayeta ba Fatuu kam har saida tay kaman
zatai murmushi cikin ranta take ayyana kyama yi ki gama, har saida ta k'ara tambayarshi sannan idonshi
akan waya yay mata nuni da Fatun yace "ask her" d'an ta6e baki tay ta nufi Fatun suka had'a ido tana
kokarin bata menu d'in itama tace ta kawo mata babban robar ice cream da shawarma tace Ok ta juya
Haisam yay ma Fatun kallon k'asan ido ya furta "Wannan ne zai isheki?" Yar dariya kawae tay bata ce
mashi komae ba, bada jimawa ba waitress d'in ta dawo d'auke da k'aton tray wurin Haisam ta fara zuwa
ta aje mashi nashi kafin ta nufi fatuu, tana niyyar tafiya Haisam ya tsaidata ta kalleshi sai lokacin suka
had'a ido dashi yace ta kawo mashi pepper chicken da soft drink sai ruwa cikin kashe murya ta
tambayeshi kaman ya complete chicken ko half yace complete ta d'an juya ido ta furta Ok kafin ta tafi,
har ta kawo mashi bai fara cin fried rice d'in ba bayan ta aje mashi tace aci lafiya ta juya Fatuu ta d'an
ta6e baki tabita da ido, tana juyowa taga ya turo pepper chicken d'in gabanta ta kalli kazar sai kuma ta
kalleshi taga yana sakin wani Murmushin gefe nan take ta gane mi hakan ke nufi dama tasan tunda tay
Maganar kaza yace ko tana son ci ne tabbas sai ya siya mata, tura mashi baki tay yay mata alamar ta fara
ci shima ya fara cin nashi a nutse, ita kuwa Waitress d'in wuri ta samu can gaba ta zauna ta fiddo
wayarta tana lallatsawa can wata ma'aikaciyar ta shigo d'auke da tray ta kai ma wasu bayan ta aje masu
ta juya da tray d'in anan ta hango d'ayar zaune ta nufi inda take tana zuwa ta dafa shoulder d'inta tace
"Su Billy manya shine kika bar aiki kika zo nan kikai zaune ko" wani d'an iskan kallo tay mata tana d'an
Murmushi tace "zaman dole nike zuciya ce taga abunda take so" bud'a ido tay jin abunda billyn tace sai
kuma ta juya tana k'are ma wurin kallo nan take idanunta suka sauka kan su Fatuu,

"Kice bak'in Farar fata mukae,to ke burgeki sukae kenan shiyasa kikai zaune kina k'are masu kallo"? d'an
juya ido Billy tayi tace "ya dae burgeni" da sauri d'ayar tace "yau naga ikon Allah daga ganin Mutum
kuma kika sani ma wadda yazo da ita ko matarshi ce ko kuma budurwarshi" d'an ta6e baki Billy tai tace
"I don't care ni dae yayi man ne baki ji dad'in voice d'inshi ba wllh, kuma ma ni ban tunanin wai ko
matarshi ce ko budurwarshi nafi tunanin kanwarshi ce ma" d'ayar tace "kanwarshi kuma,haka kawae sai
ya d'aukko kanwarshi ya zo da ita nan cin Abinci ko ba wani abu bane hakan ai nasan dae ba ita kadae ce
kanwarshi ba",

"Ke baki san in kud'i sukae ma Mutum yawa ba komae yi yake, ba kamar su daga gani ba cikakkun
hausawa bane nafi tunanin half caste ne kuma ai zai iya yuwuwa yafi ji da ita ne acikin k'annan nashi"
ta6e baki d'ayar tayi tace "lallai aiki ya sameki to, ki tashi kici gaba da aiki ko inje in kai k'ararki" ta
k'arasa Maganar tana kokarin tafiya billyn tay dariya tace "ai na gama da kowa ba abunda zanyi" gyad'a
kai tay tayi gaba abunta ita kuma billyn taci gaba da lallatsa wayan tana satar kallon yadda Haisam yake
cin Abincinshi a nutse bai ma san tana yi ba,

Fatuu na cikin shan ice cream idonta akan tv tana kallon maimaicin shirin dadin kowa da aka fara yi a
tashar Arewa 24 hankalinta ya tafi har bata san sadda robar ice cream d'in ta kubce mata ba gaba d'aya
ya zube akan after dress d'inta duk ta 6aci dashi da sauri ta mik'e tana d'an yarfa hannu idon Haisam a
kanta suka had'a ido dashi ta d'an yamutsa fuska d'an ta6e baki yay tace mashi yanzu ya zatayi ya d'age
gira yace "ni nasa ki sake shi" d'an tura baki tay kaman zatai kuka ya bita da ido yana d'an murmushi, duk
abunda ke faruwa akan idon billy hakan yasa ta taso ta nufo su tana zuwa cikin kashe murya tace
"Subhanallahi 6are maki yay ne?" Kai Fatuu ta d'aga mata tace bari ta taimaka mata ta ciro rigar Fatun
tace to, ta kai hannu ta cire Billyn ta kar6a ta juya, duk sai kuma Fatun tajita wani iri da ba rigar don
kayan ba k'aramin tighting nata sukae ba hakan yasa tay tunanin tabi bayan billyn in an wanke sai tasa,
fita tay daga cikin seat d'in ta nufi hanyar data ga billyn tayi Haisam yabi bayanta da kallo, tunda suke bai
ta6a kafeta da ido ya k'are mata kallo irin haka ba bare har ya fahimci yadda jikinta yake ya dae san ba
ramamma bace kuma yana jin ana Magana kan structure d'inta kaman can baya lokacin da Najeeb yay
Magana kan hakan, dressing d'in ba karamin fiddo mata da shape yay ba don har shatin undies nata ana
gani kasantuwar kayan roba ne, a hankali ya d'an juya lokaci guda yay noticing gaba d'aya hankalin
mutanen dake wurin ya koma kanta maida idon yay a kanta har takai tsakiyar wurin don kayan basu
barinta sauri a hankali take tafiya d'an d'aga murya yay yace "ZARAAH" dakatawa tay lokacin da kiran ya
sauka cikin kunnanta Slowly ta juyo ta kalleshi don tasan shine ya kirata da kai yay mata alamar tazo ta
juyo ta nufo shi idanunshi a kanta har ta k'arasa kafin tace wani abu yace "Sit and wait for her zata kawo
maki ne" d'aga mashi kai tay don dama da tana tafiyar ta lura da yadda ake kallonta alama yay mata taci
kazar a shagwa6e tace ai tayi mata yawa yace taci wanda zata iya,

"To kai bazaka ci ba" ta tambayeshi, shiru ya d'anyi sai kuma taji yace taci in ta rage zaici bud'a ido tay
tace "ba baka cin saura ba?" Yar harara ya wurga mata tasa dariya ta kai hannu ta fara ci, can saiga billy
ta dawo maimakon ta nufi Fatuu sai ta nufi Haisam cikin salo tace "amm Yalla6ai na wanke rigan tana
can na shanya under fan don ta bushe da wuri in zaku tafi sai ayi man Magana in d'aukko mata" Slowly
ya d'ago da fararen idanunshi tar masu d'auke da bakar kwaya mai baki sosae ya d'aura a kanta har saida
taji fad'uwar gaba fuska a sake ya furta mata "thanks" wani far tay da ido ta washe baki tace "u'r
welcome" daga haka ya maida idon yana cigaba da cin Abincinshi tay tsaye tak'i tafiya tana kallon sumar
kanshi dake ta kyalli tasha gyara duk abun nan idon Fatuu na kanta ta gama kasheta da mamaki kasa
jurewa tay tace "kar ki sa ya kware fa" kaman daga sama billy taji Maganar hakan yasa ta juya da sauri ta
kalli Fatuu dake kallonta fuskarta ba yabo ba fallasa cikin dabarbarcewa billyn tace "a....am ina jira ya
gama ne in d'auke kayan kar nayi tafiya biyu ba wani abu ba" wani kallo Fatun tayi mata cike da rainin
Wayo tace "ba zaki kawo rigan ba ai sai ki d'auka lokacin ko" da sauri tace hakane ta manta ne ta juya
cike da jin kunya ta tafi, kallon k'asan ido yay mata ta tura mashi baki yay d'an murmushi kawae bai ce
mata komae ba, bai cinye fried rice d'in ba Fatuu ta mik'o mashi pepper chicken d'in ya d'an ci kadan
daga haka ya yagi tissue ya fara goge hannu da baki tana ganin haka itama ta yaga ta goge tana kokarin
mik'ewa taje ta amso rigar yace ta zauna ya mik'e ya nufi cikin wurin don kunya tasa billy ta bar wurin a
can daga ciki ya ganta yace ta d'aukko rigar ta amsa da Ok ya juya ya koma bada jimawa ba sai gata tana
wani shan k'amshi ta mik'a ma Fatuu rigar da d'an murmushi tace mata ta gode ba tare data kalleta ba
tace ba damuwa ta juya taba Haisam bill d'in abunda suka ci ya fiddo Wallet ya biya yay mata kyautar
dubu biyar tana Murmushi tace ta gode ya d'aga mata kai kawae ya tashi Fatuu ma ta fito bayan ta saka
rigar tana zuwa saitin billy dake tattara kayan da suka yi amfani dasu ta tsaya tace "kiyi Hakuri in kinji
haushi na sati mai zuwa ne d'aurin Aurenshi ban so ki wahalar da kanki ne" daga haka tay gaba abunta
Billyn ta bita da ido baki bud'e acikin ranta ta fara ayyana to ko Fatun ce zai aura.

Suna barin wurin Zoo and park ya wuce da ita bayan ya yankan Masu ticket suka shiga, wurin namun daji
su zaki, giwa da dai sauranau suka fara zuwa suna kallo cike da nishadi daga baya suka koma wurin liluna
ganin tayi tsaye tana murmushi yasa yace taje ta hau wanda take so amman sai cewa tay ita kunya take
ji har saida ya d'an bud'a ido alamar mamakin yau Zaraah ce da kunyar hawa lilo, ganin ta toge yasa yace
suje su hau tare cike da mamaki ta bishi ya biya masu irin mai juyawa suka hau suna facing juna sai
faman dariya take shidae murmushi kawae yake yayinda Mutane keta bin su dana mujiya don a zaton
mafi akasari ba hausawa bane, daga baya suka sauka ta hau swing ya d'an rinka turata can kuma ya
k'yaleta taci gaba da yin abunta yaja gefe yana kallon yadda take yin sama tana dawowa, sosae Fatuu ta
samu nishad'i anan yay sallar la'asar a Masallacin wurin sai wuraren k'arfe biyar saura sannan yace mata
su tafi gidan Abbas bayan sun fito yace suyi ma Abdul shopping a Supermarket d'in wurin, leda biyu
sukae yace d'aya tata ce tay mashi godiya kafin suka wuce, suna kan hanya ya kira Abbas d'in ya tambayi
yana gida yace mashi a'a yana kan hanyarshi dae ta komawa daga Jami'a yace Ok su had'e yana kan
hanya shi da Zaraah, suna dab da shiga gate d'in Estate d'in shima Abbas ya iso suka shiga tare a bakin
gate duk suka tsaya Abbas ya fito ya bud'e masu gate d'in suka shiga shima ya koma Mota ya shiga,
bayan duk sun parker Motocin suna fitowa Abbas ya nufeshi yana fad'in "the latest Ango" shidae
murmushi kawae yake ya bashi hannu sukai shaking kafin ya maida idon kan Fatuu yace "Mom Zarah
barka da zuwa" da d'an murmushi tace mashi yauwa yace "kin rako ango zaga garin bankwana kenan"
shiru tay still da murmushi akan fuskar Abbas yace su shiga suna shirin juyawa sai ga Abdul ya fito da
gudu ya nufi Fatuu ta rungumeshi yana ta dariyar Farinciki itama dariyar take mashi ta d'agoshi Haisam
yace ta d'aukko abunshi tace to ta bud'e back door ta fiddo ledan kayan kwalama da suka siyo mashi ta
mik'a mashi ya amsa yace nashi ne tace eh cike da murna yace "thank u so much Aunty Zarah I love u"
gaba d'aya suka sa dariya Abbas na fad'in ba dole kasota ba tunda ta kawo maka abu da sauri yace "No
Daddy wllh ba saboda su bane ina sonta tana da kirki kuma tana da kyau" murmushi duk suka yi Abbas
yace "yau da alama Mom Zarah ta tafi da hankalinka shiyasa ko ta baban naka bakayi ba balle ka
gaidashi ko" da sauri ya nufi Haisam yana fad'in "Good Evening Baba Zakee Ango" gaba d'aya suka sa
dariya daga haka suka nufi ciki hannun Abdul cikin na Haisam, cike da Farinciki Feenah ta tarbi Fatuu don
sun kwana biyu basu had'u ba bayan sun gaisa tace bari ta shirya table dama Abbas d'in bai ci Abincin
rana ba shima tana shirin mik'ewa Haisam yace mata a koshe yake tace ma Fatuu ai ita zata ci ko tace
mata a'a itama a koshe take ganin yamma ne tasan dole sunci Abinci yasa ta k'yalesu Abbas ma yace ba
yanzu zai ci ba, d'aki Abdul yaja Fatuu wai suje suyi game su ci kayan dad'in data kawo mashi Feenah ma
tace baza'a barta ba da ita za'a ci tabi su Abbas na dariya yana fadin da girmanta zata cinye ma yaro abu,
bayan barinsu parlon hirar tafiyarsu Haisam d'in gobe suka shiga yi can ya tambayeshi yadda akai suka
koma Normal da Mom Zarah anan ya bashi labari yace ba abunda yake tunani bane kawae ta damu da
tafiyar da zaiyi ne don basu ta6a hirar Aurenshi da ita ba so abunne yazo mata unexpected kuma gashi
bazata je bikin ba, da mamaki Abbas ya tambayi dalili yace mashi zasu fara final Exams ne Next week
d'in, shiru Abbas yay kaman mai tunanin wani abu lokaci guda ya tuna da ba Next week ake fara Waec
ba sai Upper week wato sati na sama nan take ya fahimci Fatun k'arya tay ma Haisam hakan kuma ya
tabbatar mashi da zarginshi akanta duk da ba zargi bane duk alamu sun tabbatar da son Haisam take
kawae shima don bai da experience kan hakan yasa yak'i fahimta shiru yay kawae bai ce komai game da
hakan ba sai da sukayi Magrib sannan sukae masu sallama suka rako su gaba d'aya har bakin Mota anan
Feenah ke ce ma Fatuu "Mom Zaraah sai mun had'e Abuja ko" Abbas yay saurin cewa "Mom Zaraah
bazata samu zuwa ba don lokacin sun fara Waec" kallonshi fatuu tay suka had'a ido ya saki wani
murmushi da yake akwae haske sosae sam Feenah bata ji dad'in hakan ba haka ma Abdul daga haka
suka shige Mota Abbas nace ma Haisam sai sun had'e goben suka tafi bayan ya bud'e masu gate, akan
hanyarsu ne yake ce mata zadae ta raka shi Airport gobe ko tunda da yamma zai tafi har saida gabanta
yay wata kalan bugawa kafin da k'yar tace mashi eh ai bazata ma je Makarantar ba ta fad'i mashi hakan
ne don kar yama zo daukarta, tambayarta yay dalili tace mashi ba komae kawae shiru yay bai ce komae
ba har suka iso gidan ba wanda ya k'ara tankawa, jiki a mace tace mashi ta gode ya jinjina mata kai kafin
yace ta d'auki ledan baya tace to, bayan ta d'auka ta nufi gida ko juyowa batayi ba ya bita da ido har ta
shige ya lura da canjawar da tayi nan take zuciyarshi ta ayyana mashi saboda zancen tafiya da yayi mata
ne d'age kanshi yay a fili ya furta "I too gonna miss u Zaraah" iska ya d'an fesar ya d'ago ya kai hannu ya
ja Motar.

Next Day........

Bayan sallar juma'a misalin k'arfe 3:30 sun gama shirin tafiya tsab Hajiya tasha adon lifaya haka ma
Saude tana sanye da doguwar rigar Atamfa da babban gyale don da ita za'a tafi Tk kuma zai tafi garinsu
ne gobe daga can zai tafi tare da iyayenshi, gaba d'aya Tk ya gama fita da kayayyakinsu yasa acikin Mota,
lokacin da suka k'araso parking space Gwaggo ta shigo cikin gidan tana ta sauri ta nufesu tana fad'in ayi
Hakuri ta taushe hannu don ta sanar da Hajiyar zata raka su dama suna haka sai ga Haisam da Abbas sun
fito daga part d'inshi sun nufo parking space din Haisam na sanye da wani d'anyen bak'in voile haka
hular kanshi da takalman kafafunshi da agogon hannunshi suma duk bak'ak'e ne wato shigar complete
black yay just Ma sha Allah, suna isa Abbas ya gaishe da Hajiya don bai shiga wurinta ba sannan ya
gaishe da gwaggo tanata fara'a ta amsa Haisam ma ya gaishe da ita har zai bud'e Mota sai kuma ya
dakata ya kalli gwaggo yace "Zaraah fa?" shiru ta d'anyi Hajiya tace "wllh nima inata son in tambayeta
nasan dae yau ba islamiyya ai", ganin duk ita suke jira tayi Magana yasa tace "d'ana Haisam kar ka damu
mu tafi kawae" jimm yay haka Abbas ma Hajiya tace "wani abu Dije, ina Fateemar take?" Da yar damuwa
tace "tana can tun jiya da daddare take abu guda yau ko Makaranta bata je ba sai aikin kuka ba irin
lallashinta da ban yi ba amman a banza tunda ba jin Magana take ba" yar dariya Hajiya tayi sai kuma ta
d'an girgiza kai tace "Allah sarki kinsan yadda sabo yake dole ta shiga damuwa Yayanta Handsome zai
tafi gashi ba samun zuwa bikin zatai ba ko ni banji dad'in hakan ba itace ya kamata ace k'irjin bikin"
gwaggo tace "to amman ai saitai hak'uri tunda kukan ba canja komae zaiyi ba kuma don an tafi ai ba
shikenan an rabu ba ko" gyad'a kai Hajiya tayi tace suje kawae duk suka shiga Jeep d'inta Tk na niyyar
shiga wurin driver don ya jasu Haisam ya tsaidashi yace ma Abbas ya kaisu shi zai taho tare da Tk d'in ya
d'aga mashi kai da murmushi kan fuskarshi ya shiga mazaunin driver ya tashi Motar suka tafi, kallon Tk
yay yace ya shiga shi kuma ya zagaya ya bud'e mazaunin driver d'in ya shiga daga haka yaja Motar Suka
tunkari gate Officer na mashi Allah ya tsare sai ya zo suka wuce, A daidai gidan su Fatuu ya taka burki
yace ma Tk yana zuwa,bud'e motar yay ya fita ya maida kopar ta rufe ya nufi cikin gidan................

*ASM Bk2016*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*This page is dedicated to Hajiya Kubra (Mommy) Allah ya k'ara girma da daukaka da nisan kwana Amin
🤲🥰*

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.........Yana shiga gidan Parlor ya nufa ganin ba kowa yasa ya wuce direct d'akinta tun kafin ma ya shiga
ya jiyo shesshekar kukanta ya kai hannu ya d'aga labulen,tana zaune a k'arshen gado ta had'e kai da
gwuiwa ga gashinta duk ya tarwatse, har ya shigo ya tsaya a tsakiyar d'akin yana kallonta bata sani ba
goya hannuwan shi yay a k'irji idonshi akanta yama rasa mi zaice mata, a hankali k'amshin turaren shi ya
fara kurd'ad'awa yana kai ma hancinta ziyara tun tana jinshi sama sama har ya cika mata hancin ta
tabbatar k'amshin Ya Haisam ne hakan yasa ta d'ago a zabure idanunta suka sauka akanshi, zare ido tay
tana kallonshi da idanuwanta da suka canja kala sunyi jawur gashi sun kankance sosae tsabar kuka duk a
tunaninta sun ma tafi, lokaci guda ta kama kanta ganin kallon da yake mata ta fara jan jiki tana matsowa
ta zo bakin gadon cikin hard'ewar murya tace "Y..ya ha.i..sam" shiru bai amsa ba yana cigaba da kallonta
sai yan kame kame take tana kallonshi can yay sigh da wata irin murya yace "is this the Promise u ave
made to me Zaraah" girgiza mashi kai tay tana yamutsa fuska kaman zata sa kuka,

"Why, why all dis Zaraah kina son in tafi da damuwa ne?" tun kafin ya rufe baki tafara girgiza mashi kai
ganin yadda yake Maganar da damuwa kwance akan fuskarshi shiru yay yana kallonta cikin muryar kuka
ta fara fad'in "Don Allah kayi hakuri Ya Haisam wllh kukan ne yake zuwa da kanshi nayi nayi ya daina
yak'i" ta k'arasa tana had'iye kukan wani irin tausayinta ne ya kamashi slowly yay moving zuwa gaban
gadon ya samu wuri can gefenta ya zauna da sauri ta sunkuyar da kanta don duk kamshin turaren shi ya
cika hancinta shiru ya d'anyi yana kallonta can yafara Magana Slowly "am so sorry Zaraah I caused u pain
am sorry" ya k'arasa da breaking voice ya d'an cije baki d'agowa tay ta kalleshi hawaye na sauka daga
idonta da sauri ya kai hannu cikin pocket d'in rigar shi ya fiddo farin hanky ya mik'a mata ta amsa ta fara
goge kwallan yana ta kallonta yama rasa tunanin da zaiyi ji yake kaman kar ya tafi ko don ta daina
damuwa but he knows isn't possible ita kuma ga exams d'inta kuma yasan ko taje ma in ta dawo still sai
ta damu na wani lokaci saboda rashin shi sai faman dirzar ido take bata da niyyar tsayawa a hankali ya
kai hannuwanshi ya kamo duka hannayenta ya sauke su k'asa suka kalli juna cikin ido picifically yace
"kiyi Hakuri Zaraah am feeling almost d same thing am not happy zamu yi nisa da juna after being
together for gud 3 years but we can still be together though we're in distance right?" Jinjina mashi kai
tay alamar eh, yace "ok ki daina damuwa pls" nan ma kai ta jinjina mashi shiru ya d'anyi sai kuma yace
"tunda baki son rakani ba wani abu lokaci na tafiya zamuyi Magana" daga haka ya saki hannuwan nata
ya mik'e har ya juya yaji ta kira sunanshi da disasshiyar murya ya juya ya kalleta ta saukko daga kan
gadon ta mik'e a hankali tace "zan raka ka" fuska a d'an sake ya d'an bud'a ido yace "really?" Kai ta d'aga
alamar eh d'an murmushi yay ya nufeta yace ina ribbom d'inta ta juya kan gado ta d'aukko tana kokarin
sawa ya mik'a hannu ya amsa yay mata alamar ta duk'o da kan kallonshi tay cikin ido sai kuma a hankali
ta duk'ar da kan ya matsa dab da ita ta yadda har kan nata ya d'an gogi broad chest d'inshi a nutse ya
fara tattara gashin don ba kaman na Fanan bane nata yafi cika hannu sosae bayan ya gama ya d'ago da
ita yana mata murmushi ita kuma tana mashi wani kallo a hankali ta furta "I will miss u Ya Handsome"
kawae sai ya janyota yay hugging nata very tight ya d'aura ha6arshi saman gashinta, sosae itama ta
k'ank'ameshi idonta a rufe wata kalan natsuwa taji tazo mata yayin da scent d'inshi ke k'ara narkar mata
da zuciya tana cikin hakan taji cool voice d'inshi yana fadin "I will miss u too Zaraah, I will miss ur
everything ur smile,jokes and d whole moment we spend together......" Yadda Maganar ke sauka acikin
kunnanta yasa ta k'ara kankameshi yana jin yadda kirjinta ke sama da kasa saboda numfashin da take da
sauri da sauri hakan kuma yasa Haisam d'in jin wani bak'on yanayi a tattara dashi wanda sam bai ta6a jin
irin hakan ba a tare da Fanan, ita da bai ma jin komae in ya had'a jiki da ita don koda Maganar Aure ta
shiga tsakaninsu tana nan a matsayin da ya d'auketa cikin ranshi sai daga baya ne data k'ara girma ya
fara jin canji game da hakan shiyasa yake kokarin kiyayewa bai cika son suna had'a jiki da ita ba sai ta
kama ita ce dae in zai biye mata to kullum suna manne, jin abun na k'aruwa sosae yasa da sauri ya
d'agota don shi kanshi yasan bai kamata ya had'a jiki da ita ba har saida ya nemi tsari yay istigfari cikin
ranshi, sam ta kasa kallonshi don da k'yar take ma bud'e idonta wani bak'on yanayi take ji a jikinta,
shima juyar da kanshi yay gefe trying to get ease kafin ya kai hannu ya kamo hannunta ya kaita gaban
mirror bai iya tanka mata ba da hannu yay Mata alamar ta gyara fuskarta ta kai hannu ta d'auki puff d'in
powder tana goge fuskar idonta akan shi suna kallon juna ta cikin mirror d'in suna haka wayarshi ta fara
ringing ya kai hannu cikin pocket d'in rigarsa ya fiddo yaga Hajiya ce ke kiran nasa yay picking yana
d'auka tace mashi yana inane yasan dai jirgi bai jiran Mutum ko yace mata he's on his way heading there
d'aga haka yay cutting ya maida wayar Fatuu na kallonshi yace mata ina veil d'inta ta matsa wurin
wardrobe ta ciro hijab tasa ya kama hannunta suka fita, back door ya bud'e mata da kanshi bayan sun
fita ta shiga ta zauna ya rufe shi kuma ya bud'e gaban ya shiga ya ja Motar, a kai kai yake kai ido kan
mirror ya kalleta wani lokacin su had'a ido wani lokacin kuma ta duk'e tana goge kwalla can ta d'ago
kawae taga yana mik'o mata hanky kallonshi tay kafin ta mik'a hannu ta amsa, a hankali take kai hanky
d'in fuskarta ta d'an goge kwallan in suka had'a ido dashi sai ta sadda kan kasa, basu d'au tsawon lokaci
ba suka k'araso Airport bayan sun yi parking sun fito ya nufi inda su Hajiya suke Fatuu da Tk na bayanshi,
Hajiya na ganinshi ta sha mur ganin Fatuu yasa bata dae ce mashi komae ba gwaggo ma tunda suka
had'a ido da ita sau d'aya bata yarda sun k'ara ba don taga kallon da tay mata mai kaman harara Abbas
kuwa sai murmushi yake mata a sanyaye ta gaishe dashi kafin ta nufi wurin Hajiya ta gaidata tana kallon
fuskarta ta amsa kafin ta dafa shoulder d'inta tace "kiyi hakuri kinji Fateema ai ba an rabu ba kenan da
zaki damu kanki har haka, dubi idanunki yadda suka kumbura kukan ya isa haka kinji" kai ta d'aga mata
lokacin kuma aka fara sanarwa nan da mintuna biyar jirgi zai k'araso don haka matafiya su shirya Hajiya
ta juya tana k'ara yin sallama dasu gwaggo da Abbas suka ce sai sun zo daga haka suka nufi cikin
departure Haisam ya mik'a ma Abbas hannu suka yi sallama shima yace mashi sai yazo haka Tk da
gwaggo duk suka yi mashi fatan a sauka lpy, juyawa yay side d'in Fatuu ya d'an kalleta for few seconds
sai kuma ya tafi ba tare da ya ce mata komae ba har yayi kaman taku ukku zuwa hud'u yaji ta kira shi
hakan yasa ya dakata ya juya nufo shi tay tana zuwa gaban shi ta mik'a mashi hanky d'inshi da ya bata a
cikin Mota kaman bazai amsa ba sai kuma ya amsa ya juya yana niyyar cigaba da tafiya yaji Muryata tana
fad'in "Thank u Sweetheart Ya Handsome, thank u for all dat u have done to me May Almighty Allah
reward u Abundantly, ina rokon Allah ya dawwamar da kai cikin farinciki har abada kamar yadda kake sa
bayinsa farinciki, Allah ya jibanci lamuranka ya baka y'ay'a wanda zasu ji k'an ka, Allah ya....." Kasa
k'arasawa tay ta duk'e a wurin tana wani irin kuka mai cin rai duk abun nan yana tsaye cak ba tare da ya
juyo ba yana jin yadda take Maganar cikin breaking voice dake bayyana she's in serious pain runtse
idonshi yay can kuma ya bud'e yaci gaba da tafiyar saida zai shige wurin sannan ya dakata ya d'an juya
suka had'a ido tana a durk'ushen sai kuka take can ya juya ya shige, kowa ta bashi tausayi har gwaggo
saida jikinta yay sanyi ta sani sabo ba abunda bai sawa ba kamar su sabonsu na Musamman ne, Abbas
ne ya nufeta ya duk'a ya kamo hannunta ta d'aga kai ta kalleshi tana gunjin kuka ya jinjina mata kai
alamar ta mik'e, Mota ya nufa da ita ya bud'e baya yace ta shiga gwaggo ma ta bud'e d'ayar kopar ta
shiga yace ma Tk ya taho da Jeep d'in yace to, tunda suka taho hanya take aikin kuka kanta na kan
kafafunta ta rufe fuska Abbas sai bata hakuri yake har dae ta k'ule gwaggo ta fara surfa mata fad'a cikin
harshen fulatanci Abbas na bata hak'uri duk da baisan mi take cewa ba amman daga ji yasan fad'a take
mata, suna akan hanyar jirginsu Haisam d'in ya wuce, Allah sarki Ya Haisam d'in mu shikenan ya tafi
wayyo Fatuu I feel ur pain ko baki son Haisam dole ne ki ji zafin tafiyarshi🥹, suna k'arasowa kopar gida
gwaggo ta bud'e Motar bayan tayi ma Abbas godiya ta wuce gida abunta da k'yar ta iya bud'e Motar ta
fita sakamakon k'afafunta da sukae mata nauyi sai faman shessheka take tana niyyar tafiya bayan ta rufe
Motar Abbas ya bud'e ya fito har ta juya ya kira sunanta ta juyo da runannun idanunta ta kalleshi ba tare
da ta amsa ba cikin muryar lallashi ya fara Magana,

"Am so sorry Zaraah, i know how are feeling but I want u to know Allah yana jarabtar bawa ba don baya
son shi ba and if u'r destined for sadness there is always a reason all u need is to put ur trust in Allah,
shine kadae mai maida abunda ake tunanin bai ta6a yuwuwa ya yuwu cikin tsananin sauki, so all I can
say to u is kiyi HAKURI kiyi HAKURI" kai ta jinjina mashi tasa hannu tana goge kwallan ya kuma cewa "Da
gaske baki son zuwa Abujan?" Da sauri ta d'aga mashi kai alamar eh, shiru ya d'an yi, ya gama fahimtar
ta sosae yasan what she's going through abune mai tsananin rad'ad'i a zuciya, sigh yay yace "ko in kawo
maki Abdul ya taya ki zama kafin mu dawo tunda itama Grandma d'in naki zasu je tare ma zamu
H,Zakeen yayi mun Magana" murya na rawa tace "a'a ka barshi shima ai yana son zuwa" shiru yay yana
kallonta tabbas Abdul na son zuwa kullum sai yayi Maganar bikin Baba Zakee ya fiddo da sabbin kayan
da aka d'inka mashi saboda bikin, can yace "is Ok zaki iya tafiya amman don Allah ki daina damuwa haka
kinji nasan ba zai yuwu cikin sauki ba dole sai a hankali amman try ur possible best kiga kin cireta a ranki
ki focusing kan karatunki ba kamar da final Exams dinku is approaching kar ki bari hakan yaja maki
Matsala don O level is very important shine tushen kowane karatu Mutum ke son yi without O level u'r
going no where" kai ta jinjina mashi yaci gaba "in kina da wani matsala kar kiji komae ki sanar dani
H,zakee yace ya siya maki waya right?" Shiru ta d'anyi alamar tunani sai kuma ta girgiza mashi kai don ita
dae tasan bai bata waya ba,

"Ok amman tabbas yace ya siya maki waya nasan zata zo hannunki so zan amshi phone no dinki sai mu
rink'a communicating" kai ta d'aga mashi yace zata iya tafiya har ta juya taji muryarshi na fad'in "
_Destiny may be delayed but cannot be changed Mom Zaraah_" da sauri ta juya ta kalleshi taga yana
sakin murmushi ya jinjina mata kai alamar tabbatar mata da abunda yace kafin yace "kar ki wasa da
ADDU'A" daga haka ya koma cikin Motar yay mata alamar ta shiga gida kafin yaja kopar ya rufe ya tafi
tana tsaye tana kallon bayan Motar har yay nisa sannan ta juya da gudu ta shige gida d'akinta ta nufa
tana zuwa ta fad'a saman gado ta dasa sabon kuka abunda yafi damunta shine yadda Abbas ya fahimci
abunda ke damunta amman Haisam bai fahimta ba, tun dae gwaggo na jan tsoki tana sambatun abu
yak'i ci yak'i cinyewa sai kace an rabu kenan har dae ta saduda ta nufi d'akinta ta fara bata hakuri gudun
kada kukan yaja mata wata matsalar, a jikinta ta rungumeta tana ta bata baki har ta fara sauka can ta
d'agata tace suje tay wanka kota ji karfin jikinta ta d'aga mata kai, saida ta rakata har bakin toilet d'in
sannan ta juyo tana girgiza kai da d'an murmushi kan fuskarta, sosae taji dad'in jikinta bayan tayi
wankan ta zura doguwar riga tana gama shiryawa sai ga Haulat suka zauna kan gado tana kwalla take
sanar da ita Ya Haisam ya tafi ya barta ita kanta Haulat saida taji ba dad'i hakuri taci gaba da bata ganin
tana zubda kwalla.

ABUJA NIGERIA

(Wata School mate dina ta ce dai Abuja kiran Allah sai kace Macca🤣)

Tuni jirginsu yay landing har anje an daukkosu gaba d'aya sun hallara a tamfatsetsen Parlon gidan mai
d'auke da sets d'in Sofas sun kai ukku kama daga Royal sofas, Leathers da sauransu gaba d'aya sun
jigunu komae na falon mai k'ayatarwa ne a tsare yake akwae dining area mai d'auke da dining table mai
seats sha biyu haka duk inda set d'in kujeru suke akwae kayan kallo wato duk inda Mutum ya zauna zaiyi
kallonshi ba tare da wani ya takura ma wani ba akwae manya manyan windows da zaka ga harabar gidan
sosae kana daga cikin falon haka akwae manyan kofofi da zaisu kai ka wasu k'ananun parlos d'in masu
d'auke da bedrooms, daga gefe da gefen dining area wasu had'addun tagwayen bene ne da zasu kai ka
sama ma'ana sun sa dining area d'in tsakiya su Kansu abun kallo ne gaba d'aya yanayi da tsaruwar falon
kai kace ba a Nigeria bane, in nace zanyi bayanin komae na gidan to tabbas har ranar d'aurin auren
Haisam d'in sai tazo ban gama ba don haka na barma mai karatu ya idasa fasalta gidan da kanshi, zaka yi
mamakin irin kirkin mutanen dake rayuwa a gidan don sai ka d'auka zasu yi girman kai amman sam ba
haka suke ba bala'in kirki ne dasu sam daular da suke ciki bata saka su girman kai ba Haisam ma dae
misali ne ai, gaba d'aya sun baje sai hirar biki ake dama sun k'agara Haisam d'in yazo kullum sai sun kira
Hajiya game da hakan sai tace shine ya tsaidasu da tuni sun taho, sai tsare tsarensu suke yayin da
hankalin Haisam gabadaya ya tafi kan tunanin halin da Fatuu take ci don ba k'aramin karyar mashi da
zuciya tay ba a Airport d'in nan hotonta yak'i barin zuciyarshi jefi jefi yake saka masu baki suna hakan har
aka yi Magrib duk suka tashi don yin salla Haisam da sauran mazan harda Mahaifinsu suka nufi Masallaci
dake gefen gidan kaman dae na gidan Hajiya shima kalan fentin gidan ne sai dae su sai sun hau Mota
suke fita su je don ba hanya ta cikin gidan kuma tafiyace in ace suje a k'asa don kafin ma a fita daga
harabar gidan har a shanye jikin gidan a isa Masallacin aikine, sai da suka yi har Isha sannan suka dawo
lokacin kuma an gama shirya table duk suka hallara harda Saude tana gefen Hajiya saida Senator Alee
yasa Haisam yay masu Addu'a kaman yadda suka saba duk in za'a ci Abinci sai yasa wani yayi Addu'a, a
nutse suka fara ci bayan ya gama Addu'ar still tunanin Fatuu yake bai wani ci da yawa ba ya mik'e duk
suka ce badae har ya k'oshi ba yace ehh Senator ya ta6e baki yace "Wato Son har yanzu baka cin Abinci
sosae ko?" Hajiya tay karaf tace "bai kuwa ci ba don d'aga k'arfe ba da tuni shida muciya basu da
maraba" duk aka sa dariya Senator Alee yace "to Ango ne dae kai u need to be eating more Food" nan
ma dariyar akai su Jidderh na sussuna kai shidae d'an murmushin gefen baki yay ya juya ya fara hawa
staircases da d'an gudu gudu cike da k'warewa Senator na fad'in ya dawo ya k'ara Abincin ya d'ago
mashi hannu kawae, wai saman benen ma ma sha Allah, ko ina walwali ke tashi saboda hasken da
k'ayatattun fitilun wurin ke saki su kansu sai Mutum yay kauyanci akansu, yana kaiwa k'arshe dakakkar
kopar dake kallonshi ya tura ya shige, to jama'a gamu a wata Aljannar duniyar, had'addan Falo ne mai
d'auke da leather chairs ruwan Madara fess dasu suma L-shape ne Carpet da Curtains suma duk ruwan
Madara ne sai tarkacen kayan kallo dasu surround sound systems akwae frames masu kyau da hotuna,
yana shiga bai tsaya falon ba bedroom ya wuce shima dae ya k'awatu da tsadaddun furniture kai kace
d'akin wata yar gayun Amarya ne sam tsarin d'akin baida hayaniya ga Ac nata aiki, a bakin gado ya zauna
ya fara k'ok'arin kiran Amadu kwatsam kafin yay sending kiran sai ga kiran Fanan ya shigo still yay yana
kallon screen d'in har kiran ya katse yana tsinkewa wani ya sake shigowa he ave no option dole yay
picking kiran don in ya k'i d'agawa ta kira taji yana waya bazata ji dad'i ba kuma tunda suka iso ta kira
yace mata suyi waya anjima ko ba haka bama shi d'in ba mai wulakanci bane, waya suka shiga yi cike da
shauki tun suna yi a zaune har ya gaji ya kwanta yana facing ceiling sosae suka 6ata lokaci suna wayar
wanda yawanci kan dae Maganar bikinsu ne sai da ya nuna mata yana jin bacci sannan ta k'yaleshi
saidae koda ya duba Agogo dare yayi sosae don sha d'aya ta kusa, kifa wayar yay saman cikinshi can
kuma sai ya mik'e ya nufi toilet after some minutes ya fito sanye da bathrobe ya nufi press bayan ya
gama shiryawa cikin sleeping dress ya nufi gado saida ya latsa switch hasken d'akin ya d'auke kafin ya
kwanta kanshi saman pillow nan take zuciyarshi taci gaba da tariyo mashi yanayin Fatuu a Airport a
hankali ya fara reminiscing old times tun ranar farkon had'uwarsu har zuwa yau wani wurin yay
murmushi wani lokacin dariya wani sa'in ya girgiza kai can ya kai hannu ya d'aukko wayarshi ya shiga
gallery duk wani hotonta dake a wayan saida ya kalla wani ma ko ita Fatun bata san dashi ba a haka
bacci yay awon gaba dashi ba tare da ya fita daga images d'in ba wayar a saman cikinshi...........
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wannan
no 09013804524._

*ASM Bk2018*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.........A ranar Fatuu na dawowa daga Makaranta da yamma bayan taci Abinci gwaggo ta k'wala mata kira
ta isketa a cikin d'aki ta zauna kan kujera tace ma gwaggo dake zaune a bakin gado ga ta,

"Dama Maganar tafiyarmu ce Habuja, d'azun nan Abbas ya kira Amadu yake sanar dashi gobe da
Asuba zai zo mu wuce duk nayi tunanin sai jibi to amman wai a goben in munje zasu wuce Lagos ne
akwae shagalin da zasu yi acan to kinga ba yadda za'ai ba zai fasa tafiyarshi ba saboda mu tunda dae
hidimar ta su ce, tuni ma na gama kintsawa Amadu bai dad'e daya dawo ba bayan na kirashi a waya
gwara yazo ya shirya don bansan a 6atawa Abbas d'in lokaci daga abun Arziki" shiru Fatuu tay lokaci
guda jikinta yay wani irin weak gwaggo taci gaba "ni gaskiya bazan barki ke kadae a cikin gidannan ba
kaman yadda kika ce rannan sai kace ana hauka dae, da tunanin da nike ko in kai ki gidan Zaliha to
amman can d'in zai maki nisa da Makaranta gaskia to amman dae k'arshe dole hakan za'ai tunda nasan
ai ba'a rasa masu zuwa Makarantar taku daga can ba" sadda kanta tay k'asa batare data ce komae ba
gaba d'aya ba abunda ke mata dad'i tafi buk'atar taji ta ita kadae,
"Kinyi shiru kin d'ukar da kai" taji gwaggon ta fad'a, a hankali ta d'ago idonta har sun canja don ma ta
cije ta hana kwalla su zubo mata cikin rawar murya tace "to ko inje gidansu Haulat kafin ku dawo" d'an
jimm gwaggon tay sai kuma tace "ba wai na k'i bane ni kaina zanso ki zauna can zaifi maki sauki to
amman nayi duba ne da halin da ake ciki na babu kar kaje ka k'ara ma Mutum nauyi kan wanda yake
fama dashi", Fatun tace "ai ma har munyi Magana da Haulat din dana ji kince ba zaki barni in zauna anan
d'in ba kuma tace tana komawa zata fad'i ma innarsu" gyad'a kai gwaggon tay tace "shikenan to zan ga
abunda za'ai yanzu zaki islamiyya ne?" girgiza mata kai tay tace "ina son in yi wanka ne kuma naga
lokacin ya k'ure" gwaggo tace "to je kiyi wankan sai ki had'a kayan da zaki amfani dasu anjima sai munje
in kai ki" mik'ewa tay kawae har ta nufi kopa sai kuma ta juyo tace "ko ba sai na d'auki kaya ba sai in
rink'a zuwa ina yin wanka anan" shiru gwaggon tay tana nazari hakan yasa Fatun cewa "sai mu rink'a
zuwa da haulat" gyad'a kai gwaggon tayi alamar amincewa Fatun ta juya ta fice tana kukan zuci wanda
yafi na fili ciwo, tana fita gwaggo ma ta fita ta nufi kitchen ta fara tunanin yi ma Fatun cin cin dama suna
da lemuka a fridge tasan zata ji dad'in shi, Bayan sallar Isha suka nufi gidansu Haulat din lokacin duk suna
a tsakar gida suna cin Abinci innarsu na jin sallamar gwaggo ta mik'e tana mata maraba fuskarta d'auke
da fara'a haka ma gwaggon, innar tace su shiga daga ciki gwaggo tace ba komae su tsaya a wajen tunda
duk anan ake innar ta nufi daki da sauri ta d'aukko mata darduma bayan ta shimfida tace mata Bismillah
ta zauna, gaisawa suka shiga yi a mutunce tayi mata ya aiki gwaggon ta amsa da Alhamdulillah bayan sun
gama gaisawar tace "dama zuwa nai rokon Alfarma, gobe in Allah ya kaimu zamu tafi bikin su Hajiya
shine nake son in ba damuwa Fatuu ta zauna anan kafin mu dawo tunda bazata samu zuwa ba Saboda
jarabawa da zasu fara" yar dariya innarsu haulatun tay tace "Haba gwaggo wannan ai ba wani abu bane
da har sai kin taso kin zo, nan ai gidansu Fatima ne ko kina nan taji tana ra'ayin tazo ta kwana ai hakan
ba matsala bane wllh, ba wani abu Allah ubangiji ya tsare ya kiyaye hanya shima babansu zasu je da
sauran limaman su Malam Tanimu amman sai ana gobe d'aurin auren ni kaina naso zuwa to amman
yace basai naje ba sai dae in yi Addu'a kawae Allah ubangiji yasa Alkhairi ya basu zaman lpy da zuria
dayyiba, amman yaron yana da kirki wllh da ya barni koda iya kud'ina kenan sai naje har bashi ma zan iya
ci wllh don inje bikin nashi" gwaggo na yar dariya ta amsa da Amin tay mata godiya kafin ta dasa yabon
Haisam har tay mata tayin Abinci tace Alhamdulillah a k'oshe take, duk abun nan Fatuu na cikin dakinsu
haulatu tun bayan da suka shigo ta gaida innarsu haulatun ta jata d'aki, zaune sukae a gefen yar katifar
Haulat sukae jugum a hankali kwalla ke gangaro ma Fatuu haulat na kai hannu tana goge mata tana bata
hak'uri suna cikin hakan taji muryar gwaggo tana cewa tafito su tafi ta mik'e bayan ta gyara fuskarta
haulat ta bi bayanta suka fita, sosae gwaggo ta k'ara yima innar tasu godiya kafin ta fiddo kud'i ta bata
amman tak'i amsa tace Allah ya kyauta don Fatima zata zauna gidan ta amshi kud'i gwaggo tace wllh ba
don haka ta bata ba, da k'yar dae ta kar6a sanin dama tana yi mata Alheri, a tare suka rakosu innar na
fad'in ai tayi zaton Fatun tazo kenan gwaggo na murmushi tace sai gobe in zasu tafi innar tace Allah ya
kaimu goben lafiya daga haka suka k'ara sallama ta koma haulat kuwa saida ta rakosu har bakin lungu
sannan gwaggo tace ta koma tay masu saida safe tace ma Fatuu sai sun had'u gobe ta d'aga mata kai
kawae suka tafi.
Zaune suke gaba d'ayansu kan Dining table suna cin dinner har saida aka k'ara wani table d'in shima mai
kujeru sha biyu a haka ma wasu saidae zama sukae kan kujeru a falo, a Table d'in farko anan Senator da
matanshi da kakanninsu Haisam sai Her Excellency Hajiya Zainab, Hajiya da Sameer da Haisam duk suke,
lafiyayyun Abincine aka jere don musamman dama anyo hayar kwararrun chefs Saboda bikin to wasu
tun yau sun fara aikinsu, yau dae dole kowa Serving nashi ake Saboda Hajiya Zainab ko ba don ita bama
ba yadda za'ai Sameer yay serving kanshi Abinci Never yanzu ma a hakimce yake umarnin ma sai ya mula
yasha iska yake iya badawa shima da kai ko hannu, tsit kake ji sai karar cokulla can sun yi nisa kakansu ya
dakata idonshi akan Sameer da turanci yace "shi wannan sai yaushe zai yi auren ne?" Kakar mace tace
"ya kamata ace shima yay Aure gaskiya" yar dariya Hajiya Zainab tay tace "wannan ina tunanin har yanzu
ba'a haifi Matar da zai aura ba" waro ido duk sukae Senator yace "kar dae kice man baida wadda ya
tsayar zai aura har yanzu?" Girgiza kai tay tace "I don't think so" tay Maganar idonta akan Sameer d'in da
ko kallonsu ma bai yi ba tunda suka fara Maganar, jinjina kai Senator yay kafin yace "duk laifin Son ne ya
zaka tsaida mata shi ka barshi ko baiso sai ka tursasa mashi ai" d'an guntun murmushin gefe Haisam yay
yasan kawae dad d'in nashi ya fad'a ne amman ba wanda bai san halin Sameer ba ba yadda za'ai ayi
masa dole don kuwa rai zai 6aci ne,

"Ai kuwa ba zuba mashi ido za'ai ba k'ato dashi yay ta zama ba mata yakamata a nema mashi tunda shi
baida Niyya, Akwae k'anwar wadda D'an uwan nashi zai Aura ita yakamata a nema mashi" duk suka yi
murmushi sai lokacin Sameer d'in ya d'aga ido ya kalli Senator da yay Maganar bakin shi ya d'an d'aga
kad'an wai a hakan murmushi yay shima na mamakin jin shi za'a had'a da mata, can sai ma ya mik'e don
baison kallonshi da ake d'agowa anayi ya nufi upstairs yana taka staircases d'in cike da isa suma sunga ta
kansu, duk bin shi sukai da ido Haisam dae d'an murmushi yay cikin ranshi yana imagining yadda zaman
Aure zai yiwu tsakanin Sameer da Farha, kuma abunda basu sani ba shine yana da yan mata kawae
ra'ayin Auren ne baida shi, bayan sun gama shima Haisam upstairs din ya haye part d'inshi nan ya iske
Sameer d'in kan gado yana latsa waya dama duk in yazo a part d'in Haisam yake sauka yana shiga
wayarshi ta fara ringing Amarya tay kira bayan ya d'aga tace tana son suyi Video call ya amsa da Ok kafin
yay connecting da laptop d'inshi dake kan bedside suka fara magana akan program d'in gobe da za'ayi a
Lagos duk abun nan ko kallonsu Sameer bai yi ba tamkar bai ma jin abunda suke can Fanan tace waye a
bayanshi yace mata Sameer ne tace bari su gaisa, d'an janye jikinshi yay ya juya yace zasu gaisa ko tanka
shi bai ba har saida Fanan d'in tace"Hi Sameer!" sannan ya d'an juya ba yabo ba fallasa ya bita da ido
saidae yanayin fuskarshi ya d'an canja a hakan wai murmushi ne yay mata tana murmushi tace "hope u'r
coming to Lagos 2morrow" D'an jinjina mata kai yay kawae daga haka ya maida kanshi kan wayar
Haisam ya juya suka cigaba da Magana kafin daga baya sukae sallama ya juya ya kalli Sameer ya kai
hannu ya kwace wayar yana fad'in bari yaga abunda yake da ya janye attention d'inshi ya kasa sakin jiki
ya gaisa da bride d'inshi sosae, d'an d'age bakin dae yay Haisam ya kai idonshi kan screen d'in wayar da
sauri ya d'aga kai yay mashi wani kallo Sameer d'in ya d'age mashi gira sigh Haisam yay yace "Bro stop
decieving people and ur self Just get married" wani guntun murmushin gefe yay ma sha Allah ashe k'ilan
yasan kyaun da yake in yay murmushi shiyasa bai cika yi ba shima dae yana da dimples kaman Haisam
d'in saidae nashi biyu ne mik'ewa yay ba tare da ya ce mashi komae ba walking majestically ya nufi
hanyar toilet, aje mashi wayar yay ya d'aura kanshi akan pillow yana son ya kira Fatuu yaji halin da take
ciki amman yana ganin kaman dare yayi can dae ya kai hannu ya d'auki wayarshi yay sending mata kira
baiwar Allah lokacin tana kwance kan gado tayi lamo don ta kasa bacci sai tsumayen kiranshi take don
kwana biyu kullum da wayarshi take bacci tana haka taji ringing alamar kira da sauri ta kai hannu

tana ganin shine tay murmushi kafin tay picking ta kifa wayar a Kunnenta,

"Zaraah" a hankali tace "na'am ina wuni" amsawa yay yace ya akai batayi bacci ba tana murmushi tace
hakanan baccin ne bai zo ba, d'an murmushi yay kawae ya tambayi ya take tace mashi lpy lou daga haka
suka ci gaba da wayar yana cikin yi Sameer ya fito k'ugunshi d'aure da towel ya nufi press sai lokacin ya
juya ya kalli Haisam lokaci guda ya gane da mace yake Magana jin ya ambaci Zaraah cikin husky voice
d'inshi don ba irin muryarsu d'aya ba yace "U what do you think u'r doing, ain't u deceiving??? Wani
kallo Haisam d'in yay mashi shi kuma ya ta6e baki ya juya yana kokarin sa short da sauri Haisam ya juyar
da kai don yasan ba kunya ta ishe shi ba kimono yasa iya gwuiwa ya d'auki laptop d'inshi ya fice daga
bedroom d'in ya nufi Parlor, sosae suke fira har yake ce mata gobe su Abbas zasu zo he isn't happy da
batare da ita za'a zo ba saidae tay murmushi kawae daga baya yace ta kwanta gobe akwae skul sukae
sallama sai gashi kuwa tayi bacci bada jimawa ba.

Ana kiran sallan Asubar farko wayarta tay ringing har saida gabanta ya fad'i ganin lokacin da aka kiratan
gashi bata san lambar ba, can dae ta d'aga tay shiru tana son jin waye ya kira on the Other hand taji an
kirata da Zarah lokaci guda ta gane Abbas ne cikin muryar bacci ta amsa ta gaidashi yace gasu nan kopar
gida a bud'e ma Feenah da sauri tace to ta saukko daga gadon, d'akin gwaggo ta nufa ta fad'i mata suka
fito tare gwaggo ta nufi wajen taje ta bud'e Abbas ya fito yazo wurinta suka gaisa yace zai wuce
Masallaci gasu Feenah nan zasuyi salla in ya dawo sai su wuce tace to ya juya Feenah ta shigo tana ruke
da hannun Abdul ta rungume Nasreen gwaggo ta kar6eta Fatuu kuma taje ta kama hannun Abdul suka
nufi d'akin gwaggo gaba d'aya bayan sun zauna suka shiga gaisawa Fatuu ma ta gaishe da ita tace "Allah
sarki Zarah banji dad'i ba dake za'a ba wllh" Abdul ma yace "nima haka momy" ita dae d'an murmushi
tay haka gwaggo ma Feenah ta sake cewa "Amman dae ba gida zaki zauna ke kadae ba ko" gwaggo tay
saurin cewa "eh zata zauna a makwabta ne gidan kawarta da suke Makaranta d'aya" Feenah tace yauwa
hakan yayi daga baya suka tashi jin an kira salla, bayan sun gama gwaggo tace kota dafa masu wani abu
Feenah tace a'a bata iya cin abu yanzu amman akwae Abinci a Mota a hanya sai su ci, su Abbas da
Amadu na dawowa daga Masallaci Amadun ya shigo ya fara fita da kayayyakinsu ba 6ata lokaci suka fito
don tafiya gwaggo tace ma Fatuu ta d'aukko jakarta da uniform sai a ajeta gidansu Haulat, da tace zata
zauna in safiya tayi saita shirya ta tafi Makaranta in ta dawo sai ta wuce can amman gwaggon ta k'i
amincewa don gaba d'aya ma don ba yarda zatayi ne yasa zasu tafi su bartan, bayan ta daukko komae
suka fita Amadu ya kulle gidan gwaggo tace ya ciri makullin guda yaba Fatun yace to, Amadu ne ya shiga
gaba sai su kuma suka shiga baya Abbas na ganinta yace da ita za'a kenan gwaggo tace a'a za'a ajeta can
gaba gidan da zata zauna yace Ok yayinda a ranshi yake jin wani irin tausayinta in ba so da rashin Adalci
ba ya za'ai ace Mom Zarah bata je bikin Haisam ba da ranta da lafiyar ta, a daidai bakin lungunsu Haulat
aka ajeta duk jikinta yay wani iri gwaggo tace taje ganin tayi tsaye rungume da jaka cikin breaking voice
tace " Allah ya kiyaye hanya ya kaiku lafiya...." Da sauri ta juya jin tana niyyar fashewa da kuka Abdul ya
kwala mata kira ta juya ya fito da hannunshi yana mata bye bye itama ta d'an d'aga mashi sai kuma
Feenah da gwaggo har da Amadu suma suka d'ago suna yi mata kawae sai ta juya ta fashe da kuka saida
suka ga shigarta gidan sannan suka tafi, kopar Marusa low-cost suka wuce aka d'auki Nana kaman yadda
Haisam ya ba Abbas sak'o sai fatan a sauka lafiya.

Tana shiga d'akinsu Haulat ta aje jakar gefe ta kwanta kan katifa ta rufe fuskarta da bakinta tana ta kuka,
haulat dake gefenta tana ta bata hak'uri itama kaman zatayi kukan har saida wata k'anwar haulat taje ta
gayo ma innarsu ta shigo tana fad'in "Fatima ya da kuka kuma da girmanki don an tafi unguwa an barki
ai kaman gobe ne zata dawo ko haba daina kuka k'annenki nata kallonki sai suyi maki dariya ma" jin
hakan yasa ta sassauta kukan, da gari ya idasa wayewa da k'yar haulat ta samu tasa ta tashi suka fara
shirin tafiya Makaranta bayan sun gama aka kawo mata abun kalaci biredi da kosai da tea don Haulat ta
fad'i ma innarsu Fatun bata shan koko, bata wani ci da yawa ba tace ta k'oshi haulat taitai da ita ta k'ara
ta kafe akan ta k'oshi amai take ji dole ta kyaleta da aka kai ma innar tasu tace suje su ci, k'arfe bakwai
da rabi suka fito suka iske innar a yar barandar da take sana'ar koko haulat tace zasu tafi har ta k'irgo
kud'i zata basu cikin disasshiyar murya Fatuu tace ta barshi gwaggo ta bata kud'in da zasu rink'a yin
break innarsu haulatun tace kuma dae banda wanda ta bata, godiya tay tayi masu a dawo lafiya kafin ta
k'ara ba Fatuu hakuri suka tafi, jikinta sukuku suka nufi bakin hanya wai kuma sai take jin dama ta bisu
don kwata kwata ta rasa mike mata dad'i a haka suka k'araso bakin titi bada jimawa ba sai ga School bus
suka tafi.

Tafiya yankin Azaba,Amadu sai dae ya d'anyi bacci ya farka ya kalli hanya yayin da cikin ranshi yake ta
Murna yau dae Allah yayi zaije Abuja, akan hanya suka samu wuri acikin wani gidan mai da bai aiki suka
yi breakfast don Abdul nata kukan yunwa harda Nana don bata wasa da cikinta shiyasa gata nan
tubarkallah, bayan sun gama suka sake d'aukar hanya aka dasa baka jin komae sai muryar Nana da
Abbas dake ta hira abunsu don ita Feenah tafiya galabaitar da ita take sai jefi jefi take saka masu baki,
Alhamdulillah Allah yayi an iso a Abuja wuraren Azahar, sakin baki Amadu yay yana kallon ikon Allah da
kafin su shigo Abujar a garuruwan bakin hanya har yana ce ma Abbas dama haka Abujar take Abbas na
dariya yace ya jira tukun kafin ya yanke hukunci, sakin baki yay sai faman kalle kalle yake kaman d'an
kauye yazo birni Abbas na ta faman yi mashi dariya gwaggo ma dae bata ta6a zuwa ba amman bata nuna
k'auyanci kaman Amadu ba don shi fa tsakaninshi da Allah a k'asar waje yake ganinshi ba kaman
shimfidaddun tituna masu girma da bai saba ganin irinsu ba, ko ina titi haka yake ta fad'i can kuma yace
wai ba Keke Napep ne da babura sai motoci kawae yake gani Abbas dae dariya kawae yake yace mashi
akwae bangaren da keda akwae su nan dae inda suke babu, saida suka sake 6ata kusan awa Saboda go
slow na Motocin ma'aikata kafin suka iso gidansu Haisam d'in, "Ya ilahi ya rabbil alamen" haka Amadu ya
fad'a acikin zuciyarshi saidae baisan ya fito fili ba Nana ma cewa tay "kan uban nan!,wai anan Zakee ke
rayuwa shine don cutar kai ya koma Katsina ya tsugunna" gaba d'aya ta basu dariya, gwaggo ma dai ta
yaba ba abunda take fad'i sai "Ma sha Allah" da alama fa Amadu yay mutuwar tsaye don mamaki ya
gama cikashi tunda uwar data haifeshi bai ta6a ganin gida irin wannan ba nan take ya fara jinjinawa hali
irin na Haisam harma da yan uwanshi yadda basu d'auki Duniya da zafi ba, bayan Abbas ya parker Motar
a wagegen parking spot d'in gidan mai d'auke da jerin jigunannun motoci duk suka fito Abbas ne ya
hangi Nameer yana nufar Mota dake can gefe ya k'wala mashi kira ya juyo yana yin arba dasu ya washe
baki ya nufesu, yana zuwa ya shiga gaishe dasu yana yi masu sannu da zuwa duk suka amsa Nana tace
"yauwa mai kama da Zakee" still dariya yake ya kai hannu ya dafa shoulder d'in Amadu yace "Mutumina
barka da zuwa" murmushi yay mashi wanda yafi kama dana yak'e yace mashi yauwa, Nameer d'in ya
kuma cewa "Ya banga yar gidan ya Haisam ba mai kumatu?" Dariya duk suka yi gwaggo ta sanar dashi
bazata samu zuwa ba Saboda jarabawa da zasu fara yace baiji dadi ba, Abbas yace "zaka wani wuri ne?"
Yace "No bakin gate zanje akwae wadanda zan shigo dasu wai security sun hanasu shigowa" Abbas na
dariya yace "Ok muma saida aka tantance mu, amman ya naga ansa security sosae lafiya dae ko?"

"Eh lafiya lou akwae na Momyn Nasarawa ne" D'an bud'a ido Abbas yay "kace her Excellency na nan
ashe" kai ya d'aga alamar eh yace yaje bari ya shiga dasu Nameer d'in yace bari ya kai Amadu d'akinshi
sai ya dawo ya d'aukar mashi jakar goyonshi Amadun na cewa ya bari ya d'auka yace ya bashshi ai shi
bak'on shi ne suka nufi part d'inshi dake saman bene, ta baya suka bi don akwae benen da zai kaika
saman Amadu dai na biye dashi zarare zarare tamkar rakumi da akala,

Suna akan hanyarsu ta shiga mai Entrance na gidan Nana ke tambayar Abbas wacece Her Excellency d'in
data ji suna Magana don Mutum yay taka tsantsan, sosae Abbas yasa dariya kafin yay mata bayaninta
harda alak'arsu da Haisam ita gwaggo dama tasan labarinta, suna shiga parlon sukae kacibus da Jidderh
cike da Farinciki ta nufosu tana masu sannu da zuwa ta gaishe su duk suka amsa suna mata Murmushi
Abbas yace ta kaisu wurin Hajiya tace to tay gaba suka bi bayanta har part d'in da Hajiya take, lokacin da
ta gansu sosae tay murna sai sannu da zuwa take masu harda rungume gwaggo bayan sun gaggaisa da
Mutanen dake a parlon nata ta jasu cikin bedroom tace su huta duk suka ce salla zasu yi, kafin su gama
sallar an jere masu Abinci da abun sha suna gamawa suka hau cin Abincin don suna buk'atar shi, saida
suka samu natsuwa sannan Hajiya tay masu jagora part d'in Mahaifiyar Haisam d'in lokacin duk suna
zaune a k'ayataccen parlonta harda Hajiya Zainab da Auntynsu Haisam nan su Nana suka ga ikon Allah
sun rasa gane wacece ma Mahaifiyar Haisam d'in har saida Hajiya tay masu bayani suma Matan gidan ta
gabatar masu dasu gwaggon duk da sun santa Feenah ma ta ta6a zuwa sau d'aya wani zuwa da sukai da
Abbas ya kawota suka gaisa Nana ce dae ba'a sani ba duk ta wani natsu sai kace ba ita ba, faram faram
suka amshe su sunata godiya da Addu'ar Allah ya bar zumunci ita dae First Lady d'an murmushi kawae
tay masu daga baya Hajiya ta koma part d'inta dasu,

Abbas na fita part d'in Haisam ya wuce anan ya iske shi da Sameer da Saleem dama shi yana a gidansu
na Abuja, duk sunyi mamakin ganinshi don bai gaya masu sun iso ba last wayar da sukai da Haisam basu
kaiga isowa ba hannu ya ba kowannen su suka gaisa harda Sameer don sun san juna ta dalilin Haisam
daga baya yay joining nasu cin Abincin, Nameer na shiga da Amadu part d'inshi duk ya k'ara shan jinin
jikinshi ganin kyawawan yan gayun samarin dake ciki harda yan Ethiopia bedroom ya wuce dashi nan ma
dae ya iske wasu kyawawan guda biyu kan gado suna game a laptop cikinsu d'aya d'an Hajiya Zainab ne,
Nameer ya kallesu da murmushi yace "Guys meet my Friend from Kt" d'aya ne ya d'ago yace mashi an zo
lpy shikam d'an uwan Sameer d'in ko ci kanka bai ce ba da alama duk haka suke, Nameer ya lura da
yanayin Amadu hakan yasa ya dafa shi yace "just feel at home" d'an murmushin yak'e dai kawae yay ya
kai jakarshi cikin press kafin ya nuna mashi toilet yace ko zaiyi amfani dashi bari yaje ya shigo da
mutanen yanzu zai dawo yace to Nameer d'in na fita ya shige toilet, farko jigum yay saman seat dake
rufe hakanan duk sai yaji ya raina kanshi can kuma ya mik'e yay abunda zaiyi ya d'auro Alwala ya fito,
yana fita cikin sa'a yaga basu saman gadon ashe yana shiga toilet Ashraf k'anin Sameer yace su koma
d'akinsu nan ana interrupting nasu dama ba anan suke da zama ba shine suka fita, wani sanyi Amadu yaji
ya fara kokarin gane inda gabas take saidae ya kasa dole ya zauna gefen gado har Nameer ya dawo
d'auke da tray d'in kayan Abinci bawan Allah shi yaje ya amso mashi, tambayarshi gabas yay ya nuna
mashi ya zauna ya jirashi har ya gama sannan yace ga Abinci nan yaci ya k'oshi bari yaje ya dawo aikuwa
wa Allah ya had'a da Abinci ba Amadu ba sosae ya saki jiki ya kwashi gara ganin shi kadae ne a d'akin
yana gamawa cike da karfin hali ya d'auki tray d'in ya fita bayan ya sauka k'asa ta baya cikin sa'a yaga
d'aya daga cikin ma'aikatan dake aiki a babban Kitchen d'in dake bayan ta amsa tray d'in shi kuma ya
juya ya koma upstairs yana shiga bedroom ya haye gado nan da nan kuwa bacci yay awon gaba dashi.
Ana gama sallar la'asar masu tafiya Lagos suka fara shiri duk Abokan Haisam ne banda iyaye ko su
Jidderh baza'a dasu ba sai dae Laila da Amal k'anwar Sameer itama kusan sa'ar Lailan ce da wasu daga
cikin yan Ethiopia, haka Nameer ma banda shi da alama sha'anin na manya ne Jidderh harda kukanta
taje ta fad'i ma Mom dinsu tana son zuwa don Allah tasa aje da ita tace tay hak'uri tunda ance baza'a da
ita ba Hajiya Zainab tasa baki tace yakamata aje da ita itama ai yan mata ce da kanta ta kira Haisam tay
mashi Magana akan a sama mata ticket itama sannan akace za'a tafi da ita, kusan su goma sha biyar
harda Nana aka kaisu Airport wasu dama already suna can Najeeb ma acan ya sauka don bai k'asar, ba
6ata lokaci jirginsu ya tashi.

THIS IS LAGOS........

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wannan
no 09013804524._
*ASM Bk2019*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

........Tuni jirginsu yay landing har an daukesu Matan na gidansu Fanan angwayen kuma na a Guest house
d'in Dad dinsu Fanan nan da nan aka fara shirye shiryen event d'in da za'ai wato Indian Night, Misalin
k'arfe Goma na dare aka fara d'aukar Mutane zuwa inda za'ayi wanda katafaren Hall ne acikin wani
tsadaddan Hotel wanda na Mahaifin Fanan ne had'in gwuiwa da wasu Abokansa turawa, Wow! Wow!!
Wow!!! Just Speechless abun ba'a cewa komae sai wanda ya gani Hall d'in ya k'awatu matuk'a kai kace a
India ne koda yake indiyawan ne sukai decorating Hall d'in da taimakon Mommyn wata Friend d'in
Fanan da suka yi karatu tare suma indiyawa ne amman a Lagos suke zaune duk ita ta tsara komae
furanni kota ina, zuwa k'arfe 11 na dare duk an hallara Matan sun sha sari kala kala wasu masu wando
wasu dogayen riguna wasu na nad'awa yayinda mazan ma ke sanye da nasu wanda yawanci fakistan ne
na Maza, Farar fata kawae kake gani a wurin bak'ak'en yan k'alilan ne irinsu Abbas suma sai sukai kaman
bak'ak'en indiyawa gashi dama Lagos badae fararan fata ba sun taru wurin sosae dama suna da wannan
had'in kan sai dae basu ji ba har turawan duk shigan kayan indiyawan sukae can Ango da Amarya suka
shigo Tubarakallahu ma sha Allah har saida Alk'alami na ya su6uce ba tare dana ankare ba saida zan ci
gaba da rubutun na fahimci hakan, gaba d'ayansu shigan Red sukae Haisam na sanye da Pakistan riga
red sai wandon golden brown haka takalmanshi ma red ne anyi masu adon golden brown tamkar na
sarauta sumar nan tasha gyara sai salki take wuyanshi rataye da scarf irin wanda indiyawa ke sawa
shima golden brown wohoho ba ka ta6a cewa ba ba'indiye bane tabbas da Fatuu tazo wurin nan
zuciyarta na iya bugawa ganin ta rasa zuk'ek'en miji kamar Haisam yayin da Amarya Fanan aka sha
rantsattsan Sari ja tun daga kafarta har wuyanta gwala gwalai ne ta fito sak ba'indiyyar Amarya masu
Arziki don kuwa ba kananun kud'i bane a jikinta to d'iyar Hajiya Maryam face yar kasuwa ta kirki data
san kaya masu daraja, su kansu kayan Haisam d'in da wad'anda Abokansa su Abbas suka sa duk daga
India aka kawo su aka rarraba masu different colours and designs, a bayansu Haisam d'in su Hajiya
Maryam ne dasu Laila harda kakarsu Fanan ta wurin uba baturiya da wasu daga cikin danginsu, su Farha
ansha sari riga da wando yellow da fari sai faman yauk'i take, fuskar Haisam a sake suka shigo Fanan
kuwa sai fara'a take fuskarta cike da tsantsan farinciki komae yayi mata yadda take so suna shigowa
Friends d'inta suka hau watsa masu furanni, bayan duk an zauna an natsu MC wanda yake ba'indiye ne
amman yana jin turanci sosae ya fara gabatar da abunda aka zo yi in yayi da indiyanci sai ya fassara da
turanci, babbar kawar Amarya wadda mamanta ta tsara wurin ita ta fito tay ma kowa sannu da zuwa ta
bada tarihin Amarya da indiyanci bayan ta gama sai khairat data sha sari maroon ta fito tayi da turanci
bayansu sai aka bukaci babban Abokin ango Abbas ya fito cike da shak'iyanci ya bada da turanci yana yi
yana kwa6awa da indiyanci gaba d'aya yaba Mutane dariya bayan ya gama aka kira k'awayen Amarya
indiyawa harda khairat don da ita akai rehearsal d'in rawar da za'ayi aka sakar masu wak'ar indiya suka
fara cashewa cikin gwanancewa ba tare da suna missing steps ba abun ba k'aramin nishadantar da
mutane yay ba bayan sun gama aka bukaci Amarya da Ango su fito su taka Fanan ta mik'e dama ta shirya
ma hakan amman sai Haisam d'in yak'i tashi don shi baya rawa balle kuma rawar indiya shi gaba d'aya
program din ma baiso ba kawae don yaga tana so ne ya biye mata amman kuma shima abun ya k'ayatar
dashi, ita kadae aka kunna ma wak'ar ta fara rawa a nutse tana yi tana zagaye haisam wani lokacin ta
duk'a gabanshi ko ta sak'o kanta ta gefen kanshi kota d'aura fuskarta saman gashinshi yadda take bin
wak'ar kai kace ita ta rairata sai k'arar sarkokinta ke tashi kowa sai murmushi yake saki hardae sarkin jin
kai saida ya d'an murmusa wato Sameer, wak'ar na zuwa k'arshe ta kama hannuwan Haisam alamar ya
mik'e ta rungume shi gaba d'aya aka sa tafi da sowa, haka aka ci gaba da gabatar da abubuwan nishad'i
ana raba ma Mutane lemuna, har Abbas da Najeeb saida sukae rawa da yan Matan da sukae, oh su
Abbas an yada mata a Abuja anata fantamawa🙄, can bayan wani lokaci aka bada damar cin Abinci kowa
abunda yake so za'a zuba mashi yawanci duk Abincin indiyawa ne 6angare 6angare, Bangaren shinkafa
akwae su chicken Briyani,Veg Briyani,Briesd beef rice,Butter chicken rice, bangaren kaji kuwa akwae su,
Chicken Masala,finger chicken,chicken grilled,chicken prame, haka bangaren Salad akwae su Antipasto
salad,chicken salad,crispy salad,ponir mix salad da sauransu dae haka lemun ma akwae su Orange
juice,Apple,grape,pine apple juice da sauransu kowa saida yaci yay hani'an nima dae ba'a barni a baya
ba naci na sha Alhamdulillah😋,wadanda suka ce bazasu zo ba kun ma kanku ai ☹️

Sai wurin biyun dare aka tashi kowa ya koma masaukinsa masu bacci sukayi masu hirar abunda akayi
suka dasa, Washe gari kuma aka hau shirin komawa Abuja, kai Jama'a masu kud'i na abunda suka
gadama dama iya abunda yasa aka zo Lagos d'in fa kenan🤔, Wuraren sha biyu wasu suka tafi yawanci
Haisam ne da Abokansa dasu Nana da wasu daga cikin k'awayen Fanan d'in su kuma sai da akayi La'asar
dasu Hajiya Maryam da dangin mahaifinsu lokacin sun gama duk wani shiri suka tafi don a Abuja
hidiman take.

Suna komawa ranar aka hau shirin yin Ethiopian Night wanda Laila ta matsa sai anyi har Mahaifiyar
Haisam d'in ma tana so ayi dole Haisam ya bada had'in kai ba yadda ya iya, bayan sallar Isha duk an
gama shiri danginsu na Ethiopia dasu Laila su Jidderh harda su Amal Amarya Fanan da wasu daga cikin
kawayenta duk sunyi shigar kayan gargajiya na Ethiopia wato habesha khamis kala kala duk dogayen
riguna Matan suka sa farare masu adon golden mazan ma riga da wando ne farare sai gaban rigunan
anyi adon golden, wasu adon maroon, green da sauransu har iyaye su Mahaifiyar Haisam d'in da Hajiya
Zainab da sauransu ba'a barsu a baya ba abun ya matuk'ar bada citta su Fanan dasu Jidderh har iyayen
duk anyi masu irin gyaran gashinsu ya bud'e d'innan kaman fanka, ba wani wuri aka je ba a cikin gidan
akai program d'in anata d'aukar hotuna a wurare daban daban har a saman staircases suka jere abun
gwanin k'ayatarwa daga baya aka ci aka sha, Washe gari Alhamis Arabian night akayi a tsadaddan Event
center nan ma da taimakon danginsu Laraba aka tsara komae ya tafi daidai su Ango da Amarya dasu
Abbas an sha shigan larabawa anci dabino ansha tea an kuma sha Fruit dasu Alkubzu can na hango wasu
daga cikin yan Comment section su Bahillot,husnarh,Ma'ulee,munah bature,Boss bature,Bajatu,sis
Asma,Maman Amir,habibty, shafa adili,Angel love,Aisha da sauransu dae anata kwasan saura ana ci ana
zubawa a jaka wasu harda dabinon k'asa suke tsinta an fake da ba'a murna da bikin kuma anzo ana
k'walama lol🤣,

FRIDAY.....

Juma'at babban rana Allah ya kawo mu Abuja ta kar6i bak'uncin Manyan Mutane na gida da kasashen
k'etare don halartar d'aurin auren jarumin mu, hidima ta kacame acan cikin gidan bak'i ta ko ina sai zuwa
suke banda wad'anda dama sunzo tuni, tun safiyar ranar aka fara sanya anko, Abokan Haisam gaba d'aya
na a wani apartment na Senator dake a cikin layin nan aka sauke su har shima Haisam can ya koma yayin
da Senatorn kuma da bak'inshi na a katafaren Guest hause d'inshi, Ana gama sallar juma'a a Central
Mosque dubban Mutane suka shaida d'aurin auren ENGR. HAISAM ALEE ADAMU ZAKEE DA DR. FANAN
MOHAMMED ABRAHAM akan sadaki Naira 500k, Haisam yaga kara Al'umma ko ta ina ba K'aramin dad'i
yaji ba, su babansu Haulat duk sun zo haka yan wurin aikinsu babbar Mota suka yo mata da maza har
yan gym dinsu ma ba'a barsu a baya ba mata da maza harda Anah duk sun zo kai wasu ma shi kanshi
Haisam d'in bazai tuna inda ya sansu ba sai zuwa ake ana gaisawa dashi ana mashi fatan Alkhairi
fuskarshi cike da annuri yasha babbar rigar Farar shadda haka sauran Angwayen ma duk Farar shadda
suka sa, to a can gida ma dae duk farinciki ake kar ma Fanan taji sam bakinta ya kasa rufuwa kamar ta
zuba ruwa a k'asa tasha ba wata kunya da take ji sai faman godiya take ga Allah daya nuna mata wannan
rana cike da murna ta kira Haisam lokacin sun nufi Hotel da za'a yi reception yana d'auka ta fashe mashi
da kuka tana fad'in at long last ta zama matarshi Murmushi kawae yake saki kafin yace mata shima yana
farincikin hakan su Abbas dake gefenshi suka fara mashi tsiya yace zai kira later, daga cikin manyan
bak'in dake zuwa yin Allah yasa Alkhairi harda Hajiya Kubra ta Comment section dama Abuja tasu ce can
na hangota cikin shiga ta Alfarma ta zo harda iyalinta aka kar6esu hannu bibbiyu ba kamar data gabatar
da kanta a matsayin Fan d'in Haisam, bayan wani lokaci tace zata tafi Hajiyar Sanata tace ya kamata ta
tsaya aje dinner dasu anjima tace to zasu je anjima zasu sake dawowa ta bukaci sanin time d'in da za'a yi
dinner d'in aka fad'i mata,

Jama'a wai ya Fatuu????


Gaba d'aya ranar ta k'ara harmutsewa sanin yau ne d'aurin auren Haisam k'arfin hali kawae take a
Makarantar amman ko daga yanayin fuskarta zaka fahimci ba daidai take ba, ba abunda haulat ke gani
kan fuskar tata face tsantsar tashin hankali, bayan an tashi suna zuwa bakin lungun gidansu Haulat tace
mata gida zata anjima zata zo kasa dakatar da ita haulat d'in tay ta bita da ido har tay nisa, tana zuwa ta
bud'e gidan ta maidashi ta datse tun a bakin kopar daki ta saki jakar ta fizge hijab dinta ta nufi gado da
gudu sai lokacin ta samu damar sakin kukan dake ta cinta, sosae ta shiga rizgar kuka tana cikin kukan ta
mik'e taje ta jawo drawer chest ta mirror d'inta ta curo IV d'in bikin ta koma kan gado tana kallo tana
cigaba da rizgar kuka har time d'in da akasa za'a d'aura Auran yay tana a hakan sai ma abunda ya k'aru
ma daga kukan duk ta fita hayyacinta fuskarta tay jajir can kuma a fusace ta fara Magana tana fad'in
"nasan na rasa ka yanzu bazan ta6a samunka ba Ya Haisam kayi Aurenka ka barni cikin mawuyacin hali
ko kirana ma ka daina yi to nima na daina sonka,na daina na daina na daina.......".

Haulat na komawa gida ganinta ita kadae yasa innarta tambayarta Fatuu tace mata ta wuce gida ta
d'aukko abu, bayan tayi wanka tay salla taje wurin innarta a d'aki tace a bata Abincin Fatuu zata kai mata
tana kallonta tace "to ba zata dawo ba?" Yan kame kame ta fara yi tace "eh amman tace sai anjima"
shiru innar tayi sai kuma tace "wai kodae wani abu na damunta ne naga duk ta canza kamar tana cikin
damuwa ko?" Yan kyafcen kyafcen idanu haulat ta hau yi murya na d'an rawa tace "a'a... ba wani abu
kawae dae har yanzu tun ciwon data yi kwanaki bata ida warwarewa ba ta koma kaman da" gyad'a kai
innar tay tace Allah ya bata lpy da sauri ta amsa mata da Amin, bayan ta zuba Abincin haulat tasa Hijab
ta nufi gidansu, tana isa kopar gidan ta iskeshi a rufe ta fara buga kopar shiru shiru ba'a bud'e ba kuma
tana da tabbacin Fatun na ciki, can ta aje yar warmer d'in a gefe taci gaba da bugawa amman shiru har
gabanta ya fara faduwa ta fara tunanin kar dae wani abu ya samu Fatun wata zuciyar kuma tace ko dae
ba gidan ta dawo ba, ta kuma raya mata to ina zata tabbas tafi tunanin tana ciki, cigaba da bugawa tayi
da k'arfi can ta tuna da Fatun nada waya ai da sauri ta fara kokarin kiranta har saida ta kira sau biyu tana
niyyar tura kira na ukku taji ana bud'e kopar har saida taji wani sanyi a ranta a hankali ta d'an bud'e
kopar ta lek'o da kanta suka had'a ido da Haulat ganin itace yasa ta idasa bud'e kopar haulat din ta d'an
waro ido tana kallonta da Al'ajabin ganin yadda fuskarta ta koma idanuwanta sun kumbura gaba d'aya
ma fuskar ta kumbure da gani ba d'an k'aramin kuka ta sha ba, a sanyaye haulat ta shiga bayan ta
d'aukko Abincin ta tsaya tana kallonta tace "Fatuu ya zaki lahanta kanki akan..." Bata k'arasa ba Fatun ta
fad'a jikinta tana fad'in "Haulat na daina son Ya Haisam daga yau, yayi Aurenshi ya manta dani inata
wahala" nan da nan idanun haulat suka kawo kwalla cike da k'arfin hali ta d'ago ta tace shikenan su shiga
ciki hannunta cikin nata bayan ta rufe gidan suka nufi d'akin Fatun, a gefen gado duk suka zauna Haulat
ta aje Abincin k'asa kafin ta d'ago ta kama hannuwan Fatuu tace "Haka yakamata, ki daure ki daina
sonshi tunda kinga yanzu yayi Aurenshi yana can yana farinciki shida matarshi ke kuma kina nan zaki ma
kanki illa kuma ki sani duk abunda ya sameki kece a wahala iyaka kawae nasan bai wuce su kira ki a waya
suyi maki sannu an k'ure ya turo kud'in magani, ki daure ki cije Fatuu ki raya mafarkin ki na son zama
Doctor kinga jarabawa ke tunkaro mu bada jimawa ba kuma tattare da ita ne zaki raya burinki ko ki
kashe shi ki duba irin d'awainiyar da gwaggo ke maki Fatuu kan karatunki Saboda rayuwarki ta inganta ta
baro ki da garinku ta kawo ki nan ya kike tunanin zata ji in kika kashe mata kwarin gwiwar da take da a
kanki? ki yi hakuri ki bar ma Allah komae kinji?" Kai ta d'aga mata duk tayi sanyi sai kace ba Fatuu ba,
hannu Haulat ta kai ta d'aukko kulan Abincin tace "ga Abinci na kawo maki zaki ci ko?" Kai ta d'aga mata
alamar eh, tace "to kin ma yi salla kuwa?" girgiza mata kai tayi cikin disasshiyar murya tace "banyi ba
amman yunwa nike ji sosae" yadda tay Maganar gwanin ban tausayi, bud'e mata kulan haulat tay tace to
taci in ta gama sai tayi Salla tace to haulat na kokarin zuwa ta d'aukko mata spoon a Kitchen taga ta sa
hannu ta fara ci ta koma ta zauna tana kallon yadda take tura Abincin da gani ba k'aramar yunwa take ji
ba dama ko da akayi break a makaranta bata ci komae ba wani irin tausayinta ne ya kama haulat ta mik'e
taje ta daukko mata ruwa ta kawo mata saigashi ta cinye Abincin tass cikin d'an lokaci Haulat na d'an
murmushi don taji dad'in yadda ta ci Abincin ta mik'a mata ruwan shima ta shanye shi tass haulat tace to
taje tayo Alwala suka mike tare tana kokarin daukan kulan Haulat tace ta barshi ita ta d'auka suka fita,
bayan ta gama sallan da kanta tace bari tayo wanka har saida haulat ta rakota bakin toilet kafin ta koma
d'aki tana ta juya abun a ranta tana kuma Addu'ar Allah ubangiji yasa ta daina jin son nashi ko kuma ta
rage tunda tasan ba abune da zai yuwu lokaci guda ba sai a hankali, bayan ta fito ta shirya cikin riga da
skirt na atampa ta d'an fad'a daka kalli wuyanta amman dirin ta na nan yadda yake, falo suka koma suka
kunna kallo saidae ita Fatun idonta ne akan tv d'in amman zuciyarta na duniyar tunane tunane sai faman
imagination take akai akai Haulat ke juyowa ta kalleta su had'a ido ta sakar mata murmushi itama sai ta
d'an yi mata na yak'e.

Bayan isha aka shiga shirin tafiya Dinner zuwa k'arfe tara aka fara kwasan Mutane, wohoho Jama'a kuzo
Kuga tsaruwar wurin dinner d'in Naira tasha kashi a wurin iya decoration d'in wurin abun tsayawa
kallone, Ango yasha tsadaddun suit bak'ak'e yayin da Amarya Fanan ke sanye da wedding gown fara tun
daga kunnanta wuyanta hannunta da yatsunta duk Diamond ne mai d'an karan tsada haka takalmanta
da yar jakar hannunta masu d'auke hankalin Mutum ne, Angwayen ma duk shigan suit sukae haka
k'awaye da yan'uwan Amarya ansha ankon rantsattsan leshi jama'a ina masu sana'ar lalle da d'inki ku zo
ku dau style iri iri wani d'inkin sai kace na Aljanu gaba d'aya an watse karamar leshin, ina ganin Farha na
hau tunanin yadda akai tasa fitted gown d'in jikinta k'arshe dai na yanke a raina k'ilan a Jikinta aka d'inka
ta, Ma sha Allah an ci an sha an kuma nishadantu can na hango Hajiyar Sanata da Hajiya kubra suma duk
sun sha leshi ashe dae ta dawo da gaske to Momy muna godiya Allah ya bar zumunci, su Fanan a banza
an kadaddabe Haisam balle yanzu da igiyan Aure ya shiga tsakani sam bata barshi ya wataya ba tabi ta
k'ank'ame abunta amman banga laifinta ba mijinta ne halak malak, sai wurin d'aya aka tashi Haisam duk
ya gaji da hidindimun don shi ba mai son hayaniya bane, Washe gari Asabar akai Mother's eve wanda
yazama tamkar Walima don a cikin gidan akayi shi ranar ankon shadda aka sha abun dae sai dae ace ma
sha Allah, sai bayan isha taro ya watse masu tafiya suka tafi Misalin k'arfe goma da wasu mintuna
Haisam na tare da Abbas a gaban parking lot basu dad'e da shigowa ba daga wurin sauran bak'in su da
basu kaiga tafiya ba don wasu duk sun tafi tun jiya Sameer ma sun tafi yau da safe, zaune suke a saman
boot duk suna sanye da shadda dinkin sen style duk basu da huluna akan suna cikin fira wayar Haisam
dake ajiye gefe ta fara ringing ya kai idonshi kanta Amarya ce tay kira hannu ya kai ya dauka kafin yay
picking call d'in ya kara a kunne tun kafin yace wani abu ta riga shi da tambayar inda yake taje part
d'inshi bai nan ya bata amsa da inda yake daga haka tay cutting call d'in ya maida wayan inda take Abbas
na murmushi ya tambayi Amarya ce ya d'aga mashi kai kawae, bada jimawa ba sai gata ta 6ullo ta baya
jikinta sanye da wata matsiyaciyar fitted gown ta atampa super daga k'asa ta bud'e sai tay kaman kifi
mermaid kanta tayi fav d'aurin kallabinta wato Zaraah buhari tana sanye da fashion d'an kunne da yan
hannu hannunta ruk'e da wayarta yayinda kafarta ke sanye cikin flat shoes sumarta ta linkata ta yadda ta
dawo daidai tsakiyar bayanta, wani kalan fitinannan kamshi mai narkar da zuciyar wanda ya shaka take
saki ba a kayanta ba ba kuma a Jikinta ba don ba k'aramin gyara tasha ba tun daga cikin jikinta zuwa kan
fatarta ita kanta tana jin canji a jikinta sosae ta tsumu da yawa, tunda ta tunkaro su idon Haisam na
kanta haka Abbas ma sai sakin murmushi yake tun kan ta k'araso kamshin ta ya rigata isowa tana zuwa
gabadaya ta fad'a jikin Haisam ta d'aura kanta a saman shoulder d'inshi don a zaune yake, wani kalan
lumshe ido yay ya d'an juyar da kai yana kallonta daga yadda take ta gaishe da Abbas dake zabga
murmushi ya amsa yace "Amarya ya gajiyar hidima?" K'asa k'asa tace "akwae shi don am completely
exhausted" d'ago kan tayi idonta akan Haisam sukae ma juna kallon cikin ido seductively ta furta "I ave
been looking for u since nayi trying no d'inka bai shiga ba sai yanzu" kallonta kawae yake yadda take
Maganar underneath his breath ya furta"What's it, do u have any problem?" K'ara kwantar da kan tayi
ba tare data ce komae ba, Abbas yace "baka ji tace she's exhausted ba I think she needs some fresh air
ko ta rage gajiya ya kamata ta d'an ga gari ai ansha hidima da yawa?" daga yadda take tace "u'r right
Abbas" wani kallo Haisam yay ma Abbas d'in ganin dariyar da yake yasa ya fahimci da biyu yay Maganar
da yayi sigh yay yace "aiki ya sameka sai ka shiga kai driving muje" wata yar iskar dariya Abbas yay yace
"aiki ya same ni ko ya same ka ko kana nufin mun gama ma hidiman bikin Matan ma mu zamu yi maka
dawainiyar ta in zaka tashi kai aikin matarka ka tashi ni wllh ba in da zani zuwa ma zanyi in kwanta don
nima a gajiyen nike" daga haka ya diro ya aje mashi car key d'in yay gaba yana dariya yana fad'in sai sun
dawo, Abbas na tafiya ya kai hannu ya d'ago da face d'inta suka k'ura ma juna ido Fanan sai faman
lumshe ido take shima nashi a d'an lumshen suke duk sun cika juna da k'amshi, dirowa shima yay ya
kama hannunta ya zagaya other side d'in Motar ya bud'e mata ta shiga ya kai bakinshi ya manna mata
kiss a cheek d'inta ta wani kalan lumshe ido bayan ya rufe Motar ya zagaya driver side ya bud'e ya shige
bayan ya tashi Motar ta kai hannu ta kama hannunshi guda daga haka yaja suka nufi hanyar gate suna
isa aka bud'e masu suka fice..............

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wannan
no 09013804524._

*ASM Bk2020*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

........Suna hawa hanya wayar Haisam tay kara alamar shigowar message a hankali ya janye hannunshi
daga rik'on da ta yi mashi ya d'auki wayar yana k'ok'arin dubawa,

_Take it easy on her sabon shiga._

Abunda aka turo kenan kuma ba kowa bane ya turo fa ce Abbas, d'an guntun murmushin gefe yay ya fita
daga wurin ya maida wayan ya ajiye suka cigaba da tafiya, Abbas na komawa part d'in Haisam bedroom
ya nufa ya fad'a saman gado nan take yaji kewar matarshi ta rufe shi wanda in ba don hidima ba ba
yadda za'ai suna wuri d'aya har yaji kewarta can ya yunk'ura ya tashi zaune ya kai hannu ya d'auki
wayarsa dake gefenshi ya shiga call log, lambar Feenah ya kira saida ta kusa katsewa tay picking yadda
tay Magana daga jin muryarta ta fara bacci, bayan sun gaisa ya tambayeta yara tace duk sunyi bacci yace
Ok yana son ganinta ta tambayi inda yake yace ta biyo ta kopar baya yana nan ta amsa da ok, saida ta
d'aura hijab a kayan baccin dake jikinta sannan ta fita, tana zuwa bayan ta hango shi a tsaye d'an can
nesa ta nufeshi tana zuwa gabanshi da murmushi tace mashi "Dear bakai bacci ba" d'an ta6e baki yay
yace "yea na kasa shiyasa na kira ki ki taya ni fira" a d'an shagwa6e tace "kai dear wani irin fira yanzu
bacin k'asan inda muke hakanan ka tado ni ina bacci na..." bata k'arasa ba ya janyota jikinshi ta waro ido
kafin tace wani abu ya rigata fad'in "Wato kin manta dani ko har kina iya yin bacci hankalin ki kwance"
tana ganin yadda yay Maganar ta fara k'ok'arin raba jikinta da nashi tana fad'in kada wani ya gansu, K'in
sakinta yay ya riketa gam yace "to a gammu mana zunubi muka aikata ko me" d'an yamutsa fuska tay ya
fara kokarin janta yace suje tay mashi massage k'ilan yay baccin turjewa tay a marairaice tace "amman
Dear kasan fa a inda muke yanzu fisabilillahi a ina zan maka wani massage" ya bata amsa da part d'in
Haisam idanu waje tace "ya hakan zai yuwu cikin Abokanka!" d'an murmushi yay yace mata ai ba kowa
shi kadae ne Haisam d'in ma ya fita da Amaryarshi tana jin haka ta d'an bud'a ido Abbas d'in yay dariya
yace su je mana, to dae itama tana kewan mijin nata hakan yasa ta bishi suka nufi kopan baya mai stairs
da zasu kai ka parts d'in sama ta baya, suna shiga kopan ya sungumeta yana taka staircases d'in sai yan
nok'e nok'e take don gaba d'aya a d'arare take Allah yaso har suka haye ba wanda ya gansu ya tura
kopar ya shige da ita, to dae Allah ya kyauta jin kunya ko tashin yara,

Suna hawa hanya sosae ya tambayi Fanan ko tana jin yunwa tace a'a just abu mai sanyi take buk'ata ya
jinjina kai still hannunsu na cikin na juna a gaban wani cold store ya parker motan yace mata yana zuwa
ya fita, after some few minutes ya fito hannunshi ruke da Leda mai d'auke da tambarin wurin ya zagaya
ya shiga Motan bayan ya mik'a mata ya rufe kopan kafin yaja suka tafi, bud'e ledan tay Manyan robobin
ice cream ne guda biyu ta curo d'aya ta bud'e ta fara sha cike da salon jan hankali ta rink'a d'e6owa tana
kaiwa bakinshi ba tare daya ce komae ba ya rink'a d'an bud'e bakin yana sha, zagayawa yay da ita gari
bayan wani lokaci ya tambayeta is she calm su koma gida sai ta wani langa6ar da kai cike da
marairaicewa tace "I know su khairat aren't sleeping yet suna can suna shouting and it caused me
headache" nodding kai yay idonshi akan hanya can ya tambayeta yanzu ina take so suje ba tare da ya
kalleta ba, tace "somewhere very quiet and calm" d'an juyawa yay ya kalleta idonta akanshi ta d'an
d'age mashi gira, d'an murmushi yay ya maida idon kan hanya can kuma sai ya taka burki a gefen hanya
tana kallonshi yace ta fito tay driving d'in zai yi wani abu ta amsa da Ok ta bud'e kopan lokacin shima ya
fito saida ta d'an shafi gefen fuskarshi yay mata Murmushi kafin ta zagaya ta zauna a driver seat shi
kuma ya shiga inda ta tashi ya zauna bayan duk sun rufe kopopin kafin ta ja Motar ya kai hannu ya d'auki
wayarta dake ajiye a gaba lokacin ta tambayeshi ina zasu yace mata yana zuwa hakan yasa ta dakata
bata ja Motar ba, Google map d'in wayarta ya shiga ya rubuta inda zasu sannan ya aje mata inda zata
rink'a gani ta kai idonta kan wayan tana ganin wurin daya sa ta d'an juyar da kanta gefe ta saki wani
kayataccen murmushi kafin taja Motar tana bin Map d'in suka tafi shi kuma yanata latsa wayarshi da
alama yana wani abu ne, kusan 30 minutes sannan suka iso harabar katafaren Hotel d'in ta nufi inda aka
tanada don ajiye Motoci ta sama ma tasu wuri a cikin jerin rantsattsun Motocin dake wurin, juyawa tay
ta kalleshi tace sun iso ya d'aga mata kai sai kuma ya d'ago daga kallon wayar yay mata alamar suje da
kai tana k'ok'arin bud'e Motar taji cool voice d'inshi yace "Are u going like this?" Dakatawa tay ta
langa6ar da kai shi kuma ya d'age mata gira alamar jiran amsarta sam ta manta ta d'aukko mayafi can ta
tuna da kallabinta babba ne ta curo shi ta bud'e ta rufa saman kan ba laifi ya saukko har kusan k'ugunta
sannan ya bud'e Motar itama ta bud'e ta fita, suna zuwa reception ba 6ata lokaci aka basu key d'in
d'akin da tuni ya kama masu online suka nufi VIP inda d'akin yake ya bud'e yay mata alamar ta shiga
kafin shima ya shiga kopan ta rufe, babban single room ne mai d'auke da had'addun Furniture d'akin ya
k'awatu ga ni'imtaccen sanyin Ac had'i da sanyayyan kamshi na tashi, gefen gadon Fanan ta tsaya idonta
akan shi har ya k'araso ciki ya aje wayoyinsu da keys kan bedside drawer ya d'ago shima ya tsaya a
gabanta suka cigaba da kallon juna, wani kalan kallo da basu saba yi ma juna irinshi ba suke bin juna
dashi kasa jurewa Fanan tay ta d'an sadda kanta don wani irin kwarjini yay mata, d'an murmushi ya saki
ya kai hannuwanshi ya dafa shoulders d'inta da sauri ta d'ago ta kalleshi ya jata jikinshi yay hugging nata
ta wani kankameshi sosae kawai sai jin sobbing d'inta yay alamar kuka take slowly ya d'ago da ita ya ga
da gasken kukan take tak'i had'a ido dashi, da wata irin murya ya kirata"FANAN" yarrr taji tsigar jikinta ta
tashi don rabon da ya kira sunanta har ta manta ganin tak'i dagowa yasashi sa hannuwanshi ya d'ago da
face d'inta ta kalli cikin idanunshi da idonta jage jage da hawaye underneath his breath yace "what
for??" Motsa baki ta fara a hankali tace "ba komae Ya Haisam am just feeling dat am d happiers person
on earth now, nagode ma Allah burina ya cika mun zama married couple" murmushi kawae yake saki
yana kallon yadda take Maganar, ya sani tana matuk'ar kaunarshi shima kuma yana jin sonta a ranshi,
Cupping face d'insu yay suka cigaba da shakar kamshin juna gaba daya she's irresistible ga lafiyayyan
Namiji at dat moment a hankali ya d'ago da face d'inta ta yadda har tsinin hancinsu ya had'u slowly ya
had'e lips dinsu wuri guda without wasting time suka shiga ba juna deep French kiss kasa daukarsu
kafafunsu sukae suka kai gadon suna cigaba da bawa juna very hot romances na wani lokaci ba k'aramin
kokari Haisam yay ba ya iya controlling urge d'insa a lokacin ganin suna niyyar kaiwa wani mataki da bai
shirya ma hakan ba, da k'yar ya d'an ja jikinshi breathing rapidly Fanan na ganin hakan ta kalleshi da
idanunta da tuni sun canja daga sufar su ta ainihi shima kallonta yake ganin yanayinta yasashi d'an
jawota ya kai bak'inshi saitin kunnanta cikin trembling voice ya furta "am sorry isn't proper in a Hotel
room" da sauri ta runtse idanunta all she needs at dat Moment was for him to do it with her don ba
k'aramin tsumuwa tay ba shi kanshi dauriya ce kawae don kuwa bacin kasancewarshi lafiyayye Abbas da
Najeeb sai da shima suka gyare shi tsabb, kasa cewa komae tay ta kife kanta a chest d'inshi tana ci gaba
da breathing quickly a hankali kuma wasu siraran hawaye suka fara zubo mata amman bata bari ya gani
ba, jin yadda take numfashin yasashi kai hannu yana rubbing soft skin d'in bayanta dat's opened alamar
rarrashi ta lumshe ido a hankali numfashinta ya fara daidaituwa bayan wasu mintuna ya d'an d'agota jin
tayi tsit ya ga tayi bacci ashe bin face dinta yay da kallo kafin ya kai hannu ya goge yan guntun kwallan
dake mak'ale a idanunta wanda bazai tantance na miye ba kafin ya gyara kwanciyarshi ya daurata kan
chest d'inshi sosae, shiru yay duk jinshi yake wani iri don abunda ya faru tsakaninshi da ita abune da bai
ta6a aikatawa ba shi ko had'a jiki da mace ma in ba ita ba da yan'uwanshi ko Farha bai ta6a had'a jiki da
ita ba sai dai ya dafata ko ya kama hannunta in ta kama SAI KUMA ZARAAH zuciyarshi ta raya mashi
hakan lumshe ido yay ya fara tunaninta kwana nawa bai ji ya take ba Saboda hidima lokaci guda yaji
yana son ya kirata yaji ya take a hankali ya mik'a hannu kan side drawer ya d'aukko wayarshi saidae yana
duba time yaga dare yayi sosae shi kanshi baisan dare yayi haka ba kusan d'aya saura na dare, shiru yay
yana kallon wayar sai kuma ya shiga messaging ya rubuta mata sak'o kamar haka,

_Hope u'r doing gud Zaraah._

Daga haka ya maida wayar ya ajiye,shiru yay yana tunanin yakamata su koma gida gashi duk baijin dad'in
jikinshi yana son yay taking shower amman kuma baison maida kayan jikinshi kawae sai yay deciding in
yaje gida yayi tunda ba wani abu ya same shi ba, kallon Fanan yay da alama in ba ya tasheta ba ba tashi
zatai ba, a nutse ya fara tashin ta whispering her name a hankali ta fara motsa idanunta suka fara
bud'ewa tana yi tana lumshe su har ta idasa ware su a kanshi ta k'ura mashi ido kaman bata ta6a
ganinshi ba d'age mata gira yay ya furta "My Lazy wife..." tura mashi baki tay ta maida kan jikinshi tay
lamo yaci gaba da fad'in "it's already late yakamata mu tafi u can rest more there" jinjina mashi kai tay
ya d'an duk'a a hankali yace "do u need to take bath?" shiru tay har saida ya k'ara maimaita mata sannan
ta d'aga kai alamar eh ya d'aga ta yace suje ya taimaka mata ba tare da ya jira cewarta ba bayan ya mik'e
ya sunkuceta gaba d'aya yay toilet da ita. Tunda su ka hau hanya ta juyar da kanta tana kallon gefe akai
akai yake kai ido ya kalleta can ya kamo hannunta ya d'an matsa ta juya ta kalleshi ya d'age gira yace
"Why are u sulking?" a hankali ta girgiza mashi kai alamar ba komae suka ci gaba da tafiya ita kanta ta
rasa mike mata dad'i ma jinta take wani iri, koda suka isa bai nufi Parking space ba a gefen Entrance d'in
gidan ya parker Motar suka fito a tare ya zagaya wurinta ya kama hannunta suka shiga main parlon ba
kowa tsit kake ji da alama kowa yayi bacci don kusan k'arfe 1:30 na dare, har bakin part d'in da aka
saukesu ya kaita ya manna mata kiss a goshi had'i da fad'in "Good Night" ta d'an yi mashi murmushi
kafin ta juya ta shige shima ya nufi hayar fita, tana shiga parlon ta iske khairat kwance kan doguwar Sofa
tana waya koda ta ganta ta shigo da sauri ta tashi zaune Fanan d'in ta nufeta ta fad'a gefenta ta zauna ta
d'age kai sama ganin haka yasa khairat ce ma wanda suke wayan "Honey excuse me I will call back" daga
haka tay cutting call d'in idonta kan Fanan tace "bestie where u from at dis time nata nemanki ban ganki
ba I even call ur phone yana ringing baki d'aga ba" daga yadda take ta juyo da kanta tana kallonta ba
tare data ce mata komae ba itama khairat d'in bin ta take tayi da kallo can idonta ya sauka a kan Fanan
d'in da rabinshi ke bud'e k'ura ma gashinta ido tay sai kuma ta kai hannu ta ta6a da sauri ta sauke
hannun ido waje ta ke kallon Fanan da itama kallon nata take far far da ido khairat tay tace "what am i
seeing kar dae kice man he has taken ur pride tun baku bar Kasar ba?" Sigh Fanan tay ta furta "dat's
what i wished.." gwalo ido khairat tay ta maimaita abunda Fanan d'in tace cikin d'aurewar kai ta nuna
kanta tace "but d wet hair..." tura baki Fanan tay kawae, cikin k'aguwa Khairat tace "pls tell me d truth
abunda nike tunani ya faru ko?" D'an guntun tsoki Fanan tay kafin tace "uwar gulma to ba abunda ya
faru khairat it nearly happened but he said it's improper to do it in a hotel room yanzu kin ji ko sai ki
kyale ni pls" bud'a baki khairat tay sai kuma ta kyalkyace da dariya can tace "ai da kun fad'a man na baku
keys d'in guest house d'in Dad sai kuyi shagalin ku a can ni ina nan ina aikin nemanki ashe kina can kina
enjoying" harara Fanan ta galla mata ba tare data ce mata komae ba khairat d'in ta sake cewa "U know
what gara da ba abunda ya faru asirinku a rufe don yadda mijin nan naki yake k'akk'arfa I am very sure if
to say it has happened definitely u would come back with bow legs" tana rufe baki Fanan d'in ta kai
hannu ta fara bugunta sosae ta mik'e da sauri tana fad'in bafa ita ta kashe zomon ba.

Yana fita ya shiga Motan ya kai ta Parking space bayan ya parker ya d'auki d'ayar robar ice cream d'in da
bata sha ba ya bud'e still akwae sanyi don lokacin da ya siyo shi a kankare yake a nutse ya fara sha don
yunwa yake ji tun a Hotel d'in ma yaso su ci Abinci amman ganin dare yayi sosae yasa bai sa su tsayan
ba, saida ya shanye shi duka sannan ya bud'e Motar ya fita ya nufi part d'inshi ta baya, yana shiga
bedroom d'in ya had'a ido da Abbas dake kishingide jikinshi sanye da sleeping dress da alama bai dad'e
daya kwanta bama yana ganin shi ya fara sakin wani shu'umin murmushi Haisam ya nufi edge d'in gadon
ya zauna fuskarshi a sake Abbas yace "I thought can zaku kwana ai" d'age mashi gira yay ba tare daya ce
komae ba, dagowa Abbas yay ya kai hannu gefen kafadar rigarshi inda jan bakin Fanan ya d'an goga ya
bud'a ido yace "zargi na ya tabbata dae hope baka dae illata masu yarinya ba a Hotel H,zakee" hannu ya
kai ya buge mashi hannu ya mik'e yana fad'in "We're Adult so we know what's right" daga haka ya nufi
Toilet Abbas nata mashi dariyar shak'iyanci. Washe gari lahadi Abbas yaso su tafi to amman yana son
ganin tashin su Haisam d'in hakan yasa yace ma su gwaggo sai washe gari in suka wace suma sai su d'au
hanya tace Allah ya kaimu, Ranar Litinin Misalin k'arfe goma saura na safe su Haisam sun gama shirinsu
tsab dam ba wani shiri bane sosae don daga su sai kayansu ita dama Fanan acan aka siya mata komae
duk da gidan da zasu zauna Companyn da Haisam zaiyi aiki ne suka basu akwae komae a ciki amman duk
da haka saida aka k'ara siya mata wasu abubuwan, Misalin k'arfe goma duk aka fito don rakasu Airport
harda kakar Fanan da wasu daga cikin yan'uwansu da suka zo za'a tafi Farha ma taso ta bisu amman
Hajiya Maryam tace ba yanzu ba sai in zata je sai su tafi tare gaba d'aya yan gidan dasu Abbas da
gwaggo,kawu Amadu harda Saleem da Najeeb shima daga nan zai koma Lagos acan jirginsu zai tashi
gobe dama bikin kawae ya kawo shi, Amarya Fanan na sanye da hadaddar jallabiya dark green ta fito
mata da gasken ta sosae yayinda Haisam ke sanye da fararen suit bayan sun isa Airport d'in suka tsaya
suna sake yin bankwana Farha sai kuka take yar uwa zata tafi suka rungume juna itama Fanan d'in
hawaye take bayan ta saketa ta nufi Mommynta ta rungumeta sai lokacin tasa kuka sosae itama Hajiya
Maryam d'in k'arfin Hali kawae take amman kad'an ya rage tasa kukan tana rungume da ita take k'ara
jaddada mata fad'an da tayi mata game da rayuwar gidan Aure da biyayyar miji,haka dae sukae
bankwana da kowa Senator ma ya k'ara yi ma Haisam nasiha kan Amanar Fanan da aka damka mashi ya
tabbatar mashi da zai ruk'e Amanarta, saida ya rungume duk yan uwanshi su Laila Jidderh nata kuka
haka su twins ya duk'a a gabansu yana rarrashinsu ya tabbatar masu in akae Hutu zai sa akawo su
Jidderh na jin haka cikin muryar kuka tace "Big bro nima" ya d'aga kai ya kalleta da d'an murmushi ya
jinjina mata kan, bayan ya mik'e ya nufi su gwaggo da Kawu Amadu yayi masu sallama duk sukai mashi
fatan Alkhairi da godiya sosae ya kai idonshi kan Nameer dake ta sakin murmushi yace "Sarkin murmushi
sai yaushe?" Yar dariya yay yace "ai ni nan zan zo in cigaba da karatu ba mun gama magana ba" jinjina
mashi kai yay daga haka ya nufi Mahaifiyarshi ya kama hannunta duk ta shiga damuwa sai kace yau zai
fara mata nisa, cikin breaking voice tayi mashi Addu'oi da fatan Alkhairi kafin suka rungume juna daga
nan kuma Hajiya ya nufa ya tsaya gabanta suna ma juna murmushi ya kamo hannuwanta slowly yace
"Thank u for everything Sweetheart, am gonna miss u....." bai ida ba ta fashe mashi da kuka ya jawota
ya rungumeta sosae, yana matuk'ar k'aunarta kamar yadda take kaunarshi yadda yake jinta ko
Mahaifiyar shi bai ji haka lokaci guda idanunshi suka canja yaso ta bishi amman ta k'iya ko jiya saida yayi
mata Maganar to tama k'i zaman Abuja balle kasar waje, haka Fanan ma ta zagaya

tay sallama da kowa shi Dad d'inta ya koma Lagos amman shima ya mata Nasiha kafin ya wuce kuma shi
ganinshi a wurinta ba matsala bane don US gidane a wurinshi, bayan Haisam yayi sallama da kowa
yan'uwanshi sannan ya nufi Abokanshi na Amana sukae mashi fatan Alkhairi kafin ya juya ya tafi sai
kuma ya dakata ya kira Abbas ya nufeshi ya tsaya gabanshi idonshi akanshi shima Abbas d'in kallonshi
yake yana jiran yaji mi zaice can yace mashi "Abbas pls ka kula da ZARAAH, i entrusted her to u yarinyar
ta damu da nisan da zanyi pls make sure bata yi maraicin YA HANDSOME ba" yana kai k'arshen Maganar
yaji wani abu mai kaman kwalla na son taruwa a idonshi tunowa da yadda suka rabu da sauri ya d'an
d'aga masu hannu ya juya Fanan da sauran masu tafiyan suka rufa masu baya anata d'aga masu hannu
masu kwalla nayi, nima dae nayi kwallan Ya Handsome d'in mu ya tafi😭Muna maka fatan Alkhairi.
Uhmmmm, an gama Takun Farko da Sabon salo yanzu saura kuma An yanka ta tashi, amman fa ba wani
abu nike nufi ba face Kaza aka yanka ta tashin🤣

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wannan
no 09013804524._

*ASM Bk2021*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.....Suna komawa gida su Abbas suka fara shirin tafiya dama tun jiya kowa ya kimtsa kayanshi ba 6ata
lokaci sukae sallama da kowa aka rakosu parking space bacin an had'a masu sha tara ta Arziki Senator
har 50k yaba kowanne na shan ruwa a hanya Nameer ma uban kaya yaba Kawu Amadu harda sababbi
dasu takalma a cikin madaidaicin trolley sosae yayi mashi godiya d'an zaman nan da suka yi sun shaku
sosae ji yake kaman karsu rabu gwaggo ma saida tayi mashi godiyar dama tun jiya ya bashi kayan, su
Hajiya,Mommyn Haisam Hajiya Maryam,Laila,Jidderh,twins duk suka rakosu ana ta sake yin bankwana
Farha dae na ciki tana aikin kuka dama kuma ko ba kukan take ba ba lalle ma ta rako sun ba, Hajiya ji
take kamar ta bisu to amman Senator ya hana yace ba yanzu zata koma ba sai ta huta gajiyar biki Saude
tun ran Asabar ta wuce ita da wasu yan'uwansu Hajiya na Daura Hajiyar ta hadasu sanin bazata koma
yanzu ba Nana tabi wasu yan wurin aikinsu yanzu daga gwaggo sai Amadu Feenah da Abbas sai su Abdul.

Tunda gari ya waye Fatuu keta faman farincikin su gwaggo zasu dawo har fuskarta ta kasa 6oye hakan
dama duk kad'aicin su ya isheta kullum sai taje gidan tayi zaune, bata je Makaranta ba don kuwa jibi
Laraba zasu fara Waec suna tashi bayan sunyi Karin kumallo Fatun tace ma Haulat tazo ta rakata taje ta
gyara gida ta tambayi innarta tace suje, bayan sun koma gidansu Fatun zagewa sukae ba 6ata lokaci suka
fara gyara ko'ina na gidan yay fes dashi bayan sun gama Fatuu tace su d'aura girki amman haulat tace
mata ta bari sai d'an Anjima Abuja fa ba nan kusa bace in sukae da wuri zai iya dankarewa a cikin kula
tace to su je bakin hanya su siyo Nama da zasu sa a Abincin haulat tace to, basu wani dad'e ba suka
dawo suka zauna a Parlor suna kallo can Fatuu ta tuna da sauran cin cin d'in da gwaggo tay mata taje ta
de6o masu suka had'a da lemu suna sha, bayan wai lokaci Fatun ta kira gwaggo ta tambayeta ko sun
taho tace mata eh gasu a hanya ta shiga yi masu Addu'oi gwaggon na amsawa tana yar dariya don daga
yadda taji muryar Fatun akwae tsantsar farinciki a cikin ta, tana gama wayar tace ma Haulat su d'aura
girkin yanzu don suna hanya tace to ta mik'e suka nufi kitchen suka fara shirye shiryen abunda zasu dafa,
zuwa Bayan Azahar sun gama dafa Abincin wanda Farar shinkafa ce da miya dama suna da cefane a cikin
d'an fridge d'in gwaggo na kitchen harda Coleslaw suka had'a da suka je bakin hanya suka siyo harda
kayan had'in shi saidae yanka su cabbage d'in kawae sukae basu ida hadashi ba gudun lalacewa ko
mayonnaise din ta saki sun bari sai sun iso sai su had'a, bayan sun gama Fatuu ta tafi kai markaden Aya
da dama sun gyarata don tasan gwaggo na son kunun Aya bata dad'e ba ta dawo suka hau had'awa sai
kamshi ke tashi dama Fatuu ba dae iya Abinci ba komae ta koya a wurin gwaggo haka 6angaren na yan
gayun ma duk ta koya a wurin Saude, zuwa k'arfe ukku duk sun gama komae haulat taci Abinci ta koshi
ita kuwa Fatuu wai sai sun dawo ba yadda bata yi da ita ba amman tak'i ci k'arshe ta kyaleta tay
kwanciyarta ta hau yin bacci ita kuwa Fatuu zaune tay duk bayan lokaci take kiran layin gwaggo taji sun
kawo ina wani lokaci ta samu layin wani lokaci ace out of reach can dae da yunwa ta isheta taje ta zubo
Abincin kad'an ta ci kafin ta wuce toilet tayo wanka lokacin data fito an fara kiran sallar la'asar ta yi
Alwala ta wuce d'aki, ubansun leshi tasa riga da skirt sabbi dal farko kamar karta sa kayan don acikin
kayan da Haisam ya yi mata ne sai kuma wata zuciyar ta raya mata in bata sa ba zubar dasu za'ai kuma
shi ai ba sanin bata sa ba zai yi hakan yasa ta sanya kayan, tayi kyau sosae bayan tayi Salla harda yar light
make up tayi yaushe rabo ita kanta taga kyaun da tayi tay tsaye a gaban mirror tana ta sakin murmushi
kafin ta koma Parlor ta tashi haulat koda ta tashi bin Fatuu tay da kallon mamaki tace "k'awata kinga
kyaun da kikae kuwa wllh sai kace Amarya" wani kallo tay mata mai kaman harara tace "ke kika d'aura
man auren ko" haulat na dariya tace "Eh mana keda Ya Haisam" nan da nan fuskar Fatun ta canza ta
daureta sosae Haulat na ganin haka ta hau bata Hakuri tana fad'in wasa take mata amman dae tana fata
daga haka ta mik'e ta fita itama sallar taje tayi tana gamawa tayi wanka dama ta taho da kayan da zata
canja, koda Haulat ta fita daga parlon lamo fatuu tay tana juya Maganar haulat d'in ta tana fatan ta
zamo Matar Ya Haisam to ta ya ya? Fatun ta jefi kanta da tambayar ita yanzu ta riga ta fidda ran ma
samunshi matsayin miji lokaci guda ta tuna da sakonshi data gani jiya da safe a ranta ta ayyana yanzu bai
ma da lokacin kirana kada matarshi taji haushi haka ta dingi tunane tunane can da ta ga abun na neman
yay yawa sai ta mik'e ta hau k'ara gyara gidan tasa turaren wuta, har Magrib ta gabato basu iso ba Fatuu
na zaune jigum a falo har ta fara damuwa haulat na toilet bayan ta fito ta nufi Parlon k'arar tsayawar
Mota da taji a kopar gidan yasa ta fasa shiga Falon ta nufi hanyar waje tana lekawa taga sune da sauri ta
koma cikin gidan tana fad'in "Fatuu gasu sun iso...." tun kafin ta rufe baki Fatun ta fito da gudu kallabinta
a hannu ko ta kan Haulat bata bi ba tay kopar gida daidai lokacin duk sun fito daga cikin Motar da gudu
ta nufi gwaggo ta k'ank'ameta tana fad'in "ga gwaggota ga gwaggota" dariya sosae gwaggon keyi itama
tana fad'in "ga Autata ga Autata" duk suka ba su Abbas dariya Haulat ma dariyar take tayi a gefe guda,
Boot Amadu ya bud'e ya fara shigar da kayayyakinsu dama su kadae suka rage don an sauke Feenah
Saboda tafi kusa da shigowa gari, bayan Amadu ya fito ne yace ma su gwaggon to su shiga ciki mana sai
ta maida ita ciki ma kawae gwaggon na dariya tace ai sai ta maida tan daga haka ta juya ta kalli Abbas
dake tsaye ya dafa kopar Mota ta shiga yi mashi godiya da Addu'oi da fatan Allah ya huce gajiya tace sai
tazo k'ara yin godiya har gida a gaishe mata dasu Abdul yana dariya yace ai ba komae suka juya yana ta
kallon Fatuu itama murmushi kawae take mashi ba tare data ce mashi komae ba Amadu ma yay mashi
godiya sosae ya nufi gida har sun kusa shiga gida Fatuu ta juyo ta dawo ta tsaya gefen Motar tana kallon
Abbas da har lokacin yake defe da kopar Motar yana mata Murmushi, shiru tay ta kasa mashi Magana
don Haisam kawae take gani sai yan kyafcen kyafcen idanu take tana d'an motsa baki,

"Mom Zarah kina lafiya?" Jinjina mashi kai tay kafin a Hankali tace "lafiya lou kun dawo lpy?" Kai ya
d'aga mata kafin yace "ya shirye shiryen Waec yaushe zaku fara ne?" Tace "jibi zamuyi paper d'in physics
practical sai Islamic da yamma" jinjina kai yay ya d'an yi shiru tana bin shi da ido can taji yace "Ya
damuwar ta rage ko?" d'an tura baki tay kaman bazata ce komae ba ganin ya kafeta da ido yana
murmushi yasa tana tura baki tace "eh na daina damuwa ai shima ya yi Aurenshi ya manta dani da yana
kira na amman yanzu ya daina" da alama abun na mata ciwo shi kuwa Abbas fad'ad'a murmushin shi yai
cikin ranshi ya ayyana kishi kumallon mata ganin murmushin da yake yasa ta sadda kanta k'asa ita kanta
bata san ya akai tayi Maganar ba ji tay ya kira sunanta ta d'aga kai ta kalleshi yace "kiyi hakuri amman ba
haka H,zakee yake ba shi mutum ne mai damuwa da wanda ya damu da shi in dae yasan kuna gaisawa
ya jika shiru yana tuntubar mutum yaji ko lpy ke kanki ba hakanan ya daina kiranki ba hidima ne yayi
yawa amman nasan da ya zama well settled zaki ji daga gareshi ke ai yar gatan shi ce kina d'aya daga
cikin mutanen da ya damu dasu sosae hakan ma ne yasa ko yau kafin ya bar Kasar saida yay Maganar ki"
d'an bud'a ido tay ya jinjina mata kai alamar tabbatar mata da abunda yace kasa jurewa tay tace "to
miya ce game da ni?" Yana murmushi yace "ya bani Amanarki ne yace kar na bari kiyi maraicin shi" zaro
ido tay sai kuma tay yar dariya tace "to sai ka dawo gidan Hajiya kenan" dariya kawae yay itama tay shiru
tana maimaita Maganar da Abbas d'in yay cikin ranta har taji sanyi don da tayi tunanin ya manta da ita
ne,

"Akwae Account da yace man a bud'e maki so ki fad'a a gida zuwa gobe da safe sai muje kafin ku fara
exams d'in" taji Abbas d'in ya fad'a idonta akanshi ta d'an tura baki tace "Account d'in me kuma?" Da
murmushi yace "Bank Account mana yana bukata ne nasan Saboda ya samu sauk'in turo maki kud'i ne"
yamutsa fuska tay kaman zatai kuka tace "to ai ya bani kud'i masu yawa da zai tafi ni bani buk'atar wasu
kud'i" Abbas yace "ke da zaki cigaba da karatu aikuwa kina buk'atar kud'i sosae Mom Zaraah our future
Doctor, ai dama kin bishi can kin yi karatun cikin sauk'i" wani kallo tay mashi tace "kam Matarshi taga na
lik'ewa mijinta ta koro ni, nima bazan ma je ba" dariya yasa ganin yadda tay Maganar kafin yace bari ya
wuce Magrib ya kusa ya tambayeta tana da passport guda biyu tace eh ganin yana k'ok'arin shiga Mota
tace "Ya Abbas ka tsaya kaci Abinci sannan ka tafi" dakatawa yay ya kalleta yace mata kar ta damu sun ci
Abinci a hanya kuma gida zai koma zai ci acan" tura baki tay a shagwa6e ta langa6ar da kai tace "ni dae
don Allah ka tsaya kaci nifa na dafa shi" k'ura mata ido yay yana murmushi acikin ranshi yake ayyana
yanzu ya gane dalilin da yasa suka shak'u da Haisam sosae sam in kana magana da ita baka jin ka k'osa
komae nata nada burgewa katse mashi tunani tay da fad'in "Ya Abbas zaka ci ko don Allah?" Sigh yay
yace "Ok ki zubo man in tafi dashi sai in ci a gida yanzu Magrib ya kusa amman fa bada yawa ba" washe
baki tay alamar taji dad'i tace to ta juya da sauri ta d'aura kallabin saman kai ya bi bayanta da kallo har ta
shige hakanan shima yana son ta da Haisam don ba k'aramar fahimtar juna za'a samu ba tsakaninsu ba
ita kanta yanzu yadda akanshi ta fara sanin so to ba lalle ta so wani Namiji har ta samu natsuwa da shi
kaman haisam d'in ba to amman yasan kasancewarsu tare matsayin ma'aurata ba k'aramin abu bane
gashi yasan Haisam baida ra'ayin mata biyu saidae hakan ba matsala bane don yasan Mutane masu irin
ra'ayin nashi wanda yanzu suna da mata fiye da d'ayan amman kuma ita kanta Fanan zata iya zama
shamaki kan hakan don Ya fahimci ba k'aramin kishi zatayi ba a k'arshe ya yanke duk hakan k'aramin abu
ne a wurin Ubangiji in dai ya kaddaro masu zama ma'auratan, rungume da Warmers babba da k'arama
ta fito sai Leda yar babba ruk'e a hannun ta sak'o robobin kunun Aya da Coleslaw tana ta washe mashi
baki ta nufeshi bud'a ido yay lokacin data k'araso yace "Mom Zarah wannan ai kin kwaso man Abincin
yayi yawa" bata ce komae ba ta bud'e kopar baya ta saka Warmers d'in da ledan bayan ta rufe tana
dariya tace "ai ba naka bane kai kadae harda Abdul da Aunty Feenah na zubo mawa in kuka ci ina jira ka
fad'i man yayi dad'i ko bai yi ba" yana dariya ya jinjina mata kai kawae ta juya tana ce mashi sai Allah ya
kaimu yace Ok zai kirata ya fad'i mata time da zasu fita daga haka ya shige Motar ya tafi.

Tana shiga d'akin gwaggo ta nufa lokacin tana cikin cin Abincin da Haulat ta zubo mata ta nufeta ta
zauna ta jingina da jikinta a Shagwa6e take fad'in "shine kuka je kukai zaman ku bacin tun ran Juma'a aka
d'aura Auren baku damu da kun bar ni ni kadae ba ko" dakatawa gwaggo tay tana dariya tace "to ayi
hakuri auta kamawa tay nima duk na damu da rashin ki kusa amman kuma dae ai nasan ba ke kadae na
bari ba ko" tura baki tay haulat dae nata dariyar yadda Fatun keta shagwa6a, yabon Abincin gwaggo ta
shiga yi da yadda suka gyara gidan tace sunyi kokari sosae hakan yasa ta warware ta fara dariya cike da
tsokana gwaggo tace "shiyasa bani da wani shakku akan ku in ku kai aure" turo baki Fatun tay tace "in
dae tay aure" gwaggo tace "kema ai zaki yi ne ko an dingi karatun ne ba ranar gamawa?" Tace "ai kona
gama ni bazan yi aure ba" da sauri gwaggo tace "ba Amin ba ban fata in ma kina cikin karatun Allah ya
kawo Nagari ai aurar dake zanyi kawae Kya idasa a d'akin mijinki" shiru tay kawae cikin ranta tana
ayyana da nasamu wanda nike so ma kafin in fara karatun zanyi aure na kallon haulat tay suka had'a ido
tay mata Murmushi ita kuma ta tura mata baki, Bayan Magrib duk sunyi salla gwaggo ta kwala masu kira
suka shigo d'akin suka zauna ta janyo wata katuwar jaka cikin kayan da suka zo dasu ta tura ma Fatun
tace "ga sak'on Yayanki nan tunda bazaki tambayeshi ba da Auntyn taki Amarya, d'an kallon juna sukai
ita da Haulat cikin kama kai tace "ai na tambayi ya Abbas ne fa shiyasa banyi maki Maganar ba" gyad'a
kai tay Haulat ta kai hannu ta bud'e jakar wadda ta bikin ce mai d'auke da sunayensu a cikinta ma duk
tarkacen souvenirs ne da aka rarraba a bikin kaya jibgi guda sai kace d'an gidansu ne yay auren ai ko d'an
gidansu ne bazata samu rabin su ba ma, wata k'atuwar Calendar Haulat ta fiddo ta bud'e har bata san
lokacin data furta "Wow! Gaskia sunyi matuk'ar kyau wllh" gwaggo ta amshe da fad'in "ah ai ba'a cewa
komae Haulat sai Mutum ma yaje hidimar abun sai san barka wllh amman an yi matuk'ar kokari kowa
yabo da fatan Alkhairi yake masu" Haulat dake murmushi tace "Allah ubangiji yasa Alkhairi ya basu
zaman lafiya" gwaggo ta amsa da Amin Fatuu ma ta amsa a hankali duk jikinta yay sanyi lakwas, mik'a
mata Calendar d'in Haulat tay kaman bazata amsa ba sai kuma ta amsa ta zuba mata ido Haisam kawae
take kallo sun yi kyau iya kyau hoto ukku ne a jiki babba na sama sai biyu a k'asa gefe da gefe sunyi shiga
daban daban ta Alfarma dake nuna mawadatan Mutane ne ko ina Fanan tayi dariya shi kuma d'an
Murmushi yayi wuri d'aya ne yay yar dariyar da har dimple d'inshi ya lotsa da sauri ta mik'a mata
Calendar din jin kwalla na niyyar taruwar mata a idanu, Haulat taci gaba da fiddo abubuwa harda
jakunkunan kwali suma masu d'auke da pic dinsu gwaggo ta sake janyo wata jakar ta fiddo yan buckets
masu kyau guda ukku suma dai na bikin ne tace ma Fatuu ga kuma sak'on Hajiya suma haulat ce ta bud'e
marfinsu d'aya dublan ne d'aya cincin da doughnuts d'ayan kuma Alkaki ne da cake gwanin sha'awa d'an
murmushi tayi ta tambayi gwaggo ita sai yaushe zata dawo tace bata sani ba amman zata d'an kwana
biyu, suna haka Amadu ya shigo ya zauna hiran bikin ya shiga yi masu harda pictures da Vedios ita dae
Fatuu zugudum tayi Haulat nata washe baki tana tsuma had'i da yabawa sai faman zuzuta bikin yake da
gidansu ya Haisam d'in da gaba d'aya garin Abujar don sun fita da Nameer ya zaga gari dashi bama sau
d'aya ba gaba d'aya jikin Fatuu yayi weak lokaci guda ta yanke tun farko sunyi kuskuren da har sukae
tunanin Haisam zai so ta don kwata kwata ba ajinta bane ma, sai da akayi isha Haulat tace zata tafi gida
gwaggo ta d'ibar mata abubuwan bikin tace ta kai ma Innarta ta kuma bata kud'i farko K'in amsa tay
saida gwaggon tace yaushe suka fara wasa irin haka sannan ta amsa tayi godiya itama Fatuu ta d'ibar
mata komae cikin nata ta rakata har gida koda innarsu taga abubuwan da aka bata sosae tay godiya har
tana zolayar Fatuu tana cewa da yake fa gwaggo ta dawo gashi nan tana ta fara'a yanzu ita dae yar
dariya kawae tay daga baya tay masu sallama haulat ta rakota bakin lungu ta tafi, da wuri gwaggo tay
bacci ita kuma sam baccin ya k'aurace ma idanunta tay zaune saman gado ta tasa Calendar d'in tana
sake kallo bata yi kuka ba saidae wata irin kewar Haisam d'in take ji k'arshe ta kwanta hannunta kan
fuskarshi tana shafawa tana d'an murmushi mai ciwo tunowa da abubuwa da dama a haka dae har bacci
yay awon gaba da ita.Washe gari tana cikin yin Breakfast Abbas ya kirata yace wurin 11 zai zo ya
d'auketa ya d'an shiga Jami'a ne tace to sai lokacin ta tuna bata ma fad'i ma gwaggo ba dama suna tare a
falon ta sanar mata godiya ta shiga yi da yima Haisam d'in Fatan Alkhairi tace tay sauri ta shirya kar
lokaci ya k'ure yazo ta 6ata mashi lokaci ta amsa to ta mik'e, kafin lokacin ta gama shiryawa cikin
doguwar rigar Atamfa ta d'an yi yar light make up k'arfe 11 saura yan mintuna yazo ta yafa gyalen da
suka hau da kayan da takalma ta d'auki yar jakarta ta fita saida ta lek'a tace ma gwaggo sun tafi sannan
ta nufi wajen, lokacin data isa bakin Motar kwankwasa glass tay ya bud'e yana sanye da jeans da t-shirt
ta d'an lek'a tana murmushi tace gaba zata shiga ko baya sosae ta bashi dariya jin tambayar da tayi
shima ya tambayeta a Motar ya Handsome ina take zama ta nuna mashi gaba yace to nan zata zauna
sannan ta bud'e Motar ta shiga tana yar dariya ta gaidashi tay mashi ya gajiyar hanya ya amsa sannan
yaja suka tafi, basu wani 6ata lokaci mai tsawo ba a Bank d'in aka gama mata komae bayan sun fito gari
ya d'an zagaya da ita saida ya tabbatar ta warware sosae dama Abbas d'an barkwanci ne sosae yake ta
saka ta dariya har tambayarshi tay game da Abincinta yace yayi dad'i sosae Feenah ma da Abdul sun
yaba har santi sukae sosae ta washe baki can tace to in mark zai bata nawa zai bata, d'an jimm yay sai
kuma yace "zan baki 95%" d'an jujjuya kai tay tace "Gaskia Ya Abbas ban yarda ba ka cike man 5 marks
d'in kawae mana ba kace har santi su Aunty Feenah sukai ba" yana dariya yace "No bazan baki 100 ba da
dai a gidan mijinki kika yi shi confirm kin cancanci 100%" d'an murmushi kawae tay bata ce komae ba, a
wani Eatery ya tsaya yace suje suci Abinci batare data musa ba tace to suka nufi ciki ya tambayi abunda
zata ci bayan sun zauna tace "Burger and ice cream" yar harara ya wurga mata kafin yace "I mean Abinci
ba kayan kwad'ayi ba" tace "to ai suma Abincin ne tunda ana koshi" girgiza kai yay yace ta dai fad'i
Abinci a shagwa6e tace "ni dai su nike so inna koma gida naci Abincin...." Tun kafin ta rufe baki ya fara
girgiza mata kai kaman zatai kuka tace "Wayyo bafa haka Ya Haisam ke man ba dana fad'i abunda nike
so yake man kuma kace Amanata aka baka fa" dariya sosae yasa yace shikenan yaja ma kanshi dama bai
fad'i mata ba dariya itama take yasa akawo mata abunda take so d'in shima ya fad'i abunda za'a kawo
masa, bayan duk an kawo masu suna cikin ci wayar Abbas dake gefenshi ta fara ringing ya kai idonshi
kan screen d'in yana ganin mai kiran ya dakata yana murmushi ya kai hannu yay picking kafin ya karata a
kunnanshi yace "Latest Ango Mutanen US....." Jin hakan yasa Fatuu ta kalleshi da sauri............

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wannan
no 09013804524._

*ASM Bk2022*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


.......wayar Abbas dake gefenshi ta fara ringing ya kai idonshi kan screen d'in yana ganin mai kiran ya
dakata yana murmushi ya kai hannu yay picking kafin ya karata a kunnanshi yace "Latest Ango Mutanen
US....." Jin hakan yasa Fatuu ta kalleshi da sauri yaci gaba da fad'in "Mutanen Waje ya gajiyan hidima da
tafiya" Haisam d'in ya amsa mashi da Alhamdulillah cigaba da fira su kae har Abbas d'in na tambayar shi
lokacin da zai ci gaba da aiki yace sai Next week Abbas yace "Allah ya kaimu" amsa mashi yay da Amin ya
d'an yi shiru Abbas d'in yace "gani tare da Mom Zaraah mun dawo daga bank an bud'e Account d'in
amman mun tsaya Eatery muna cin Abinci" yar dariya Abbas d'in yay jin amsar da Haisam d'in ya bashi
yace to, daga haka ya cire wayar Fatuu dake kallonshi lokaci guda ta yanke a ranta koma yace a batan ko
bai ce ba, ita dama tasan ya daina damuwa da ita ne kawae don yayi Amarya tana cikin zancen zucin
taga Abbas ya mik'o mata wayarshi yace gata, bin shi da ido tay yace "Vedio call ne zaku yi da Ya
Handsome d'in ki" yay Maganar yana yar dariya jiki mace ta mik'a hannu ta amshi wayar kafin ta kalli
screen d'in har saida gabanta ya d'an fad'i da suka had'a ido dashi, yana zaune kan leather sofa ya d'an
kishingid'a jikinshi sanye da armless data bayyanar da suffarshi abunka da zuciya tuni Fatuu taga ya canja
mata yayi mata wani irin Fresh, bin shi da ido tay ta kasa ce mashi komae Abbas dae ya ci gaba da cin
Abincin shi,

"Zaraah ina wuni" ta ji cool voice d'inshi ta fad'a, d'an tura baki tay ta d'auke idonta don tasan da biyu
yace haka can ta sake kallonshi taga still kallonta yake cikin shaky voice tace "..ina wuni, an je lpy" shiru
yay mata ta fara yamutsa fuska ta k'ara gaidashi ya k'ara yin shiru d'an tura baki tay kaman zata sa kuka
tace "to kayi hakuri" wani d'an guntun murmushi yay dama da biyu yak'i amsawa just yana son ganin
reaction d'in da face d'inta zatai displaying, bin shi da ido kawae tay can yasa hannu ya shafi beard d'insa
yace "ina fushi dake" da sauri tace "to mi nayi maka?"

"An d'aura man Aure but u couldn't call and rejoice wit me" d'an motsa baki tay ta sadda kai tabbas
bata kirashi ta taya shi murna ba kuma har Haulat saida tace mata ta kira shi amman ta k'iya, d'agowa
tay a hankali still kallonta yake duk ta kame kanta cikin rawar murya tace "to don Allah ka yi hak'uri Ya
Haisam dama inata so in kira" d'an ta6e baki yay baice komae ba ta tura mashi baki fuskarta a yamutse
alamar ya tanka amman yak'i cewa komae sai kallonta yake kawae sai da ya ga dama sannan ya tambaye
ta ya Exams tace mashi Alhamdulillah yay mata fatan Alkhairi ta amsa sai lokacin ta tambayeshi ya Aunty
Fanan yace tana lafiya daga haka yace zasu yi magana ta d'aga mashi kai ta mik'a ma Abbas wayan yana
amsa yace "wai ina Amaryar ne ta barka kai kadae zaune"? Ya bashi amsa da tana Bedroom cike da jan
Magana Abbas yace "d'anyen aure amman kai kana Parlor ita tana Bedroom ko har kun fara fad'a ne"
yar dariya Haisam d'in yay jin wata magana ta Abbas d'in sai kace wasu k'ananun yara wai har sun fara
fad'a sigh yay yace mashi tana hutawa ne bata jin dad'i, d'an buda ido Abbas yay kafin yace
"Subhanallahi mi ya same ta ne naga lafiya lou ku ka tafi" bin shi da ido yay kawae Abbas d'in ya k'ara
tambayar shi abunda ya same ta yasan in ba fad'i mashi yay ba bazai k'yaleshi ba hakan yasa shi ce
Masha is Nausea daga tafiyan da sukai amman duk da haka saida Abbas d'in yace "amman dama tana
hakan naga ta saba hawa jirgi sosae fa" ya k'are Maganar yana guntse dariya Haisam d'in yace zasu yi
magana da sauri Abbas yace "No yakamata mu gaisa ai muyi mata ya jiki ga ma Mom Zarah itama zata
gaidata" ya d'aga ido ya kalli Fatuu yace "Auntyn ki ce bata lafiya zaki gaidata ko?" Tura mashi baki tay
yay yar dariya ya maida idon kan screen d'in yace ma Haisam Zarah zata mata sannu ya kai mata laptop
d'in ya amsa da Ok kafin ya yunk'ura ya mik'e, had'add'an Bedroom ne mara hayaniya sosae komae na
cikinsa fari ne tass sai d'an ratsin baki kadan a wasu wuraren, tana kwance ta kudundune cikin lallausan
farin bargo ya tunkareta saida ya aje laptop d'in ta kalli can gefe kafin ya fara tada Fanan d'in a hankali ta
fara motsi kafin ta yaye bargon daga fuskarta suka had'a ido, yar harara ta wurga mashi tana kokarin
rufe fuskar k'asa k'asa yace Abbas ne zasu mata sannu shi da Zarah wani kallo ta wurga mashi tun kafin
tace wani abu ya riga ta fad'in it's connected yay mata nuni da laptop d'in da ido, shiru tay ta fasa yin
Magana ganin bata da niyyar tashi yace mata "sit up" d'an yamutsa fuska tay dama fuskar duk a
harmutse take tay jajir abunka da fara ga idanunta ma sun d'an kumbura da gani dai tasha kuka gashin
kanta ma duk ya harmutse haka lips d'inta ma sun d'an kumbura suma, cikin disasshiyar murya tace "but
u know I can't am feeling pain al over my body" kallonta kawae yake yana tuna gumurzon da suka sha da
ita wanda gaba d'aya ita taja har yay losing control yasa ta jigata sosae sam baiji dad'in hakan ba don da
bakinta ta rink'a gaya mashi she hates him tunda shi mugu ne baida tausayi duk da yasan Azaba ce tasa
ta fad'in hakan abun ne ma ya isheshi yay zaune a Falo har ya kira Abbas d'in a waya don su gaisa ko ya
rage damuwa, matsawa yay ya kai hannu ya taimaka mata ta zauna ta jingina da heardboard sai faman
fad'in ahhh take bayan ya zaunar da ita ya kai hannu can gefe ya d'aukko mata hula yasa mata duk abun
nan Abbas na jin su duk da bada sauti sosae suke Maganar ba shi dama yasan ba wani ciwon tafiya dake
damunta sai kace yau ta fara tafiya ai koda ma tana yin hakan to badae har abun ya kaita ga kwanciya ba
ashe mazan gaske taji ya ayyana a mind d'inshi, juyo da laptop d'in yay ta kalli screen d'in suka had'a ido
da Abbas dake mata murmushi itama da k'yar ta d'an yi mashi na yak'e yace "sannu Amaryarmu ashe
baki ji dad'i ba yanzu yake fad'a man wai Nausea na damunki" d'aga ido tayi tay ma Haisam dake tsaye
ya goya hannuwanshi a broad chest d'inshi wani kallo kafin ta kalli Abbas tay murmushi kawae bata ce
komae ba yace ga Zaraah zata gaidata ta d'aga mashi kai ya mik'a ma Fatuu wayar kaman bazata amsa
ba amman ba yadda ta iya ta kar6i wayar ta kalli Screen d'in suka had'a ido da Fanan kafin tace wani abu
Fanan d'in tace "Zaraah how are u?" A hankali tace mata lafiya lou kafin tace ya jiki ta amsa mata da da
sauki, shiru Fatun tay tana ta kallonta ita kuma sai d'an yatsine yatsine take tana sa hannu tana dafa
forehead d'inta can ta kalli Fatun tace "naga baki zo biki ba gwaggo ta fad'a man kina Exams" jinjina
mata kai Fatun tay tace Allah ya bada sa'a ta amsa da Amin daga haka ta mik'a ma Abbas wayar shima ya
k'ara yi mata Allah ya sawake Haisam na d'auka yace mashi zasu yi magana kawae yay disconnecting don
yasan halinshi yana iya mashi wata Maganar da bata kamata ba a gaban Zaraah, tun da su ka gama
wayar taji komae ya fita mata a rai zuciyarta harta yanke mata Fanan d'in ciki ne da ita don tana jin
k'awayenta in suna ma wad'anda zasu yi aure cikinsu da sun gama Makaranta Addu'ar Allah yasa suna
zuwa first night su samu ciki wata tara su zo suna, Abbas ya lura da yanayinta da ya canza yace mata ta
ida cinyewa su tafi ta d'aga mashi kai kawae haka ta rink'a turawa ba don tana jin dad'in su ba, bayan
sun gama ya biya suka tafi ya maida ta gida kafin ta tafi yay mata fatan Alkhairi a jarabawarta tay mashi
godiya sannan ta tambaye shi yaushe zai kawo mata Abdul wuni yace karta damu in ta gama exams in
dae suka samu Hutu zai kawo shi yay mata hutun yanzu dae ta dage tayi karatu sosae Allah ya bada sa'a
ta amsa da Amin daga haka suka rabu, koda ta shiga gida sosae tay yak'i da zuciyarta wurin kauda
damuwa ta d'aukko littattafan da zata karanta ta fara karatu.

Washe gari Laraba Misalin k'arfe tara na safe suka shiga paper d'in practical physics sam bata yi mata
wuya ba duk da lokacin da aka rink'a koya masu tana cikin damuwa sosae amman kuma ta fahimta
tunda tana da brain mai kyau, kafin lokacin da za'a gama ma ita har ta gama ta taimaka ma Haulat wurin
da ta kakare ko da Malaminsu ya zo Lab d'in yay going around yana ganin yadda suke yi yana zuwa kanta
ya duba da murmushi yace "Weldone Sp kinyi komae daidai" d'an murmushi tay yace ta d'an taimaka ma
na kusa da ita wanda basu gane ba tace to amman tana tsoron supervisors dake cikin lab d'in kar tay laifi
yace ba wani abu sun yi magana dasu, aikuwa sosae ta shiga taimaka ma sauran students tana nuna
masu yadda zasu yi, bayan sun fito ne kuma ta rarraba ma wasu daga cikin k'awayenta abubuwan bikin
Haisam da ta kwaso, zo ka ga yadda Students suka rud'e suna yaba kyaun da sukae wasu na cewa sun ji
sanarwar bikin a Radio wasu a Tv, wasu harda Addu'ar suma Allah ya basu mijin Novel yayin da wasu ke
tambayarsu su d'in Matan Novel ne da zasu samu mijin Novel haka sukae ta shak'iyanci sosae suke ta
Fatuu dariya wata har tana ce ma Fatun itama tasan mijin Novel zata aura tunda tana da suffar Matar
Novel ita dae dariya kawae tayi yayin da cikin ranta ta ayyana na samu kuma na rasa, har Malamai duk
wanda yazo wucewa yaga Calendar d'in ko wani abu mai hotonsu sai ya tsaya ya tanka har discipline
master d'insu da ya gani yace yana so shima aka bashi Calendar dasu jotter, basu koma gida ba a Cikin
Makarantar suka ci Abinci har Abbas ya kirata yay mata ya Exams haka gwaggo ma da Kawu Amadu,
k'arfe 3:00 suka shiga next paper ta IRS wannan ai ko awa ba'ayi ba ta gama ana fara amsa duk suka
bada don itama Haulat d'in ta gama cike da farinciki suka koma gida.

After 2 Months,

A kwana a tashi ba wuya a wurin ubangiji, a yau su Fatuu na cikin tsananin farincikin da Allah ya nuna
masu gama jarabawar su lafiya sai murna suke suna celebration don har anko sukae dogon skirt da yar
top sai coat mai d'auke da year d'in da sukae graduation da department d'in da Mutum yay wasu sun sa
himar wasu hula facing cap wasu kuma gyale sukae rolling sai d'aukar hotuna suke harda Malamai sukae
d'an party, Fatuu ba tayi komae ba ta raba kaman da Jsce, gwaggo ta so yi mata abubuwa don har kud'i
Haisam ma ya turo mata yace tay hidiman graduation d'in amman tace ma gwaggo duk asara ne ayi wani
abun dasu kawae, tun wurin Azahar suka gama amman basu fita daga Makarantar ba sai wuraren La'asar
a k'asa suka taho suna ta nishad'i ganin suna ta tafiya haulat tace mata ita dae gaskiya ta gaji amman
Fatun tace aikuwa yau k'asa zasu je gida, suka ci gaba da tafiya har suka fara yin nisa sosae, suna cikin
tafiya wata galleliyar Mota ta tsaya a gefensu da yake a gefen titin suke tafiya juyawa sukae a tare suka
kalli Motar kafin suka juya don cigaba da tafiya kawae sai gani sukae glass d'in Motar ya fara sauka nan
take sukae arba da mai tuk'a Motar wanda matashi ne zai iya kaiwa shekaru 28 haka wankan tarwad'a
ne yana sanye da kananan kaya kuma da gani Hutu ya zauna mashi sosae, lek'o da fuskar shi yay da d'an
murmushi yace "Barka dae yan graduation" Haulat ce ta tsaya ita kuwa Fatuu gaba tay abunta itama
d'an murmushin tay tace mashi yauwa yace "I just passed sai na gan ku shine nace bari mu gaisa" tana
murmushi tace sun gode d'an juya kanshi yay ya kalli Fatuu da tay gaba yace "ita friend en naki bata
gaisawa da wanda bata sani bane" juyawa tay itama ta kalli Fatuu dake ta tafiyarta kafin ta maido idon
kanshi tace "kusan hakane kasan ba kowa ake yadda dashi ba yanzu" yar dariya yay yace "hakane nima
bai kamata in tare ku a bakin titi ba, in ba damuwa ki bani no d'in ita friend d'in taki sai in zo gida mu
gaisa da ita" d'an jimm Haulat tay sai kuma ta juya ta k'ara kallon Fatun tunani ta shiga yi tasan ko ta
bashi no d'in Fatuu aikin banza ne don ko ya kira ma ba saurararshi zatai ba don sam ta haramtawa
kanta yin saurayi, dubara ce ta fad'o mata ta juya tace mashi "kayi hakuri ko na baka no d'in ba zatai
maka wani amfani ba don ita d'in akwae sa rana a kanta dama da mun gama Makaranta za'ai bakin ta
kuma gashi mun gama d'in to ba lalle ta saurare ka ba" d'an buda ido yay sai kuma yayi murmushi yace
"Ok bansani ba ne amman ba wani abu Nagode sosae" tana murmushi tace to har zata juya yace su zo ya
kai su subar tafiya cikin rana, juyawa tay da niyyar yi ma Fatun Magana kawai sai ta ga har ta tsaida masu
Keke Napep kallon shi tay tace yayi hakuri ta riga ta tsaida masu abun hawa yace to ba matsala tace
mata yana mata fatan Alkhairi Haulat d'in ta amsa da to daga haka glass din ya d'aga ita kuma ta tafi,
lokacin da ta k'arasa Fatun har ta shige cikin Napep d'in itama sai ta shiga dama ita suke jira mai Napep
d'in ya tambayi inda zai kaisu Haulat tace mashi Barhim sabuwar Abuja ya ja suka tafi, kallon Fatuu tay
da yake mai Napep d'in ya kunna Wak'a tasan ba jin su zai ba tace "Wannan Mutumin fa don ke ya tsaya
har cewa yay na bashi no d'in wayar ki sai ya kira tunda baki tsaya ba amman nasan ba lalle ki saurare shi
ba shiyasa nay mashi k'aryar an kusa bikin ki" d'an ta6e baki Fatun tay tace "gwara da kika ce mashi
hakan ya kama gabanshi don kuwa ba sauraran nashi zan yi ba" idon Haulat a kanta ta d'an girgiza kai
tace "Wai Fatuu miyasa kike korar samari ne, da wuya mu fito ba'a samu wanda ya nuna yana son ki ba
Amman sam kin k'i ki fara saurarar kowa komi kice karatu to karatu yana hana ayi saurayi ne ko kuwa
zaki ta karatun ne ba ranar da zaki aure??" wani kallon gefe tay ma Haulat d'in ba tare da ta ce mata
komae ba Haulat taci gaba "nasan duk Saboda Ya Haisam ne baki saurarar kowa ba wani abu ba, zuwa
yanzu yakamata ki cire son shi kwata kwata a ranki kema ki tsaya ki samu wanda zaki rayu tare dashi
kada kita korar Mutanen kirki ba tare da kin sani ba, ki yi hakuri in na 6ata maki rai amman gaskiya nike
fad'i maki kaman yadda ya samu abokiyar rayuwa wadda yanzu na tabbatar bata rasa juna biyu kema ki
fara tunanin sama ma kan ki wanda zaku rayu tare ki hak'ura da ya Haisam don matuk'ar yana ranki to fa
bazaki ma kanki abunda ya dace ba shawara ce nake baki a matsayina na mai son cigaban rayuwarki" a
hankali tace mata ta gode kawae don kuwa son Ya Haisam na nan a cikin ranta ta rasa ta yadda zata cire
shi, suna haka wak'ar da mai Keke Napep d'in ya kunna ta k'are wata ta shiga ta Labarina baitikan wak'ar
suka fara kaman haka

🎶🎶Dawo bamu gama zama ba, dama ba mu raba jini ba, wai nikam mai naiwa kauna bata mi ni wuri ba
labari da kai ne dawo bamu gama zama_🎶🎶
_🎶🎶Ban gani duhu haka na kwana, yanzu ma hakan na ishi rana, damuwa ta damu da gani na gashi ta
raba ni da wani na, mi nai wa kauna ne guna bata iya zama ba, yafe man in na mutu so ne bai gama salo
ba...🎶🎶_

Natsuwa sukae suna sauraran wak'ar dama Fatun kusan kullum sai ta saurareta ji take tamkar ita a kai
ma wak'ar lokaci guda kwalla suka fara zubo mata sharrr da sauri Haulat tace ma mai Napep d'in "Malam
don Allah in ba damuwa ka canja wata wak'ar" yace "yanzu kuwa Hajiya ai dama don jin dad'in ku muke
sawa bari a canja maku" ya kai hannu yana yana k'ok'arin canzawa ana fara taken wak'ar Fatun ta saki
d'an murmushin takaici don kuwa itama wak'ar kamar dae waccan ita wannan ma jinta take kaman ita ta
raira ma kanta ita ta hamisu breaker ce mai taken ' _so gaskiya ne yadda yay min ni na gane, in dai amo
ne kanshi ban daina shi zancen gaskiya_🎶🎶 da sauri Haulat tace "Don Allah malam ka kashe wak'ar duka
ta cika mana kunne" wannan karon juyowa yay yana niyyar yi mata Magana idonshi ya sauka kan fuskar
Fatuu yana ganin kwalla yay d'an murmushi had'i da girgiza kai ya juya ba tare da ya ce komae ba a cikin
ranshi ya ayyana ta Kamu da mugun ciwo ya kai hannu ya kashe gaba d'aya kaman yadda Haulat d'in ta
buk'ata, suna gab da isa gwaggo ta kira Fatuu bayan ta d'aga ta tambayeta har yanzu basu taho bane
don d'azun sun yi waya lokacin da suka gama Exams, ce mata tay gasu nan sun kusa isowa tace to ta
taho harda Haulat ta amsa da to, dai dai gefen shagon Amadu dake a rufe mai Napep d'in ya tsaya suka
fito bayan sun biya shi suka nufi cikin gidan mai Napep d'in ya bisu da ido a ranshi yake ayyana "Gata dae
tubarkallah ko wani ya yaudareta ko kuwa wani take so ta rasa shi Allah kadae ya sani" daga haka yaja ya
tafi, suna shiga cikin gidan suka jiyo Wak'a na tashi ta happy graduation Fateema Zarah a cikin falo da
sauri suka nufi falon suna shiga sukae turus a bakin kopar da tsananin mamaki akan fuskokinsu gaba
d'aya an k'awata falon da flowers da balloons cards da sauransu kaman dae irin decoration d'in birthday
a bangon dake kallon Mutum in ya shiga an had'a rubutun Happy Graduation Fateema Muhammad Ardo
and Haulat is'haq a tsakiyar d'akin kuma k'aton cake ne saman table da sauran abubuwan ci, da gudu
Fatuu ta nufi gwaggo dake tsaye tana masu dariya ta kankameta cike da farincikin surprise da suka mata
sakin ta tay ta nufi Kawu Amadu dake gefe shima ta rungume shi sai kuma ta fashe da kuka duk suka sa
dariya Amadu ya hau goge mata kwallan yana fad'in yau ranar Murna ce don daga yau ne ta hau matakin
cikar burinta ta jinjina mashi kai yace yana mata fatan nasara cikin muryar kuka tace ta gode haka Haulat
ma saida gwaggon ta rungumeta duk suka yi mata fatan sa'a tana ta dariya tay masu godiya, ci gaba da
celebration d'insu sukai su hud'u gwanin burgewa Fatuu sai rawa take da wak'arta da aka yi mata ba tare
da ta sani ba hakan aikin Amadu ne yaba wani abokin shi yay mata kuma tayi dad'i sosae daga baya
Fatuu da haulat suka yanka cake Amadu na masu Videos da iPhone d'in wani abokin shi da ya aro
Saboda hakan, sosae su kae hotuna kuma sunyi matuk'ar yin kyau sai bayan Magrib sannan Fatuu ta raka
Haulat bayan an d'ibar mata komae cake d'in ma mai yawa aka bata tanata godiya, Fatuu na dawowa
tasa Kawu Amadu ya tura mata pics d'in da videos ta shige d'aki ta fara aikin d'aura su a Status kan kace
mi aka fara mata comments na taya murna wasu ma duk suka d'auka suma suka d'aura sai farinciki
Fatuu ke yi jin yadda ake ta yabawa har wasu Friends d'insu na cewa shine ko a gayyace su, tana cikin
duba wad'anda suka d'aurata kwatsam taci karo da na Haisam da mamaki ta bud'e hoton farko wanda
akai mata ita kadae a gaban rubutun cikin falon tayi dariya duk dimples d'inta sun lotsa sosae a k'asan
shi ya rubuta 'Wishing u success in ur Exams beloved sis Zarah' na gaba kuma wani d'an short video ne
tana ta dariya had'i da yin Magana sam bata ma san anyi mata shi ba can kuma ta tura yankin cake a
baki duk ya 6ata mata gefen baki kai da ganinta a Videon zaka fahimci tana cikin tsantsar farinciki sosae
tasa Dariya da ta ga Videon wato tun kafin Amadu ya turo mata ya tura ma Haisam, tana cikin hakan
kuma sai ga kiranshi ta d'auka ta gaishe dashi bayan ya amsa yace mata congratulations tace mashi
thanks waya suka cigaba da yi wadda rabon da su jima suna yin waya har ta manta har ta tambaye shi
Fanan yace tana wurin aiki da yake su can rana ce tace shi yana ina yace shima yana wurin aiki k'arshe
ma cewa yay bari ya maida Video call tace to dama akwae haske d'akin koda ya maida tana ta sakin
murmushi shima haka suka ci gaba da yin firan har yana nuna mata Office d'inshi na can ta yaba sosae da
had'uwar shi don irin manya Office d'in da take gani ne a Fina finan turawa.

Bayan sati d'aya da yin candy d'in su Haulat tazo gidan ta sanar da ita zata tafi Nijar kuma bazata dawo
ba har lokacin bakin ta dama a can za'ayi, Fatuu bata ji dad'i ba har tana ce mata ba sai bikin ya kusa ba
sannan zata tafi tace itama tayi tunanin hakan to amman innarsu tace taje ta zaga dangi kafin bikin don
ta dad'e bata je ba, Ranar Juma'a da zata tafi har tasha Fatuu da Kawu Amadu suka rakasu da yake da
yayanta Usman zata tafi suna ta kuka suka rabu Fatuu tace mata sai sun zo biki, Allah sarki Haulat k'awar
Arziki.

Satin Haulat d'aya da tafiya lokacin ya kama satinsu biyu da gama Makaranta ran Asabar Fatuu ta dawo
daga islamiyyar safe tana tafe tana ta tunane tunanenta da suka zame mata jiki don yanzu wani irin
kad'aici ne ke damunta, ba Haisam ba Haulat gashi Hajiya har yanzu bata dawo ba balle ta d'an rink'a
zuwa can a haka har ta k'araso gida tana shiga tun a zaure ta jiyo Muryar gwaggo cikin harshen fulatanci
tana ta fad'a, lokacin da ta k'arasa a tsaye ta ganta gaban kitchen sai kai da kawowa take ga wayar
Amadu kange a kunnanta tana yin waya, tsayawa tay tana bin ta da ido hakan ya bata damar jin
Maganar da take a lokacin kamar haka "Sam bazan yarda ba wllh! Lokacin da aka bani ita ai ba ace man
za'a rabani da ita ba hasali ma kowa ba son ta yake ba anata muzguna mata sai yanzu da aka ga ta zama
Mutum shine za'a nuna man iko da ita, to bari kaji bazan ta6a yarda ta dawo ba sai dai komae zai faru ya
faru na shirya ma hakan!!!" daga haka ta katse kiran ta juyo a fusace ta mik'a ma Amadu wayar kafin ta
wuce d'akinta fuu tana ta kwafa, juyawa Amadu yay ya shige d'akinshi yayin da Fatun tay tsaye jikinta
duk yayi sanyi yaushe rabon data ga gwaggo na fad'a haka sam ta kasa fahimtar inda zancen da ta ji tana
yi ya dosa, har zata nufi d'akinta sai kuma ta juya ta nufi d'akin Amadu lokacin data shiga yana zaune a
gefen katifa yayi jigum da alama shima abun ya dameshi sosae, d'aga kai yay ya kalleta ganin hakan yasa
ta duk'a tana kallonshi itama, a sanyaye ta tambayeshi abunda ke faruwa, farko shiru yay mata yana dai
ta kallonta saida ta marairaice mashi kaman zata sa kuka tana had'ashi da Allah sannan ya sauke ajiyar
zuciya mai nauyi yama rasa ta ina zai fara ganin dae ta zuba mashi ido ne yasa yay k'arfin halin cewa
"Dama Baffan ki ne ya kira yace zai zo ya tafi dake wai Ard'o ya bada auren ki" wani bugu k'irjinta yay ta
zaro ido tana kallonshi kafin cikin sark'ewar murya tace "y...ya bada au..aurena, ni...d'in???" Kai ya d'aga
mata alamar eh, a razane tace "Waye ya ba aurena??" Shiru ya d'anyi shima duk damuwa ta bayyana
akan fuskarshi can yace "Chairman Alhaji Lawal ya nema ma d'an shi wai Dr Khalid Auren ki tun lokacin
da muka je shekara ukku da ta wuce shine ma yace a barki sai kin gama Secondary don da tun lokacin
Ard'on yace ya bashi................

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wannan
no 09013804524._

*ASM Bk2023*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.........bin Kawu Amadu kawai take da ido da alama tayi mutuwar zaune abun kaman a mafarki take jin
shi wai ita za'a ma Aure kuma ma a garinsu, shima Kawu Amadun zugudum yay yana kallonta can ta
yunk'ura da k'yar ta mik'e hannunta ruk'e da jakarta ta fita daga d'akin ta nufi d'akinta har wani Jiri Jiri
take ji a haka ta isa tana shiga ta aje jakarta a gefe ta nufi bakin gado ta zauna sai zare ido take sam tama
rasa tunanin da zata yi can zuciyarta ta fara tunano mata da Mutumin wato wanda ta iske a fadar Ard'o
har ya rink'a mata tambayoyi da turanci ashe da biyu yayi mata hakan kenan,wai d'anshi Dr Khalid za'a
aura mata! haka ta dingi maimaita sunan a cikin ranta tana haka wayarta dake cikin jakar islamiyya ta
fara ringing da k'yar ta yunk'ura ta nufi jakar ta fiddo wayar kafin ta koma bakin gadon sai lokacin ta kalli
screen d'in taga mai kiran nata, My Lovely Dad shine sunan da ta gani wato Baffan ta ne kenan, d'an
jimm tayi cike da fargaba kafin hannu na rawa ta d'aga kiran ta kara a kunne kafin tayi Magana daga can
yace "Inna wuro" har saida gabanta ya d'an fad'i kafin a hankali tace "ah Baffa",

"Kin dawo daga Makarantar kenan Amadu ya fad'a man kina can" wani abu ta had'iya jin muryar shi ta
canza sosae a hankali tace mashi eh ta dawo ta gaida shi ya amsa, shiru ya biyo baya daga ji yana son
mata magana ne amman ya kasa, can tay k'arfin halin cewa "Baffa wai da gaske an bada ni za'a man
Aure?" D'an jimm yay kafin ya fara Magana "Wallahi tallahi inna wuro wannan duk aikin Ard'o ne ni sam
bansan da Maganar wai ya bada ki ba sai wata guda da ya wuce lokacin kuna cikin yin jarabawa shine ya
kira ni yake sanar dani wai in fad'a maku ya bada ke ga yaron chairman kuma ya sanar mashi kun kusa
k'are karatun naki don haka kuna gamawa in zo in d'aukko ki, Wllh inna wuro ranar banyi bacci ba
Saboda tashin hankali ban k'ara shiga damuwa ba sai bayan da kuka gaman ya kira ni yace ai Chairman
ya fad'a mashi kun k'are don haka in zo in d'aukko ki ranar gwuiwa na a k'asa na rokeshi da a kyale ki
karatu kike son yi in kika yi za'a amfana sosae amman da bud'ar bakin shi sai cewa yay ina kokarin nuna
mashi iko da ke abunda wani bai ta6a yi mashi ba, duk yadda na so in fahimtar dashi abun ya gagara don
ce man yay ba don Alhaji Lawal d'in ya ce a barki ki k'are karatun ba ai da tun lokacin da ya nuna yana
son a bawa yaron nashi za'ai maku auren yanzu kuma ba abunda zai fasu don har sadaki ya amsa yana
wurin shi, tun ranar inna wuro banda cikakkar lpy wllh nasan kina son karatu sosae kuma muma duk
muna so hakan yasa na kasa ma kira in sanar daku don wannan Auren dole ne....." D'an dakatawa yay
yana maida numfashi dama tunda suka fara Magana ta fahimci canji a muryarshi, ci gaba da magana yay
"bayan sati guda da yay man Magana ya ga ban zo na taho dake d'in ba shine ya tara yan gidan yana
masu kukan na nuna mashi iko da d'iyata ina son bashi kunya to kowa ya shaida in dae na hana Auren
bashi ba ni, nan abun ya zama abun Magana gaba d'aya aka tsangwame mu ni da iyali na ana ta
maganganu dama suna jin haushi yadda Ardon ke d'aura ni akan komae nashi nan aka samu wasu suka
zugeshi yace bai son in k'ara sa mashi hannu a

harkokin shi, jiya naga tashin hankali inna wuro cewa yay in tattara in bar masa gida ya yafe ni kuma in
har ban bari anyi auren ba Allah ya isan shi bai yafe man ba......" Karyewa muryarshi tay ya fashe da
kuka, wani irin zaro ido Fatuu tay jin Mahaifin nata na kuka abunda bata ta6a gani ba ko ji da Hankalinta
da sauri cikin rawar murya tace "Baffana kuka kake!!" Had'iye kukan yay yace "inna wuro har ga Allah
ban son abun nan ban so wllh na fi so kiyi karatun ki zai amfanemu gaba d'aya in kika gama ko kuma kina
cikin yi Allah yasa kina da wanda kike so ku ka daidaita sai ki yi auren ki amman ba ai maki dole ba, yanzu
bansan ya zanyi ba" sosae jikin Fatuu yay wani irin mugun sanyi wani irin tausayin Mahaifin nata ne ya
kamata lokaci guda taji ranta ya 6aci da abunda ake masa wani irin kwarin gwiwa ta ji ta samu tace
"Baffana ka daina damuwa na yarda ayi man auren kazo ka d'auke ni!" murya na rawa yace "Inna wuro
kin yarda kenan kin hak'ura da karatun?"d'an murmushin takaici tay kafin tace "Eh Baffa in dae hakan zai
fitar da kai cikin halin da kake ciki to na hak'ura in Allah ya sa ina da rabo ko ba yanzu ba zanyi in kuma
bani da rabon yi ko ba ai man auren ba bazan yi ba" sosae ya shiga yi mata godiya yana fad'in "Nagode,
Nagode inna wuro yadda kika sadaukar da farin cikin ki Saboda nawa farincikin in sha Allahu ko ba yanzu
ba kema zaki dawwama cikin farin ciki har k'arshen rayuwarki, Nagode Allah ya jik'an Mahaifiyar ki dama
Aysha Alkhairi ce a gurina gashi nan har bayan ranta ina ganin Alkhairin ta..." Shesshekar kukan shi
kawae take ji hakan yasa itama kwalla suka zubo mata sharrr saidae bata bari kukan yayi sauti ba don
kar ya ji cikin breaking voice tace mashi don Allah ya daina kuka bata jin dad'in hakan da sauri yace to ya
bari, can taji yace "yanzu ita gwaggon ki fa naga ta d'auki zafi da Maganar sosae" damm gaban Fatuu ya
fad'i tunowa da yanayin da ta riski gwaggo tabbas ba k'aramin 6aci ran ta yay ba sai kuma ta ayyana
k'ilan in ta nuna ta amince zata saukko hakan yasa tace mashi kar ya damu zata fad'i mata ta amince
tasan zata saukko, sosae ya shiga yi mata godiya yana saka mata Albarka da harshen fulatanci tana
Amsawa kafin ta tambaye shi yaushe zai zo d'aukan ta d'in yace zai sanar da ita ta fara shiri dae sannan
zai tura na Amadu kud'i in akwae abunda zata siya na amfanin kitchen tunda yaga a birni jere ake mashi
ta amsa mashi da to kafin suka yi sallama, k'ura ma wayar ido tay bayan ta cire ta daga kunnanta sai
lokacin kuma ta fara tunanin anya bata yi gangancin saurin Amincewa ba kuwa, tasan waye za'a aura
mata? tsuru tay tana ta faman zare idanu can kuma ta yanke koma waye zata aureshi ko don ta fitar da
Mahaifinta daga halin da yake ciki don tasan dama can ana bak'in cikin yadda Ardo yafi ji dashi yanzu in
ta k'iya sun samu abun da suke so, shiru tay tana tunanin yadda zata tunkaro gwaggo don wata irin
shakkarta ce ta kamata can ta yanke bari ta bari sai Anjima lokacin tasan ta d'an huce, tana haka aka fara
kiran sallar Azahar ta mik'e don yin salla lokacin data fito suka yi kacibus da gwaggon ta yo Alwala zata
koma d'aki fuskarta sam ba walwala ko kallon Fatun bata yi ba ta wuce d'aki hakan ba k'aramin k'ara ma
jikin Fatuu sanyi Yay ba, bayan ta gama sallar zaune tay a d'aki tana ta sak'e sak'e a ranta gaba d'aya
gidan yayi tsit kai kace sakon Mutuwa aka fad'a masu kowa yana d'aki ko Abinci ba wanda ya nema
kuma tuni gwaggon ta gama don lokacin data gama tana kitchen ne Amadu ya kai mata wayar, mik'ewa
Fatuu tay ta fito ta nufi kicin ta zubo ma Kawu Amadu da shima tunda ya dawo daga Masallaci yana
d'aki, lokacin da ta shiga ya d'an kishingida kan Katifar shi da alama tunani yake jin sallamar Fatun yasa
shi kai idanunshi kopar shigowar, a bakin katifar ta aje plate d'in Abincin da d'an murmushi tace "Kawu
Amadu ga Abincin ka" tashi yay zaune yana mata kallon mamaki ganin ta ba wata damuwa sosae a
tattare da ita don ya d'auka zuwa yanzu tana can tasha uban kuka koma tana cikin yi, ganin kallon da
yake Matan ne yasa tace "Baffa na ya kira ni yayi man bayanin komae kuma nace mashi na amince da
auren" bud'a ido Amadu yay yana kallonta wit surprise written boldly all over his face don bai ta6a
tunanin hakan ba ta cikin sauki surprisingly yace "yanzu kenan kin yadda ayi maki auren kin hak'ura da
karatun?" D'an guntun murmushin takaici tay kafin cikin karewar murya tace "to Kawu Amadu ya zanyi
Baffana na cikin matsala kuma zai k'ara shiga wata in har ban Amince ba don Ard'o yace ya bar mashi
gida in dae bai zo ya d'aukko ni an Mani auren ba kuma wai bai yafe mashi ba...." Sai lokacin tasa kuka
ba k'aramin sanyi jikin Amadu yay ba dama yasan ba yadda za'ai Baffanta ya goyi bayan hakan cikin
sauk'i don kuwa duk Abunda Fatun ke so shima shi yake so, rarrashinta ya shiga yi yace ta daina kukan,
sam bai son Al'amarin don bai dace ayi mata hakan ba ba kamar da Kamalu yayi mashi bayanin wanda
za'a aura Matan d'azun da ya kira shi don jin Karin bayani, sauke nannauyar ajiyar zuciya yay kafin yace
mata Allah ya za6a abunda yafi zama Alkhairi tace Amin, tambayarta yay ita ta ci Abincin tace a'a yace
to suci tare, bayan sun gama yace ta k'aro masu farko tace ta k'oshi yace bai yarda ba dole ta k'aro suka
ci bayan sun gama ta d'auke plate d'in ta maida kitchen har zata shiga d'akinta ta dakata tana kallon
kopar d'akin gwaggo a ranta tana tunanin anya ma gwaggon ta ci Abincin don bata ga alamun ta d'iba ba
can ta juya ta koma kicin d'in ta zubo mata ta nufi d'akinta lokacin data shiga tana zaune kan dardumar
salla da alamu tunda ta gama sallar bata mik'e ba, amsa sallamar da Fatun tay ba tare data kalleta ba ta
nufi gefenta ta duk'a ta aje plate d'in Abincin a sanyaye tace "Gwaggo ga Abinci ki ci" jimm tay kafin ta
juyo ta kalleta har saida gaban Fatun ya d'an fad'i ganin yadda idanunta suka sauya kaman itama kuka
tayi, ganin yadda fatun ke kallonta yasa ta d'an k'ak'alo murmushin yak'e tace mata ta gode Fatun ta
mik'e ta bita da kallo har ta fita wani irin tausayin yarinyar ne ya kamata don duk a tunanninta Fatun
bata san abunda ke faruwa ba, k'ara dawowa tayi ta kawo mata ruwa ganin bata ko ta6a Abincin ba yasa
a marairaice tace "Don Allah gwaggo ki ci" fuskarta a sake ta d'aga mata kai alamar to, har ta juya taji
tana tambayarta ita taci Abincin ne tace mata eh sun ci da Kawu Amadu kai ta k'ara d'aga mata Fatun ta
fita ta koma d'aki ta zauna a bakin gado tana wasi wasin ko in ta gama taje tayi mata Maganar tana ta
sak'e sak'enta ta d'an kwanta har bata san bacci ya kwashe ta ba saida akayi la'asar gwaggo tazo ta tada
ita tace bazata islamiyya bane, ba 6ata lokaci ta shirya ta canja wasu Uniform d'in ta tafi, Bayan sallan
isha lokacin Fatuu ta gama cin Abinci ta maida plate d'in kitchen bayan ta fito tay tsaye bakin kopar
d'akin gwaggo tana sak'e sak'e can dae tay shahada ta shiga da sallama lokacin gwaggon na zaune kan
sallaya hannunta ruk'e da cazbaha ta jingina bayanta da jikin gado tana lazimi, daga can gefe Fatun ta
duk'a idon gwaggo a kanta ita kuma sai sussuna kai take ganin haka yasa gwaggo d'aga hannuwa ta
shafa Addu'a kafin tace mata da wani abu ne, farko Fatun shiru tay ganin yadda gwaggon ta zuba mata
ido yasa cikin rawar murya ta fara Magana "d..dama d'azun Baffana ya kira ni ya sanar dani abunda ke
faruwa wai Ard'o ya bada ni za'a man Aure...." Wani murmushin takaici mai d'an sauti gwaggon tayi kafin
a harzuk'e tace "ki k'yale ni da shi zan nuna masa nima ina da iko dake ba Ard'o ba ko lamid'o ne shi sai
inda k'arfi na ya k'are wllh don ina ji ina gani bazan k'yale a lalata maki rayuwa ba har wani ne d'an
chairman can" ta k'arasa tana huci ba k'aramin tashi hankalin Fatuu yay ba murya na rawa kaman zata sa
kuka tace "A'a gwaggo don Allah ki yi hak'uri ki k'yale shi ni na Amince ayi man Auren....." Bata k'arasa
sakamakon wata gigitacciyar tsawa da gwaggon ta daka mata tace "dum hetsi!!!" ba k'aramin firgita
Fatuu tay ba har saida ta dan goce daga zaune jikinta ya hau kerma tana zare ido, a fusace gwaggon tace
"a wodi hakkilo! tashi ki fita ki ban wuri!!" Fashewa Fatuu tay da matsanancin kuka ta hau bata Hakuri
tana mata magiya akan ta Amince in ba haka ba Baffanta na cikin matsala Ardo tsine mashi zai yi, haka ta
shiga fad'i mata halin da baffanta ya fad'i mata yana ciki gwaggon tay banza da ita kanta a k'asa can ta
d'ago idanunta cike da tsantsar 6acin rai a kausashe tace "iyakata zaki nuna man Fatuu??? Da sauri ta
girgiza mata kai tace "a'a don Allah gwaggo kar kice haka kawae ina son na fitar da Mahaifina daga halin
da yake ciki idan aka hana Ard'o yin yadda yake so zai tsine masa ne kuma yace ya bar masa gida ma don
Allah ki bari ayi man Auren kawae ni na hak'ura da karatun kuma dama kwanaki ba kince in ina cikin
karatun ma na samu miji ba aurar dani zaki na idasa karatun acan gidanshi to ki barni don Allah gwaggo
in da rabo sai in yi acan d'in" duk abun nan idanun gwaggo na akanta ta d'an kya6e baki can tay wani
guntun murmushin takaici irin mai nuni da yaro yaro ne kafin cikin raunatacciyar murya tace "ki je kiyi
duk yadda ranki ke so!" Tana niyyar sake cewa wani abun gwaggon ta mik'e a fusace tayi kanta tana
fad'in "ki fita ki ban wuri shashasha...." Kasa k'arasawa tay sakamakon muryarta da ta karye kawae sai
tasa kuka tana fad'in "ni ai da yake bani na haife ki ba shiyasa baki damu da damuwata ba" da gudu
Fatuu ta nufi d'akinta ta fad'a kan gado tana wani irin kuka mai cin rae to itama dae gwaggo kukan tasa
tay zaune a gefen gado ana cikin haka Amadu ya shigo gidan yana jiyo kukan Fatuu ya nufi d'akinta ko
sallama bai yi ba ya kutsa kai jin yadda take kuka hankali a tashe ya shiga tambayarta abunda ke faruwa
amman abu d'aya take fad'i shine "Gwaggo ce...." Cikin rashin fahimta yake tambayarta mi gwaggon tayi
mata ganin bata da niyyar bashi amsa yasa shi fita ya nufi d'akin gwaggon sai dae ba shiri yay turus
bayan ya shiga d'akin ganinta zaune tana ta matsar k'walla jiki a mace ya k'arasa gabanta ya duk'a bisa
gwiwowinshi idanunshi har sun kawo kwalla, dafa knees d'inta yay cikin rawar murya yace "gwaggota
Mike faruwa kike kuka" shiru bata bashi amsa ba bata kuma kalleshi ba, hawayen idonshi ne suka fara
sauka ya fara mata magiyar ta fad'i mashi abunda ke damunta can ta kalleshi cikin muryar kuka tace "ni
Fatuu zata watsa ma k'asa a ido ina k'ok'arin kwatar mata yancinta amman ta nuna man iyakata duk irin
kokarin da nike akanta amman ta kasa bani goyon baya Saboda ni bata damu da farin ciki na ba..." Sosae
tasa mashi kuka ya mik'e da sauri ya janyota jikinshi ya shiga lallashinta yana bata baki had'i da yi mata
Nasiha da k'yar ya samu ta d'an saukko tace "Shikenan taje Allah ya taimaka na cire hannuna daga kan ta
tayi duk Abunda yafi mata" da sauri Amadu ya girgiza kai yace "a'a Don Allah gwaggo kar kice hakan..."
Katse shi tay da fad'in "To mi kake so in ce, zan ci gaba da damuwa da ita ne bacin ta nuna man iyakata,
ko da yake dama nima ce da katsaladan da nike kokarin shiga tsakanin uba da yar sa"

"Gwaggo kema ai kaman matsayin uwa kike a wurinta iya Abunda Mahaifiya zata ma d'iyarta kike
mata" girgiza mashi kai tay cike da 6acin rai tace "a'a Amadu ni ba matsayin uwa nike ba a wurinta tunda
gashi ta nuna" duk Maganganun da suke Fatun na la6e tana sauraran su ta rufe bakinta da tafin
hannunta jin Maganar Gwaggon ta k'arshe yasa ta watsa da gudu d'aki tana cigaba da rizgar kuka, sosae
Amadu ya shiga kwatanta ma gwaggo dalilin Fatun na amincewa da Auren yana rok'on ta akan tayi
hak'uri kar tai fushi da ita in sha Allahu komae zai daidaita, to a Daren ranar dai tsakanin gwaggo da
Fatuu ba wanda ya runtsa shi kan shi Amadun baccin shi Sama sama ne ya ma rasa tunanin da zai yi don
samun mafita shin zai ce ma Fatuu kar ta yi ma Mahaifinta biyayya tayi ma Mahaifiyarshi ko ya ya? Itama
Fatun sak'e sak'e kawae take in wata zuciyar ta nuna ta yi ma gwaggo biyayya sai wata zuciyar kuma ta
ce kenan ta Amince mahaifinta ya shiga mawuyacin hali akanta duk da zata iya taimaka mashi???

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._

*ASM Bk2024*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


............A kan kunnanta aka fara kiran farko na sallar Asuba ta yunk'ura ta saukko idanunta sun yi luhu
luhu ta fita, Alwala ta d'auro tazo ta kabbara Nafila bayan ta gama tana kuka tana Addu'oi, lokacin da
gari ya waye sosae ta fito don ta share gidan tayi wanke wanke kafin ta wuce islamiyya duk jinta take
wani iri kaman wadda ta tashi daga ciwo jikinta sam ba k'arfi, d'akin gwaggo ta fara zuwa ta gaisheta
amman ko kallon Arzik'i bata samu ba haka ta fito tana goge kwalla da gefen hannunta, tsintsiya ta
d'aukko tana fara sharar gwaggon ta fito daga d'akinta fuskar ta a daure tamau da hannu tay mata alama
ta aje tsintsiyar cikin muryar kuka tace "don Allah gwaggo ki yi hakuri ki bari in share" a fusace tace "to
ban so ko gidanki ne, kuma daga yau ban amince ki k'ara ta6a komae da sunan aiki ba ki bar man kayana
zan yi na riga na yaye ki wanda kikai kuma nagode" daga haka ta juya ta koma d'aki, kallon Amadu dake
tsaye bakin kopar d'aki Fatun tay da fuskar kuka ya d'an girgiza mata kai alamar ta barin da sauri ta aje
tsintsiyar ta shige d'aki sai gashi ya biyo ta ya zauna a gefen gado ya fara rarrashinta cikin kuka tace
"Kawu Amadu ya zanyi gwaggo ta kasa fahimta ta ni wllh ba wai ban damu da damuwarta bane ko ban
son abunda take so, nasan Saboda in yi karatu ne yasa bata son ayi man Auren to amman Baffana na
cikin matsala in ban taimaka mashi ba kana iya ganin Allah ya ki bani sa'a ma a karatun amman inna
taimaka mashi in da rabo sai kaga Allah nima ya taimaka man ya cika man buri na" ajiyar zuciya ya sauke
kafin yace "na fahimce ki sosae ki yi hak'uri Kinji ki bi komae a hankali dole dama zata shiga damuwa
kuma ranta ne ya 6aci sosae shiyasa take ta maganganu kar ki damu ki daina yawan kuka kar wani ciwon
kuma ya kama ki" kai ta d'aga mashi alamar to yace taje ta de6o breakfast ta ci ta tafi islamiyyar cikin
karyayyar murya tace "amman tace fa kar in k'ara ta6a mata komae" d'an murmushi yay yace "kar ki
damu da hakan kije ki de6o bazata hana ki ba kuma aikin ma in bata nan sai ki yi in kuma ta nuna maki
bata son abu a yanzu ki daina jayayya da ita tunda ranta a 6ace yake" tare suka fito ya tsaya a bakin
kitchen d'in har ta zubo ta koma d'aki sannan shima ya nufi d'akinshi, sam tama kasa cin wani na kirki
karshe d'auka tay ta mayar kicin d'in ta dawo ta shirya, koda ta fito saida taje bakin kopar d'akin
gwaggon tace mata ta tafi islamiyya sanin ba amsa mata zatai ba ya sa ta tafi, lokacin da ta fito Kawu
Amadu ya bud'e shago saida ya k'ara mata magana kan ta daina damuwa tace to kafin ta wuce, Koda
taje islamiyyar duk takurewa tay wuri guda da ka kalleta zaka fahimci tana cikin damuwa har wasu na
tambayarta sai dae tace ba komae sam hankalinta bai kan abunda ake koyawa a haka har Malaminsu na
hadda ya shigo wato discipline d'in su Malam Nazifi, d'aya bayan d'aya ya rink'a bi yana amsar hadda da
ya basu har aka zo kan Fatuu ya kira sunanta saidae kwata kwata bata ji shi ba har saida wata ta kusa da
ita tay tapping nata sannan ta dawo cikin hankalinta k'awar ta nuna mata saitin Malam tace yana
magana da sauri ta kai idonta kan shi ganin kallon da yake mata yasa tasha jinin jikinta ta kusa da itan
tace mata haddar ki zaki bada, shiru tay sai zare ido take to inama ta ga kwanciyar hankali jiya da har
zata yi hadda, ce mata Malam Nazifin yay ta mik'e tsaye bayan ta mik'e yace ta bashi haddar tay wuri
wuri da ido sai faman mommotsa baki take ta rasa yadda zata yi kawae sai tasa mashi kuka dama so
yake yay Nazarinta sosae shiyasa yay mata hakan alamu yay mata na ta zauna ta koma da sauri ta zauna
duk jikin sauran daliban yay sanyi, cigaba da amsar haddar yayi har aka kammala ya basu wata bayan ya
gama ya mik'e zai fita lokacin Fatuu ta d'ukar da kanta ya kira sunanta ta d'ago da jajayen idanu yace ta
biyo shi daga haka ya fita ta mik'e ta bi bayan na shi tana fita yan ajin suka fara chapter kan ta.

Can k'ark'ashin wata k'atuwar bishiyar dalbejiya dake a cikin Makarantar ya nuna mata yace ta jira shi ya
nufi Staffroom bada jimawa ba ya fito ruke da plastic chairs ya nufeta bayan ya aje su ya nuna mata
d'aya yace ta zauna shima ya zauna kan d'aya ya zuba mata ido hakan yasa ta sunnar da kan ta can ya
kira sunanta ta amsa ba tare da ta kalleshi ba yaci gaba "Fateema Muhammad Ardo na fahimci kina cikin
damuwa ba tun yanzu ba tun wasu watanni can baya kin canja sosae akan yadda na san ki in ba damuwa
ina son jin miye damuwarki ko da taimakon da zan iya yi maki kan hakan" Shiru tay tana sheshsheka har
saida ya k'ara tambayarta sannan ta d'ago fuskarta duk hawaye ta fara Magana "Malam ba komae, ba
abunda ke damuna" d'an murmushi yay kafin yace "sai dae in baki son in sani ne amman ai duk wanda
ya sanki yasan kin canja Fateema yaushe rabon da ki yi laifin da na d'aga bulala na bugeki wanda inda da
ne ba yadda za'ai a kwana biyu baki laifin da ban buge kin ba" shiru tay tana ta matse ido ya nisa yace "
in baki son in sani ne bazan takura maki ba zaki iya tafiya dama ina tunanin ko da shawara haka in kina
buk'ata sai in baki watak'il ta taimaka maki", shiru tayi can ta d'ago cikin muryar kuka tace "Malam
abubuwa ne duk basu man daidai farko na rasa wani abu da nike tunanin nawa ne yanzu kuma wata
matsala ce a gida na rasa yadda zan yi" sosae take kuka tana goge fuskarta da gefen hijab d'in ta, hanky
ya fiddo daga cikin Aljihun shi ya mik'a mata yace ta goge kuma ta daina kukan zasu yi magana tace to,
saida ya ga ta natsu sannan yay gyaran murya ya fara Magana,

"Wato Fateema ita rayuwa da kike gani dama cike take da k'alubale kala kala, dole kana musulmi mai
cikakken imani ka rink'a fuskarta jarabawa kala kala ba kuma don Allah bai son bawan sa bane yake
jarabashi sai don ya gwada imanin bawa ya ga zai yi hakuri ya cinye jarabawa ko kuwa zai butulce,
wanda in bawa yay hakuri silar hakan Allah ubangiji zai daukaka shi, hakan na nufin duk abubuwan da
suke faruwa da bawa marasa dad'i Alkhairi ne atare da shi matuk'ar yay hakuri, akwae ayoyi a cikin
surorin Al'qur'ani da yawa da sukae Magana kan hakuri misali:

Suratul Ali Imran Aya ta 200 fad'inshi Allah SWT, Bismillahir Rahmanir Rahim "ya ku wad'anda suka yi
imani ku yi hakuri,kuma ku jure kuma ku zama acikin shiri, kuma kuji tsoron Allah zaku rabauta".
Suratul zumar Aya ta 10 fad'in SWT "hak'ika masu hak'uri ne kawae ake cikawa ladansu ba da lissafi ba".
Haka suratul Anfal Aya ta 46 fadinshi SWT "kuyi hakuri hak'ika Allah yana tare da masu hak'uri".

Suratul Ali Imran karshen Aya ta 146 ".....Allah yana son masu hak'uri".

Sannan akwae jerin ayoyi a Cikin Suratul baqara daga k'arshen Aya ta 155 zuwa Aya ta 157, fad'in shi
SWT ".....kuma kuyi Albashir ga masu hak'uri(155) "sune wadanda idan wata musiba ta same su sai su ce,
mu na Allah ne kuma mu wurinsa zamu koma" (156) "wad'ancan gafarar Allah ta tabbata a gare su da
rahamarsa, kuma wadancan su ne shiryayyu". Haka a cikin Suratul Ma'arij Aya ta 5 fad'inshi Allah SWT
"ku yi hakuri, hakuri mai yawa", da sauran dai Ayoyi da sukae Magana kan hakan,

"Sannan Magana ta farko da kika yi ta kin rasa wani abu akwae Aya ta 216 a cikin Suratul baqara da Allah
SWT yay Magana akan hakan, "An wajabta maku yak'i a kan ku alhali kuwa shi abin k'i ne a gare ku,
akwae fatar cewa ku k'i wani abu alhali shi ne mafi Alkhairi a gare ku, kuma akwae fatar cewa kuna son
wani abu alhali kuwa shi ne mafi sharri a gare ku, kuma Allah ne yake sani kuma ku ba ku sani ba"

"Anan Fateema ina mai baki shawarar ki yi hakuri akan duk wani abu dake damunki ki fawwala ma Allah
ki kuma d'age da yin Addu'a dare da rana in sha Allah zai yaye maki dukkan damuwar ki, sannan Jinkirin
samun biyan buk'atar ki tare da naciyarki wajan Addu'a kada ya zama sanadiyyar debe kaunar ki. Allah
ya laminta ne zai amsa Addu'ar bawa akan abun da ya za6a mashi ba akan abun da shi ya za6awa kan shi
ba, a lokacin dashi ya ga dama ba a lokacin da kai ka ke so ba, jinkirin samun biyan bukata kan abunda
mutum ke tsananin buri da fatan mallaka na daga jarabawa amman idan akayi hakuri sai Allah ya ba
mutum wannan abun ko ma wanda ya fi shi " Sosae Malam Nazifi yay mata Nasiha kuma ta ji sanyi a
ranta harda Nafilolin da zata rink'a yi ya rubuta mata tay mashi godiya sosae.

(Abunda na fad'a daidai Allah ya bamu Ladan in da nayi kuskure Allah ka yafe man).

Tafe take bayan an tashi tana ta juya Maganganun Malam Nazifi tana fatan Allah ubangiji ya kawo mata
k'arshen matsalolinta, tana gab da isa bakin lungun da zata bi wata budurwa da zata yi sa'an Fatun ko
kuma ta d'an girme mata kad'an don ta fi Fatun tsawo ta 6ullo ta mik'o hanya tana sanye da pink Hijab
Fatuu na ganin ta ta ayyana wani abu a ranta da sauri ta k'wala mata kira tace "Jamila" juyowa budurwar
tayi sai lokacin ma ta lura da Fatun ta nufo ta tana mata murmushi a gabanta ta tsaya tace "Fatuu wllh
bamma lura dake ba daga islamiyya kike" kai Fatun ta d'aga mata alamar eh ita kuma ta gyad'a kai har
zata juya Fatun tace "Jamila don Allah ina son rok'on ki wani abu" tsayawa tayi da alamun mamaki kan
fuskarta tace to, Fatuu taci gaba "dama so nike in rok'e ki abubuwan da nayi maki a can baya ki yafe man
lokacin harda yarinta" dariya Jamila tayi tace "kai Fatuu abunda ya wuce ai ba wani abu kuma ma ni ai
rigima dake Alkhairi ta zamar man wllh, zaki iya tuna wani lokaci can da kika 6arar man da awara har
kafin ki zubar wani mutum ya raba mu?" Da sauri Fatuu ta jinjina mata kai, taci gaba "to ai d'an gidan
Hajiyar Sanata ne nasan k'ilan baki rasa sanin shi to ta silar hakan wata rana ya ganni ina tallan k'osai da
safe da yake ranar da kika zubar man da awaran shi ya bani kud'i anan na fara sanin shi to shine ya
tambayeni miyasa bana zuwa makaranta na fad'i mashi baban mu ne bai lpy...." Nan ta kwashe komae
da Haisam yayi masu ta fad'i mata tace "kinga yanzu bamu da matsalan komae na bar tallan Saboda shi
innata ke yin sana'ar a cikin gida babana kuma ya samu lafiya sosae Shima Yana yin sana'ar su hatsi da
cefane anan k'opar gida kuma har yanzu suna gaisawa da babanmu da zai yi aure ma babanmu yaso
zuwa shi yace ya barshi" Fatuu dake ta bin ta da idanu jin tayi shiru yasa ta gyad'a mata kai kawae Jamila
tace "ko baki lpy ne na gan ki sukuku" a sanyaye tace "kai na ne ke ciwo" tayi mata Allah ya sawak'e daga
haka tace bari ta wuce dama innarsu ce ta aikota cikin unguwa, ba k'aramin sanyi jikin Fatun yay ba jin
abunda Haisam yayi ma su Jamilar a ranta ta rink'a ayyana "dama haka halin shi yake mu kuma Mu kai
tunanin so na yake" wani irin k'una zuciyarta ta fara mata a fili ta ke fad'in "ina son ka Ya Haisam duk da
nasan na rasa ka har Abada" cigaba da tafiya tay sukuku da ita abubuwa sun mata yawa gashi ba Haulat
balle ta tausheta ko ta waya wuyar samu take mata don k'aramar waya ce a hannunta tun kafin ta tafi
tata ta lalace aka ce bazata gyaru ba sai ta sayar ta amshi k'arama, farko da suka je Nijar da wayar
Yayanta Usman suke chat yanzu kuma shi ya dawo dama rakata yay d'an sauk'inta shine Kawu Amadu
sosae ya damu da halin da take ciki yake yawan bata baki gwaggo kuwa abun ba'a Magana, Washe gari
da safe wurin karfe 11 na safe lokacin gwaggo ta tafi aiki Amadu ya isketa a d'aki ya bata kud'i Naira
dubu d'ari yace Baffanta ne ya turo yace a bata daga haka ya fita, bin kud'in da Kallo Fatuu tay ganin
abun take kamar almara wai kud'in da zata Siya kayan kicin d'in gidan auren ta ne ta rasa tunanin da zata
yi kan kud'in ta san ko ta kai ma gwaggo ma ba amsa zata yi ba ita gashi ba iya zuwa kasuwa zatayi ba da
sunan siyo wani abu kawae sai ta mik'e taje ta saka su cikin wardrobe, haka suka ci gaba da yin zaman
doya da manja ita da gwaggo sam in tana ma gidan Fatun k'umshe wa take a d'aki bata samun sukuni sai
in ta tafi aiki gashi ta kasa bin yadda gwaggon ke so na bijirewa Maganar auren Don har Baffanta ya
sanar da ita sati mai zuwa zai zo ya d'auketa har tayi rama Saboda damuwa amman duk da hakan bata
wasa da yin Addu'a,

Ranar Laraba tana fitowa don tafiya islamiyya sai ga Tk ya taho kan mashin d'in shi zai nufi gida yana
ganinta ya tsaya yana murmushi itama d'an Murmushin ta ke mashi yace "Manyan gari kwana biyu ina
kika 6oye?" itama tambayarshi tay a sanyaye tace "Tk ashe ka dawo?" Yace "eh tunda uwar d'akina ta
dawo ai kinga dole in dawo" d'an bud'a ido tay tace "Hajiya ta dawo ne?" Yace "eh tun ranar Monday ma
ashe baki sani ba" girgiza kai tay tace bata sani ba yace to ta dawo, har zai ja mashin d'in sai kuma ya
dakata yace "Amman dae baki lpy ko" d'an cije lip d'inta na k'asa tay kafin ta d'aga mashi kai alamar eh
yace ai ga alama nan Allah ya sawak'e daga haka ya ja ya tafi, tsaye tayi tana tunanin zuwa gun Hajiyar
yanzu ko sai ta dawo can ta yanke bari ta koma gida ta aje jakar ta canja kaya sai ta je kawae, doguwar
rigar material da mayafinta ta sa bayan ta koma gidan ta fito ta nufi gidan Hajiya, lokacin da ta shige gate
bin part d'in Haisam da kallo tay rabon da ta shigo gidan tun kafin yay aure d'an girgiza kai kawae tay ta
wuce, Hajiya na zaune a Falo idanunta sanye da glasses tana kallon tv Fatun tay sallama ta shiga har
saida gabanta ya fad'i don tana shiga tay arba da wasu manyan hotuna wanda a da babu su, d'aya
Haisam ne da Fanan da ganin yanayin shigar da suka yi da bikin su ne sunyi matuk'ar kyau shine a tsakiya
sai gefe d'aya kuma Hajiya da su ne sun sakata a tsakiya duk sunyi dariya sai d'ayan gefen kuma hoton
Fatun ne ita da Haisam wanda aka yi masu da kayan Fulani a cikin falon Hajiyan yayi kyau sosae, juyowa
Hajiya tayi tana kallonta ta cikin gilashin har ta k'arasa ciki ta zauna kujerar kusa da ita da d'an murmushi
tace "Hajiya ina wuni an dawo lpy" d'an kya6e baki Hajiyar tay kafin tace "idon ki kenan Fateema, ai nayi
zaton sai na nemo ki da kaina ace kwana biyu na dawo amman baki zo kikai man sannu da zuwa ba har
Dije dae ta shigo, ko don yayan ki ya bar gidan shiyasa za'ai man tawaye ko da yake tun ma kafin ya tafi
ai kika d'auke man k'afa" ita dae d'an murmushi kawae tayi Hajiyan tayi mata murnar gama Makaranta
da fatan sa'a a hankali ta amsa mata, shiru ya biyo baya can taji Hajiyar tace "Wai Fateema ko dae har
yanzu ba ki jin dad'i ne naga duk kin yi wani iri gashi har rama ma naga kin yi sosae" sadda kanta tay ba
tare da tace mata komae ba hakan yasa Hajiya k'ara tambayar tata aikuwa kawae sai tasa mata kuka, bin
ta da ido hajiyar kawae tayi with mouth agape ganin bata da niyyar dainawa yasa ta kai hannu kan
shoulder d'inta tace "shikenan ya isa hakanan kuka ai bai magani in baki lafiyan ne ko wani abu na
damun ki ai sai ki fad'a man ba kita kuka ba, fad'a man miye?" Shanye kukan tay ta d'ago fuskarta duk
hawaye cikin shaky voice tace "Gwaggo ce...." Sai kuma tayi shiru tana motsa baki Hajiyar tace tana
saurarenta mi dijen tayi mata Fatun taci gaba "f...fushi take da ni, bata man magana, bata kula ni ta hana
ko aikin gida in rink'a yi...." Cigaba da kukan tayi da tsananin mamaki Hajiya tace "Dijen ce ke maki haka
harda gaba da girmanta to mi ki kai mata Fateema da har yay zafi haka?" Cikin muryar kuka Fatun ta
bata labarin duk abun da ke faruwa, jinjina kai Hajiya ta shiga yi ita kanta ta girgiza da jin batun auren
har ta kasa magana Fatuu nata sheshsheka can tace mata ya isa haka tayi shiru kafin tace "Amman Dije
bata kyauta ba gaskiya to da mi zaki ji ne, ni Sam koda ta shigo bata man Maganar ba kuma komae ai a
hankali ake bin shi ko ba ta dau zafi haka ba hakan zai samar da mafita ne, ki k'yale ni da ita" ta k'arasa
ta sigar lallashi kai kawae Fatun ta d'aga mata tace ta daina kukan ta share hawayenta, bayan ta goge
Hajiyar tace bari a zuba mata Abinci ta ci farko cewa tay ta k'oshi amman hajiyar tace a'a sai ta ci, bayan
ta k'wala ma Saude kira ta bata umarnin ta kawo ma Fatun Abinci a nan cikin Falon bayan ta kawo mata
har saida Saude ta tambayi Fatun bata lpy ne lokacin da ta gaisheta tay shiru sai Hajiya ce cikin 6acin rai
tace mata ita da Dije ne, sai da Hajiya tasa ta taci sosae bayan ta gama tace taje d'akinta ta watsa ruwa
ta kwanta tace to ta mik'e ta d'auki plate d'in Abincin walking slowly ta kai Kitchen kafin ta wuce d'akin
Hajiya, bayan tayo wankan ta kwanta a k'asa kan carpet tana ta tunani bada jimawa ba bacci ya kwashe
ta, sosae Fatuu tasha bacci don har Hajiya ta shigo don yin sallar Magrib da ake kira bacci take ta yi saida
ta tasheta kafin ta tashi tayi salla bayan ta idar saida ta jira Hajiya ta gama don tana dad'ewa in tana yin
salla sannan tace mata zata tafi amman Hajiyar tace tay zamanta a nan bayan sallar Isha zata je ta samu
Dijen a hankali Fatun tace to, ganin kaman ta k'i sakin jiki yasa Hajiya ce mata taje d'akin Saude tace to ta
mik'e ta nufi hanyar fita idon hajiya a kanta tana kallonta cike da tausayi yarinyar da koda yaushe take
cikin nishad'i ce ta koma sukuku da ita, bayan sallar Isha hajiya ko cire hijab bata yi ba ta nufi gidansu
Fatun baiwar Allah bata ma jin dad'in k'afafunta ciwo suke mata dama tana da ciwon shiyasa ma Senator
ya hana ta dawo don sai da suka je US checkup daga can suka biya gurin su Haisam tare da Mahaifiyarshi
harda Aunty da Hajiya maryam da mahaifin Fanan d'in duk aka je ganin d'aki, lokacin data isa da sallama
ta shiga gwaggo ta fito daga d'akinta tana ganin hajiyar ta fara mata fara'a ta nufo ta tana yi mata sannu
da zuwa.......
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._

*ASM Bk2025*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.......Parlor Gwaggo tace su shiga, a saman 2 seater Hajiya ta zauna gwaggo ta zauna kan one seater tana
fuskantar ta ta shiga gaida ta rai a 6ace Hajiya tace "bazan amsa gaisawar ki ba Dije don kin ban mamaki
wllh" waro ido gwaggon tayi a d'an rude tace "Hajiya mi kuma ya faru?" a d'an harzuk'e tace "haba Dije
ace da girman ki ki tasa yarinya gaba kina gaba da ita sai kace wata kishiyarki to da me kike so ta ji ne?
Baki tunanin hakan na iya jefata cikin wata matsalar kuma sakamakon damuwa da tayi mata yawa! Haba
Dije in ran ki ya 6aci ai ba Kya bari hankalin ki ya gushe ba komae a hankali ya kamata a bi shi, nasani
abun Sam ba dad'i to amman wannan abun da kike ba shine zai samar da mafita ba sai ma ya jaza wata
matsalar" tana yin shiru cikin karewar murya gwaggo tace "amman hajiya mafitar nike son samo wa
amman Fatuu ta watsa man k'asa a ido ta nuna man iyakata ta goyi bayan Mahaifinta...." Katseta Hajiya
tayi a fad'ace tace "ta k'i bin bayan mahaifinta Dije duk D'iya ta gari kina tunanin zata ga mahaifinta a
cikin matsala ne alhali tana da hanyar da zata taimaka mashi kuma ta k'i, ko kece Fateema na tabbatar
hakan za ki yi kada ki zama mai son kan ki mana, sannan Maganar nuna iyaka ba wata iyaka da Fateema
ta nuna maki kema kina da naki muhimmancin kamar yadda mahaifinta keda nashi" dakatawa tay tana
maida numfashi yayin da gwaggo ta sadda kanta tana matsar k'walla Hajiya ta koma lallashinta tana bata
baki akan a bi komae a hankali itama Fateemar ta san ba son Al'amarin take ba kawae bata da yadda
zatayi ne don haka sai ayi Addu'a Allah ya za6a abunda yafi zama Alkhairi kawae amman ta daina abunda
take Matan don zai iya jawo wata matsalar, sosae ta lallasheta har saida ta ga gwaggon ta saukko sosae
sannan ta mik'e don tafiya bayan sun fito tsakar gida tace ma gwaggo taje ta d'aukko mata kayan baccin
Fateema bama zata dawo gidan ba tunda dama kora da hali ake mata, d'an guntun murmushin yak'e
gwaggon tayi kafin taje ta d'aukko mata saida ta sawo hijab ta rakata har wurin gidanta tana ta ta koma
kafin suka yi sallama hajiyar na jaddada mata kan aci gaba da Addu'ar Allah ya za6a abunda yafi zama
Alkhairi, lokacin da ta koma gidan a d'akin Saude ta iske Fatun kwance ta bata kayan baccin tace mata ta
sa tay kwanciyarta har zata fita kuma sai ta dakata ta tambayi Saude Fatun ta ci Abinci tace mata a'a wai
ta k'oshi hajiyar tace ta tashi taci ba yadda ta iya dole ta tashi Saude taje ta zubo mata Abincin, bayan ta
gama komae tasa kayan baccin ta kwanta tunanin yadda Hajiya tayi da gwaggo ta shiga yi, Hajiya na
komawa bedroom d'in ta toilet ta shiga tayo wanka bayan ta fito tayi shirin kwanciya ta kwanta, tunanin
Maganar auren Fatun ta shiga yi ita kanta bata farinciki da Al'amarin sai dae tana fatan Allah ya za6a
mata abunda yafi zama Alkhairi. Washe gari bayan sun yi breakfast Fatuu na zaune a d'akin Saude
tunanin gwaggo ya dameta hakanan take jin son ganinta lokacin Hajiya ta koma bacci Saude ta shigo
bayan ta gama gyara gidan da murmushi ganin Fatun ba bacci take ba tace mata ko ta tashi tay wanka
tafi jin dad'in jikinta tace to, bayan ta fito ne ta maida kayan jiya data zo da su gidan tace ma Saude zata
je gida ta canza kaya tace to, lokacin da ta isa a zaure ta tsaya tana ta wasi wasi can dae ta shiga ciki ba
kowa a tsakar gidan hakan yasa bata yi sallama ba daga yanayin kopar d'akin gwaggon ta gane tana nan
a ciki d'an jimm tayi kafin tay shahada cike da fargaba tay yar sallama ba tare da ta shiga ba shiru ba'a
amsa mata ba hakan yasa ta k'ara yi sai lokacin ta jiyo muryar gwaggon ciki ciki ta amsa mata a hankali ta
d'aga labulan ta shiga gwaggon na kwance saman gado tana huta gajiyar aiki da ta gama, ta ji shigowarta
saidae bata bud'e idanunta dake a rufe ba balle ta kalleta, saman kujera ta kai ta zauna a d'arare idonta
akan gwaggon, har bayan wani lokaci bata kalleta ba hakan yasa Fatuu shan jinin jikinta ta ji kamar ta
tashi ta fita don ta lura kaman gwaggo bata huce ba can dae tayi k'arfin halin kiran sunan gwaggon
murya na rawa shiru bata amsa ba bata kuma bud'e ido ta kalletan ba don sama fuskarta ke facing ta
tada kai da Pillow, murya na rawa Fatuu ta ci gaba da cewa "Gwaggo don Allah ki yi hakuri ki yafe man ki
daina fushi da ni wllh ban jin dad'i don ke matsayin Mahaifiya ta ce bazan so in ga kina fushi da ni ba,
kuma ba iyakar ki nike son nuna maki ba kawae ina tausayin Baffa na ne don ban son Ard'o ya tsine
mashi hakan matsala ne a gareshi kuma kinsan Ard'on zai iya kema nasan bazaki so hakan ta faru ba" ta
k'arasa cikin karewar murya tana share hawayenta duk Maganganun da take gwaggon na jinta har can
k'asan ranta wani iri take ji, mik'ewa Fatuu tay ta nufi gaban gadon ta duk'a akan gwuiwowinta ta dafa
bakin gadon da hannu cikin muryar kuka tace "gwaggo don girman Allah ki yi hakuri ban son ganin ki a
cikin damuwa..." sai lokacin ta bud'e idanun jin Maganar a kusa a hankali ta sauke su kan fuskar Fatun
dake share share da hawaye sai kuma ta yunk'ura ta tashi zaune ta jingina bayanta da kan gadon shiru
kaman bazata yi magana ba fatuu nata kallonta can ta sauke ajiyar zuciya murya ciki tace "Shikenan
Allah ya za6a abunda yafi zama Alkhairi" a hankali Fatuu ta amsa da Amin kafin ta sadda kai tana kallon
saman gadon can taji gwaggon tace ta tashi taje tay abunda zatayi ta d'ago suka had'a ido tana son ta
k'ara bata Hak'uri amman ta kasa ganin yanayin fuskar tata, mik'ewa tay jiki a mace ta nufi hanyar fita
gwaggon ta bita da ido har ta fice, d'akinta ta nufa tana shiga ta zauna a gefen gado tay zugudum
hakanan hankalinta ya k'i kwanciya da yanayin gwaggon tana ta zaune can ta mik'e ta nufi wardrobe don
ta canja kaya tana k'ok'arin fiddo kayan kud'in da baffanta ya aiko mata suka fad'o k'asa d'aukko su tay
har zata maida su ciki sai kuma tay wani d'an tunani ta fasa maidawar ta aje su a gefen gado, bayan ta
gama shiryawa d'aukar kud'in tayi ta fita ta sake komawa d'akin gwaggon k'irjinta na bugawa, lokacin da
ta shiga har sannan gwaggon na zaune yadda ta barta, a bakin gadon ta tsaya da kermar murya tace
"gwaggo gashi" kallon kud'in da take mik'a Matan tay kafin ta d'aga ido ta kalleta without saying
anything ganin haka yasa Fatun cewa "d..da...dama Baffa ne ya turo ma Kawu Amadu wai ya bani in Siya
k... kayan kitchen" da k'yar ta kai Maganar gwaggo na jin hakan nan da nan yanayinta ya canza sosae ta
juyar da fuskarta gefe kaman bazata ce komae ba ita kanta Fatuu k'irjinta bugawa yake sosae bayan d'an
wani lokaci ta ji gwaggon tace "sai ki je ki siyan ko" da sauri tace "ai ni bansan ma ina ake saida su ba
kuma bansan mi zan siya ba" nan ma shiru gwaggo tay sai daga baya tace "sai kije in Saude bata komae
ta raka ki tunda ita tasan inda ake saidawar zata taimaka maki da abunda ya dace" shiru Fatun tay ganin
tak'i tafiya yasa gwaggon juyowa ta kalleta sai lokacin ta juya jikinta sukuku ta nufi hanyar fita gwaggon
na bin ta da kallon takaici, d'akinta ta koma ta zauna a gefen gado tana tunanin ko ta kai ma Saude ko
kuwa kar ta kai can ta mik'e ta yafa gyalen ta ta fita saida ta tsaya bakin kopar d'akin gwaggo tace mata
ta tafi gidan Hajiyar shiru tay mata da farko saida ta k'ara maimaitawa sannan ta jiyo muryar ta ba yabo
ba fallasa tana fad'in a dawo lafiya, Lokacin da ta isa Hajiya na zaune a parlon saman 2 seater tayi wanka
ta shirya tana kallo bayan tayi sallama hajiyar ta amsa mata da d'an murmushi ta nufeta, gefenta ta nuna
mata taje ta zauna tun kafin tayi Magana Hajiyar tace "ai d'azun nike tambayar Saude ke tace man kin je
canza kaya nace ko dae kin kasa jurewa kinje ganin masoyiyar taki" ta k'arasa tana yar dariya itama
Fatun murmushi take yi Hajiya tace "in ce dae ta sake maki yanzu?" Kai Fatuu ta d'aga kafin tace "eh"
jinjina kai Hajiyar tayi tace "komae d'an hakuri ne kuma duk abunda Allah ya kaddara sai ya faru to kuwa
ba makawa sai ya farun shiyasa ake son komae a rink'a bin shi a hankali ba a dau zafi ba" shiru Fatun tay
kan ta a k'asa can Hajiyar tace mata ko taje d'akin Saude ta k'ara hutawa sai lokacin ta d'ago ta kalleta a

hankali ta mik'a mata kud'in hannunta hajiyar ta kalli kud'in kafin ta kalleta kafin tayi Magana Fatun tace
"dama Baffana ne ya turo man su wai in sayi kayan kitchen to lokacin gwaggo tana fushi ban bata ba sai
yanzu shine tace in je in sayi kayan nace mata ban san inda ake saidawar ba sai tace in zo in Aunty Saude
bata komae ta raka ni" ta kai Maganar kamar zata sa kuka, yar ajiyar zuciya hajiyar ta sauke kafin ta
amshi kud'in tace taje d'akin Sauden ta amsa da to ta mik'e jiki a sa6ule ta wuce, shiru Hajiya tay tana
bin kud'in da kallo cikin ran ta tana ayyana da gaske dae Auren zasu yi mata Sam itama bata son hakan
saidae ta san in Allah ya kaddaro hakan to fa ba makawa sai ya faru, ajiye kud'in tay a saman hannun
sofa taci gaba da kallon can kuma Haisam ya fad'o mata a rai ta san ba lalle in yasan da Maganar ba
hakan yasa ta kai hannu gefenta ta d'auki wayarta ta fara kokarin kiran shi, Lokacin da kiran ya shiga
Haisam d'in na zaune kan kujera 3 seater a Parlor yana operating laptop dake ajiye a saman table d'in
gaban shi Fanan kuma na kwance kan ta na a saman cinyoyin shi tana bacci daga ita sai wasu matsiyatan
lingerie da suka bayyana kaf surar ta sunan dae tasa ne kawae, hannu ya kai ya d'auko wayar da ke ajiye
a gefen laptop d'in yana ganin sunan da yay appearing saman screen d'in yay d'an guntun murmushi
had'i da maida bayanshi jikin kujera ya jingina sosae kafin yay picking tun kafin tay magana cikin cool
voice d'inshi yace "Sweetheart how a'r u" daga can d'ayan bangaren ta amsa mashi da tana lafiya kafin
ta tambayi ya suke yace mata lpy,

"Ina rigimammar matarka?" Ta tambaya da yar dariya still da murmushi akan fuskarshi ya d'an kai idon
shi ya kalli Fanan d'in, kamar kuwa tasan rigimar ta gama yi mashi kafin tay bacci ita ala dole suje a duba
lafiyar su ganin har yanzu bata samu juna biyu ba dama tun suna wata guda da auren take Maganar
samun cikin shi kuma yace is too early a fara wannan kuma yasan lafiyar su lau kawae time ne bai yi ba,
amsa mata yay da tana bacci tace su fa dare ne ko ya amsa mata da yea,
"Yar gidanka dae Aure za'ai mata nace bari in sanar maka nasan ba lalle in ka sani ba" Hajiya ta fad'a
bayan sun gama gaisawar, shiru ya d'an yi lokaci guda yanayin fuskar shi ya d'an canja don ya fahimci
wadda take Magana akai slowly ya yace "waye zai mata aure?" Hajiya tace "wllh can garin su wai kakan
ne ya bayar da ita sai dae kawae Mahaifinta ya kira ya sanar zai zo d'aukar ta......" Nan ta kwashe komae
ta fad'i mashi har da halin da Fatun ke ciki ita da Dijen, sosae ya 6ata fuska ya ma kasa cewa komae har
saida Hajiyar tace "Haisam are u there?" Sigh yay yace "yea" taci gaba "abun ba dad'i wllh yarinyar na
son yin karatu to kuma ga Maganar aure" Haisam d'in yace "but this's a forced marriage I think zaki iya
yin wani abu bai kamata ayi mata aure ba" sauke ajiyar zuciya Hajiya tay tace "kagane su a wurinsu
hakan daidai ne don haka suka saba za6a ma yara miji ...." Katseta yay "amman ita ba a wurin su take ba
ai why za'a mata haka? U ave to do something sweetheart I think is part of ur work right?" D'an guntun
murmushi mai sauti Hajiya tay tace "abunda nike son ka gane wannan family issue ne kaman yadda na
fad'i maka haka suke ma yaran su yanzu inna ce in shiga Maganar ba lalle in yi nasarar hana yi mata
auren ba in kuma aka yi nasarar to kuwa mahaifin nata ne a matsala kamar yadda na fad'i maka d'azun
hakan ne ma yasa ita Fateema ta nuna ta Amince don fitar da mahaifinta daga halin da yake ciki" fuska a
kwa6e yake saurararta bayan ta gama yace "so now u mean there's no way out dole ayi mata auren?"
Hajiya tace "to ya za'ai in haka Allah ya kaddaro dole sai anyi mata auren sai dae ai fatan Allah ya zaba
abunda yafi zama Alkhairi, ita kanta Fateemar ta ban mamaki wllh ban yi tunanin zata yi k'arfin hali har
haka ba to amman nasan ba yadda zata yi ne bata son mahaifinta ya shiga matsala ne Saboda ita, yanzu
tace sati mai zuwa mahaifin nata zai zo d'aukar ta yanzun nan ma ta kawo man kud'i da ya turo mata
don ta sayi kayan kitchen" shiru bai ce komae ba har saida hajiyar tace ko shima ya fara baccin ne
sannan ya yi magana yace Allah yasa hakan yafi zama Alkhairi ta amsa da Amin daga haka su kae sallama
tace ya gaishe da Fanan, tun bayan da suka gama wayar still yay hannunshi dake ruk'e da wayar ya d'an
dafa ha6arshi da shi kwata kwata bai ji dad'in Maganar auren ba sosae ran shi ya 6aci don har fuskar shi
ta bayyana hakan, ya dau lokaci a hakan mutsu mutsun da Fanan ta fara yi ne yasa shi kai idanun shi
kanta slowly ta fara bud'e nata idanun kafin ta ware su a kan fuskar shi tana ganin yanayin fuskar tashi ta
yunk'ura ta tashi zaune shi kuma ya d'age kan nashi yana facing sama duk a tunanin ta Saboda rigimar
zuwa Asibitin da ta gama yi mashi ne hakan yasa ta kai hannu ta kamo hannun shi guda a sanyaye tace
"babe are u angry with me?" Shiru bai ce komae ba bai kuma d'ago ba cikin breaking voice ta kuma cewa
"am sorry for dat son da nike maka ne yasa am eager to ave child wit u..." Kwalla ne suka taru a idonta
tay shiru sai lokacin ya d'ago ya bita da ido kawae, shi kan shi bai san miya sa Maganar auren Fatun ta
dame shi ba, sosae yake jin ba dad'i a ran shi da k'yar ya d'an yi mata guntun murmushi yace kar ta damu
ba wannan ke damun shi ba, cike da kulawa ta tambayi abunda ke damun shi kawae sai ce mata yay bai
jin dad'in jikin shi ne da sauri ta matsa ta fara tatta6a jikin nashi wai ko fever ce shi dae bai ce mata
komae ba can ya fara k'ok'arin tashi yace zai je ya kwanta itama mik'ewa tay ya kai hannu zai d'auki
laptop d'in ta rigashi d'auka bayan ta rufeta suka nufi bedroom d'in shi yana shiga ya kwanta dama
shima sleeping dress ne a jikinshi, Fanan duk ta damu don tunda suka yi aure bata ta6a ganinshi a cikin
irin yanayi haka ba yawanci in taga canji tattare da shi ta tambaye shi zai ce ya gaji ne ko kan shi na
mashi ciwo yanzu kuma ta fahimci kamar yana cikin damuwa ne, cike da kulawa ta zauna a gefenshi ya
kalleta tace mashi ko ta had'o mashi coffee ko tea ya d'an girgiza mata kai alamar a'a tace to miya ke
damun shi ta d'aukko mashi magani tun da taji ba fever a jikin shi d'an murmushi yay mata ya kai hannu
ya jawo ta ta hawo gadon sosae a hankali ya furta "am Ok" da yar damuwa tace "are u sure?" Lumshe
mata ido kawae yay ta kwantar da kan ta a chest d'in shi tana shafa lallausar sumar dake kwance a wurin
da hannunta guda akai akai take d'aga ido ta kalli fuskar shi ya rufe idonun shi hakan yasa tay tunanin
yay bacci a wani bangare na zuciyarta kuma she's thinking what makes him so worried sanin shi ba abu
kadan ke sa a ga damuwar shi ba, jin saukar numfashin ta a saman chest d'in shi yasa shi gane tayi bacci
slowly ya ware idanunshi dama yayi hakan ne don bai son taci gaba da tambayan shi abun da ke damun
shi gashi ya kasa sanar da ita zancen Auren da za'a yi ma Fatun don baison ma yin maganar, a nutse ya
kai hannu ya janyeta daga jikinshi ya tashi zaune ya had'e hannuwan shi ya d'aura habar shi sam ya rasa
ma tunanin da zai yi ba kamar da Hajiya ta nuna ba abunda za'a iya yi a hana su yi mata auren can ya
sauke hannuwan ya kai hannu kan side drawer ya d'auki wayar shi saida ya gyara ma Fanan kwanciya ya
lullu6e mata rabin jikinta da duvet ya rage hasken d'akin sannan ya juya ya fita, Parlor ya nufa ya zauna
kan kujerar da ya tashi ya fara kokarin kiran layin Fatuu........

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._

*ASM Bk2026*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


.........Tana zaune kan darduma ta gama salla tana lazimi a d'akin Saude wayarta dake aje a gefen katifa
ta fara ringing, a hankali taja jiki ta matsa ta kai hannu ta d'auki wayar ta duba mai kiran nata, Jim tay
ganin sunan Ya Haisam ya bayyana kafin tayi picking ta kai kunne, shiru sukae gaba d'aya kaman bazasu
yi Magana ba can Haisam d'in ya kira sunanta "Zaraah" har saida gabanta ya d'an fad'i jin yanayin da ya
kira sunan nata cikin shaky voice tace "N..na'am Ya Haisam ina wuni" bai amsa mata ba ta sake cewa "Ya
Aunty Fanan" sai lokacin yace "she's fine" shiru suka d'an k'ara yi kafin yace "I heard u'r going to get
married right?" Har saida ta had'iye abu cikin karewar murya tace mashi eh,

"Kin hak'ura da zama Doctor kenan?" d'an runtse ido tay lokaci guda kuka yazo mata tace "Ehhh.. "
yana jiyo sheshshekar da ta fara yi a hankali, d'an yamutsa baki yay kafin yace "Why are u crying, ba kina
so ba shiyasa kika amince" cikin kuka tace "a'a Ya Haisam wllh bani so ba ni da yadda zan yi ne in ban
amince ba Baffana zai shiga matsala ne Baban shi Ard'o zai tsine mashi yanzu haka ma duk yan gidan sun
juya masu baya Saboda ya nuna bai so ayi man Auren shiyasa kawae na Amince don in taimake shi"
sosae yake jiyo sheshshekar kukan nata yanzu slowly ya runtse idonshi ya d'age kan shi sama boiling
from inside, ba k'aramin abu ke k'ona mashi rai ba amman wannan Al'amarin sosae ya ta6a mashi zuciya
ba kamar yanzu da yake jiyo kukan ta ya fahimci itama abun ya ta6a mata zuciya sosae, sun dau d'an
lokaci haka kafin ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ya kira sunanta ta amsa yace "is Ok, I get u so stop
crying and pray for d best" jinjina kai tay kaman yana ganinta sai kuma tace to daga haka yace mata zai
kwanta su dare ne yanzu tace mashi sai da safe, koda suka gama wayar zaune yay a wurin bai tashi ba
still kan shi a d'age yake saidae ya bud'e idanunshi ya k'ura ma ceiling ido da alama tunani yake, suna
gama wayar taci gaba da kukan da take yi wanda ba na komae bane face tabo da Haisam ya fama mata,
a cikin ran ta take ayyana da ta aure shi duk da yanzu bata shiga wannan halin ba tunda ba wanda zai ce
ai zai mata aure tana cikin haka Saude ta shigo don tace mata ta fito ta ci Abinci ta iske ta haka da sauri
ta zauna gefen Katifar ta janyo kan Fatun saman cinyarta ta shiga tambayarta lafiya cikin kuka take fad'in
ita bata son auren nan, sosae ta ba Saude tausayi don Hajiya ta fad'i mata zancen Auren da za'ai ma
Fatun, lallashinta ta shiga yi tana mata Nasiha har sai da tayi shiru sannan ta kama ta ta kaita toilet don
ta wanke face d'in ta bayan ta gama ne suka nufi Parlor. Kullum gidan Hajiya take wuni ba laifi gwaggo
na d'an sake mata amman ba wani sosae ba, ranar Friday da safe Baffanta ya kirata ya sanar da ita game
da zuwan shi ranar lahadi in Allah ya kaimu yace mata akwae wani Abokin shi da zai kawo shanaye
kasuwar charanchi ranar lahadin in zai koma sai su tafi tare koda akwae kayan da za'a d'auka tunda
Motar tashi babba ce, wata irin kyerma jikinta ya fara yi a dabarbarce take amsa mashi bayan sun gama
wayar zaune tay tana ta zare ido ya dae tabbata auren za'ai mata ji take tamkar ana zare mata lakar
jikinta ta d'au lokaci a haka kafin da k'yar ta mik'e taje ta sanar ma gwaggo to itama dae ta girgiza da jin
zancen amman bata nuna ba kawae sai ce mata tay Allah ya kaimu bata ji komae ba da yanayin yadda
gwaggon ta bata amsa don tama saba da yadda take mata Magana yanzu, bayan ta fito ta koma d'aki
gyale ta yafa ta nufi gidan Hajiya lokacin da ta je hajiyar na bedroom d'inta da sallama ta shiga ta amsa
mata da murmushi gefenta ta baza wasu takardu da alama tana duba wani abun ne, gaida ta Fatuu tayi
ta nuna mata gefenta tace ta zo ta zauna bayan ta zauna ne hajiyar ta tambayeta lafiya ta ganta sukuku
nan da nan idanunta suka kawo ruwa tana kyakkyafta idanu don kada su zubo murya na rawa ta fad'i
mata game da zuwan baffan nata itama hajiyar Maganar ta dake ta tay shiru can kuma sai tace Allah ya
kawo shi lafiya Fatuu ta amsa da Amin yayin da kwallan da take ruk'ewa suka fara zubowa Hajiya ta fara
lallashinta had'i da yi mata Nasiha mai tsuma jiki sosae taji ta samu natsuwa.
Washe gari Asabar Fatuu da ta je islamiyya ta yi ma k'awayenta bankwana had'i da neman yafiyar su duk
sunyi mamakin jin zancen Auren don ba wanda ya san da Maganar har Malaman su ma sun yi mamaki
sun kuma yi mata Addu'oi har Malam Nazifi na cewa bata fad'i da wuri ba da an yi mata sauka amman ko
bayan ta tafin in sha Allahu zai sa ayi mata bai amshi hadda ba a lokacin sai kawae yayi masu Wa'azi
game da rayuwar gidan Aure da yin biyayya ga miji sun sha kuka ita da k'awayenta yan ajin su da aka
tashi har saida suka rakota har gida, tunda ta dawo take k'umshe a cikin d'aki ko Abinci ta kasa ci Alwala
kawae ke fiddo ta haka ma gwaggo kowa dae yana cikin matsananciyar damuwa, bayan sallar la'asar ne
tana zaune kan abun salla wayarta tay ringing ta mik'e taje bakin gado inda take ajiye ganin hajiya ce
yasa ta d'auka da sauri bayan ta gaishe ta ta tambayeta tana gida ko ta tafi islamiyya tace mata tana gida
tace to ta zo yanzu ta amsa da to, dama akwae hijab a jikinta wucewa kawae tay bayan ta lek'a ta sanar
ma gwaggo hajiya na kiranta ta d'aga mata kai kawae, a Parlor ta iskesu ita da Saude da Tk ga wasu
manya manyan kwalaye guda biyu dake a bud'e shak"e da kayan amfanin kitchen gaida su tayi su duka
suka amsa mata fuska a sake hajiya ta nuna mata kayan tace "Fateema ga kaya nan ki duba in akwae
abunda kike so wanda babu sai ki yi Magana, can waje a bayan Mota akwae freezer da gas cooker ba'a
shigo dasu ba kar ai wahalar sake fitar dasu kuma" mutuwar tsaye Fatuu tay tana ta zare ido ganin uban
kayan dake gabanta wai kuma nata ne, ganin bata da niyyar dubawar yasa Hajiya ce ma Saude ta firfito
mata da kayan ta gani ta amsa da to ta duk'a ta fara fiddo kayan, ba abunda babu da zaka samu a
kitchen d'in yan gayu tun daga kan kaya masu amfani da wuta da sauran kayan amfani a cikin d'ayan
kwalin harda rantsattsun zannuwan gado da labulaye sai daga baya ne ma Fatun ta lura da k'aton kwalin
plasma TV dake can gefe itama Hajiyar tace tata ce she was completely speechless sai bin komae take da
ido Hajiyar ta tambayeta akwae sauran abunda take so wanda babu girgiza mata kai kawae tay don ta
kasa Magana ganin abun take tamkar a mafarki tana cikin hakan Hajiya ta mik'o mata kud'i tace "ga
wannan kud'in da kika kawo man ne Yayan ki ne ya turo da kud'i aka siya maki komae sai ayi wani
amfanin da su" idanu raurau ta kalli hajiyar tace ta kar6a mana sai kawae ta saka mata kuka Hajiya tace
"Fateema wannan koke koken yayi yawa zai iya ja maki wata matsalar ina mun gama Magana dake?" Kai
ta d'aga mata tace to tayi shiru sai lokacin ta yi mata godiya Hajiya tace ma Tk ya tashi su maida su cikin
Mota a had'a da sauran akai can gidan ya amsa da to ya mik'e Saude ma ta tashi ta kama mashi suka fara
fita da su, gaba d'aya da Sauden da Fatuu aka tafi lokacin Amadu na shago Tk ya parker hilux d'in Hajiyar
duk suka fito Amadu na ganin su shima ya fito suka fara kai kayan ciki, jin anata kacaniyar shigo da kaya
yasa gwaggo fitowa tana yin arba da kayan tay turus tana bin su da ido Fatuu ce ta nufe ta ta tsaya a
kusa da ita a sanyaye tace "wai Hajiya ce tace a kawo Ya Haisam ne ya turo da kud'i aka siya ga wanda na
kai mata tace a yi wani abun da su" ta kai Maganar tana mik'a ma gwaggo kud'in hannunta a hankali
tace ta ruk'e a hannunta, lokacin Saude ta k'araso ta gaishe da gwaggon da d'an murmushi ta amsa mata
tayi mata godiya, bayan an gama shigo da komae su Tk d'in sun tafi Amadu ya fara firfito da komae cike
da mamaki yana dubawa itama gwaggo idonta na akai lokacin da ya gama ya d'ago ya kalli Gwaggo yace
"Naira dae tasha kashi a wurin nan wannan ai an kashe million koma fi, ji wannan k'atuwar freezer da
gas cooker don Allah ga plasma ma babbar" ajiyar zuciya kawae gwaggo ta sauke kafin a hankali tace an
gode Allah ya saka da Alkhairi Amadu ya amsa da Amin ganin tana niyyar juyawa ta koma d'aki yace ba
za'a shiga dasu bane ta dakata tace tunda tafiya za ai dasu su kauda su gefe daga haka ta shige d'aki
bada jimawa ba kuma sai gata ta fito sanye da hijab ta nufi gidan Hajiya don yin godiya, da daddare
lokacin Fatuu ta gama komae ta kwanta tay tunanin yakamata tayi ma Ya Haisam godiya duk da bata son
Auren taji dad'in kayan don ko d'iyar wasu masu kud'in ce iyakar abunda za'a mata kenan, lokacin da ta
kira dawowar shi kenan daga Masallaci sallar Asuba a edge d'in gado ya zauna yay picking call d'in bayan
ta gaida shi ya amsa ta shiga yi mashi godiya yace ba wani abu shiru suka d'an yi jin kaman tana kuka
yasa shi fara lallashinta suna cikin hakan Fanan ta shigo jikinta sanye da jalbab da alama itama sallar tayi
zama tayi kusa da shi tana sauraran yadda yake Magana cikin kwantar da murya har saida ta d'an yi
mamakin da wa yake Magana haka, sosae ya kwantar mata da hankali kafin sukae sallama yay mata
Allah ya tsare hanya yace sai ya sake kira, yana cire wayar Fanan ta tambaye shi wacece yake lallashi
haka bin ta da ido yay ganin ta kafe shi da idanu alamar amsa take jira yasa shi d'age mata gira yace
"kishiyar da zan maki ce" wani kalan kallo ta jefa mashi ta d'aure fuska tamau can kuma sai ta ce "Babe I
hate dis kind of jokes" murmushin gefen baki yay ya ja jiki ya jingina bayanshi da heardboard yana cigaba
da kallonta ta wani sha murr ita ala dole bata son zancen kishiya ganin baida niyyar yi mata bayani yasa
ta k'ara tambayarshi da wa yake wayan sannan yace mata Zaraah ce with surprise tace to mi ya faru taji
yana lallashinta haka sai lokacin ya sanar mata zancen Auren da za'ai mata itama ta nuna bata ji dad'in
hakan ba k'arshe tace Allah yasa hakan yafi zama Alkhairi. Washe gari da safe lokacin da ta je gaida
gwaggo tace mata ta shiga makwabta tay masu sallama tace to, duk inda taje da an ji zancen Auren sai
anyi mamaki jin abun kwatsam akai tayi mata fatan Alkhairi harda masu bata kud'i amman ta k'i amsa
daga baya ta wuce gidan su Haulat lokacin da ta sanar ma innarsu haulat batun Auren sosae ta girgiza
don abu ne da ba wanda ya ta6a tunani Fatun harda kwallarta innar ta shiga bata Hak'uri anan ta
tambayeta Haulat kuwa ta sani tace mata a'a bata samun ta a waya innar tace in sha Allahu zata kirata ta
sanar mata, da zata tafi ta d'aukko wani glass jug da kwalin set d'in Warmers da unbreakable plates cikin
kayan Auren haulat ta bata Fatun na ta bassu tace sai ta amsa in ba haka ba zata aika mata dasu gida
dole ta amsa tay mata godiya ta tafi innar nata jajanta abun a ran ta, Sai wuraren La'asar Baffan Fatun ya
iso sosae taji dad'in ganin shi sai dae tana kallon shi ta fahimci ya rame sosae har duhu ma yayi hakan ya
tabbatar mata da duk abunda ya fad'a na halin da yake ciki dama kuma ta gasgata shi tun da ya fad'i
mata, a d'akin Kawu Amadu ya sauka bayan sun gaisa Amadun ya fita ya rage daga shi sai Fatuu dake
gefenshi tana mashi murmushi yace "inna wuro an saka ki cikin damuwa ko?" d'an girgiza mashi kai tayi
yace "ah kar ki man k'arya da ganin ki kina cikin damuwa fuskar ki ya nuna" tana murmushi tace "Baffana
kai ma ai ka rame sosae" d'an murmushi shima yay yace "Ya za'ai sai Addu'a kawae, ki yi hakuri don
Allah" da sauri tace "ba komae Baffa na rungumi hakan a matsayin kaddara ta" jinjina kai yay lokacin
gwaggo ta shigo da sauri ya tsugunna itama ta duk'a daga can wurin bakin kopa ya shiga gaidata cikin
harshen fulatanci tana amsawa fuskarta ba yabo ba fallasa tay mashi an zo lpy ya amsa da lafiya lou suka
d'an yi shiru sai kuma ta mik'e tace Allah huta gajiya ta fita, a sanyaye ya kalli Fatuu suka had'a ido ya
tambayeta har yanzu bata hak'ura ba ne tace mashi kar ya damu ta hak'ura ya dae yi shiru kawae
amman daga yanayin da yaga gwaggon yasan tana cikin fushi don yadda suka saba gaisawa ma ba haka
tay mashi ba duk da yasan dama dole tay fushi sosae don ba'a kyauta mata ba ita tasan wahalar inna
wuro gashi an nuna mata fin k'arfi, da k'yar Fatuu ta sa ya d'an ci Abincin da aka kawo mashi ba sosae ba
bayan ya gama tace yazo yaga kayan da Ya Haisam ya siya mata farko cewa yay ba sai ya gani ba tunda
dasu zasu tafi amman ta matsa mashi saida ya fita duk da ya hana ta bud'a amman shima yayi mamakin
uwayen kayan, bayan sallar Isha tare da Fatun yaje gidan Hajiya yin godiya lokacin tana Bedroom Fatuu
taje ta kirata da fara'a ta fito tana mashi maraba lale shima ya mik'e yana mata dariya bayan ta iso ta
zauna har k'asa ya duk'a ya gaishe da ita tana ya mik'e haba ya zauna, sosae suka shiga tattaunawa game
da batun Auren da za'a ma Fatun bawan Allah harda kukan shi ya nuna bai ji dad'in hakan ba Hajiyar ce
ta nuna mashi ya daina damuwa ya bita da Addu'a Allah yasa haka yafi zama Alkhairi daga baya suka hau
yabon Fatun irin sadaukarwar da tayi ta hak'ura da karatun ta ita dai d'an murmushi kawae take, da zasu
tafi sosae yayi mata godiyar kaya da abun Arziki da ake masu ta nuna mashi ai an zama d'aya su kai
sallama Hajiyar ta tambaye shi lokacin da zasu tafi yace gobe bayan an gama sallar Asuba har hajiyar na
cewa bazai bari ya k'ara hutawa ba yace ai da Abokin shi ne zasu tafi Saboda kaya kuma Abokin nashi
gobe zai tafi tace ta fahimta sai Allah ya kaimu zata lek'o in zasu tafi, suna komawa gida Baffan nata yace
taje ta kwanta tunda da wuri zasu tafi ta amsa da to tayi mashi sai da safe, tana komawa d'akin ta
wayarta ta fara ringing taga Abbas ne bayan ta d'aga ta gaishe dashi yace ashe abunda ke faruwa kenan
shi bai sani ba tunda bai nan sai yanzu Haisam ke fad'i mashi tace eh ga ma Baffanta har ya zo gobe da
Asuba zasu tafi, sosae ya jinjina Al'amarin ya nuna baiji dad'in hakan ba daga baya yay fatan Allah ya
za6a abunda yafi zama Alkhairi tace Amin yace in sha Allahu zai zo d'aurin Auren ta fad'a mashi Date d'in
tace yanzu dae bata sani ba amman in ta tambayi Baffanta zata turo mashi yace Ok, suna gama yin
wayar saiga Alert na 50k daga Abbas d'in ya turo mata text message cewa tayi amfani da su ba yawa har
saida tay yar kwalla, a wannan Daren dai tsakanin Fatuu da gwaggo ba wanda ya runtsa har gwara Fatun
tana d'an yin baccin sai kuma ta farka ta fara tunane tunane, yanzu abunda yafi damunta shine waye
zata aura??? Wace irin rayuwar Aure zasu yi ita bata son shi kuma shima ta san ba son ta yake ba tunda
dae Auren had'i ne ko ganin juna basu ta6a yi ba.

Washe gari kiran sallar farko Abokin baffan nata ya iso ba 6ata lokaci suka fitar da kayan aka shirya su a
bayan babbar Motar suna gamawa suka nufi Masallaci don yin sallar Asuba lokacin itama Fatuu taje tayo
wanka tazo ta kabbara sallar dama tuni ta gama shirya kayanta da zata tafi dasu don ba komae zata
d'auka ba k'aton Akwatin da Haisam ya bata ne sai trolley d'inshi anan ta shirya kayanta na sawa ta bar
ma gwaggo na tsakiyan sai wata jaka da ta zuba littattafanta da sauran abubuwan ta da take so, tana
zaune Kawu Amadu ya shigo yace ta gama shiryawa tace eh ya fara fitar mata da kayanta lokacin da ya
dawo zai d'auki na k'arshe ne Fatuu dake tsaye ta kira sunan shi ya kalleta kaman zata sa kuka ta mik'a
mashi wayarta tace " gata kaci gaba da amfani da ita sai ka bani taka" waro ido yay baki bud'e alamar
mamaki kafin yace "a'a ki bar abun ki can ma ai zaki iya amfani da ita" da sauri tace "ai shiyasa nace ka
bani taka kaga can bama wani Network ke da akwae ba mai kyau ko naje da ita bazata yi man amfani ba
sosae kaman yadda kai zata maka don Allah ka amsa" ta k'arasa hawaye na zubo mata hannu ya kai yana
goge mata yana cewa tayi shiru zai amsa, dama ta goge abunda zata goge tace ya tura mata abubuwan
da ta bari kafin su tafi yace to ya amshi wayar ya d'auki d'ayar jakar da yazo d'auka ya fita, gari na fara
wayewa suka fito don tafiya har lokacin Fatuu bata ga fuskar gwaggo ba lokacin da ta shiga don yi mata
sallama a zaune kan abun salla ta isketa ta d'ukar da kanta k'asa, duk'awa tay gefenta ta gaishe da ita ta
d'aga mata kai kawae shiru Fatun tayi can kuma tay k'arfin halin cewa "G...gwaggo zamu tafi" farko shiru
tay sai kuma murya a disashe taji tace "Allah ya tsare hanya yasa Alkhairi Amadu zai kawo maki sak'o"
daga haka tay shiru sosae gaban Fatuu ya fad'i don daga jin muryarta kuka tayi cikin rawar murya Fatun
tace "to gwaggo ke bazaki zo ba?"shiru tay mata ta k'ara tambayarta nan ma tay mata shiru kawae sai
tasa mata kuka tana fad'in "Don Allah gwaggo ki yi hakuri ki yafe man kar ki ce bazaki zo ba, kowa in za'a
mata aure Mahaifiyarta na mata fad'a da nasiha ni waye zai man in kika k'i zuwa??" sai lokacin ta d'ago
idanunta sun yi jawur cike tabb da k'walla tay d'an guntun murmushin takaici kafin tace "ga yadikkon ki
ga kuma wasu iyayen naki cike da gida Fatuu" sosae take kuka tana rok'onta ita dae don Allah ta zo suna
cikin haka Hajiya ta shigo gidan da sallama jiyo kukan Fatun yasa ta nufi d'akin gwaggon tana fad'in
"koke koken ne har yanzu ba'a gama ba an bar mutane nata jira a waje tafiya bata kusa ba" d'aga
labulan kopar tayi ta shiga ganin yadda fatun ke kuka ta tambayeta abunda ya faru cikin kuka ta sanar
mata, wani kallo tay ma gwaggon rai 6ace tace "haba Dije wai miyasa kike haka ne don Allah, yarinya
zata tafi baza kuyi rabuwar Arziki ba ki faranta mata rai sai ki fad'a mata abunda zaki tada mata hankali
haka" girgiza kai gwaggon tayi tace "nifa ban ce mata bazan je ba ita ta yanke hukunci" Hajiya ta kai
hannu ta mik'ar da Fatun tsaye tana ce mata tayi shiru tama isa tace bazata je bikin ba suna nan zuwa
harda ita sai lokacin taji sanyi a ranta suka nufi hanyar fita tana ta waiwayen gwaggo da tayi zaune bata
da niyyar mik'ewa bare ta rakata, waje suka fito dama ita kawae ake jira Hajiya ta kaita har bakin Motar
tace ma Baffanta gata nan su tafi kar suyi dare a hanya cike da girmamawa ya amsa mata da to ya bud'e
ma Fatuu kopar Motar ta baya ta haye ta lek'o da kanta tana kallon su Tk da Amadu da Saude harda
wasu daga cikin makwabta da suka fito sai kuka take Amadu ma ya kasa jurewa saida ya yi kwalla da
k'yar ya matsa ya mik'a mata wayar tashi cikin kuka tace "Kawu Amadu zaka zo ko?" Da sauri ya jinjina
mata kai ya kamo hannunta guda yace "in sha Allahu tun kafin bikin ina nan zuwa ki yi hakuri don Allah ki
kwantar da hankalin ki kin ji" kai ta d'aga mashi lokacin Baffanta yace ma Amadu ya rufe mata kopar
yace to ya saki hannunta ta maida kan ta ciki ya rufe sannan ta sake lek'o da kan ta windown kopar,
zagayowa Baffanta yay ya yi masu sallama ya k'ara ma Hajiya godiya duk suka yi masu Allah ya tsare ya
kai su lafiya ya amsa masu daga haka ya juya ya nufi gaban Motar ya shige shima Abokin nashi wanda
shine driver d'in da zai tuk'a Motar ya lek'o yay masu sallama daga haka ya maida kan nashi ya tashi
Motar wani bugu gaban Fatuu yay ta d'aga hannu tana masu bye bye tana ta kuka suma duk suka d'aga
mata Tk da Saude ma duk kasa jurewa su kai sai da suka zubar da kwalla Motar na fara tafiya kawae sai
ganin fuskar gwaggo tay ta lek'o sosae ta d'aga mata hannu ta kira sunanta da k'arfi "Gwaggo!!!" hakan
yasa duk aka waiga ana kallon gwaggon don ba wanda ya lura da ta fito da k'yar ta d'aga ma Fatun
hannu guda itama tay mata bye bye..........

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._

*ASM Bk2027*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

...........Saida Motar ta bar layin sannan duk suka juya Hajiya ta kalli Gwaggo ganin hawaye a fuskarta ta
shiga bata baki kafin suka wuce gida ita dasu Saude Amadu kuwa tsaye yay duk jin jikin shi yake ba dad'i
yana ganin gwaggo ta koma ciki shima ya shige gidan ya nufi d'akin shi ya kwanta, akai akai yake kai
hannu yana share kwallan dake gangaro ma shi, gwaggo na shiga d'aki ta haye gado tasa kuka mai cin
rae taci guri in Allah ya nuna mata auren Fatuu sai gashi komae ya juye zata yi aure ba tare da tana farin
ciki da hakan ba, sosae ta sha kuka daga baya ta lallashi kanta ta yi shiru. Tun da suka hau hanya take ta
kuka Baffanta da Abokin nashi nata bata Hak'uri har dae ta yi shiru sai dae kwalla basu daina zubo mata
ba tana kai gefen gyalen ta tana gogewa daga baya bacci ya kwashe ta, sosae Baffanta yaji dad'in hakan
don ba k'aramin ta6a mashi zuciya kukan da take ke yi ba, sai da suka tsaya Kano sannan ta farka suka
siya abunda zasu ci aka mik'a mata nata kamar bazata ci ba baffanta yace tayi hak'uri ta ci idanunta duk
suyi luhu luhu ba yadda ta iya dole taci don tana jin yunwa Bayan sun d'an huta suka sake d'aukar hanya
duk garin da suka tsaya sai Baffanta ya siya mata abu wani ta ci wani ta k'i ci, Alhamdulillah sai Bayan
la'asar wuraren karfe biyar na yamma suka isa tunda suka iso jumeta Fatuu ke jin tamkar za'a kaita
kurkuku sai ma da suka isa rugar kukan zuci kawae take, Motar na tsayawa gaban gidan Kamalu da su
Mino dake ta dakon isowar su suka nufo Motar cike da farinciki Baffan Fatun ya zagaya ya bud'e mata
kopar ta fito sai murnar ganinta ake ita kam ta kasa yin ko murmushi ganin yanayinta yasa Kamalu da
Mino suma d'an shiga damuwa baffanta yace su shiga daga ciki Mino ta kama hannunta shi kuma
kamalun yace ya tsaya su sauke kaya, bin Mutane da ido kawae ta rink'a yi ana mata sannu da zuwa kan
kace mi labarin zuwanta ya isa ko ina a cikin gidan harda uban kayan da aka zo dasu yan gidan duk aka
fito wasu suka lek'o ta Katanga ganin kwakwaf ita dae kallon su kawae take tamkar yau ta fara ganin su,
kafin su isa sashen su sai ga yadikko ta fito cike da farinciki ta zo ta rungume Fatun tana mata sannu da
zuwa lokacin da ta d'agota suka had'a ido kawae sai ganin kwalla tay ta zubo mata da sauri ta Sunna kai
k'asa sosae jikin yadikko yay sanyi ta kama hannunta suka nufi ciki, an gyara sashen na su sosae har da
su fenti haka d'akin yadikkon an maida shi ciki da falo har da bathroom a cikin uwar d'akan, zaunar da ita
yadikko tay kan kujera ta zauna gefenta haka su Mino ma duk suka zazzauna suna kallon ta ta sadda kai
k'asa, kan kace mi d'akin ya cika da yara harda wasu daga cikin Matan gidan suka shigo yi mata sannu da
zuwa suna ce ma yadikko ashe Amarya ta iso ita kuma tana bin su da eh kawae don tasan yawanci duk
gulma ce ta kawo su, sai Bayan wani lokaci mutanen suka lafa yadikko tace ma sauran yara suje su
k'yaleta ta huta bayan duk sun fita ya rage saura yan'uwan Fatun kawae cike da nuna damuwa yadikkon
tace "Fatuu ki yi hakuri kin ji, kowa yasan ba'a kyauta maki ba wllh duk bamu ji dad'in wannan abun ba
ba yadda zamu yi ne da muka nuna bamu so baki ga halin da muka shiga ba akai ta mana wulak'anci da
Maganganu duk aka tsangwame mu Baffan ki har ciwo yayi...." Dakatawa tay tana goge kwallan da suka
taru haka ma su Mino duk kwalla suke zubar wa a hankali Fatun ta d'ago ta kalli yadikko cikin rawar
murya tace "ba komae ki daina kuka ai gani na zo sai suyi man Auren" kamata tay ta rungume tana mata
godiyar taimakon su da tayi ta amince da wuri wanda duk basu yi tunanin hakan ba ta tambayeta har
yanzu gwaggo fushi take don baffanta ya sanar da ita ta d'au ki zafi sosae Fatun tace mata a'a ta hak'ura
tana nan zuwa sosae yadikko taji dad'in hakan, d'agota tay tace bari ta zubo mata Abinci ta barta da
yunwa ga gajiyar hanya Fatun ta mik'e tace band'aki zata shiga da sauri Mino ta mik'e tana nuna Mata
cikin d'aki tace an yi sabo a ciki suka nufi cikin tare, harda Alwala tayo Bayan ta fito ta kabbara salla a
cikin uwar d'akin lokacin Baffanta da Kamalu suka shigo d'akin a Falo suka tsaya baffan ya tambayi Mino
inna wuron ta kwanta ne tace mashi tana salla ne ya nemi wuri ya zauna Kamalu ma ya zauna lokacin
yadikko ta shigo ta jere ma Fatun kayan Abinci kafin ta zauna a gefe tana ma Baffan ya gajiyar hanya
Kamalu ya shiga basu labarin uban kayan da Fatuu tazo da su yace yawanci ma shi duk bai san mi ake
dasu ba wasu dae ya san su a cikin film harda wanda ake gasa kaji duk su kae yar dariya kafin kuma shiru
ta biyo baya can kuma Baffan yace ma yadikkon kayan na a d'akin shi aka kai su da d'akin Kamalu za'a sa
to kuma kar a lalata wani abun tunda bashi kadae bane a ciki tace hakan yayi suna haka Fatuu ta fito duk
suka d'aga ido suna kallonta ta k'araso da d'an murmushi zata zauna a k'asa kan leda Baffan yace tazo ta
zauna kusa dashi yadikko tace ai Abinci zata ci yace to, saida ta tambaye ta abunda zata ci tace duk
wanda ta zuba mata tasa mata burabusko tace in ta cinye sai a k'ara mata wani Abincin ita dae shiru
kawae tay, Sam ta kasa sakin jiki ta ci Abincin sai dae tai ta juya cokali baffanta ne da ya kula da hakan
yace ta daure ta samu ta ci tace to ta d'an k'ara tsakura kafin ta ture tace ta k'oshi, yadikko tace ai bata
ci komae ba tace bata jin dad'in bakinta ne, fura ta zuba mata tace ta daure ta sha zata ji k'arfin jikin tace
to, ba laifi ta sha da d'an yawa suna son suyi fira da ita saidae kowa bai cikin yanayi mai dad'i ba kamar
ganin yanayin Fatun duk sunyi jigum jigum sai jefi jefi suke Magana daga baya Baffanta da Kamalu suka
tafi yin salla suma suka Mik'e don su yi, Bayan sun gama sallar ne su Aysha suka matsa ma yadikko kan
tazo ta ga kayan da aka zo dasu har saida ta mik'e ta bisu, koda taga kayan kitchen d'in tsananin mamaki
ne ya kamata don ta san ba kananun kud'i aka kashe ba don kuwa ta ta6a yin aikatau a gidan wasu yan
gayu a Abuja duk ta san amfanin kayayyakin yan gidan ma duk suna ta zuwa suna gani tuni labarin irin
kayan da aka zo da su ya kai ma su Yaya, Bayan yadikkon ta koma d'aki ne ta zauna a gefen gado da d'an
murmushi tace ma Fatuu dake zaune kan sallaya "ko zaki je ki gaisa da su Yaya nasan sun san da kun iso
tuni" tura baki Fatuu tay ta juyar da kanta wani irin haushin Yayar take ji don ta san harda ita aka had'a
komae, ganin bata ce komae ba yasa yadikkon k'ara mata Magana a hankali ta juyo tace mata ta gaji ba
yanzu ba sai ta huta, d'aga mata kai kawae tayi itama gudun Magana ne yasa tace taje su gaisan don
tasan sai anyi tsegumin rashin zuwan nata ta gaishe dasu, shiru suka d'an yi kafin yadikkon tace "naga
uban kayan kicin gaskia gwaggo ta kashe kud'i ba kad'an ba, ni baffan ki ce man yay dubu d'ari ya tura
har ina cewa sun yi kad'an don jere ake ma kicin sosae a birni kuma kayan suna da kud'i to sai yace man
bai gama biyan kud'in kayan gado da kujeru ba don shi kad'ai aka bari da hidimar Ard'o ne kawae ya
bashi shanu guda d'aya ya siyar yayi maki kayan d'aki sai kuma kud'in sadakin ki dubu 100, shi kuma so
yake yayi maki kaya irin na yan birni shiyasa duk ya tattara kud'in shi ya biya don kayan fin rabin miliyan
ne za'a maki" shiru Fatun tay yayin da tausayin mahaifin nata ya k'ara kamata,

"Wai nikam Fatuu ina Ya Handsome d'in ki??" Har saida kirjin Fatuu ya d'an buga damm jin tambayar
da yadikkon tayi mata, shiru ta d'an yi sai kuma a hankali ta kalleta ganin tana kallon ta alamar jiran
amsa yasa tace "Ya yi aure" dan bud'a ido yadikko tay kafin tace "Allah sarki yaushe?" tace "kusan wata
ukku yanzu" rausayar da kai yadikko tay kafin ta sake cewa "a nan Katsina?"

"A'a basu nan k'asar suna America" da k'yar ta bata amsar ta d'ukar da kanta k'asa jin kwalla na niyyar
zubo mata girgiza kai yadikko tay tace "Allah bai k'addara mijin ki bane don ni da nayi tunanin son ki
yake wllh koda kika ce man ba haka bane wancan lokacin kawae na jiki ne na zata yana son ki ne ya bari
sai kin k'ara girma don hidimar da yake tayi yawa yawanci zaki ga irin hakan ba hakanan mutum ke yi ba
da dalili ashe shi don Allah yake yi" a sanyaye Fatun ta d'ago tace "shine ma ai ya turo kud'i aka siya
wancan kayan" hannu yadikko tasa ta ruk'e ha6a tace kai don Allah Fatun ta d'aga mata kai alamar eh,

"Kai amman dae wannan mutumin d'an Arziki ne wllh ni bamma ta6a jin mutum mai Alkhairi irin nashi
ba, ace daga makwabta ka ya dinga hidima haka ni fa wllh nayi mamakin kayan can don ko banza sai sun
yi miliyan ko ma fi" dakatawa tay tana maida numfashi kafin da d'an murmushi ta dafa kafad'ar Fatun
tace "amman da gaske bai son ki kuwa?" D'agowa Fatuu tay ta kalleta idanunta sun k'ara sauyawa a
hankali tay shaking kanta tace "bai ta6a so na ba, dama yana tare da wadda ya auran yar uwarshi ce"
cike da zolaya yadikko tace "to amman ke nasan ai kina son shi ko?" bin ta da ido Fatuu tay ta kasa ce
mata komae kawae sai ganin kwalla yadikko tayi tana zubo mata zaro ido tay Fatun ta kifa kanta a jikin
kafafun yadikkon ta sa kuka, wani irin sanyi jikin yadikkon yay ta kai hannu ta d'ago ta ta zaunar da ita
gefenta ta rungumo ta ta gefe cikin kuka Fatun ke fad'in "ina son shi sosae yadikko nayi tunanin shima
yana sona ne ashe ba haka bane bai ta6a so na ba ina ji ina gani yayi auren shi ya tafi ya barni" har
idanun yadikko sun ciko da k'walla ita dama tayi mamakin saurin amincewa da Fatun tay ai mata auren
ashe ashe ciwo ne da ita a zuciya sosae ta bata tausayi ta shiga rarrashinta tana bubbuga bayanta tace
"kiyi hakuri Fatuu na fahimci yadda kike ji ki bar ma Allah komae in har shi rabon ki ne Allah ya k'addaro
zaku rayu matsayin mata da miji ko ba dad'e ko ba jima hakan sai ta faru don in dae abu rabon ka ne
kana zaune zai iske ka har inda kake har kai ta mamakin yadda hakan ya kasance wannan kad'an daga
ikon Allah ne don ni kaina shaida ce na so Mahaifin ki kamar mi muna cikin soyayya aka ce an bayar dani
ga wani abokin mahaifina ina ji ina gani aka man Auren dole kaman zan yi hauka naje gidan shi sam ba
kwanciyar hankali ga wulak'anci dama shi bai d'auki mace a bakin komae ba tamkar riga haka yake canja
mata shima Baffana harda kwad'ayi yasa ya bashi aure na k'arshe ya yi man sakin wulakanci lokacin
yunwa duk ta k'arar dani abun bak'in cikin lokacin Mahaifin ku har yayi auren shi koda na tuntu6e shi
Bayan na gama idda sai ya bani hak'uri ya nuna man bai da ra'ayin mata biyu, ya dae fad'a man haka ne
kawae amman nasan kawae ya daina so na ne dama na samu labarin irin son da yake ma matarshi wato
mahaifiyar ki gata yar birni mai ilimin boko a lokacin ne na samu aka man hanya na tafi aikatau Abuja
nayi nisa da garin to ashe Allah bai kaddaro zasu rayu tare tsawon lokaci ba wllh lokacin na girgiza da jin
labarin mutuwarta don lokacin ni nama fidda ran auren nashi na nemi number d'in shi ta hanyar wani
Yayana na kira don yi mashi gaisuwa to anan muka samu lambar juna mu ka d'an rink'a gaisawa ina d'an
kwantar mashi da hankali ana haka Bayan wani lokaci watarana sai kawae yayi man Maganar Aure yace
in ba damuwa lokacin na k'ara gasgata girman ubangiji don kuwa in nace ban son shi to fa nayi k'arya
Saboda son gaskiya nike mashi wanda bai k'arewa, ba 6ata lokaci na nuna mashi na amince sanin yana
cikin hali ga marayun yara kuma duk da ina jin dad'i a in da nike aikatau haka na baro Abuja na dawo mu
kai Aure" lamo Fatuu tay yayin da cikin ranta ta ke kokonton anya Ya Haisam zai zama mijinta ita tama
fidda ran hakan, to yaushe ma ita da zata auri wani shima kuma yana can yana auren wata, Yadikko taci
gaba da cewa "ina so ki sani Al'amarin mumini dukkan sa Alheri ne, in samu yay Alheri ne in ya rasa ma
Alheri ne, acikin wani hadisi aka fad'i mana hakan lokacin ina zuwa islamiyya a Abuja don haka ki sa a
ranki duk abunda ya faru dake mai kyau ne ki daina damuwa don duk abunda zai faru da bawa an riga da
an rubuta ki ci gaba da Addu'a muma kuma muna yi maki" kai Fatun ta d'aga mata ta d'ago da fuskarta
tana share mata hawayen da d'an murmushi akan fuskarta bayan ta gama goge mata tace ta tashi tayi
sallar Isha sai ta ci Abinci ta amsa da to, bayan ta ci Abincin wanka tayo ta saka kayan bacci ta haye gado
ta fara tunanin gwaggo tana son kiranta amman kuma tana zullumi don tasan in da Lafiya lau bata fushi
ba yadda za'ai ace har yanzu bata kira taji ya suka iso ba tana cikin hakan wayarta ta fara ringing ta
d'auka ta duba Kawu Amadu ne mik'ewa tay zaune ta kara wayar a kunne bayan ta d'auka, gaisawa
sukae yay mata anje lafiya ta amsa kafin ta tambaye shi gwaggo yace tana d'aki shiru tay bata ce ya
kaima ta ba shima bai ce zai kai Matan ba, yar hira suka yi yawanci dae lallashin ta ya k'ara yi kafin daga
baya sukae sallama ta cire wayar, zaune tay bata koma ta kwanta ba gaba d'aya ta rasa ma tunanin da
zata yi komae bai mata dad'i tana cikin hakan wayarta ta sake yin ringing ta kai idonta kan screen d'in
sunan Ya Haisam ta gani lokaci guda ta saki murmushin da ita kanta bazata tuna when last da tayi irin shi
ba don taji dad'in kiran nashi ko ba komae ta fahimci ya damu sosae da halin da take ciki, picking tay ta
kara kunne kafin a hankali tay mashi sallama ya amsa mata a sake ya tambayeta ya suka isa tace mashi
lpy Lou, shiru suka d'an yi sai kuma taji yace "kin daina kukan ko?" tana murmushi tace eh yace "dat's
gud ki yi hakuri haka rayuwan yake we plan but God plans d best for us and all tests from Allah are
Alkhair" jinjina kai tay ta d'an had'e lips d'inta sosae take jin dad'in yadda yake mata Magana bayan d'an
shiru cike da zolaya yace "kin had'u da groom d'in naki ko?" Tura baki tay kaman yana ganinta, yace "ba
tura man baki zaki ba ki ban amsa" waro ido tay jin ya gane abunda tay a hankali tace "a'a ni har yanzu
ban san shi ba" d'an murmushi yay sai kuma yace "Ok in kun had'u sai mu gaisa in bashi amanar ki" d'an
murmushi tay bata ce komae ba yace "ko baki so?" Da sauri tace "ina so" shiru suka d'an yi can tace
mashi ya Aunty Fanan yace yana wurin aiki itama tana wurin aiki tace to, "baku da Network mai kyau da
na maida vedio call in ga sore eyes d'in ki" zaro ido tay da yar dariya kawae yace "ko idanun basu
kumbura ba?" Tura baki tay tace "sun kumbura" lallashinta ya shiga k'ara yi suna haka yadikko ta shigo
dama tana falo ita da yaran ta hana su shigo don kar su takura mata har saida tay mamakin ganin Fatun
zaune tana waya kuma harda murmushi akan fuskarta ganin kallon mamakin da take mata ne yasa tace
ma Ya Haisam d'in ga yadikko zasu gaisa yace Ok ta cire wayar ta mik'a mata ta fad'i mata ko wanene da
sauri ta amsa ta zauna a bakin gado tana ta washe baki suka gaisa kafin ta hau yi mashi godiyar abun
Arziki yace ba wani abu sosae tay mashi Addu'oi kafin ta mik'a ma Fatuu wayar tana amsa yace bari ya
kyaleta ta huta sukae sallama, bayan sun gama firar Haisam d'in ta shiga yi ma Yadikko ita kuwa ganin
sakewar da tay yasa ta biye mata, Washe gari tana cikin yin karin kumallo don bata tashi da wuri ba
Baffanta ya shigo duk suka gaishe dashi da fara'a yabi Fatun ya samu wuri kan kujera ya zauna yana
amsa gaisuwarta yadikko ma ta gaishe dashi ganin ya shirya tace har zai fita ne yace "Eh ina son zan je
can jumeta ne wurin masu kayan gadon" yadikko tace "za'a d'aukko ne?" Shiru ya d'an yi kafin yace
"tukunna dae kinsan har yanzu akwae sauran kud'i da zan cikashe masu dubu 200, da nayi tunanin zan
samu wasu kud'i ne to amman tunda lokaci k'urewa yake zan k'ara kai shanuwa guda kasuwa sai a basu
kawae" da yar damuwa yadikko tace "amman shanayen ba biyu ne suka rage ba kuma kace zaka sayar
da d'aya Saboda hidimar bikin yanzu in ka saida wannan shikenan fa sun k'are" yar dariya yay yace "to ai
biyan buk'ata yafi dogon buri sai a gode ma Allah da ya sa akwae" shiru kawae tay acan k'asan ranta
kuwa haushi ne ya turnuke ta na Ard'o duk shi ya tattago hidimar ba tare da an shirya ba, shi yakamata
ace ai yay kusan duk hidimar amman ya k'ame hannu duk tulin Arzik'in da ke gare shi, shiru Fatuu tay
tana bin su da ido can kuma sai ta mik'e ta nufi cikin uwar d'akin bada jimawa ba ta dawo ta nufi gefen
baffanta ta zauna da d'an murmushi ta mik'a mashi abunda ta d'aukko, bin yan kunnan dake a tafin
hannunta yay da kallo kafin ya maida idanun nashi kanta cikin alamun rashin fahimta tace "Baffa wannan
zinari ne kuma 200k aka siye shi in kasan in da ake sayarwa sai ka saida kayi amfani da kud'in" ba shi ba
har Yadikko waro ido sukae cike da Al'ajabi baffan ya tambayeta ina ta same su ta fad'i mashi da Ya
Haisam makwabcin su zai yi aure ne ya bata kud'in shine Gwaggo ta siya mata yan kunnan, jinjina kai
duk sukayi a tare suka shiga yabon Haisam d'in baffan yace "to inna wuro abu mai daraja haka ai bai
kamata a sayar dashi ba" yar dariya tay tace ai don ajiyar kudin aka siya tunda yanzu ana buk'ata ba sai a
sayar ba, duk yadda tayi K'in Amincewa baffan yayi da a saida yan kunnan yace ta bar abunta zai mata
amfani ba abunda zai gagara in sha Allah, bata ji dad'i ba ta yamutsa fuska cike da wasa yace ko tayi kuka
ba zai amsa ba gwara ta adana hawayenta, can ta tuna da kud'in da ya tura mata ta siya kayan kitchen ta
mik'e da sauri tace to tana zuwa, bayan ta dawo ta d'aura mashi kud'in kan cinyarshi tace "to ga
wad'annan su dae dama kai ka tura man kud'in kayan kitchen to kuma an siya komae sai kai amfani dasu
sannan ga Atm d'ina akwae dubu 70 a accnt d'in sai ka cire su ka had'a" baki bud'e suke kallonta ganin
haka yasa tay mashi bayanin inda ta samu kud'in cikin account d'in nata 50k da Abbas ya tura mata sai
dama akwae 20k cikin sauran kud'in Graduation da Haisam ya tura mata,

"Amman inna wuro ke ba amfanin da zaki da kud'in ki ne da kin bar su dama na ta6a sadakin ki" da
sauri tace "a'a ba abunda zanyi da su Baffa kayi amfani dasu kawai" yace zai cire dubu 50 ta bar 20k d'in
ta mata wani amfanin, sosae suka shiga yi mata godiya shida yadikko harda yar k'wallar shi yace in sha
Allahu yadda ta za6i farin cikin shi fiye da nata ita ma Allah zai faranta mata haka ya shiga jera mata
Addu'oi tana amsawa da Murmushi daga baya ya mik'e yay masu sallama ya tafi.

JUMETA
babban Parlor ne mai d'auke da set d'in dankara dankaran Sofas da kayan kallo irin dae falon da daka
kalla zaka shaida na masu hannu da shuni ne, a kowanne 6angare na bangon d'akin akwae hotuna
wanda yawanci duk na yan siyasa ne kama daga d'an majalisa, governor harda na shugaban k'asa, zaune
a saman 3 seater Alhaji lawal ne yana sanye da farar jallabiya idanunshi sanye cikin glasses yana kallon
labarun yamma a kai akai yake juyawa gefenshi ya kalli Matar shi Hajiya Rabi'atu dake gefenshi tana
mashi hira, babbar mace ce saidae bata manyanta ba sosae kana kallonta zaka fahimci hutu ya zauna
mata sosae, tana da kyau ba laifi gata jajir da ita sannan tana da k'iba ba irin mai muni ba jikinta sanye
da had'addan lace ta kashe d'auri kana kallon ta kaga wayayyar bafullatana, da yar sallama ya shigo cikin
parlon duk suka d'aga kai suka kalleshi, matashi ne wanda a k'alla zai iya yin shekaru 35, dogo ne sosae
sai dai sam bai da jiki kuma ja ne irin kalar fatar Mahaifiyar shi har kama suke ga sumar kan shi da ta
k'ara bayyana shi a matsayin bafullatani don a nad'e take amman bata da yawa, jikin shi na sanye da
bak'in silk wando da blue riga mai dogon hannu da ma6allai ya yi zanzaro hakan ya bayyanar da
had'addan bak'in belt d'in dake d'aure a k'ugunshi haka hannun shi na sanye da wrist watch silver,
saman kujerar dake opposite da su ya zauna fuskar shi sam ba annuri ya gaishe da su duk suka amsa
Alhaji lawal yace "Khalid ka dawo?" Amsa mashi yay da "Yes Dad"

"To ya aikin?" yace "Alhamdulillah" ita dae Hajiya Rabi'atun kallonsu take tana murmushi,

"Dama dalilin da ya sa na kira ka don in sanar da kai Amaryar taka ta iso tun jiya don haka sai ka samu
kaje ku gana da juna, sannan duk abunda ya kamata kayi in kaje sai ka tabbatar kayi ma'ana ka sallame
ta da abunda zata yi hidimarta don kasan 2 weeks ya rage so we need not to waste time" wani irin k'ara
d'aure fuska Khalid d'in yay har saida Dad d'in yace bai ji bane sannan kaman an masa dole ya ce "Ok"
kallon Hajiya Rabi'atu yay yace "Ke wurin ki ina fata kin kammala komae" tana murmushi tace "Eh an
kammala had'a lefen dama abunda ya rage akwae kayan da za'a d'inka mata already na fitar dasu suna
ma wurin d'inkin to amman ba'a d'inka ba Saboda rashin measurement nata tunda ba saninta mu kae ba
amman tunda ta zo yanzu ko zuwa gobe sai Sadeeya taje da driver su taho tare aje a d'auki
measurement d'in nasan ba 6ata lokaci zai d'inka" jinjina kai yay alamar gaisuwa sai kuma ya maida
kallon kan Khalid yace "kai yaushe zaka je d'in?" shiru ya d'an yi sai kuma ya watsa hannu yace "ko Next
tomorrow tunda naji zasu wurin d'inki goben" shiru Alhaji lawal d'in ya d'anyi yana d'an tunani can yace
"kai yakamata kaje goben ku ga juna zuwa wurin d'inkin sai a bari sai Next tomorrow d'in" d'an yamutsa
fuska yay yace Ok daga haka ya fara kokarin tashi ya tambayi shikenan Alhaji lawal d'in yace eh zai iya
tafiya yay masu sallama ya nufi hanyar fita................
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._

*ASM Bk2028*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.........Bin Khalid da ido Mahaifiyar shi tay har ya fuce fuskarta d'auke da d'an murmushi a ranta take
ayyana in ba don yarjejeniyar dake tsakanin shi da Mahaifin shi ba tasan ba yadda za'ai ya yarda da
wannan Auren had'in saidae ta wani 6angaren taji dad'in hakan don rashin Auren nashi na damun su
tana fatan kuma ya zama silar canzawar shi. Bayan Fatuu ta gama breakfast d'in gyara d'akin ta fara yi
yadikko na ta bari tace zatayi, sosae ta gyara su Mino duk sun tafi Makaranta tun kafin ta farka da sun
nuna basu zuwa yadikko ta ce in dae don Adda d'in tasu ne ta zo kenan Saboda a garin zata zauna a cikin
gidan Gonar Chairman shi kan shi yana zuwa Hutu da iyalan shi wani lokacin amman Khalid d'in ya fi su
zama a gidan, bayan sallar Azahar Fatuu tayi wanka ta shirya cikin riga da skirt na atampa da sukai mata
cif a jiki dama duk haka kayanta suke sai yan k'alilan d'in dogayen riguna, ganin ta shirya yasa Yadikko
matsa mata kan ta daure taje ta gaishe da su Ard'o da Yaya ba don ta so ba ta yafa mayafi mahad'in
kayan ta tafi, a nutse take tafiya ta shiga shashen Yaya lokacin da ta shiga ba kowa a filin wurin sai su
K'anwar Altine dake wanke wanke a gefe, kallonsu kawae tay ta wuce kaman daga sama taji sun sa
Dariya k'anwar Altine tace ma d'ayar mai suna zakiyya "Yar uwata ki bar wani yanga da ji da kai wai ke
zaki auri mai kud'i duk fa munsan kalan mijin da zaki Aura" Fatuu na jin hakan ta dakata don sai taji tana
son jin wani irin miji ne zata auran dama kuma da biyu suke Maganar shiyasa ma suke yi da hausa,
Zakiyyar tace "Bai kamata fa in rink'a yanga ba kuka yakamata in yi zan auri mashayi wanda har giya
yake sha ya shigo gari yana niyyar taka mutane da Mota" sosae k'anwar Altine ke dariya kafin tace
"dama iya hakan ya tsaya ai da sauki kin manta da d'ayan aika aikar da kowa yasan yana yi...." Da sauri
zakiyya tasa hannu ta rufe mata baki tana fad'in kada aji mutuwar sarki a bakin su, wata irin mutuwar
tsaye Fatuu tay mi take ji haka game da wanda zata aura, Mashayi kuma! Kuma miye d'ayan abunda
yake aikatawar, a hankali ta juya ta kallesu sai tik'ar dariya suke suna kashe wa, wani irin nauyi
k'afafunta sukae mata taji tamkar bata iya taka su ga jikinta tamkar ana zare mata laka take ji da k'yar ta
daure taci gaba da tafiya, lokacin da ta je kopar d'akin Yaya ji tay kaman ta koma kawae ganin takalma
tasan ba ita kadai bace da wasu mutanen kuma a halin da take ciki tsoron k'ara jin wani abun da zai iya
tarwatsa mata zuciya take sanin sun iya ya6a bak'ar Magana, shahada kawai tay ta cire takalmanta ta
shiga da yar sallama duk mutanen cikin d'akin suka d'ago suna kallonta hakan yasa ta sadda kanta duk
suna zaune a k'asa su hud'u sai Yaya d'in na zaune a bakin k'aramin gadon k'arfe idon ta akan Fatuu har
ta k'arasa gefenta ta tsaya, d'aya daga cikin Matan ta mik'e tana fad'in bari ta bata abun zama tasan yan
birni basu zama a k'asa, darduma ta shimfid'a mata Fatun ta hau ta zauna tay shiru kaman bazata ce
komae ba can ta d'aga ido a hankali ta gaishe da Yayar dake ta faman bin ta da ido, d'an ta6e baki tay
tace "Amarya Sai yanzu aka ga damar zuwa gaishe dani kenan" shiru bata ce mata komae ba innar su
Altine tay yar dariya tace "Yaya kin san Amaryar ta Manyan Mutane ce" d'an guntun murmushi yayar tay
tace "haka fa ai na manta mune ma Yakamata muje mu mik'a gaisuwa, an zo lafiya Amarsu?" K'asa k'asa
tace lafiya lou, innar su Altine tace "to muma bari mu mik'a gaisuwa ga Amaryar manya, ina wuni
Amarya an zo lafiya?" Kafin Fatuu ta bata amsa wata tace "aikuwa saidae mu d'in mu gaishe da itan
tunda Yaya ma da k'yar ta samu gaisuwar ballantane mu" ita dae Fatuu shiru tay masu can Yaya tace "sai
kuka ji abun arzik'i kwatsam abun farinciki, ai dashi Baffan naki har zai maki bakin ciki Allah ya baki miji
d'an Arziki muka dage kai da fata tunda da Arziki a garin wasu ai gara a naku a gidan ku ma, ko ba haka
ba?" Banza Fatun tay mata ita dama tasan duk zugar Su ce tasa Ard'o ya tursasa ma Baffanta kan
Maganar, tsam ta mik'e tace masu sai anjima Yayan na ba ta bari tasha ruwa ko don kar su je gidanta
suma ta basu, bata tanka ta ba ta yi wucewarta tana jiyo yadda su innarsu Altine ke dariya suna fad'in ai
kuwa dole a basu ruwa harda Naman kaji ma su da sukae ruwa sukae tsaki za'a auri mai Arziki, bayan
fitar ta wata mai suna Hasiya ta kya6e baki tace "Sai wani d'aure fuska take don a ga bata so" a harzuk'e
Yaya tace "aikuwa ko mutuwa zata yi sai an yi auren nan badae ita ga mara d'a'a ba bata ganin kowa da
gashi an d'aure mata wutsiya ta raina kowa dama nace sai nayi maganin ta ai shiyasa Ard'o na yin
Maganar Auren ta da d'an gidan chairman d'in na nace sai abun ya yuwu, inda lafiya lafiya ai wllh cikin
yaran ku zan sa wata ta Aure shi a k'yaleta to amman gwara ita ta aure shin yadda zata kwashi kashin ta
a hannu waye bai san rashin Mutuncin d'an gidan Chairman ba Mutumin dake taka kowa yadda ya ga
dama kinga daidai da ita kenan sai taje tayi mashi rashin kunyar da ta saba ma Mutane" kyalkyacewa da
dariya innar su Altine tay tace "ya kuwa sassa6a mata kaman ni wllh, wannan wa zai so yaron shi ya aure
shi banda shaye shaye ga lalata yaran Mutane yanzu ji bi yarinyar nan Danejo yadda ya d'irka mata ciki
hankalin shi kwance k'arshe kuma ya zubar mata tak'amar shi likita ne" Hasiya ta amshe "yo ai ba itace
farko ba mata kala kala yake kawo wa a gidan Gonar nan aka ce harda arna" haka suka cigaba da
tattauna mugun nufin su kan Auren Fatuu. Har wani duhu duhu take gani ta nufi sashen su lokacin da ta
shiga falon su Mino ne zaune suna cin Abinci hakan yasa ta wuce cikin uwar d'aki ba tare data tanka ma
kowa ba, Mino na kiranta ko jin ta bata yi ba, tana shiga ta haye saman gado can k'arshe tayi rubda ciki
tana numfashi da k'arfi da karfi tana zare ido waye wanda za'a aura mata? Da gaske mai shaye shaye ne?
Ita da a rayuwarta ta tsani mashayin mutum shine yanzu zai zama mijinta, shin miye d'ayar aika aikar da
taji su zakiyya sun fad'a? Tana haka Mino ta shigo ta zauna a bakin gado tana kallon Fatuu ganin tak'i ce
mata komae yasa a sanyaye tace "Adda Fatuu" shiru bata amsa mata ba bata kuma kalleta ba Mino ta
sake cewa "Adda Fatuu miya faru kin yi shiru?" Sai lokacin ta kai idonta kanta amman still ta kasa tanka
mata ganin hakan yasa ta mik'e ta fita bada jimawa ba sai gata sun dawo tare da Yadikko, a bakin gadon
ta zauna ta kai hannu ta ta6a jikin Fatun da harshen fulatanci ta shiga tambayarta lafiya Mike damunta
can ta yunk'ura ta tashi zaune idonta akan yadikko cikin karyayyar Murya tace "Don Allah waye za'a Aura
man??" Da mamaki yadikkon tace "dama Baffan ki bai fad'i maki wanda zaki Auran ba?" da sauri tace "Ya
fad'i man d'an Chairman ne amman ina son ki fad'a man wane irin Mutum ne?" Dam k'irjin yadikko ya
buga ta hau had'iye miyau ganin ta kafe ta da ido alamar jiran amsa take yasa tace "Mutum ne kamar
kowa kuma likita ne...." Katse ta Fatuu tay "ba wannan nike son sani ba wane irin hali gare shi?" Shiru
yadikkon tay tana kallon Fatun ganin haka yasa tasa mata kuka ta kama hannuwanta tana fad'in "ki fad'a
man yadikko don Allah da gaske Mashayi ne?" Zaro ido tay cikin rawar murya tace waye ya fad'a mata
hakan nan take ta kwashe firan da ta ji su zakiyya nayi ta fad'a mata, shiru bakin yadikko ya mutu don
bata san mi zata ce mata ba Fatun ta hau rok'onta kan ta fad'a mata, juyawa yadikko tay tace ma Mino
da ke yin hawaye ta fita ta ce to, bayan ta fita yadikko ta juya kan Fatuu ta kama hannuwanta tace "haka
ake cewa amman ni ban san ko gaske bane tunda ban ta6a gani da ido na ba na dae san shi tunda yana
yawan zama nan gidan Gonar bayan ya gamo karatun likitancin da yayi a K'asar waje..." Tun kan ta rufe
baki Fatuu ta tari numfashin ta "to bayan shi naji sun ce akwae wani abun da yake aikatawa miye?" Wani
abu Yadikko ta had'iya a ranta take raya taya zata ce mata yana neman Mata ko shaye shayen ta san da
gaske yana yi don kada ta tada mata hankali ne yasa ta nuna mata bata san ko gaske bane, ganin tayi
shiru yasa Fatuu d'an girgiza hannunta tace "Yadikko ta don Allah kar ki 6oye man ki fad'a man" sauke
ajiyar zuciya tay cikin rawar murya tace "k...kin gane w..wai ana zargin yana neman Mata ne a gidan
gonar da yake zama....." Zaro ido Fatuu tay a kidi'me tace "Neman Mata kuma kenan Mazinaci za'a Aura
man!!" ganin yadda ta rud'e yasa da sauri yadikkon tace "a'a fa kawae ana zargi ne wai ana ganin shi da
mata amman kuma ai zai iya yuwuwa Abokan aikin sa ne tunda ba wanda ya ta6a shiga ya kama su suna
aikata ba daidai ba kinsan irin Wannan baka saurin gasgata wa" girgiza kai Fatuu ta shiga yi cikin kuka
take fad'in "ai yadikko in dae aka cika Maganar abu to tabbas akwae alamar gaskiya, mi zai sa ya rink'a
zuwa da mata gidan gona in Abokan aikin nashi ne suyi aikin acan wurin aikin su mana, ni dae na bani na
lalace k'arshe na ya zo za'a lalata man rayuwa taya zan yi rayuwar Aure da Mashayi kuma Mai neman
mata, Ya akai Baffana ya amince a jefa man rayuwa cikin had'ari yadikko ya akai kuka amince bacin kun
san halin shi haka yake so kuke ya lalata man rayuwa ne??" Itama Yadikkon kukan ta sa tana fad'in "a'a
Fatuu kar ki ce haka Don Allah kin fi kowa sanin yadda muke son ki muka damu da rayuwar ki hakan ne
ma yasa lokacin da Ard'o ya sanar da zancen Auren naki Baffan ki ya shiga mawuyacin hali har yay
sanadin kwanciyar shi ciwo duk Saboda jin Mutumin da za'a aura maki k'arshe dae har zuwa yay wurin
Chairman ya rok'e shi kan a hak'ura da had'a ku Aure koda ya tambaye shi dalili bai 6oye mashi komae
ba game da halin yaron nashi da ake fad'a kuma ya nuna mashi ke karatun likita kike son yi anan ya nuna
mashi ya kwantar da hankalin shi in dae wannan ne damuwar shi to saida ya tabbatar da d'an nashi ya
shiryu ya daina komae sannan kuma har yarjejeniya sukae kan ko bayan auren ya kama shi yana aikata
wani abu ba daidai ba sai ya sa6a mashi don dama a bisa sharad'i ya nema masa auren kuma ya tabbatar
ma Baffan ki cewa da kunyi auren zaki cigaba da karatun ki don ya fahimci kina da kokari sosae tun
lokacin da ya fara ganin ki tun sannan yaji kin burgeshi har yayi sha'awar D'an nashi ya aure ki, wannan
ne dalilin da ya sa har Baffan ki ya gamsu sanin chairman d'in Mutumin Arzik'i ne ba zai ta6a had'a
aurenku don son zuciya ba" shanye kukan Fatuu tay sai taji hankalin ta ya d'an kwanta ganin haka yasa
Yadikko cigaba da lallashin ta tana k'ara kwantar mata da hankali had'i da nuna mata wani abun da biyu
suka fad'a dama don su tada mata hankali su k'untata mata, ganin ta d'an samu natsuwa yasa ta d'agota
ta tambayeta taje ta gaida Ard'o ta girgiza mata kai alamar a'a ta ce to ta daure taje in Baffanta ya dawo
yaji bata je ba bazai ji dad'i ba a sanyaye tace to ta sauka daga saman gadon ta fita idon yadikko akan ta
cike da tausayi take kallonta tana d'an girgiza kai. Koda taje iske shi tay da Mutane hakan yasa ba yabo
ba fallasa ta gaishe su ta juyo ta dawo ta koma kan gado tay lamo. Sai bayan Magrib Baffanta ya shigo
d'akin lokacin duk sun gama salla suka gaishe shi da fara'a ya amsa kafin ya zauna a nan yake sanar da
yadikko game da zuwan wanda Fatun zata Aura gobe in Allah ya kaimu da yamma ta amsa da to ya nuna
mata k'atuwar ledan da ya shigo da ita yace ga cefane nan sannan a yanka kaza ayi amfani da ita wurin
shirya mashi Abinci ta amsa da to Fatuu dae tay tsit kanta a k'asa don wani irin bugu kirjinta ke mata jin
wanda aka ce zai zo d'in, ganin yanayin ta yasa Baffan tambayar ta lafiya ta d'ago da d'an murmushi tace
mashi lafiya lau daga baya ya fita, da daddare bayan ta kwanta duk kewar gwaggo ta dame ta don har
yanzu basu yi waya ba can ta d'auki wayarta ta kirata tana jin ta fara ringing ta tashi zaune har kiran ya
kusa katsewa bata yi picking ba har Fatun ta fidda ran zata d'auka sai gashi gab da zai tsinke ta d'aga tay
yar sallama wani kalan lumshe ido Fatuu tay da d'an murmushi ta gaidata gwaggon ta amsa mata suka
d'an yi shiru can gwaggon tace "anje lafiya, koda yake mun yi Magana da Kamalu yace kun isa lafiya"
Fatun ta amsa mata da lafiya lau daga haka tace mata ta kwanta sai da safe bata jira cewarta ba tay
cutting kiran, cire wayar tay daga kunnanta ta bita da ido kawae.

Washe gari tun bayan da ta gama gyara d'akunan da suka gama karin kumallo wanda bata wani ci sosai
ba ta yi wanka tasa doguwar riga ta haye gado, tana kwancen yadikko ta shigo ta zauna gefen gadon da
d'an murmushi tayi mata sannu a hankali Fatuu ta amsa mata da yauwa yadikkon tace "Dama shawara
nazo tambaya ku yan birni kun fi mu sanin kalolin Abinci masu dad'i wanne kike ganin ya kamata ay ma
bak'on naki" shiru Fatuu ta d'an yi sai kuma cikin sanyin murya tace "Yadikko kema ai kin san Abincin
masu dad'i ko" yar dariya tay tace "to ai duk na manta zuwa yanzu kuma ai nasan akwae wasu iri iri da ni
ban sani ba" kaman bazata ce komae ba ganin yadikkon na kallonta yasa tace "ba naji Baffa yace a yanka
kaza ba kawae ayi mashi pepper chicken ba sai anyi wahalar yi mashi wani Abinci na daban ba" shiru
yadikkon ta d'an yi alamar tunanin sai kuma tace "amman kina ganin shi kawae ya isa, kamar da Abincin
zai fi nike gani" d'an ta6e baki Fatuu tay tace "ai ba lalle fa yaci Abincin ba fa in aka yi wannan d'in sai a
had'a mashi da fura sai in ga ya isa" cike da gamsuwa yadikkon tace hakan yayi ta mik'e Fatun ma ta
yunk'ura zata tashi tace mata tay kwanciyar ta zasu yi komae dasu Mino daga haka ta fita, komawa tay
ta kwanta don duk jikinta a sake yake ga fargaba had'i da zullumi da suka mata yawa, Bayan sallar
Azahar Baffan ya dawo ya kawo Drinks masu sanyi yace ma yadikko tasa wanda za'a bashi cikin cooler
sauran sai su sha tayi mashi godiya, koda Fatuu tay salla komawa tay ta kwanta da aka mata Maganar
Abinci cewa tayi ba yanzu ba saida Yadikko ta matsa mata sannan ta d'an tsakura kad'an, ganin har k'arfe
ukku tana kwance yasa Yadikko ta shiga tayi mata Magana kan ta tashi ta shirya kar yazo kuma bata
kimtsa ba, zuru Fatuu tay mata har saida ta k'ara mamaita abunda tace Matan sannan tace ba sai ta
shirya ba ai tayi wanka d'azun,
"To ki tashi ki canza kaya ko" tsuke fuska tay idanunta har sun kawo ruwa ganin haka yasa yadikkon
fara rarrashin ta ta shiga nuna mata in tayi shigar kirki hakan zai sa ya mutunta ta amman in taje mashi a
yamutse zai iya raina ta, da k'yar ta tashi don ta shiryan, wanka tayo lokacin an fara kiran la'asar hakan
yasa ta d'auro Alwala saida tay salla sannan ta fara kokarin shiryawa tama rasa wane kaya zata saka can
dae ta fiddo wata straight gown ta Maroon lace da touch d'in golden ta saka ta sa yan kunnan zinarin ta
da yan hannu tana cikin shiryawa ta jiyo Muryar Kamalu a Parlor yana fad'in "Yadikko ga bak'on nan ya
iso" ta amsa mashi da to ta mik'e tana tambayar yana ina ne yace mata yana a Fadar Ard'o, shigowa tay
cikin uwar d'akan ta iske Fatuu zaune a gefen gado ta rafka tagumi itama ta zauna gefenta ta dafa
Shoulder d'inta tace "bak'on naki ya iso Fatuu" kallonta tay ta fara d'an ta6e baki alamar zata fara kuka
yadikko ta girgiza mata kai tace "Don Allah Fatuu ki yi hakuri ki fawwala ma Allah komae, shi mai ji ne
kuma mai gani yafi kowa sanin halin da kike ciki don haka ki dogara da shi na tabbatar zai baki mafita ya
za6a maki abunda yafi Alkhairi gare ki" d'aga mata kai tay ta kama hannunta ta mik'ar da ita, gaban
mirror ta kai ta tasa ta ta shafa powder har jan baki tace ta shafa amman ta k'i tasa lip glow kawae
yadikkon ta gyara mata d'aurin kallabin ta ya zauna sosae gashin ta dama ta lankwasa shi ya fito yay tum
a baya, golden brown gyale mahad'in kayan ta yafa haka takalma ma sosae tay kyau duk da ba wani
make up tay ba, tun da ta fito ta nufi hanyar soron k'irjinta ke bugu tamkar ana mata luguden ta6are
hakanan take jin tsananin fargaban zuwan ganin abun take kaman almara ba gaske ba wai wurin wanda
zata Aura nan da sati biyu zata je, da yar sallama ta shiga lokacin da ta k'arasa ko cire takalman
k'afafunta bata yi ba tun a bakin kopar kamshin turaren da ya baza a jikinshi ya d'aki hancinta, a d'arare
ta idasa shiga idonta a kan shi yana zaune akan kujerar da Ard'o ke zama ya sadda kanshi yana latsa
wayarshi yana sanye da shadda brown wanda ta hau da fatar jikin shi sosae anyi mashi irin fav d'inkin
Haisam wato senator style saidae basu amshe shi kaman yadda suke amsar jikin Haisam ba don yanayin
halittar jikin ba d'aya ba, bai sa hula ba hakan ya bayyanar da sumar shi dake a lallank'washe hannunshi
sanye da brown wrist watch, ba laifi shigan tay kyau kana ganin shi kaga wayayyan d'an boko, tsaye tayi
daga d'an can nesa bayan ta shigo tana kallon shi tana haka su Mino suka shigo da kayan Abinci suka nufi
gaban shi suka aje had'i da gaishe dashi kaman bazai amsa ba sai kuma yace "lafiya" ba tare da ya d'ago
ba balle su samu Arzik'in kallo suka juya suka fita, sun d'auki lokaci a haka sai da ya mula ya sha iska
sannan slowly ya d'ago ya sauke mayatattun idanunshi tamkar na mai jin bacci akan Fatuu dake tsaye a
gaban shi, kallo suka bi juna da shi tun bayan da ya d'ago Fatuu ke mashi kallon sani hakanan taji kaman
ta ta6a ganin shi to amman a ina? Shine abun da take son ta gano, wani irin jarababben kallo yake bin ta
dashi from head to toe tsam ya mik'e walking slowly toward her, a gabanta ya tsaya har saida Fatun tay
stepping back Saboda yadda ya k'ure mata, a hankali ta kai idanunta kan fuskar shi lokaci guda k'irjinta
yay wani irin bugu tuna inda ta ta6a sanin shi d'an buda ido tay sai kuma da sauri ta sadda kan ta kasa,

"Why am I having d feeling dat I know u somewhere??" taji husky voice d'in shi ta fad'a wato shima
ashe yaji ya santa wani wurin, K'in d'agowa tay gaban ta naci gaba da fad'uwa wani irin mugun tashi
hankalinta yay ganin shi matsayin Mutumin da zata aura, "Hey!" taji ya fad'a da d'an d'aga Murya a
hankali ta d'ago duk ta kame kanta sai zare ido take ya k'ara kankance idon shi yana kallon ta da alama
so yake ya tuna inda ya santa can bayan d'an lokaci kawae sai gani tay yay wani kalan murmushin
mamaki ya d'an kya6e baki kafin ya furta "Wonders Shall Never End, so u'r My Wife to be!!!" bin shi da
ido kawae take sai faman sakin Shu'umin Murmushi yake.........

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._

*ASM Bk2029*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.......Juyawa yay walking majestically ya koma inda ya ta so ya zauna idon shi a kanta,

"zaki ta tsayuwa ne?" Ya tambaya had'i da d'age mata gira wani kuka cikinta ya fara yi, kaman k'wai ya
fashe mata a ciki ta fara moving zuwa gefe inda wata kujerar take ta zauna tana cigaba da kallon shi,
"From all indications kema kin gane husband to be en naki ko?" wani wahalallan miyau ta had'iya bata
dae ce komae ba,
"I ave been wondering wata kucakar Dad ya sama man matsayin Mata a Wannan tsukukun k'auyen
ashe ba kucakar bace mara kunya ce mai zagin iyayen Mutane" still bata ce mashi komae ba yaci gaba
"But duk da haka am so happy Dad has made a right Choice for me, it's nice meeting you my lovely wife"
bakin Fatuu fa ya mutu murus ba kamar da ta ga irin murmushin da yake saki tasan ba har zuciya yake
fad'ar abubuwan da yake fad'i ba,

"Kin bi ni da ido ko baki farin ciki da ganin husband en naki bane shiyasa ko Welcoming dina bazaki ba
balle in sa ran za'a gaida ni, koda yake I know who my wife to be is ba lalle in ta iya gaida Mutane ba"
d'an motsa baki tay sai kuma ta sunnar da kai katsa yayin da a cikin ranta ta furta innalillahi Wa'inna
ilaihir raji'un, sam ta kasa bud'e baki tace wani abu don ba k'aramin Al'ajabi ne ya kamata ba, a hankali
ta saci kallon shi taga still kallon ta yake hakan yasa ta idasa dagowa cikin trembling voice tace "ina wuni
an zo lpy" d'an tafa hannu yay yace "Wow what a sweet voice, lafiya lou wife hope na same ki lpy?"
tabdijan ya gama kashe Fatuu da mamaki duk yadda tay zaton zai mata ba haka take gani ba ganin tayi
kasak'e tana bin shi da ido yasa ya d'age mata gira yace "Wife Kaman ke baki farin cikin gani na a
matsayin wanda aka za6a maki ba ko" murya a hard"e tace "a'a nayi" jinjina kai yay yace "To ya Katsina
fatan kin zo lafiya" tana d'an kikkafta ido tace mashi lafiya lau yaci gaba "dama ina ji ana cewa Katsina
akwae beautiful babes masu ilimi da wayewa yanzu na shaida haka even though ke d'in asalin yar nan ce
amman su suka maida man ke yadda nike son wife ena ta kasance" ya k'arasa yana wani juya
yaudararrun idanun sa, sunnar da kanta tay k'asa don Maganar tashi ba wanda ta tuno mata sai Haisam
Saboda shi ne ya maida ta yadda take,

"na fa san kina Magana so ki daina acting as if baki magana ko yana maki wuya, ki saki jiki ki kuma bud'a
baki ki man magana kaman ranar da kika zage ni" da sauri ta d'ago ta kalle shi ya bud'a mata ido d'an
yamutsa fuska tay cikin breaking voice tace "ni fa ba zagin ka nayi ba kuma Kaine ka fara zagi na ai"
Shegen murmushin shi ya saki yace "kika rama kuma ko, anyway ai baki ji nace kin yi laifi ba ya wuce
koma kin yi ai Amarya bata laifi if u wish yanzu ma zaki iya zagi na I won't feel offended" ya ilahi ya rabbil
alamen mutumin nan nema yake ya tarwatsa ma Fatuu zuciya, shiru suka d'an yi sai faman k'are mata
kallo yake can yace "Wife ina buk'atar ruwa or I should serve myself ?" a hankali ta juya ta kalleshi sai
kuma ta mik'e ta nufi gaban shi ta duk'a ta fara kokarin zuba mashi lemu hannunta har d'an rawa yake,
bayan ta zuba ta d'ago da niyyar bashi taga gaba d'aya hankalin shi na a wani wuri a jikinta hakan yasa ta
d'an d'ukar da idonta don taga abunda yake kallo ashe saman boobs d'inta da sukae fam fatar wurin fari
fat da ita ya kafe da ido yana kallo sakamakon wuyar rigar da yake a bud'e sosae, da sauri ta ja gyalen ta
rufe wurin hakan ya sa shi dawo wa cikin hayyacin shi ya kalleta da murmushi kafin ya kai hannu ya
amshi glass cup d'in had'i da furta "thanks my beautiful wife" mik'ewa tay ta koma ya bi bayanta da kallo
har ta zauna sannan ya kai cup d'in baki ya fara sipping lemun saida yasha kaman rabi sannan ya ajiye ya
kalleta ta d'ukar da kanta tana d'an wasa da yatsunta taji ya d'an yi gyaran murya hakan yasa ta kalle shi
yace "Wife miye labari" d'an watsa hannu tay tace "babu" yace "What about preparations na bikin mu?"
Kaman bazata ce komae ba sai kuma tace "ana yi" gyara zama ya d'an yi yace "Ok dame dame zaku yi
ne?" tace "ba komae" d'an buda ido yay alamar mamaki yace "Haka zaku yi bikin ba wasu programs
kaman zaki auri enermy en ki" ido kawae take bin shi da shi yaci gaba "koda yake baki da Friends anan
ko?" Kai kawae ta d'aga mashi ya jinjina nashi,

"To yanzu kaman nawa kike buk'ata na abunda kike ganin zaki yi like gyaran jiki and so on" ya tambaya,
tace "zanyi ba sai ka bani ba" yar dariya yay ya d'an shafi sumar shi yace "Ashe wife en nawa Hajiya ce"
shiru bata ce komae gaba d'aya sai taji ta k'agara ma ya tafi kota koma ciki don gaba d'aya kanta a d'aure
yake bata da natsuwa,

"Gobe sister d'ina zata zo zaku je wurin tailor zai taking measurement naki sai ki shirya" kallon cikin ido
tay mashi yace "let me have ur digits so dat lokacin da zasu zo sai in sanar maki" karanto mashi phone
number d'in ta tay bayan ta gama ya kira jin wayan na ringing ba anan ba yasashi tambayar inda wayan
take tace tana cikin gida yace to in ta koma sai tay Saving harda fad'i mata sunan shi Khalid ya tambayi
nata tace mashi Fateema yana murmushi ya furta "Fatima Zaraah" har saida kirjinta ya buga damm,
ganin yana kokarin mik'ewa yasa tace bai ci Abincin ba yana wani kashe mata ido yace he's Ok bai jima
da ya ci Abincin ba but next time in ya zo zai ci daga haka ya mik'e itama tana ganin hakan ta mik'e ya
nufo in da take ya tsaya suna facing juna ya kafeta da mayaudaran idanunshi seductively ya furta "Hope
ban yi laifi ba da ban ci ba kar next time a ki dafa man don nasan girkin ki must ba as hot as u'r" wani
dam dam k'irjin ta ke yi ganin yadda yake mata Magana ba zato ba tsammani sai ji tay ya kawo hannu ya
janyota ya had'e jikinsu a gigice ta shiga kiciniyar kwace jikinta saidae ta kasa a rud'e tace "Don Allah ka
sake ni kar wani ya shigo fa ayi tunanin wani abu nike yi" gaba d'aya ya zuba ma lips d'inta ido yadda tay
Maganar ba k'aramin tafiya tay da shi ba kokarin had'a face d'in su yake a kidi'me Fatuu ta tattara duk
k'arfinta ta tura shi tay baya ta fad'a kan kujerar da ta tashi, wata yar iskar dariya ya saki yace "Wife zaki
ji ma kan ki ciwo fa and miye abun rud'ewa haka kaman na aikata wani abu ba daidai ba, ko basu yi
informing naki an biya sadakin ki bane?" Kasa cewa tay komae sai numfashi take fitarwa da sauri da
sauri duk ya gama tsorata ta, still dariyar yake yace "I forgot wife en tawa Secondary graduate ce but at
least be romantic Babe" daga haka yasa hannu a cikin Aljihun rigarshi ya fiddo rafar yan dubu dubu guda
biyu ya d'aura mata akan cinyarta kafin ya sake sa hannu a aljihun ya fiddo farin glass ya sa a fuskar shi
yana murmushi yace sai sun sake had'uwa daga haka ya fice, Mutuwar zaune Fatuu tay tama rasa
tunanin da zata yi akan shi da k'yar ta iya yunk'ura wa ta mik'e jikinta har lokacin rawa yake ta nufi cikin
gidan a kan hanya ta had'u da Mino tace mata taje ta kwaso kayan abincin da suka kai tace to, a Falo ta
iske yadikko zaune tana ganinta tay mata Murmushi tace har ya tafi ta d'aga mata kai kafin ta wuce cikin
d'aki tana shiga ta cillar da takalmanta ta cire gyalen shima ta wurgar ta haye gadon sai zare ido take
tunani kala kala acikin ranta ba kamar akan had'a jikinsu da yay hakan yasa ta fara shakkun anya ba
gaskiya bane yana neman mata in ba haka ba mi zai sa daga fara haduwar su yau ya had'a jikinsu bama
wannan ba kadae har fa kusan had'a bakunan su yay ba don ta samu ta fizge ba, wata zuciyar kuma ta
ayyana mata ai yace don an biya sadakin ta ne to amman ai ba'a d'aura masu aure ba ko, gashi sam ta
kasa yadda da yanda ya sake mata sai take ganin kamar akwae dalilin hakan, tana ta zancen zuci har
Yadikko ta shigo bata sani ba saida ta zauna ta kira sunanta sannan ta kai idanunta kan ta, tambayarta
tay lafiya dai ko taga ta shigo ta kwanta ko wani abun ya faru ne ta k'ak'alo murmushin yak'e tace mata
a'a lafiya lou,

"To Allah yasa dae kun fahimci juna yayi maki kuma" d'an ta6e baki Fatuu tay a sanyaye tace "koma bai
man ba yadikko ya zanyi dole ai in Aure shi ko" shiru tay tana kallonta gaba d'aya tausayinta take ji don
daga yanayin ta sai taga kaman bai mata ba, tambayarta tay ya akai taga bai ci komae ba Fatun tace
"Yace ya k'oshi sai ya sake dawowa zai ci" jinjina kai tay tace mata to ta taso suje ta ci farko taso ta k'i
tace ta k'oshi saida Yadikkon ta matsa mata sannan ta saukko lokacin ta nuna mata kud'in da ya batan na
abubuwan da zata yi tace to ta ruk'e a wurinta. Da daddare tana cikin yin shirin kwanciya sai ga kira ya
shigo wayarta koda ta duba bata gane mai kiran ba hakan yasa tak'i d'agawa taci gaba da abunda take
sai gashi an sake kiran, zama tay bakin gado ta d'aga ba tare da ta ce komae ba on the other hand taji
ance "Wife ko kin yi bacci ne" rass gabanta ya buga jin muryarshi sai lokacin ta tuna da d'azun ta bashi
no dinta har ya kira yace tay Saving, sake maimaita tambayar da yayi mata yay sai lokacin tace mashi a'a
yanzu zata kwanta,

"Gani na kasa bacci Saboda tunanin ki wannan shi ake kira da luv at first sight all I need in ji ki gefe na
hope kema hakan?" shiru tay mashi har saida ya k'ara tambayar tata sannan ta tura baki tace "a'a" tana
jiyo sautin dariyar shi yace "Don't worry Babe zan koya maki yadda kema zaki rink'a jin hakan game da
ni" shirun dae ta k'ara ita duk ta fara tsorata ma da shi haka ya dingi yi mata kalaman soyayya harda
tambayarta wace tarba zata mashi a first night d'in su ita dae a tak'aice take bashi amsa wani wurin
kuma ta mashi shiru jin shiru shirun nata yay yawa yasa shi tambayar ko ta fara jin bacci ne tace mashi
eh yace bari ya barta ta kwanta harda cewa tayi bacci mai dad'i kuma tayi mafarkin shi shima zai yi nata
ita dae shiru tay mashi tana niyyar cire wayar taji sautin wani matsiyacin kiss da yay mata har cikin
dodon kunnanta da sauri ta cire wayar ta k'ura ma screen d'in ido kirjinta na beating very fast can ta
runtse idanunta sai ga kwalla sun fara zubowa ba kowa ne ya fad'o mata a rai ba face Ya Haisam ji take
inama shine yake nuna mata so haka ba wannan ba da take tunanin duk k'arya ne da biyu yake mata
hakan ba don yana sonta tsakani da Allah ba, tana ta tunane tunanenta har bacci yay awon gaba da ita,

Washe gari bayan sun kammala yin breakfast ta gyara d'akin sai ga kiran shi wai ya kira ya ji ya ta tashi
tace mashi lpy Lou anan yake sanar da ita ta shirya around 1:00 za'a zo atafi da ita ta amsa da to, lokacin
ta sanar ma yadikko ita kuma ta kira Baffanta a waya ta gaya mashi yace to ta dawo lafiya ta so ace Mino
ta dawo daga Makaranta ta rakata, wurin karfe d'aya saura tana cikin shiryawa yadikko ta shigo cikin
d'akin ta sanar da ita game da zuwan wadda tazo tafiya da ita wato Sadeeya tace to, doguwar rigar
shadda sabowa dal acikin irin kayan da Haisam yayi mata Navy blue tasha aiki blue da fari yayi kyau
sosae ta sa yan kunne da sark'a sai Agogo duk silver sai farin mayafi haka takalma ma high heels ne
farare ta d'auki yar clutch dark blue, a saman kujera Sadeeya ta zauna ita da wata yarinya da zata yi
shekara bakwae da suka zo tare tana sanye da jeans da t-shirt kanta sanye da hula da bayanta ya d'an yi
tudu alamar gashin ta a fake yake, itama Sadeeyar a shekaru zata yi shekara 25 zuwa 26 itace k'anwar
Khalid ta biyu, ta farkon wato Yayar Sadeeyar tayi Aure, a ABU Zaria Sadeeya ke karatu itama fara ce
saidae bata kai Khalid haske ba sannan ita da Chairman take kama duk da ta wani 6angaren ta d'an yi
yanayi da Khalid d'in tana da d'an jiki ba kamar khalid ba, sanye take da doguwar rigar atampa d'inkin
Abuja Boubou ta kashe daurin kallabi hakan ya bayyanar da wutsiyoyin kitson dake kanta da ta tubke, da
fara'a lokacin da yadikko ta fito ta sanar mata Fatun na fitowa tana k'arasa shiryawa ne itama tana
fara'ar tace Ok ba damuwa, ruwa da Abinci yadikko ta kawo masu Sadeeyar na cikin shan ruwan Fatuu ta
fito ba shiri ta cire cup din daga bakinta ta bi ta da kallo wanda ke bayyanar da mamaki akan fuskarta,
sam bata taba tsammani ganin ta hakan ba duk da ta samu labarin ba anan take ba batai tunanin ganinta
a waye haka ba ba kuma kaman da taji Secondary graduate ce, kujerar dake gefen su Fatuu ta nufa ta
zauna fuska a d'an sake ta gaishe da Sadeeyar da sauri tace "Ah Auntyn mu ni ai yakamata in yi wannan"
tay Maganar tana ma Fatuu dariya ita dae d'an murmushi kawae tay kafin tace sun zo lafiya Sadeeya ta
amsa mata da lafiya lau, shiru sukae Fatuu ta lura da kallon da take mata hakan yasa ta d'an juyar da
kanta gefe, can Sadeeyar tace "Auntynah if u done we can go driver is waiting for us outside" juyowa
Fatuu tay ta kalleta sai kuma ta kalli Abincin gaban su a nutse tace "But u aven't ate d Food" d'an lumshe
ido Sadeeya tay kafin tace "bamu jin yunwa ne amman tunda kin yi Magana bari mu d'an ci" tana niyyar
tashi don ta zuba masu Sadeeyar tace mata ta bashshi bari ta zuba masu yarinyar da suka zo tare sai
kallon Fatun take can ta d'an duk'a saitin fuskar Sadeeya tace "Aunty Sady who is she?" d'agowa tay tana
yar dariya tace "she's ur New Aunty Ya Khalid's bride" waro ido yarinyar tay Sadyn tace taje ta gaida ta ta
nufi Fatun tana zuwa ta tsaya gabanta ta gaishe ta da turanci Fatun ta amsa mata ta tambayi sunanta
tace mata Basma, ba wani mai yawa Sady ta ci ba ita basma ma bata ci ba suka tashi don tafiya Yadikko
tace ma Fatuu ta biya dasu su gaisa da Yaya ba don ta so ba ta amsa mata da to kawae itama Yadikkon
gudun tsegumi yasa tace su je don zai iya zama abun Magana, kaman ko yaushe tana zaune da yan taya
ta gulma su ukku lokacin da suka shiga cikin d'akin Yaya na d'aura idonta kan Sadeeya ta gane yar gidan
Chairman ce hakan yasa ta nuna mata gefen gado tace ta zo ta zauna ita dae Fatuu tsaye tay Sadeeya ta
shiga gaishe dasu da fara'a suka amsa suna ma Basma wasa, Yaya ce ta tambayi Sadeeya daga gidan
Chairman ko tace mata eh sun zo zasu tafi da Amarya ne za'ai mata awon d'inki ta jinjina kai alamar
gamsuwa daga baya ta mik'e tay masu sallama suka fita ba tare da Fatuu tace ma kowa komai ba, bayan
fitar su Yaya ta ta6e baki had'i da yamutsa fuska cikin harshen fulatanci tace "Yi ma yarinyar can aure ba
k'aramin rufa mata Asiri akai ba don Allah kadae yasan abunda take aikatawa a can, kuji irin yadda take
saka sutura kai kace itace d'iyar Chairman d'in ma a ina ita kakar ta ta taga kud'in da zata rinka d'inka
mata suturun da da gani masu tsada ne" Hasiya ta kar6e "ai fa dama da gani idonta a bud'e yake wllh"
Yayar tace "kin ga an za6a mata miji daidai da ita kenan" haka suka cigaba da yi ma Fatun kazafi, suna
fita kopar gida Driver ya fito ya bud'e ma Fatuu kopa bayan ya gaidata ta amsa mashi a sake Sadeeya ta
zagaya d'ayar kopar ta shiga Basma kuma ta shige gaba, Tafiyar kamar Minti 35 ta kawo su a bakin k'aton
gate d'in gidan Driver yay horn mai gadi ya lek'o kafin ya koma ya bud'e masu ya shigar da Motar, bayan
sun fito da murmushi Sadeeya tay ma Fatuu jagora zuwa cikin gidan lokacin da suka shiga Main Parlor
d'in gidan ba kowa hakan yasa tace ma Fatuu su je cika ta nufi wata babbar kopa suna shiga wani
madaidaicin Parlor ne da bai kai na farkon ba, zaune akan sofa 3 seater Hajiya Rabi'atu ce jikinta sanye
da doguwar rigar Atamfa a gefenta kuma wata mata ce itama tana sanye da doguwar rigar shadda
kafad'arta d'aya rataye da gyale da gani bak'uwa ce tayi, suna shigowa duk suka kalle su da sauri
Sadeeya ta d'aga gyale ta rufe saitin Fatuu tana dariya tace "Mom sai kin biya zaki ga face en bride d'in
mu" tana rufe baki Basma ta ruga ta fad'a saman jikin Mom d'in nasu tana dariya tace "Mom she's very
beautiful" d'an buda ido Mom d'in nasu tayi sai kuma ta d'aga basmar ta mik'e tana dariya ta nufi
Sadeeya tana zuwa tasa hannu ta d'an tureta gefe tana fad'in sai ta ja mata rai zata bari taga Daughter
d'in ta gaba d'aya harda k'awar tata sukae dariya, had'a ido sukai da Fatuu bayan ta janye Sadeeyar ta bi
ta da kallo hakan yasa Fatuu ta sadda kan ta k'asa, tana sakin kayataccen murmushi tace "U'r highly
welcome My Beautiful Daughter nayi matuk'ar farin cikin ganin ki" a hankali Fatuu ta d'ago ta kalleta a
sanyaye ta gaishe da ita tana ta fara'a tace su je ta zauna sai su gaisa sosae tay patting shoulder d'inta
suka wuce, kan one seater ta Zaunar da ita kafin ta koma inda ta taso itama ta zauna k'awar tata tace "in
ce Amaryar Khalid d'in ce" ta amsa mata da itace tace "Ma sha Allah kyakkyawa da ita Allah yasa Alkhairi
ya kaimu Ranar" duk suka amsa da Amin idon Momy akanta tana ta mata murmushi ita dae Fatuu sai
faman sussunar da kai k'asa take, "Daughter fatan an zo lafiya" ta tambayi Fatun a hankali tace mata lpy
lau ta k'ara cewa "Ya Grandma d'in taki ance a wurinta kike zaune" wani iri Fatuu taji jin an ambaci
gwaggo kafin ta d'an kalleta tace tana lafiya, "Ya karatun ki ai kin gama ko" kai Fatuu ta d'aga tace eh,

"Mom ya kika ga Amaryar Ya Khalid?" Sadeeya ta tambaya Yar dariya tay ta furta "Tubarkallah
Daughter d'in nawa, sai fatan Allah ya kaimu ya basu zaman lafiya da fahimtar juna" duk aka amsa da
Amin, kallon Sady tay tace taje tasa a shirya table ta amsa da Owk ta mik'e ta fita suka cigaba da hira da
bak'uwar tata sai dae akai akai take juyawa ta kalli Fatun da murmushi wani lokacin su had'a ido, bayan
Sady ta dawo ta sanar da Momy an shirya tace to suje da ita taci Abinci Fatuu tace ta k'oshi amman tace
dole ta ci ai nan gidan su ne yanzu ta mik'e suka fita da Sadeeya, bayan fitar su k'awar tata ta kalleta
tace "a ina take ne?" Momy ta bata amsa da a Kt take zaune tace "University ta gama ne naji kina ta
gama karatu?" d'an girgiza kai tay tace "No, I mean Secondary school" jinjina kai tay tace "yanzu nan
Secondary graduate ce haka wayayya da ita kai kace yar Jami'a ce" Momy ta amshe "Wllh Hajiya Safeena
nima cikin raina saida nayi mamakin ganin ta haka don I never thought zan ganta haka duk da nasan ba a
k'auyen take ba har na fara tunanin akwae abubuwan da yakamata a k'ara zubawa acikin lefenta" Dariya
Hajiya Safeena tasa tace "to da ba'a sa na kirki bane komi?" Itama Momy dariyar take tace"Ah ba laifi an
sa kaya masu kyau to saidae ganin dressing d'in jikinta yanzu gaskiya we need to add wasu kayan taje tay
ta d'aukar wanka tana kashe mijinta da gayu" gaba d'aya sukae dariya ta k'ara cewa "Yarinyar ta burge ni
sosae wllh yanzu na fahimci dalilin da yasa Yalla6ai shima ta kwanta mashi a rai har yay sha'awar had'a
auren na su gashi yace tana da kokari sosae" cigaba da yabon Fatun sukae daga baya Hajiya Safeena ta
tafi, sai da akai la'asar sannan Driver ya sake d'aukar su ya tafi dasu shagon d'inkin bayan sun gama
komae duk a tunanin Fatuu za'a wuce da ita gida ne amman sai suka koma gidansu Sadeeyar lokacin
Magrib ta gabato, bayan sunyi salla gaba d'aya a Main Parlor suka zauna Sadeeya da Basma wadda itace
auta sai Haidar wanda Basma ke bi mawa, Fatuu duk ta k'agara ta bar gidan suna zaune Momy ta fito da
murmushi ta zauna tana facing Fatuu tace "Daughter kin k'i sakin jiki dae kuma nan d'in gidan ku ne so
just feel at home" d'an murmushi kawae tay bata ce komae ba suna haka sai ga Khalid ya shigo da yar
guntuwar sallama, damm kirjin Fatuu ya buga da suka had'a ido da sauri ta sunkuyar da kanta k'asa yana
sanye da Jeans da T-shirt kujerar da Fatun ke zaune ya nufa ya zauna kan hannun kujerar yana bin ta da
kallo a hankali ta d'ago ta kalle shi suka had'a ido ta gaida shi yana sakin murmushi ya amsa mata ta
maida kan k'asa suma su Momyn duk murmushin suke sosae taji dad'in yadda Khalid d'in ya nuna ta yi
mashi tun jiya da ya dawo shima Chairman yaji dad'in hakan don suna tare bayan ya dawon ya fad'a
masu, kallon Momyn tashi yay yace "Mom how do you see My Wife?" Yar dariya tay tace "the Match
was absolutely perfect" hannu ya kai ya shafi Beard d'insa yana cigaba da yin murmushi ya k'ara juyawa
ya kalli Fatuu ganin kaman bata saki jiki ba ya kalli Mom d'in nashi yace sun ma yi fira kuwa tana
murmushi tace "ai ta k'i sakin jiki tana ta bak'unta" d'an ta6e baki yay yace "kuma tana Magana Kaman
parrot fa" da sauri Fatuu ta d'ago kai ta kalleshi ya d'age mata gira Momy tace "Ashe mu ne ba'a son yin
firan da mu" Khalid yace "No nima bata saki jiki da ni ba jiyan ina Maganar can baya ne" da d'an alamun
mamaki Momy tace "Kenan dama ka santa" yace "Yes we once met a rugan su" kallon shi kawae Fatuu
ke yi tana zare ido gabanta na fad'uwa tsoron ta kar ya ce ta zage ta ya lura da yadda ta d'an razana
hakan yasa Ya rink'a sakin wani shu'umin murmushi sai dae bai k'ara cewa komae ba can ya kalli Sady
yace "Ya preparation na biki, ita tace bazata yi komae ba cos bata da Friends anan" da sauri Sady tace
"dat's not a problem ai tunda akwae Family and Friends d'in mu" tambayarta yay mi zasu yi tace zasu yi
Kamu da Bridal shower Momy ma zata yi Walima yace lafiya lou duk abunda ake buk'ata tay mashi
Magana tana murmushi tace "Ok bro" kokarin tashi ya fara yi Momy ta tambayi inda zashi yace zai je
sallar Isha ne tace to in ya gama yazo sai ya maida ta tana jira su gaisa da Daddyn su ne shiyasa bata sa
an maidata ba yace ai yayi zaton zata kwana ne har saida Fatuu tay mashi wani kallo Momy na dariya
tace so yake a biyo sawunta tunda ba'a ce zata kwana ba, Bayan gama sallar Isha d'in Chairman ya dawo
Momy ta kai Fatun falon shi don su gaisa cike da farin ciki ya amsa gaisuwarta yay mata an zo lafiya, tana
a falon Khalid ya dawo ya zauna nan Daddyn ya yi masu nasiha ya nuna yaji dad'in yadda suka kar6i juna
had'i da yi masu Addu'oi ita dae Fatuu kanta na a k'asa ta rasa mi yake mata dad'i komai ganin shi take
tamkar mafarki ba gaske ba, bayan ya gama Momy tace ma Khalid suje dare na k'ara yi yace Ok had'i da
mik'ewa Dad d'in nace mashi ya kula sosae yana dariya ya d'aga mashi hannu alamar Ok, tare da Momy
dasu Sadeeya aka rakota harda ledar turarurruka dasu Humra aka bata tay godiya, ji take kaman tace
bata son ya kai ta saidae ba yadda ta iya haka ta bud'e front seat ta shiga Sady ta rufe mata kopar tana
ce mata sai tazo kaita gyaran jiki suna daga mata hannu ya ja Motar suka tafi...................

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._

*ASM Bk2030*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

..........Tun da suka hau hanya ba wanda ya tanka ma wani Fatuu ta juyar da kanta tana kallon gefe yayin
da Khalid ke driving sai dae a akai akai yake d'an juyowa ya kalli Fatun, hannu ya kai ya kunna music ya
rage volume sosae kidan na tashi kad'an kad'an, har lokacin kuma bata kalleshi ba can ya juya ya kai
hannu ya kamo hannunta da ta d'aura akan lap d'inta a firgice ta juyo ta kalleshi duk da dare ne tana
d'an ganin fuskar shi sakamakon hasken fitilun wasu Motocin dake wucewa, ganin murmushin da yake
saki yasa ta tamke fuska ta fizge hannun nata ta k'ara juyar da fuskarta, bai tanka mata ba ya kai hannu
yana kokarin bud'e glove box jin k'arar bud'ewa yasa ta d'an juyo tana kallon abunda yake wani abu ya
fiddo ya maida wurin ya rufe saidae bata gane mi ya d'aukko ba hakan yasa ta sake juyawa, wani d'an
babban kwali ya fiddo sam nima na kasa gane na miye har saida ya bud'e yasa baki ya ciro cigarette
guda, ashe kwalin sigari ne saidae ina tunanin ba irin tamu bace ta nan daga yanayin kwalin da kuma
yanayin shi kan shi karan sigarin, amfani yay da lighter dake a cikin kwalin ya kunna kafin ya mayar da
kwalin ya fara sha idon shi a kan hanya, a hankali warin ta ya fara kaima hancin Fatuu ziyara can ta juyo
kaman an zabure ta lokacin da ta tabbatar daga cikin Motar warin yake, a razane take kallon Khalid dake
smoking hankalin shi kwance idon shi akan hanya, wani irin bugu kirjin Fatuu ke yi gaba d'aya hankalin ta
ya tashi nan take ta fara gasgata zancen su Zakiyya na yana shaye shaye, duk kallon da take mashi yana
gani ta wutsiyar idon shi can ya d'an juya yana murmushi yace "kin k'i man hira as if am alone in d car
dat's why na fiddo abunda zai taya ni hiran" sam ta kasa ce mashi komai bin shi da ido kawae take,
cigaba da driving yay yana shan abun shi cike da k'warewa wasu kwalla masu zafi ne suka ciko a
idanunta a rayuwarta ta tsani ta ga mutum na shan sigari ko warin ta ma bata so don ma wannan bata
k'auri sosae amman duk da haka har zuciyarta ta fara tashi hakan yasa ta juya da sauri tasa gefen
gyalenta ta toshe hancinta da bakinta lokacin kuma ta samu damar fara zubda kwallan da suka taran
mata, Har suka k'araso bata sani ba jin ya tsaya yasa ta d'ago da sauri tana kallon wurin da k'yar ta gane
inda ya parker wato a farkon gidan bai je kopar gidan ba daga inda suke tana hango inda teburin Kamalu
na rake yake da sauran Mutane dake zaune a kofar gidan harda yara dake wasa, da sauri ta kai hannu
zata bud'e ta fita hakanan taji bata yarda da inda yay parking d'in ba aikuwa kafin ta bud'en taji carabb
ya kamo hannun ta a fusace ta juya ta kalleshi tace ya sakar mata hannu ta tafi, shiru kaman bazai tanka
mata ba tana ta kiciniyar kwacewa ta kasa don ba k'aramin ruko yay ma hannun nata ba ganin bata iya
fizge hannun yasa ta fara mashi magiya kan ya kyaleta cikin kararrar murya, d'an murmushi mai sauti yay
kafin yace "Wife why ain't u romantic at all? ko ni driver d'in ki ne ya kamata ki fita kawae ba tare da kin
man godiya ba..." Tun kafin ya k'arasa da sauri tace "To Nagode" yar dariya yay ganin duk ta rud'e yace
"ni ai ba driver en bane I just give u an example ba wai godiyar nike so ba at least a single kiss da zai
nuna u'r grateful" waro ido tay ya wani lumshe mata ido yana pointing lips d'in shi da sam basu yi kalan
na masu shaye shaye ba da yake yana kula da hakan sosae, da sauri ta girgiza mashi kai alamar bazata yi
ba sai kace ba yanzu a gabanta ya gama shan sigari ba ai koma bai sha ba bazata yi ba tunda tasan ba
kyau, kokarin janyo ta ya fara yi ta toge hakan yasa ya d'an matso gab da ita kiciniyar kwace hannunta
taci gaba da yi tana cikin hakan ba zato ba tsammani sai jin d'ayan hannunshi tay Saman boobs d'inta
wata kalan gigicewa tay don abu ne da ba wanda ya ta6a mata hakan koda kuwa yar uwarta mace to
mima zai kai hannun wata ko wani kan chest d'inta ita da ba yar iska ba, ganin gaba d'aya hankalin ta ya
koma kan cire hannun na shi yasa ya shammace ta ya saki hannunta d'aya ruk'e ya kai hannun nashi ya
tallabo kan ta ya had'e fuskokin su tana bud'e baki da niyyar yin Magana kuma ya had'e lips d'in su, iya
k'ok'ari Fatuu tayi na ta janye bakinta abun ya gagara sai gunji take tana gurnani had'i da bugun shi saida
yay sucking up duk wani saliva na bakinta sannan ya saki kan nata ya maida nashi jikin headrest
breathing rapidly, a gigice ta bud'e Motar ta fice ta duk'e anan kan kace mi ta fara Kwara amai kaman
yan cikinta zasu fito tana ji ya ja Motar ya tafi bayan ya tillo mata ledar turarurrukan ta, saida ta amayar
da komae na cikinta a wurin kafin tasa wani irin kuka mai cin rai wannan wane irin bala'e ne a yanzu kam
ta gasgata zancen su zakiyya gaba d'aya in ba d'an iska bane mi zai sa yayi mata hakan, da kanta ta
rarrashi kanta ta mik'e kaman bazata d'auki ledan ba sai kuma ta d'auka kallabinta a kwance tana tafiya
tana goge kwallan da suka k'i daina zubowa had'i da tofar da yawu sai sheshsheka take wani iri take jinta
duk ba k'arfi a jikinta, har ta shige ba wanda ya lura da ita lokacin da ta shiga falo su Yadikko duk suna
zaune dasu Mino da k'yar ta k'ak'alo d'an murmushin dole tayi masu sannu su Mino na mata sannu da
zuwa cikin wasa Yadikko tace ai tayi zaton a can zata kwana bata ce komae ba ta wuce cikin d'akin tana
shiga ta cire gyalen ta don duk kyankyamin shi take don sai take jin k'aurin sigarin da ya sha a jikin shi,
aje ledar hannunta tay ta wuce band'aki don yin wanka, bayan ta fito ta shirya cikin doguwar rigar bacci
da ta wuce gwuiwar ta ta haye gado zuciyarta nata tariyo mata abunda ya faru duk sai take ji ta
tsangwami kanta ba kamar bakin ta ji take kaman ta cuzge shi duk kuwa da irin dirzar da ta yi mashi a
bathroom, tana kwancen Yadikko ta shigo dama ta shigo d'azun ta taras tana wanka a bakin gadon ta
zauna da d'an murmushi tace "an dawo lafiya?" a hankali tace mata lafiya lou, shiru ta d'an yi sai kuma
ta k'ara cewa "Ya yan gidan nasu sun yi maraba da ke kuwa?" Kai ta d'aga mata kafin tace Momynsu na
gaidata da fara'a tace tana amsawa Fatun ta lumshe idanunta jin kwalla na niyyar zubo mata yadikko ta
bita da kallo can tace "Ya akai ne na gan ki duk wani iri ga idon ki kaman kin yi kuka ko dae kin 6oye man
wani abu" bud'e idon tay ta d'an yamutsa fuska tace mata har ta fara bacci ne sannan aka maido ta cike
da gamsuwa yadikkon ta jinjina kai tace to ta tashi ta ci Abinci kafin taci gaba da baccin, tana son ci don
cikinta ba komae amman da ta tuna abunda Khalid yay mata sai taji bata iya ci tace mata a k'oshe take
kawai, tana kwance bayan fitar Yadikko sai ga sak'o ya shigo wayarta ta d'auka tana dubawa bata gane
wanda ya turo ba saida ta shiga ta fara karantawa ta gane Khalid ne Don bata yi saving number d'in tashi
ba, sak'on ban hak'uri ne ya turo mata ya nuna son da yake mata ne yasa ya kasa resisting har hakan ta
faru kuma kar ta damu hakan ba wani abu bane tunda ya biya sadakin ta ba yaudarar ta yake ba amman
tun da bata so bazai k'ara mata ba har sai an d'aura masu aure yana fatan zata yafe mashi sosae yay
mata kalaman da zasu kwantar mata da hankali, ta dad'e tana kallon sak'on kafin ta kife wayar, ba laifi ta
d'an ji sanyi a ranta ba kamar da yace bazai sake mata hakan ba sai dae kuma abunda ya fi damunta da
yace sai an d'aura masu aure don ita yanzu k'yamar shi ma take can sai gashi ya kira K'in picking tay sai
bayan da ta yanke wani kiran ya sake shigowa sannan tay picking ta kara wayar a kunnanta ba tare da ta
ce komae ba sanin tana sauraran shi yasa yaci gaba da bata hakuri yana kwantar mata da hankali har dae
ta saukko ta fara tunanin k'ilan da gaske ne ya canza hali kamar yadda Mahaifin shi ya sanar da Baffanta
dama kuma yadikko tace duk zargi ne abun da su zakiyya suka fad'a ba wanda ya tabbatar, da wannan
tunanin ta d'an sake mashi suka d'an yi hira kafin daga baya yace ta kwanta saida Safe, Washe gari
Juma'a sai gashi yazo da daddare bayan sallar Isha koda ta fita yana zaune a Mota yace ta shigo tace a'a
ba sai ta shiga ba yana yar dariya yace to shi bai iya fitowa ya tsaya kaman wani d'an k'auyen su, k'arshe
da yaga ta toge duk da yace ba abunda zai mata sai yace ta shigo sai tabar kopar bud'e sannan ta
amince, Ranar Lahadi wurin sallar Azahar aka kawo lefen Fatuu dankara dankaran akwatuna guda
takwas set biyu masu hud'u hudu shak'e da kaya na gani na fad'a masu kyau da tsada abun ka da aikin
Naira gaba d'aya wad'anda za'a d'inka har an gama, a d'akin Yaya aka kai su nan kowa ke zuwa gani sai
yabawa ake ana zuba k'auyanci, sam Fatuu bata yi farin cikin kayan ba da su Mino suka zo suna fad'a
mata bin su da ido kawae take yanzu dae ta idasa tabbatarwa da gaske Aure za'ayi mata, wurin k'arfe
ukku na rana Khalid ya kirata bayan ta d'aga ya sanar da ita zai zo bayan sallar la'asar zasu d'an je wani
wuri, shiru ta d'an yi mashi a ranta ta shiga tunanin ina kuma zasu har saida yace bata ji bane sannan
tana tura baki tace ina zasu yace bata ji yace wani wuri zasu bane, sam ran ta bai kwanta da fitar ba don
ita yanzu tsoron shi take hakan yasa tace mashi ita bazata je ko ina ba, shu'umin murmushin shi yay yace
Ok tunda shi bai isa da ita ba bari ya kira wanda ya isa dashi ya sata ta bi shi nan take ta gane Ard'o zai
fad'a mawa k'arshen ta kuma ya sanar da Baffanta ta san kuma bazai ji dad'in hakan ba, ba yadda ta iya
tace mashi zata shirya tamkar ta fasa ihu, bayan la'asar ta gama shiryawa tasa jallabiya bak'a tay rolling
veil d'in tana gamawa bada dad'ewa ba sai gashi ya kirata ya sanar da ita yana a kopar gida, a Falo ta
samu yadikko tace mata sai ta dawo da yake ta sanar da ita game da fitar tace a dawo lpy, Yana zaune a
Mota ta fito ya k'ura mata ido har ta k'arasa ta bud'e gaban ta shiga fuskarta a d'aure ta gaishe dashi
yana murmushi ya amsa yace ta rufe su tafi bin shi da kallo tay tace "Wai ina zamu ne?" d'age gira yay
yace "zan saido ki ne" tura baki tay ba tare da ta ce komae ba ganin bata da niyyar rufe kopar yace mata
zai kai ta ta gaisa da wasu ne sannan ta rufe yaja suka tafi, Yar tafiya sukae suka k'araso bakin garin
daidai k'aton gidan Gonar su ya karya kan Motar ya shige gate d'in farko dake a bud'e mai gadi na d'aga
mashi hannu yay mashi horn ba tare da ya tsaya ba, wata tafiyar suka k'ara yi kafin suka sake isowa wani
gate d'in na fence ya tsaida Motar ya fita ya bud'e Fatuu nata bin wurin da ido bayan ya dawo yaja suka
kutsa ciki, wurin parking ya nufa ya parker Motar ya kalleta da Murmushi yace ta fito, a hankali ta kai
hannu ta bud'e Motar bayan ta fita tay tsaye tana k'are ma wurin kallo shi kuma ya koma yaje ya rufe
gate d'in tana cikin kallon wurin zuciyarta ta ayyana mata nan ai kaman gidan Gonar su ne dammm
kirjinta ya buga sam ita da farko bata gane ba sai yanzu bayan ya dawo in da take tsaye yace mata su
shiga yay Maganar yana nuna mata k'aton Flat d'in dake gaban su togewa tay tana bin shi da ido yace
"Let go in wife" tana tura baki tace "Amman ai gidan kaman ba kowa" yana murmushi yace waya gaya
mata ba kowa bata ga gida bane lafiya lou, shiru tay tana nazari lokacin Maganar yadikko da ta ce har
Chairman d'in da Matan shi suna zuwa Hutu nan ta fad'o mata hakan yasa tay tunanin k'ilan da gasken
akwae Mutane ganin ta d'aga k'afa yasa yay gaba yace su je tabi bayan shi suka nufi entry d'in, Babban
falo ne mai d'auke da duk wani abu da zaka samu a falon yan gayu akwae corridors a 6angaren dama da
hagu bin falon da kallo Fatuu tay Khalid d'in ya nuna mata ciki wajen da Sofas suke yace suje, zaunawa
yay kan 3 seater ya nuna mata gefen shi yace ta zauna tay tsaye tana kallon shi kafin tace mashi ina
wad'anda zasu gaisa d'in yace ta zauna mana ko zai cinye ta ne kaman bazata zaunan ba sai kuma ta d'an
d'osana ta zauna a d'arare tana ta kallon shi, yana ganin ta zauna ya fad'ad'a murmushin shi had'i da
d'an kwantar da kan shi yace ko ita fa, shiru tay ganin kallon da yake mata yasa fuska a d'aure tace "Wai
ina Mutanen?" Hannu ya kai ya shafi sumar shi still da murmushi akan fuskar shi ya fara Magana "Wife
ba fa wasu da zaku gaisa I just want us to spend time together yadda zamu k'ara fahimtar juna don naga
kin k'i sakin jiki da ni gashi nan da few days zamu zama Couples" wani kallo ta bi shi da shi baki bud'e shi
kuma sai faman lumshe mata ido yake can ya fara matsawa wurinta tay zumbur ta mik'e ta kumbura
baki a fad'ace tace "shine duk gidan mu bai isa ba sai ka kawo ni nan harda yi man k'arya to ni dae ka
tashi ka maida ni ko in tafiya ta tunda nasan hanya!" d'an ta6e baki yay kawae bai ce mata komae ba
aikuwa a fusace ta juya ta nufi hanyar fita daga falon saidae tana kaiwa kopar taji ta a rufe gam wani
bugu kirjinta yay kenan kulle kopar yay bayan sun shigo, juyawa tay ta kalle shi ko kallon ta bai yi ba
hakan yasa jikinta mutuwa ta nufi cikin Falon gefen kujerar da yake ta tsaya idon ta a kan shi kamar
zatayi kuka tace "Don girman Allah kai hak'uri ka maida ni gida" bai kalleta ba sai ma cigaba da latsa
wayar shi da yake yay kwalla ne suka fara zubo mata taci gaba da yi mashi magiya saida ya mula yasha
iska sannan ya d'aga ido ya kalleta cikin kashe murya yace "Don kin ga na damu da ke shiyasa kike taking
advantage d'in hakan kina neman wahalar dani ko? Kuma ni kike ce ma makaryaci don kawae na buk'aci
mu kasance tare dama ashe har yanzu baki daina rashin kunya ba?" d'an girgiza kai tay tace "a'a kai kace
zamu gaisa da wasu ne ai da ka fad'i man gaskiya" kya6e baki yay ya d'age gira yace "in na fad'i maki
gaskiya zaki zo ne?" shiru tay tana ci gaba da yamutsa fuska yaci gaba da cewa "Zuwa yanzu yakamata ki
d'auke ni kaman yadda na d'auke ki just 6 days ya rage a d'aura mana aure what's there don na bukaci
mu kasance tare, da wasu ne ma yanzu tuni sun d'auki kan su matsayin ma'aurata, kodae ban yi maki
bane?" Wani wahalallan yawu ta had'iya a halin yanzu dole ta bi shi gudun kada yay mata wani abun
ganin daga ita sai shi gashi ya kulle kopa, sake tambayarta yay bai yi mata bane a dabarbarce tace a'a
yayi mata yace to ta kwantar da hankalin ta ba wani abu zai mata ba kuma nan gidan da take gani nan
za'a kawo ta don haka gidan tane ya nuna mata gefe inda ta tashi yace ta zauna suyi hira tace to sai
yaushe zasu tafi yace bada jimawa ba, bata da yadda zatayi dole ta koma ta zauna ya kai hannu kan c-
table ya d'auki remote ya kunna masu kallo, bayan ya koma ya zauna yana murmushi yace mata miye
labari a hankali tace mashi babu ya tambayi taga kaya akwae abunda babu tace mashi kawae akwae
komae duk kuwa da bata ma ga kayan ba, tambayarta yay abubuwan da take so da wanda bata so ta
kasa bashi amsa yace shi bari ya fad'i mata ya shiga lissafo mata tana dae ta kallon shi can ya tambayeta
wai tana da saurayi farko shiru tay mashi don tsoron bashi amsa take ganin hakan yasa shi cewa in fa
tana son ya maida ta gida ta bud'e baki ta rink'a mashi Magana ta girgiza mashi kai a hankali tace bata da
shi yana dariya yace ta dai fad'a ne ya za'ai mace kaman ta ace bata da saurayi yace "Ni kin ga inada yan
mata saidae ba wadda ta yi man matsayin Matar aure na don duk basu da qualities irin naki" sototo tay
tana kallon shi haka ya ci gaba da bata mamaki ta hanyar yi mata kalamai masu d'aure kai har dae ta
d'an fara sakewa sai gashi har tana yin d'an murmushi in ya kama can ya mik'e yace bari ya d'aukko
masu lemu kishi yake ji itama tana bak'uwa ya barta ba ko ruwa duk da nan d'in gidanta ne, bada jimawa
ba ya dawo ruk'e da babbar robar Fanta da glass cups guda biyu ya d'aura su akan c-table ya bud'e ya
fara tsiyayawa cike da tsokana yake fad'in "nasan Fulani da son jan lemu" kallon shi kawae take sai kace
shi ba bafullatanin bane, bayan ya zuba ko ina ya mik'a mata cup d'aya ta amsa ta ruk'e shima ya d'auki
d'ayan ya koma ya zauna ya kai baki ya fara sha, ganin ta ruk'e wanda ya batan yasa shi ce mata ta sha
mana ko tsoron sha take bata ga shima ya sha ba jin hakan yasa ta kai cup d'in ta fara sha......

***** *****

Bayan Wani Lokaci, A hankali ta fara motsa idanunta da sukae mata nauyi kafin da k'yar ta idasa waresu
kan Pop ceiling d'in da take facing, k'ura ido tay tana kallo kaman mai nazarin wani abu can ta mik'e
zaune zumbur da mamaki ta kai idonta saman gadon da take zaune kafin ta bi cikin d'akin da kallo with
extreme surprise tunanin abunda ya kawo ta d'akin ta shiga yi da yadda akai har ta kwanta kan gadon,
lokaci guda kwakwalwarta ta fara tariyo mata abubuwan da suka faru kafin yanzu, to miya faru da ita ne
bayan ta sha lemun da ya bata? ta jefa ma kanta tambaya, wani irin bugu k'irjinta yay da sauri ta kai
idonta jikinta ta fara bin kanta da kallo abun mamakin lafiya lou rigarta na a jikinta haka dogon skin tight
d'in da ta sa a ciki shima yana nan hannu ta kai ta shafi kanta dake bud'e amman gashinta na a fake
shima, kan ta ya gama d'aurewa tana cikin hakan taji an turo kopar da sauri ta kai idonta wurin Khalid ne
ya shigo jikinshi sanye da singlet sai wandon jeans d'in da yazo da shi suna had'a ido ya sakar mata
k'ayataccen murmushi ya tsaya a jikin kopar ya goya hannuwan shi a kirji yace mata ta tashi kenan,
tabdijancan! ido waje take kallon shi murya na rawa tace "Ya akai nazo nan waya kawo ni??" d'an
yamutsa baki yay yana lumshe ido yace "kin yi bacci ne and u'w not comfortable there har kina niyyar
fad'owa shine na maido ki nan" k'ara zaro ido tay ta furta Kalmar ya maido tan nan da ya fad'i, a kidi'me
tace "to ya akai nayi baccin ni bansani ba?" d'an watsa hannuwa yay alamar bai sani ba ta k'ura mashi
ido alamar bata yadda ba can murya kaman zata yi kuka tace "Daga shan lemu sai bacci..." dakatawa tay
tana tunani can ta tuno da maganin bacci da Kawu Amadu ya ta6a amso mata a rud'e tace "k...ko dae
maganin bacci kasa man kai man wani abun???" d'an ta6e baki yay yace "u can check ur body" daga
haka ya juya ya fita, da sauri ta saukko daga kan gadon ta nufi gaban dressing mirror tana kallon kanta ko
zata ga wani canji amman bata ga komae ba da sauri ta d'aga rigarta sama ta k'ura ma k'irjinta ido boobs
d'inta na acikin bra lafiya lau sakin rigar tay ta gwada yin tafiya don tasan in dae yayi mata wani abun a
gurin zata gane amman bata ji komae ba lafiya lou take tafiya kasa yadda tay ta nufi wata k'opa da take
tunanin toilet ne ta tura sai gashi toilet d'in ne ta shige, sosae ta duba under d'inta lafiya lau bata ga
wani canji ba tsaye tay sam ta kasa yarda da bai mata wani abu ba don zuciyarta na raya mata wani abu
yasa a cikin lemun nan, hakanan bazata yi nauyin baccin da har zai maido ta d'aki ba ba tare da ta farka
ba tana haka taji wani abu na yawo cikin rigarta da sauri ta zura hannu ta jawo sai ganin hannun bra
d'inta tay wani irin bugu kirjin ta ya fara yi ta zazzaro ido waje da sauri ta k'arasa gaban mirror d'in dake
cikin wurin ta k'ara d'age rigar sama sai lokacin ta lura da bra d'in bata kamata sosae ba kamar yadda ta
sata, hannu na rawa ta fiddo breast d'inta guda tana dubawa koda ta kalli nipple d'in da sauri tasa hannu
ta rufe bakinta ganin yadda yay jajir da shi gashi ya fito sosae, wani irin kuka Fatuu ta saka tana fad'in ta
shiga ukku ta bani ta lalace sakin rigar tay a fusace ta juya ta fita ta nufi falo, lokacin da ta shiga yana
zaune ya kishingid'a jikin kujera ta tsaya gaban shi kaman an jefota cike da Masifa tace "Ashe abunda
zaka aikata man kenan yasa ka kawo ni nan, dama an ce kai d'in manemin mata ne d'an shaye shaye
kuma dama ban yarda da duk abubuwan da kake fad'a man ba, ba wani so na da kake yaudarata kawae
kake kana son ka cutar dani don in kana sona da gaske bazaka man haka ba nima kuma ban son ka ban
kaunar ka na tsaneka kuma bazan Aure ka ba wllh!!!" d'age gira yay yana kallonta da d'an murmushi
hakan yasa ta k'ara k'ulewa taci gaba da zazzaga mashi Masifa har tana kiran shi da Mazinaci aikuwa
tana fad'in hakan ya daka mata tsawa ya mik'e har saida ta d'an ja baya fuska tamke ya fara Magana "Kar
ki k'ara kirana da wannan sunan! Ke in ni Mazinaci ne kina tunanin yadda na samu dama akan ki zan
kyaleki ne iya hakan??" Duk da ta tsorata tay k'arfin halin cewa "ai duk d'aya ne miyasa zaka bud'e man
jiki har ka ta6a man jikina!" tay Maganar kwalla na zubo mata, sassauta murya yay cikin sigar rarrashi
yace "it's just a romance wife and ba don na biya sadaki ba ba abunda zai sa in ta6a ki kuma duk laifin ki
ne kin k'i ki saki jiki da ni, I truly love u shiyasa nike maki hakan kuma bai kamata ki tada hankalin ki ba
komi nai maki ai ni zaki aura ko......." A fusace tace "Allah ya kyauta! wllh bazan Aure ka ba na tsane ka
kuma sai Allah ya saka man abunda kai man tunda dai ba d'aura mana aure akai ba" yar dariya yay ya
girgiza kai yace "Do u think is as simple as u said?" banza tay mashi tana huci kwalla naci gaba da zubo
mata yace "Look Wife ki bar wannan a tsakanin mu ba wani abu bane muje in maida ki" wani kallo take
bin shi da shi cike da takaici ranta na mata wani irin suya ya wuce Bedroom d'in bada jimawa ba ya dawo
ya maida rigar shi ya mik'a mata veil d'inta kaman bazata amsa ba yace ta amsa su tafi Magrib ta kusa in
kuma zata kwana ne anan to, amsa tay ta yafa yay mata alamar suje tayi gaba yana bin ta a baya suka
fita ba yadda ta iya ba don ta so ba ta shiga Motar don kuwa akwae tafiya ga Magrib tayi, tunda suka
hau hanya take sheshsheka yana bata hak'uri had'i da nuna mata ba fa wani abu bane shi yanzu ma ji
yay ya k'ara sonta don gaba d'aya yadda yake son Matar shi ta kasance haka take, suna isowa ta bud'e
Motar ko rufewa ba tayi ba tay gaba, Lokacin da ta shiga falon iske Yadikko tay tana salla ta wuce uwar
d'akan ta fad'a kan gado tasa kuka mai cin rae yadikko na sallame sallar ta shigo d'akin da sauri don tun
tana sallar take jiyo sauti kukanta, hayewa tay Saman gadon ta d'ago Fatun tana tambayarta abunda ya
faru cikin kuka ta kwashe komae ta fad'a mata tace "ban son shi yadikko don Allah ki fad'a ma Baffana
kada a Aura man shi mutuwa zanyi in na aure shi, wllh da gaske d'an iska ne kuma yana shaye shaye"
Ajiyar zuciya kawae yadikko ke saukewa tasan hakan ba mai yuwuwa bane ba kamar yanzu da ya rage
saura yan kwanaki bikin, sosae ta shiga rarrashinta tana nuna mata lokaci ya k'ure kuma ita a tunaninta
da gaske don ya biya sadakin yasa yay mata hakan tunda yana ganin saura yan kwanaki ta zama Matar
shi ta daina damuwa tunda ma shi d'in da yay mata hakan zata Aura kuma da bai son ta abunda yafi
hakan zai aikata mata ya dawo yace kuma bazai Aure ta ba, ita kanta yadikkon hankalinta ya tashi sosae
da jin abunda ya faru hakanan ta danne don kar ta k'ara tada ma Fatun hankali da k'yar ta shawo kanta
ta d'an saukko har taje tayo wanka ta dauro Alwala bayan ta gama sallar ta d'aga hannu tana kuka tana
rokon Allah kan ya kawo mata Mafita, kasa cin Abinci tay duk da tana jin yunwa ta sha yar fura kawae,
koda ta kwanta sak'e sak'e taci gaba da yi a ranta da ta tuna wani ya gane mata jiki har ya ta6ata sai wani
kunci ya k'ara lullu6e ranta lokaci guda ta fara tunanin yadda zata guje ma Auran Khalid abunda bata
ta6a tunanin yi ba tunda aka fara Maganar Auran sai yanzu...........
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._

*ASM Bk2031*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

..........Tana cikin tunanin neman mafita wayarta ta fara ringing da k'yar ta kai hannu ta d'aukko ta duba
screen d'in ganin Number yasa ta gane Khalid ne ta kife wayar kawai ba tare da tayi picking ba, sake kira
yay sai kawae ta kashe wayar ma gaba d'aya ta cillar da ita taci gaba da tunaninta da k'yar bacci ya
dauketa, Washe gari da zazza6i ta tashi da k'yar tayi sallar Asuba ta koma ta kwanta sai da yadikko ta zo
tashin ta don tayi karin kumallo tasan bata lafiya da k'yar ta lalla6ata ta tashi ta yi breakfast d'in ta bata
Magani ta sha kafin ta koma gado, sai wurin sallar Azahar ta farka ba laifi ta samu sauki sosae hakan yasa
ta wuce bathroom tayo wanka ta d'auro alwala, bayan ta gama sallar ta zura doguwar riga ta fita falo
anan ta iske Yadikko itama ta gama salla da murmushi tay mata ya jikin tace ta samu sauki ta samu wuri
kan kujera ta zauna, ganin yanayin damuwa tattare da ita yasa yadikko ta shiga rarrashin ta kan ta
kwantar da hankalin ta da k'yar ta lalla6a ta ta zubo mata Abinci tana cikin ci sai ga Sadeeya tazo tana
sanye da jallabiya tay rolling veil da fara'a yadikko ta tarbeta ta nuna mata wurin zama kafin suka shiga
gaisawa daga baya ta kalli Fatuu da fara'a ta gaishe da ita anan take sanar ma yadikko tazo ne zasu je
wurin gyaran jiki lokaci guda yanayin fuskar Fatun ya canza yadikko ta lura da hakan ita kanta Sadeeyar
ta ga canji a Fuskar ta nan yadikko ke sanar mata yau ta tashi bata jin dad'in jikinta ne amman ta samu
sauki da ta sha Magani cike da nuna damuwa Sadeeya ta shiga yi mata sannu har tana cewa amman dae
Ya Khalid bai sani ba ko tunda bai fad'a masu ba yadikko tace eh ai yau ne ta tashi da ciwon, kallon Fatuu
tay da bata da niyyar tashi tace taje ta shirya su je tunda da sauk'i sosae kaman ta saka ihu haka taji ba
yadda zatai dole ta mik'e ta wuce ciki, gyale kawae ta yafa akan doguwar rigar material din jikinta tasa
takalma ta fito, lokacin da suka fita kopar gidan ja tay ta tsaya ganin Motar Khalid sam bata yi tunanin shi
ya kawo Sadeeyar ba daba abunda zai sa ta fito tay zaton driver ne kaman rannan ganin ta toge yasa
Sadeeya ce mata suje mana da K'yar ta ja k'afa suka nufi Motar don bata son ta gane da wani abu duk
Khalid d'in na kallon ta duk da Motar a rufe take ruff kuma glass d'in black tinted ne, Front seat Sadeeya
ta bud'e mata ta shiga bayan ta rufe itama ta bud'e baya ta shiga, wani kalan d'aure fuska tay ba tare
data kalle shi ba shi kam sai kallonta yake with smile on his face yace tana lafiya kafin ta bashi amsa
Sadeeya tace "Big bro Bride en ka fa bata lafiya" d'an bud'e ido yay idon shi akan Fatuu ya tambayi Mike
damunta da kyar ciki ciki tace mashi zazza6i, shiru ya d'an yi still idon shi na akanta ita kuma ta juyar da
fuskarta can taji yace ko su wuce Asibiti ya duba ta ne, ba shiri tay mashi wani kallo ya d'age mata gira
baki kumbure tace ta samu sauk'i yace Ok daga haka yaja Motar suka tafi, sai firar bikin suke shida
Sadeeya tay masu banza tamkar ma bata acikin Motar sam Sadeeya bata kawo komae ba ta d'auka don
bata jin dad'in jikinta yasa tay shiru kuma dama ta san bata Magana sai ta kama, lokacin da suka isa
shagon Fatuu na niyyar fita taji ya kamo hannunta akan idon Sadeeya tay d'an murmushi kawae ta fita
Fatuu na jin ta rufe kopar ta fara k'ok'arin fuzge hannunta amman ta kasa a fad'ace tace "Ka sakar man
hannu!" d'an lumshe ido yay yana mata wani irin kallo ganin bai da niyyar sakin yasa idanunta suka
cicciko da kwalla murya kaman zata yi kuka ta k'ara cewa ya sakar mata hannu ita ba yar iska bace da zai
rink'a ta6a ta sai lokacin yay d'an murmushi cikin kashe murya yace "nima ba d'an iska bane wife......" A
fusace ta katse shi da fad'in "wllh kai d'an iska ne in ba haka ba mi yasa zaka bud'e man jikina ka ta6a
ni!" Daga yadda tay Maganar zaka fahimci ba k'aramin ciwo abun yay mata ba, d'an ta6e baki yay still da
murmushi akan fuskar shi yace "Ok mu barshi a hakan na yadda ni d'an iska ne but nan da next 5 days
zan assuring naki hakan" damm k'irjin ta ya buga ta bi shi da ido ya wani d'age mata gira, d'ayan
hannunta ta sa tana goge kwallan dake zubo mata ya kai hannu ya bud'e glove box ya fiddo hanky ya
mik'a mata don ta goge kwallan k'in amsa tay tabi hanky d'in da kallo ba komae ya tuna mata ba sai
ranar da Ya Haisam zai tafi, ganin ta k'i amsa ne yasa shi ce mata in fa bata amsa ta goge su ba bazai bari
ta fita ba sai dae suyi ta zama har sai sanda ta gogen, ba yadda ta iya cike da takaici don ita k'yamar
hanky d'in take Saboda rannan a cikin wurin ya fiddo kwalin cigarettes, saida ya ga ta goge su tass
sannan ya kyaleta ta fita lokacin Sadeeya tuni ta shige cikin wurin gyaran jikin.

Da yamma wurin k'arfe biyar ya dawo d'aukar su bayan da Sadeeya tay mashi waya ta sanar mashi sun
gama, a gida ya fara sauke Sadeeya tana cewa Amarya bazata shiga su gaisa da Momy ba yace yamma
yayi yana so yay dropping nata before Magrib tay ma Fatun sallama, tun da suka hau hanya jininta akan
a kaifa yake har sukae nisa bai tanka mata ba yana ta sauraren music d'in da ya kunna yana bi a hankali,
saida suka iso bakin gari wurin gidan Gonar su sannan ya kalleta ta juyar da fuskarta tana kallon gefe
yace "Wife ko muje ki huta anjima sai in maida ki" tun kafin ya rufe baki ta juyo a harzuk'e tay mashi
wani kallo, k'ok'arin juya kan Motar ya fara yi aikuwa a firgice har bata san ta kai hannu kan hannunshi
dake ruk'e da steering murya na rawa ta fara mashi magiya ya kaita gida wani irin lumshe ido yay
sakamakon shak'ar daddad'an k'amshin da jikinta ke fitarwa dama tunda ta shigo Motar yake d'an
bugun hancinshi ba shiri ya taka burki, jin ya tsaida Motar yasa ta juya ta kalleshi tana ganin yadda
idanuwan shi suka koma da sauri ta cire hannunta ta juya zata bud'e Motar da sauri ya kai hannu yay
locking Kopar ido waje ta juya ta kalle shi yana ta bin ta da wani irin mayen kallo tana ganin haka ta fara
yamutsa fuska nan da nan ta fara kuka tana had'a shi da Allah kan kada yay mata wani abu hakan bai da
kyau ya bud'e mata ita zata tafi a k'asa ma, Still kallonta yake bai san miya sa ba komae yarinyar tay
sha'awa yake bashi shi kad'ai yasan yadda yake ji ko jiya a gidan gona ba k'aramin yak'i yay da zuciyar shi
ba har ya iya k'yaleta don ya fahimci bata san namiji ba daga yadda take tsoron ya ta6a ta shiyasa ma ko
tunanin kaiwa can ma bai yi ba ko ba haka ba bai iya yin hakan tana a yanayin bacci don zai zama kaman
yay raping nata ne shi kuma abunda ya tsana kenan shi yasa ko ada da yake kula mata wani abu bai shiga
tsakanin shi da mace face da amincewar ta, Kuka sosae take mashi duk ta rud'e can ya sauke ajiyar
zuciya cikin kasalalliyar murya yace mata tay shiru ba abunda zai mata in kuma bata yi shirun ba to zai
wuce da ita gidan gonar ne ba Arziki tay tsit sai motsa baki take tana zare ido, idanu a lumshe yake
kallonta sai kikkafta ido take taji yace tana so su tafi, da sauri ta d'aga mashi kai alamar eh jinjina kai yay
yace "I want a single kiss pls" k'ara zaro ido tay baki bud'e take kallon shi ta kasa cewa komae yaci gaba
"in kikai man hakan zamu tafi in kuma kika k'i saidae muyi ta zama anan har dare yayi sai mu wuce gidan
gona mu kwana can" k'ara rud'ewa tay ganin on a serious note yay Maganar murya na rawa tace
"amman fa kasan babu kyau tunda ba'a d'aura mana Auren ba" still bin ta yake da kallo yay d'an guntun
murmushi yace "But ai zamu yi auren ne ko, kuma miya rage abunda yake dole saida shi ake d'aura
auren already an bada so ba wani abu bane" kuka ta fara k'ok'arin ci gaba da yi yace ko na jini zatai in
dae bata yi mashi ba ba tafiya zasu yi ba kuma da gaske gidan gona zasu wuce, wani irin bak'in ciki ne ya
turnuk'eta taji ta k'ara tsanar Auren shi ganin da gaske bazasu tafin ba don yama jingina da seat ya d'age
kan shi yasa tace zata yi mashi jin hakan yasa ya d'ago yana murmushi ita kuma ta d'aure fuska tamkar
bata ta6a yin dariya ba nuna mata lips d'in shi yay alamar anan zata yi mashi ta ce ita bazata yi mashi
anan ba yace Ok bata shirya su tafi ba kenan ganin yana niyyar maida kan yasa tace to zata yi mashi
amman kar ya ta6a ta yace ya yarda tana kukan zuci da har ya bayyana kan fuskarta ta fara matsawa shi
kuma sai sakar mata murmushi yake, kasa yi mashi tay tana ta yamutsa fuska can dae ta daure ta cije ta
rufe ido ta kai bakin ta saitin fuskar shi amfani yay damar daya samu ta rufe idon da tay ya kai hannu ya
kamo kan nata ya had'e bakin su, irin yadda yay mata ranar da ya maido ta daga gidan su yau ma yay
mata, lokacin da ya saketa wani irin kukan bak'in ciki Fatuu ta saki tana yi mashi Allah ya isa kuma Allah
sai ya saka mata in sha Allahu bazata Aure shi ba, bai ce mata uffan ba don shi kadae yasan abun da yake
ji da k'yar ya tashi Motar suka tafi, suna isowa tun kafin ya idasa tsayawa ta kai hannu zata bud'e kopar
Allah yasa a rufe take har saida ya tsaya sannan ya bud'e kopar a fusace ta fice ya bita da ido ta cikin
glass har ta shige cikin gida, sai da ya d'au d'an lokaci kafin da k'yar ya ja Motar ya tafi, Tana shiga saida
ta tsaya a soro ta goge fuskar ta sosae sannan ta shiga ciki lokacin da ta shiga falon su da yar sallama cak
ta tsaya ta kasa k'arasa sallamar sakamakon wadda ta gani a zaune ta d'an kishingid'a kan kujera suna
had'a ido ta fara sakar mata murmushi da tsananin mamaki Fatuu ta furta "HAULAT.....!" tashi zaune
sosae Haulat tay tana dariya tace "Na'am k'awata Amarya" aikuwa da gudu Fatuu ta nufeta ta fad'a
jikinta cike da farinciki haulat sai dariya take yi, d'agowa Fatuu tay fuskarta d'auke da tsantsar farin ciki
tace "yaushe kuka zo ne?" Haulat tace "bamu dad'e ba salla kawae nayi ko Abinci kin ganshi ban ci ba
nace sai na gan ki tukunna na dae sha fura, ance gyaran jiki kika je gaki nan ai sai annuri kike kin fito sak
Amarya" ta k'arasa tana murmushi Fatuu ta tura mata baki kafin tace "keda wa kuka zo" tace "da kawu
Amadu ne" da d'an mamaki tace "shine bai sanar da ni ba,to Gwaggo fa?" Haulat tace "gaskiya mu biyu
muka zo sai kaya k'ilan ko ita sai daga baya ina jin" shiru Fatuu tay sai kuma ta mik'e da sauri tace mata
tana zuwa tay hanyar fita Haulat ta bita da kallo tana ta murmushi, d'akin su Kamalu dake a soro ta nufa
tana zuwa ko sallama bata yi ba ta kutsa kai tana shiga ta iske Kawu Amadu kwance yana latsa waya ta
nufe shi tana kiran sunan shi ya d'ago ido yana ganinta ya saki murmushi yana kokarin tashi zaune, a
gefen shi ta zauna tana kallon shi tace "Kawu Amadu ashe kun zo" yana murmushi yace "Eh Amaryarmu
bamu dad'e da zuwa ba na tambaye ki aka ce kun fita" a sanyaye tace "Gwaggo fa, haulat tace ku biyu
kuka zo" shiru ya d'an yi sai kuma yace "Eh amman tace zata zo ta bada kaya ma akawo" kafe shi da ido
Fatuu tay kaman bata yarda ba tace "to yaushe zata zo?" Shiru yay baisan ranar da zai ce mata ba don in
ma yayi mata k'arya yasan ranar zata zo kuma ba zuwa gwaggon zatai ba, ganin haka yasa fuskarta
canzawa tamkar zata sa kuka tace mashi bazata zo ba ko, farko shiru yay ganin ta kafe shi da ido yasa ya
d'aga mata kai alamar eh, kuka ta fashe mashi da shi tana fad'in ashe bata hak'ura ba har yanzu fushi
take da ita, side hug Amadu yay mata ya shiga rarrashin ta yana tayi hakuri a hankali komae zai wuce
yasan dole zata zo ne koda bayan anyi auren ne can ta d'ago tace mashi Hajiyar Sanata fa itama bazata
zo ba, da yar damuwa yace mata Hajiya bata lafiya ciwon kafafu take yanzu ko wurin aiki ma ba zuwa
take ba amman taso ta zo koda taji gwaggo bazata zo ba har fushi tay da ita, sosae ya rarrasheta ya nuna
mata tayi hak'uri wannan jarabawa ce daga Allah, kiran sallar Magrib yasa shi tashi yace mata ta koma
ciki zai je yay salla ya dawo, zaune tay a cikin d'akin tana cigaba da matsar k'walla sai daga baya ta tashi
ta nufi cikin gidan lokacin da taje d'akin su a k'urya ta iske Haulat na yin salla itama taje tayo Alwala tazo
gefenta ta kabbara salla, bayan sun gama Haulat ta kalleta da Murmushi tana ganin yanayin fuskar Fatun
tace "K'awata lafiya dai ko, idanun ki naga sun canja kuma dama naga har rama kin yi" kaman zata sa
kuka tace "Haulat baki ji Auren dole za'a man bane?" da yar damuwa Haulat tace "naji Fatuu lokacin da
innata ta kira waya can Nijar ta sanar da ni na matuk'ar girgiza da jin zancen tun lokacin nike kokarin
kiran ki amman bata shiga daga baya ne na kira kawu Amadu ya fad'i man komae, na matuk'ar tausaya
maki Fatuu wllh Allah ne shaida har kuka nayi sosae nace Ashe ba rabon dae kiyi karatu kuma ki auri
wanda kike so" kuka sosae Fatuu ta fashe dashi tasa hijab d'in jikinta ta rufe bakinta don kar sautin ya
fita itama Haulat kwallan ta fara yi ta shiga rarrashinta tana cewa tayi hakuri kowa a rayuwa da kalar
kaddarar shi ita kuma wannan ce tata, cikin kuka tace "Haulat za'a man Aure ba tare da gwaggo ta zo ba
Saboda tana fushi dani don na amince aman auren, nima don banda yadda zan yi ne amman wllh ban
son Auren nan....." sosae taci gaba da yin kuka suna haka yadikko ta shigo a rud'e ta shiga tambayar ko
lafiya Haulat tace ba komae Saboda gwaggo bata zo bane nan itama tasa baki suka cigaba da rarrashin ta
tare suna ce mata dole gwaggo zatai fushi yanzu amman zata saukko ko ba yanzu ba, sai da aka kira
sallar isha suka tashi suka yi Bayan sun gama ne Yadikko ta nuna mata kayan da su Haulat suka zo dasu
Manyan bokitan su cin cin da dublan ne dasu zannuwan gado da labulaye harda kayan gara su buhun
shinkafa biyu katan d'in Taliya da Macaroni suma bibbiyu jarkar Mai su gishiri Man shanu da sauran su
dae bin kayan da ido kawae tay ba tare da ta ce komae ba, tana gama nuna mata tace bari taje wurin
Yaya ta d'aukko kayan lefenta da shiru har yanzu ba'a maido su nan ba, lokacin da Yadikkon taje bayan
sun gaisa da wad'anda suke d'akin ta sanar ma Yaya ta zo d'aukar kaya ne, wani kallo ta jefa mata cikin
harshen fulatanci tace to cinye kayan zasu yi da har sai an biyo sahu d'an murmushi had'i da d'an ta6e
baki Yadikko tay tace dama daga gidan su Angon ne ake ta kira ana son aji ko akwae abunda baiyi ba
kaman takalma da kuma d'inkakkun kaya anata ce masu bata gwada ba shiyasa tazo ta tafi dasu ta
gwada amman bari taje sai a sanar masu har yanzu Amaryar bata ma ga kayan ba, tana fad'in hakan ta
fara kokarin juyawa ta tafi Yayar ta tsaidata Fuska a murtuke tace ai sai su yi ta d'auka kuma dole za'a
fitar ma da Mutanen gida nasu, ita dae Yadikko bata ce komae ba don tasan yanzu ace tayi rashin kunya
kaman yadda aka saba cewa, guda biyu ta fara d'auka duk suna kallonta ba wanda yay yunkurin taimaka
mata sai bayan da ta kai su daki ne ta dawo tare da Haulat da Mino suka kwashe sauran, bayan sun
maida su can suka zauna don sake kallon kayan dama basu samu sun duba ba sosae da suna can, sosae
Haulat ta shiga yaba kayan duk yadda akai da Fatuu tazo taga kayan ta gwada k'iyawa tay tace ai ba sai
tasa ba tunda tailor ya gwadata, suna cikin kallo sai ga Kawu Amadu da Kamalu sun shigo yadikko tace
yazo shima ya ga lefen sosae shima ya yaba saidae acan k'asan ranshi sam bai farin ciki da Auran ba
kamar da Kamalu yay mashi bayani kan wanda za'a aura matan don shima ba so yake ba yafi son tay
karatun ta kamar yadda shima yake da burin ya koma Katsina don yay karatu, bayan sun gama gani
yadikko ta kawo ma Haulat Abinci da k'yar ta matsa ma Fatuu ta d'an ci suna gamawa Haulat ta shiga
bathroom tayo wanka don a mugun gajiye take bayan ta fito tay shirin kwanciya itama Fatun ruwan ta
watso bayan ta shirya ta hau gadon lokacin tuni bacci yay awon gaba da Haulat, Sam Fatuu ta kasa bacci
sai faman sak'e sak'en mafita take rashin zuwan gwaggo ya dameta sosae ga Auran da shima bata son
ayi can wata zuciyar ta ayyana mata ko ta kira Haisam ta fad'a mashi halin da take ciki game da wanda
za'a aura matan sai kuma ta ayyana to in ta fad'i mashi shi mai zai iya yi mata tasan ba iya sa Ard'o ya
fasa zai yi ba k'arshe ya bata hak'uri kawae dama a k'ule take dashi don kwata kwata ya daina kiran ta,
haka taci gaba da yin tufka da warwara ta sak'a wannan ta kwance wannan har dare ya raba ba tare da
ta ankare ba, can wuraren Asuba ta mik'e ta saukko daga kan gadon ta nufi inda akwatunan da tazo da
su suke ta bisu da ido kaman mai nazarin wani abu kafin ta kai hannu ta d'aukko trolley d'in a hankali
don kar ya saki sauti, k'asa ta aje shi ta bud'e ta sake d'aukko babban shima ta bud'e ta fiddo wasu kaya
ta saka acikin trolley d'in ta d'aukko wasu takalma daga can gefe suma ta saka ciki duk wani abu da tasan
zata buk'ata ta saka sannan ta rufe babban Akwatin ta maida shi inda yake ta d'aukko wata Handbag
d'inta dake rataye ta bude kud'in da Khalid ya bata ne a ciki dama bata ta6a ko yar biyar ba ta curo su ta
nufi akwatunan lefenta ta d'an bud'e d'aya daga ciki ta cusa kud'in kafin ta rufe ta dawo wurin trolley
d'in ta rufe shi ta kai hannu ta d'aukko Hijab d'inta dake sagale jikin gadon ta saka har ta d'auki trolley
d'in ta nufi hanyar fita sai kuma ta dakata ta juya tana kallon Haulat dake kwance tana bacci hakanan ta
ji kamar bata kyauta mata ba in ta tafi ba tare da ta sanar mata ba, a hankali ta jingine trolley d'in ta nufi
gadon ta hau a hankali tasa hannu ta fara tashin ta da yake haulat bata da nauyin bacci a nutse ta bud'e
idanunta tana ganin Fatuu a gabanta ta yunk'ura da sauri da alamar mamaki akan fuskarta tace "wai har
Asuba tayi kin ma yi salla kenan" a hankali Fatuu ta girgiza mata kai murya k'asa k'asa tace "Asuba bata
yi ba Haulat" ganin yadda tay Maganar yasa itama Haulat yin k'asa da murya ta tambaye ta miya faru,
shiru ta d'an yi tana kikkafta ido kafin tace "Gida zan koma" cikin rashin fahimta Haulat ta sake tambayar
ta wane Gidan tace mata Katsina waro ido Haulat tay baki bud'e jin abunda tace Fatuu taci gaba da
cewa "Haulat ban son Auren nan, ban so gwara in gudu kawae in dae aka ga bana nan ai dole a fasa" a
razane Haulat tace "Amman Fatuu baki ganin lokaci ya k'ure saura fa yan kwanaki a d'aura auran ki
miyasa tun farko baki nuna baki so ba sai yanzu" kuka ta fara yi k'asa k'asa tace "Saboda Baffana ne
Haulat Kawu Amadu baya fad'i maki ba" kai ta d'aga mata tace eh ya fad'i mata taci gaba da fad'in
"Yanzu ban son auran nan Haulat....." Katse ta tay tace "amman Fatuu kina ganin abu ne mai sauk'i fasa
auran nan don kin gudu, ni a ganina kawae zaki jawo wata matsalar ne ki k'ara jefa su Baffa cikin wani
tashin hankalin" Fatun tace "ai dama gwaggo bata so dalilin hakan ne yasa take fushi da ni don na k'i
goyon bayanta nace na amince aman auren yanzu in naje nasan zata yi wani abun a fasa" shiru Haulat
tay tana kallonta kawae ta lura ganin hakan take abu mai sauk'i can ta dafata tace "Fatuu ni a ganina ki
hak'ura kawae tunda har an zo nan....." Cikin kuka tace "Allah bazan Aure shi ba in ba haka ba mutuwa
zanyi don baki san wanene za'a aura man bane yasa kike cewa in hak'ura, Mashayi ne fa mai neman
mata kuma..." Nan ta kwashe komai harda gidan gona da ya kaita da Maganin bacci da ya saka mata a
lemu harda abunda yay mata jiya da yamma da ta dawo ta isketa ta zo, hannu Haulat tasa ta rufe
bakinta cike da Al'ajabi kafin ta cire a sanyaye tace "Shikenan Fatuu in dai kina ganin gwaggon zata iya
yin wani abu da zai sa a fasan kije" da sauri ta goge kwallan fuskarta ta juya zata sauka daga gadon
Haulat tace "Amman Fatuu ni fa?" juyowa tay ta kalleta tace "ba sai ku dawo da kawu Amadun ba"
gyad'a kai Haulat tay sai kuma ta sake cewa "amman lafiya lau zaki iya tafiya dare fa ne" jinjina mata kai
Fatuu tay tace zata iya lafiya lou ba abunda zai sameta in sha Allahu daga haka ta idasa sauka ta nufi
hanyar fita idon Haulat a kanta tana kallon ta cike da tausayi har ta kai hannu zata d'auki trolley d'in taji
muryar Haulat ta kira sunanta juyawa tay ta kalleta ta saukko ta nufo inda take tana zuwa tace "bari mu
tafi tare" da mamaki tace "amman haulat jiya fa kuka zo ko hutawa sosae baki yi ba ki kwanciyar ki daga
baya sai ku dawo" girgiza mata kai tay tace su tafi ba komae har cikin ran Fatuu taji dad'in hakan, Hijab
Haulat ta d'aukko ta saka ta maida kayan da ta cire jiya cikin jakarta dama ita kadae ta zo da ita ta d'auka
Fatuu ma ta d'auki trolley a hankali tasa k'afa cikin Falon ba kowa sai k'annenta dake ta bacci kan
shimfid'a dama cikin d'akin daga ita sai Haulat Yadikko na d'akin Baffa, cikin sa'a suka fito daga cikin
d'akin gaban Haulat nata bugawa gaba d'aya a tsorace take suna fitowa Fatuu tay ma Haulat nuni da
hanyar bayan gidan a hankali cikin rad'a tace ta can zasu fita bata kopar waje ba...........

*Uhmmmm, shin su Fatuu zasu samu fita daga cikin gidan kuwa? In sun fita zasu samu komawa Katsina?
Gwaggo zata saurari Fatuu in sun samu komawar? Za'a fasa auran ko baza'a fasa ba???*

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._

*ASM Bk2032*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

..........Tafiya mai d'an tsawo sukae cikin sand'a suka karaso katangar dake bayan gidan wadda take
gajera bata da tsawo sosae Fatuu ce ta taimaka ma Haulat ta dira ta mik'a mata jakunkunan nasu sannan
itama ta hau ta dire duk suka d'auki kayan suka bar wurin da sauri, Tafiya suke cikin sauri sosae Haulat
duk a tsorace take ganin ko ina dumd'um ga haushin karnuka da ya karad'e ko ina cikin ranta tana ta yin
Addu'oi Fatuu kuwa sam bata wani jin tsoro burinta kawai taga sun bar k'auyen ita ke ma Haulat jagora
tana haska masu da fitilar wayarta saidae tana yi tana kashe wa ne, cikin sa'a suka k'araso bakin garin
lokacin aka fara kiran sallar farko na Asuba tsaye sukae suna jira ko zasu samu abun hawa amman har
bayan wani lokaci ba mai abun hawan da ya wuce Fatuu duk ta damu ganin an fara kiran salla tasan
yanzu ayi sallar gari ya fara wayewa, Haulat dae saboda tsananin gajiya duk'ewa tay a wurin ga gabanta
dake ta faman fad'uwa can Fatuu tace mata ta daure su d'an yi gaba kar azo a gan su ta yunk'ura da k'yar
ta mik'e ganin haka yasa Fatuu ta d'aura trolley d'inta a saman kai ta d'auki jakar Haulat d'in a hannu
tanata ta kawo ta ruk'e tace mata a'a ta bashshi zata iya, tafiya suka ci gaba da yi k'arfin hali kawae
Fatuu ke yi amman ta gaji itama ga kaya, suna cikin haka sai ga wani mai amalanken shanu ya taho ta
gabansu zai wuce da sauri Fatuu ta tsaida shi amman sai yak'i tsayawa tana ganin yana niyyar wuce wa
ta sha gabanshi da sauri tana fad'in Don Allah ya tsaya, tsayawa yay cikin harshen fulatanci yace ta bashi
wuri ya wuce hakan yasa ta fahimci k'ilan bai jin hausa ta bud'a murya cikin fulatanci tace Don Allah ya
taimaka masu ya kaisu Jimeta, wani kallo yay mata duk da duhu ne yace bazai d'auke suba don ba can
yay ba, rok'on shi ta shiga yi tace zasu biya shi yana kallonta yace yasani ko Aljanu ne su zai d'aukesu ta
shiga yi mashi rantsuwar Mutane ne su zasu koma garin su ne, shiru ya d'anyi kafin ya tambayi nawa
zata bashi ya kaisu da sauri tace dubu ukku d'an bud'e ido yay alamar mamaki sai kuma ya tambayeta ta
tabbatar zata bashi hakan tace eh wllh yace to su hau cike da jin dad'i ta hau yi mashi godiya yace ba sai
ta gode mashi ba su da zasu biya, saida ta taimaka ma Haulat ta hau suka saka kayan su sannan itama ta
hau ya tambayi sun hau tace mashi eh sannan ya juya amalanken suka tafi Fatuu sai sauke ajiyar zuciya
take Haulat dai tay zuru zuru jininta akan a kaifa yake in ba gani tay sun fita daga garin ba gaba d'aya
hankalin ta bazai ta6a kwanciya ba, Anata sallar Asuba suka isa Jimeta suna shiga garin yace to su sauka
anan zai aje su Fatuu ta rokeshi ya kaisu tasha sai sun je can zata fitar da kud'in da zasu biyashi basu
dasu a hannu, fuska d'aure yace dama tasan ba kud'in suka ce zasu bashi tace ai akwae kud'in a cikin
banki suke a tashar motar tasan ana fitarwa sai su bashi yana kunkuni yace to gaskiya saidae su k'ara
mashi dubu biyu sannan ya kaisu da sauri Fatuu tace suje zasu bashi, Lokacin da suka isa cikin sa'a akwae
mai Pos Fatuu ta fitar da sauran kud'in da suka rage mata gaba d'aya wanda Baffanta yace ta bari 20k ta
biya mai amalanken dubu biyar d'inshi yana ta washe baki yay masu Allah ya kiyaye, Cikin sa'a suka samu
Motar da tay Katsina direct suka hau aka shigar masu da kayan su aka ce su shiga seat d'in baya su
zauna, bayan sun zauna zuru sukai kowacce kirjinta na bugawa zuciya na raya masu za'a zo a kama su sai
Addu'oi suke acikin ran su, shiru shiru Mota bata cika ba har gari yay haske gaba d'aya tsoro ya kama su
can Fatuu tace ma Haulat su sauka su hau ta Kano kawae tace to anata ce masu su k'ara hakuri mana ta
cika suka ce sauri suke dole aka fiddo masu da kayan su suka koma ta Kano da ta kusa ciki suna shiga
duka Mutum biyu suka k'aru Motar ta tashi har saida Fatuu ta d'an saki murmushi, Sai fatan Allah ya
sauke su Lafiya.

Koda Yadikko ta shigo da safe sam bata kula da babu su a saman gadon ba duk tunaninta sunyi salla sun
koma bacci, sai bayan da ta gama had'a Breakfast a falo tace ma Mino taje ta tashe su Suzo su karya in
sun gama sun ci gaba da baccin ko don bak'uwa, lokacin da ta shiga bata ga kowa ba ta dawo ta sanar
mata sam yadikko bata kawo komae ba a ranta tace k'ilan ko sun fita ne ko wurin Amadu, bayan su Mino
sun gama suka wuce Makaranta, har Yadikko ta gama gyara d'akin shiru basu shigo ba tana tunanin
zuwa ta duba su sai ga Kamalu ya shigo amsar masu abun karin kumallo nan ta tambaye shi ko su Fatuu
na wurin su yace a'a su yanzu ma suka tashi da mamaki ta ce to ina suka je da sanyin safiya Kamalu yace
basu nan ne tace eh yanzu aka je taso su aka ga basu nan yace k'ilan wani wuri suka je zasu dawo, tun
dae abun bai damun yadikko har ta fara damuwa ta fara neman su har bathroom d'in cikin d'akin ta
duba duk da tasan ba yadda za'ai su shiga nan su biyu, cikin gidan ta fita ta zaga d'akuna tana
tambayarsu cikin hikima ta yadda baza'a zargi wani abu ba ko ina aka ce basu zo ba, bayan ta dawo d'aki
zaune tay kan kujera tana ta tunanin to ina suka je ne can ta mik'e ta nufi k'uryar d'aki tay tsaye tana
kalle kalle idanunta suka sauka akan babban akwatin Fatuu ta k'ura mashi ido tana kallo can ta ankare da
guda d'aya ne a wurin kuma tasan guda biyu ne, to ina d'ayan ta jefa ma kanta tambaya tare da nufar
wurin shi da sauri, duk iya dubawar da tay bata ga trolley ba nan ta tuna da jakar Haulat da ita ta aje
mata ita da hannunta ta juya da sauri inda ta aje ta idanunta suka gane mata wayam wani irin bugu
k'irjin Yadikko yay lokacin da zuciyarta ta raya mata kodae guduwa sukae in ba haka ba mi zai sa aga ba
kayan su kuma babu su, nan da nan jikinta ya fara rawa k'afafuwanta sukai mata nauyi da k'yar ta koma
falo ta zauna kan kujera ta rafka uban tagumi. Sai Azahar Allah ya sauke su kano baiwar Allah Haulat ta
mugun gajiya anan tasha Fatuu ta siya masu Abinci suka ci bayan sun gama ba 6ata lokaci suka hau
Motar Katsina da gasu nan available sai ka za6a ka darje nan da nan suka hau hanya sai fatan a sauka
Lafiya, kiran duniya Yadikko tay ma layin Fatuu amman sai ace mata a kashe yake har waje ta fita tasa
Kamalu ya kira wai ko laifin wayarta ne kiran yak'i shiga shima yayi mamakin jin har yanzu basu gidan, to
shima dae a kashen aka ce mashi wayan take dole ta dawo cikin gida tama rasa tunanin da zata yi da
k'yar jiki ba kwari ta tashi don yin girki,
Bayan da su Fatuu suka kama hanyar Katsina ne ta bud'e wayarta sakamakon tunanin halin da su
Yadikko suke ciki daya tsaya mata a rai, sak'o ta rubuta ta tura ma Kamalu ta sanar dashi bata son Auren
nan don haka ta koma gida tana tura mashi ta k'ara kashe wayar, lokacin suna tare da Amadu a kopar
gida message d'in ya shigo wayarshi da tsananin mamaki yake karantawa har Amadu ya lura da yanayin
fuskarshi ya shiga tambayar shi ko lafiya ya mik'a masa wayar shima ya karanta, kasa Magana Amadu yay
Saboda tsabar mamaki da Al'ajabi shi yazo biki Amarya ta tafi ta barshi, tare da Kamalu suka tashi suka
shiga cikin gidan don sanar ma yadikko a d'aki suka isketa ta rafka uban tagumi su Mino da suka dawo
daga Makaranta suna zaune suna cin Abinci ita ta kasa ma ko ci don zuciyarta ta gama yanke mata cewa
Fatuu guduwa tay ita da k'awarta tana ganin su Kamalu sun shigo ta mik'e tana tambayar su ko sun
dawo Kamalu ya girgiza mata kai da alamun damuwa ya fad'i mata sak'on da Fatuu ta turo ba shiri
Yadikko ta saki salati tana fad'in dama tayi zargin hakan wllh yanzu ya zasu yi da wannan babbar
matsalar, miyasa Fatuu tay tunanin ta gudu ba tare da ta yi tunanin abunda zai iya biyo baya ba duka
saura yan kwanaki a d'aura Auren, jin hakan yasa su Mino mik'ewa ba shiri jin Adda d'in su ta gudu, gaba
d'aya sun yi jugum jugum sai kiran layin Fatun ake kaman yadda Yadikko ta buk'ata saidae kiran bai shiga
sakamakon wayar da ake cewa a kashe take can Yadikko ta d'aukko wayarta ta kira Baffan su Fatuu
hankali tashe ta sanar dashi abunda ke faruwa yace ya akai tun d'azun bata sanar dashi halin da ake ciki
ba tace sam ita bata yi tunanin guduwa suka yi ba yace gashi nan zuwa gidan, zama su Amadu sukae
haka su yadikkon duk suka zazzauna sai jimami kowa yake suna a haka har Baffan ya dawo, lokacin da ya
shigo da alamun tashin hankali a kan fuskarshi yana shigowa yadikko ta mik'e shima tsayen yay murya na
rawa ya k'ara tambayarta game da abunda ta fad'a mashi a waya nan ta sake kora mashi bayani da
tsantsar tashin hankali yake kallonta can ya tsugunne don kafafunsa nema suke su kasa d'aukarshi
yadikko na ganin hakan ta juya tace ma su Mino da tuni sun fara zubar da k'walla su fita waje ko su shiga
cikin kuryar daki, suna tafiya Kamalu ma ya fara kokarin tashi Yadikko ta ce ya tsaya ya kawo wayarshi
yaga sak'on da ta turon, bayan ya shiga cikin message d'in ya mik'e ya kai ma Baffan nasu hannu na rawa
ya amsa ya k'ura ma screen d'in ido can ya d'ago ya mik'a ma Kamalu wayar ya idasa zaunewa k'asa
idanunsa har sun canza sun yi ja cikin tashin hankali ya fara fad'in "Miyasa inna wuro zata man haka, in
tasan bata son auren ai da tun farko bata nuna ta Amince ba sai ta k'yale mu duk halin da zamu shiga mu
shiga ba sai yanzu da lokaci ya k'ure ba, sam inna wuro bata kyauta mana ba ban ta6a zaton zata iya
aikata haka ba duk da tasan irin halin da hakan zai k'ara jefa mu amman ta za6i mu shiga cikin matsala,
da ina Alfahari da ita don ta damu da damuwar mu tana jin tausayin mu ashe sam ba haka bane tunda
zata iya za6ar k'ara jefa mu cikin mawuyacin halin yanzu ina amfanin haka ya take so muyi, duka saura fa
yan kwanaki bikin nan....." Kasa cigaba yay sakamakon Muryar shi da ta karye kwalla suka fara zubo
mashi da sauri Yadikko tace "Don Allah kar ka zubar mata da hawaye kar hakan ya zame mata matsala
wllh duk abunda kaga ya faru laifin su Zakiyya ne har cikin ranta ta amince da Auran nan amman sune
suka fara cusa mata k'in auran ta hanyar fad'a mata Maganganun da suka tashi hankalinta" nan take ta
kwashe komae ta sanar mashi ba iya wannan ba harda abubuwan da shi Khalid d'in ke mata da gidan
gona daya kaita yasaka mata maganin bacci a lemu duk bata 6oye mashi ba duk da su Amadu na a wurin
gaba d'ayan su sun matuk'ar girgiza da jin hakan kowa ran shi ya sosu ba kamar Baffan nata da tsananin
mamaki yake bin yadikko da kallo kafin rai 6ace yace yanzu dama yaron bai canja hali ba aka fad'a mashi
ya shiryu yadikkon tace wai don ya biya sadaki a fusace Baffan yace biyan sadaki d'aura aure ne da zai
nemi lalata yarinya su Kawu Amadu dae sun kasa cewa komae saidae kowa ran shi ya 6aci da jin wannan
Magana shi dama Kamalu ya tsani Khalid d'in sanin halayen shi marasa kyau da yay shi kam Kawu Amadu
wani irin tausayin Fatuu ne ya kama shi taya nutsattsiyar yarinya kamarta za'a had'a ta da irin wannan
Mutumin nan take cikin ran shi ya goyi bayan guduwar da tayi duk da yana shakkun ba lalle Gwaggo ta
saurareta ba amman tabbas zai kira gwaggon ya k'ara tunzura abun duk yadda za'ai a fasa, shima Baffan
tunani na daban ya fara yi a cikin ranshi yana jin bai kamata ya k'yale a Aura mata wannan Mutumin ba
saidae taya zai dakatar da auren shine abunda ya tsaya mashi a rai, tsam ya mik'e ya fice daga d'akin
yana fita Kamalu ya fara Maganganu kan rashin dacewar Aura ma Fatuu Khalid yana fad'in shi dama
yasan ba wani canzawar da yay za'a cuce ta ne kawai.

Sai wurin la'asar suka iso tun kafin su shigo Katsina Fatuu na hango Welcome to Katsina taji wani irin
sanyi a ranta koda suka shigo har saida ta juya suka had'a ido da Haulat tay mata Murmushi itama ta yi
mata amman fa na yak'e don ta gaji har ba sauran wuri, suna zuwa roundabout d'in Liyafa suka ce a
sauke su anan don in suka wuce tasha tafiyar ta k'ara nisa, bayan sun sauka suka tsaida Keke Napep suka
hau bayan sun fad'i mashi inda zai kai su yaja suka tafi Fatuu sai kalle kalle take sai take ganin kaman ta
shekara da barin garin, tunda suka k'araso bakin Unguwar su gabanta ke fad'uwa har suka iso kopar
gidan, bayan ya tsaya suka fito harda kayan suka biya shi, tsaye Fatuu tay tana zare ido suna kallon juna
da Haulat itama dae gabanta fad'uwar yake don bata san irin tarbar da gwaggon zata masu ba can dae
tace ma Fatun su shiga, Gwaggo na a wurin filin wanke wanke tana yin Alwala gamawarta kenan ta
yunk'ura zata mik'e Fatuu ta sako kai ba tare da tayi Sallama ba, cak ta tsaya sakamakon had'a ido da
sukae da gwaggon da ta ida mik'ewa tsaye, bin Fatun da ido kawai tay saidae a bad'ini ta matuk'ar
razana da ganinta a ranta ta fara tunanin ko gizo take mata saidae kuma ganin Haulat ta sako kai itama
yasa ta gasgata Fatun ce dae, hannu Haulat ta sa ta d'an zunguri Fatuu a hankali suka had'a ido tay mata
alamar taje da ido, aje trolley d'in tay anan slowly ta nufi gwaggon duk ta kame kanta a d'an gabanta ta
tsaya murya na rawa tace "G.. gwaggo......" kallon ta kawae take can kuma ta fara k'ok'arin wucewa ciki
aikuwa da sauri Fatun ta durk'ushe gabanta ta kama k'afarta guda ta fashe da matsanancin kuka tana
fad'in "Don Allah gwaggota ki yi hak'uri ki yafe man nasan nayi maki laifi, ke mahaifiyata ce dama ya'ya
suna yi ma iyayen su laifi kuma su yafe masu Saboda k'aunar da suke masu, kiyi hakuri gwaggo banda
hankali ne banda wayau shiyasa na kasa gane abunda kike jiye mun...." Dakatawa tay tana cigaba da
kukan Gwaggon ta d'age kanta sama tana jin wani iri a ranta har idanunta sun fara tara kwalla, tun da
Fatuu ta tafi bata k'ara lafiya ba kusan kullum sai ta zubar da kwalla har rama tayi Amadu bai fad'i ma
Fatun bane don kar ta tada hankalinta, Allah ya jarabeta da tsananin k'aunar Fatuu kallon Ayshar ta take
mata, ganin tak'i cewa komai ga Fatuu nata kuka yasa Haulat k'araso wa ciki inda suke itama ta duk'a ta
kai hannu ta kama d'ayar kafar itama kwalla suka fara zubo mata cikin muryar kuka tace "Gwaggo don
girman Allah kiyi hakuri ki yafe mata ta gane kuskuren ta na k'in goya maki baya" d'an ta6e baki gwaggon
tay still kanta na d'age sama, cigaba da rok'on ta suka yi can ta sauke ajiyar zuciya tana kokarin maida
kwallan idonta ta saddo kan tana kallon Fatuu da fuskar ta tay jage jage itama kallon gwaggon take, d'an
nisawa tay kafin murya can k'asa tace suje ciki aikuwa da sauri Fatuu ta mik'e ta fad'a jikinta ta
k'ank'ameta tana wani irin Kuka saida dai tasa k'wallan gwaggon zubowa ta d'agota suka nufi ciki ta kalli
Haulat itama tace mata ta taho, wucewa tay da sauri inda kayansu suke ta jawo trolley d'in da jakar ta
sannan ta bi bayansu suna zuwa saitin d'akin Fatuu Gwaggo tace su shiga kafin tay salla har suna had'a
baki wurin cewa to suka nufi ciki Haulat ma ta shiga da kayayyakin, Gwaggo na shiga d'aki kujera ta nufa
ta zauna tay tagumi tama rasa tunanin da zata yi kan dalilin dawowar Fatun don tasan tabbas ba
hakanan ta dawo ba ana saura yan kwanaki a d'aura mata aure dole da dalili can ta mik'e dai ta kabbara
sallar bayan tasa Hijab, bayan ta sallame ta kai hannu saman gado ta d'aukko wayarta da tunda tana
salla taji tana ta ringing tana dubawa taga Amadu ne tabi bayan kiran ringing d'aya ya d'aga bayan sun
gaisa yana d'an inda inda ya tambayeta Fatuu ta iso k'asa k'asa tace mashi eh, dama tun d'azun yake son
ya kira zullumi ko Fatun bata iso ba yasa yak'i kiran sai yanzu da yay tunanin sun isa isowa sallama yay
mata kawai don baisan ko basu yi Magana ba ta kashe wayar, suma su Fatun sallar sukae bayan sun
gama sukae Zaune jugum, bayan da gwaggo ta gama Addu'oi shiru tay kaman mai nazari can bayan d'an
wani lokaci ta k'wala ma Fatuu kira wani kalan fad'uwa gabanta yay ta amsa suna Kallon juna ita da
Haulat har taje d'akin gwaggon tace ta kira Haulat itama ta dawo ta kirata, duk a k'asa suka zauna idon
gwaggo a kansu sai da ta nisa sannan ta fara Magana,

"Miya faru kuka dawo?" Shiru sukai suna kallon juna kafin Fatuu ta sauke idanunta kan gwaggo murya na
rawa tace "b..ban son Auren ne" zuba mata ido kawae gwaggo tay ganin kallon da take mata yasa Fatuu
d'an sunnar da kai can taji tace "Baki son auren, kenan gudowa ki kai?" a hankali ta d'aga mata kai still
gwaggo tay tana kallonta kawae da alama tama rasa mi zata ce mata ne,

"Saura kwana nawa a d'aura maki Auren?" a sanyaye Fatuu ta bata amsa da hud'u, kya6e baki gwaggo
tay tace "Saura kwana hud'u shine zaki ce baki son auren to yanzu da kika zo man nan ni mi zan maki??"
Idonta akan gwaggo idanunta sun kawo kwalla tace "Don Allah gwaggo kar ki bari ayi man Auran nan"
d'an murmushin takaici gwaggon tay kafin ta d'aure fuska a kausashe tace "ni ba abunda zan iya yi maki
yanzu, lokacin da nike tunanin inada yadda zanyi nuna wa ki kai baki son hakan don haka yanzu bakin
Alk'alami ya riga da ya bushe dole ki koma ai maki Auren, kuma ke da kika amince don ki taimaki
Mahaifinki ki fitar dashi daga halin da yake ciki shine yanzu zaki za6i k'ara jefa shi a wani halin saura
kwana hud'u bikin ki kice wai baki so kina da hankali kuwa!" tuni Fatuu ta fara kuka gwaggon ta juya kan
Haulat rai 6ace tace "Ke Haulat ke kika bata shawarar ta gudo ne da kuka taho tare?" Da sauri murya na
rawa Haulat tace "a..a gwaggo jiya bayan munje ne shine da tsakar dare ta tashe ni tace man gida zata
taho lokacin nima na nuna mata had'arin dake tattare da hakan nace tayi hak'uri amman sai tay man
bayanin irin mijin da ake so a aura Matan tace dama kema baki so in ta dawo zaki taimaka mata a fasa,
to da ita kad'ai ma zata taho daga baya nace bari mu taho tare" d'an ta6e baki gwaggon tay tace "to ni
kam yanzu ba abunda zan iya yi kan hakan don haka sai ku tattara ku sake komawa tayi hakuri taje a
d'aura mata Auren kaman yadda tun farko ta amince...." Kuka sosae Fatuu take yi ta fara mata Magiya
tana fad'in "Don Allah gwaggo ki taimaka man wllh ban iya rayuwar Aure da shi in aka aura man shi
mutuwa zan yi d'an iska ne mai neman mata kuma mashayi...." Nan Fatuu ta kashe komae duk abunda
ya ta6a yi mata ta fad'i ma gwaggon, a zahiri sai kace abun bai dake ta ba amman a bad'ini ba k'aramar
kad'uwa gwaggo tay ba da jin hakan ba kamar gidan gonar da ta ce ya kaita har ya zuba mata maganin
bacci ya ta6a ta duk da haka fuskarta ta nuna tashin hankalinta rai 6ace ta tambayi Fatun ta fad'a ma
wani cikin iyayenta wannan zancen da sauri tace eh ta fad'a ma Yadikko amman sai ta bata hak'uri tace
lokaci ya k'ure kuma wai itama tana ganin don ya biya sadaki ne yasa yay mata hakan kamar yadda yace,
a fusace gwaggo tace "Zancen banza kenan! a ina biyan sadaki ya zama aure da har zai samu damar ta6a
ki???" Shessheka kawae Fatuu ke yi gwaggo taci gaba da fad'in "ni dama tun farko abunda na guda
kenan don Kamalu ya fad'a ma Amadu yaron ba nutsattse bane in ba don haka ba wllh bazan tsani yi
maki aure ba, tabbas nasan zan ji ba dad'i don ina son ki yi karatu amman kuma nasan darajar kowace
yarinya d'akin mijinta ne ba kamar zamanin nan da mazajen aure ke wuya sai kaga yarinya ta gama
karatun kuma sai mijin aure ya gagara shiyasa iyaye masu dubara da yarinya ta gama secondary suka ga
tana da tsayayye sai kiga sunyi mata aure sun ce taci gaba da yin karatun a d'akin mijinta don kar a rasa
damar da aka samu, to ke kanki da ace naji an yaba da yaron wllh zan goyi baya ne in kin je can Kya yi
karatun amman Kika watsa man k'asa a ido kika nuna ke kin amince, nasan da niyya mai kyau kikai hakan
amman yanzu baka cewa zaka kashe kan ka don ka raya wani ba kaman akan abunda ansan da matsala
yanzu in akai maki Auren matsala ta biyo baya ke ce a ciki shi kan shi mahaifin naki ba samun kwanciyar
hankali zai yi ba kina cikin matsala shiyasa maganin kada ayi to kada a fara da kin ban dama da nayi duk
yadda zan yi inga an fasan in dae Allah ya nufi hakan in kuma nayi bakin k'ok'ari na naga na kasa sai abar
ma Allah, Yanzu ni gaskiya bansan ya zanyi in tsaida Al'amarin nan ba lokaci ya k'ure" rai a tsananin 6ace
take Maganar ta k'arasa tana girgiza kai Fatuu ta matsa gabanta ta kamo hannuwanta tana cigaba da
rok'onta Haulat sai matsar k'walla take to itama dae gwaggo kasa jurewa tay saida kwallan suka zubo
mata Fatuu nata mata Magiya tana fad'in ita bata san ashe dalilin da ya sa bata son ai mata Auren ba
kenan can gwaggo ta nisa tace mata abar ma Allah komae tayi Addu'a ya tabbatar da abunda yafi zama
Alkhairi ta jinjina kai, mik'ewa gwaggo tay ta fita bada jimawa sosae ba ta dawo hannunta ruke da tray ta
aje masu tace ga Abinci nan su ci ta sake fita sai gata ta dawo da ruwa da lemu ta aje masu kafin ta nufi
bakin gado ta zauna hannunta dafe da ha6arta gaba d'aya kanta ya gama k'ullewa ta rasa tunanin ma da
zata yi, a hankali suke cin Abincin jikin kowannan su ya gama yin sanyi ba laifi sun ci sosae bayan sun
gama atare suka fitar da kayan gwaggo tace suje suyi wanka tunda Magrib bata k'arasa yi ba suka amsa
da to ta bi su da ido gwanin tausayi, Haulat ce ta fara yo wanka sannan Fatuu gaba d'aya sun ji dad'in
jikin su saidae kowa da fargaba a cikin ran shi ba kamar Fatuu, bayan sun canza kaya zaune su kae a cikin
d'akin jigum saida akai sallar Magrib suka fito bayan sun gama sallar gaba d'aya suka 6ingire a kan abun
salla suna baccin gajiya lokacin da akai Isha da k'yar Gwaggo ta tashe su suka yi salla tayi masu Maganar
Abinci duk suka ce basu jin yunwa tace to su hau gado dama Haulat bata ma yi tunanin tafiya gida ba
tunda tsugunne bata k'are ba, Allah sarki gwaggo sam ta kasa ma kwanciya sai kai da kawowa take a
cikin d'akinta wani lokacin ta zauna a bakin gado abun duniya duk ya isheta ba k'aramin k'una ranta ke
mata ba can ta d'auki waya ta kira Mahaifin Fatuu bayan ya d'aga sun gaisa ne take ce mashi yanzu ashe
sun san halin wanda za'a aura ma Fatuu amman suka amince a jefa rayuwar yarinya a cikin matsala
kamar zai kuka ya fara mata rantsuwa yana fad'in harda k'arin hakan yasa shi kwanciya ciwo lokacin da
Ard'o ya fad'i mashi hakan kuma har wurin mahaifin yaron yaje don ya rok'eshi a kan a fasa harda
Maganar halin yaron nashi yay mashi amman sai ya tabbatar mashi da cewa ya kwantar da hakalinshi
yaron ya canza hali ya shiryu shiyasa ma ya nema mashi aurenta ya kuma tabbatar mashi da ko bayan
bikin yaci gaba da yin hali mara kyau shi da kan shi zai d'auki mataki gwaggon ta tambaye shi yaji
abubuwan da yay ma Fatun yace eh Yadikko ta fad'a mashi tace to yanzu ina canza hali anan yace babu
kam, tambayar shi tay yanzu wane mataki zai d'auka ko kuwa a hakan za'a aura mata shi cikin karewar
murya yace shi wllh ya rasa mafita amman har ga Allah bai son ayi mata auran gwaggo na jiyo
sheshshekar shi sake tambayar shi tay an san Fatun ta gudo yace ba wanda ya sani iya su ne tace to
abunda za'ai in Allah ya kaimu yaje ya fad'i ma Ard'o harda dalilin da yasa ta gudon kar ya rufe komae,
d'an jimm yay kafin ya amsa mata da to sukae sallama, koda suka gama wayar cigaba da tunanin mafita
tay gashi Hajiya bata nan bare taje neman shawara jiya da yamma Senator yasa aka tafi da ita Abuja
Saboda ciwon kafar da ya taso ta gaba, k'arshe dai Alwala taje tayo tazo ta kabbara salla don neman
mafita wurin Allah, Washe gari bayan da su Fatuu sukae salla komawa sukai sai da gwaggo ta gama
breakfast taje ta tashe su sukai breakfast d'in bayan sun gama suka gyara gidan tsaff gwaggo na d'aki
bata je aiki ba dama kwana biyu tana gida Saboda bata jin dad'in jikinta sai jiya ta koma yau kam gaba
d'aya bata jin dad'i damuwa tay mata yawa hakan yasa ta kira ta fad'a bazata samu zuwa ba, har d'akin
ta suka je don su gyara tace su bar shi in ta tashi sai a gyara, Wanka su kai Fatuu ta tsuke cikin jeans da t-
shirt har ta jita ta dawo Fatunta ta da duk da da sauran rina a kaba ta ba Haulat doguwar rigar Material
don kayanta masu nauyi ne duk na cin biki ne ta tafi da su, tsaye Fatuu tay gaban dressing mirror tana
kallon kanta tana ce ma Haulat wai kaman yadda fuskarta ta rame hips d'in ta ma sun rame don ita ji
take kaman sun rage girma dariya kawae Haulat d'in ke yi can ta tuno da abunda Khalid yay mata ta
d'aure fuska ta dawo gefen gado ta zauna Haulat na ganin yanayinta ya canja ta fara tambayar ta abunda
ya faru idanun Fatuu cike da kwalla tace ta tuna abun da Khalid yay mata ne yanzu shikenan ya gane
mata jiki Haulat ta dafata tace "ki daina damuwa k'awata yaje don kan shi kuma bi'iznillahi ta'ala ya yi
mashi ganin farko kuma na k'arshe" a sanyaye Fatuu tace Allah ya sa suna haka wayarta ta fara ringing ta
d'aukko tana duba mai kiran ganin Abbas ne yasa tay picking bayan sun gaisa yace "Mom Zarah Amarya
kwana biyu inata jira baki turo man invitation card ba shiyasa nace bari in kira in ji Date d'in" shiru ta
d'anyi sai kuma tace mashi "ai na dawo gida fa" da alamar mamaki yace "wane gida?" Tace "Nan
Katsina" still da mamakin yace "ba dae har an d'aura Auren ba anan zaku zauna ne?" Har saida Fatun tay
yar guntuwar dariya jin abunda yace kafin tana tura baki tace "a'a ba'a d'aura ba banson auren ne shine
na gudo jiya" Abbas yace "What! Kin gudo?" kaman zatai kuka tace "Eh Ya Abbas ni ban son Auren" tana
jin yadda ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yayi d'an shiru kafin ya tambaye ta yanzu haka tana gidan su
tace eh yace Ok gashi nan zuwa yanzu.................

*ASM Bk2033*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


.........After some minutes sai gashi ya kira yace mata yana waje tace to, babban gyale ta d'aukko a cikin
wardrobe ta d'aura saman kayan jikinta tace ma Haulat tana zuwa ta d'aga mata kai, bayan ta fito daga
d'akin saida ta shiga d'akin gwaggo har sannan tana kwance saman gado ta fad'i mata ga Ya Abbas nan
yazo zata je gwaggon ta d'ago da kai ta kalleta tace kiran shi tay ta fad'i mashi ne Fatun tace "a'a d'azun
ya kirani wai ban tura mashi Iv ba har yanzu shine nace mashi ai na dawo ya tambaye ni yadda akai shine
nace ban son Auren ne na gudo" ta k'arasa tana d'an sunnar da kai, shiru gwaggo ta d'an yi kamar mai
tunanin wani abu sai kuma ta d'aga kai tace taje, tana fitowa daga cikin gidan Abbas ya bud'e kopar
Motar ya fito idon shi akanta har ta k'araso ta tsaya d'an gaban shi tana ta kikkafta ido ta gaishe da shi,
da alamun mamaki yace "Mom Zarah so u'r serious kin gudo d'in dae kenan" d'an tura baki tay bata ce
komae ba yace "Amman miyasa kikai hakan ba kince man kin amince bane Saboda Daddy en ki yanzu da
kika gudo baki tunanin zaki k'ara jefa shi a wata matsalar da ta fi wanccan?" Yamutsa fuska ta fara nan
da nan idanunta suka kawo kwalla cikin rawar murya tace "Ya Abbas ban son wanda za'a aura man d'in
ne....." Katseta yay "ai nasan hakan Zarah kuma dama ai ba don kina son nashi kika amince ba why saida
aka kusa zaki hakan" ya kafeta da ido rasa abun ce mashi tay kawae sai ta saka mashi kuka tana fad'in
"Ya Abbas mai neman mata kuma mashayi ake son aura man fa" waro ido Abbas yay da alamun ya d'an
razana da jin Maganar tata ita kuma sai kuka take, nuna mata other side en Motar yay yace su shiga ciki
ta juya tana matsar k'walla shima ya juya ya shiga, bayan ta shiga cigaba da kukan tay Abbas da shima ya
shigo yace mata is ok ta daina kuka, d'an tsagaitawa tay yanata kallonta yace "Mom Zarah ya akai kika
san abunda kika fad'a game da shi" shiru tay tana tunanin ko ta fad'a mashi shima tunda ta ga da ta fad'i
gwaggo hakan ta saukko Abbas d'in ya lura kaman tana 6oye wani abu hakan yasa yace mata kar taji
komae ta fad'a mashi yankewa tay gwara ta fad'i mashi kawai ta d'aga kai ta kalli gefen shi cikin muryar
kuka ta fara fad'i mashi tiryan tiryan tun farko abunda ya fara mata har zuwa gidan gonar da ya kaita da
washe gari da suka dawo daga wurin gyaran jiki tana kai wa k'arshe ta sake fashewa da kuka mai cin rai,
iya girgiza Abbas ya girgiza da jin abunda ta fad'an fuskar shi har ta nuna yama kasa Magana sai kawae
ya maida kan shi jikin heardrest ya d'age sama wani irin bak'in ciki ne ya turnuk'e shi, ya d'an d'auki
lokaci a hakan kafin ya sauke kan yana kallonta sai kuka take hannu ya kai ya bud'e glove box ya curo
tissue ya yagi mai d'an yawa bayan ya maida ya mik'a mata yace tayi shiru ta daina kukan hakanan, amsa
tay ta fara goge fuskar saida ta gama ta ruk'e tissue d'in a hannu sannan ya fara mata magana cikin
murya mai tattare da 6acin rai yace "But Mom Zarah are sure daga hakan bai cutar dake ba?" ta fahimci
mi yake nufi hakan yasa ta fara girgiza kai tace "Wllh daga hakan bai man komae ba, ko lokacin da na
gane yasa man maganin bacci ina mashi Masifa har nace mashi Mazinaci shine ya fara man fad'a har
yana cewa da shi Mazinaci ne ai da bai k'yale ni ba duk da damar da ya samu" tana kai k'arshe ta d'ukar
da kanta d'an yamutsa baki kawai Abbas yay cike da takaici, suna cikin hakan sai ga Haulat ta fito ta
zagayo side d'in da Fatuu take ta d'an kwankwasa glass tana ganinta ta bud'e kopar ta d'an duk'a kan ta
ta gaida Abbas da k'yar ya amsa mata tace mashi dama gwaggo ce tace tana Magana yace Ok gashi nan
zuwa daga haka ta juya ta koma, kallon Fatuu yay suka had'a ido yace su je a tare suka fito daga cikin
Motar, lokacin da suka shiga Parlon gwaggon na zaune tayi mashi sannu da zuwa ya amsa yana kokarin
zama, nuna ma Fatuu wuri tay tace ta shiga ta zauna ta kalli Abbas cike da damuwa tace "d'ana Abbas
tayi maka bayanin abunda ke faruwa ne?" d'aga mata kai yay alamar eh ta sauke Ajiyar zuciya taci gaba
"abun dae sam ba dad'in ji gashi ni na rasa mafita shiyasa nace a kira man kai koda shawarar da kake
ganin zaka bani, na so ace Hajiya na nan to kuma bata nan gashi lokaci ya riga ya k'ure amman sam bai
kamata ta auri Mutumin nan ba tunda daga ji baida hali" girgiza kai Abbas yay yace "tabbas bai dace ta
aure shi ba gaskiya, amman su can yanzu da ta taho mi suka ce ne?" d'an yarfa hannu tay tace "to jiya
dae da daddare munyi Magana da Babanta yace Matar tashi ta fad'a mashi dalilin tahowar Fatuun ya
nuna shima bai son ta auri Mutumin saidae baisan taya zai dakatar da Al'amarin ba, anan nake tambayar
shi ko mutan gidan nasu sun san Maganar tahowar tata yace ba wanda ya sani to dae nace ya je ya sanar
da Ard'on komae dake faruwa, har yanzu dae bai kira ni ba balle in san halin da ake ciki" sigh Abbas yay
yana d'an jinjina kai kafin yace "Yanzu za'a jira shi ne aji ko akwae abunda kike ganin za'a yi?" a sanyaye
tace "eh to ni da na yanke shawarar zan tafi can garin ne gobe gwara ayi wacce za'ai tun kafin ranar
d'aurin auren tunda su can dangin Angon bama su san ita Fatuun ta taho ba" d'an biting lower lip d'in shi
yay ya k'ura ma carpet d'in k'asan parlon ido da alama yana tunanin wani abu ne can ya d'ago yace mata
shikenan ta shirya gobe idan Allah ya kaimu zai zo da Asuba sai suje can garin tare gwaggon tace "a'a
d'ana Abbas ai ba'ayi haka ba kaima ai kana da hidindimun ka da za'a k'ara d'aura maka nauyin tafiya
dama dae shawara nike nema don kaina ya k'ulle gaba d'aya gashi dama ba cikakkar lafiya ce da ni ba"
tana k'arasa Maganar tasa k'asan rigarta tana goge kwallan idonta, tsananin tausayin ta ne ya kama
Abbas d'in ya shiga bata baki yana ta kwantar da Hankalinta in sha Allahu Allah zai kawo mafita duk
yadda za'ai baza'a yi auren nan ba, sosae gwaggo tay mashi godiya da Addu'oi daga baya yay mata
sallama yace sai yazo goben suka fito gaba d'aya, daga bakin kopar fita gwaggo ta komo ciki ita kuma
Fatuu ta bishi har waje, jikin Motar ya jingina yana kallonta kanta a k'asa gaba d'aya duk tausayin su yake
ji yasan dole zuciyoyin kowannansu na cikin wani hali, kiran sunanta yay ta d'ago suka had'a ido yace ta
daina damuwa in sha Allahu zai yi iya bakin k'ok'arin shi wurin ganin ba'ayi mata Auren da mutumin ba
tay d'an murmushi had'i da jinjina mashi kai yace gobe in Sha Allah zasu je can ai masu Addu'a tace to
daga haka yace ta shiga ciki ta saida tay mashi Allah ya kiyaye hanya sannan ta juya ya bita da ido har ta
shige cikin gida kafin ya koma cikin Motar yaja ya tafi, tana shiga d'akinta cike da farinciki ta nufi gado ta
fad'a tana sakin murmushi Haulat dake kallonta ta tambaye ta ya akai ta fad'i mata game da tafiyar da
Gwaggo zatayi da Ya Abbas itama d'an murmushin tay tayi fatan Allah ya kaisu lafiya yasa ayi nasara
suna cikin haka wayar Fatuu tayi ringing ta kai hannu ta d'aukko tana d'aura idonta akan screen d'in
wayar mood d'in ta ya canza tay rejecting kawae ta kife wayar Haulat dake bin ta da ido ta tambayi waye
kaman bazata fad'i mata ba sai kuma tace "wanccan d'an iskan ne" nan take haulat ta fahimci wanda
za'a aura mata ne, k'ara kira yay Fatun ta buga uban tsoki ta kai hannu a fusace ta d'auki wayar ta saka
ta a silent kawae ta sake aje ta ganin yadda ranta ya 6aci yasa haulat yin d'an murmushi tace "ina ma ace
Ya Haisam yaji kawae yazo yasa a d'aura auran da shi" wani kallo Fatuu ta bita da shi baki bud'e Haulat
d'in ta d'age mata gira tace "in shine ai nasan zaki yarda ko?" D'an ta6e baki Fatuu tay tace Uhmm
kawae Haulat dake dariya tace "ko yanzu kin daina son nashi ne?" Shiru ta d'an yi sai kuma ta sauke
ajiyar zuciya yanayin fuskar ta ya k'ara canzawa a sanyaye tace "kema Haulat ai kin san in nace na daina
son shi nayi k'arya tunda son gaskiya nike mashi kawai dae nasan ba ta6a samun shi zanyi ba zan ta
wahala ne shiyasa na rarrashi zuciya ta kawai" d'an girgiza kai Haulat tay itama dama ta fad'a ne kawae
tasan har Abada ba lalle ta daina son Ya Haisam ba saidae ta hakuran kawae,
"Amman in ace yace zai aure kin zaki yarda" wani kallo Fatuu tay mata tace "Fad'a ma 6ata baki ne
Haulat" gaba d'aya su kai yar dariya Haulat tace "in Allah ya kaddaro mijin ki ne duk aje a dawo wllh sai
kin aure shi kina zaune zai kawo kan shi ma" d'an ta6e baki Fatuu tay tana murmushi ta gyad'a mata kai
kawae, a ranar da daddare gwaggo tace suzo su je gidan su Haulat tace ma Fatuu ta d'aukko kayan da
zatai amfani dasu don a can zata zauna kafin ta dawo Fatun tace to, bayan sun je Innar su Haulat ta
matuk'ar girgiza da jin abunda ke faruwa da gwaggo ta mata bayani, itama sam bata goyi bayan ai auran
ba daga baya tay ma gwaggon fatan sa'a, tare dasu Fatuu ta dawo zasu kwana nan da safe sai su koma
gidan su Haulat d'in. Washe gari ana gama sallar Asuba Abbas yazo ba 6ata lokaci gwaggo dasu Fatuu
suka fito bayan an rufe gidan suka shiga cikin Motar Abbas ya gaishe da gwaggo tay mashi ya kwanan
iyali su Fatuu ma suka gaida shi, a daidai bakin lungun su Haulat aka aje su suna d'aga masu hannu suna
Allah ya tsare saida suka ga tafiyar au sannan suka nufi gidan.

Alhamdulillah kafin la'asar wurin k'arfe ukku na rana suka isa da yake Motar gida ce ba tsaye tsaye tun
suna akan hanya Abbas ya tsara ma gwaggon abunda yake ganin yakamata suyi har ya nuna ace Fatun
tana da wanda suke son juna hakan zai sa asamu sauk'in matsala tsakanin Mahaifinta da kuma shi
Ard'on in Allah yasa aka janye batun Auren sosae gwaggo ta fahimce shi, a kopar gidan Motar Abbas ta
parker duk idanun mutanen dake wurin ya dawo kanta gwaggo ce ta fara fitowa akan idon Kamalu da
Amadu dake zaune a bakin teburin saida raken shi aikuwa da sauri suka tashi suka nufo ta baki washe
itama dariyar take masu, a gabanta suka tsaya suna mata sannu da zuwa tana amsa masu lokacin Abbas
ya fito shima yana sanye da manyan kaya shadda ash da hula da takalma yayi too match Amadu na ganin
shi ya nufe shi da Murmushi shima murmushin yake mashi yana zuwa ya mik'a mashi hannu suka gaisa
Kamalu ma ya zagaya suka gaisa, tuni su Mino sun je sun fad'o ma Yadikko zuwan gwaggon, kallon su
Abbas gwaggo tay tace mashi su shigo suka nufi hanyar shiga gidan ta lura da kallon da Mutanen gidan
dake zaune a wajen ke mata basu da niyyar yi mata ko sannu da zuwa hakan yasa itama ta share su sai
Abbas ne ke d'aga masu hannu yana gaida su suma suna d'aga mashi, suna shiga Yadikko ta tarbe su da
fara'a tana masu sannu da zuwa tace su shiga ciki mutan gidan kaman ko yaushe sai lek'owa suke suna
ba ido hakkin shi yan kad'an ne suke ma gwaggon sannu da zuwa itama ta gulma, a falo suka zauna
yadikko ta zauna a k'asa tana gaishe su fuska a sake Abbas ya amsa mata su Amadu ma suka zazzauna
shiru ta d'an biyo baya can gwaggo tace "sai muka ga Amarya ta dawo" d'an rausayar da kai yadikko tay
bata ce komai ba gwaggon ta tambayi ina Baffan Fatuu tace yana d'aki bai jin dad'i ne bari tay mashi
Magana, saida ta fara kawo masu Abinci da fura sannan taje ta fad'o ma Baffan game da zuwan nasu
suka dawo tare yana biye da ita, bayan sun shigo a k'asa ya durkusa yana gaida gwaggon da fulatanci ta
amsa Abbas ma ya gaishe dashi suka k'ara yin shiru Yadikko ce ta katse shirun da ce masu su ci Abincin
gwaggo tace ba damuwa zasu ci basu jin yunwa ne don sun ci Abinci a hanya, maida idon ta tay kan Baffa
da ya sadda kai k'asa ta tambaye shi yayi ma Ard'o Maganar halin da ake ciki ya d'ago yace eh,

"To ya kukai da shi ne?" Gwaggo ta tambaya shiru ya d'an yi yana motsa baki kafin cikin rawar murya
yace "ran shi ne ya 6aci yace wai ai ba wani abu bane ita tamkar Matar shi ce tunda ya biya sadaki, yanzu
haka yau zuwa gobe ya bani in je in dawo da ita in ba haka ba ko bata nan za'a d'aura Auran wai sai mijin
nata yaje ya d'aukko ta k'arshe ma cewa yay mu muka k'ulla komae muka sa ta gudu duk yabi mutan
gidan ya fad'a masu mun sata ta gudu" wani murmushin takaici gwaggo tay ta maida idonta kan Abbas
da shi ma 6acin rai ke kwance akan fuskar ta shi tace "d'ana Abbas kaji wani son zuciya ko" jinjina mata
kai yay kawae gwaggon tace "to sam bazan yarda a lalata ma yarinya rayuwa ba wllh tunda shi kan shi
kawae ya sani..." Maida idonta kan Baffan tay ta tambaye shi ance yaron a Jimeta yake ko yace mata eh
yaron chairman ne ta kalli Abbas tace ya ci Abinci in sun huta sai suje Jimetan farko cewa yay ya k'oshi
Baffan Fatuu yace don Allah ya ci sun kwaso hanya kuma yace bazai ci Abinci ba sai a lokacin gwaggo ta
gabatar masu da Abbas a matsayin abokin Haisam duk sukai mashi godiya suka ce Allah ya bar zumunci,
ba laifi ya ci Abincin ba kamar da yake yadikko akwae tsafta d'akin tass yake suma tsab da su bayan ya
gama ne Baffan yace su je d'akin shi sai ya huta yace to suna fitowa daga falon idon Abbas ya sauka akan
Mino dake zaune da k'annanta a gefe don yadikko ta hana su shiga murmushi yay ganin sak fuskar Mom
Zarah ya kirata ta mik'e taje gaban shi itama tana mashi murmushi ganin yana yi mata, dafa Shoulder
d'in ta yay yace ya sunanta tace mashi Ameenatu amman Mino ake ce mata ya tambayeta tana zuwa
makaranta tace mashi Eh aji ukku ma take, sake tambayar ta yay yaushe itama zata zo Katsina still
murmushin take tace ai tana son zuwa su Baffane suka hana wai tunda Adda Fatuu na can jinjina kai
kawae yay daga haka ya wuce Baffa dake tsaye gefe yana masu d'an murmushi yay gaba suka nufi d'akin
nashi, bayan tafiyar Abbas gwaggo ma cikin k'uryar d'akin ta shiga ta shiga band'aki ta watso ruwa tazo
ta kwanta don ta rage gajiya saidae tunane tunane sun hanata ta hutan don in dae ba fasa auren nan
akai ba to fa bazata samu kwanciyar hankali ba gashi bata san ya zasu kwashe da iyayen yaron ba. Sai da
akai la'asar wurin k'arfe biyar suka shirya tafiya Jimeta lokacin da ta fito ne ta shiga gaida Yaya duk aka
bita da ido yayar ta nuna mata abun zama ta zauna suka gaisa da ita da sauran Mutanan da ta taras a
d'akin Yaya ta kya6e baki tace ma gwaggon ashe sai suka sa Amarya ta gudu, yar guntun murmushi
kawai gwaggon tayi Yayar tace "to dae ko bata nan sai an d'aura Auren ta gama guje gujenta ta dawo"
still gwaggo bata ce mata komae ba don bata son Maganar tay tsawo k'arshe ma sai ta mik'e tay masu
sallama ta nufi hanyar fita sauran Mutanan duk suka ta6e baki suka bita da d'an iskan kallo bayan ta fita
aka dasa tsegumi har suna cewa a Wurin gwaggon idanun Fatuu suka k'arasa k'ek'ashewa, tana fitowa
waje tay ba tare da ta tsaya gaisawa da Ard'o ba don tasan shima surutan zai mata cikin sa'a kuma bai
fito waje ba ta nufi Mota da tuni Abbas ya shige dasu Amadu da Kamalu da zai nuna masu hanya Baffan
Fatuu dake tsaye yay masu Allah ya kiyaye yasa a dace tace Amin ta shige. Cikin 30 minutes suka isa
gidan bayan Abbas yay horn maigadi ya fito suka gaisa ya tambayi daga ina suka ce su baki ne daga rugar
Baffa Ard'o yana jin haka yace ko dangin Amaryar Khalid ne banza gwaggo tay sai Kamalu ne yace mashi
eh kawae yana washe baki ya juya ya bud'e masu gate d'in suka shiga, har Main falo ya shigar dasu ya
fara kwala ma mai aikin Hajiya kira bayan ta fito yace taje ta sanar ma Hajiya ga bak'i anyi dangin
Amaryar Khalid ne tace to bayan ta gaishe dasu ta juya, bada jimawa ba sai ga Hajiyar ta Fito tana sanye
da doguwar riga jallabiya ta yafa mayafinta ta nufo su fuskarta d'auke da murmushi ta zauna, gaisawa
suka shiga yi a mutunce tay masu an zo lafiya gwaggo tace lafiya lau daga baya suka d'an yi shiru can
tana murmushi tace "an ce man daga ruga ko?" Gwaggo tace "eh amman ba yan rugar bane daga
Katsina muke" Momy tace "Allah sarki yan biki ne kenan, ya hanya an zo lafiya" gwaggo ce ta k'ara amsa
mata da lafiya lou lokacin mai aikin ta kawo masu lemu da ruwa ta aje masu ganin basu da niyyar sha
Momy na murmushi tace don Allah su sha ruwa lokacin gwaggo tace "dama mun zo wurin mai gidanne
in yana nan sai ai mana iso" d'an jimm Momy tay kafin tace "eh yana nan bai dad'e ma da shigowa ba
kuwa" gwaggo tace to don Allah a sanar mashi tace to ta mik'e lokacin su Kamalu suka bud'e bottle
water d'in da aka kawo suka tsiyaya a cup suna sha ita gwaggo ma bata jin zata iya ko shan ruwan in ba
anyita ta k'are ba can sai gata ta dawo bata k'araso cikin parlon ba tace masu bismilla su shigo gwaggo
ce ta fara mik'ewa tace ma Amadu yaje ya shigo da Abbas ya amsa da to, parlon chairman ta kai su yana
zaune shima jallabiyar ce a jikinshi da murmushi yake kallon su suna shigowa ya nuna masu Sofas alamar
su zauna, bayan sun zauna su Abbas suka shigo da sallama ya amsa masu suma ya nuna masu wurin
zama duk suka zazzauna, gaisawa suka fara yi cikin girmama juna daga baya shiru ta biyo baya Chairman
d'in ne yace yaji ance dangin Amaryar Khalid ne daga Katsina ko gwaggo tace "Eh hakane nice kakarta
dake ruk'onta" yana fara'a yace Allah sarki to sun zo lafiya tace lafiya lau Momy ma dake zauna ta k'ara
fad'ad'a murmushin ta tace mata sun zo lafiya ta amsa da Alhamdulillah suka k'ara dan yin shiru, again
Chairman d'inne yace yaji ance suna son ganin shi Allah yasa lafiya sauke ajiyar zuciya gwaggon tay ta
juya ta kalli Amadu tace su jira su a Parlor suka amsa da to had'i da mik'ewa, saida suka fita sannan ta
maida kallon ta kan chairman ta fara Magana "Alhaji nasan ba lalle in kun san abun da ke faruwa ba..."
da sauri suka had'a ido da Momy kafin ya d'an gyara zama ya tambayeta Mike faruwa ne gwaggo taci
gaba "game da auran yaron ku da ita yarinyar waje na, to dae zancen da nike maka ta komo gida tun
shekaran jiya tace bata son auren har tayi ikirarin mutuwa zatai in ka d'aura mata aure da shi" waro ido
sukae gaba d'aya a rud'e Chairman yace to mi yay zafi haka gwaggo taci ba "koma miya faru Alhaji laifin
yaron ku ne shine ya k'ara cusa mata k'iyayyar auren har hakan ta faru sakamakon wasu abubuwa da
basu dace ba da ya rink'a yi mata...." Nan gwaggo ta kwashe komae ta fad'a masu a razane su duka suke
kallon gwaggo har ta gama kora masu bayani chairman yasa hannu ya kama ha6arshi ya kasa cewa
komae ma Saboda Al'ajabi sai faman jinjina kai yake can ya kai hannu gefenshi ya d'auki wayarshi, Khalid
ya kira yace komi yake ya bari yazo yanzun nan gida yana son ganin shi daga haka yay cutting kiran,
ganin yadda duk fuskokin su suka nuna tsantsar damuwa yasa gwaggo tace masu sai hakuri yara ne ka
haife su amman baka haifi halin su ba jinjina kai kawae sukae bada jimawa ba sai ga Khalid d'in don
dama yana kan hanya ya kira shi yayi shigar complete black riga mai dogon hannu da ma6allai harda
necktie sai bakin wando mahad'in rigar da gani daga wurin aiki yake, da yar sallama ya shigo parlon ya bi
bak'in fuskar da ya gani da kallo kafin ya nufi gefen Momy ya zauna suma su Abbas kallon suka bi shi da
shi gwaggo a ranta tana raya gashi dai in ka ganshi a ido baka cewa yana da aibu in ma da abunda za'ai
mashi sharrin shi to rashin jiki ne, gaida Dad d'in shi yay kaman bazai amsa ba sai kuma k'asa k'asa ya
amsa ya kalli Mom d'in shi itama ya gaida ta kafin ya k'ara bin su gwaggo da kallo Chairman ya d'an yi
gyaran murya Khalid d'in ya kalle shi yace bai ga Mutane bane sai lokacin ya gaida gwaggo ta amsa mashi
tun kafin ya tanka ma Abbas ya d'an d'aga mashi hannu alamar gaisuwa shiru ta sake biyo baya,

"Khalid yaushe rabon ka da wadda zaka aura?" Yaji Dad d'in shi ya jefo mashi tambaya idon shi akan
shi yace tun shekaran jiya da ya maidata daga wurin gyaran jiki dad d'in yace shikenan basu k'ara
had'uwa ba Khalid yace a'a jiya ya kirata yana son yaje saidae bata yi picking ba sai kuma wani uzurin ya
taso mashi bai je ba amman d'azun wurin 12:00 yaje sai brother d'in ta yace bata nan sun fita, shiru dad
yay yana d'an jinjina kai idanun shi akan carpet Khalid nata bin shi da ido don ya lura da canzawar da
yanayin fuskar shi tay, d'agowa chairman yay a kausashe yace "miya kai ka gidan gona da ita???" Rasss
gaban Khalid ya fad'i don tambaya ce da bai tsammaci jin ta ba shiru yay ya rasa amsar da zai bashi don
yasan tunda yay mashi tambayar to tabbas yasan yaje da ita gidan gonar, har saida ya sake maimaita
mashi sannan cikin trembling voice yace "b...ba komae just na biya ne da ita" Dad yace "ka biya da ita ka
ci zarafin ta ko!" da sauri ya girgiza mashi kai yace "No Dad na kaita ta ga gidan ne" d'an murmushin
takaici Dad d'in yay gwaggo ma ta kya6e baki Abbas kuwa d'an juyar da kan shi yay gefe wani irin haushi
yake bashi, Dad yaci gaba "shi maganin bacci da ka saka mata a drink fa ko shima duk cikin ganin gidan
ne?" Wani abu Khalid ya had'iya ya shiga motsa baki saidae ya kasa cewa komae ganin haka yasa Dad
buga hannun Sofa ya daka mashi tsawa yace "Am asking my Friend!!!" runtse ido kawae Khalid yay bai
taba zaton maganar zata je kunnan wani ba bare yay tunanin iyayen shi zasu sani can ya kalli Dad d'in
cike da k'arfin hali yace "Dad ban bata wannan ba" duk kowa kallon shi yake Dad d'in ya yamutsa baki
yace Ok bari ya d'aukko mashi Al'qur'ani sai ya rantse mashi, ganin yana kokarin tashi yasa da sauri
Khalid d'in ya dakatar da shi ta hanyar fad'in "No Dad ba sai ka d'aukko ba it's true na saka mata saidae
bada niyya bane sharrin shaidan ne kuma ban cutar da ita ba" komawa yay ya zauna cike da takaici yace
"ka bata maganin bacci ka gane mata jiki har ka ta6ata shine baka cutar da ita ba! Idan aka ma k'anwarka
Sadeeya haka zaka ji dad'i???" cije lower lip d'in shi yay remorsefully yace "am so sorry dad wllh sharrin
zuciya ne tasa naga ai ni zan Aureta amman nasan nayi kuskure don Allah ka yafe man" banza Dad d'in
yay mashi ya juya ya kalli Mom d'in shi da ido tay mashi alamar ya duk'a ya bashi hakuri slowly ya sauka
on his knees ya shiga bashi hakuri can ya d'ago idanun shi sun yi ja yace ba shi zai ba hakuri ba ga dangin
ta nan su suka cancanci ya ba hakuri don su yay ma laifi har suka tako suka zo garin Saboda hakan,
juyawa yay ya kalli Gwaggo ya fara bata hak'uri yana yasan yayi ba daidai ba don Allah su yafe mashi
Abbas dae sadda kan shi yay yana jinjina shi gwaggo ma rasa abun cewa tay can taji muryar Dad yana
fad'in "Don Allah Hajiya ku yi hakuri kaman yadda kika ce yaro ne ka haife shi baka haifi halin shi ba
amman ina mai tabbatar maki zan d'auki kwakkwaran mataki kan abun da ya aikata ai man Alfarmar
hakan" yana rufe baki Mom ma ta d'auka ta hau bata Hakuri can gwaggo ta sauke nannauyar ajiyar
zuciya tace "Hakuri ya zama dole Alhaji tunda aikin gama ya riga da ya gama" gaba d'ayansu murmushi
suka saki suna mata godiya ta sake cewa "Amman Alhaji nima ina son in rok'e ka wata Alfarmar kuma ina
fatan za'a yi man" jinjina kai Dad yay yace in sha Allahu ta fad'i yana ji, gyara zama gwaggo tay taci gaba
"Ina son ka dubi girman Allah ka janye batun auren nan....." Zaro ido sukae shi kam Khalid wani kallo ya
bita dashi cikin yar in ina Dad yace "a... amma Hajiya yanzun nan kika ce fa kin hak'ura kuma na fad'a
maki zan d'auki mataki to miya kawo Maganar a janye batun auren kuma ko baki hakuran bane?" Girgiza
kai tay har idanun ta sun ciko da k'walla tace "dalili na na son a fasa auren shine saboda ba auran had'i
bane auren dole ne za'a ma ita yarinyar kuma nasan duk kun san illolin da auren dole ke haifarwa ba
kamar yanzu da ita yarinyar ta tsani auren har tana ikirarin mutuwa zatayi in aka mata" dakatawa tay
tana goge kwallan da suka fara zubo mata gaba d'aya kan su ya gama d'aurewa ganin tana kuka yasa
Chairman cewa "Hajiya ai abun duk bai kai na haka ba kuma ni nasan tun tsawon shekaru ukku na nemi
auren ita yarinyar don da bakinta ta fad'a man lokacin tana aji ukku na matuk'ar yabawa da komae nata
shiyasa nayi sha'awar ta shigo Family na saidae a lokacin tayi k'arama kuma sai ya kasance shima yaron
nawa lokacin yana k'asar waje bai ida gama karatun shi ba shiyasa sai nace a bari ta k'arasa Secondary
d'inta ala bashshi in sukae Auren sai taci gaba aka kuma amince man" yana rufe baki gwaggo ta d'auka
"to mudai bamu san da Maganar an bada itan ba sai sati biyu zuwa ukku da suka wuce kawae aka kira
mu wai za'a zo d'aukar yarinya an bayar da ita, wllh Alhaji bazan 6oye maka ba rabon da in shiga tashin
hankali irin na jin wannan batun tun rasa Mahaifiyarta da nai bawai ina k'in ai mata aure bane saidae
abu ne da ban ta6a zato ba don nayi tsammanin an bani ita kuma ko za'a raba ni da ita bai kamata a
nuna man fin k'arfi ba, ban ta6a samun sa6anin da har nay fushi da ita ba sai akan auren nan, na zubar
da kwalla har bansan adadin ta ba ba kuma don komai ba sai Saboda amincewa da tayi wanda ita kanta
don bata da yadda zatayi ne Mahaifinta ya kira yana kuka ya sanar mata cewa shima bai son a mata
auren amman mahaifin shi Ard'o yace in har bai amince ba zai yafe shi ne kuma dole ya bar mashi
gida........." Nan gwaggo ta kwashe duk yadda akai har Fatuu ta taho don amata auren da niyyarta na k'in
zuwa biki Saboda bacin ran da take ciki har halin ciwon da take ciki, lokacin da ta gama rufe fuskarta tay
tana ta kuka, sam Chairman bai ji dad'in jin abubuwan da suka faru ba don shi ya d'auka tuni sun san da
Maganar, sai lokacin Abbas ya fara Magana cikin natsuwa da nuna shi mai ilimi ne ya shiga kwatanta ma
Alhajin illar da yin auren zai iya haifarwa tunda har yarinyar ta gudu yanzu to in aka matsa mata za'a iya
ganin ba daidai ba don yanzu kwata kwata abun ya fitar mata a rai a k'arshe ya tabbatar ma da Chairman
d'in tana da wanda take so kuma shima yana sonta bai k'asar don haka shi abunda yake gani a k'yale ta
ta auri wanda take so kawae kar a mata dole don ko addininmu ba'a ce ai ma yarinya dole ba a aure,
shiru Chairman yay hannunshi ruk'e da ha6arshi har Abbas ya gama cike da gamsuwa ya shiga jinjina kai
kafin ya fara Magana "Duk na fahimci bayanan ku kuma har ga Allah ni dama ba wai son zuciya ne yasa
zan had'a auren su ba kawae don yarinyar ta kwanta man ne kuma wllh da ina da wani yaron ba Khalid
ba to da shi zan nema ma auren ta, amman yanzu daga abunda ya aikata mata na fahimci sam basu dace
da juna ba sannan Hajiya ki sani duk abunda bazan so ya faru da yata ba to bazan so ya faru da yar wani
ba tunda d'a ai na kowa ne kuma ta cika yar halak da har ta sadaukar da farin cikinta don mahaifinta ta
k'ara burge ni sosae ta cancanci itama a faranta mata Saboda haka zan maki Alfarma kamar yadda kika
buk'ata matuk'ar hakan zai saka ki farinciki, Hajiya a yanzu na Janye maganar auren su a barta ta auri
wanda take so Allah yasa hakan yafi zama Alkhairi" ido waje Khalid ke kallon mahaifin nashi har ya rufe
baki ita kuwa Hajiya Rabi'atu girgiza kai kawai take sam bata so hakan ya faru ba don tasan wata
matsalar ce zata kunno kai tsakanin Khalid da Mahaifin na shi saidae har cikin ranta Gwaggon da Fatuu
sun bata tausayi.................

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._
*ASM Bk2034*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*Wannan page kyauta ne a gareki Mommy Kubra ki yadda kika ga dama dashi🤩 Allah ubangiji ya bar
mana zumunci Amin*😍

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

..........cike da farinciki gwaggo ta hau yi mashi godiya had'i da Addu'oi yana jinjina mata kai yana fad'in
ba komae haka ma Abbas godiyar yay mashi daga baya gwaggo tace kar dai ya gaji don Allah tana k'ara
neman Alfarmar yaje suyi Magana da Ard'o yace ba komae yanzu dae yamma tayi amman zuwa da safe
yana nan zuwa karta damu duk abunda ya kamata za'a yi sosae suka k'ara yi mashi godiya suka Mik'e
zasu tafi Mom ma ta mik'e jikinta duk ya mutu a sanyaye tace su bari su ci Abinci mana Gwaggo tace sun
gode wllh saida suka ci Abinci suka taho, ita ta rakosu bayan fitar su Khalid ma ya mik'e zai tafi Dad ya ce
bai sallame shi ba ya koma ya zauna, bayan tafiyarsu d'aki Momy ta koma duk ta rasa mi ke mata dad'i ta
d'auki wayarta ta kira su Sadeeya suna can suna shirin Bridal shower da zasu yi gobe ta sanar mata da su
dakata da komai su dawo gida matsa mata tay da tambayar abunda ya faru nan ta kwashe komae ta fad'i
mata ba k'aramin tashi hankalin Sadeeya yay ba Mom na jiyo yadda take ta sakin salati. Tsitt kake ji sai
Ac da tv dake ta aiki Chairman nata d'an jinjina kai da k'afa Khalid kuma ya sadda kan shi k'asa sai da aka
d'an d'auki lokaci sannan Dad yay ajiyar zuciya cikin karyayyar murya ya fara fad'in "Ka kyauta mun
Khalid ka nuna man irin muhimmancin da nike dashi a wurin ka....,amman ka sani ba ni kai mawa ba kan
ka kai mawa, kanka ka zubar ma da k'ima da daraja koda yake dama baka da su don duk mai su bazai
rungumi sa6on Allah ba....." Dakatawa yay har saida Khalid d'in ya d'an d'ago ya kalle shi kafin yaci gaba
"Allah ne shaida ta na fita hakkin ka a matsayi na na uba duk wani hakki na sauke kuma nasan ban yi
maka tarbiyar da zata sa ka rink'a sa6a ma Allah ba hasali ma har Al'qur'ani ka sauke ba sau d'aya ba
sannan kuma ka haddace wasu bangarori nashi masu yawa amman duk da haka ka za6i take sanin da ke
gare ka kake aikata manyan laifukan da Allah ne shaida ta ban aikata su balle in ce abun da nike yi ne
nima ake man...." Kwalla ne suka ciko idanun shi ya sa hannu yana gogewa sosae hankalin Khalid ya tashi
sai zare ido yake kallonshi Dad yay yace "Khalid ka rasa abun da zaka rink'a aikatawa sai Zina!! duk da ka
sani ka karanta kasan illolinta k'asan hukuncin mai aikata ta, mina rage ka dashi ne a rayuwar nan? Duk
wata ni'ima Allah ubangiji yayi maka ita ya baka lafiya ya wadata ka ta yadda idan mata hud'u kake so ka
aura a rana guda zaka iya amman shine ka za6i sa6a ma wanda yay maka wannan baiwar, Ya Allah! d'ana
na ciki na shi ke neman mata shi ke shaye shaye....." Muryar shi ce ta karye ya fashe da kuka a gigice
Khalid ya saukko ya durk'ushe a gaban shi ya fara fad'in "billahi Dad kaji na rantse maka na daina tun last
Maganar da mukae da kai akan yarinyar nan Danejo ban k'ara aikata hakan da kowa ba, Yes nasan in na
6oye maka bazan 6oye ma Mahallici na ba ina ta6a mata kuma nasan hakan baida kyau kawae son
zuciya ne amman nayi maka alk'awarin na daina daga yau Dad kuma ko shaye shaye da kace shima
nasan ina yi amman wllh na rage kaji na rantse, don Allah Dad ka daina man kuka kar abun ya k'ara man
yawa" dakatawa yay yana goge k'wallan dake zubo mashi duk wannan abun akan idon Mom da tun
d'azun ta shigo tana tsaye gefe itama kukan take jin sheshshekar ta yasa Khalid juyowa ya hau rokonta
kan ta taya shi rok'on Dad kar ya k'ara yin fushi da shi girgiza kai kawae take dama dalilin auren Fatuu
suka k'ulla yarjejeniya har ya amince yasa suka shirya da Mahaifin nashi yanzu kuma ga wannan,
matsawa Mom tay itama ta duk'a suka taru suna ta bashi hak'uri, sosae fasa Auren ya ta6a mashi zuciya
don yarinyar ta shiga ran shi kuma yana tunanin ta silar ta Khalid d'in zai natsu to amman duk da da laifin
Khalid d'in yasan haka Allah ya k'addara yarinyar ba Matar shi bace, can ya sauke nannauyar ajiyar zuciya
ya d'ago ya kalle su d'an murmushin takaici yay yace ma Khalid "Ka tashi kaje komi kai don kan ka kuma
kowa yay da kyau zaiga da kyau sannan ka sani kayi ma kanka don ban tunanin zaka k'ara samun
nagartacciyar Matar aure kaman Yarinyar nan kuma ba baki nay maka ba wllh I assure u sai kayi da na
sani u should mark my words" daga haka ya mik'e yay hanyar Bedroom d'in shi ya shige, yana shigewa
Mom ma ta mik'e ta bi bayan shi idon Khalid a kan ta, ya rage saura shi kadae tunanin rayuwarshi ya
shiga yi tabbas yasan bai kyauta ma kan shi ba abubuwan da yake yi daga zuwa karatu ya biye ma
gur6atattun abokai ya canza daga halayar shi mai kyau zuwa maras kyau tabbas yasan ya cuci kan shi, a
hankali tunanin shi ya gangaro kan Maganar Dad d'in shi ta k'arshe da ya ce sai yay dana sanin rashin
Auren Fatuu ko bai fad'a mashi ba shi yasan yayi asarar mace har mace yarinya ce mai tarin baiwa lokaci
guda suffarta ta fara mashi gizo ya dingi tariyo lukkuttan da suka kasance a tare yanzu shikenan ya
rasata! Wani Sarawa kan shi yay mashi da k'yar ya yunk'ura ya mik'e hannunshi guda dafe da gaban kan
shi ya nufi hanyar fita daga parlon, Uhmmmm dama ance rashin hakuri na rana guda kan iya ja ma
mutum dana sani na har Abada Bature kuma yace Once Opportunity lost would never be regain, Allah ya
kiyashe mu aikin dana sani ya k'ara shirya mu ya shirya mana zuri'a Amin ya hayyu ya kayyum.

Cike da farinciki Gwaggo ke sanar ma dasu yadikko da Baffa lokacin da suka koma kowa yay murnar jin
hakan don abu ne da basu tsammaci fasuwar shi cikin sauk'i ba saidae kuma a d'ayan bangaren na
zuciyoyin su suna fargabar abunda zaije ya dawo in Ard'o ya sani gwaggo ce ta nuna su kwantar da
hankalin su in sha Allahu komae zai zo cikin sauk'i kaman yadda ya faru yanzu. Washe gari Misalin k'arfe
11 na Safe sai ga Chairman Alhaji Lawal harda Hajiya Rabi'atu a Fadar Ard'o suka sauka yasa aka kira
kowa manyan gidan harda mata su Yaya da Gwaggo da Baffan Fatuu Abbas da dai sauran su bayan an
gaggaisa a nutse cikin Fahimta ya bayyana masu ya janye Maganar aure Saboda yarinyar bata so tana da
wanda take son Aure aikuwa nan aka fara zantuttaka Ard'o yace sam baza'a fasa auren ba wllh Yaya ma
a harzuk'e take fad'in ba'a fasa shi su za'a maida kananun mutane aja masu abun kunya, harda ce ma
Alhaji Lawal duk wannan makarkashiya ce ba wani wanda yarinya ke so komae tsarawa akai don wata
manufa ta daban, gwaggo bata tanka ba Abbas ne ya shiga nuna masu da gaske ne tana da wanda take
so bai K'asar ne shi Amininsa ne kuma da ya dawo zai zo a d'aura masu auren, da k'yar Alhaji Lawal yasa
kowa ya natsu nan ya shiga nuna masu illar dake tattare da yi ma yaro auren dole tunda har bata so to a
kyaleta shi bai ji komae ba don yasan komae mukaddari ne daga Allah, Allah ya k'addaro ba Matar yaron
shi bace tun bai rufe baki ba Ard'o yace sam fa yana raye hakan bazai faru ba dole abi Maganar shi ai ba
itace ta farko da aka fara za6a ma miji ba kuma suma sauran ai basu rasa wad'anda suke so d'in Yaya sai
k'ara tunzurashi take tana Kumfar baki haka wasu daga cikin yan uwan Baffan Fatuun ma k'arshe dae da
k'yar Alhaji Lawal ya shawo kan Ard'o ta hanyar nuna mashi ita yarinyar a birni ta taso ba za'a had'ata da
sauran yara na nan ba kuma a birni in hukuma taji za'a ma yaro auren dole baiso to kuwa d'aukar
kwakkwaran mataki suke don har kotu ake zuwa don haka gwara su kyaleta, abun ka da mutumin k'auye
da tsoron hukuma ta haka ya samu suka sassauto k'arshe Ardon yace yaji za'a fasan amman sai dae a
d'aura da wanda aka ce suna son juna don tayi girma da yawa ba aure kuma shi karatun nasaran ai ana
yin shi ko bayan anyi aure ko, har saida cikin Abbas ya Murd'a shi da ya tsara hakan suka d'an saci kallon
juna da gwaggo, da k'yar cike da k'arfin hali yay masu bayanin bai nan ne yaje yin wani aiki ne shiyasa ayi
hakuri ya dawo Ard'on yace ai ko miji bai kusa ana yin aure ganin yadda ya d'auki zafi sosae yasa Alhaji
Lawal sa baki yace ayi hakuri ya dawon sai ita yarinyar ta fara ma karatun ta da k'yar dae aka tankwara
kafaffen tsohon harda kukan shi Yaya kam kamar ta had'iya zuciya ta mutu sam Al'amarin bai mata dad'i
ba duk da haka bata hak'ura ba saida ta kawo zancen wai to a maida auran kan Mino mana sosae
hankalin Baffan su ya tashi bashi kad'ai ba har su gwaggo da Abbas saida hakan ya bayyana a fuskokin
su, d'an murmushi Alhaji Lawal yay ya tambayi wacece ita aka ce mashi k'anwar ita Fatun ce still da
murmushin yace ya gode amman ba sai anyi hakan ba a k'yaleta ta auri wanda take so itama sannan ya
tambayi bata karatu ne Abbas ya bashi amsa da tana yi har ta kai J.s 3 ma, Chairman d'in ya shiga fad'i
masu muhimmancin karatun ya'ya mata yace don haka a k'yaleta tay karatun ta, Jama'a zuciyar Yaya
zata buga a fusace tace ma Baffa ai sai aje a kwaso masu kayan su tunda ba gadon su za'a ci ba Chairman
na a barsu ai ko daga baya a turo a d'auka amman Yaya ta kafe sai an d'aukko, tsamm Gwaggo ta mik'e
ta bita da wani mugun kallo bada jimawa ba suka dawo tare da Yadikko dasu Kamalu suka shigo da
akwatunan duk da haka saida tasa aka bud'e kowanne wai kada a nemi wani abu a rasa anan aka ga
kud'in da Fatuu ta saka Yadikko tace shi Khalid d'in ya bata su ranar da ya zo chairman ya jinjina kai, daga
baya taro ya tashi wasu na farinciki yayin da Zuciyoyin wasu ke k'una aka fitar masu da akwatunan suka
tafi. A hayye shagali zo kaga farinciki wurin su Gwaggo har bai 6oyuwa. Washe gari Juma'a yanda kasan
ranar ake bikin don kuwa musamman Baffa ya yanka masu k'atuwar tunkiya su gwaggo aka hau suya
wad'anda suka ga zasu yi ma kan su buk'ulu ba Arzik'i suka shigo akai aikin da su aka yi Abinci mai uban
yawa Yaya dai na can zazza6in bak'in ciki ya rufeta, da rana kowa yaci gayun Juma'a aka ci aka sha harda
lemuna da Abbas ya kawo daga Jimeta da ya je Salla tare dasu Kamalu, a ranar da yamma sai ga
akwatuna guda biyu da kit d'in su daga wurin Chairman yace akai ma Fatuu harda kud'i dubu d'ari kowa
yayi tsananin mamakin hakan duk d'inkakkun kayan da akai mata ne a ciki da wasu abubuwan su
Cosmetics takalma komae saida aka d'ebo gwaggo murna kamar ta zuba ruwa a k'asa tasha wai akace
hassada ga mai rabo taki ranar dae ta shiga tarihin su, sosae Kamalu ya zagaya da Abbas yaga rugan ya
kuma yi hotuna da daddare suka fara shirye shiryen tafiya don dasu Yadikko za'a tafi kamar yadda suka
buk'ata Baffa ma na zaune a parlon Abbas kuma basu kaiga dawowa shida su Amadu ba anan yake ma
Gwaggo Maganar kayan kitchen d'in Fatun yace daga baya zai sawo su a Mota a maido tace hakan yayi
tay mashi Maganar yadda za'ai da kayan d'aki da aka riga aka siya yace wannan ba matsala bane tunda
kayan amfani ne yasan za'a samu yadda za'ai dasu zai tuntu6i wad'anda suka yisu ko zasu fanshe su tace
to duk yadda ake ciki sai ya sanar mata sai kuma kayan gara nan tace kowanne su d'auki d'ai d'ai suyi
amfani dashi buhun shinkafa, taliya, macaroni, aka fiddo su man shanu da su dublan aka zuzzuba su
Mino suka hau rabo sauran gidajen har 6angaren Yaya saida aka kai.

Washe gari ana gama sallar Asuba aka fara shirin tafiya aka zuba kayan da za'a tafi dasu su shinkafa da
akwatunan da aka ba Fatuu a booth bayan duk sun yi sallama da yan gidan suka hau Mota, gwaggo da
yadikko sai su Mino a baya gaba kuma Amadu da Kamalu shi Baffa banda shi sai zai maida kaya yana
tsaye yana murmushi had'i da d'aga masu hannu suka tafi Katsina za tay di6a su Mino sun kasa 6oye
farincikin su yau dae Allah ya kira su zasu je Katsina Yadikko ma bata ta6a zuwa ba haka Kamalu sai fatan
Allah ubangiji yasa su isa lafiya Amin.

KATSINA TA DIKKO DAKIN KARA KUNYA GARE SU BA DAI TSORO BA.

Tun suna kan hanya Fatuu keta faman kira tana tambayar gwaggo sun kawo ina sam bata san da su
Yadikko aka taho ba kuma bata san an fasa Auran nata ba don duk inta kira don jin halin da ake ciki sai
gwaggo tace mata tay ta Addu'a dai ko jiya da ta kira kaman zatayi kuka ta hau rok'on Gwaggo kan ta
fad'i mata wai gabanta sai fad'uwa yake Saboda zullumi nan ma cewa dai tay taci gaba da Addu'a gobe
zasu dawo zata ji komi ake ciki, yau da Asuba bayan sun tashi ne gwaggo ta kirata tace mata su koma
gida ita da Haulat suyi Abinci mai d'an yawa. Kaman dae lokacin da suka je yau ma cikin ikon Allah kafin
la'asar suka iso zo kuga su Mino yan kauye an zo birni sam sun kasa tsaida idanun su a wuri d'aya sai
zuba k'auyanci suke su gwaggo da Abbas na masu dariya yadikko ce kadae bata k'auyanci ita da tay
zaman Abuja amman har Kamalu kasa rufe baki yay, tun suna shigowa gari Amadu ya kira Fatuu ya sanar
mata lokacin da suka isa Unguwar tun kafin su k'arasa kopar gidan suka hangota a tsaye tana sanye da
doguwar rigar atampa ta yafa d'an mayafi a kanta ai koda ta gane sune tun kafin Motar ma ta tsaya ta
nufo ta da sauri, lokacin da tay arba da su Mino da yadikko kuwa wata uwar k'ara ta fasa ta hau tsalle
tana kwad'a ma Haulat kira gaba d'aya gyalenta ma ya fad'i k'asa sai tulin gashinta dake a fake, suma sai
murnar ganinta suke kowa baki yak'i rufuwa sai gwaggo ce ta d'aukko gyalenta dake yashe a k'asa ta
yafa mata a kan, tana cikin murnar take tambayar yadikko an fasa Auren da sauri Mino tace mata eh,
tafin hannuwanta tasa ta rufe baki cike da tsantsar farinciki, gwaggo ce tace to su shiga ciki sai ai
murnar da kyau duk suka juya gwaggo ta kalli Abbas dake jingine da Mota tace ya shigo ya ci Abinci
amman sai yace mata a'a zai k'arasa gida duk yadda tay dashi yak'i yace kada ta damu, sosae tay mashi
godiya da fatan Alkhairi tace sai tazo har gida yanata dae dariya har ta juya sai kuma tace ya d'an jira
zata aiko da sak'o a kai ma su Abdul yace to, har Fatuu zata shige gidan sai kuma ta dawo ta tsaya gaban
Abbas d'in tana ta washe baki kamar gonar auduga da tsananin mamaki tace "Wai ya Abbas da gaske an
fasa Auran?" K'ura mata ido yay da d'an murmushi kaman bazai ce komae ba can yace "Eh an fasa
amman an d'aura maki da ni" waro ido tay baki bud'e ganin hakan yasa shi sakin dariya itama sai tay
dariyar don ta fahimci wasa yake ta sake tambayar shi wai ya akai aka fasan yace mata ikon Allah sun
dogara da shi shiyasa aka samu mafita ta jinjina kai cike da gamsuwa kafin tace "Alhamdulillah" yar
dariya Abbas d'in yay ya jinjina mata kai suka d'an yi shiru sai faman kallonta yake har ta kula ta d'an
yamutsa fuska sai ya fad'ad'a murmushin shi suna haka Haulat ta fito ruk'e da babbar leda ta ba Abbas
tace inji gwaggo ya amsa yay godiya harda tsokanarta wai mai rako Amarya ta gudo ta saki dariya haka
Yadikko ma tace mata da ta ganta, juyawa yay ya bud'e back door ya saka bayan ya rufe ya d'ago suka
had'a ido da Fatuu yana murmushi yace "Wai Mom Zarah ban ji kin yi Maganar Mutumin naki ba" tace
"Wa?" d'age gira yay yace "Wa kike tunanin zan maki Maganar shi ko na Jimetan?" Tura mashi baki tay
yasa dariya tace "Wai Ya Haisam ai ya manta da ni" ta d'an d'aure fuska Abbas dake dariya yace "Haba
shi ya isa ya manta da Mom Zaraah d'in shi kawae nasan k'ilan aiki ne yay mashi yawa" tace "tun fa da na
tafi sau d'aya mukai waya" Abbas yace "kingane bai nan ne Company d'in su sun tura shi wata seminar
ina tunani bai samun isasshen time ne" d'an ta6e baki tay yace "shi kike tura ma bakin?" Yar dariya tay
tace a'a, sigh yay yace bari ya wuce sai sunyi Magana ta d'aga mashi kai tace ya gaida su Abdul sai tazo
ya d'aga mata kai ta wuce gida shi kuma ya shige Mota ya tafi.

Koda ta koma cikin gidan farin cikin suka ci gaba da yi anata murna bakin kowannan su yak'i rufuwa su
Mino sai santin gidan suke basu kad'ai ba har Yadikko da Kamalu gidan ya burge su a d'aki Fatuu ke
tambayar Mino yadda akai aka fasa Auranta tace ita bata sani ba gaskiya, sai bayan da suka huta gwaggo
ta k'wala mata kira anan ta nuna mata Akwatunan da aka bata Fatuu was completely speechless tayi
matuk'ar mamakin jin an bata su a rud'e ta shiga tambayar gwaggon yadda akai aka fasa har aka bata
wannan uban kayan ta kwashe komae ta fad'i mata Yadikko nata yabon kirkin Chairman gwaggon ma
tace wllh ita kanta ta matuk'ar yabawa da karamcin da yay masu ta hau yi mashi Addu'oi tana Allah ya
shirya mashi yaron nashi da sauran yara ita dae Fatuu shiru tay tana bin ta da ido tunowa da Khalid,
gwaggo tace ta kwashe su ta kai d'akinta ta k'wala ma Haulat kira tace su zo ita da Mino, bayan sun
maida su d'akinta ne ta fara k'ok'arin gwada kayan wanda ada ta k'i sosae kowanne ya amsheta su
Haulat nata santin yadda kayan su kai mata kyau tana fad'in ita gaba ta kaita gobarar titi a Jos Fatuu na
dariya tace amman dae ai anyi asarar k'walla galan galan duk suka sa dariya, sai dare Haulat tace zata
tafi gwaggo ta bata su dublan tace ta kai ma innarta tay ma Yadikko sallama tana sai tazo gidan su, Fatuu
da su Mino ne suka rakata har gida, sosae innar su Haulat tay farinciki da jin zancen an fasa tay ma su
Mino an zo lafiya daga baya Haulat ta rako su bakin lungu suka tafi. Washe gari da safe bayan sun yi
Breakfast sai ga kiran Abbas bayan sun gaisa yace mata tace ma su Mino su shirya zai zo ya kaisu su ga
gari, zo kaga murna ba tare da 6ata lokaci ba suka hau shiri Fatuu ta taimaka masu sukai kwalliyar yan
birni Mino ma ita ta bata kaya ta saka koda Kamalu yaji cewa yay aikuwa ba za'a bar shi ba shima ya fara
shiri gwaggo tace ma Yadikko itama to ta shirya tace abun yara ta bisu kuwa tace eh mana ba ganin gari
bane tace to daman tana so, Wurin k'arfe sha biyu na rana yazo d'aukar su duk sun shirya har Fatuu ma
ta d'auki ado da wata fitinannan fitted gown ta Atamfa acikin kayan da aka kawo mata koda ta fito
yadikko taga shigar da tayi ga d'an mayafi da bai rufe ta ba sosae kasa hak'uri tay tace mata gaskiya
kayan sun kamata kuma ga mayafin ba babba ba gwaggo ta k'arasa fitowa daga cikin d'akinta cikin fad'a
take fad'in haka take fama da ita da son saka matsattsun kaya kuma tasan ba kyau, k'arshe cewa tay
kodae taje ta saka babban mayafi ko kuma ta cire kayan ba sai an je da ita ba tana tura baki ta koma
cikin d'aki, yadda Rigar tay mata sai taji data saka babban mayafi gwara ta cireta ta saka wasu riga da
skirt na lace bayan ta d'aura kallabi ta laga mayafin kayan sannan ta fito, koda suka fito waje Abbas na
ganin ta yace ta koma ba da ita za'a ba tunda ita ba bak'uwa bace tasan ko ina, cikin sigar shagwa6a tace
Allah sai an je da ita Yadikko nata dariya yace su shiga Mota yana ta yaba Kwalliyar su Mino da Aysha
suna dariya, Sosae ya zaga gari da su ko ina da yakamata haka ya rink'a siya masu abubuwan ciye ciye
har park and zoo ya kai su da Fatuu taga zasu yi k'auyanci sai ta taka masu burki Abbas ya rink'a masu
hotuna da wayarshi sai yamma ya wuce da su gidan shi sosae Feenah tay murnar ganin su ta tarbe su
hannu bibbiyu bayan sun zazzauna aka shiga gaisawa ta kalli Fatuu cike da zolaya tace "Amarya Sai kika
gudo munata shirin zuwa mu sha biki" duk akai dariya daga baya ta tayata murna tace Allah yasa hakan
yafi zama Alkhairi suka amsa da Amin, bada dad'ewa ba Abdul ya dawo daga Tahfiz yana ganin Fatuu ya
ruga suka rungume juna bayan ya d'ago yace "Aunty Fatuu Daddy yace man an fasa Auran ki ko" kai ta
d'aga mashi ya k'ara cewa "gara da aka fasa dama ban son ki tafi yanzu kin ga sai ki zaman ki anan in ma
zaki Auren sai kawae ki auri Baba Zakee kin ga shi Babana ke kuma Mamana" gaba d'aya aka sa dariya
Fatun tace to shikenan hakan za'ayi, sai bayan Magrib Abbas yazo maida su Feenah na fad'in kamar kar
su tafi sunata dariya harda kayan shafa taba su Mino, Washe gari Monday wurin k'arfe sha d'aya da wani
abu Yadikko da Fatuu suna aikin Abincin rana Yadikko na cikin kitchen Fatuu na daga waje tana yanka
Alayyahu suna fira taji wayarta ta fara ringing Aysha ta kwad'a mata kira tana fad'in "Adda Fatuu an
bugo maki waya" d'an d'aga murya tay tace ta kawo mata, Koda ta kawo mata ta duba screen d'in taga
mai kiran nata har saida ta d'an bud'a ido ta d'ago ta kalli yadikko dake kallonta a bakin Kitchen ganin
yadda ta kame kanta yasa yadikko yin yar dariya tace halan Ya Handsome ne itama yar dariyar tay ta
jinjina mata kai ganin tana niyyar d'auka yasa tace mata ta d'an ke6e mana murmushi kawae tay ta mik'e
tana tunanin inda zata can ta nufi d'akin Kawu Amadu Saboda bai nan suna shago shida Kamalu, a bakin
mattress d'in shi ta zauna bayan tay picking ta karata a kunne, shiru ba wanda yay Magana har bayan
wasu sakannai sannan taji yace "Zaraah" wani yammm taji jikinta yayi harda d'an runtse ido tunda take a
rayuwarta bata taba ganin Namijin dake da murya mai sanyin dad'i ba irin ta Haisam, a hankali tace
"uhyum" sigh yay kafin ya k'ara cewa "kin picking and u can't talk" d'an tura baki tay kaman yana kallon
ta tace "Fushi nike da kai" har saida ta d'an ji sautin murmushin da yay,

"Did I offended you?" can taji ya tambaya tana tura baki tace eh sigh ya k'ara yi kafin ya tambayeta
tana cikin Mutane ne tace a'a ita kadae ce yace Ok bari ya maida Video Call yaga angry face din tay d'an
murmushi, bayan ya maida zaune yake kan Sofa jikin shi sanye da silky sleeping dress riga da wando
farare ya zuba mata ido suna kallon juna tana sanye da yar riga v-neck ta mata cib burst d'inta ya fito
sosae kanta d'aure da d'an bak'in gyale daya d'an zame bak'in gashinta ya d'an bayyana bai hango skirt
d'in dake jikinta ba wanda iya gwuiwa ne don a zaune take, ita shamm tama manta a yadda take Fuskar
shi a sake kaman zai murmushi ya tambayeta suna lafiya tace mashi lafiya lou sai kuma taji yace "So tell
me laifin mi na maki?" d'an yamutsa fuska tay a d'an shagwa6e wanda hakan yama zame mata jiki tace
"ba ka manta dani ba" still yay yanata kallonta kaman bazai tanka ba har saida ta d'an tsargu da kallon ta
d'an kauda idonta can taji yace "am sorry it wasn't intentionally, naje wani wuri ne and I have been
trying to call but u'r out of reach kinsan k'auyen ku ba Network mai kyau" wani kallon k'asan ido tay
mashi kawae sai taga yay dariya har jerarrun fararen hak'oran sa suka d'an bayyana, idasa d'agowa tay
tana ta kallon shi ya d'age mata gira ya tambayi ta yi hak'uri bata san ma ta d'aga mashi kai ba alamar
eh, ya furta mata "thanks" tay yar dariya, shiru ta d'an biyo baya kafin ta tambaye shi ina Aunty Fanan
yace mata tana wurin aiki da d'an alamun mamaki tace amman ba taga kaman dare bane yace eh acan
zata kwana ne ta jinjina kai,

"Sai kika gudo ko" tura mashi baki tay tana kikkafta ido tace "to ai ni ban son Auren fa" d'an d'age gira
yay da d'an murmushi kawae tana dai ta kallon shi ta lura kaman yanayin face d'in shi ya canza yana nan
yadda yake saima wani fresh daya k'ara yi gashi ya d'an tara suma a sajen shi ba kaman da ba duk yana
lura da kallon da take mashi duk da sai kace ba kallonta yake ba can taji yace ya akai take k'are mashi
kallo haka, yar dariya tay dama tasanshi da rashin son kallo tace "naga fuskar ka kaman ta canza" fuska
sake yace mi face d'in nashi tay tace kaman ta d'an fad'a ko bai lafiya ne, hannu yasa ya shafi forehead
d'in shi slowly yace "Yea but na samu sauk'i" tace Allah ya k'ara sauk'i ya amsa da Amin ta sake cewa
"Amman a haka kana ciwon ka tafi wurin da ka ce ka je?" idon shi a kanta yace eh, cikin nuna damuwa
tace "ai da sai kace baka lafiya kai zaman ka gida" d'an ta6e baki yay yace "ai ni ba lazy bane kaman ke"
waro ido tay tace itace lazy d'in yace "yeah komae kuka" aikuwa a shagwa6e ta fara yarfa hannu tana
fad'in wllh ita ba raguwa bace shima ai ya sani still yay yanata kallonta da d'an murmushi komae nata
burge shi yake ba kaman in tana shagwa6a duk da ba ita kadai ke mashi hakan ba Fanan ma na yi mashi
sosae amman sai yafi ganin kyaun abun in Zaraah tayi, har saida yace wasa yake sannan ta daina mitar,
cigaba da firar sukae har yana ce mata daga yanzu in tasan tana cikin Matsala ta rink'a sanar dashi in ma
bata same shi ba ko Abbas ne ta kira ta fad'a mashi Koda wani abu ne take so ta amsa mashi da toh, fira
tayi fira saiga su Fatuu harda kwanciya kan Katifar shima can ya mik'e ya d'auki laptop d'in ya koma
Bedroom d'in shi, gado ya hau ya jingina da headboard ya d'aura laptop d'in akan laps d'in shi, Hira da
Masoyi dad'i😍 sai ga Fatuu da fara yin gyangyad'i tun tana yi tana bud'e idon har takai baccin ya kwashe
ta dai abun sai ma ya bashi dariya kamar ba ita bace ta tada jijiyar wuya ba don an ce mata lazy, sam ya
kasa disconnecting ya kafeta da ido sai kallon face d'in ta yake ba kamar eyelashes d'inta da lips d'inta da
tun ba yanzu ba yake ganin kyawun shape d'in su yadda na k'asan yake da d'an fad'i sosae, slowly ya
mik'a hannunshi kan screen d'in ya sauke dogon yatsan shi manuni daidai lips d'inta ya fara zagaye su
tamkar mai tracing ya d'an d'auki lokaci yana hakan can kuma ya janye hannun ya katse kiran ya maida
laptop d'in saman bedside drawer bayan ya rufeta, idasa kwanciya yay idon shi na kallon sama tamkar
mai tunanin wani abu a hankali kuma ya lumshe su...........

*ASM Bk2035*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

..........Yadikko tayi zaton wayar suke tayi hakan yasa taci gaba da aikin ita kad'ai, sai da aka kira sallar
Azahar su Amadu sun shigo yin salla ne ya ganta baje kan katifarsa tana ta sharar bacci d'an tsoki yay ya
girgiza kan shi kaman bazai tashe ta ba sai kuma ganin lokacin salla yayi yasa ya tada ita yace ta je tay
salla, tay matuk'ar yin mamakin yadda akai tayi baccin daga yin waya, Koda ta fito bata iske Yadikkon a
cikin Kitchen d'in ba don tuni ta gama komae ta wuce d'aki don tayi salla itama Fatuu d'akin ta nufa, jibi
su Yadikko zasu tafi hakan yasa washe gari talata suka hau shiri har Kasuwa gwaggo ta rakata tayo
siyayya Fatuu duk ta damu bata son su tafi haka ma Mino tun ranar ta fara kuka Fatuu na bata hak'uri
gwaggo ma tace mata in sha Allahu bada jimawa ba zata dawo da ita nan ta dae dage da karatun ta tace
to, akwati guda na kaya Fatuu ta bata hakan yasa ta washe tana ta murna gwaggo ma tayi masu siyayya
sosae shima Kamalu kaya sosae Amadu ya bashi, Washe gari da Asuba Abbas yazo kai su tasha dama tun
jiya ya kira Fatuu sanin yau zasu tafin yace zai zo ya kaisu Fatuu ta so bin su tasha amman gwaggo ta
hana don kar asa Abbas wahalar dawowa sai Fatan Allah yasa a sauka Lafiya, bayan tafiyar su duk
kad'aici ya damu Fatuu don ma Haulat na nan, Ranar Juma'a da daddare bayan Isha Fatuu na zaune tare
da gwaggo a Parlor gwaggon na zaune akan Carpet don ba kasaifai take son zama kan kujera ba har ta
dad'e Fatuu ce zaune akan kujerar can ta tambayi gwaggon in jarabawar su ta fito a ina zata ci gaba da
karatu, d'an jimm tay kafin tace a nan Katsina Fatuu ta d'an bud'a ido tace "amman gwaggo ai ba'a fa
karatun Medicine anan sai Kano ko Zaria ko sakkwato" gwaggo dake kallonta ta d'an girgiza kai tace "ina
tunanin ai kawae zaki canza abunda zaki karanta ne" da yar damuwa Fatuun ta tambayeta Saboda me
tace "gaskiya banson ki tafi wani gari karatu ko ba don komae ba don abunda ya faru kinga yanzu idanun
dangin mahaifin ki na akan ki abu kad'an suke jira tunda dama ba son karatun suke ba, ni a shawarce ki
fara yin School of Nursing ta nan ala bashshi tunda naji ance gab ake da a fara karatun likitancin anan
har an maida Asibitin Medical center na koyarwa don hakan kinga Ko kina cikin karatun aka fara sai ki
koma shi in kuma har kika gama wannan d'in ba'a fara ba tunda shekara ukku ne lafiya lou ai shima duk
aikin Asibitin ne kuma ko lokacin aka fara karatun likitancin zaki iya yi zaki ma fi jin sauk'in karatun tunda
kin karanci abunda ya dangance shi" d'an shiru Fatun tay kamar mai yin tunani bata son abunda zai sa ta
k'ara samun sa6ani da gwaggon har ta 6ata mata rai hakan yasa tace Shikenan Allah yasa haka yafi zama
Alkhairi murmushin jin dad'i gwaggon tay tace Amin haka yakamata duk abu ya faru da mutum yay fatan
kasancewar shi Alkhairi in har ba Alkhairin bane sai kaga Allah ya canza ma, cike da gamsuwa Fatun na
yar dariya tace "Hakane gwaggo ni shaida ce" duk suka sa dariya kafin gwaggon tace "in ce dai kun rabu
dashi yaron kwata kwata ko?" Fatuu ta gane Khalid take nufi hakan yasa yanayin fuskarta ya d'an canza
ta ta6e baki tace "Eh, da dai Farko yana ta takura man da kira har da kina can ma sai yay ta kira na har
message ya turo man yana rok'on wai don Allah in yi hakuri in saurare shi yana son muyi wata Magana
ne ni kuma kawae sai nayi blocking d'in shi ma" jinjina kai gwaggon tayi tace hakan ya kamata tunda an
rabu ba shikenan ba yaje kowa Allah ya had'a shi da rabon shi, can ta d'an kya6e baki tace wai da fa
Mino za'a k'ak'aba ma shi, zaro ido Fatuu tay da Al'ajabi tace "Mino kuma!" gwaggon tace "Eh wllh duk
tuggun Yaya ne Allah dai ya taimaka hakk'atta bata cimma ruwa ba, in ba don mugun nufi ba ba akwae
sauran yara ba a gidan a bashi mana" ta6e baki Fatuu tay ta shiga fad'in ai dama ko itama tasan duk
k'ullin su Yayan ne su suka tunzura komae Gwaggon tace "ai da yake da Allah muka dogara kuma shi ba
azzalumin bayin shi bane gashi nan ai ya bamu mafita da basu ta6a zata ba" ta k'arasa tana sakin
murmushi wanda da gani ba k'aramin dad'i take ji ba a ranta Fatuu dake kallon ta itama tana murmushin
tace "Wllh Gwaggo ina son in ga kina farin ciki kyau kike sosae" yar harara ta wurga mata tace bayan ta
gama sata kukan da rabon da tayi irin shi har ta manta da sauri Fatuu ta sauka daga kan kujera taje ta
rungumeta tana fad'in "Am very sorry my lovely Kakus in sha Allahu bazaki k'ara zubar da hawaye
Saboda ni ba zan ta saka ki farin ciki kuma zamu rayu tare har in yi aure inyi ya'ya harda jikoki" sosae
gwaggo ke dariya tana fad'in anya bata so kanta ba da yawa ita ina zata kai wannan lokacin da sauri
Fatun tace insha Allahu zata kai, jin tak'i ta d'aga daga jikinta yasa gwaggon ce mata ta d'agata ta fara
d'aura mata gajiya shiru Fatun bata tanka ba kuma bata d'agata ba hakan yasa gwaggon ta kira sunanta
da d'an k'arfi sai lokacin ta d'ago tana d'an murmushi ganin yanayin idonta yasa tace mata badae har tayi
bacci ba tana muttsike idonta guda tace Wllh har ta fara gyangyad'i da d'an mamaki gwaggo tasa hannu
ta ruk'e ha6arta tace "Wai ni kodae shawara ke damun ki ne Fatuu, na lura dake kwanan nan kin fiye
bacci bunu bunu kin 6ingire bacci" tana yar dariya tace "Ramuwar baccin da ban samu yi da ina cikin
damuwa ba ne" d'an ta6e baki gwaggo tay Fatuu ta k'ara cewa "Haka rannan ma fa Ya Haisam ya kira ni
Video Call muna cikin yin Magana nay bacci ban sani ba" bud'a ido gwaggo tay alamar mamaki sai kuma
tace "ashe kun yi Magana bayan kin dawo" Fatuu tace "Eh tun ma su Yadikko na nan" kai gwaggo ta
d'aga sai kuma ta tambayeta suna lafiya dai ko Fatuu tace "eh lokacin yace Aunty Fanan ma na wurin aiki
amman shi naga fuskarshi kamar ta d'an fad'a shine na tambaye shi ko bai lafiya ne yace eh baijin dad'i
amman ya samu sauk'i" girgiza kai gwaggo ta shiga yi alamar jajantawa kafin tace "Allah sarki Allah ya
k'aro sauki, amman to kin k'ara kiran nashi kin ji ya jikin ko" d'an bud'a ido Fatuu tay ta girgiza kai alamar
a'a gwaggon tace "Amman baki kyauta ba gaskiya ai Kya kira ki ji ya ya k'ara ji ke in kece yaji baki lafiya
kina tunanin zai dau kwanaki bayan jin hakan bai kira ki ya k'ara jin ya kike ba?" hannu Fatuu tasa ta rufe
baki tana dariya sai kuma ta cire tace to ta kira shi yanzun gwaggon tace haka dae yakamata da sauri ta
mik'e ta nufi hanyar fita daga parlon don wayar na d'akinta gwaggo ta bita da ido fuskarta da d'an
murmushi har ta fice.

Tana shiga ta nufi gado ta fad'a saman shi tay rubda ciki, bayan ta kai hannu ta d'auki wayar tay sending
mashi kira saidae har wayar ta katse ba'a d'aga ba tana kokarin sake kiran sai gashi ya kira picking tay ta
kara a kunne gudun kada yay complain kamar ranar nan na k'in yin Magana yasa tace "Hello Assalamu
alaikum" cikin cool voice en shi ya amsa mata, d'an murmushi tay tace "Ya Handsome ina kwana nasan
ku nan safiya ne ko?" d'an murmushi ya saki jin sunan data kira shi dashi ya bata amsa da eh, tace
"Dama na kira in ji ya jiki rannan da kace baka jin dad'i" shiru ya d'an yi sai kuma slowly yace ta damu da
ciwon da yake ne, tura baki tay a shagwa6e tace "A'a nifa kawae na tuno ne shiyasa na kira",

"Dat's mean baki damu da ciwon ba kenan" ya tambaya tace "a'a....na damu ba kai ne ba..." Sai kuma
tay shiru ya tambaye ta shine mi tace sai yace ta damu, d'an murmushi mai sauti yay yace to ba gashi
tace ta damu ba miya fad'i ba daidai ba, shiru tay ta rasa mi zata ce ma har saida ya kira sunanta a
shagwa6e ta amsa yace mata ya warke ya gode da kulawa tace to, bai cika son ya kara waya a kunne yay
ta Magana ba hakan yasa ya maida kiran video call yana zaune da gani a Office ne jikinshi sanye da
Maroon suit yayi kyau har ya gaji ganin bai ganinta sosae yasashi tambayar ta ba wuta ne tace eh
amman ai akwae sola bari ta kunna wannan hasken na rechargeable globe ne ya amsa da Ok, bayan ta
kunna haske ya gauraye d'akin ta koma kan gadon ta zauna ta d'age k'afafuwan ta ta jingine wayar ajikin
su, tambayar shi tay ya Aunty Fanan yace tana nan lafiya da bud'ar bakinta sai cewa tay wai tana da ciki
shiru yay kawae yana bin ta da kallo hakan yasa tasha jinin jikinta ita kanta hakanan taji tayi tambayar ba
tare da shiri ba su6utar baki ce, duk ta kame kanta sai nonnoke fuska take ganin yadda take yi yasa shi
yin d'an murmushi yace zata zo ne kallon shi tay kaman bazata ce komae ba sai kuma tace tazo ina yace
nan in Fanan d'in ta haihu da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a fuskar shi a sake yace "Why ba sai ki
mata rainon ba" tana tura baki tace ita bazata yi karatu ba sai raino, yar guntuwar dariya yay sai kuma ya
tambayeta yaushe zata ci gaba da karatun ta kwashe yadda sukae da gwaggo ta fad'i mashi a tunaninta
ko zai ce zaiyi Magana da gwaggon kan a barta taje tay Medicine d'in amman sai taji yace hakan yayi
yace amman ai kaman dole saida Jamb tace a'a taji ana cewa Basic Nursing ba saida Jamb ba yace Ok
tace mashi yanzu result kawae take jira yace Ok Allah yasa aga Alkhairi ta amsa da Amin, shiru suka d'an
yi can tace mashi yaushe zai zo idon shi akanta ya tambayi tana son ganin shi ne da sauri tace a'a ba
gashi ko yanzu tana ganin shi ba kawae ta tambaya ne yay nodding kai kafin yace mata bazai samu zuwa
yanzu ba tunda bai dad'e da yazo ba kuma Hajiya daga Abuja zata zo nan ta d'an zauna dasu Saboda
ganin likita tace Allah ya bata lafiya ya amsa da Amin daga baya da kanta tace bari ta k'yale shi ta hana
shi aiki yay d'an murmushi kawae yace mata take care ta d'aga kai daga haka ta katse kiran, d'akin
gwaggo ta nufa don ta fad'i mata ya warke ta iske har tayi bacci. Fatuu an samu natsuwa har ta koma
islamiyya washe gari yan islamiyyar sunyi farinciki da ganinta sai tambayarta ake yadda akai ta dawo
tace an fasa auren ne kawae Malam Nazifi har ke6ewa yay da ita ya tambayeta Allah yasa dae lafiya ta
dawo tace mashi lafiya lou dama bata son auren na dole ne za'a mata to kuma an fasa daga yanayin
fuskar shi ta fahimci yaji dad'in hakan yace ba komae bane ya ja hakan face Addu'a shiyasa ake son bawa
ya mik'a lamuransa wurin Ubangiji to kuwa a komae zai samu mafita Fatuu ta jinjina kai tay mashi godiya
sosae har yana tsokanarta yace sai a dasa rashin ji ko tana dariya tace ai ta daina wannan yanzu ta girma,
Washe gari bayan ta dawo daga islamiyyar safe ne Amadu ya shigo d'akinta lokacin tana cikin gyara
wardrobe d'inta ta kalleshi tana murmushi shima murmushi yake mata yace "Amaryar mu" tura mashi
baki tay tace don Allah ya bari bata so, wayarta ya kawo mata yace ta bashi tashi tace a'a Ya barta kawae
yace don me ai itama tana son abunta ko kuma ga Makaranta zata fara tace ai tashin ma lafiya lou daga
baya ta canza, duk yadda yay da ita k'in amsa tay k'arshe yay mata godiya ya tafi, acikin satin da ya kama
Haulat ta koma Nijar don bikinta bai fi saura sati biyu ba, ranar Laraba sai ga Baffan Fatuu sun kawo
Kayanta na kitchen kamar yadda yace Fatuu tay farincikin ganin shi sosae, a d'akin Fatun can gefe akai
masu wuri manyan kuma su freezer aka kai su d'akin Amadu bayan sun zauna da gwaggo ta tambaye shi
yadda akai da furniture d'in yace wad'anda suka yi su sun fanshe su duk da sun rage kud'in gwaggo ta
girgiza kai tace Allah ya kyauta bayan Gwaggo ta tafi Fatuu taje wurin shi d'akin Amadu da aka sauke shi
sukai fira anan ya bata kud'i dubu d'ari yace ta d'auki 50k d'inta da ta bashi tay amfani da sauran dubu
hamsin d'in gun shirye shiryen fara karatun ta dama cikon dubu d'arin data bashi kud'in sadakin ta ne,
k'in amsa tay tace ai ba sai ya maido mata ba itama ai Saboda auren aka bata yana dariya yace to ai ba'ai
auren ba ko ta dingi zuba mashi shagwabar bazata amsa ba yana dariya daga baya da k'yar ya sata ta
amsa kwanan shi biyu ran Friday ya tafi, Bayan sati guda suka shirya zuwa Niamey K'asar Nijar bikin
Haulat harda Kawu Amadu gwaggo tayi masu hidima sosae don kayan kitchen d'in Fatuu ta d'ibar mata
masu yawa harda zannuwan gado da labulaye innarsu haulat d'in kafin su tafi lokacin tay tsananin
farinciki da yake su da wuri suka tafi su kuma su Fatuu saida bikin ya zo, Tafiya yankin Azaba Fatuu an ji
jiki sai lokacin ta gane daga Katsina zuwa Adamawa ba komae bane akan wannan tafiyar da sukae don
farko Marad'i suka fara zuwa daga can suka hau luxurious bus suka kwana suna tafiya don ma Motar
nada dad'in hawa akwae su Ac harda Tv, lokacin da suka isa da k'yar take iya taka k'afafunta don tafiyar
tayi daga Katsina zuwa Lagos in ma bata fi ba, Haulat tay tsananin farinciki da zuwan nasu haka danginsu
sun tarbe su hannu bibbiyu an sha shagali an ci an sha anyi wadaqa da nama don mutan Nijar badai cin
nama ba bakamar in suna hidima gashi ba Laifi dangin mijin nada d'an hali saidae wani Abincin fa su
Fatuu kasa ci sukae sai wanda yay irin namu na nan, Alhamdulillah ranar Asabar aka d'aura auren Haulat
da Angonta wanda yake d'an uwanta ne wato Nuraddeen suna zaune Fatuu na dariya tace mata da
rabon dae sai ta rigata yin aure duk sukae dariya, Sosae Fatuu akai kasuwa don wanka na Mutunci ta
rink'a d'auka da bikin don ma gwaggo na taka mata burki har samari ta hanata saurara tace ba wannan
ne a gabanta ba to itama dai dama ba mai kula samarin bace, bayan biki da kwana biyu suka sake
d'aukko hanya aka taita yi har Allah ya maido su Lafiya Fatuu cike da kewar Aminiyarta, tun suna can aka
saki result d'in Waec suna dawowa Abbas yazo ya dauketa suka je dubawa gaba d'aya ta samu credit
saidae chemistry ne ta samu pass tun can ta fara k'walla don bata tsammaci hakan ba sakamakon tasan
ta maida hankali lokacin da sukae exams d'in gashi dole saida shi zata iya yin School of nursing din Abbas
ne ya shiga kwantar mata da hankali yace a jira Neco ta fito in sha Allahu yasan zata samu, koda ta dawo
gida ma gwaggo duk da bata ji dad'i ba amman bata nuna mata damuwa ba sosae itama tace a jira
d'ayar daga baya ma sai ga Haisam ya kirata don Abbas ya fad'i mashi komae harda yarda ta tashi
hankalinta sosae ya kwantar mata da hankali yace ai akwae alternative so a jira Neco fuska jage jage tace
mashi to anan ma saida ya k'ara ce mata lazy ta tura mashi baki daga baya sai gashi har saida yasata
dariya, bayan sati biyu Neco ta fito wannan karon k'in zuwa tay dubowar saidae Abbas ne yaje, a k'opar
gida ya tsaya bayan ya dawo ya kirata ta fito tunda ya tafi dubowar dama gabanta keta fad'uwa duk ta
sha jinin jikinta ba kamar da taga fuskar Abbas d'in bai dariya a gefe ta tsaya ta gaida shi a sanyaye ya
amsa duk ya d'an damu kaman zatai kuka tace mashi itama akwae matsala ko ya d'aga mata kai alamar
eh nan da nan tasa hannu zata fara matsar kwalla ya fiddo result d'in daga gefen shi ya mik'a mata, k'in
amsa tay tace ita mizatai dashi tunda bata ci abunda ake so ba saida ya d'an matsa mata sannan ta amsa
ta amman ta k'i dubawar yace ta duba mana, hannunta har rawa yake ta d'aga da ido d'aya ta d'an kalli
paper d'in da sauri kuma ta ware idanun a tunaninta ko abunda take gani gizau ne ba gaske ba, tabbatar
ma da kanta tay da sauri ta kalli Abbas taga yana murmushi a rud'e tasa hannu ta rufe bakinta ganin ta
cinye duka harda su A (distinctions) nan da nan ta fara murna tana yarfa hannu sai faman fad'in
Alhamdulillah take Abbas na mata dariya, koda ta shiga gida gwaggo ta gani tay matuk'ar murna harda
duk'awa wai Fatun ta hau ta goyata ta kuwa haye aikuwa da k'yar ta mik'e don ma gwaggon k'akk'arfa ce
dik'ir take, ganin tana ta nishi yasa Fatun saukkowa tana ta kyalkyatar dariya,

Lokacin da aka fara saida Form na Makarantar Abbas ne yaje Bank ya siyo mata ya kawo mata suka cike
tare suka maida can School d'in bayan wani lokaci suka je don yin jarabawar shiga wato Entrance exam a
lokacin ne ta had'u da wata da suka zauna tare har ta fad'a mata sunanta Fauziyya Ahmad ta tambayi
Fatun itama ta fad'i mata nata Fauziyyar tay masu Fatan Nasara Fatuu ta amsa da Amin, bayan sun gama
ne tace ma Fatuu ta bata phone no d'inta ta bata don ta lura tana da kirki ga fara'a bunu bunu tayi
murmushi, bayan kaman sati biyu da yin jarabawar aka kafe lists d'in wanda suka ci Fauziyya ce ta kira
Fatun ta sanar mata ta samu itama haka don taga sunanta cikin yan Katsina local Government itace ma
ta biyu sosae Fatuun tay murna duk da da sauran rina a kaba don dama farko sai su d'auki Mutane fin
d'ari cikin mutane wurin 500 koma fi da sukai applying sai a hankali za'ai ta zubar da su don bai wuce
Mutum 130 ko 150 bane zasu ci entrance exam d'in suma kuma wurin interview za'a k'ara zubar da wasu
haka Bayan an fara karatunma, cikin Nasara Fatuu taci interview da sukae ta samu Admission d'in
Kasimu Kopar Bai School Of Nursing Katsina dake acikin General Hospital, kowa yay farin ciki karma dae
gwaggo taji haka Abbas ma har Haisam saida ya kira ya tayata murna daga baya suka fara Class ranar
farko har Video call sukai da Haisam tana cikin fararen Uniform d'inta da takalma sai faman zabga
dariyar dad'i take ya k'ara tayata murna ya kuma ce sai ta d'age don still bata zama cikakkar daliba ba
har sai tayi passing Intro Exam tace in sha Allahu, tun ranar da suka je interview Fauzy kamar yadda
Fatun ta fara kiranta dama kuma tace haka ake ce mata ta tambayi Fatuu Day zatai ko Boarding tace
mata Day Fauzyn tace mi zai hana tayi Boarding don itama ita zatai Fatuu ta tambayeta ba'a nan garin
take bane tace eh ita yar Funtua ce amman akwae Yayarta dake Aure nan Katsina a Goruba Road, Fatuu
tace to ba sai ta zauna a wurinta ba Fauzyn tace ita tafi son zama a school don mutum yafi samun time
na karatu balle wannan Makarantar da ba'a wasa da karatu dole sai Mutum ya dage zadai ta rink'a zuwa
wurinta weekend, to bayan sun fara shiga Class ma saida ta k'ara yi ma Fatuu Maganar tace an bata d'aki
dama akwae wata yar garinsu da suka gama a d'akinsu zata zauna Don Allah ta dawo boarding sai su
zauna tare ganin yadda ta dage tana ta nuna mata Muhimmancin zama a cikin Makaranta ne yasa Fatuu
tace to in ta koma gida zata tambaya in an barta sai ta dawo Fauzy harda yi mata Addu'ar Allah yasa a
barta ita dae Fatuu yar dariya kawae tay, A ranar da daddare bayan sallar Magrib ta iske gwaggo a d'aki
ta gama salla ta zauna gefenta bayan tay mata sannu ne tayi mata Maganar komawarta boarding, shiru
gwaggo tay tana kallonta can ta nisa ta tambaye ta miyasa take son zama a Makarantar Fatun tace an fi
samun lokaci kuma ko Assignment aka bada mai wuya za'a taru ayi tare sannan ana tattaunawa game da
abunda aka koya, d'an jimm gwaggo tay kafin tace "Gaskiya ni banson zaman Makarantar nan don yana
da illoli ba kuma wai don ban yarda dake bane amman nafi son ki rink'a zuwa kina dawowa" gyad'a kai
Fatuu tay tace Shikenan Gwaggo ta fahimci yanzu duk inta nuna ga yadda take son abu bata gardama
mata hakan yasa tace mata in kamar an basu aikin ko zasu tattauna kan karatun zata iya tsayawa can
amman ba wai ta koma gaba d'aya ba Fatun tace to ta tashi ta koma d'akinta............
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._*ASM Bk2035*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

..........Yadikko tayi zaton wayar suke tayi hakan yasa taci gaba da aikin ita kad'ai, sai da aka kira sallar
Azahar su Amadu sun shigo yin salla ne ya ganta baje kan katifarsa tana ta sharar bacci d'an tsoki yay ya
girgiza kan shi kaman bazai tashe ta ba sai kuma ganin lokacin salla yayi yasa ya tada ita yace ta je tay
salla, tay matuk'ar yin mamakin yadda akai tayi baccin daga yin waya, Koda ta fito bata iske Yadikkon a
cikin Kitchen d'in ba don tuni ta gama komae ta wuce d'aki don tayi salla itama Fatuu d'akin ta nufa, jibi
su Yadikko zasu tafi hakan yasa washe gari talata suka hau shiri har Kasuwa gwaggo ta rakata tayo
siyayya Fatuu duk ta damu bata son su tafi haka ma Mino tun ranar ta fara kuka Fatuu na bata hak'uri
gwaggo ma tace mata in sha Allahu bada jimawa ba zata dawo da ita nan ta dae dage da karatun ta tace
to, akwati guda na kaya Fatuu ta bata hakan yasa ta washe tana ta murna gwaggo ma tayi masu siyayya
sosae shima Kamalu kaya sosae Amadu ya bashi, Washe gari da Asuba Abbas yazo kai su tasha dama tun
jiya ya kira Fatuu sanin yau zasu tafin yace zai zo ya kaisu Fatuu ta so bin su tasha amman gwaggo ta
hana don kar asa Abbas wahalar dawowa sai Fatan Allah yasa a sauka Lafiya, bayan tafiyar su duk
kad'aici ya damu Fatuu don ma Haulat na nan, Ranar Juma'a da daddare bayan Isha Fatuu na zaune tare
da gwaggo a Parlor gwaggon na zaune akan Carpet don ba kasaifai take son zama kan kujera ba har ta
dad'e Fatuu ce zaune akan kujerar can ta tambayi gwaggon in jarabawar su ta fito a ina zata ci gaba da
karatu, d'an jimm tay kafin tace a nan Katsina Fatuu ta d'an bud'a ido tace "amman gwaggo ai ba'a fa
karatun Medicine anan sai Kano ko Zaria ko sakkwato" gwaggo dake kallonta ta d'an girgiza kai tace "ina
tunanin ai kawae zaki canza abunda zaki karanta ne" da yar damuwa Fatuun ta tambayeta Saboda me
tace "gaskiya banson ki tafi wani gari karatu ko ba don komae ba don abunda ya faru kinga yanzu idanun
dangin mahaifin ki na akan ki abu kad'an suke jira tunda dama ba son karatun suke ba, ni a shawarce ki
fara yin School of Nursing ta nan ala bashshi tunda naji ance gab ake da a fara karatun likitancin anan
har an maida Asibitin Medical center na koyarwa don hakan kinga Ko kina cikin karatun aka fara sai ki
koma shi in kuma har kika gama wannan d'in ba'a fara ba tunda shekara ukku ne lafiya lou ai shima duk
aikin Asibitin ne kuma ko lokacin aka fara karatun likitancin zaki iya yi zaki ma fi jin sauk'in karatun tunda
kin karanci abunda ya dangance shi" d'an shiru Fatun tay kamar mai yin tunani bata son abunda zai sa ta
k'ara samun sa6ani da gwaggon har ta 6ata mata rai hakan yasa tace Shikenan Allah yasa haka yafi zama
Alkhairi murmushin jin dad'i gwaggon tay tace Amin haka yakamata duk abu ya faru da mutum yay fatan
kasancewar shi Alkhairi in har ba Alkhairin bane sai kaga Allah ya canza ma, cike da gamsuwa Fatun na
yar dariya tace "Hakane gwaggo ni shaida ce" duk suka sa dariya kafin gwaggon tace "in ce dai kun rabu
dashi yaron kwata kwata ko?" Fatuu ta gane Khalid take nufi hakan yasa yanayin fuskarta ya d'an canza
ta ta6e baki tace "Eh, da dai Farko yana ta takura man da kira har da kina can ma sai yay ta kira na har
message ya turo man yana rok'on wai don Allah in yi hakuri in saurare shi yana son muyi wata Magana
ne ni kuma kawae sai nayi blocking d'in shi ma" jinjina kai gwaggon tayi tace hakan ya kamata tunda an
rabu ba shikenan ba yaje kowa Allah ya had'a shi da rabon shi, can ta d'an kya6e baki tace wai da fa
Mino za'a k'ak'aba ma shi, zaro ido Fatuu tay da Al'ajabi tace "Mino kuma!" gwaggon tace "Eh wllh duk
tuggun Yaya ne Allah dai ya taimaka hakk'atta bata cimma ruwa ba, in ba don mugun nufi ba ba akwae
sauran yara ba a gidan a bashi mana" ta6e baki Fatuu tay ta shiga fad'in ai dama ko itama tasan duk
k'ullin su Yayan ne su suka tunzura komae Gwaggon tace "ai da yake da Allah muka dogara kuma shi ba
azzalumin bayin shi bane gashi nan ai ya bamu mafita da basu ta6a zata ba" ta k'arasa tana sakin
murmushi wanda da gani ba k'aramin dad'i take ji ba a ranta Fatuu dake kallon ta itama tana murmushin
tace "Wllh Gwaggo ina son in ga kina farin ciki kyau kike sosae" yar harara ta wurga mata tace bayan ta
gama sata kukan da rabon da tayi irin shi har ta manta da sauri Fatuu ta sauka daga kan kujera taje ta
rungumeta tana fad'in "Am very sorry my lovely Kakus in sha Allahu bazaki k'ara zubar da hawaye
Saboda ni ba zan ta saka ki farin ciki kuma zamu rayu tare har in yi aure inyi ya'ya harda jikoki" sosae
gwaggo ke dariya tana fad'in anya bata so kanta ba da yawa ita ina zata kai wannan lokacin da sauri
Fatun tace insha Allahu zata kai, jin tak'i ta d'aga daga jikinta yasa gwaggon ce mata ta d'agata ta fara
d'aura mata gajiya shiru Fatun bata tanka ba kuma bata d'agata ba hakan yasa gwaggon ta kira sunanta
da d'an k'arfi sai lokacin ta d'ago tana d'an murmushi ganin yanayin idonta yasa tace mata badae har tayi
bacci ba tana muttsike idonta guda tace Wllh har ta fara gyangyad'i da d'an mamaki gwaggo tasa hannu
ta ruk'e ha6arta tace "Wai ni kodae shawara ke damun ki ne Fatuu, na lura dake kwanan nan kin fiye
bacci bunu bunu kin 6ingire bacci" tana yar dariya tace "Ramuwar baccin da ban samu yi da ina cikin
damuwa ba ne" d'an ta6e baki gwaggo tay Fatuu ta k'ara cewa "Haka rannan ma fa Ya Haisam ya kira ni
Video Call muna cikin yin Magana nay bacci ban sani ba" bud'a ido gwaggo tay alamar mamaki sai kuma
tace "ashe kun yi Magana bayan kin dawo" Fatuu tace "Eh tun ma su Yadikko na nan" kai gwaggo ta
d'aga sai kuma ta tambayeta suna lafiya dai ko Fatuu tace "eh lokacin yace Aunty Fanan ma na wurin aiki
amman shi naga fuskarshi kamar ta d'an fad'a shine na tambaye shi ko bai lafiya ne yace eh baijin dad'i
amman ya samu sauk'i" girgiza kai gwaggo ta shiga yi alamar jajantawa kafin tace "Allah sarki Allah ya
k'aro sauki, amman to kin k'ara kiran nashi kin ji ya jikin ko" d'an bud'a ido Fatuu tay ta girgiza kai alamar
a'a gwaggon tace "Amman baki kyauta ba gaskiya ai Kya kira ki ji ya ya k'ara ji ke in kece yaji baki lafiya
kina tunanin zai dau kwanaki bayan jin hakan bai kira ki ya k'ara jin ya kike ba?" hannu Fatuu tasa ta rufe
baki tana dariya sai kuma ta cire tace to ta kira shi yanzun gwaggon tace haka dae yakamata da sauri ta
mik'e ta nufi hanyar fita daga parlon don wayar na d'akinta gwaggo ta bita da ido fuskarta da d'an
murmushi har ta fice.

Tana shiga ta nufi gado ta fad'a saman shi tay rubda ciki, bayan ta kai hannu ta d'auki wayar tay sending
mashi kira saidae har wayar ta katse ba'a d'aga ba tana kokarin sake kiran sai gashi ya kira picking tay ta
kara a kunne gudun kada yay complain kamar ranar nan na k'in yin Magana yasa tace "Hello Assalamu
alaikum" cikin cool voice en shi ya amsa mata, d'an murmushi tay tace "Ya Handsome ina kwana nasan
ku nan safiya ne ko?" d'an murmushi ya saki jin sunan data kira shi dashi ya bata amsa da eh, tace
"Dama na kira in ji ya jiki rannan da kace baka jin dad'i" shiru ya d'an yi sai kuma slowly yace ta damu da
ciwon da yake ne, tura baki tay a shagwa6e tace "A'a nifa kawae na tuno ne shiyasa na kira",

"Dat means baki damu da ciwon ba kenan" ya tambaya tace "a'a....na damu ba kai ne ba..." Sai kuma
tay shiru ya tambaye ta shine mi tace sai yace ta damu, d'an murmushi mai sauti yay yace to ba gashi
tace ta damu ba miya fad'i ba daidai ba, shiru tay ta rasa mi zata ce ma har saida ya kira sunanta a
shagwa6e ta amsa yace mata ya warke ya gode da kulawa tace to, bai cika son ya kara waya a kunne yay
ta Magana ba hakan yasa ya maida kiran video call yana zaune da gani a Office ne jikinshi sanye da
Maroon suit yayi kyau har ya gaji ganin bai ganinta sosae yasashi tambayar ta ba wuta ne tace eh
amman ai akwae sola bari ta kunna wannan hasken na rechargeable globe ne ya amsa da Ok, bayan ta
kunna haske ya gauraye d'akin ta koma kan gadon ta zauna ta d'age k'afafuwan ta ta jingine wayar ajikin
su, tambayar shi tay ya Aunty Fanan yace tana nan lafiya da bud'ar bakinta sai cewa tay wai tana da ciki
shiru yay kawae yana bin ta da kallo hakan yasa tasha jinin jikinta ita kanta hakanan taji tayi tambayar ba
tare da shiri ba su6utar baki ce, duk ta kame kanta sai nonnoke fuska take ganin yadda take yi yasa shi
yin d'an murmushi yace zata zo ne kallon shi tay kaman bazata ce komae ba sai kuma tace tazo ina yace
nan in Fanan d'in ta haihu da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a fuskar shi a sake yace "Why ba sai ki
mata rainon ba" tana tura baki tace ita bazata yi karatu ba sai raino, yar guntuwar dariya yay sai kuma ya
tambayeta yaushe zata ci gaba da karatun ta kwashe yadda sukae da gwaggo ta fad'i mashi a tunaninta
ko zai ce zaiyi Magana da gwaggon kan a barta taje tay Medicine d'in amman sai taji yace hakan yayi
yace amman ai kaman dole saida Jamb tace a'a taji ana cewa Basic Nursing ba saida Jamb ba yace Ok
tace mashi yanzu result kawae take jira yace Ok Allah yasa aga Alkhairi ta amsa da Amin, shiru suka d'an
yi can tace mashi yaushe zai zo idon shi akanta ya tambayi tana son ganin shi ne da sauri tace a'a ba
gashi ko yanzu tana ganin shi ba kawae ta tambaya ne yay nodding kai kafin yace mata bazai samu zuwa
yanzu ba tunda bai dad'e da yazo ba kuma Hajiya daga Abuja zata zo nan ta d'an zauna dasu Saboda
ganin likita tace Allah ya bata lafiya ya amsa da Amin daga baya da kanta tace bari ta k'yale shi ta hana
shi aiki yay d'an murmushi kawae yace mata take care ta d'aga kai daga haka ta katse kiran, d'akin
gwaggo ta nufa don ta fad'i mata ya warke ta iske har tayi bacci. Fatuu an samu natsuwa har ta koma
islamiyya washe gari yan islamiyyar sunyi farinciki da ganinta sai tambayarta ake yadda akai ta dawo
tace an fasa auren ne kawae Malam Nazifi har ke6ewa yay da ita ya tambayeta Allah yasa dae lafiya ta
dawo tace mashi lafiya lou dama bata son auren na dole ne za'a mata to kuma an fasa daga yanayin
fuskar shi ta fahimci yaji dad'in hakan yace ba komae bane ya ja hakan face Addu'a shiyasa ake son bawa
ya mik'a lamuransa wurin Ubangiji to kuwa a komae zai samu mafita Fatuu ta jinjina kai tay mashi godiya
sosae har yana tsokanarta yace sai a dasa rashin ji ko tana dariya tace ai ta daina wannan yanzu ta girma,
Washe gari bayan ta dawo daga islamiyyar safe ne Amadu ya shigo d'akinta lokacin tana cikin gyara
wardrobe d'inta ta kalleshi tana murmushi shima murmushi yake mata yace "Amaryar mu" tura mashi
baki tay tace don Allah ya bari bata so, wayarta ya kawo mata yace ta bashi tashi tace a'a Ya barta kawae
yace don me ai itama tana son abunta ko kuma ga Makaranta zata fara tace ai tashin ma lafiya lou daga
baya ta canza, duk yadda yay da ita k'in amsa tay k'arshe yay mata godiya ya tafi, acikin satin da ya kama
Haulat ta koma Nijar don bikinta bai fi saura sati biyu ba, ranar Laraba sai ga Baffan Fatuu sun kawo
Kayanta na kitchen kamar yadda yace Fatuu tay farincikin ganin shi sosae, a d'akin Fatun can gefe akai
masu wuri manyan kuma su freezer aka kai su d'akin Amadu bayan sun zauna da gwaggo ta tambaye shi
yadda akai da furniture d'in yace wad'anda suka yi su sun fanshe su duk da sun rage kud'in gwaggo ta
girgiza kai tace Allah ya kyauta bayan Gwaggo ta tafi Fatuu taje wurin shi d'akin Amadu da aka sauke shi
sukai fira anan ya bata kud'i dubu d'ari yace ta d'auki 50k d'inta da ta bashi tay amfani da sauran dubu
hamsin d'in gun shirye shiryen fara karatun ta dama cikon dubu d'arin data bashi kud'in sadakin ta ne,
k'in amsa tay tace ai ba sai ya maido mata ba itama ai Saboda auren aka bata yana dariya yace to ai ba'ai
auren ba ko ta dingi zuba mashi shagwabar bazata amsa ba yana dariya daga baya da k'yar ya sata ta
amsa kwanan shi biyu ran Friday ya tafi, Bayan sati guda suka shirya zuwa Niamey K'asar Nijar bikin
Haulat harda Kawu Amadu gwaggo tayi masu hidima sosae don kayan kitchen d'in Fatuu ta d'ibar mata
masu yawa harda zannuwan gado da labulaye innarsu haulat d'in kafin su tafi lokacin tay tsananin
farinciki da yake su da wuri suka tafi su kuma su Fatuu saida bikin ya zo, Tafiya yankin Azaba Fatuu an ji
jiki sai lokacin ta gane daga Katsina zuwa Adamawa ba komae bane akan wannan tafiyar da sukae don
farko Marad'i suka fara zuwa daga can suka hau luxurious bus suka kwana suna tafiya don ma Motar
nada dad'in hawa akwae su Ac harda Tv, lokacin da suka isa da k'yar take iya taka k'afafunta don tafiyar
tayi daga Katsina zuwa Lagos in ma bata fi ba, Haulat tay tsananin farinciki da zuwan nasu haka danginsu
sun tarbe su hannu bibbiyu an sha shagali an ci an sha anyi wadaqa da nama don mutan Nijar badai cin
nama ba bakamar in suna hidima gashi ba Laifi dangin mijin nada d'an hali saidae wani Abincin fa su
Fatuu kasa ci sukae sai wanda yay irin namu na nan, Alhamdulillah ranar Asabar aka d'aura auren Haulat
da Angonta wanda yake d'an uwanta ne wato Nuraddeen suna zaune Fatuu na dariya tace mata da
rabon dae sai ta rigata yin aure duk sukae dariya, Sosae Fatuu akai kasuwa don wanka na Mutunci ta
rink'a d'auka da bikin don ma gwaggo na taka mata burki har samari ta hanata saurara tace ba wannan
ne a gabanta ba to itama dai dama ba mai kula samarin bace, bayan biki da kwana biyu suka sake
d'aukko hanya aka taita yi har Allah ya maido su Lafiya Fatuu cike da kewar Aminiyarta, tun suna can aka
saki result d'in Waec suna dawowa Abbas yazo ya dauketa suka je dubawa gaba d'aya ta samu credit
saidae chemistry ne ta samu pass tun can ta fara k'walla don bata tsammaci hakan ba sakamakon tasan
ta maida hankali lokacin da sukae exams d'in gashi dole saida shi zata iya yin School of nursing din Abbas
ne ya shiga kwantar mata da hankali yace a jira Neco ta fito in sha Allahu yasan zata samu, koda ta dawo
gida ma gwaggo duk da bata ji dad'i ba amman bata nuna mata damuwa ba sosae itama tace a jira
d'ayar daga baya ma sai ga Haisam ya kirata don Abbas ya fad'i mashi komae harda yarda ta tashi
hankalinta sosae ya kwantar mata da hankali yace ai akwae alternative so a jira Neco fuska jage jage tace
mashi to anan ma saida ya k'ara ce mata lazy ta tura mashi baki daga baya sai gashi har saida yasata
dariya, bayan sati biyu Neco ta fito wannan karon k'in zuwa tay dubowar saidae Abbas ne yaje, a k'opar
gida ya tsaya bayan ya dawo ya kirata ta fito tunda ya tafi dubowar dama gabanta keta fad'uwa duk ta
sha jinin jikinta ba kamar da taga fuskar Abbas d'in bai dariya a gefe ta tsaya ta gaida shi a sanyaye ya
amsa duk ya d'an damu kaman zatai kuka tace mashi itama akwae matsala ko ya d'aga mata kai alamar
eh nan da nan tasa hannu zata fara matsar kwalla ya fiddo result d'in daga gefen shi ya mik'a mata, k'in
amsa tay tace ita mizatai dashi tunda bata ci abunda ake so ba saida ya d'an matsa mata sannan ta amsa
ta amman ta k'i dubawar yace ta duba mana, hannunta har rawa yake ta d'aga da ido d'aya ta d'an kalli
paper d'in da sauri kuma ta ware idanun a tunaninta ko abunda take gani gizau ne ba gaske ba, tabbatar
ma da kanta tay da sauri ta kalli Abbas taga yana murmushi a rud'e tasa hannu ta rufe bakinta ganin ta
cinye duka harda su A (distinctions) nan da nan ta fara murna tana yarfa hannu sai faman fad'in
Alhamdulillah take Abbas na mata dariya, koda ta shiga gida gwaggo ta gani tay matuk'ar murna harda
duk'awa wai Fatun ta hau ta goyata ta kuwa haye aikuwa da k'yar ta mik'e don ma gwaggon k'akk'arfa ce
dik'ir take, ganin tana ta nishi yasa Fatun saukkowa tana ta kyalkyatar dariya,

Lokacin da aka fara saida Form na Makarantar Abbas ne yaje Bank ya siyo mata ya kawo mata suka cike
tare suka maida can School d'in bayan wani lokaci suka je don yin jarabawar shiga wato Entrance exam a
lokacin ne ta had'u da wata da suka zauna tare har ta fad'a mata sunanta Fauziyya Ahmad ta tambayi
Fatun itama ta fad'i mata nata Fauziyyar tay masu Fatan Nasara Fatuu ta amsa da Amin, bayan sun gama
ne tace ma Fatuu ta bata phone no d'inta ta bata don ta lura tana da kirki ga fara'a bunu bunu tayi
murmushi, bayan kaman sati biyu da yin jarabawar aka kafe lists d'in wanda suka ci Fauziyya ce ta kira
Fatun ta sanar mata ta samu itama haka don taga sunanta cikin yan Katsina local Government itace ma
ta biyu sosae Fatuun tay murna duk da da sauran rina a kaba don dama farko sai su d'auki Mutane fin
d'ari cikin mutane wurin 500 koma fi da sukai applying sai a hankali za'ai ta zubar da su don bai wuce
Mutum 130 ko 150 bane zasu ci entrance exam d'in suma kuma wurin interview za'a k'ara zubar da wasu
haka Bayan an fara karatunma, cikin Nasara Fatuu taci interview da sukae ta samu Admission d'in
Kasimu Kopar Bae School Of Nursing Katsina dake acikin General Hospital, kowa yay farin ciki karma dae
gwaggo taji haka Abbas ma har Haisam saida ya kira ya tayata murna daga baya suka fara Class ranar
farko har Video call sukai da Haisam tana cikin fararen Uniform d'inta da takalma sai faman zabga
dariyar dad'i take ya k'ara tayata murna ya kuma ce sai ta d'age don still bata zama cikakkar daliba ba
har sai tayi passing Intro Exam tace in sha Allahu, tun ranar da suka je interview Fauzy kamar yadda
Fatun ta fara kiranta dama kuma tace haka ake ce mata ta tambayi Fatuu Day zatai ko Boarding tace
mata Day Fauzyn tace mi zai hana tayi Boarding don itama ita zatai Fatuu ta tambayeta ba'a nan garin
take bane tace eh ita yar Funtua ce amman akwae Yayarta dake Aure nan Katsina a Goruba Road, Fatuu
tace to ba sai ta zauna a wurinta ba Fauzyn tace ita tafi son zama a school don mutum yafi samun time
na karatu balle wannan Makarantar da ba'a wasa da karatu dole sai Mutum ya dage zadai ta rink'a zuwa
wurinta weekend, to bayan sun fara shiga Class ma saida ta k'ara yi ma Fatuu Maganar tace an bata d'aki
dama akwae wata yar garinsu da suka gama a d'akinsu zata zauna Don Allah ta dawo boarding sai su
zauna tare ganin yadda ta dage tana ta nuna mata Muhimmancin zama a cikin Makaranta ne yasa Fatuu
tace to in ta koma gida zata tambaya in an barta sai ta dawo Fauzy harda yi mata Addu'ar Allah yasa a
barta ita dae Fatuu yar dariya kawae tay, A ranar da daddare bayan sallar Magrib ta iske gwaggo a d'aki
ta gama salla ta zauna gefenta bayan tay mata sannu ne tayi mata Maganar komawarta boarding, shiru
gwaggo tay tana kallonta can ta nisa ta tambaye ta miyasa take son zama a Makarantar Fatun tace an fi
samun lokaci kuma ko Assignment aka bada mai wuya za'a taru ayi tare sannan ana tattaunawa game da
abunda aka koya, d'an jimm gwaggo tay kafin tace "Gaskiya ni banson zaman Makarantar nan don yana
da illoli ba kuma wai don ban yarda dake bane amman nafi son ki rink'a zuwa kina dawowa" gyad'a kai
Fatuu tay tace Shikenan Gwaggo ta fahimci yanzu duk inta nuna ga yadda take son abu bata gardama
mata hakan yasa tace mata in kamar an basu aikin ko zasu tattauna kan karatun zata iya tsayawa can
amman ba wai ta koma gaba d'aya ba Fatun tace to ta tashi ta koma d'akinta............

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._

*ASM Bk2036*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


.........Sosae Fatuu ta dage da karatu ita da Fauzy don seat d'in su guda a hankali suka zama abokai sosae
duk da ita Fatun Day take yi tare suke yin break wani lokacin daga gida tana kai mata abubuwan ci,
Bayan wata ukku sukayi jarabawar pre intro wadda daga ita bayan wasu wata ukun zasu yi intro exam
d'in wadda itace yar bala'en wadda kowa ke tsoro don mutane sosae ake zubar wa, cikin Nasara ita da
Fauzy sun ci pre intro din wad'anda basu ci ba kuma aka rink'a karfafa masu guiwa don su dage kafin ai
d'ayar. A bangaren Khalid yana can yana fama da ciwon so don tun bayan da aka fasa Auran su Allah ya
jarabe shi da tsananin son Fatuu gashi yasan ya rasata kenan har Abada don mahaifin shi kaifi dayane
kuma ita kanta Fatun ta rufe duk wata kafa da zai samu yin Magana da ita gaba d'aya ya zama salihin
k'arfi da yaji ga Dad d'in shi bai kula shi sosae bai dae yi fushi da shi ba amman bai shiga har kar shi Mom
ce kawae ke kula shi ta damu sosae da halin da yake ciki haka Sadeeya ma da tuni ta koma school tana
yawan kiran shi don jin yadda yake da kuma k'arfafa mashi gwuiwa kan ya daina damuwa, har Abokan
aikin shi wasu sun fahimci yana cikin damuwa, Ciwon so ba dad'i Khalid ma an d'and'ana Allah ya bada
lafiya.

Zaune suke a cikin d'akin su na Hostel da yake Saboda jarabawar dake gaban su yasa Fatuu ta dawo cikin
Makarantar kamar yadda sukae da gwaggo don itama tasan had'arin dake tattare da ita shiyasa ta barta
ta dawo don yin karatu sosae duk ranar Monday in tazo sai juma'a da an tashi take komawa gida, gado
biyu ne acikin d'akin nasu d'aya a 6angare dama d'aya kuma a hagu, d'akin baida girma sosae sun gyara
shi komae tsab, Fatuu na zaune saman gadon dake hagu tana facing Fauzy dake zaune a saman na dama
kowannen su ruk'e da littafi suna karatu akai akai suke tambayar juna abu, can bayan wani lokaci Fatuu
ta d'ago da niyyar yi mata magana sai taga ta kife fuskarta akan gwuiwowinta wanda da ba haka take ba,
kiran sunanta Fatuu tay shiru bata amsa ba hakan yasa tay tunanin ko bacci ne ya kwashe ta daga
karatu, d'aga murya tay tace "Fauzyyy tashi baki ga ta yin bacci ba a wannan lokacin in ba munyi passing
Intro ba" shiru bata tanka mata ba bata kuma d'ago ba ta sake kiran sunan ta da d'an k'arfi k'asa k'asa
taji muryar ta tace "ba bacci nike ba" yadda Fatuu taji sautin muryar ta sai taji kaman tana kuka da
alamun mamaki tace "to mi kike, naji kaman ma kuka kike ko" daga yadda take ta girgiza mata kai Fatun
tace to ta d'ago ta gani, a hankali ta sak'a hannunta ta cinyoyinta Fatuu na ganin haka ta gane so take ta
goge kwalla ne da sauri ta saukko daga kan gadon tana sanye da Vest da dogon skirt kan ta ba d'an
kwali, gadon da Fauzyn take ta haye tasa hannu ta d'ago da face d'inta, Har saida gabanta ya fad'i ganin
fuskar ta jage jage da hawaye sai kace ba ita bace suke karatu suna magana ba a d'an rud'e Fatuu ta
shiga tambayarta abunda ya faru take kuka shiru bata ce mata komae ba sai faman sheshsheka take
hakan yasa Fatuu cewa "Saboda Exam d'in da zamuyi kike kuka?" Girgiza kai tay da yar damuwa Fatuu
tace "To don Allah Fauzy miye?" cikin muryar kuka tace "Mujaheed........" Sai kuma ta Sake fashewa da
kukan kan Fatuu ne ya d'aure jin sunan da ta ambata ta rasa gane wanene shi sannan kuma miya faru da
shi, ganin wayarta a gefenta yasa Fatun cewa "Rasuwa yayi ne?" Da sauri ta girgiza mata kai alamar a'a,
d'an yarfa hannu Fatuu tay tace "to don Allah ki fad'a man waye shi kuma miya faru kinsa ni na rud'e fa"
shanye kukan Fauzy tay tasa hannu tana goge k'wallan kafin ta fara magana "Mujaheed shine silar zuwa
na wannan Makarantar Zarah na kasa man cewa da abunda yay man duk yadda naso na manta" cikin
d'aurewar kai Fatuu ta tambayi waye shi kuma miya mata, goge kwalla ta k'ara yi taci gaba "Tsohon
saurayi nane kusan in ce ma shine saurayi na farko kuma na k'arshe kusan shekararmu hud'u tare...."
Dakatawa tay ganin hakan yasa Fatuu sake tambayar ta abunda ya faru tsakanin su, cigaba tay "Mun
had'u dashi ne lokacin da na dawo gida nayi Jsce da yake Boarding nayi lokacin na raka wata Yayata
wadda muke uba d'aya don Matan babanmu biyu mamarmu da tasu dinner party d'in k'awarta to
lokacin da muka je sun tashi su da k'awayen su suna rawa an bar ni ni kadae zaune sai gashi ya zo inda
nike da murmushi ya tambayeni ya na zauna ni kadai bazan je nima in yi rawar ba na d'an yi mashi
murmushi kawae a tunani zai tafi ne sai kawai naga ya zauna kujerar kusa dani yaci gaba da latsa wayar
shi lokaci bayan lokaci yake d'agowa ya kalle ni da murmushi nima sai in d'an yi mashi can ya k'ara
d'agowa ya tambaye ni sunana na fad'a mashi Fauziyya da bud'ar bakin shi sai cewa yay sunan ya dace
da mai shi ina dae ta dariya daga baya ya mik'e ya bar wurin har yana ce man wai ya zo ya tayani fira ne
dama kyauta nace mashi Nagode, ba'a kaiga tashi ba muka fito don tafiya Saboda in muka kai har lokacin
da za'a gama to zamu ja ma kan mu ne wurin Abban mu dama da K'yar aka bar mu muka zo ba tare da
ya sani ba, muna fitowa sai ga mutumin ya biyo bayanmu yace man tafiya zamuyi na d'aga mashi kai sai
yace to bari yay dropping namu muka bishi inda ya parker Motar shi,lokacin da muka isa layin gidan mu
bamu k'arasa ba muka ce ya ajiye mu anan Farko farko ya tambayi ina ne gidan namu muka ce yana a
d'an can gaba yana murmushi yace to ya k'arasa damu mana da sauri muka ce a'a Ya tambayi dalili anan
Yayata Fareeda tace mashi bamu son baban mu ya gan mune yace Ok, dama ni ce a seat d'in gefen shi
kafin mu fita yace na bashi no d'ina nace ai ni ban fara rike waya ba ya tambayi dalili nace Saboda nayi
k'arama kuma Makarantar kwana nike yi yana yar dariya yace shi bai ga wata k'aranta tawa ba anan ya
tambayi ajina nawa nace mashi Jsce nayi zan tafi s.s 1 ganin ita Fareeda nada waya ne yasa yace to ko
tata ce a bashi sai mu rink'a gaisawa ya zama yayana harda tambayata ko ban so ina dariya nace mashi
ina so aka bashi ta Fareeda d'in, tun daga wannan lokacin muka fara yin waya dashi daga baya watarana
har yazo gidan mu da yake ba'a hana mu tsayawa da samari Saboda da mun gama Secondary Matan
gidan mu ake mana aure maza ne ke cigaba da karatu, yan gidan mu suka fara tsokanata nayi saurayi
don sun san ban saurarar samari ko zancen su ma ban so ay man inta faman rantse masu shi ba saurayi
na bane don bai ce yana so na ba sai su ce wai ai in aka ga kare na Sunsuna takalmi to d'auka zai, lokacin
dana tashi komawa S.s One sosae yay man hidima kinga uban provisions d'in da ya siya man muka raba
ni da K'anwata da muke makaranta d'aya ko Fareeda ma boarding tay amman ita lokacin da nayi Jsce ta
gama, bayan mun koma Makaranta Zaria saida nay yadda mukae muka rink'a waya da shi da wayar wani
malami mai shago da muke siyayya har lokacin kuma bai furta man so ba kuma har Visiting yake zuwa
man in dae yana Funtua...." D'an dakatawa tay tana maida numfashi Fatuu dae ta zuba mata ido duk ta
k'agu taji abunda yay matan can taci gaba "Saida muka shiga Ss 2 wato aji biyar sannan ya furta man
yana so na bayan mun dawo wani hutu, Sosae naji dad'in hakan don dama tuni ni na Kamu da son shi
Saboda Mujaheed Namiji ne wanda da wuya mace tay rejecting soyayyarshi yana da kyau sosae duk da
ba fari bane bak'i ne amman bak'in nashi mai kyau ne ba kamar da Yake hutu ya zauna mashi da yake
Family d'in su sanannu ne a garin suna da Kud'i, lokacin da ya furta man so na sanar da shi mu gidan mu
da an gama Secondary ake yin aure saidae mutum yaci gaba da karatu a d'akin mijin shi in yana so yace
man lafiya lou ai shima ya kusa kammala Karatun shi da yake a K'asar Malaysia ranar da farinciki na
kwana Zarah, koda yan gidan mu suka ji suma duk sunyi murna ba kamar mahaifiyata, tunda ya furta
man so ban sake kula wani Namiji ba don ya nuna man zai aure ni duk da kuwa lokacin sosae ake cewa
ana sona,tunda nike da Mujaheed a wannan lokacin bai ta6a nuna yana son ta6a jikina ba hakan ne ma
yasa nike k'ara bala'en son shi don a gani na mutumin kirki ne sai Bayan da na gama Secondary ne ya
fara kaman man hannu haka in muna zance wani lokacin har d'an kiss yake man a bayan hannu, sam
hakan bai canza daga kallon da nike mashi ba a ganina bai wuce iyaka ba, Bayan mun gama Secondary
da kamar wata d'aya watarana da yazo duk sai na ganshi a cikin damuwa na fara tambayar shi mi ke
damun shi farko ce man yay ba komae sai dana matsa mashi ne yace zai fad'a man don Allah in fahimce
shi kar in tada hankali na tunda naji hakan gabana ya fara fad'uwa amman sai nace mashi to kawai ya
kama hannuwana ya fara fad'a man wai a gidan su ne ake son had'a shi aure da wata Cousin d'in shi an
matsa mashi sai ya aure ta shi kuma baison ta ni yake so, wllh tunkan ya rufe baki jikina ya fara rawa nan
da nan sai kuka ban san lokacin da na fara rok'on shi kan ya fad'a man gaskiyar Magana in ita zai aura
amman sai ya nuna man shi fa ba wanda zai masa dole don haka in kwantar da hankali na dama kawai ya
fad'a man ne, sosae ya kwantar man da hankali lokacin har da hugging d'ina yay saida yaga hankali na ya
kwanta sosae sannan muka rabu...." K'ara dakatawa tay tana share kwallan da suke zubo mata kafin taci
gaba "bayan kaman sati biyu da yin hakan Mahaifina yasa in yazo in ce yana son ganinshi akayi hakan
bayan sun gama naje wurin shi yana murmushi yake fad'i man cewa akai ya turo sosae nai murna har na
kasa boyewa anan yake ce man amman yaba Dad d'ina hak'uri sai after 1 Month don Dad d'in shi bai
K'asar nace Allah ya maido shi lafiya, tun bayan wannan Maganar sai ya rage zuwa sai dae muyi waya har
tambayar shi nayi sai ya nuna man ba ya fad'i man Dad d'in shi bai nan ba to ai shike kula da harkokin
kasuwan cin shi nace na Fahimta, ina ganin acikin watan da yace a bashi bai fi sau biyu ko ukku ya zo ba
aka shiga wani watan to shi kwata kwata ma bai zo ba saidai waya har dae na k'ara mashi Maganar
turowa sai yake ce man tafiya ce ta kama shi in fad'a a gida ayi hak'uri sai ya dawo lokacin jikina ya fara
yin sanyi amman sanin yana tafiye tafiye yasa ban kawo komae ba nayi mashi fatan ya dawo lafiya, tun
daga wannan ranar inaga sau d'aya na k'ara yin waya da shi kullum wayarshi bata shiga haka in nayi
mashi Magana ta chat itama bata shiga a haka har akayi 1 month aka shiga wata na biyu tun ban
damuwa sosae hardai na fara ganin haka yasa Momynmu ta tambayeni kodae wani abu ya faru ne ko
munyi fad'a nace mata nidai nasan ba muyi fad'a ba kuma ban masa komae ba na fad'a mata Maganar
da yay Mun kafin ace ya turo ta auren Cousin d'in shi tunda naga yanayin fuskar ta a lokacin na fara
sarewa tace man kar in damu in ci gaba da Addu'a nace to, abu sai gashi har anyi wata ukku ba
Mujaheed babu dalilin shi a lokacin harna fara tunanin ko in je gidan su in duba in lafiya duk da bansan
ta ina zan fara ba don gidan su Babban gida ne, ban kaiga zuwa gidan ba bayan kwana biyu an aike mu
bakin kasuwa nida sister d'ina da muke boarding tare lokacin ta dawo Hutu muna tsaye bakin titi zamu
tsallaka kaman ance in juya sai na hango wani abokin Mujaheed mai suna Usman wanda sun sha zuwa
wurina tare da shi har da ina Makaranta ya ta6a zuwa dashi kusan sau biyu ya fito daga Motar shi ya nufi
wani shagon Pos aikuwa da sauri nace ma Ummi muje wurin shi, lokacin da ya ganni har saida naga
kaman ya d'an razana bayan Mun gaisa nace mashi ina Mujaheed ne farko shiru yay yanayin shi ya canja
lokaci guda na rud'e cikin rawar murya na tambaye shi kodae ya mutu ne da sauri ya girgiza man kai yace
yana nan raye na hau rok'on shi kan ya fad'a man yana ina da k'yar ya iya bud'e baki ya gaya man
Maganar da tunda nike a rayuwata ban ta6a jin abunda ya razanar da ni ba irin ta wai Mujaheed yayi
aure kusan wata ukku....." K'ara dakatawa tay tasa kuka sosae Fatuu da itama idanunta har sun cika da
kwalla ta jawota jikinta tana bata hakuri, bayan ta d'an tsagaita ne ta d'ago taci gaba ".....nidae tunda ya
fad'a man hakan ban san miya faru ba kawai dae na farka na ganni a gadon Asibiti ake sanar dani
kwanana biyu anan, Zaraah ko ban fad'a maki ba kema kinsan dole na shiga wani hali na samu
Heartbreak, nayi kuka har na gode Allah saida nayi sati biyu a Asibiti koda muka koma gida ma bai lafa ba
sai sambatu da koke koke ganin abun yay yawa yasa aka k'ara maida ni Asibiti anan likita ya tabbatar
kwakwalwata ta d'an ta6u a maida ni psychiatric muga likitan can a tak'aice dae can ma d'in nayi wani
watan har Doctor yace yakamata a nemo man abunda nike so amman da yake ran Abbanmu ya 6aci
sosae yace ko da wasa kar wani yace zai nemo Mujaheed har ya kira shi inyi hak'uri kawae don ko
dawowa yayi wllh bazai bashi aure na ba, sam banga laifin shi ba Saboda ya matuk'ar yarda dashi bashi
kad'ai bama duk yan gidanmu saboda yardar da Abbanmu yay dashi yasa har yake barin mu muna yin
zance a cikin Mota wanda ba wanda ya ta6a ma hakan dole saidae aje sitting room d'in shi ko kuma a
tsaya a waje amman badai a shiga cikin Mota ba, haka naci gaba da jinya a gida duk da yadda kowa ke
kokarin ganin ya faranta man kaman yadda likita ya bada shawara amman abun gaba yake k'arawa don
na kasa mantawa ga zuciya tay ta tunzura ni akwae ranar da har na d'aga maganin kwari zan sha k'arfin
imani ne ya hana, na dau tsawon lokaci ina cikin hali hardae na fara rarrashin zuciyata da kaina kaman
yadda kullum Mahaifiya ke nuna man in yi hakuri kar in ma kaina illa don shi yana can da matarshi bai
san ina yi ba, akai akai Usman ke zuwa duba ni dana fara warwarewa ne watarana nike ce mashi
Mujaheed ya zalunce ni da yayi man hakan don mi bazai gaya man zancen auren ba kamar yadda da
farko ya gaya man gidansu an matsa ya aure ta ai ni da zan fahimce shi ko mu biyu ne sai ya aura banda
matsala da hakan cike da tausayawa Usman yace bari ya fad'i man gaskiya ba wani matsa mashi da akai
dama can yana tare da ita cousin d'in tashi don tare ma sukayi karatu a Malaysia kawai ni yace ina
bala'en burge shi ne, yace man tun kafin mu dad'e tare dashi saida ya bashi shawarar indae yasan ba
Aure na zaiyi ba ya rabu dani Amman sai yace wai yasani ko Allah yasa ya aure nin ko da zai yi auren
saida yace mashi ya had'a mu ya aura sai yace wai gidan su baza'a bari ba, Saboda haka har d'an sa6ani
suka samu lokacin dashi har yana ce mashi wai to shi ya aure ni mana yace ba don sa rana dake a kan shi
ba wllh da ya Aure ni, wannan bayanin da Usman yay man yasa raina ya 6aci sosae wani irin haushin shi
yakamani don na fahimci shi d'in mugu ne macuci kuma Azzalumi in ba haka ba yasan akan shi nasan
miye so kuma Ba wanda nike tare dashi sai shi ko da wasa ban ta6a tunanin ba wani dama ba sai shi
amman bai ji komae ba ya iya rabuwa dani, ba abunda ya k'ara bani haushi irin cewa da yay wai burge
shi nike...., amman ba komae ai akwae Allah shi mai ji ne kuma mai gani ban mashi ko Allah ya isa ba
amman nasan sai Allah ya saka man wllh....." Fashewa tay da matsanancin kuka ta fad'a jikin Fatuu da ta
kumbura baki tamkar zata fashe wani irin takaici had'i da haushin Mujaheed d'in ne suka turnuk'e ta a
yadda take ji da yana a kusa da ita ba abunda zai hana ta d'udd'ura mashi ashar har bugu ma in tasamu
dama Wannan zalunci har ina kuma ita bata ga aibun Fauzy ba indae kyau ne Tubarkallah tana da shi
don su rumawa ne harda tsagar 11 gareta a gefen fuskarta ga farinta mai kyau ga gashi duk da bata kai
Fatuu ba amman tafi Fatuu tsawo sannan tana da d'an dirinta daidai gwargwado ko a hostel d'in ce ma
d'akin su ake d'akin kyawawa, (Uhmm irin hakan na faruwa ko a zahiri don wani 6angare na labarin nan
true life story ne, bansan miyasa wasu mazan ke yaudarar mata haka ba duk da a Matan ma ana samun
masu yaudarar maza amman ba kamar Mazan ba wanda hakan tsagwaron zalunci ne ko ba'a fad'a ba, ka
6ata ma yar mutane lokaci kayi mata k'arya ta d'auki dukkan yardarta ta d'aura akanka amman kazo ka
cuce ta wllh duk mai irin wannan yasani Allah bazai k'yale shi ba don kuwa ya haramta zalunci a tsakanin
bayin shi ba yadda za'ai mutum yay haka kuma yaci bulus, duk da mun san wani bai auren matar wani
haka wata bata auren mijin wata in ma rabuwar ta kama to ayi ta ba tare da an zalunci juna ba misali
kana son ta tsakani da Allah itama haka sai kuma Allah yasa kaddaro dole a rabu amman bawai tun farko
ayi tarraya ta k'arya ba kasan bazaka aureta ba initially don me zaka rufe, wasu Matan ta dalilin irin
hakan sun samu ta6in hankali wasu sun Kamu da ciwon zuciya wasu ma d'ungurugum kashe Kawunan su
suke Saboda an samu irin hakan ba sau d'aya ba ba sau biyu ba ko 6angaren labarin dana ta6o wanda ya
danganci yaudarar da akai ma Fauzy ita yarinyar ma tasha maganin k'warin Allah ne yasa da sauran
numfashinta gaba bata mutu ba amman ta shiga mawuyacin hali, anan nike son kira ga yan'uwana mata
musamman wad'anda aka yaudara da su rungumi hak'uri su d'auki hakan matsayin jarabawa suna zaune
Allah zai saka masu kar ki kuskura ki halaka Saboda wani k'ato wanda ba lalle ko gaisuwa yaje gidan ku
ba in kin mutu, nasan abun da rad'ad'i da ciwo dole zuciya ta girgiza amman in akayi hakuri duk na d'an
lokaci ne a yak'i zuciya kar a biye mata azo ai dana sani mara amfani yin hak'uri shine mafi Alkhairi
domin Allah yana tare da mai hakuri kuma bai barin zalunci).

"Yanzu ina Mujaheed d'in yake" Fatuu ta tambaya a zuciye, shanye kukan Fauzy tay tace "lokacin da
Usman ya fad'a man yace basu K'asar tunda sukae Auren amman daga baya watarana Mun ta6a
had'uwa a bakin hanya ya tsaya zai man Magana na k'i sauraren shi na tsallaka titi nay tafiyata, tun
bayan lokacin na tsani zancen soyayya balle kuma ace ana sona bana saurarar Mutum har lokacin kuma
ban daina jin son Mujaheed ba saidae kawae ina matuk'ar kokarin yakar zuciya ta kan ta manta shi, daga
baya ne ganin na warware Mijin Yayata na nan yayi ma Abban mu Magana kan ya barni inzo in yi Karatu
hakan zai sa in mance komae in ina shiga Mutane to shima din yana son in mance hakan yasa bai
gardama ba ya barni wanda nice mace ta farko a gidan mu da ta cigaba da karatu ba tare da tayi Aure ba
don ko ita Yayata Mareeya ta nan garin saida tayi aure tayi degree d'inta a nan" sauke ajiyar zuciya Fatuu
tay cikin sanyin murya tace "Kiyi hakuri Fauzy nasan yadda kike ji don nima na shiga irin wannan halin
nasan yadda rad'ad'in yake a zuciya duk da ba....." Da sauri Fauzy ta d'ago ta katseta "Zarah kema an yi
breaking heart d'in ki kenan?" Girgiza mata kai Fatuu tay tace "kusan hakan saidae ni ba wani ne yayi
man hakan ba nice na ja ma kaina don son maso wani nayi koma ince nike yi Saboda har yanzu nima
abun na damuna acikin zuciya amman na samu sauk'i sosae don ma still ina tare dashi shiyasa na kasa
cire shi a raina kwata kwata" idanunta ne itama suka ciko da k'walla cike da mamaki Fauzy ta tambaye ta
wanene don ita kallon wadda bata kula samari take mata, ganin tayi shiru yasa ta k'ara ce mata don
Allah ta fad'i mata mana ko bata yarda da ita bane kamar yadda ita ta yarda da ita Fatun tace a'a ta
yarda da ita mana nan ta fad'i mata ko waye take so, da tsananin mamaki Fauzy tace "Ya Haisam dai da
na san pictures d'inshi a wayanki wanda rannan ina maki wasa nace don Allah ki had'a ni da shi?" d'aga
mata kai Fatun tay Fauzy ta sake cewa "Amma ba kince man Yayanki bane dama ba d'an gidan ku bane?"
Ajiyar zuciya Fatun ta sauke kafin ta fara bata labarin tsakaninta da Haisam tun daga farkon haduwarsu
har zuwa lokacin da ya tafi harda bayan tafiyar tashi da auranta da aka fasa har ta fara karatu, da
tsananin mamaki Fauzy tace "Dama a gaske akwae irin wannan Mutanen da zasu rink'a yi ma mutum
Alkhairi haka don Allah! Kai gaskiya koma akwae to da wuya a samu sai dace, gaskiya banga laifin k'awar
ki Haulat ba don ko nice wllh irin tunaninta zanyi akan shi, ko bata fad'a bama irin wannan dole zuciyar
mutum ta kamu da son shi don ita tana son mai kyautata mata ni kaina iya labarin nan da kika ban baki ji
yadda ya k'ara burge ni ba sosae wllh, amman na matuk'ar tausaya maki Zarah irin wannan a kwae ciwo
ace kana son mutun amman bai sani ba" d'an ta6e baki Fatuu tay tasa hannu tana goge sauran kwallan
dake fuskarta can Fauzy tace "Amman fa da ace lokacin muna tare dake ni zan baki shawarar ki fad'a
masa ne koma in je in fad'i mashin" d'an waro ido Fatuu tay Fauzy ta jinjina kai tace "am serious duk da
ita Friend en ki da Uncle d'inki sun fad'a maki abunda yake daidai amman ni nayi la'akari da yanayin shi
na Mutum ne da yasan darajar mutane mara wulakanci mai fahimta sannan mai son yaga farincikin wani
don kin fad'a mashi bana tunanin zai k'i fahimtar ki tunda ai yasan yadda zuciya take kuma yana daga
cikin wad'anda suka fi kowa sanin halin ki balle ace k'imar ki zata zube ko yaga baki da kunya" d'an
murmushi Fatuu dake ta bin ta da ido tay kaman bazata ce komae ba sai kuma a sanyaye tace "to ko na
fad'a mashin ai bashi da wani amfani kamar yadda kowa yace tunda yana da wanda yake so zai aura
k'arshe hak'uri kawae zai bani" Fauzy tace "Yes he might do dat and he might not also kar ki manta yana
son farincikin ki ina tunanin zai iya amincewa ko don farincikin ki ita kuma Matar tashi in har tana son shi
da Gaske zata amince" d'an murmushi Fatuu ta sake yi tana girgiza kai tace "Don baki san yadda take son
shi bane wannan ai dole tay tsananin kishin shi ma wllh ban tunanin zata iya amincewa ya aureta ita da
wata ko dangin shi ba lalle su yarda ba tunda yar uwar shi ce" gyad'a kai Fauzy tai kafin tace "ina rok'on
Allah yasa rabon ki ne shi ya cusa mashi tsananin son ki har ya kasa zama ya dawo yace a d'aura maku
aure ko baki gama karatun ba" wani kallo Fatuu ta bita dashi Fauzyn tay yar dariya tace ko bata so ta
d'an ta6e baki kawae kafin tace itama tana mata Addu'ar Allah ya bata

Wanda take so da sauri tace "Mujaheed ne kadae na so kuma a yanzu ko ya dawo wllh tllh bazan Aure
shi ba duk da kuwa har yanzu da sauran son shi a zuciyata amman ko ke ai bazaki ban shawarar in Aure
shi ba" jinjina kai Fatuu tay "hakane nima na fad'a ne kawae amman ban fatar wannan azzalumin ya
zama mijin ki don baisan darajar dan'adam ba ki manta da shi kawae kina zaune Allah zai kawo maki
wanda ya fi shi a komae yanzu mu dage da karatun dake gaban mu shi yafi ba tunanin wasu da basu san
ma muna yi ba k'arshe Muzo muja ma kan mu matsala su sun riga sun gina rayuwarsu" sosae Fatuu ta
shiga bata shawarwari kan ta daina damuwa da wani Mujaheed su maida hankali, mik'ewa Fatun tay
tana fad'in itafa wllh yunwa ma take ji ta koma gadonta Fauzy da ke kallonta tace ko ta dafa masu
indomie ne,

"Ni dae na gaji da cin wata indomie wllh" yar dariya Fauzy tay tace "to ai itace mai sauk'in dafawa a
halin karatun nan da muke ciki yar gidan Ya Handsome, to ko in dafa mana Macaroni sai asa sardine
nasan zata yi dad'i" d'an yamutsa baki Fatuu tai ta fara k'ok'arin saukkowa daga gadon tana fad'in ita dae
bari ta fara shan Cornflakes gaskia bata iya jira har sai an dafa wani Abinci ta nufi inda Provisions d'in su
suke idanun Fauzy a kanta can tace "Wai ashe Ya Handsome d'in ki ne yasa maki Zarah da kika ce man
haka ake ce maki" daga inda take ta d'aga mata kai ta k'ara cewa "Allah sarki wllh k'awar nan taki ta
burgeni tana ina?" tace mata tayi Aure tana Nijar

"Da wuya yanzu ka samu irin su don k'awance yanzu ya zama abunda ya zama shiyasa ni tsoron tara
k'awaye ma nike ko da can, amman dae ke nasan nayi dace don tunda na gan ki kika burge ni kuma in
sha Allahu nima zan zamar maki madad'in Haulat bazan ce fin ta ba don duk abunda ake so a k'awa tana
dashi, tana son ki da Alkhairi bata maki bakin ciki da hassada farin cikin ki shine nata haka damuwar ki
damuwarta ce bata maki kallon bare face Yar'uwa wad'annan abubuwan duk an rasa su a k'awancen
yanzu da k'yar ake samun masu wasu daga ciki Allah yasa mudace mufi k'arfin zukatan mu dae" daga
inda take ta amsa mata da Amin tana murmushi,
"Amman dae watarana yakamata mukai mata ziyara har Nijar d'in" Fauzy ta fad'a, da sauri Fatuu ta
kalleta ta zaro ido tace "tabb ai saidae ko in ta haihu kin kuwa san yadda tafiyar take a kwana a wuni ana
abu guda lokacin da muka je bikinta baki ga yadda kafafuwana suka sumbuk'e ba" dariya Fauzy tasa
lokacin Fatun ta kawo mata cup d'in Cornflakes data had'a mata itama ta amsa tana murmushi tace
mata thanks suka fara sha.

Sosae su Fatuu suka dage da karatu don tsallake ma had'arin dake tattare da jarabawar intro dake
gabato su, Bayan wata ukku da yin pre intro suka yi ita intro d'in, cikin hukuncin ubangiji Fatuu ta
tsallake don sunanta ma ne farko a list d'in haka Fauzy ma ta tsallake sai faman murna wad'anda suka ci
suke suna kiran clean pass yayin da wad'anda basu samu ba ke a mawuyacin hali harda masu suma abun
ba dad'i wllh to amman haka tsarin yake dole sai Mutum ya dage yanzu wata shiddan da suka 6ata ya
tashi a banza sai dae hak'uri, bayan cin jarabawar ne akai masu clinical posting nan cikin Asibitin saidai
ba'a kai Fatuu da Fauzy wuri d'aya ba Fatuu Gyne aka kaita ita kuma Fauzy tana a A&E (Accident &
Emergency), su Fatuu an fara kama hanyar zama ma'aikaciyar lafiya hadda su farin glasses take sanyawa
yanzu kuma ba k'aramin kyau yake mata ba sai tayi kaman cikakkiyar nurse ba Student ba patients da
masu jinyarsu sai dae kaji anata Sister sosae Fatuu ke jin tausayin irin halin da Matan wurin ke ciki masu
lalurar data danganci haihuwa da sauransu.

Ranar Friday bayan sallar Juma'a Fatuu ta dawo daga Makaranta don sun tsaya Hostel saida aka yi salla
tana shiga gida ta aje Bagpack d'inta mai kyau mai manne da

Yar teddy jikinta sanye da sababbin uniform d'in data canza da suka zama cikakkun dali6ai, a gefen
kitchen ta aje jakar ta nufi toilet abun ya riga ya zame mata jiki da wuya ta shigo gida bata wuce toilet
ba, bayan ta fito ta d'auki jakar ta wuce ciki, d'akin gwaggo ta nufa ta d'aga labulan lokacin tana kwance
akan gado saidae ba bacci take ba suna had'a ido suka sakar ma juna murmushi Fatuu ta shiga ta zauna a
bakin gadon Gwaggo tace "ai na ji shigowar ki halan saida akai abunda aka saba?" Dariya tayi tace "ni
gwaggo banson yin fitsari a wani wuri wllh kyankyami nike ji ga toilet infection da ake kamuwa da shi in
mai cutar yayi using wuri kaima kayi shiyasa ko a Makaranta in ina can indae zan yi amfani da toilet to sai
na wanke shi fess sannan fitsari ma a tsaye nike yi sai in bi da ruwa aita ce man sarkin tsafta kuma ni
infection d'in nike tsoro don muguwar cuta ce" jinjina kai gwaggo tay tace "tabbas kuwa don har
haihuwa take hanawa, akwae wasu saiwowin magani ma da nasa a kawo sai ki rink'a amfani dasu har
acan Makarantar na tsarki ne akwae kuma na sha don wani lokacin duk yadda kake kiyayewa sai kiga ka
kamu baka sani ba gara kana yin riga kafi" d'aga kai Fatun tayi gwaggo ta tambayeta ya Makarantar tace
Alhamdulillah nan ta shiga bata labarin maras lafiyan dake ward d'in da take gwaggon nata girgiza kai
tana Addu'ar Allah ya basu lafiya can tace mata bata jin yunwa ne taga bata nemi Abinci ba tace eh da
yake sun biya hostel sun ci abu gwaggo ta tambayeta Fauziyya tace itama ta tafi Weekend gidan Yayarta
tace Allah sarki daga haka suka d'an yi shiru can tace "Na manta ban fad'a maki ba Hajiyar Sanata fa ta
dawo d'azun bayan kin tafi Makaranta don har na ma shiga na gano ta" waro ido Fatuu tay sai kuma tay
yar dariyar farinciki tace "Allah sarki Hajiyata ashe ta dawo wllh nayi missing d'inta" gwaggo na
murmushi tace "itama haka don sai tambayarki take wllh ba kamar da ta ji abunda ya faru ta jajanta
sosae har tace ta k'osa ta ganki" mik'ewa Fatuu tay da sauri tace bari taje to gwaggo ta d'aga mata kai ta
nufi hanyar fita, bayan ta aje jakar goyon tata a d'aki ta fito ba tare da ta cire uniform d'in ba da glass
d'inta manne a fuska ta nufi gidan Hajiyar Sanata.............

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._

*ASM Bk2037*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.........A bakin gate ta tsaya suka gaisa da Officer har yana ce mata yaushe za'ai mashi allura tana dariya
tace sai ya shirya daga haka ta shige, lokacin data shiga Parlon ba kowa saidae a gyare yake tsab sai
daddadan k'amshi ne ke tashi, Bedroom d'in Hajiya ta wuce ta tura ta shiga a hankali da yar sallama
idonta suka sauka akan Hajiyar dake kwance saman gado ta d'ago kai don ganin mai shigowa suna had'a
ido Fatuu ta sakar mata murmushi Hajiya ta yunk'ura tana kokarin tashi zaune itama da murmushin akan
fuskarta, daga gaban gadon ta tsaya tace "Hajiyar Sanata ina wuni an dawo lafiya" da hannu ta nuna
mata gefen ta alamar ta zauna tana amsa gaisuwar tata, dafa Shoulder d'inta tay da murmushi tace "Ma
sha Allahu Fateema yar Makaranta naji dad'in ganin ki haka sosae, ashe abu haka ya kasance da bani
nan?" Kai Fatuu ta d'aga a hankali tace mata eh, tace "An gode ma Allah daya kawo k'arshen Al'amarin
cikin sauk'i duk aikin Addu'a ne da kuma biyayya da kika ma mahaifin ki shiyasa ya za6a maki abunda yafi
zama Alkhairi" ita dae Fatuu murmushi kawae take can tace mata ya jiki still da fara'a ta amsa "Ah k'afa
Alhamdulillah na samu sauk'i tuni fa sune suka hana ni dawowa wai sai in zauna can" yar dariya Fatuu
tay tace "suna son su rink'a ganinki a kusa dasu ne Hajiya" ta6e baki tay "suda suke tafiyar su aiki su
barni yini zungur daga ni sai mai aiki to ba gwara a k'yale ni in dawo ba, shiyasa ina ganin Azumi ya taho
nace to wllh gida zan dawo in yi shi cikin yan'uwana ba Arziki da suka ga ina niyyar hana masu sukuni aka
barni na dawo" ta k'arasa tana yar dariya itama Fatun dariyar take Hajiyar tace "To ya Karatun Fateema
ana maida hankali ko" kai ta d'aga tace mata eh sosae, tace "Kin iya allura?" Fatuu na dariya tace "na iya
ta tuni bama ita kadae ba na iya abubuwan duk da aka nuna mana sosae don yanzu muna cikin Asibiti
ne" jinjina kai Hajiya tay tace "Ma sha Allahu kice ni yanzu ina da mai duba ni a gida, Allah Ubangiji yasa
ma karatun Albarka ya bada sa'a Amin" itama Fatuu ta amsa da Amin, shiru suka d'an yi can Hajiyar tace
"Fateema kije ki ci Abinci naga kaman yanzu Kika dawo daga Makarantar dama Akwae na Yayan ki da bai
ci ba akan table d'in" da sauri Fatuu ta d'aga ido ta kalli Hajiya jin abunda tace kafin da mamaki akan
fuskarta tace "Ya Haisam yazo ne?" Hajiya tace "Eh tare muka zo shi ya maido ni saida nace ma ya tsaya
Saboda aikin shi zan iya dawowa amman ya k'iya sai kace zan 6ace, tunda muka dawo ma ya fita kinga
har yanzu bai dawo ba k'ilan ko wurin Abbas yaje" shiru Fatuu tay fuskarta da d'an murmushi sai kuma ta
sunkuyar da kanta ta rasa gane farinciki take da jin yazo ko kuwa can ta d'ago tace ma Hajiya bari ta
barta ta huta anjima ta dawo hajiyar tace bazata ci Abincin ba tace a k'oshe take daga haka ta mik'e tay
mata sai anjima Hajiyar nata mata Murmushi sosae take jin dad'in ganin Fatuu haka da ka kalleta yanzu
kasan bata da damuwa ta dawo kamar da koma ta fi don har kumatu ta k'ara sai kace ba Student ba ga
Fuskarta ta k'ara yin Smooth hakan yasa Farinta ya fito sosae, Fatuu na fitowa ta maida glasses d'inta a
fuska dama da zata shiga d'akin Hajiyar ne ta cire, kamar taje d'akin Saude sai tay tunanin k'ilan ma bacci
take hakan yasa ta nufi hanyar fita daga parlon, tana zuwa kopar Fita Haisam na shigowa har saura
kad'an su bangaje juna da sauri Fatuu ta dawo baya ta tsaya ta kai idonta kan shi shima kallon nata yake
yana sanye da farar shadda k'al anyi mata Fav d'inkin shi wato sen style ta amshe shi Sosae d'inkin ya
bayyanar da kirar shi ta k'akkarfa kan shi ba hula sai sumar shi dake faman salk'i, wani fitinannan k'amshi
ke tashi daga jikin shi, bin juna sukae da ido Fatuu ta kasa tanka mashi sai faman had'iyar abu take a
yadda taga Fuskar shi ta dawo daidai ba kamar can baya ba da ta fad'a Saboda ciwon da yace mata yayi
gashi yay wani irin fresh Fatar nan ta k'ara mulkewa to weather ba d'aya ba ga sajen da ya fara bari
sumar ta d'an k'ara yawa a kwance lub amman bai barta ta taru sosae ba, wani kalan kallon k'urulla
yake mata tun daga sama har k'asa ganin haka yasa ta kai hannu a hankali ta cire glass d'in fuskarta ta
ruk'e a hannu kafin da k'yar Saboda tunda ta gan shi k'irjinta ke wani irin bugu ga wani abu da ya tsarga
mata tun daga kanta har zuwa babban yatsan ta tace "Sannu da zuwa, anzo lafiya" bai bata amsa ba sai
yay mata alamar su shiga da hannu ta ja gefe ya fara wucewa kafin ta bi bayanshi tana kallon yadda yake
tafiyar shi mai cike da isa duk da ba don nuna isar yake yin ta ba haka yake tafiya dama, saman sofa 3
seater ya zauna Fatuu na kokarin zama kan 1 seater dake can gefe yay mata nuni da d'an can gefen shi
alamar ta zo ta zauna, bayan ta zaunan shiru tay tana d'an kallon shi sai kuma ta kauda kai shima still
idanun shi na akanta sai duk ta tsargu da kallon nata da yake tayi sanin shi ba mai kafe mutum da ido
bane kamar yadda shima bai son a kafe shi da idanun,
"Ya School?" taji saukar cool voice d'in shi lokacin ta d'an duk'ar da kanta tana wasa da glass d'in
hannunta, d'agowa tay suka had'a ido a hankali tace mashi Alhamdulillah ya jinjina kai sai kuma ya k'ara
cewa "hope u'r concentrating?" Da sauri ta d'aga mashi kai alamar eh bai ce mata komae ba sai ita tace
mashi ya Aunty Fanan ya amsa da tana lafiya tana gaisheta tace tana amsawa suka d'an k'ara yin shiru ta
maida kanta k'asa kaman daga sama taji yace "baki tambayi ko ta haihu ba" da sauri ta kalleshi sai taga
yay d'an murmushi d'an kwa6e fuska tay tace "ai in ta haihu zan ji ko" ta6e baki yay kawae wata shirun
ta biyo baya sai take ganin kaman ya canza mata don a waya sosae yake sakar mata baki suyi Magana
duk da a nan ma d'in wata Maganar sai ya d'an ja lokaci kafin yayi ta tunawa tayi da koda can ai baya
Maganar sosae itace ke ja har yayi yasa bata kawo komae a ranta ba, wayarta ce da ke acikin Aljihun
rigar uniform d'inta ta fara ringing ta kai hannu ta ciro sunan Fauzy ne ya bayyana akan Screen d'in tay
picking bayan ta kara a kunne suka fara magana tambayarta tay ya taje gida ya su gwaggo ta amsa mata
da lafiya lou suke itama ta tambayeta Aunty Mareeya daga baya suka yi sallama Fatun na jin da ita kad'ai
ce da ta fad'i mata Ya Haisam yazo, bayan ta cire wayar ruk'eta tay a hannu tana d'an tatta6a ta jin
shirun Haisam d'in yay yawa yasa ta juya ta kalleshi sai taga shima ya d'ago ya kalleta ranta ne ya bata
wayar hannunta yake kallo hakan yasa lokaci guda ta kama kanta cikin d'an rawar murya tace "D....dama
ba waccan wayar bace daka siya man, ita lokacin da zan tafi Yola ne sai mukai musanya na amshi ta
Kawu Amadu Saboda naga shi zata fi mashi amfani a nan tunda mu bamu da network mai kyau to dana
dawo aka fasa auren shine ya maido man sai nace ya barta nak'i amsa da ya matsa man, to da Baffana
yazo maido kaya ne ya bani dubu d'ari duba hamsin Ya Abbas ne ya bani sai dubu hamsin shi ya bani
yace in yi amfanin Makaranta to shi ya Abbas dama Saboda Auren ne ya bani su da nayi mashi maganar
su daga baya sai yace ai ya riga ya bani ne kyauta shine na had'a da wayar Kawu Amadun da kud'in na
bashi ya canza man wannan" ta k'arasa tana nuna mashi wayar shi kam tunda ta fara mashi Maganar
bakinta kawae yake kallo har ta gama ganin tana mik'o mashi wayar ya d'an ta6e baki kawae had'i da
d'an murmushin gefe don ya fahimci tayi tunanin wayar yake kallo yasa tay mashi dogon bayanin
abunda bata sani ba shi yanzu yama manta wace irin wayace ya siya mata, ganin ya k'i amsa ya bita da
ido kawae yasa ta d'an tura mashi baki ta janye wayar shi kuma gyara zama yay ya d'an kwantar da kan
shi yana facing sama ganin haka yasa tace "Bazaka ci Abinci ba?" d'an jimm yay sai kuma ya jiyo da
fuskar shi ya kalleta ta sake cewa "Hajiya tace baka ci Abincin ba ka fita" fuskar shi a sake ya d'age mata
gira yace "Tambayarta kikae ne?" Da sauri ta girgiza mashi kai ta fad'i mashi yadda akai ta sani yay shiru
kawae, ba wata yunwa yake ji ba amman jin ita bata ci ba yasa ya yunk'ura ya fara kokarin mik'ewa
bayan ya tashi yace mata zaije Masallaci in ya dawo sai su ci daga haka ya nufi hanyar fita don da suna
zaune aka fara kiran sallar la'asar, bin shi tay da ido har ya kusa kai bakin kopar ta ga ya d'aga hannunshi
na dama ya had'e yatsunshi biyu suka d'an yi sauti nan take ta gane mi hakan ke nufi wato yasan kallon
shi take, murmushi tay ta jingina da kujera komae na shi mai burgewa ne Allah ne shaidar ta tana
tsananin son shi saidae ba yadda zatai k'addara ta riga fata, ganin zuciyarta na kokarin maida ta ruwa
don har k'walla sun fara taran mata a idanu yasa tay saurin kawar da tunanin ta yunk'ura ta mik'e itama,
d'akin Saude ta nufa lokacin data shiga Sauden ta fito daga toilet da alamu Alwala tayi tana ganinta ta
washe baki tace "Fateema yan Makaranta an dawo" itama murmushi take mata tace "Eh Aunty Saude
kin dawo lafiya" ta amsa mata da lafiya lou Fatun tace mata zata yi salla ne ta amsa da to ta nufi Toilet,
bayan tayo Alwalar a kusa da Sauden ta shimfid'a abun salla ta kabbara, saida suka gama sannan Saude
tayi mata Maganar Aurenta da aka fasa tace d'azun da gwaggo ta shigo take fad'a masu taji mata dad'i
Allah yasa haka yafi zama Alkhairi Fatuu ta amsa da Amin can wayarta ta fara ringing ta kai hannu gefen
Katifa ta d'aukko sunan Ya Haisam ta gani hakan yasa ba tay picking ba ta yunk'ura tay ma Saude Sallama
ta fice,

Zaune a Dining area ta hango shi ta nufi can yana ta lallatsa wayar shi ganin haka yasa ta fara k'ok'arin
serving nashi ta tambaye shi mi zai ci yace mata abunda ya kamata d'an murmushi kawae tay ta fara
zuba mashi gaba d'aya sanyayyan k'amshin da jikinta ke saki ya cika mashi hanci saidae bazaka ta6a gane
yanayin shi ba lokacin idon shi na akan wayar hannun shi baya ta gama ne tace "Ya Haisam bismilla"
Slowly ya d'ago ya kalli Abincin da ta zuba mashi shak'e da plate kafin ya d'aga idon ya kalleta ta nufi
d'ayan bangaren ta zauna opposite dashi ganin kallon da yake mata ta kuma san dalili yasa ta yin yar
dariya tace "ai nasan yanzu kana cin Abinci sosae shiyasa na zuba maka haka" d'an murmushin da iyakar
shi lips d'inshi yay kafin yace "Who told u?" tura baki tay tace "Ba kayi aure ba" wani kalan kallo yake
mata har saida tasha jinin jikinta a d'an rud'e tace "dama na ta6a ji Ya Abbas yace in kayi aure zaka rink'a
cin Abinci hannu baka hannu kwarya lokacin daka fara kaini gidan shiyasa nace haka" ta k'arasa had'i da
sunnar da kai still kallonta yake ya kuma tuna da lokacin da Abbas d'in yay Maganar kusan 4yrs yanzu
amman bata manta ba, hannu ya kai ya d'auki spoon ya fara cin Abincin a nutse itama ta fara kokarin
zubawa saidae kaman rabin nashi ta zuba tana yi tana satar kallonshi yay kaman bai ganin mi take yi,
tana fara ci ya dakata yace "how can u eat comfortably da wannan" yay Maganar yana mata nuni da kan
shi ta gane Hijab d'in jikinta yake nufi hakan yasa ta kai hannu ta cire ta dama yar k'arama ce saidae
kuma kanta ba kallabi sai tulin gashita dake fake ganin bai kamata ta zauna ba kallabi ba kuma ana cin
Abinci yasa ta ninka Hijab din tay irin d'aurin ture kaga tsiyar nan taci gaba da cin Abincin, wohoho maza
masu abun ban mamaki wai kuma sai yadda d'aurin yay mata yay mashi kyau ba kamar yadda tulin
gashin ya fito waje ko don matarshi ba irin gashin gareta ba kuma ita ta saba sakin shi oho dae shi yasan
dalili, duk in ta d'ago sai sun had'a ido yana kallonta sai ta d'an mashi murmushi abun mamaki saiga
Haisam ya take Abinci ba tare daya ankare ba abun shima ya matuk'ar bashi mamaki Fatuu kuwa ta hau
yi mashi dariya tana fad'in ashe Ya Abbas da gaske yake saidae kawae yay mata murmushi, kusan a tare
suka gama Fatuu ta kwashe kayan da sukayi amfani dasu takai kitchen saida ta wanke su sannan ta fito
ta maida hijab d'inta lokacin shi har ya koma cikin parlon hakan yasa ta nufi can tana zuwa a gefen shi ta
tsaya tace zata wuce gida d'an shiru yay yana kallonta sai kuma ya mik'e yace suje zai bata abu yay gaba
tabi bayan shi, hanyar part d'in shi ya nufa hakan yasa tabi shi lokacin da ta shiga Falon har bata san
sadda ta saki murmushi ba bata yi zaton zata k'ara shigowa cikin shi ba duk da tasan dama dole zai rink'a
zuwa to amman a tunanin ta zai rink'a zuwa da Matar shine, ce mata yay ta zauna shi kuma ya nufi
hanyar Bedroom ta ci gaba da k'are ma parlon kallo tamkar yau ta fara shigowa kuma yana nan yadda
yake ba abunda ya canza sai gyara da yasha k'amshi na tashi, bayan wani lokaci ya fito hannun shi ruke
da abu da bata gane ko minene ba a gefenta ya ajiye sai lokacin ta gane sabuwar Laptop ce ya koma
daga can gefe ya zauna ganin ta bishi da ido yasa a hankali yace tata ce tayi amfani da ita d'an waro ido
tay sai kuma tay murmushi tace mashi ta gode Allah ya saka da Alkhairi ya k'ara bud'i ya jinjina mata kai
can kuma sai ta d'an kwa6e fuska ganin haka yace "What?" A shagwa6e tace "ban wani iya amfani da ita
ba" still yay yana kallonta kafin yace a Secondary school ba'a koya masu ba ne tace "an koya mana
amman ai duk theory ake duka bai fi sau a k'irga ba aka kaimu Lab yin practical kuma mudae in munje
game d'in jirgi dana had'a bangarorin jikin mutum muke" yadda tay Maganar sai kace wata k'aramar
yarinya yasa shi yin dariya batare da ya shirya ba ta zuba mashi ido tana kallon tsantsar kyau bayan ya
dakata ya d'age mata gira yace "shikenan ai sai kici gaba da game d'in jirgin" tura mashi baki tay tana
yamutsa fuska ganin haka yasa shi mik'a dogon yatsan shi ta kalli tissue box d'in da yake nuna mata sai
kuma ta kalleshi cikin rashin fahimta yace mata in ta fara kuka sai ta yaga ta goge tunda kuka bai mata
wuya sai lokacin ta fahimci abunda yake nufi tay dariya sigh yay yace taje da daddare zai zo ya koya mata
abunda ya kamata tace to ta d'auki laptop d'in had'i da mik'ewa tace mashi sai anjima ya jinjina mata kai
kawae ta nufi hanyar fita, bayan ta fice d'age kan shi yay yayin da a ranshi ya fara tunanin wani abu da
shi kadae yasan minene, ya dan d'auki lokaci a haka kafin ya yunk'ura ya mik'e duk jin jikinshi yake wani
iri hakan yasa shi yin tunanin tafiya Gym ya nufi Bedroom don ya shirya. Cike da farinciki Fatuu take
nuna ma gwaggo Laptop d'in itama sai washe baki take tana saka Albarka kamar yasan Fatun dama ta
fara Maganar siyan computer d'in har tambayarta gwaggo tayi ko ita tace ma shi tana buk'atar ta ne da
sauri tace mata a'a wllh da kan shi ya kawo mata tace yayi kyau bata son ta rink'a tambayarshi abu ta
bari sai in shi ya tambayeta sannan Fatun tace mata to dama ita bata hakan kokarin tashi ta fara yi don
taje tayi wanka, bayan ta gama ta shiryawa da doguwar riga mai gajeran hannu gwaggo ta shigo cikin
d'akin Fatuu ta kalleta da murmushi ta nufi bakin gado ta zauna itama Fatuu zama tay gwaggon tace har
ta gama shiryawa tace eh, shiru ta d'an yi sai kuma tace "da nace wai tunda Abinci tazarce muka yi ko
za'a had'a mashi wani abu maras nauyi haka?" Fatuu dake kallonta tace "wai Ya Haisam" tace "Eh ba
kince zai zo koya maki Computer d'in ba?" d'aga kai tay tace "Eh haka yace, to mi za'a had'a?" d'an shiru
gwaggo tay alamar tunani kafin tace "ko ayi mashi fatan dankalin turawa yaji Alaiyahu" Fatuu tace "eh
kuma kinga ba Abinci bane mai nauyi dama asa harda kifi" yar dariya gwaggo tay tace to bari sai a siyo
gasasshen kifi tarwad'a ayi amfani dashi ta tambayeta da ta wuto shagon Amadu yana ciki tace mata a'a
a rufe yake tace to bari ta kira taji k'ilan ma kasuwa ya wuce daga Makaranta in yana can ma sai ya siyo
komae daga haka ta mik'e ta nufi hanyar fita, bayan ta koma d'aki ta kira Amadun cikin sa'a kuwa yace
mata yana kasuwa taji dad'in haka nan ta bashi saftun duk abunda take so, gab da Magrib Amadu ya
dawo ya siyo komai Gwaggo ta kira Fatuu tazo ta fara feraye dankalin ita kuma gwaggo ta fara gyara kifin
zuwa bayan Magrib sun kammala komae gwaggo tace ma Fatuu sai taje tayi wanka kada taje wurin
mutane tana k'arnin kifi duk da ba ita ta gyara ba amman yana iya kama mata jiki tace to, tana fitowa
daga wanka tayi Alwala bayan ta shiga d'aki ta tsaya gaban wardrobe tana tunanin kayan da zata saka
can ta fiddo wasu light blue riga da skirt yan kanti kayan na da d'an k'auri amman roba ne ta saka sun
mata kyau sosae shape d'inta ya fita har ba'a Magana tasa bak'ar hula a kanta bayan ta gama ta kabbara
sallar isha, ana gama salla sai gashi yazo lokacin itama Fatuu bata dad'e da gamawa ba ta jiyo cool voice
d'in shi yana sallama mik'ewa tay tasa hannu ta cire hijabin ta aje bakin gado sannan ta fito lokacin yana
tsaye gefen Parlor jikin shi sanye da k'ananan kaya da murmushi ta isa gabanshi shima ya d'an yi mata
tace ya shigo mana tay gaba ya bi bayanta, a saman 3 seater ya zauna tana tsaye sai kuma ta juya ta nufi
Freezer don d'aukko mashi lemu da ruwa yabi bayanta da kallo har ta bud'e ta d'aukko yana ganin zata
juyo ya kauda idon shi kanshi baisan miyasa yake yawan kallonta ba abunda ba halinshi bane, a saman
Carpet ta ajiye su ta bud'e Coke d'in ta tsiyaya mashi a cikin glass cup kafin ta mik'e still da murmushin ta
d'an rankwafa tana mik'a mashi yana kokarin kallonta idanunshi suka sauka akan saman boobs d'inta da
suka d'an bayyana sakamakon duk'awar da tay da sauri ya kawar da idanun shi had'i da amsar cup d'in
ya furta thanks ta koma gefe ta zauna kan kujera one seater kamar sau ukku yay sipping ya ajiye bayan
ya d'ago suka had'a ido Calmly yace "go and bring d Laptop" tace to ta mik'e still dae kallon yabi ta da shi
har ta fita, tana fita gwaggo ta shigo da fara'a ta zauna suka shiga gaisawa ta k'ara mashi ya gajiya don
d'azun sun gaisa da taje gidan, godiyar Laptop tay mashi yace ba wani abu ta k'ara mashi godiya da
Addu'oi yana amsawa a hankali daga baya ta mik'e ta fita Fatuu ta shigo ta mik'a mashi ya amsa ya gyara
zama yana kokarin bud'e ta ita kuma ta sake juyawa ta fita, kayan Abincin taje ta kawo ta tambaye shi ta
zuba mashi yanzu ya d'an d'aga mata hannu alamar a'a idon shi akan Screen hakan yasa ta mik'e tana
kokarin komawa inda ta tashi ta zauna ya dakatar da ita ta hanyar nuna mata gefen shi alamar ta zauna
nan bayan ta zaunan ganin ya d'aura laptop d'in akan laps d'in shi yasa tace ko ta daukko d'an table ya
d'aga mata kai alamar eh, bada jimawa ba ta dawo ta aje a gabanshi ya d'aura laptop d'in a sama daga
haka ya fara nuna mata abubuwan da yakamata ta iya dama duk ya tura mata Apps ba laifi kuma tana
catching yafi koya mata Ms-Word inda zatayi typing duk in yayi abu sai itama tayi abunda yafi bata
wahala in tazo yin highlighting dasu dragging sai ya rik'a kubce mata dama sun fi sauk'i yi inda mouse ne
tana cikin yi taji ya kawo hannunshi ya kama hannun nata da sauri ta d'an kalleshi ganin bai ko kalleta ba
yasa ta maida idon kan screen d'in yana ruk'e da hannun ya rink'a koya mata tun tana jin wani iri hardae
ta saki jiki saidae gaba d'aya kamshin jikinshi wani irin narkar mata da zuciya yake sakamakon kusancin
da suke dashi a zaunen,sosae ta koyi abubuwa harda yadda zata tura abu a turo mata da yarda in kamar
zasu yi online class da dae sauransu lokacin da suka gama kusan goma saura ganin yana niyyar ta shi
yasa a shagwabe tace to Abincin fa still yay yana bin ta da kallo kafin yace bai son Abinci mai nauyi da
daddare da sauri ta sauka ta fara bud'ewa tana fad'in ai tasani ya gani ba mai nauyi bane light food ne
wani irin daddad'an kamshi ne ya buge parlon ganin baice komai ba yasa kawae ta fara zuba mashi
kaman d'azun ta shak'e mashi plate tana yi tana kallon shi tana yar dariya ganin tana kokarin d'aura
mashi saman table d'in ya dakatar da ita yace zai ci a kan carpet ta aje a nutse ya sauko ya mik'ar da
k'afaffun shi ta yadda Abincin ke a gefen shi ya kalleta yace ta d'aukko wani spoon d'in tace to bayan ta
dawo ta mik'a mashi da kai yay mata alamar ta ci ta langa6ar da kai tana fad'in nashi ne ai bin ta yay da
wani irin kallo hakan yasa ta matsa gaban Abincin suka fara ci a nutse, sosae Abincin yay ma Haisam
dad'i can sun yi nisa Fatuu ta d'ago da d'an murmushi suka had'a ido ta d'age mashi gira tace "da dad'i?"
murmushin gefen baki yay bai ce komae ba, ba laifi sosae suka ci Abincin don har k'ara masu Fatuu tay
saida suka gama ya kalleta cikin ido yace "Yayi dad'i da yake bake kika yi ba" waro ido tay sai kuma ta
fara rantsuwar ita tayi abu kad'an gwaggo tayi still yay yana ta kallonta fuskar shi a sake sai faman
rantsuwa take a shagwa6e tana fad'in ai shima dae yasan ta iya girki ko can Calmly ya furta "Ok kin yi
kokari" tace ta gode sannan ta mik'e ta kwashe kayan ta kai kitchen, lokacin da ta dawo har ya mik'e zai
tafi ta tsaya gabanshi suna Facing juna tace tafiya zai yi ya d'aga mata kai tace suje to ta raka shi ta fara
K'ok'arin juyawa kawae sai taji ya kamo hannunta cak ta tsaya ta zaro ido kafin slowly ta juyo still yana
ruk'e da hannun suka zuba ma juna ido kan Fatuu ya gama d'aurewa gaba d'aya ganin shi take tamkar
bashi ba Saboda bak'in abubuwan da yake mata wanda ko ada can da bai da aure bai mata hakan ya lura
da irin kallon da take mashi hakan yasa a hankali ya saki hannun kafin Slowly ya furta "It's already late ba
sai kin raka ni ba" tamkar yar k'adangaruwa ta jinjina mashi kai kawai don gaba d'aya jin ta take wani iri
don kallon da yake mata bai saba yi mata shi ba, kokarin bi ta gefenta ya fara da sauri taja gefe tana ci
gaba da kallon shi har ya fice .............

Mun gama Sabon salo da An yanka ta tashi yanzu mun shiga WASA FARIN GIRKI😂
*ASM Bk2038*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.......Da k'yar taja k'afafunta ta koma kan kujera ta fad'a da6as duk jikinta yay weak ta kasa gane wannan
bak'in Abubuwan da yake mata na miye, bai jin komae yanzu yake ta6a ta ga wani irin kallo da yake
mata wanda ada sam ba irin shi yake mata ba, shiru tay kamar mai nazari can wata zuciyar ta ayyana
mata kodai son ta yake tunda ada da bai mata hakan ai ba son ta yake ba kuma ko Fanan da tazo itama
yana ta6a ta lokacin kuma soyayya suke can kuma wata zuciyar ta tuno mata da labarin Fauzy wanda
itama ai tace Mujaheed na ta6ata kuma k'arshe ya yaudareta, rasa tunanin ainihin dalilin canzawar
Haisam d'in tay k'arshe jiki a sanyaye ta mik'e ta d'auki laptop d'in bayan ta kashe hasken parlon ta nufi
d'akinta don ta san tuni gwaggo tay bacci, kayan jikinta ta cire ta sa na bacci ta haye gado sam tunanin
Haisam yak'i barinta wani iri take ji ran ta sai bata yake ko dae da gaske son nata yake in kuwa haka ne
da zata yi farinciki to amman mizai sa sai yanzu zai so ta bacin yana da mata wata zuciyar ta k'ara raya
mata nan fa ta shiga wasi wasi k'arshe ganin tana neman harmutse kwakwalwarta da tunane tunane ta
bar ma ran ta ba son ta yake ba kawae, Fauzy ce ta fad'o mata a rai tay tunanin ko ta kirata ta sanar
mata game da zuwan shi sai kuma ta ayyana kamata yay ta bata surprise suje tare da shi to amman ya
zata yi wata zuciyar tace in kince ya kai ki ai zai kai ki ne, d'an murmushi kawae tay k'arshe ta jawo
d'ayan pillow dake gefen kanta ta rungume shi sosae ta lumshe ido a haka bata san lokacin da bacci ya
kwashe ta ba, Haisam na komawa part d'in shi ya nufa duk da bai dad'e da yayi wanka ba da zai je
gidansu saida ya k'ara watso ruwa ya fito d'aure da farin towel a k'ugun shi ya nufi press don saka
sleeping dress, yana gamawa ya nufi switch ya kashe hasken d'akin kafin ya kunna bedside lamb guda
d'aya ya haye gado ya kwanta yana facing sama da alama dae Haisam ya d'aura aure da tunani yana
haka wayarshi ta fara ringing ya kai hannu gefen shi ya d'auka sunan Lovely Wife ya bayyana wato Fanan
ce ta kira picking yay yasa speaker ya aje wayar kusa da kan shi cike da k'auna ta fara Magana tana nuna
yadda tay missing nashi shima yace yayi nata ta tambaye shi ya akai bai bacci ba ko rashin ta by his side
ne ya hanashi yi d'an murmushi kawae yay sai kuma yace mata Yeah, haka suka cigaba da hiran yawanci
itace mai Maganar shidae saidae yay murmushi mai d'an sauti ko ya bata amsa a tak'aice daga baya
sukai sallama har tana ce mashi zata zo a cikin dream d'in shi tayi mashi duk abunda ya kamata yana
murmushi ya furta mata Ok had'i da take care, yana cire wayar ya aje akan bedside ya koma yana facing
sama kaman da farko had'i da lumshe ido saidae bansan ko duniyar tunanin ya k'ara tafiya ba ko kuma
baccin ya yi ba.

Washe gari sai wurin k'arfe 10 na safe Fatuu ta tashi tunda weekend ne ba school, bayan tayi breakfast
ta fara gyara gidan zuwa k'arfe sha d'aya da rabi ta gama komae taje tayo wanka ta shirya cikin short
skirt da yar vest zaman school ya koya mata sa guntayen kaya dama kuma zafi ake, saman gado ta haye
ta d'auki wayarta ta fara lallatsawa nan ta fara doubting na kota kira Haisam d'in tayi mashi Maganar
zuwa gidan su Fauzy ko kuwa ta k'yale shi,to in ta Kira kawae sai tace tana son ya kaita gidan k'awarta ita
bata iya zuwa ne dole zai ya kaita haka tay ta wasi wasi can dai ta yanke kiran nashi lokacin da kiran ya
shiga yana zaune a Parlor bai jima da gama yin Breakfast ba anan part d'in na shi don ko kayan ma ba'a
kaiga zuwa an d'auke ba yanata Operating system jikin shi sanye da farar jallabiya jin ringing d'in wayar
yasa ya kai hannu gefenshi ya daukkota ya kalli screen d'in kafin yay picking yasa speaker ya aje ta
agefen laptop d'in d'an shiru sukae Fatun ce ta fara cewa "Ya Haisam ina kwana an tashi lpy" amsa mata
yay da "Alhamdulillah and how was ur night?" Itama tace Alhamdulillah sai kuma tay shiru shi kuma
yana ta lallatsa computer d'in gabanshi rasa ta yadda zata fad'i mashi tay sai kawae tace "d..dama na
kira in k'ara maka godiyar Laptop" jinjina kai yay tamkar tana gani sai koma ya furta is Ok suka k'ara yin
shiru can taji ya furta "then What else?" d'an gwale ido tay jin ya gano akwae abunda take son fad'a
cikin yar inda inda tace "d....dama so nike in ba damuwa ka kaini gidan wata k'awata zaku gaisa da ita na
ta6a bata labarin ka" shiru yay ita kanta sai taji kaman she sounds stupid da ta fad'i mashi hakan can taji
yace "Magana ta kike da wasu kenan" rud'ewa tay bata zaci zai fad'i hakan ba cikin shaky voice tace
"a...a wllh Ya Haisam kaji na rantse ni ba Maganar ka nike yi ba ita kadae ce itama don k'awata ce sosae
kuma saida taga pic d'in ka a waya na ne ta tambayeni na fad'a mata kai yayana ne shine...shine..." sam
ta rasa mi ma zata ce, shikam d'an ta6e baki yay fuskarshi d'auke da d'an murmushi can taji ya kira
sunanta "Zarah" kaman zatayi kuka tace "Na'am" yace "unhun am listening shine what" abu ta had'iya
da k'yar tace "na fad'a mata lokacin baka K'asar kayi Aure, kawae dama don ku gaisa ne amman a
bashshi ma" still murmushin yake yi kafin yace "by what time?" d'an waro ido tay had'i da yin d'an
murmushi tace "duk lokacin da yayi maka ni yau ba abun da nike yi" taji yace "is it Ok by 4:00?" Da sauri
tace eh yayi yace Ok till then tayi mashi godiya kafin ta kashe wayar yaci gaba da latse latsen shi, murna
ce ta lullu6eta bayan ta gama ta fad'a saman gadon harda su mirgina mirgina can kuma a fili ta furta "Ya
Haisam kai na daban ne wllh I so much luv u" ta rungume hannayenta a k'irji had'i da runtse ido. Misalin
k'arfe hud'u saura kwata ta gama shiryawa har Salla tayi kaya kawae ya rage ta saka tay tsaye gaban
wardrobe d'inta tana tunanin wanda yakamata ta sa, in ta janyo wannan sai taga bai yi ba ta maida ta
fiddo wasu sai faman ruwan ido take k'arshe dai ta fiddo wasu riga da skirt na atampa da bata ta6a saka
su ba cikin kayan da Chairman ya bata, atampar na da zanen flowers army green da kuma light green ba
k'aramin amsarta kayan sukai ba dama kuma saida aka aunata kafin aka yi su, yar light make up tayi tasa
yan kunne da sark'a silver sai Agogo haka gyale da jaka da takalma duk mahad'in kayan ne takalman half
cover ne masu tsini jakar ma mahad'insu ce bata sa turare sosae ba don gwaggo ta hana ta iya roll on ta
goga sai ta shafa Humra a jiki kayan kuma dama suna sakin kamshinsu sakamakon turaren kaya da suke
amfani dashi, k'arfe hud'u saura yan mintuna da basu wuce 2 ba sai ga kiran shi yace in ta gama yana
waje tace to, bayan ta fito saida ta lek'a d'akin gwaggo don yi mata sallama dama tun lokacin da tay
Magana da Haisam d'in ta sanar mata, sosae gwaggo ta hau yabon kyaun da tay tana ce mata sai kace
Amarya ita dae Fatuu sai dariya take har waje gwaggo ta biyota ta tsaya a bakin kopar d'akinta tana
kallon Fatun cike da jin dad'i har ta fice sannan ta koma ciki, tunda ta fito ya kai idonshi kanta ta zagayo
ta gaban Motar ta zo d'ayan side d'in duk idonshi na akanta saidae ita bata gani don glass d'in
blacktinted ne, bud'e kopar gaban tayi ta shiga bayan ta rufe ta juya da murmushi ta gaida shi shima
kallonta yake ya jinjina mata kai kawae wani abun mamaki sai kace yasan kayan da zata saka don kuwa
shima wani d'anyen Voile ne army green ya saka sumar nan tasha gyara hatta Agogo da takalman
kafarshi duk army green ne sosae kayan suka fito mashi da farin shi ita kanta Fatuu a cikin ranta saida
tay mamakin kalar kayan ganin sun hau dana jikinta sosae, saida suka hau hanya idon shi akan titi ya
tambayeta ina zasu tace mashi Goruba road yaci gaba da tafiya ba tare daya ce komae ba, tsit kake ji ba
wanda ya k'ara cewa uffan Fatun ta juyar da fuskarta tana kallon hanya yayin shi kuma yake driving
saidae akai akai yake d'aga ido ya kalleta ta cikin mirror a haka har suka iso ita ta rink'a nuna mashi
hanyar da zai bi har suka k'araso gaban gidan ya parker, da murmushi tace mashi zata shiga tay mata
magana ya d'aga mata kai ta fita idon shi akanta, da sallama ta shiga Parlon gidan saidae ba kowa a ciki
ta wuce d'akin Fauzy ta tura kopar da yar sallama ta shiga lokacin Fauzy na kwance saman gado tayi
rubda ciki wayarta ruk'e a hannu da alama wani abu take kallo tana sanye da doguwar rigar material
koda ta d'ago taga Fatuu ce mai yin sallamar wata yar k'arar farinciki ta saki ta saukko da gudu ta
tarbeta, kama hannunta guda tay tana k'are mata kallo kafin tace "Yar matar nan wai kinga kyaun da
kika yi kin wanku wllh sai kace wata Amarya" dariya Fatun tayi Fauzyn ta sake cewa "koda yake in sha
Allahu Amaryar ce ta Ya Haisam da zai yi" zaro ido Fatuu tay ta d'an bud'e baki tace "ki rufa Asiri kar
Aunty Fanan ta ji mu" yar dariya Fauzy tay tace "to sai me in Allah ya k'addaro ai bata isa ta hana ba wllh
duk min kishinta" Fatun tace "amman dae Fauzy ai ana barin halak ko don kunya ko" wani kallon kina da
hankali tay ma Fatuu tace "Halak....Kunya, ke yanzu idan yazo yace yana son ki zai aure ki sai kice a'a
kenan duk da son da kike mashi Saboda matar shi?" Fatuu tace "Uhmm Fauzy mubar Maganar nan
tunda bai ce ba d'in, ni kinga zo muje waje zaki gaisa da wani ne" da mamaki ta maimaita wani kuma
Fatun tace mata eh still da mamakin ta sake ce mata wanene tace tazo dai suje ta gani ta juya taje ta
d'aukko gyale ta dawo suka nufi waje tana ce ma Fatun kodae Sabon saurayi tayi ita kuma tay murmushi
tace suje dae, tunda suka fito take bin Motar da kallo duk ta k'agu taga wanene a ciki a tare suka isa
driver side d'in yana ganinsu a bakin kopar Motar glass d'in ya fara sauka slowly lokacin da fuskarshi ta
bayyana mutuwar tsaye Fauzy tay har saida kirjinta ya buga don bata ta6a kawo ma ranta irin halittar da
zata gani kenan ba jin saukar muryar Fatuu tay tace "Fauzy ga Ya Haisam ya zo" tana murmushi tay mata
Maganar har saida ta had'iye miyau Kutt kafin tay murmushin yake tamkar yar koyo tace "Ina wuni Ya
Haisam an zo lafiya" da k'yar ta k'arasa a haka ma ba k'aramin kokari tay ba wurin daidaita Maganar
amman duk da haka saida muryarta tay d'an rawa cikin cool voice d'in shi yace "lpy ya School" wohoho
Fauzy na ganin Mujaheed ya gama had'uwa acikin Mazan Nigeria to yau ga Kakanshi ta gani wanda
komae nashi mai tafiya da mutum ne amsa mashi tay da Alhamdulillah ya jinjina mata kai kawae daga
haka bai k'ara cewa komae ba, a hankali ta matso gefen Fatuu cikin rad'a tace "bari in yi ma Aunty
Mareeya Magana su gaisa don Allah na bata labarin da muka yi da ke" bata jira cewar Fatuu ba ta juya
da sauri ta tunkari gate shi kam bai ma san suna yi ba don ya maida kanshi jikin Headrest, bata dad'e ba
ta dawo tun daga bakin gate d'in tay ma Fatuu alamar su shigo ta juya ta kalli Ya Haisam d'in sai ma ta
rasa ya zata ce mashi can dae ta kira shi ya juyo da face din shi kanta cikin yar inda inda tace wai zai
shiga su gaisa da Auntynta da take zaune wurin ta wani kallo ya bita dashi da sauri ta sunkuyar da kanta
k'asa can taji yana kokarin bud'e Motar ta d'ago da sauri sai kuma taja gefe ya fito, alamar suje yay mata
da kai tay gaba yana biye da ita suka nufi gidan, lokacin da suka shiga Parlon da yar Sallama ya shiga
Aunty Mareeya dake a tsaye da fara'a ta shiga yi mashi sannu da zuwa ta nuna mashi wurin zama ya
zauna itama ta zauna gaidashi tay duk da da gani ta girmeshi tayi mashi an zo lafiya ya iyali a nutse ya
amsa mata shiru ta biyo baya idonshi a kan carpet Fauzy ta fito ruk'e da k'aton tray data d'auro ruwa da
lemu ta d'aura saman c-table Aunty Mareeya ta kalli Fatuu dake zaune tace "Zarah zuba mana" tana
niyyar tashi ya dakatar da ita ta hanyar d'an d'aga mata hannu ya furta "am Ok" Aunty Mareeya na
murmushi tace ai yakamata yasha ruwan zumunci ko yace bai jin kishi ne can kuma sai ya mik'e yay mata
sallama itama ta mik'e tana mashi godiya ya fita, kallon juna sukae su duka ukkun Aunty Mareeya ta d'an
gwalo ido har saida ta basu dariya su duka tace "Zarah dama Akwae irin wad'annan Mutanen a Nigeria"
Fauzy ta kar6e "wllh Aunty nima lokacin da ya sauke glass nay arba da face d'in shi har tsoro naji nafa
san shi a picture amman gaba d'aya ban gane shi ba don sai naga ma ya fi kyau a fili....." Aunty Mareeya
ta sake cewa "Tubarkallah ma sha Allah kai kace hausa bazata fito daga bakin shi ba koda yake ai kun ce
ruwa biyu ne koma ace ukku, Zaraah banga laifin ki ba wllh kin yi namijin kokari da kika iya danne son shi
baki furta mashi ba ai inni ce wllh ban san lokacin da zan fad'a mashi ba" gaba d'aya suka sa dariya dama
Aunty Mareeya yar barkwanci ce anan Fatuu ta gaya ma Fauzy zancen Laptop d'in daya kawo mata ta
hau murna tana fad'in su Shar sun yi computer suma Aunty Mareeya ta hau yabon kirkin shi tana fad'in
ita ko a labari bata ta6a jin mutum da ya had'a abubuwa irin nashi ba ga kyau ga kud'i ga tsananin kirki
k'arshe ta hau yi ma Fatuu Addu'ar Allah ya mallaka mata shi in rabon ta ne Fauzy ta amsa da Amin ita
kuma tay murmushi kawae can tace bari taje kada yay ta jiranta Aunty Mareeya harda fad'in yi maza kar
ki rink'a 6ata mashi rai kita mashi biyayya har mu samu yazo hannu duk suka kwashe da dariya, tare da
Fauzy suka fito lokacin ya rufe glass d'in side d'inshi suka zagaya d'ayan side d'in Fatuu ta bud'e ta shiga
Fauzy ta d'an rankwafa tana ce mata sai sun had'u a School ran Monday kafin ta kalli Haisam tay mashi
sai anjima da godiya, kud'i ya mik'a ma Fatuu yace ta bata yan dubu dubu ita kanta bata san ko nawa
bane lokacin har Fauzy ta juya Fatun ta kirata ta juyo ta mik'a mata tace in ji Ya Haisam waro ido tay
alamar mamaki sai kuma ta amsa ta sake lekawa tay mashi godiya kai kawai ya d'aga ba tare daya kalleta
ba, a d'an can gefe ta tsaya saida taga tafiyar su sannan ta nufi cikin gidan da gudu a Parlor ta iske Aunty
Mareeya bata shiga ciki ba ta nufeta tana dariya ta d'aura mata kud'in saman jikinta tace shi ya bata,
hannu tasa ta ruk'e haba Fauzy ta zauna gefen ta da yake saman 3 seater take nan suka dasa hirar
Haisam har Aunty Mareeya na cewa wannan dole ma Matar shi ai tay kishin shi. Bayan sun baro
Unguwar EE ya wuce da ita tunkan ya tsaya Fatuu ta fara yin Murmushi tunawa da randa ya zo da ita,
bayan yayi parking a parking space ya kalleta yace su je a tare suka fito suna shiga entryway ya nufi
shagon saida wayoyi Fatuu ta bishi lokacin da suka shiga da fara'a masu shagon suka tarbeshi suna mashi
sannu da zuwa ya amsa kafin ya tambayi wanda ke gabanshi ko sun kawo iPhone 15 yace mashi a'a
amman in sha Allahu gobe zata iso akwae ma wad'anda suka bada akawo masu zai iya yin payment
shima ya fiddo card ya mik'a mashi ba 6ata lokaci ya fitar da kud'in ya bashi receipt yace a zo dashi
goben ya furta Ok daga haka suka fito, waje suka nufa wurin packing space ya bud'e ya saka receipt d'in
da aka bashi a shagon waya Fatuu na tsaye gefe ya juyo bayan ya rufe Motar suka kalli juna Calmly yace
mata yana son shiga gym ko zata jira shi a pack wani kallo tay mashi kafin ta d'an tura baki tace ita mi
zata yi a park kaman wata k'aramar yarinya komawa yay ya jingina da jikin Motar ya bita da ido kawae
ganin kallon da yake Matan ne yasa ta yamutsa fuska tace "Ko fa da can ma da muka zo ai na girmi wurin
balle yanzu" d'an murmushin gefe yay ya jinjina kai kaman bazai ce komae ba sai kuma yace to ta shiga
Mota su tafi da sauri ta kalleshi tace ina ya bata amsa da gida tana kallon shi tace ya fasa yin gyming d'in
ko zai dawo yace mata yadda ya yuwu ganin zai bud'e Motar duk sai bata ji dad'i ba don sai take ganin
kaman zata hana shi yin abun da yake so da sauri ta dakatar dashi ta hanyar fad'in "To muje gym d'in
tare mana ba sai in tsaya wurin Aunty Anah ba" juyowa yay ya kalleta Calmly yace "bata nan yanzu" tace
tana ina ya bata amsa da dama Service ya kawo ta garin ta d'an zauna yanzu ta koma garin su, jinjina kai
Fatun tay tace "Allah sarki Aunty Anah, to ai nasan baka rasa sanin wasu ba sai ka had'a ni da su ba nima
inyi exercise d'in dama wllh ina d'an jin nauyin jikina" d'age gira yay yana mata wani kallo tace "bafa
zanyi bane da kaina sai a koya man nike nufi" kaman bazai ce wani abu ba sai kuma yace "taya zaki da
wannan dressing d'in?" Yay tambayar yana mata nuni da kan shi ta d'ukar da kanta ta kalli kayan jikinta
skirt din straight skirt ne yay mata k'yam a jiki ko tafiya da sauri bata tunanin zata iya yi balle kuma
exercise d'agowa tay ta bishi da ido kawae ya juya zai bud'e Motar ta sake tambayar shi tafiya zasuyi
baza su je gym d'in ba yace ta shigo zasu je su dawo ne tace to ta zagaya ta shiga, yar tafiya sukai bayan
sun bar wurin ba mai tsawo sosae ba suka iso bakin wata plaza yace su je ta bud'e Motar, Wani k'aton
shago suka nufa wanda kayan sports ne kawae a ciki shak'e, bayan sun shiga ya gaisa da masu shagon ya
fad'i masu irin kayan da suke so aka d'aukko masu kamar kala biyar don su za6a da kai ya nuna ma Fatun
yace ta d'auki wanda take so ta bishi da kallon mamaki don bata yi zaton inda zasu zo ba kenan k'arshe
ta zabi wasu riga da wando rigar tight long sleeve ce sai wandon ta shigen wanda Fanan ta ta6a sawa a
gabanta, bayan ya biya su aka saka masu a babbar leda mai tambarin wurin suka fito, within Few
minutes suka dawo EE d'in yace ta d'aukko kayan suka nufi ciki, lokacin da suka shiga gym d'in a bakin
bangaren mata ya tsaya ya fiddo wayarshi ya kira wata mai suna Deborah yace ta fito yana son Magana
da ita suna gama wayar sai gata ta fito cikin shigar gym tana ganinshi ta washe baki tana gaishe da shi ya
amsa, nuna mata Fatuu yay yace pls ta shiga da ita ta taimaka mata tay gyming bata iya ba da sauri ta
amsa da Ok ta kai idonta kan Fatuu lokaci guda taga kaman ta san Face d'inta can ta tuna tace mashi
kaman itace suka ta6a zuwa ko yace mata yeah sosae tay mamakin ganin girman da Fatun tay ta gaishe
da ita ta amsa da fara'a ta kama hannunta suka shiga shi kuma ya wuce side d'in su dama ya taho da
jakar shi komae na ciki har kayan da zai canza, bayan su Fatuu sun shiga ne ganin bak'uwar fuska yasa
aka fara tambayar Deborah bak'uwa akayi ne tace eh, wad'anda suka dad'e suna zuwa wurin tay masu
bayanin kowacece nan fa suma sukai ta mamaki suna fad'in ta girma ita dae murmushi kawae take, wata
k'opa Deborah ta nuna ma Fatuu tace change room ne taje tasa kayan tace to ta nufi d'akin after some
minutes sai gata ta fito uhmm nasan ko ban fad'a ba kowa yasan kayan zasu yi mata kyau ko don dirinta
zo kaga idanu gaba d'aya ta janye hankulan su nan fa aka shiga yabawa ana Maganar shape d'inta duk da
kasancewar ta mai k'ananun shekaru gashi dama kanta ba kallabi shima gashin ba'a k'yale shi ba sai da
suka tanka ganin abun yayi yawa yasa Fatuu ta rink'a fad'in Tubarkallah a hankali, Sosae tay exercise d'in
kuma ta matuk'ar jin dad'i don komae ta iya a nutse Deborah ta kokkoya mata cike da kiyayewa gudun
kada a sake samun matsala,Sai lokacin da aka tashi sannan suka dakata ganin kowa na fita a yadda yake
yasa Fatuu yin tunanin ba sai tasha wahalar mayar da kayanta ba tunda ga gyale sai tay rolling d'in shi
kawae ta shiga ta d'aukko kayan data cire dama ta saka su a cikin ledar kayan, lokacin da ta fito Deborah
na tsaye tana jiranta da murmushi ta ce suje H.zakee na nan waje yana jiranta suka nufi hanyar fita, yana
d'an can gefe suka fito suka nufe shi idon shi akan Fatuu har suka k'arasa Deborah na murmushi tace
mashi gata nan tayi kokari don ta iya komae kuma tayi sosae ya d'aga mata kai kafin ya furta mata
thanks tay masu sallama ta tafi, kallonshi Fatuu tay tana murmushi ganin sun yi tsaye tace su tafi tana
kokarin yin gaba kawai taji ya kamo hannunta guda yay pulling d'inta back har saida ta d'an bangaji
gefen jikinshi, zaro ido tay tana kallon shi lokaci guda hankalinta ya tashi ganin kallon da yake mata ya
d'an 6ata rae ta fara tunanin mi tayi mashi a kausashe taji yace "How can u go out like dis!" Sai da yay
Maganar ta fahimci laifinta murya na d'an rawa tace "n...naga wai Mota zamu hau ne kuma nasa gyale"
kallonta kawae yake wai tasa gyale komi wannan d'in yay mata ganin ta d'an tsorata yasa shi sassauta
d'aure fuskar da yay yace "amman haka kika fito gida?" da sauri ta girgiza mashi kai ita sai lokacin ma ta
tuna da ba hakan ta fito ba da sauri tace bari taje ta maida kayanta ta juya sam ya kasa janye idon shi
daga kanta har ta shige wurin, lokacin data fito ta maida kayanta bata ganshi a wurin ba hakan yasa ta
nufi hanyar fita saida ta fita can waje ta hango shi a tsaye jikin Mota yana ganinta ya bud'e ya shiga
itama ta k'arasa ta bud'e ta shiga ba tare da ya ce mata komae ba yaja suka tafi..........

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2039*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*Wannan page tukuici ne agare ki Mrs Haisam Kano ina matuk'ar godiya Allah ya k'ara dankon kauna
keda Haisam ya sauke ki lpy Amin*😍

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


.........Tunda suka hau hanya ba wanda yace uffan idon shi na akan hanya ko ta mirror bai kalleta ba
yanata driving itace ke d'an juyowa ta saci kallon shi, a hanya ya tsaya bakin wani Masallaci ba tare da ya
kalleta ba yace zai yi salla ta d'aga mashi kai tana ta kallon shi har ya fita, bayan an gama ya dawo suka
tafi saida ya k'ara tsayawa bakin wani Cafe ya fita bada jimawa ba ya dawo hannunshi ruk'e da ledoji
masu d'auke da tambarin wurin guda biyu ya bud'e back door ya saka sannan ya dawo ya shige driver
seat ya ja suka tafi duk jikin Fatuu yay sanyi ganin ko kallonta bai yi, a bakin kopar gidansu ya tsaya ta
kalleshi a sanyaye tace "Nagode" sai lokacin ya d'an kalle ta ya jinjina mata kai kawae har ta bud'e Motar
taji voice d'in shi yana fad'in ta d'au abun dake baya a hankali tace to ta idasa fita ta rufe kopar, ganin
ledojin biyu ne yasa ta d'auki guda d'aya ta k'ara mashi godiya still kan ya jinjina mata ta rufe mashi
kopar ta nufi gida shi kuma yaja ya tafi, tsaye tay a bakin wurin tana kallon bayan Motar har saida yasha
kwanar gate d'in gidan sannan ta juya sukuku da ita ta nufi cikin gida, d'akin gwaggo ta nufa ta shiga da
yar sallama lokacin tana zaune akan abun salla tana yin tasbih Fatun ta nufi ciki ta zauna akan kujera,
juyowa gwaggo tay da d'an murmushi tace sun dawo Fatuu ta d'aga mata kai ta k'ara cewa "Amman dai
ba iya gidansu Fauziyyar kuka je ba ko" kai Fatuu ta d'aga tace "Eh daga can gym muka wuce" cikin
rashin fahimta gwaggo ta tambayi ina ne hakan tace mata wurin motsa jiki gwaggon ta jinjina kai suka
d'an yi shiru sai kuma tace ma Fatun ya taga kamar wani abu ma damunta da sauri ta k'ak'alo
murmushin yak'e tace ba komae ta gaji ne ta yunk'ura ta aje ledar hannunta a gaban gwaggon tace shine
ya siyan mata gwaggo ta hau godiya tana shi Albarka, ganin Fatun na niyyar mik'ewa tace ta d'auka ta
d'iba sai ta d'ibar ma Amadu shima ta mik'a mashi tace to ta d'auki ledar ta nufi kopa ta fita, bayan ta
d'an d'iba su shawarma ne harda ice cream ta kaima Kawu Amadu waje har yana tsokanarta yana fad'in
Amaryarmu harda tsaraba ta d'an tura mashi baki yasa dariya don yasan bata so shiyasa yake tsokanarta
yana ce mata hakan tun bayan da aka fasa aurenta, da k'yar ta ci don duk komae bai mata dad'i bayan
tayi sallar isha ta watso ruwa ta canza kaya zuwa na bacci ta haye gado, tana son ta d'an duba littattafan
ta amman ta kasa tay kwance kawae. Tun bayan da ya koma gidan saida ya fara zuwa part d'in Hajiya ya
kai mata d'ayar ledar ganin yana niyyar tafiya tace ya tsaya yaci Abinci mana sai ya tafi gaba d'aya yace
Ok tasa Saude ta kawo mashi anan Parlor yana ci Hajiya dake zaune tana mashi fira har ya gama sukae
bankwana ya koma part d'in shi, wanka yayi ya shirya cikin sleeping dress yana son ya d'an yi wani aiki a
computer amman sai yaji bai iyawa ya haye gado kawae ba tare da ya kashe Switch d'in d'akin ba ya
kwanta yana facing sama hannunshi na dama ruk'e da beard d'in shi kafarshi d'aya a mik'e d'ayar kuma
ya d'an d'agata a lankwashe yana d'an girgiza ta da gani akwae abunda yake tunani. Sai faman juyi take
don ta kasa ma yin bacci ga Maganar Aunty Mareeya dake ta mata yawo ta d'azun da tace kar ta rink'a
6ata mashi rai gashi ta fahimci kamar ranshin ya 6aci ta ayyana ita sam bata san hakan zai 6ata mashi rai
ba ai da bata fito hakan ba ta tsaya ta canza kayan, wata zuciyar ce ta bata ta kira shi kawai ta bashi
hak'uri zai fi kaman bazata yi hakan ba can kuma sai ta tashi zaune ta kai hannu ta janyo wayar ta bud'e
ta shiga call log sai da ta d'an yi jimm kafin can kuma tay sending mashi kira, yana a yadda yake kiran ya
shigo ya juya ya kalli wayar dake akan bedside kafin ya mik'a hannu ya d'aukko ta idon shi suka sauka
kan screen d'in ya bi kiran da kallo kaman bazai picking ba can ya d'aga yasa speaker ya juya daman shi
ya aje wayar saitin fuskar shi, shiru sukae ba wanda ya tanka har bayan d'an wani lokaci sannan yaji cikin
sanyin murya ta fara Magana "Ya Haisam dama ina so in baka hak'uri don Allah in ranka ya 6aci am
sorry" yanayin fuskar shi ne ya canza kamar zai yi murmushi kafin yay sigh taji yace "kin man wani abu
ne?" d'an yamutsa fuska tay tace "Abunda ya faru d'azun naga kaman kayi fushi" lumshe ido yay sai
kuma slowly ya ware su taji yace karta damu bai yi fushi ba har saida ta d'anyi murmushi,

"Miyasa baki bacci ba har yanzu?" Tura baki tay a shagwa6e tace "ba Kaine ba ka canza man fuska" d'an
murmushi yay har saida ta jiyo sautin shi a ranshi ya ayyana har yanzu bata canza ba kaman yadda ya san
ta da bata son taga anyi fushi da ita duk sai ta damu, ce mata yay ya wuce ta daina damuwa tace to suka
d'an yi shiru can taji yace yanzu sai tay baccin ko tace ai bata fara jin baccin ba yace Ok suka d'an k'ara
yin shirun, kaman daga sama taji yace to ta bashi labari ba shiri ta waro ido don abun da bata zaci jin shi
ba daga bakin shi bane tana murmushi tace "to ai ni banda labaru don daga gida sai Makaranta nike
zuwa saidae in baka na Asibiti" sosae yake jin dad'in voice d'inta in tana Magana a shagwa6e, shima
murmushin yake yace mata bai son wannan ta manta matarshi Doctor ce tace Shikenan suka k'ara yin
shiru,

"Baki fad'a man yadda akai calling off Auren ki ba" wannan karon k'irjinta ne ya buga jin tambayar da
ya jefo mata har saida ta had'iye miyau Kutt, taya zata fad'a mashi abunda Khalid yay mata wanda shine
silar komae, lokaci guda taji bata ma iya yi mashi wannan bayanin jin tayi shiru yasa shi ce mata yana
saurarenta cikin dabarbarcewa tace "Ya Abbas bai fad'a maka ba?" Yace ya d'an fad'a mashi yana son
yaji komae ne daga wurinta, a rud'e don har wata yar zufa taji a fuskarta tace mashi to ai abunda ya fad'i
mashi shi ya faru ya furta mata Ok har saida ta dafe k'irji irin tasha da k'yar d'in nan,

"Zaka dad'e ne anan?" ta tambaye shi d'an shiru yay kafin yace "Nah Next tomorrow zan wuce" d'an
zaro ido tay tace ranar Monday kenan yace mata Yea shiru ta d'an yi duk sai taji wani iri jin tayi shiru
yasa shi tambayar ta koda wani abu ne da sauri tace "a'a Allah ya kaimu" a hankali ya amsa da Amin sai
kuma ta k'ara ce mashi sai Allah ya kaimu yace baccin yazo kenan tace eh yace "Ok gud nyt" tace to ta
kashe wayar a hankali ya lumshe ido, to bansan dai ko bacci bane shima yazo mashi ba, aje wayar tay
gefe ta koma ta kwanta tay lamo hakanan take jin wani iri tunda taji yace jibi zai tafi a haka da k'yar
bacci ya kwashe ta.
Washe gari wurin k'arfe 11 lokacin ta gama gyaran gidan tana zaune a d'aki saman gado tana duba
littafin ta idanunta sanye cikin glass sai ga kiran Haisam ya shigo d'an murmushi tay ta d'aga ta gaida shi
yay mata ta tashi lpy ta amsa da Alhamdulillah d'an shiru yay daga baya kuma sai yace mata ta fad'a ma
gwaggo zasu d'an fita around 3:00 tace mashi to suka yi sallama ta sauka daga gadon ta iske gwaggon a
d'aki tana kwance, koda ta sanar mata d'an murmushi tay tace ba komai Allah ya kaimu Fatun ta amsa
mata da Amin kafin ta fito ta dawo d'aki, kasa cigaba da karatun tay ta tattare books d'in ta mayar cikin
bag ta nufi wardrobe don ta za6i kayan da zata za ba sai lokacin ba ta kasa za6a, wani dark purple
material lace ta fiddo yana da kananun flowers light purple da tsabu tsabun ash mai kaman silver d'inkin
straight gown ne yayi kyau sosae ta fiddo gyalen shi light purple da takalma sai yan kunne da sarka silver
da yar please purse itama silver komae ta aje a gefen gado sauran jiran lokacin saka su, zuwa k'arfe biyu
da rabi tayi wanka taci Abinci ta hau shiri ba 6ata lokaci ta gama lokacin ukku ta d'an gota da Minti biyar
daidai ya kirata yace yana waje tace to, saida taje tay ma gwaggo sallama yau ma tana ta yabon gayun
nata Fatun sai dariya take tace mata sai sun dawo ta fito, idon shi a kanta har ta zagayo ta bud'e gaban
Motar ta shiga bayan ta rufe ta juya suka had'a ido tana murmushi ta gaishe shi shima fuskar shi a sake
ya amsa yana sanye da complete bak'ak'en kananan kaya jeans da t-shirt haka agogon dake d'aure a
hannunshi itama bak'a ce sumar nan tasha gyara sai salk'i take ga k'amshi da ya cika Motar abun ba'a
Magana kasa d'aurewa Fatuu tay ta d'an juyar da kanta gefe ta lumshe ido ya Haisam naso ya ida
kasheta da salon gayun shi, jan Motar yay suka tafi ba tare da wani ya k'ara cewa komae ba sai sanyin Ac
dake ratsa sassan jikin kowannen su, a daidai wata k'atuwar plaza ya karya kan Motar ya shiga ciki lokaci
guda Fatuu ta ga kaman tasan plaza d'in bayan ya parker a wurin da aka tanada ya kalleta yay mata
alamar suje da kai ta bud'e ta fito ya nufi cikin plaza din tabi shi saida ta ga shagon da suka tunkara mai
d'auke da sunan Zee Collections sannan ta gane wurin har saida tay d'an murmushi, shi ya fara shiga tabi
bayanshi ba kowa a Parlon sai wata yarinya da gani ba ita bace wadda ke a shagon ba lokacin da suka
ta6a zuwa wato Esther saidae itama yarinyar Christian ce k'ilan ko k'anwar waccan ce tana ganin su ta
mik'e da sauri tana ce masu welcome kafin ta gaishe dasu cikin harshen turanci suka amsa Haisam ne ya
tambayeta Ogar tata tace tana ciki bari ta kirata ta juya da sauri Fatuu tabi kanta da kallo da akai ma
k'waryar molo kamar dae waccan Esther d'in a ranta take ayyana kawae a aske mata gashi ai sai tayi
hauka wllh, zama Haisam yay kan doguwar Leather sofa d'in dake a wurin yay ma Fatuu alamar ta zauna
ta nufi can gefen shi ta zauna lokacin Zee ta fito tana sanye da doguwar rigar Boubou ta Atamfa tana yin
arba da Haisam ta waro ido alamar mamaki shi kuma yay mata d'an murmushi can daga gefensu ta
zauna saman wata kujerar tace "Zakee Manyan gari ko in ce Manyan dawa kai ne a K'asar tamu saukar
yaushe?" Fuska a sake ya fad'i mata lokacin da yazo tana ta murmushi tace mashi an zo lafiya ya amsa
mata lokacin Fatuu ta gaishe da ita ta kai idonta gareta tana amsawa da fara'a can tace "Wai kaman
Zarah ko?" Yar dariya Fatuu tay tace itace Zee ta bud'a ido had'i da ruk'e ha6a tace "Zarah kece kika
girma haka halan kin gama Secondary ma?" Fatuu tace mata eh ta gama ta tambaye ta taci gaba da
karatu tace mata eh,

"Wani School kike ne?" Zee d'in ta tambaya Fatuu ta bata amsa da "School of Nursing" jinjina kai zee
tay tace "Gud, Allah ya bada sa'a" ta amsa mata da Amin, maida idonta tay kan Haisam dake latsa waya
tace "H,Zakee ya Matan ka ta haihu kuwa ai ina jin kaman anyi 9 Months da auren ku ko?" Kai ya d'aga
mata alamar eh, tace "halan ta haihun don nasan ba lalle ka fad'a ba koda yake da ta haihu ko a wurin su
Jidderh na ji ai, ba da ita ka zo bane?" Kai ya sake d'aga mata alamar eh tace Allah sarki sai kuma ta kalli
Fatuu dake ta murmushi itama tayi mata ta sake maido dubanta kan Haisam tace "Wai ni H,Zakee ko dae
kai zaka mana Wuff da Zarah ne?" Kamar saukar aradu haka Fatuu taji Maganar ba shiri da sauri ta kalli
Zee dake ta murmushi sai kuma ta juya kan Haisam suka had'a ido da sauri ta kauda idon nata ta sadda
kanta k'asa wani kallo yay ma Zee tana ganin haka tasa dariya tace "Serious ka Aure ta kawai kaga kayi
kiwon abun ka kenan?" d'an murmushin gefe kawae yay bai ce komai ba ta kai idonta kan Fatuu da har
lokacin kanta ke sadde tace "Zaraah ko baki son Yayan naki?" Shiru bata ce mata komae ba bata kuma
d'ago ba hakan yasa Zee cigaba da yin dariya Haisam yay sigh kafin yace mata zata za6i kaya ne Fatuu na
jin haka ta d'ago da sauri ta kalle shi tana niyyar yin magana Zee tace "a'a Zarah kar muyi haka dake fa
kaya aka ce zaki za6a ki tashi kawae muje dama Akwae d'ibar farko ta salla suna ciki ban kaiga fiddo su
ba sai an fara Azumi kin ga rabon ke zaki fara za6a ne" shiru Fatuu tay don ta riga ta kashe mata baki
tace suje tana kokarin mik'ewa itama Fatun ta mik'e har sun tafi Zee ta juyo tace ma Fatuu ta shiga ciki
tana zuwa ta koma gun Haisam ta tambayeshi kaman kala nawa yace ta tambayeta tace Ok sai kuma ta
d'an rankwafa yadda zai ji ta cikin kaman rad'a tace "Serious H,Zakee ka auree yarinyar nan kawae wllh
don bata dace da kowa ba sai kai kaga kaci ribar rainonta da kai duk da nasan don Allah kai amman fa
gida bai k'oshi ba ba akai ma dawa ba" ba shiri Haisam yay dariyar da har fararen hak'oransa suka
bayyana Calmly ya furta "Zee Who told u gida bai k'oshi ba?" Kanne ido guda tay tace "a ina gidan ya
k'oshi ai sai Mutum yayi hud'u sannan kuma yarinyar nan da kake gani mai zafi ce don haka da irin ka
mai zafi ta dace willh" tana k'arasa Maganar ta mik'e ta juya tana dariya tana fad'in kar ya fad'i ma Matar
shi fa ya girgiza kai kawae shima yana yar dariyar, duk yadda Fatuu taso kar ta d'auki kaya da yawa saida
Zee tasa ta d'auki kala biyar da k'yar gashi duk masu tsada, laces kala biyu sai Atamfa ma biyu sai wani
had'addan cotton material harda doguwar riga jallabiya saida ta lik'a mata sannan aka d'auki mahad'in
kayan su gyale da takalma harda jaka dasu sarkoki don ma Fatun ta kafe kan ba kowanne zata d'aukar
ma mahad'in ba wanda zai hau da kaman kala biyu take d'auka, koda tay mata Maganar English wears
da Undies Fatun cewa tay duk tana da su, bayan sun fito Zee ta zauna ta kalli Haisam tana yar dariya tace
"da alama har yanzu Zarah tana tausayin ka bata son kana kashe kud'i don yanzu ma da k'yar aka za6i
kayan kaman dai other time" d'aga ido yay ya kalli Fatun ta d'an tura baki ta juyar da kanta gefe, card ya
ciro ya ba Zee d'in ta fitar da kud'in yau ma saida yace ta k'ara 30k ta siya sugar Azumi tay ta godiya
Fatuu kam shiru tay a ranta tana mamakin yadda yake kashe kud'i kamar baisan zafin su ba kai kace
kawae umarni yake badawa ake buga mashi, har Mota Zee ta rako su da kayan aka saka booth tay
wishing Haisam Safe flight tace ma Fatuu tana jiranta tazo mata yawon salla ta amsa da to suka shige
Motar ita kuma ta juya ta koma, bayan sun bar plaza d'in ganin hanyar da yabi yasa ta tambaye shi
shagon Kb zasu ne ya d'aga mata kai alamar eh tace mashi a bari ba yanzu ba ya tambayi dalili tace tana
so sai ta samu styles sai ta kai mashi baki d'aya ya furta Ok suka canza hanya, Fatuu tay mamakin ganin
sun tsaya gaban Shagon Maman Abdul mai saloon ganin tana kallon shi yace mata taje a wanke mata kai
gudun kar tay mashi gardama ta 6ata mashi rai yasa ta juya ta fita, tun kafin ta shiga ciki Maman Abdul
d'in ta fito ta tarbeta da alama hangota tay suka shiga ciki ta nuna mata kujera bayan Fatun ta zauna ta
hau gaidata ta amsa sannan cikin washe baki anga customer ta tambayeta abunda za'a mata tace Wash
and Set ta amsa da okey har zata juya sai kuma ta tsaya tana kallon fuskar Fatun da d'an alamun nazari
can tace "Ma, ur face look familiar as if u ave came here before" d'an murmushi Fatuu tay ganin yadda
dimples d'inta suka lotsa yasa maman Abdul d'in tabbatar da tasan face d'in ta koda ba anan ba ganin ta
dage sai ta tuna inda tasan ta yasa Fatun yi mata bayani aikuwa da tsananin mamaki ta ruk'e haba tana
fad'in itace wai ta girma haka miyasa ta dad'e bata zo ba Fatuu dai dariya kawae take can ta tambaye ta
ina yayanta d'in nan da ya ta6a kawota tace mata yana nan waje shine ya kawota yanzu ma, da sauri
tace "let me greet him I will come back now" tayi Maganar had'i da juyawa ti6i ti6i ta nufi hanyar fita
Fatuu ko mi zatayi ba dariya ba ganin yadda duk ta rud'e su maman Abdul anji kud'i sun zo, tana isa
driver side d'in ta d'an kwankwasa glass d'in slowly ya fara sauka tana ganin shi ta washe baki ta sunkuya
tana fad'in "Good after....oh good Evening sir" duk ta rud'e sai washe baki take, d'an murmushi yay mata
ya amsa yay mata ya kasuwa ta amsa da Alhamdulillah nan ta shiga fad'in taga Fatuu tay girma sosae
shidae murmushi kawae yake tace amman ya akai suka d'auki tsawon lokaci basu k'ara zuwa bane ko
aikin nata bai masu ba fuska a sake Yay mata bayanin tana gyarawa a gida ne Maman Abdul ta
marairaice fuska tace ya kamata dae don Allah a rik'a kawota don za'a fi gyara mata anan yace Ok in sha
Allahu tace bari tay sauri ta gyara mata kar ai keeping nashi yana jira ya jinjina mata kai ta juya da d'an
sauri sauri gudu gudu ta koma, yana zaman jiran nata akai sallar la'asar ya fita yaje Masallaci dake gefen
benen yay salla bayan ya dawo bada jimawa sosae ba aka gama ma Fatun Maman Abdul ta rakota har
bakin Mota tana fad'in tana jiranta sai ta k'ara ganinta ta amsa da Ok ta kopar da Fatun ta bud'e ta d'an
duk'a tace ma Haisam ashe yayi aure bai K'asar ma saida suna fira ne ta fad'i mata ya d'aga mata kai tayi
mashi Allah yasa Alkhairi ya amsa da Amin ta koma kan Fatuu tace mata pls ko bai nan ta rink'a zuwa
tace to, kud'i masu yawa ya fiddo yaba Fatuu ta mik'a mata zo kaga godiya tana yi tana sunkuyawa saida
yaja Motar ta koma shagon, yana ta driving ita kuma tana ta kallon hanya can taji kamar yayi magana ta
juya ta kalle shi tace Magana yake ne kaman bazai tanka mata ba idon shi akan hanya sai kuma taji yace
"cewa nay ba za'a nuna man ba yau" dariya tay tasa hannu ta rufe baki tasan wasa yake mata don ya
tuna mata da wanccan lokacin ne shima fuskar shi d'auke da d'an murmushi yake driving d'in, suna akan
hanya ya kira Abbas ya tambaye shi yana gida yace eh yanzu da la'asar d'in nan ya dawo yace Ok gashi
nan zuwa, lokacin da suka isa yay horn Abbas ne yazo ya bud'e mashi ya shigar da Motar bayan ya parker
ta ya bud'e ya fita Abbas dake gefe yana mashi dariya ya bashi hannu sukai shaking yana niyyar yin
magana Fatuu ta bud'e kopar ta fito da mamaki Abbas yace "Mom Zarah tare kuke kenan" d'aga mashi
kai tay kafin ta gaishe da shi ya amsa yana murmushi yay mata ya School ta amsa da Alhamdulillah ya
sake cewa "sai kika ga mutumin naki yazo ba ko notice?" Ita dai murmushi kawae take kafin ta tambaye
shi Aunty Feenah yace ta na ciki tace to ta nufi cikin idon shi akanta yanata wani irin murmushi can ya
juya suka had'a ido da Haisam dake jingine jikin Mota Abbas d'in ya furta "Perfect Match" wani kallo mai
kaman harara yay mashi Abbas yasa dariya yace "Wllh kun matuk'ar dacewa am telling u d truth" dan
ta6e baki Haisam d'in yay yace zai bar shi a tsaye ne da sauri yace tuba nike Angon Mom Zarah mu shiga
ciki Haisam d'in ya d'an girgiza kai kawae suka wuce, lokacin da ta shiga ba kowa a Parlon hakan yasa ta
wuce Bedroom d'in Feenah anan ta iske ta, tay matuk'ar jin dad'in ganinta tace halan ita da H,Zakee ne
Fatun na murmushi tace mata eh ta mik'e tace suje su gaisa, anan Parlor suka suna hira bayan Feenah ta
kawo masu abun ta6awa daga baya Haisam da Abbas suka ce zasu je su dawo suka ci gaba da hirarsu su
biyu har Abdul ya dawo daga islamiyya, sai bayan Magrib suka dawo Haisam d'in bai shiga ba sai Abbas
ne ya shiga ya kirata su Feenah suka rako ta da gudu Abdul ya nufi Haisam ya kankame shi yana dariya
can ya d'ago ya kalli Haisam dake murmushi shima yace "Baba Zakee don Allah ka auri Aunty Fatuu" d'an
d'age gira Haisam yay Feenah da Abbas suka sa dariya ita kuwa Fatuu sunkuyar da kai tay gabanta ya
fara fad'uwa bata ta6a zaton zai mashi wannan Maganar ba, ganin yak'i cewa komae yasa Abdul jujjuya
kai yace mashi "kaji Baba zakee kuyi aure kai da Aunty Fatuu don Allah" sigh Haisam yay slowly yace
mashi Saboda mi yake son hakan yace "kaga kai babana ne ita kuma sai ta koma mamana" Haisam na
murmushi cikin cool voice d'in shi yace "but kai kace ai tayi k'arama ta zama mom en ka" waro ido yay
baki bud'e yana son tuna sadda yace hakan can yace "gaskiya baba zakee ni ban ce hakan ba fa" Abbas
dake dariya yace ya dae manta ne a shagwa6e yace "to in ma nace haka ai yanzu ta zama babba zata iya
zama mamana kaji kuyi Auren" gaba d'aya aka sa dariya Haisam yace "ai sister na ce ita..." Da sauri
Abdul d'in ya katse shi yace "Amman dai ai ba gidan ku d'aya ba ko kai a Abuja gidan ku yake ita kuma
anan kuma a islamiyya ance sai sister d'in da ake gida d'aya ne ba'a iya aure" nan ya shiga lissafo mashi
wad'anda aka ce masu ba'a iya aure Abbas sai dariyar k'eta yake shi ma Haisam murmushi ne akan
fuskar shi yasan yaron da shegen wayau duk yadda zai zame sai ya gane hakan yasa ya d'aga mashi kai
yace to kawae nan fa ya hau tsallan murna ya tambaye shi to yaushe za'a yi bikin Haisam yace in an
shirya zai ji a wurin Dad d'in shi cike da farinciki ya nufi Fatuu da ji take tamkar ta nutse don kunya ya
kama hannunta yana dariya yace taji Baba Zakee zai aureta ko ta kasa ce mashi komae saida Abbas yace
ya k'yaleta ai taji sannan ya bar Maganar Haisam yay masu sallama Abbas yace sai yazo kai shi Airport
gobe Feenah ma tay mashi Allah ya kiyaye ya gaida Fanan yace Ok duk suka yi ma Fatuu sallama da k'yar
ta iya d'agowa ta kalle su da yake wurin fayau yake da hasken fitilu ta amsa masu kafin jikinta sukuku ta
zagaya ta shiga Motar lokacin Haisam ya shige ya fara kokarin fidda ta dama gate d'in a bud'e yake da
suka shigo, bayan sun baro gidan Abbas EE ya nufa da suka isa yace mata yana zuwa ya fita tana ta kallon
shi ta glass da yake wurin akwae haske sosae har ya shige after some minutes sai gashi ya fito hannunshi
ruk'e da yar jakar kwali mai d'auke da hotunan abubuwan da ake saidawa a wurin ya bud'e Motar ya
shiga ya aje jakar a gefe bayan ya rufe kopar yaja suka tafi, akai akai yake d'an kallonta ta juyar da kai
dama tunda suka baro gidan Abbas a haka take, lokacin da suka k'araso kopar gidansu ya parker da k'yar
ta kalleshi tay mashi godiya ya bita da ido kawae duk sai ta tsargu tana niyyar juyawa ta bud'e taji yace
ga abu nan nata ne ta juyo saida ta kalle shi kafin ta kai hannu ta d'auka tay mashi godiya sam bata san
miye a ciki ba zata fita yace mata tay ma Amadu magana yazo ya d'aukar mata kayan baya tace mashi a'a
zata iya ya d'aga kai ta juya ta fita ta rufe kopar, bayan ta fiddo kayan ta wuce har saida yaga ta shiga
gidan sannan yaja ya tafi, tana shiga d'akin gwaggo ta wuce tana zaune kan abun salla bata jima da gama
sallar isha ba, da sallama Fatun ta shiga ta amsa mata a gefenta ta aje ledar kayan da kuma jakar
gwaggon ta kalli kayan sai kuma ta kalleta a sanyaye tace mata Ya Haisam ne ya siya mata, bud'e baki
gwaggo tay da tsananin mamaki tace "kuma dae wai shi baya gajiya da hidima ne don Allah" ta k'arasa
idonta kan Fatuu ta d'an ta6e mata baki ta nufi kujera ta zauna, hannu gwaggo ta kai ta fara duba kayan
tana yi tana girgiza kai har ta gama sannan ta bud'e ledar kwalin ta fiddo kwalin dake ciki wanda ke nuni
da na waya ne gwaggo ta bishi da ido daga inda Fatuu take zaune ta saki baki tana karanta sunan wayar
har saida cikinta ya d'an yamutsa ganin iPhone 15 wayar da take taji anata zancen ta fito a social media
ba wannan ne abun mamakin ba irin kud'inta da taji ana fad'a nan ta fara shakkun anya kuwa haka
kud'in nata suke, suna haka sai ga Amadu ya shigo da sallama yana dariya yace "nazo a bani rabo na don
naga Amar....au Hajiya Fatuu ta shigo mana da k'atuwar leda" kallon shi Fatuu tay yace "tuba nike ai dae
ban k'arasa cewa Amaryar ba" d'an ta6e baki kawae tay yana niyyar duk'awa gaban kayan idanun shi
suka sauka akan kwalin wayar dake hannun gwaggo wani kalar waro ido yay with mouth agape a razane
yace "Wannan fa ta gasken ce ko kuwa kwalin ne kawae" ya kai hannu gwaggo ta mik'a mashi a kidi'me
yace "kai wllh itace da gaske ta waye??" da kai gwaggo ta nuna mashi Fatuu ba shiri yasa hannu ya rufe
baki yana fad'in "kai kai kai..." ganin yadda duk ya rud'e yasa gwaggo cewa "halan mai kud'i ce, in ce tafi
waccan da ya siya mata ko?" Wani d'an murmushin Al'ajabi yay yace "mai kud'ad'e ce zaki ce gwaggo ba
kud'i ba, iPhone 15 pro ce fa wayar data fito kwanan nan aketa Magana kusan miliyan d'aya take
wannan in ma bata fi ba" duka hannuwanta gwaggo tasa ta rufe baki ido waje kafin a tsananin razane
tace "Kai Amadu!! yanzu wannan abun ke har miliyan d'aya! ka kuwa san nawa ne miliyan!!!" Rantse
mata yay haka kud'in ta suke har yana cewa in bata yarda ba bari yay mata Googling d'inta yanzu ta gani
girgiza kai gwaggo ta fara yi tana fad'in gaskiya bazai yuwu ba dole tay mashi Magana wannan ai
almubazzaran ci ne Amadu dake kallonta da alamun mamaki yace "kaji gwaggo da wata Magana ina
ruwanki, nasan dae ba rok'onshi tay ba yaji zai iya ne miye naki na shiga Maganar, kuma da kike
Maganar Almubazzaran ci ne kin dae san shi ba mai hakan bane in aikin Alkhairi ne yana yi, ba don ma
bai yin yawa ba da sai ace nashi Alkhairin har yayi yawa, kawae wadata ce in Allah yasa mutum nada ita
sai yay abunda ya ga dama" zugudum gwaggo tay tana bin shi da ido kawae Amadun ya juya kan Fatuu
yana fad'in lalle ita mai k'ashin Arzik'i ce bin shi da ido kawae Fatuu tay jikinta duk ya mutu ita tsoron ma
wayar take ganin yanayin ta yasa Amadu cewa ya yaga kaman bata farinciki kaman zatayi kuka tace
mashi ita dae wllh tsoron wayar take gashi yanzu anata sare mutane wasu ma kashe su ake kan waya
Amadun yace in sha Allahu ba abunda zai sameta tunda tana Addu'a da kuma Azkhar amman dae ta
rink'a kiyayewa kar tay ta nuna ma Mutane a yanzu ta d'an rink'a amfani da tsohuwar tata kafin tay
yawa ta d'aga mashi kai kawae yace zai koya mata yadda zata yi amfani da ita don yasan 13 sosae kuma
ance bambancin su kad'an ne da wannan, sai zuba yake yana taya Fatuu murna gwaggo dae ta zuba
mashi ido kawae da alama takaici ya hana ta Magana, daga baya Amadu ya tashi ya fita sukae zugudum
kowa ya kasa cewa komae can gwaggo ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tace ta kwashe kayan ta kai
d'akinta, bayan ta koma d'akin zaune tay a gefen gado ta zuba ma kwalin wayar ido kamar mai tsoron
ta6a shi can dai ta kai hannu ta d'auka ta bud'e ta zuba ma wayar ido kirjinta na ta fad'uwa ta d'an d'auki
lokaci a hakan kafin da k'yar ta mik'e don yin salla, bayan ta gama ta d'an ci Abinci sannan taje tayo
wanka ta zo ta shirya cikin kayan bacci ta haye gado ta shiga duniyar tunani, ita dae tasan Haisam na
mata abubuwan Alkhairi sosae amman wannan ya matuk'ar d'aure mata kai taya za'ai ace hakanan ya
siya mata irin wannan wayar gaba d'aya ta rasa tunanin ma da zatayi da k'yar bacci ya kwashe ta...........

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2040*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

............Washe gari Fatuu na gama sallar Asuba bata koma bacci ba kasantuwar ranar Monday ce ta hau
yin shirin tafiya School, Misalin k'arfe bakwae saura tana cikin yin breakfast jikinta sanye da Uniform
wayarta dake a gefenta ta fara ringing ta kai hannu ta d'auka sunan Ya Haisam ta gani a screen d'in har
saida ta d'an yi mamaki kafin tay picking, gaishe da shi tayi bayan ta d'aga ya amsa yay mata ta tashi lpy
tace lpy Lou tambayarta yay k'arfe nawa zata je School tace mashi yanzu tana yin Breakfast ne sai wurin
kaman k'arfe 7:15 zata tafi yace Ok zai zo ya kai ta daga haka yay cutting kiran, bin wayar tay da kallo
bayan ta cireta daga kunne tana kallo can kuma ta d'an ta6e baki ta ajeta taci gaba yin breakfast d'in ta,
K'arfe bakwae da Minti goma ya kira yace in ta gama yana waje ta amsa mashi da to dama Hijab kawae
zata saka sai jakar goyon ta ta nufi gaban dressing mirror ta dan k'ara gyara fuskarta ta saka glass d'inta
daga haka ta fita, sai da ta lek'a d'akin gwaggo tay mata sallama ta bata kud'in abun hawa da Abinci tace
ta barsu Ya Haisam ne yazo zai kaita kuma dama akwae wasu canji zata yi break d'in dasu tana murmushi
ta d'aga mata kai kafin tay mata Allah ya tsare ya bada sa'a ta amsa da Amin tana nufar Kopar fita, bayan
ta shiga Motar ta rufe ta juya ta kalle shi yana sanye da jallabiya ash mai gajeran hannu da d'an
murmushi ta gaishe shi fuska a sake ya amsa yana kallonta kafin ya juya ya ja Motar suka tafi, shiru ba
wanda ya k'ara tankawa sai itace ke ta d'an kallon shi sai kuma ta juya duk yana lura da ita ta mirror can
ta k'ara juyowa shima ya juya karaf suka had'a ido ya d'age mata gira yace "What?" d'an motsa baki ta
fara yi a marairaice tace "dama akan wayan da ka siya man jiya ne" idonshi akan hanya yace mi ya samu
wayan tace "ba komae, d..dama Kawu Amadu ne ya fad'i mana kud'inta to shine muka ga tayi kud'i da
yawa don har gwaggo ma tana cewa zata yi maka magana kud'in sun yi yawa sosae" d'an guntun
murmushi yay kaman bazai ce komai ba yana ta driving ita kuma ta kafe shi da ido can yay sigh yace
"yanzu ya za'ai da shi kenan?" Da sauri tace "a barta kayi wani abun da kud'in" d'age gira yay yace "to in
ba abunda za'ai da kud'in fa?" Tura baki tay yana kallon ta ta mirror a shagwa6e tace "ya za'ai ace ba
abunda za'ai da kud'i?" shiru yay yana cigaba da driving da d'an murmushi akan face d'in shi ita kuma sai
faman k'unak'uni take tana yamutsa Fuska sai kace abun tsiya akai mata bana Arziki ba duk yana kallonta
ta mirror can taji yay sigh yace shikenan akwai yadda za'ai to, da sauri tace to ta kai hannu k'asa ta
d'aukko jakarta ta bud'e dama ta sako wayar don ta bashi, fiddota tay ta maida jakar ta mik'a mashi d'an
kallon wayar yay ya maida idon kan hanya taji yace "ai ba nine zan yi ba kece" da d'an mamaki kan
fuskarta tace "ni kuma, to ni zanje in maida masu ne?" girgiza mata kai yay kafin yace "I mean zaki iya
bayar da shi in baki so" waro ido tay da alamun Al'ajabin jin abunda yace ya d'an kalleta ya d'age gira
alamun tabbatar da abunda yace d'in ta cuno baki tana mashi wani kallo batare da ya kalleta ba taji yace
shi take harara a shagwabe tace ita ba hararan shi take ba, tasan tunda ya fad'i hakan ba amsa zai yi ba
dole ta maida ita cikin bag d'in, Lokacin da suka iso ya parker tay mashi godiya tana niyyar juyawa ta
bud'e kopar yace mata wait ta dakata ya bud'e glove box tana ganin kud'i zai ciro ta tsuke fuska bayan ya
d'aukko 5k ya mik'a mata yace tay break tak'i amsa tana kallon shi yace ta amsa mana kawae sai ta fara
jujjuya mashi kai tana mashi magiyar ya bassu gwaggo ta bata, bin ta da ido kawae yake yace tunda ya
fiddo ta amsa sai ta k'ara kawae sai ta juya mashi k'eya still yay yanata kallonta irin abubuwan
shagwabar nan da take yi ba k'aramin tafiya take dashi ba sai tai ta burge shi, jin yayi shiru yasa ta juyo
ganin kallon da yake mata ne yasa itama ta kafe shi da nata idon suka cigaba da bin juna da wani irin
kallo mai wuyar fassarawa dole Fatuu ta sare don bazata iya jurewa ba ba shiri ta sadda kanta jikinta duk
yayi weak d'an guntun murmushin gefe yay ya kira sunanta ta amsa jin bai k'ara cewa komae ba yasa ta
d'ago ta kalleshi alamar ta amshi kud'in Yay mata da kai sai ta kasa k'ara yi mashi gardama don duk ya
kashe mata jiki a sanyaye ta mik'a hannun ya bata ta furta ta gode ta kai hannu ta d'aukko jakarta zata
fita taji ya tambayi k'arfe nawa zasu tashi d'an kallon shi tay tace k'arfe biyu ya d'aga kai ta juya ta bud'e
Motar ta fita, nufar class area tay tana yi tana waiwayen Motar yana kokarin juyawa har ya tafi, tunani iri
iri a ranta har ta isa Class tana shiga Fauzy dake ta zuba idon ganinta ta mik'e da sauri ta nufo ta tana
mata welcome ta d'an mata side hug Fatun na murmushi suka nufi seat d'in su, bayan sun zauna Fatuu
tace da wuri ta taho kenan tace mata a'a ai tun jiya da daddare ta dawo suna haka malamin su ya shigo,
basu k'ara samun daman yin hira ba har saida akayi break sannan Fauzy ta shiga tambayarta ya Haisam
Fatuu tace mata shine ma ai ya kawo ta da d'an mamaki tace "kai haba, shi dae bai gajiya da yin hidima
dake bawan Allah amman mudae ba wannan muka fi so ba kawae ya fito ya mana Wuff da ke don Allah"
d'an ta6e baki Fatuu tay tace "Uhm ai ke Fauzy wannan ba komae bane hidima ai sai jiya da muka fita
dashi" cike da k'aguwa tace "ya kai bani in sha" nan Fatuu ta kwashe komae na kayan da ya siya mata
har zuwa wayar daya siya mata hannu Fauzy tasa ta rufe baki da tsananin mamaki ta maimaita sunan
wayar Fatun tace wllh bari ma ta gani ta kai hannu ta d'aukko jakarta bayan ta bud'e ta zura hannu ta
fiddo da kwalin wayar ta mik'a mata, zaro ido Fauzy tay baki bud'e da d'an k'arfi tace "Wllh iPhone 15
d'in ce da gaske" wannan Maganar da tay ta jawo hankalin yan seat d'in bayan su wata Aisha ta ja hijab
d'in Fauzy ta waiga tace taji tana iPhone 15 su ganta ta mik'a masu kan kace mi sauran wad'anda suke
cikin ajin basu fita break ba harda maza duk suka taso ganin wayar ana tambayar wake da ita Fauzy na
nuna masu Fatuu wani harda cewa ashe dae ita big girl ce mai babbar harka haka, wata student ma tace
ashe dae ita babbar Hajiya ce basu sani ba wani dake gefe ya tambayi wai nawa take ne 15 d'in na kusa
dashi ya bashi amsa nan fa wasu suka zaro idanu wasu suka hau jinjina kai, lokacin da Fauzy ta amshi
wayar ta juya don ta ba Fatuu ganin yanayin fuskar ta yasa ta tambaye ta lafiya miya faru ne kaman
zatayi kuka tace "ni fa Fauzy ban so aka san da wayar nan ba wllh don ni tsoro nike ji ina zaman zamana
in ja ma kaina bala'e" dafa Shoulder d'inta tay tace "in sha Allahu ba abunda zai same ki ki kwantar da
hankalin ki" a sanyaye tace Allah yasa, don ta k'awar mata da damuwar tace "Amman fa gaskiya Zarah
ina tunanin Ya Haisam son ki yake wllh" waro ido Fatuu tay tace "ke waya fad'a maki da har zaki rantse"
tace"uhum haba Zarah kiyi tunani mana nasan ba yau ya fara maki hidima ba amman fa hidiman ta
canza salo ke baki fahimta ba tunda yake dake ya ta6a maki hidima irin wannan ya d'auki abun har
million kacukam ya baki, je ki asa ma shi mai yawan Alkhairi ne mizai sa bazai siya maki wata irin waya ba
tunda gasu nan iri iri in ma masu uban kud'i ne duk akwae su amman sai ya za6i wannan da fitowarta
kenan kuma ba kowa ne zai iya riketa ba ke in ba don kina da wani matsayi a wurin shi ba da yafi wanda
kika sani taya zai maki hakan?" bin ta da ido kawae Fatun take dama kanta duk a d'aure yake game da
sabbin abubuwan da yake mata Fauzy ta ci gaba "ba fa wani abun mamaki bane don ya kamu da son ki
kema da ai yadda ya d'auke ki kika d'auke shi ko ta zo ta canza zani to shima d'in zai yuwu hakan ce ta
faru dashi ni wllh in hakan ta kasance sai nafi kowa farinciki ko ba komae Allah ya amshi Addu'ar mu
zuciyarki kuma ta samu abunda take muradi" sai lokacin Fatuu tay d'an murmushi had'i da yar ajiyar
zuciya,

"Yanzu ace sai ya bayyana maki yana son ki kuma yana son kuyi aure zaki hak'ura da karatun ki bi
shi?"Fauzy ta tambaye ta had'i da d'age gira wani kallo Fatuu ta jefa mata kafin tace "har ma sai na baki
amsa ai kema kinsani" dariya Fauzy ta sa tace "baki tsoron matar shi kawae sai ta ganki da mijinta
matsayin Matar shi?" Fatun tace "to ai cewa kikae in yace yana sona kuma ya aure ni kinga tunda shi ya
6allo ruwa ai shi zai san yadda zai da ita ko" duk suka sa dariya Fauzy na fad'in uwar wayo wato shi yace
yana so sai kace ita irin bata so d'in nan Fatun na dariya tace to ai irin hakan saida basaja suka ci gaba da
dariya har Fauzy na Addu'ar Allah ya nuna mata ranar da zaice yana son ta a kur kusa Fatun tace shida
ma zai tafi yau tace ai duk inda yake zai iya furta mata hakan ba wata matsala bace, daga baya Fatun
tace suje suyi break lokaci nata tafiya kar a dawo suka tafi, k'arfe biyu daidai Haisam ya kirata yace yana
inda ya ajeta da safe, tare da Fauzy suka taho suka zagaya d'ayan side d'in Fatuu ta bud'e gaban ta shiga
Fauzy ta leka tana murmushi ta gaishe da shi fuska a sake ya amsa mata tace Zarah ta fad'a mata yau zai
tafi Allah ya kiyaye a gaida Aunty Fanan ya amsa da Ok zata ji daga haka tace ma Fatuu sai sun had'u
Gobe tace to, tun bayan da ta shiga cikin Motar ta gaishe da shi ya amsa bata k'ara cewa komae ba har
suka hau hanya can ta kalleshi tace "sai k'arfe nawa zaka tafi?" Fuska sake yana kallon hanya taji yace ta
k'osa ya tafi ne da sauri tace a'a ta dae tambaya ne kawae gyad'a kai yay suka d'an yi shiru sai kuma taji
yace "ko za ki ne?" da sauri ta kalleshi tace ina yace "U.s" d'an bud'a ido tay tace "ni da nike karatu"
shiru ya d'anyi still bai kalleta ba can yace "da ba karatun za ki je kenan?" itama shirun ta d'an yi har
saida ya d'an juyo ya ce mata bata ji bane cike da jin kunya a hankali ta d'aga mashi kai alamar eh kawae
sai gani tay yay d'an murmushi ya maida idon shi kan hanya saida ya d'an d'auki lokaci sannan ya sake
cewa "kin daina tsoron matana kenan" tsuke fuska tay ta d'an tura baki tace "ai ni dama ba tsoron ta
nike ba kawae dae ina ganin in naje bazata ji dad'i ba taga bamu had'a komai ba na bika har can karshe
ma ta koro ni" d'an murmushi yay kafin yace "to yanzu da kika ce da ba karatun zaki kin daina tunanin
zata ji ba dad'in ne?" d'an watsa hannu tay tace "to ai kaine ka tafi dani ko bani nace ba in ma taji ba
dad'i kai kasan yadda zaka yi" wani kallo ya juyo yay mata duk sai tasha jinin jikinta ta fara sussuna kai
kamar daga sama taji yace "yanzu in tafi dake d'in kenan?" Da sauri ta kalleshi suka had'a ido ya d'age
mata gira alamar ta bashi amsa da sauri ta girgiza mashi kai tace "ni fa ba so nike in bika ba tun farko na
tambaye ka lokacin da zaka tafi ne don in raka ka Airport" murmushi kawae yay yaci gaba da driving d'in
shi itama ta juyar da kanta taci gaba da kallon hanya har suka iso gida ba wanda ya k'ara tankawa tay
mashi godiya ta d'auki jakarta tana kokarin bud'e kopar ta ji yace mata before 4:30 zai tafi ta d'aga mashi
kai ta fita yaja Motar ya wuce gida. Tana shiga gidan ta wuce d'akin gwaggo tay mata sannu da gida anan
ta sanar mata zancen tafiyar Haisam gwaggon tace bari ta tashi to taje tay mashi sallama, d'aki Fatuu ta
nufa ta aje jakarta kafin ta wuce kitchen ta zubo Abinci ba wani mai yawa ta ci ba don sunci abubuwa
sosae da break ita da Fauzy tana gamawa ta wuce toilet don yin wanka, Misalin karfe hud'u da yan
mintuna lokacin angama sallar la'asar Fatuu ta isa part d'in Haisam tana sanye da riga da skirt na atampa
mai jajayen flowers had'i da mayafi mahad'in su tayi d'aurin kallabi mai kyau ga glasses d'inta manne a
idanun ta, a hankali ta tura kopar parlon ta shiga da yar sallama idanun ta suka sauka kan Abbas dake
zaune kan L-shape yana sanye cikin k'ananun kaya kasumbar shi tasha gyara gashin sai kyalli yake suna
had'a ido suka sakar ma juna murmushi yace mata ta shigo mana tayi tsaye a bakin kopa ta nufi armchair
ta zauna ta gaida Abbas d'in da murmushi ya amsa mata ta tambayi Abdul yace yana school bai dawo ba
da yake yana yin lesson ta jinjina kai shiru suka d'an yi ta juyar da kanta can taji yace tazo raka mutumin
nata ne d'an murmushi tay kawai bata ce komae ba shima yar dariya yay bai k'ara cewa komae ba can
kuma sai ya mik'e yace yana zuwa in Haisam ya fito tace mashi yana Mota ta d'aga mashi kay ya nufi
hanyar fita, after few seconds sai gashi ya fito yana janye da d'an trolley da kuma jakar laptop yana
sanye da kananun kaya kai idonta tay kan shi har ya k'araso cikin parlon ya tsaya gefenta yana kallonta
ganin hakan yasa ta mik'e tana cigaba da kallon shi da d'an murmushi ta gaida shi ya amsa ta fad'a mashi
Ya Abbas yace yana Mota yana dai ta kallon ta tana Maganar kawae sai ji tay slowly yace "baki tsawo
ne?" bud'a ido tay alamar mamaki sai kuma ta d'an tura baki tace "duk tsawon da nayi, dafa a iya nan
d'in ka nike yanzu kuma kad'an ya rage in kawo shoulder d'in ka" tay Maganar tana nuna mashi inda ada
tsawonta yake a jikin shi daga inda take, shiru bai ce komae ba yana cigaba da kallonta fuska a sake
ganin bai ce komae ba yasa a d'an shagwa6e tace "to tunda baka ganin tsawona kai sai ka samman naka
tunda kana dashi kai sosae" shirun dai yay sai kuma ya d'age gira yace tana so ta d'an k'ank'ance ido ta
d'aga kai alamar eh, aje jakar laptop d'in dake a d'ayan hannun shi yay kan d'ayar armchair d'in dama ya
saki trolley d'in tunda ya tsaya kawae sai gani tay ya kai hannu d'aya ya jawota jikin shi a razane ta zaro
ido tana kallon shi shima haka still holding onto her motsa baki ta fara amman ta kasa cewa komae bata
ankara ba sai ji tay ya ida yin hugging nata sosae ta yarda har ya d'aura Ha6arshi a saman kanta, zaro ido
Fatuu tay ta d'an bud'e baki alamar Al'ajabi k'amshin turaren shi ne ya cika mata hanci har bata san
lokacin da slowly ta lumshe idanunta ba zuciyarta ta fara melting sun d'an d'auki lokaci a haka can wata
zuciyar ta fara raya mata hakan fa da sukae ba kyau miyasa zata bari ya rungume ta haka bacin tasan ba
matar shi bace ita ko har ta manta da labarin yaudarar da aka ma Fauzy ne da sauri ta bud'e idonta jin
tana kokarin d'ago da kanta yasa shi cire beard d'in nashi daga saman kanta ta d'ago ta kalle shi sam
bazata iya karantar yanayin fuskar shi ba, ganin baida niyyar sakinta yasa ta kira sunan shi cikin
disasshiyar murya ya d'an bud'a ido alamar amsawa da ido tay mashi nuni da rok'on da yay mata alamar
ya saketa ya kafeta da ido kamar bai gane mi take nufi ba hakan yasa ta d'an 6ata fuska sigh yay slowly
ya saketa had'i da furta "am sorry" shiru tay ta sadda kanta ya kai hannu zai kama trolley d'in ta d'ago
tace mashi bari ta rike bai ce komae ba ya d'auki jakar laptop d'in yay gaba ita kuma taja trolley d'in tabi
bayan shi, saida suka je part d'in Hajiya harda Abbas ta rako su har bakin Mota tana ma Haisam Allah
yasa a sauka Lafiya ya gaida su Farha da yake Lagos zai sauka daga can gobe zai wuce Us, Abbas ne ya
shiga driver seat sai Haisam na gefen shi ita kuma Fatuu ta shiga baya ya tashi Motar Hajiya nata d'aga
masu hannu har suka fuce, bayan sun hau hanya sama sama Abbas da Haisam d'in ke yin hira can Abbas
ya kalli Fatuu ta cikin mirror yace "Mom Zarah yau ba kuka kenan Ya Handsome zai tafi" dariya tay mashi
bata ce komae ba Haisam ya d'an juyo ya kalleta ta rufe Fuskar ta da gyalen ta Abbas duk yana kallon ta
ta cikin mirror yana dariya yace "yakamata yau ma a d'an rera mana gaskiya" d'an tura baki tay tace "ai
ko wanccan lokacin ma don ina tunanin ya tafi kenan ko zai zo sai an dad'e" Abbas yace "Hajiya na raye
ai dole zai rink'a zuwa ko don ita yanzu ma ai in ya tafi baza'a dad'e ba sosae zai dawo don akwai bikin
wani Friend d'in mu da za'a yi bayan babban salla kuma shine best friend d'in shi a cikin musulmai" waro
ido Fatuu tay tace shi kenan ba musulmi bane yace eh Christian ne d'an sarkin inyamurai ne sun d'an
zauna anan amman yanzu ba'a nan suke da zama ba amman shi wanda zai auren shi ke kula da wasu
wurare na mahaifin shi kamar Hotels da wasu kamfuna tare sukae Secondary da shi, jinjina kai Fatun tay
kawae shi dai Haisam bai tanka masu ba, bayan sun iso Airport d'in gaba d'aya suka fito Haisam ya
zagaya wurin Abbas ya bashi hannu yay mashi godiya shima yay mashi fatan sauka lpy ya juya ya kalli
Fatuu dake d'ayan side d'in tana kallon shi da d'an murmushi shima yay mata daga haka ya juya ya tafi
har ya d'an yi nisa Fatun ta k'wala mashi kira ya tsaya ya juyo ya kalleta da faffadan murmushi ta d'aga
hannu tana yi mashi bye bye yana murmushi ya jinjina mata kai kafin ya juya Abbas dake dariya ya
kalleta suka had'a ido ganin dariyar da yake mata yasa ta d'an cuno mashi baki yace shidae ai bai ce
komae ba ta shige cikin Motar shima ya bud'e ya shiga ya ja suka tafi. Sati biyu da tafiyar Haisam aka fara
Azumi saida ya turo mata kud'i masu yawa na siyan kayan Azumi tuni ta kai kayan da ya siya mata wurin
Kb don a d'inka da aka fara Azumin har tana zolayar gwaggo wai ya taga bata da niyyar yi mata d'inkin
salla tana dariya tace ai ita Haisam ya d'auke mata nauyin wannan kuma, a cikin kayan da ya siya mata
taba gwaggon atampa da lace amman sai ta amshi lace d'in kawae tace ta bar atampar ta k'ara ba yadda
bata yi da ita ba amman tak'i karba sai taba Fauzy ita kawai dama tana da wani material da bata d'inka
ba ta had'a mata sosae Fauzy taji dad'in kayan tay ta godiya a tare suka kai d'inkin bayan Fauzy tasa
Fatuu ta rakata itama shagon Zee ta siyo kayan sallanta har Fatuu ta k'ara siya mata wasu abubuwan Zee
taji dad'in kawo mata Customer da Fatun tay har tay adding nasu a groups d'inta da take business koda
zasu ga abu suna so, Alhamdulillah angama Azumi lpy ranar salla tare da Hajiyar Sanata harda Fauzy suka
je Masallaci ko k'unshi ma tare suka je gidan su Nanah kamar kowacce Salla, da Fauzy gida zata tafi yin
salla amman Saboda tana son su yi yawo tare da Fatuu ta fasa sai bayan sallan zasu tafi tare da Aunty
Mareeya, su Fatuu an zama yan mata sun dai sha kyau da sallar abun ba'a Magana Tk ne ya kaisu wurare
kamar yadda Haisam ya bashi umarni ko ina tare da Fauzy take zuwa har gidan Abbas suka je da sauran
wurare sun sha zafafan hotuna da iPhone d'in Fatuu harda Vedios suka daddaura a status anan Haisam
ya gani har ya yaba sosae taji dad'in yabon da yayi har saida ta kasa hak'uri ta ma Fauzy forwarding sai
ga Voice note d'inta harda su shewa tana fad'in "Zarah da alamu mutumin nan fa ya kamu wllh kawae
miskilanci ne ke d'awainiya da shi amman muje zuwa gab yake da ya shigo hannu" ita dae Fatuu dariya
kawae take, har gida Aunty Mareeya tazo tayi ma gwaggo an sha ruwa lpy bayan salla haka ma Abbas ya
kawo Feenah da suka zo gidan Hajiya, ana gama salla Fauzy ta tafi Funtua Fatuu taso ta bita amman
gwaggo ta hana satin ta d'aya ta dawo suka koma Makaranta sun ci gaba da karatu ba tare da wasa ba a
haka har babbar salla tazo wannan lokacin Yola gwaggo tace zasu je yin salla Fatuu taji dad'i sosae ana
saura kwana biyu suka tafi Hajiya ma wannan karon saida babbar salla taje Abuja don da k'arama cewa
tay bazata je ba ai bata dad'e da dawowa ba Fauzy a Katsina tay salla cike da kad'aici saida suka gama
aikin naman layya sannan suka tafi Funtua, su Yadikko sun matuk'ar yin murna da zuwan su kar ma Mino
taji ta kasa boye murnarta harda d'inki gwaggo tayi masu su duka harda baffan Fatun da shima yay farin
cikin ganin su, kud'i masu yawa da zasu siya lafiyayyun raguna biyu Haisam ya turo ma Fatuu yace suyi
layya harda kud'in da zatayi hidiman salla lokacin da ta kira don yi mashi godiya yake sanar da ita sun zo
suna Abuja har tana ce mashi zai je katsina ne yace ai Hajiya bata nan kuma suma basu nan wurin wa zai
je tace ai da an gama salla zasu koma yace suma bazasu dad'e bane amman yana nan zuwa bikin abokin
shi da Abbas ya fad'a mata tace Allah ya kaimu, ana gama salla da kwana biyu suka dawo don ba wani
Hutu suka samu ba just salla break ne, washe garin da suka dawo Fauzy ma ta dawo suka cigaba da
karatun su.

A bangaren mutanen Us ma tuni sun koma lokacin Auren su ya cika shekara harda kusan wata a lokacin
Fanan ta matsa lamba kan lalle sai suje a duba lafiyar su ta bangaren haihuwa don tun auren su bata
ta6a yin 6atan wata ba koda kuwa sau d'aya gashi tana period lpy lau, wannan karon ma dai kaman
sauran lokutta Haisam d'in cewa yay basu bukatan hakan yanzu ta bari a k'ara lokaci in bata samu ba sai
su je amman shi a wurin shi still yayi wuri amman tak'i gaba d'aya ta burkice mashi wai dole tasan wani
cikin su bai rasa matsala tunda har sun shekara amman har yanzu batai conceiving ba, sosae ta hana
mashi zaman lafiya harda su koke koke to shi mutum ne mara son yaga wani cikin damuwa balle ma ace
shine sila hakan yasa yace tayi duk abunda ya kamata sai su je d'in, sosae taji dad'i ba 6ata lokaci tay
making appointment da Doctor d'in da zasu gani a Asibitin da take aiki washe gari suka je aka fara masu
diagnosis daga baya kuma yay referring nasu wani Asibitin suga Fertility specialist anan aka cigaba da yin
binciken tun daga Family history nasu ko akwae wanda bai haihuwa zuwa su awon jini da hotuna sosae
akai investigations saidae an fi yi ma Fanan don ita yake ganin kaman in ma matsala ce to daga ita ne
sakamakon wasu tambayoyi da yay mata sai washe gari suka gama likita ya fara masu bayanin result na
binciken da akayi masu anan yake fad'i masu Fanan ce mai matsalar don tana da Polycystic ovary
syndrome (PCOS) Wato matsala ce data shafi kwan da take saki har saida Fanan ta firgita jin wannan
Maganar a razane tace how comes ita da take having regular periods! Shima Doctor d'in yayi mamakin
hakan daya kasance bata ga wani symptoms ba don yawanci indai mace nada matsalar to zata rink'a
samun irregular periods ne bazata rink'a yin period very often ba saidae kuma a tambayoyin da yayi
mata farko ta tabbatar mashi wani lokacin periods d'in yana d'an dad'e mata in yazo amman bata maida
kai kan hakan matsala bane don tun kafin tay aure ma tana hakan wanda hakan ma na daga cikin
alamomin matsalar tata sai kuma a Family history nan ma ta tabbatar mashi da Kakarta wato Hajiyar
Sanata tana da Matsalar yawan miscarriage lokacin tana haihuwa hakan yasa iya yara biyu ta Haifa a
rayuwarta daga Mahaifin Haisam d'in sai kuma Mahaifiyarta hakan ma ya k'ara tabbatar da yuwuwar
tayi gadon matsalan ne daga wurinta, tuni hawaye suka wanke mata fuska don tasan tabbas indae
tanada wannan matsalar to zata iya hana ta samun ciki balle harta haihu rarrashinta suka fara yi suna
bata hak'uri Doctor yace bai kamata ta tashi hankalinta ba tunda is treatable za'a iya dacewa ta samu
cikin nan ya shiga bata shawarwari da abunda yakamata ayi, tun bayan da suka baro Asibitin take ta
cizgar kuka tana fad'in "Ya Haisam am barren! I cannot give birth I can't give u child!!!" Duk ta firgice
abunka da fara jijiyoyin kanta duk sun firfito fuskarta ta yi jajir ya kai hannu ya ruk'o nata yana d'an
murza shi alamar rarrashi sai faman kuka take tana fad'in ta bani bazata iya haihuwa ba shikenan bazata
bashi d'a ba har shakewa take wurin yin Maganar Saboda kuka shi kam sai faman rarrashinta yake a
nutse yake fad'in ta kwantar da hankalinta hakan ai ba yana nufin kwata kwata bazata haihu bane Allah
na iya nuna ikon shi a kowane lokaci a haka har suka iso gida still yana ruk'e da hannunta suka shiga
Parlor a saman 3 seater suka zauna ya rungumeta yana cigaba da rarrashinta sai faman fad'in tasan da
wuya ta haihu tunda tayi gadone kuma gara ita Hajiya ma tana yin miscarriage amman itafa ko sau d'aya
bata taba samun cikin ba balle ma tayi 6arin, suna cikin hakan can ya ji ta tayi tsit kamar ba ita ke rizgar
kuka ba da sauri ya d'ago fuskarta da tay jage jage yaga idanunta a rufe alamar ta suma a razane ya
mik'e ya kwantar da ita akan kujerar ya nufi fridge ya d'aukko bottle water ya dawo bayan ya cire murfin
ya d'an zuba a cikin hannun shi ya yayyafa mata a fuska sai gashi ta ja wata irin doguwar ajiyar zuciya da
sauri ya rufe robar ya aje gefe ya duk'a a gabanta ya kai hannu yana d'an bubbuga face d'inta had'i da
kiran sunanta slowly ta bud'e idanun suka k'ura ma juna ido can kawae sai ta k'ara fashewa da wani
Sabon kukan daga kwancen tana girgiza kai hannu yasa yana shafa gefen fuskarta a hankali yaci gaba da
rarrashinta can ta yunk'ura ta mik'e da gudu ta nufi d'aki ya mik'e ya bi bayanta..........

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2041*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

........Sai dae ko kafin ya kai har ta kulle kopar, knocking ya fara yi yana kiran sunanta shiru har bayan
wani lokaci tak'i ta bud'e hakan yasa ya koma cikin parlon ya zauna had'i da had'e hannuwan shi ya
d'aura beard d'in shi, shi dama initially hakanan zuwa binciken lafiyar bai kwanta mashi ba kawai don ta
matsa ne yasanta sarai da k'wallafa rai akan abu in bai goya mata baya ba haka za tay ta damuwa yanzu
kuma ga wata damuwar data fi wancan, tunanin yadda akai tana da wannan problem d'in amman ko ita
bata gane ba a matsayin ta na likita ya shiga yi daga baya kuma ya tuna in Allah yaso ya 6oye Al'amari
dama ba lalle a gane ba yana ta zaune can ya mik'e ya koma kan 3 seater ya d'auki wayar shi ya fara
kokarin kiran Hajiya tana fara ringing ta d'auka suka gaisa ta tambayi ya Fanan jin ya d'an yi shiru dama
ta ji yanayin voice d'in shi kaman yana cikin damuwa, tambayar shi tayi lafiya taji kaman yana cikin
damuwa saida ya d'an nisa sannan cikin natsuwa ya fara mata bayanin komae to itama dae Hajiyar ta
girgiza da jin bayanin matsalar tabbas itama haka tay ta fama da lalurar yawan 6ari wani lokacin sai cikin
yayi kaman zai tsaya sai kuma ya zube ko kuma bayan ta haife ya koma saidae kuma tayi mamakin jin
Fanan nada irin matsalar ba tare da an ta6a fuskantar wata babbar alama ba, cikin tashin hankali ta
tambaye shi tana ina yace mata tayi locking kanta acikin d'akin tace bari ta kira wayar ta ya sanar da ita
wayan na nan parlor, cike da damuwa tace dole ta shiga mawuyacin hali ba kamar yadda take da son ta
haihu, ce mashi tay ya samu ya lalla6a ta ta bud'e kar wani abun ya sameta ba kamar da yake rarraunar
zuciya gareta ya rarrasheta sosae itama zata kira suyi Magana ya amsa mata da Ok, mik'ewa yay walking
slowly ya sake komawa bakin kopar yana knocking had'i da kiran sunanta shiru bata bud'e ba hakan yasa
shi fara tunanin kar wani abu ya sameta nan take ya yanke zuwa yasa azo a 6alle kopan yana shirin
juyawa yaji tana bud'e wa da sauri ya dakata ya kai idon shi jikin kopar yasa hannu ya tura, a tsaye ya
ganta har saida gabanshi ya fad'i ganin yadda cikin kankanin lokaci duk ta yamutse ga hancinta duk
alamun jini da alama nose bleeding tay dama yasan tana hakan tun tana k'arama in ranta ya 6aci ko ta
buge sai tayi ha6o, hannunta ya kama suka koma cikin d'akin ya zaunar da ita gefen gado shima ya zauna
idon shi a Kanta sai faman ajiyar zuciya take saukewa still yana ruk'e da hannunta guda slowly ya furta
"Fanan" kaman bazata amsa ba sai kuma a hankali tace "Na'am" cigaba yay "Why all dis? Do you want to
harm your self?" Shiru tay bata ce komae ba ya cigaba "I know how u'r feeling but kiyi hakuri muyi
Addu'a Allah ya yaye matsalan yakamata ba damuwa ba tunda is curable kowane lokaci zaki iya samun
lafiya" a hankali ta d'ago da rinannun idanunta ta kalle shi cikin disasshiyar murya tace "Babe ina tsoron
ace bazan haihu ba bansan ya zaman mu zai kasance ba" ta k'arasa kwalla na zubo mata ya kai hannu ya
jawo ta jikin shi yay mata side hug ya d'aura ha6ar shi a saman gashin ta gently yace "In sha Allah zaki
haihu and nothing will change tsakanin mu ko kin haihu ko baki haihu ba ina son wife ena itama tana
sona hakan ya wadatar dani" lumshe ido tay koba komae taji dad'in Maganar shi kuma tasan har cikin
ranshi gaskiya ya fad'a mata shiru tay tana cigaba da shak'ar daddadan k'amshin da jikinshi ke fitarwa
tana jin wata irin natsuwa na shigar ta, Allah ne shaida tana matuk'ar son Haisam tana jin tamkar da son
shi aka halicce ta tabbas tasan rasashi babbar barazana ce ga rayuwarta tana wannan tunanin wata
zuciyar ta ayyana mata wani abu da yasa gabanta fad'uwa ba shiri ta d'ago da kanta ta kalle shi shima ita
yake kallo ganin kaman tana son yin Magana yasa ya tambayeta akwae wani abu ta d'aga mashi kai
alamar eh yace ta fad'a mashi miye d'an jimm tay kafin tace "pls Ya Haisam I want a Favour from you"
jinjina mata kai yay alamar to k'ara yin shiru tay tama rasa ta ina zata fara ya lura da ta kasa fad'i mashi
Alfarmar da take son yay matan ya kai hannuwan shi ya kama duka hannuwanta yace kar ta ji komai ta
fad'a mashi zai yi iyakar kokarin shi yay mata abunda take so in dai zai sakata farin ciki kuma ta daina
damuwa haka, jin wannan batun nashi yasa ta samu k'warin gwuiwa ta fara magana cikin d'an rawar
murya tace "I.... i want u to promise me dat you'll not marry another wife" bin ta kawai yay da ido bai
ta6a zaton abunda zata fad'i ba kenan don bai ga dalilin da zata fad'i hakan ba, kaman ta san tunanin da
yake ta had'iya abu kafin tace "ina nufin koda ban haihu ba don Allah ya Haisam kai man Alk'awarin
bazaka k'ara aure ba tunda akwae hanyoyin da zamu iya samun yara zamu iya adopting ma in muna so"
still kallon ta kawai yake hakanan ya kasa ce mata komai ganin kallon da yake Matan yasa taci gaba "isn't
dat am trying to be selfish kawai ban son rasa ka ne babe in ya kasance ban haihu ba ka auro wata ta zo
ta haihu zata rink'a man gori tana kirana juya k'arshe ma ta raba ni da kai hakan ya sha faruwa wllh and I
can't survive without u" ta k'arasa kwalla na shararo mata taci gaba da tabbatar mashi da hakan zai faru
in dae ya k'ara aure rayuwarta na cikin had'ari ya taimaketa su ci gaba da zaman su tare, gaba d'aya ya
rasa mi zai ce mata bawai bazai iya yi mata alk'awarin bane amman yasan ta dama can tana da kishi ko
ba don wannan matsalar ba tana yawan rok'on shi kan kada yay mata kishiya don bazata iya sharing
nashi da wata ba da dai sauran maganganu, ganin yak'i yace komae yasa ta k'ara sautin kukan ta tana
fad'in ya taimaketa yay mata alk'awari hakan ne kawae zai sa ta samu natsuwa a cikin zuciyarta da yanzu
take mata rad'ad'i sauke ajiyar zuciya yay ya d'an yi jimm kafin calmly yace mata shikenan yayi mata
alk'awarin hakan tun kan ya rufe baki ta fad'a jikin shi ta wani k'ank'ame shi tanata mashi godiya had'i da
d'agowa tana yi mashi kiss a dukkan side d'in fuskar shi d'an murmushi kawai yay can yace ta tashi tay
wanka zata fi jin dad'in jikinta tace to suyi tare mana yace mata zai d'an yi wani abu yanzu taje tayi yana
zuwa ya fara kokarin mik'ewa yana ruk'e da hannunta ya d'agata saida ya kaita har cikin toilet d'in
sannan ya fito, Bedroom d'in shi ya nufa yana shiga bayan ya rufe kopar ya nufi bakin gadon shi ya
zauna, had'e dukkan hannuwan shi yay ya d'aura ha6arshi hakanan yake jin kaman bai yi daidai ba da
yace yayi mata alk'awarin to amman yasan in har ba yayi mata yadda take son ba bazata ta6a natsuwa
tabar damuwa ba ya d'an d'auki lokaci a haka yanata sak'e sak'e kafin can ya mik'e da k'yar don duk jin
jikin shi yake ba dad'i ya nufi toilet, sosae taji dad'in jikinta da ta fito daga wankan duk da da sauran
damuwa da kuma fargaba a cikin ranta na ko zata warke ta haihu ko bazata warke ba press ta nufa ta
ciro wata yar riga iya gwuiwa tasa ta nufi gaban dressing mirror iya turare da roll on kawae ta sa ko mai
bata shafa ba ta nufi Parlor don ta d'aukko wayarta, bayan ta dawo a bakin gadon ta zauna ta kira
Momynta gaisawa suka fara yi tace ya taji muryarta ta canza bata lafiya ne aikuwa kaman tana jira ta
saka mata kuka nan fa Hajiya Maryam ta rud'e ta hau tambayarta abunda ya faru cikin kuka ta shiga fad'i
mata komae sosae itama ta girgiza ta hau yin salati harda ce mata ta tabbatar an yi aune aunen daidai
kuwa tace mata eh kwararran likita ne suka gani sosae ta shiga damuwa amman Saboda kada ta k'ara
tada ma Fanan d'in hankali sai ta hau rarrashinta tana nuna mata kada ta damu in sha Allahu zata samu
lafiya tunda ana warkewa tambayar ta tay mi Haisam d'in yace da yaji zancen matsalar tace hakuri yake
ta bata yana rarrashinta sam bai damu ba yama yi mata Alk'awarin koda bata haihu ba bazai k'ara aure
ba zasu cigaba da zama a haka sosae Hajiya Maryam taji dad'i tace mata in sha Allahu ma zata haihu
bama d'a guda ba yanzun dae ta tabbatar ta kwantar da hankalinta tunda Haisam d'in ma bai damu ba
dama shine abun ji daga baya ta tambaye ta ta fad'a ma Daddy d'in su ne tace a'a Hajiya maryam d'in
tace to ta bari yanzu zata kira ta sanar mashi tasan zai kirata tace to ta tambayeta su Farha da sauran
yan'uwanta daga baya sukae sallama tana niyyar aje wayar kan gadon sai ga kiran Hajiya ya shigo bayan
tay picking suka gaisa ta hau jajanta lamarin kafin ta shiga kwantar mata da hankali sosae tana mata
nasiha daga baya sukai sallama ta aje wayar ta kwanta tana facing ceiling ba tunanin kowa take ba face
Haisam ita tasan ta gama yin dacen miji ba k'aramar baiwa Allah yay mata da samun shi ba slowly ta
lumshe ido wani irin son shi na ratsa zuciyarta tana haka wayarta ta sake yin ringing ta kai hannu ta
d'aukko sunan Dad d'in ta ne ya bayyana kan screen d'in da sauri ta yunk'ura ta tashi zaune, bayan tay
picking ta gaishe dashi shima dai rarrashin ta ya shiga yi yana kwantar mata da hankali yace kada ta
damu za'ai iya bakin k'ok'ari ay treating problem din yana nan zuwa ma sosae taji dad'i harda su
murmushi bayan sun gama wayar ne ta tuna da basu ci lunch ba gashi har yamma tayi sosae da sauri ta
mik'e ta fita daga d'akin ta nufi Bedroom d'in Haisam tana shiga ta iske shi saman gado a kwance jikin shi
sanye da jallabiya don yana fitowa ita kawae ya zura ya kwanta da alama dae wani abun na damun shi ko
kuwa alk'awarin da ya daukan ne Allah masani, tana isa bakin gadon ta zauna ta kwantar da kanta a
saman chest d'in shi can ta d'ago suka had'a ido ganin yanayin shi yasa da sauri ta tambaye shi mike
damun shi ne slowly yace mata ba komae ya gaji ne tace tasan harda yunwa yay hak'uri bata bashi
Abinci ba har yamma yayi sosai ya taso suje table ta mik'e tana kokarin d'aga shi ta hanyar kama hannun
shi, baida yadda zai yi dole ya tashin ya zuro da k'afafun shi amman yafi buk'atar kwanciyar ya ji shi
shiru, a daren ranar sosae Fanan ta faranta mashi duk da damuwar da take ciki da alama tukuicin
Alk'awari ne aka bashi, Allah dai yasa a wanye lpy.

A daidai kopar gidansu Keke Napep d'in ta tsaya Fatuu ta fito jikinta sanye da fararen Uniform d'inta ta
biya shi kud'in shi ya ja ya tafi tana juyawa zata nufi gida taje da d'an k'arfi ance mata "wait!" da sauri ta
juyo idanunta suka sauka akan wanda yay Maganar Matashi ne kaman tsaran Kawu Amadu ko ya d'an
girme mashi yana sanye da manyan kayan shadda blue harda hula tsaye tay tana kallon shi ya nufo ta a
gabanta ya tsaya yana mata murmushi ita kuma ta k'ura mashi ido gani take tasan mai fuskar amman
tana kokonton in shine d'in don ya canza mata sosae ganin irin kallon da take mashi ne yasa shi cewa
"halan baki gane ni ba, ko sai nace Aljana sannan" waro ido Fatuu tay baki bud'e da tsananin mamaki
tace "GAYE!" d'an d'aure fuska yay yana mata wani kallo yace "Point of correction, ba wannan sunan
yanzu Ashiru zaki ce ko kice Malam Ashiru" k'ara bud'a baki Fatuu tay tasa hannu ta rufe baki mamaki ya
gama kasheta abunda bata ta6a zaton gani ba ne take gani a gabanta shi kuwa sai faman murmushi yake
don ya fahimci Al'ajabi ya hanata magana can yace tunda bazata tay mashi Magana ba bari ya tafi da
sauri tace "to ai ni Gaye wllh mamaki yama hana ni yin magana wai don Allah da gaske kaine?" Yar
harara ya wurga mata yace "ba nace maki ba wannan sunan ba yanzu ko so kike ki zubda ma Malam
Mutunci ne" Fatuu kau mi zatay in ba Dariya harda tafa hannu ta ruk'e ha6a bin ta da kallo yay daga
sama har k'asa yace "Oh su Aljana an girma nayi k'ok'ari ma dana gane ki koda yake d'azun da safe naga
Amadu na tambaye shike ke yace man kina makaranta shiyasa yanzu ina ganin ki na gane kece a ina kike
karatu ne?" ta fad'i mashi still da mamaki akan fuskar tata don gaba d'aya ya canza Maganar ma cikin
natsuwa yake yin ta irin ta masu hankali, tambayar shi tay wai ina ya tafi ne ta daina ganinshi yace mata
yana Jos,

"Kaci gaba da karatu ne?" ta tambaya yace "Eh mana, ke da ban cigaba ba Kya ganni haka na gama
Nce" bud'a ido Fatuu tay tace "inyee yayi kyau gay....au Malam Ashiru, mi ka karanta ne?"

"Islamic studies kinsan d'an Malam ne ni nayi gado" Fatuu na murmushi tace da kyau ta taya shi murna
Allah yasa Alkhairi ya amsa mata da Amin tace "ina Abokan ka su goga" wani kallo yay mata irin baiso
tambayarba tay yar dariya tace don Allah suna ina yace duk sun yi laifi suna gidan yari Fatuu ta zaro ido
tace "kace saida dai suka je gidan yarin saura kai kenan" cike da zolaya tay Maganar aikuwa ya galla
mata harara yace "amman gaskiya ke mak'iyata ce yanzu Malam d'in kike ma fatan zuwa gidan yari
Saboda rashin Mutunci" sosae Fatuu ke dariya tana fad'in ashe har yanzu bai daina tsoron zuwa gidan
yari ba yakamata ya d'an je ko don yaci gabza shima dariyar yake yace wannan ai tata ce ita yakamata ta
ci ta koda sau d'aya ne,

"Sai Mutumin ki yay aure" tambayar shi tay wa yace "Yaya Haisam na gidan Hajiya mana ai nayi zaton
ke zai aura" yanayin murmushin fuskarta ne ya d'an canza tace waya fad'a mashi son ta yake da zai
aureta yace "kawae yanayin yadda naga yana kula ki ya damu dake acan baya yasa nay tunanin ko yana
ciki ne" d'an ta6e baki tay bata ce komai ba yace "da kin aure shi da kin more miji wllh ni tunda nike a
rayuwa ta ko a labari ban taba jin mutum mai kirki irin nashi ba don kirkin nashi har ya yi yawa kinsan fa
shine ya d'auki nauyin karatun da nayi bayan daya sa aka yafe mana laifin nan....." Nan ya kwashe komai
tun daga ranar da suka je da mahaifin shi yin godiya ya fad'a mata yace yanzu ma da ya dawo nan aikin
teaching za'a samar mashi har ma yasa ya kai ma Hajiyar Sanata takardun shi gyad'a kai Fatuu tay tace
mashi ai yasan mijin wata bai auren matar wani kowa da wanda Allah ya kaddaro zai aura yace tabbas
hakane tace shi yaushe zai auren ne yana dariya yace "ai bani da budurwa saidae ko in ke zaki taimaka ki
aure ni" wata muguwar harara ta watsa mashi kafin tay dariya tace ai ni nafi k'arfin ka gaye ko da can ma
saidai ka zama driver na sosae yake dariya yana fad'in yanzun Malam d'in ne zai zama drivern ta, ganin
kaman ta gaji yace ta shiga gida ya tsayar da ita kuma yasan ta kwaso gajiya da yunwa ta tambaye shi sai
yaushe yace ai ya dawo kenan don haka zai zo su sha hira tace to sai yazo yace ta gaida mashi gwaggo
daga haka suka rabu,tana shiga gidan bayan ta shiga toilet ta fito ta nufi d'akin gwaggo tana zaune bata
dad'e da gama cin Abinci ba don ko plate d'in bata kaiga d'aukewa ba, zama Fatuu tay akan kujera ta
gaishe da ita tana murmushi ta amsa tay mata an dawo tace eh nan ta hau bata labarin Gaye cike da
mamaki gwaggon tace ai ba abu mamaki ba ne Allah yana shiryar da bawan shi a lokacin da yaso duk
mun munin abunda yake aikatawa da Allah yasa yana da rabon shiryuwa sai kaga ya bari shiyasa ba'a so
aita hantarar mutum ana aibata shi in yana aikata ba daidai ba an fi so aja shi a jiki da fad'a da nasiha in
da rabo sai kaga ya bari ya dawo kan daidai daga k'arshe ta hau yabon Haisam da Hajiya had'i da yi masu
Addu'oi Fatun na amsawa tace taje ta zubo Abinci ta amsa da to saida ta d'auki plate d'in da gwaggo tay
amfani ta fita.

Haisam ya fasa zuwa sakamakon d'aga bikin da zai zo da akai aka maida shi sai cikin farkon sabuwar
shekara wato bayan Christmas da new year kamar yadda ya sanar da Fatuu da suna waya tace mashi
Allah ya kaimu lokacin, a cikin lokacin su Fatuu sukai jarabawar kammala aji d'aya suka shiga aji biyu.
Hajiya zaune a Parlor ta tasa Saude dake zaune akan Carpet gaba tun bayan data sanar mata cewa
Officer ya mata Maganar yana son aurenta ta sunnar da kai ba tare da ta ce komae ba,

"Saude kin k'i cewa komae ko bakya son shi ne?" a hankali ta d'ago da alamun damuwa akan fuskar ta
tace "Hajiya ba wai ban son shi bane ni gaskiya nafi son in ci gaba da aiki na" d'an murmushi Hajiya tay
tace "amman Saudatu ai yin auren yafi ko kyata zama ne gashi da sauran yarintar ki ba wani tsufa kikai
ba ki dai duba kema in kika yi ai Kya fi samun natsuwa" d'an mommotsa baki ta shiga yi tana kikkafta
idanu Hajiya tace indai bata son shi ne karta ji komai ta fad'a mata ita tasan yadda zatai in kuma har tana
son shi to tafi son ta amince mashi suyi Auren kawae sai gani Hajiya tay ta fashe mata da kuka da
mamaki take kallonta tace to miye na kuka kuma ba tace in bata son shi ba ta fad'i sai ta kama kuka
kaman wata k'aramar yarinya girgiza kai ta fara yi cikin kukan take fad'in "Hajiya ba wai auren shi ke
banson yi ba nasan aure rufin asirin mace ne ni kawae har ga Allah ban son rabuwa da ke ne shiyasa tun
farko da yay man Maganar tun ba yanzu ba na nuna mashi yay hakuri kawae tunda nasan k'arshen ta
garinsu zai kai ni ya had'a ni da d'ayar matar shi" yar dariyar jin dad'i Hajiya tay tace "nima ba don dole
ba Saude ai bazan so rabuwa dake ba to amman hakan bazai sa in so kaina ba in hana ki yin abunda
yakamata ba kuma shi Officern ma yace ke a nan zai sama maki gida ya ajiye ki wannan sai ya daina
damun ki" cikin muryar kuka tace "to aikin fa zan ci gaba ko?" dariyar dai Hajiya ke yi ta lura dae da
gaske bata son barin gidan can taji tace "to ko ku zauna anan?" Ba shiri da sauri Saude ta kalleta don
bata tsammaci jin hakan ba Hajiya taci gaba "in dai kuna so tunda ga d'akuna nan biyu a kusa da na
Tukur sai kuyi amfani da su kawae" Saude tace "to Hajiya ba matsala kuwa?" tana dariya tace "Wace
matsala kuma ba wata matsala in dae wurin yayi maku ai sai kuyi zaman ku kici gaba da zama da Hajiya
kafin mai rabawa kuma ta raba" shiru Sauden tay don Maganar Hajiyar ta k'arshe ta kashe mata jiki
kuma dai abune da ya zama dole ko ba dad'e ko ba jima saidae fatan dacewar Ubangiji, ganin tayi shiru
yasa Hajiyar cewa shikenan ko tace mashi ya tura Daura Sauden ta jinjina mata kai had'i da sadda shi
k'asa alamar kunya Hajiya nata dariya tana fad'in to miye abun jin kunya.....

Ba yawa but manage it pls😔

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2042*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


.........A kwana a tashi ba wuya a wurin Allah har anyi New year su Fatuu sun dawo daga Hutu sun cigaba
da karatu, Ranar Monday misalin k'arfe biyu saura suka dawo daga Area d'in class an tashi zasu tafi
Hostel da yake yanzu Fatuu tana d'an yawan zama a Makarantar sai Weekend ta koma gida wani lokacin
ma a Makarantar suke weekend d'in kaman Asabar sai lahadi ta je gida, tafe suke kowanne yana rataye
da jakar shi Fauzy sai faman rangaji take ta d'aura kan ta saman shoulder d'in Fatuu can tace mata "Wai
Fauzy so kike ki sauke man kafad'a ne, duk kin bi kin sakar man nauyi" a marairaice Fauzy tace "wllh
Zarah wata irin yunwa nike ji baki ji ba gashi bak'in cikina in mun koma Hostel d'in ma dole sai mun dafa"
yar dariya Fatuu tay tace "to ba sai ki nemi emergency food ki fara ci ba" yamutsa fuska Fauzy tay tace
"irin yunwar da nike ji wannan bazasu rike ni ba kin san fa bamu yi break ba Saboda discussion d'in da
muka yi just d'an biscuit muka ci" Fatuu tace to ta d'aga mata kafad'a ko sun yi sauri suje suyi girkin, jin
haka yasa Fauzy d'agowa tana kallon Fatuu tace "Gaskia Zarah yakamata kiyi saurayi ko don irin haka
kinga da yanzu kawae sai kisa ai mana take away ba 6ata lokaci" Fatuu na dariya tace "to kema kiyi
saurayin mana" yar harararta tay tace ai ita ta gama yin saurayi har abada yanzu karatun ta ne
saurayinta in ta gama kuma aikinta ne zai zama mijinta Fatuu sai dariya take tace ai shikenan sai suyi ta
zama ba samarin tunda haka suka za6a Fauzy ta fara mata magiyar don Allah ta fara saurar su tunda ana
cewa ana sonta, d'an ta6e baki tay tace "kema ai ana cewa ana son kin ko don da wuya mu fita wani bai
mana Magana ba ji wannan da ya maki Magana a Mall kika k'i saurarar shi da gani d'an gayun mai kud'i
ne ga Motar shi had'add'a" yamutsa fuska tay tace "k'yale wad'annan masu Motocin duk mayaudara ne"
yar dariya Fatuu tay daidai lokacin suka iso wurin Admin Fauzy ta kai idonta daga gefen wurin parking
space d'in Malamai kaman daga sama Fatuu taji tace "Wow ji wata zazzafar Mota can kalar su Yaya
Haisam" da sauri Fatuu ta kalli direction d'in idanunta suka sauka akan Motar kalar army green da sai
faman d'aukar ido take da gani sabuwa ce kuma da gaske ta had'u ba k'arya d'an murmushi Fatuu tay ta
juya tana fad'in wato kalar su Ya Haisam ce kenan Fauzy tace "Eh mana ai ko wacce kalar mota da kalar
irin mutanen da ke hawanta waccan ko ban fad'a ba kinsan kalar shi ce inama ace shine tun da kince
wannan Month d'in zai zo" wani kallo Fatuu tay mata tace "da yake daga Funtua yake zamu gan shi
kwatsam ko" dariya sukai su duka suna niyyar wuce saitin Motar suka ji an latsa horn Fauzy ta d'an juya
ta kalli Motar sai kuma ta maida idon kan hanya tana fad'in "Zarah ko dae kin yi kasuwa ne" ta6e baki
kawae Fatuu tay suna k'ara taku aka k'ara yin horn d'in Fauzy tace Allah da gaske kodae dasu ake Fatun
tace da yake su kad'ai ne a wurin ko wannan Maganar tasa Fauzy yin tunanin k'ilan bada su ake ba suka
cigaba da tafiya wayar Fatuu suka ji ta fara ringing ta kai hannu cikin pocket d'in rigar uniform d'inta ta
fiddo ta tana kallon screen d'in taga sunan Ya Haisam ya bayyana da d'an mamaki tace "Fauzy da alama
Ya Haisam yaji kin yi Maganar shi" kai idonta Fauzy tay kan wayar da d'an mamaki take tambayar ta
shine ya kira Fatuu ta d'aga mata kai itama tana kokarin yin picking, bayan ta d'aga tun kafin tay magana
taji yace bata ji yana mata horn bane ba shiri ta kai idonta akan Motar da tsananin Al'ajabi take kallonta
yana fad'in hakan yay cutting kiran Fauzy da itama ta kalli in da Fatun ke kallo ta juya tace mata ya akai
ne with surprise written ol over her face ta fad'i mata abunda yace waro ido Fauzy tay with mouth agape
ta sake kallon Motar kafin tace "kenan shine??" Kai Fatuu ta d'aga mata alamar eh sosae itama Fauzyn
tay mamaki wani irin arashi ne haka ita tayi Maganar ta duk don ay raha sai gashi ta tabbata kama
hannun Fatun tay tace suje, a gaban driver side suka tsaya idonsu akan glass d'in duk da basu ganin shi
slowly glass d'in ya fara sauka k'asa har fuskar Haisam d'in ta bayyana, zuba mashi ido su kai su duka
yana sanye da riga turtle neck army green irin rigar nan mai kaman ta sanyi wadda ake nad'e wuyanta
tana da dogon hannu kuma dama har lokacin akwae yanayin sanyi sai bak'in Jeans har k'iba taga ya d'an
k'ara don fuskar shi ta k'ara cikowa ga sajen da ya bari sumar ta d'an k'ara yawa yanzu kwance luff da
k'yar Fauzy tay murmushin yak'e tace "Ya Haisam ina wuni an zo lafiya" jinjina mata kai yay kafin cikin
cool voice d'in shi ya amsa mata da Alhamdulillah ta k'ara ce mashi ya Aunty Fanan yace tana lafiya
juyawa tay ta kalli Fatuu jin bata ce komae ganin ta zuba ma Haisam d'in ido yasa tay d'an murmushi ta
kai hannu tace ta kawo jakar bari taje ta yi masu Abincin bayan ta amsa ta juya tace ma Haisam sai
anjima ya d'aga mata kai, sam Fatuu ta kasa bud'e baki ta tanka mashi Saboda mamaki don ko jiya sunyi
waya fa amman bai ce mata yau zai zo ba ga wani irin bugu da k'irjinta ke yi tunda tay tozali dashi, ganin
irin kallon da yake mata ne yasa tay k'arfin halin cewa "an zo lafiya" still bin ta da ido yay dama ya jingina
kanshi da headrest kaman bazai ce komai ba can taji yace ta shigo cikin Motar jiki a sa6ule ta zagaya
d'ayan side d'in ta bud'e kopar gaba ta shiga har saida ta d'an lumshe ido bayan ta rufe kopar ta juya
suka had'a ido ta sake gaida shi had'i da yi mashi an zo lpy sai lokacin ya amsa mata da lafiya suka d'an yi
shiru tana kallon glass d'in gaba shi kuma yanata kallonta ta cikin mirror can ta juya ta kalle shi shima ya
juyo suka had'a ido tace "ashe yau zaka zo amman baka fad'a man ba kuma ko jiya mun yi waya" d'an
murmushi yay calmly yace "komae sai an fad'a ne?" d'an tura baki tay ta sadda kan ta k'asa taji ya k'ara
cewa ko yayi laifi ne da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a ba tare data d'ago ba suka d'an yi shiru can
ta ji yace mata ya School sai lokacin ta d'ago tace mashi lpy Lou ta tambaye shi Aunty Fanan yace tana
Lagos shima daga can yake Fatun ta d'aga kai suka k'ara yin shiru can ya kai hannu yana kokarin tashin
motar ta juya ta kalle shi batare da ya kalleta ba taji yace su je a samo masu Abinci bata ce komae ba ta
d'an juyar da kanta gefe had'i da yin murmushi ta ayyana Ya Haisam ba dae sanin yakamata ba, saida
suka fita daga cikin Makarantar ta tuno da girkin da Fauzy zata masu ta ayyana yakamata ta kirata tace
ta bashshi dama wayar na akan cinyoyinta ta d'auka ta fara kiranta bugu d'aya ta d'auka tace "love birds
ya ana nan anata soyewa?" d'an murmushi Fatuu tay bata ce mata komae ba gudun kar tay wata
Maganar yasa ta tambayeta ta d'aura Abincin ne tace a'a biscuit da Madara ta fara sha don bata iya
jurewa har sai ta gama amman gashi yanzu zata d'auran Fatun tace mata ta bar shi gashi za'a siyo wata
k'arar murna Fauzy tay tace "Allah maji kan bawa muma ga saurayin zai mana take away" yar dariya
kawae Fatuu tay Fauzyn tace "in fad'a maki abunda nike so" tace mata eh, harda su gyara murya ta fara
zayyano mata shawarma,pizza,farfesun yan ciki, sakwara......, saida ta fad'i abu ya kai goma cike da
mugunta Fatuu tasa speaker tace mata bata ji abubuwan da ta lissafa tana so ba muryar na yankewa ta
sake fad'i mata ba tare da ta sani ba ta hau sake lissafo mata Fatuu nata guntse dariya ta d'an waiga ta
kalli Haisam shima murmushi ne akan face d'in shi bayan ta gama lissafawa Fatuu tace mata duk ya
zatayi dasu tace kara'i zatay yaushe rabon da su ci kayan dad'i da yawa saidae suga ana kawo ma masu
samari to suma tunda Ya Haisam d'in su yazo ai dole su ci dad'i, sosae Fatuu ke dariya jin irin dariyar da
taken ne yasa Fauzy tace badai yana ji ba cikin dariya tace a'a sai ta dawo ta kashe, bayan sun je Eatery
d'in duk abunda Fauzy ta fad'a saida yasa aka basu Fatuu nata ce mashi wasa fa itama take saidae yay
murmushi kawai haka akai masu ledojin takeaways suka taho a bakin gate d'in Makarantar ya tsaya don
an riga an tashi ba'a bari a shiga, juyawa tay ta kalle shi da d'an murmushi tay mashi godiya yay shiru har
zata juya taji yace bazata koma gida ba ta rink'a zuwa ko tafi son ta zauna a school tana kallon shi tace
"to in koman ne?" guntun murmushi yay jin tayi mashi tambaya cikin tambaya yace in tana so ya rink'a
kawo ta kafin ya koma tace "to in kai mata Abincin sai in dawo?" shiru ya d'an yi kafin yace taje zai zo
bayan Magrib ya d'auketa tace to daga haka ta fita daga Motar ta rufe ta bud'e back seat ta tattaro
ledojin ta nufi cikin gate d'in tana yi tana d'an waiwayen shi duk yana kallonta ya juya Motar ya tafi,
Fauzy baje saman gado tana latsa waya Fatun ta shigo da yar sallama suka had'a ido da sauri ta yunk'ura
ta tashi zaune tana fad'in welcome ta Ya Haisam, a gabanta Fatuu ta aje dukkan ledojin tace "ga dukkan
sak'on ki nan sai kita kara'in" waro ido Fauzy tay tabi ledojin da kallo kafin da mamaki ta kalli Fatuu tace
"Wai badai fad'a mashi kikae ba?" zama Fatuu tay gefen gadon tana cire Hijab d'inta tace "kedai ba Kin
fad'i abubuwan da kike so ba kuma an kawo maki kawae kici gaba da shagali" wani kallon rashin yarda
take ma Fatun ba kamar data ga tana yin dariya magiya ta shiga yi mata kan ta fad'i mata ya akai aka siyo
wannan uban kayan daga baya Fatun ta fad'i mata shi yaji da kunnanshi tace kenan speaker tasa ta tay
shiru tanata mata dariya aikuwa tay kukan kura zata jawo ta Fatuu ta mik'e tanata kyalkyatar dariya
Fauzyn na Fad'in "U'r wicked wllh yanzu don rashin Mutunci shine kika sa man speaker na saki baki inata
maganganu don Allah ba sai ya d'auke ni acici ba kuma mai son abun duniya" ganin kaman ranta ya 6aci
yasa Fatun ta koma gefen ta tana bata hak'uri tace ai shima yasan wasa take kar ta damu kawai suyi
shagalin su aikuwa saida ta jawota ta d'uma mata dundu tana niyyar k'ara wani Fatuu ta k'wace tana
fad'in daga abun arzik'i in dai ta k'ara bugunta to bazata ci komai ba a ciki Fauzy ta harareta tace "kin ma
isa ki zubda man Mutunci kuma kice bazan ci komae ba" ta k'arasa Maganar tana fiddo takeaways d'in
tana yi tana jinjina kai tana fad'in Fatuu ta gama da ita ganin duk abunda ta fad'a an siyo shi, saida suka
wanke hannuwan su a jikin windown d'akin nasu dake a saman bene sannan suka zauna zaman ci Fauzy
tana ci tana saka wa Haisam Albarka Fatuu nata dariya anan take sanar da ita zancen tafiyar ta anjima ta
6ata rai tace "Ya Haisam ya kuma zai mun haka don Allah na samu yanzu kina zama zai dawo mun da
kad'aici" ita dae Fatuu dariya kawai take can Fauzy tace "na gano shi wato bai iya jure rashin ki kusa da
shi shine zai d'auke ki yace wani zai rink'a kawo ki ke miyasa bazaki ce kin fi son zama nan ba don Allah"
ta k'arasa a marairaice kafin Fatun tace wani abu ta sake cewa "koda yake saida hakan zaki janyo mana
zuciyar shi don na lura bata jawuwa cikin sauk'i amman gaskiya ban ji dad'i ba" Fatun ta hau ce mata
sorry, duk cin su basu iya cinye rabin Abincin ba don wasu abun ma Fatun bata ci ba tace ta bar ma
Fauzyn ta rage loneliness da su. Zuwa bayan Magrib ta gama shirya kayanta a trolley d'inta tayi wanka ta
shirya cikin straight skirt da riga na atampa sun mata k'yam ta kashe d'auri Fauzy sai yabonta take dama
ba tun yanzu ba take fad'in bata ga wadda straight skirt ke ma kyau ba irin Fatuu, yar light make up tayi
da ba zata ma yi ba Fauzy ta matsa mata ta d'an shafa humra a jikinta bayan ta gama ta zauna gefen
gado suna d'an yin fira da Fauzy har tana fad'in yau dole ta nemo mai tayata kwana don yanzu ta riga ta
saba kwana ba ita kad'ai ba Fatuu dai nata mata dariya ganin yadda take Maganar tana tura baki ita ala
dole an mata laifi, suna zaunen saiga kiran shi ya sanar da ita yana a bakin gate tace to ta yafa gyalenta a
kafad'a tare da Fauzy suka fito tana ruk'e da trolley d'in suka sauka k'asan benen, suna tunkarar gate
Fauzy taja ta tsaya ta mik'a mata trolley d'in Fatuu tace "girlfriend bazaki idasa raka ni ba" yar harararta
tay tace "in dawo ni da wa kuma ko bama haka ba Allah ban zuwa kin gama zubda man Mutunci" dariya
Fatuu tay tace "ki share kawae tunda buk'ata ta biya anci dad'i har an ture" kafewa tay kan bafa ta
k'arasawa gate d'in dole Fatun ta amshi trolley d'in tayi mata saida safe sai sun had'u gobe daga haka ta
tafi itama Fauzy har ta juya sai kuma ta sake juyowa ta k'wala ma Fatuu kira ta tsaya cikin d'an d'aga
murya tace "ki tabbatar kafin ya koma kin ida sace zuciyar ta yarda har ya kasa sukuni sai ya fad'i maki
yana son ki don duk wannan kame kamen mun gano shi" dariya sosae Fatuu ke yi ta d'aga mata hannu
kafin ta juya ta tafi itama Fauzy ta koma Hostel, tunda ta kusa isowa bakin gate d'in ya fara hangota
sakamakon hasken fitilun dake a gefe da gefen hanyar data zo bakin gate saida ta tsaya suka gaisa da
baba mai gadi da yake kusan ba wanda bai santa ba a Makarantar tun daga kan d'alibai har zuwa
Malamai sosae take da farin jini uwa uba kuma tana da abubuwan dake sa mutum ya rink'a burge
mutane kaman kokari ga kyau kuma tana da kirki duk da bata d'aukar nonsense yanzu ta sauke ma
mutum kwandon bala'e, tunda ta nufo Motar ya zuba mata idanun shi da ya d'an lumshe su yana mata
kallon k'urulla har ta k'arasa ta bud'e back door ta saka d'an trolley d'in kafin ta rufe ta bud'e kopar
gaban ta shiga yanzu ma dae k'ananan kayan ne a jikinshi bayan ta zauna ta jawo kopar ta rufe da
murmushi ta juya suka had'a ido ta gaishe da shi ya jinjina mata kai daga haka ya juya Motar suka tafi,
tsit sukai ba wanda ya k'ara tankawa yanata driving ita kuma tana kallon gefen hanya a bakin wani Cafe
ya tsaya yace mata yana zuwa ta d'aga mashi kai ya fita tanata kallon shi lokacin da ya zagayo har ya
shige cikin Cafe d'in ta d'an lumshe ido tana murmushi bai d'auki lokaci sosae ba ya fito hannunshi ruk'e
da ledoji guda biyu masu d'auke da tambarin wurin ya bud'e baya ta can side d'in driver ya saka sannan
ya koma driver seat d'in yaja suka tafi, saida ya k'ara tsayawa wurin masu Fruit saidae bai fita ba ya
sauke glass ya fad'i abubuwan da yake so aka cika manyan ledoji guda biyu yace ma mai fruit d'in ya saka
mashi a baya bayan ya biya shi suka tafi, lokacin da suka k'araso kopar gidan su Fatuu anata kiran sallar
isha ta kalle shi da murmushi tayi mashi godiya bai amsa ba sai ya jinjina kai had'i da lumshe ido har zata
bud'e kopar taji voice d'in shi yana fad'in da safe zai zo ya kaita school ta kalleshi tace to ya k'ara ce mata
ta d'auki abun baya, kowanne leda guda ta d'auka ta fruit d'in da ta Eatery d'in ta yi mashi godiya suka
had'a ido ta mirror kasa d'auke idon tay tana ta kikkafta su can taga yay d'an murmushi duk sai kunya ta
kamata ta janye kan ta ta rufe Motar saida ta fidda kayan can gefe sannan yaja Motar Amadu na ganinta
ya fito ya zo gabanta yana washe baki yace "wato ya kasa hak'uri saida ya d'aukko ki kenan" wani kallo
tay mashi had'i da tura baki ya kai hannu ya d'auki ledojin yana fad'in Juliet ta Romeo suka nufi gidan,
d'akin gwaggo suka nufa suna shiga tana sallame salla ta d'aga kai tana kallon su tana ganin Fatuu tay
murmushi Amadu yace "ga autar ki nan Romeo ya kasa hak'uri saida ya d'aukko ta" tur6une Fuska tay
tace "kai Kawu Amadu miye haka" dariya yaci gaba da yi yana fad'in tuba yake kar a hana shi tsaraba
yasan kayan dad'i ne, zama Fatuu tay kan kujera ta gaida gwaggo dake ta fara'a ta amsa mata tace an
dawo Fatun tace eh Ya Haisam ne ya d'aukko ta yace zai rink'a kaita kafin ya koma gwaggon ta d'aga
mata kai Amadu sai faman k'umshe dariya yake can ya juya yace bari ya d'aukko plate a bashi kason shi
gwaggo ta d'an ta6e baki tana girgiza kai koda ya dawo da kan shi ya d'ibi komai harda fruit d'in ya mik'e
yana fad'in Allah ya barta da Romeo suyi ta cin dad'i gwaggo ta kai hannu zata make shi ya nufi kopa
yana dariya ya fuce gwaggo ta maida idonta akan Fatun tace "ai d'azun bayan ya iso ya shigo nan mun
gaisa anan na fad'i mashi kina can Makarantar ashe zuwa yay" d'an murmushi Fatuu tay ta d'aga mata
kai itama gwaggo murmushin take duk sai Fatun ta tsargu ta mik'e tace bari ta kai kayanta d'aki ta nufi
kopar fita gwaggo ta bita da ido, bayan ta koma d'akinta saida ta cire kayan jikinta tasa na bacci bayan ta
fito ta nufi kitchen ta d'aukko plates sannan ta dawo d'akin gwaggo ta zuba masu abubuwan suka fara ci
tare suna yar hira har tana tambayarta Fauzy anan ta bata labarin abunda ya faru d'azun gwaggon tanata
dariya tace amman bata kyauta ba Fatuu tace to ba gashi tayi kara'in ba, bayan sun gama ta fidda kayan
wanda suka rage ta kai fridge ta zauna yin kallo dama ba salla take ba shiyasa bata yi sallar isha'i ba,
Washe gari talata da safe Haisam yazo ya d'auketa kamar yadda yace yaci gaba da kaitan, Ranar Alhamis
bayan sallar la'asar Haisam na zaune a Parlor tare da Abbas da ya kawo mashi dress code na Dinner d'in
da za'ayi gobe Friday ta Abokin su Prince Obinna Eze ganin harda na mata lokacin da ya bud'e kayan yasa
Haisam d'in cewa shida wa zai je da zai kawo mashi rigan mata kuma yasan Fanan bata nan dariya Abbas
yay yace to haka aka tsara daya je amso kayan aka bashi su haka kowa da matar shi zai je ko budurwar
shi don haka dole ya nemi wadda zai je da ita Haisam d'in na kishingide jikinshi sanye da jallabiya tun
bayan da ya d'aukko Fatuu ya dawo ya watsa ruwa ya kwanta bacci saida akai la'asar ya farka ana gama
sallar Abbas d'in yazo kawo mashi kayan, k'arshe ce ma Abbas d'in yay shi kadae zai je in yaje a koro shi
Abbas na dariya yace "haba H,Zakee kaifa kana cikin manyan Abokan shi ya zaka kwafsa bayan ga yadda
aka tsara kawai ka samu wata kuje tare badai na d'an lokaci bane" wani kallo mai kaman harara yake bin
shi dashi jin Maganar da yay wai ya samu wata suna haka aka turo kopar duk suka kai idanuwan su Fatuu
ce ta shigo tana sanye da riga da skirt na material kanta ba dankwali sai gyalen kayan data d'aura
asaman kan shima baida wani girma sosae gashi sai zamewa yake gashin ta na fitowa tana rungume da
k'aton littafi hard cover suna had'a ido ta sakar masu murmushi Abbas yace ta shigo mana ta nufi cikin
parlon ta tsaya tana ta murmushi ta rasa ina zata zauna Haisam na kan L-shape Abbas na kan armchair
guda Abbas ne yace ta zauna mana ga wuri nan yay Maganar yana nuna mata daga gaban inda Haisam
yake zaune saida ta kalleshi suka had'a ido fuskar shi a sake ta nufi wurin ta zauna ta gaida shi ya jinjina
mata kai ta kalli Abbas ma ta gaishe da shi ya amsa yana yar dariya yace "Mom Zarah ko ince Nurse
Zarah" gumtse baki tay bata ce komae ba can taji ya sake cewa "Mom Zarah wannan dressing haka
yakamata a rink'a sa babban mayafi" wani iri taji kunya ta kamata ta sadda kan ta k'asa ganin haka yasa
shi cewa "am sorry gudun yin laifi yasa nayi maki Magana tunda an zama d'aya" d'agowa tay tana d'an
murmushi tace "ba komae na fahimta yanzu ma don gwaggo bata ganni bane da bazata bari in fito da
k'aramin gyale ba" jinjina kai yay yace "to yakamata ana kiyayewar" tace "in sha Allah dama don naga
nan zan zo ne kuma inata sauri don kar ya fita Assignment ne na kasa nike so a nuna man" kai ya d'aga
alamar ya fahimta ta juya ta kalli Haisam tace don Allah ya duba mata kafin yace wani abu Abbas yace
"Mom Zarah ya zaki kawo ma wanda computer kawae ya sani Assignment d'in ku yan Asibiti" tana dariya
tace ai tasan zai iya Abbas d'in yace in yayi browsing ko tace ko bai yi ba yace ta kawo ya ga Assignment
d'in ta mik'e ta kai mashi ya amsa yana dubawa yana dariya yace wannan nashi ne bana Zakee ba ita dae
dariya kawae take can ta mik'e tace bari ta kawo mashi lemu to yaji dad'in yi mata yace yauwa kaman
tasan yana buk'ata H,zakee bai iya tarbar bak'o ba ta mik'e tana dariya ta nufi fridge d'in idon Haisam a
kanta Abbas na d'an satar kallonshi yana guntse dariya slowly ya maida idon kan Abbas suka had'a ido
ganin dariyar da yake yasa shi d'an ta6e baki ya maida idon shi kan Tv, bayan ta d'aukko lemun da glass
cup ta tsiyaya ta ba Abbas ya amsa had'i da yi mata godiya daga inda take ta kalli Haisam tace zai sha
shiru bai ce komai ba sai bin ta da ido da yake Abbas ne yace ta kai mashi kawai irinsu ba'a jiran sai sun
yi magana tana dariya ta wuce saida ta janyo c-table ta aje a gabanshi sannan ta d'aura lemun ta juya ta
je ta d'aukko wani cup d'in ta dawo ta duk'a tana tsiyaya mashi yau ma dae kaman rannan idonshi suka
sauka akan boobs d'inta saidae yau sam ya kasa kauda idon har ta d'ago don ta mik'a mashi bai sani ba
ta kama shi farko bata fahimci inda yake kallon ba har saida ta sadda kanta taga saman boobs d'in ya fito
sosae duk sai taji wani iri ta mik'e tsaye hakan ya maido shi cikin hankalin shi ya d'aga ido ya kalleta tay
mashi nuni da lemun da hannu ya d'an jinjina kai had'i da furta thanks jiki a mace ta koma inda ta taso ta
zauna duk sai bata ji dad'i ba tasan da tasa babban mayafi ta rufe jikinta ko hijab da hakan bata faru ba,
bayan Abbas ya gama shan lemun yace tazo taga yadda Assignment d'in yake saida ta gyara gyalenta
sosae sannan ta nufi inda yake ta zauna akan d'ayar armchair d'in ya d'aura book d'in akan hannun
kujerar ya fara nuna mata ba'a dau wani lokaci mai tsawo ba ta gane sosae tay mashi godiya had'i da
mik'ewa tay masu sallama ta tafi, tana fita Abbas ya kalli Haisam yace "mi zai hana kaje da Mom Zarah
kawai ma?" Kallo kawae Haisam d'in ya bi shi da shi Abbas yaci gaba "nasan bazata k'i zuwa ba kawae ka
fad'i mata zata raka ka dinner party sai ka bata rigar nasan dad'i ma zata ji kuma hakan yafi da a maida
masu rigan" shiru yay da alama nazari yake. Washe gari Juma'a bayan ya d'aukko ta daga school lokacin
da suka k'araso kopar gidan kafin ta fita yay mata zancen Dinner d'in yace in ba damuwa yana so ta raka
shi tace to yace amman ta fara tambaya nan ma to d'in tace ya kai hannu baya ya d'aukko jakkar da rigar
take ya bata yace wannan zata saka amman ta fara dubawa in bazata yi ba sai a canzo before time d'in,
bayan ta amshi jakar ta kai hannu ta fiddo rigar wadda doguwar riga ce Red colour mai bud'ewa daga
k'asa hannun Net gareta d'an k'arami haka ma k'asan rigar inda ya bude hawa biyu ne yadin rigar da
kuma irin net din hannun sai wuyan ta ma wani irin design akai mashi ba k'arya dae rigar ta had'u iya
had'uwa Fatuu na ganinta ta saki k'ayataccen murmushi don harma ta hango ta cikinta, bayan ta gama
dubawa ta kalli Haisam tace lafiya lou zata yi shiru ya d'anyi yana kallon ta yace amman kaman zatai
tighting nata yaga tayi k'arama tace mashi a'a lafiya lou ai roba ce zatayi ya k'ara cewa tsawon ma kaman
yayi mata yawa shima tace ai dogon takalma zata sa lafiya lou duk da haka saida yace in ta shiga ta
gwada in bata yi ba ta kira shi sai a canzo tace to daga haka ta fita, tana shiga gidan cike da zumudi ta
wuce d'akinta dama tasan gwaggo bata nan tana wurin aiki, gado ta nufa ta aje bag d'inta ta fara cire
uniform d'in hannuwan ta har kerma suke ta k'agara taga yadda Rigar zata mata, bayan ta cire kayan ta
fara kokarin saka rigar sai dae da k'yar ta shigeta don ta kamata sosae don ma roba ce yasa ta shiga,
tsaye tay a gaban mirror tana kallon kanta hannunta rufe da baki ganin yadda shape d'inta yay bala'en
fitowa tana jin tunda take bata ta6a saka kayan da suka fiddo mata da dirinta haka ba har jujjuyawa take
tana k'are ma kanta kallo tunanin anya yakamata ta je da ita wurin ta fara yi kodae ta kira shi tace a
canzo d'in haka taci gaba da yin wasi wasi saidae ita kanta yadda Rigar tay mata ya burgeta can ta yanke
kawae ta tafi da ita komawa tay gefen gado ta d'auki wayarta ta kira gwaggo ta sanar mata zancen zuwa
dinner d'in tace to Allah ya kaimu. Da daddare tana cikin yin shirin tafiya don ya sanar mata sai k'arfe 10
za'a fara gwaggo ta dawo makeup tay sosae ta saka rigar tunanin wane kalar takalma zata saka ta fara
can wata zuciyar ta raya mata ta kira shi taji su wane kalar kaya zasu saka sai tasa irin takalmin da sauri
ta juya ta d'auki wayarta tay sending mashi kira bayan ya d'aga ta gaishe dashi ya tambayi ta shirya ne
cikin yar in ina tace eh tana son taji shi wane kalar kaya zai saka yace mata Ash suit ne da red tie tace to
ta katse kiran ash d'in takalma masu tsini ta d'aukko da hadaddar purse d'in su tasa d'an kunne mai yar
ziririyar sarka silver da agogon su ta jiguno dai ba k'arya, bayan ta gama ta fara tunanin gyalen da zata
saka sai kuma tay tunanin tabbas ta fita da gyale gwaggo bazata barta ta fita da rigar ba haka ma Ya
Haisam d'in tasan in ya gani ba lalle ya bari ba dubara ce ta fad'o mata ta yanke sa ash d'in jallabiyarta in
suka je sai ta ajeta a Mota sosae hakan yay mata ta d'aukko rigar dama a goge take ta saka ta zuge zip
d'in gaban yadda ta cikin zata fito tay rolling veil d'in rigar ko a hakan ma ba k'aramin had'uwa tay ba sai
faman sakin murmushi take tana haka goma saura yan mintuna ya kira yace in ta gama yana waje tace
to, bayan ta fito ta nufi d'akin gwaggo tayi mata sallama lokacin har ta kwanta amman idonta biyu ta
tashi zaune tana kallon Fatun da murmushi ta hau yaba Kwalliyar tana fad'in had'in yayi kyau Fatun ta
sanar mata shi ya kawo mata rigar ita za'a saka ta d'aga mata kai tace taje kar yay ta jira ta ce to ta juya
tana fad'in sai sun dawo, a Ash d'in Mota zasu tafi tana zuwa ta bud'e front seat ta shiga bayan ta rufe
kopar ta juya ta k'ara gaida shi a hankali ya amsa dama Motar a kunne take ya ja suka nufi Paramount
Event Center inda za'ai dinner d'in.........
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2043*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

........ Lokacin da suka iso harabar Event Center d'in shak'e take da jigunannun motoci masu numfashi kai
ko ba'a fad'a ba kasan wani wanda ya kai ne zai yi aure, bayan ya parker Motar ya kai hannu ya d'auki
phone d'in shi dake ajiye gefe bayan ya bud'e ya shiga call log ya fara kokarin kiran Abbas ringing biyu ya
d'aga kafin yace wani abu Abbas ya riga shi tambayar sun isa wurin ne yace mashi eh yace Ok shima
gashi nan ya kusa shigowa jin haka yasa yay cutting kiran ya maida wayar inda ya d'auke ta ya d'ago ya
kalli Fatuu suka had'a ido da yake wurin fayau yake kai kace da rana ne don ba abunda ba'a gani hakan
yasa har cikin Motar akwae d'an haske da za'a iya ganin mutum duk da glass d'in blacktinted ne amman
widescreen d'in gaban bai da duhu sosae kamar na k'opopin, maida kan shi yay jikin headrest itama ta
juya tana kallon abubuwan dake faruwa a wajen cikin ranta tana jinjina irin Motocin Alfarmar da aka tara
ga Mutane ne sai kai da kawowa suke, bada jimawa ba Abbas ya shigo akan idon Haisam bayan ya
parker Motar ya bud'e ya fito yana lallatsa wayar shi ganin hakan yasa Haisam ce ma Fatuu yana zuwa ta
d'aga mashi kai ya d'auki wayar shi ya bud'e ya fita, tunkarar Abbas dake k'ok'arin kiran wayarshi yay
yana ganinshi yay dariya suka ba juna hannu ya d'an kalli gefen shi ganin bai ga Fatuu ba yace "ina Zarah
badai kai kad'ai d'in ka taho ba?" Fuskar shi a sake yai mashi nuni da tana cikin Mota ya jinjina kai shima
ya tambaye shi ina Feenah bai bashi amsa ba sai dariya kawae yake can ya juya ya bud'e Motar ya d'an
duk'ar da kan shi da alama Magana yay ya fiddo ya rufe aka bud'e front door d'in d'ayan side d'in ta fito
tana sanye da irin rigar Fatuu tunda ta fito Haisam ya tsuke fuska yana mata wani kallo ganin ba Feenah
bace wata ce daban yar doguwa ce don zata fi Fatuu tsawo saidae bata da jiki amman ba za'a kirata
siririya ba kuma fara ce duk da da gani an k'ara dana kanti ko daga yanayin hasken fuskarta zaka gane,
rigar ta amshe ta da yake roba ce amman fa da gani wurin hips d'in anyi ciko don bai tafi sosae ba kamar
na gaske, tana k'arasowa Haisam ya kauda idon shi ba kamar ganin yadda ta kafe shi da ido Abbas ne
yace mata ga Aminin shi Haisam su gaisa cike da kwanare da kisisina cikin mak'e murya ta gaishe dashi
k'asa k'asa ya amsa ba tare da ya sake kallonta ba suna haka Motar ango ta iso wata rantsattsar jeep mai
bugun zuciya tasha adon su balloons ga security gefe da gefe Motocin suka ja layi suka tsaya ba tare da
wani ya fito ba Abbas ne yace ma Haisam ya kamata Zarah ta fito tunda sun iso yanzu za'a shiga ya d'aga
mashi kai kawae dama wayar shi na ruk'e a hannun shi ya kira ta bayan tayi picking yace ta fito da yake
yasan tana ganin su tunda Motar a saitin su take, saida ta cire jallabiyar ta aje anan cikin Motar ta gyara
rolling d'in gyalen ta yadda daga bayan kan ta ya d'aga sosae Saboda gashin ta dake a fake ta kai hannu
ta bud'e Motar ta fito bayan ta rufe ta tunkare su tana tafiya slowly hips d'inta na wani sama da kasa
sakamakon takalmanta dake da tsini sosae kai kace da gayya take yin tafiyar saidae ita tsakaninta da
Allah lafiya lou take yin tafiyarta tunda ta fito Abbas ya kafeta da ido bako k'yaftawa haka budurwar
tashi, kallon Abbas Haisam yay da niyyar yi mashi magana ganin gaba d'aya attention d'in shi ya tafi kan
wani abu yasa shi d'an juyawa ya kalli direction d'in da idanun Abbas d'in suke idanun shi suka sauka
akan Fatuu da take nufo su har bai san ya hadiyi abu ba lips d'in shi suka d'an motsa kad'an wani iri yaji
ganinta haka sam bai yi tunanin zata cire jallabiyar bane ganin ta hau da dressing d'in sosae yama kasa
gane dad'in ganinta haka yaji ko kuwa akasin hakan kawai dae abunda ya sani shine sam bai dace a
ganta a haka ba, tana murmushi ta k'araso ta tsaya gefen Haisam tana kallon Abbas da shima yake d'an
murmushi shi kan shi bai so ganin ta haka ba har saida yay mamakin yadda akai Haisam ya fito da ita a
haka, rigar ta kamata sosae shape d'inta ya fita over ita kanta budurwar Abbas d'in duk sai ta raina kanta
sai faman kikkafta ido take tana had'iyar abu bakinta na d'an motsawa ta kafe Fatuu da ido tana mata
kallon k'urulla Abbas ne ya katse shirun da fad'in "Mom Zarah an yo rakiya kenan" tana murmushi ta
d'aga mashi kai kafin ta gaishe dashi ya amsa ta kalli budurwar Abbas d'in suka had'a ido ganinta da irin
kayan jikinta yasa tay tunanin tare take da Abbas tana murmushi tace mata sannu ta d'an yi murmushin
itama amman na yak'e tace yauwa had'i da d'an juyar da kai, d'aga kai Fatuu tayi ta kalli Haisam da
shima kallonta kawai yake bazaka gane yanayin fuskar shi ba d'an murmushi tay mashi bai ce komai ba
kuma bai maida mata martanin murmushin ba suna haka aka sanar amarya da ango zasu fito a shirya
entrance Abbas yace su je kaman Haisam d'in bazai je ba saida Abbas ya k'ara cewa su tafi sannan slowly
ya kalli Fatuu yay mata alamar suje tana a gefen shi suka tunkari wurin, cikin shiga ta Alfarma da ni kaina
bazan iya k'iyasta adadin dukiyar dake a jikinsu ba Bride and Groom suka fito suna ruk'e da hannun juna
Amaryar na sanye da rantsattsiyar farar wedding gown da ke sakin wani irin k'yalli mai d'aukar ido da
alama dai stones d'in da akai adon rigar kilan diamond ne dama tun daga kunnanta wuyanta har
hannunta duk diamond ne sannan aka bi da kuma irin sark'ar su da suke sawa ta duwatsu mai kaman
murjani har a saman kanta tayi kyau ba k'arya dama gasu jajur da su shima Ango Prince Obinna fararen
suit ne a jikinshi sai bak'in tie da bak'ak'en takalma shima kunnuwan shi na manne da barimar diamond
haka agogon hannunshi ma, bayan duk an fito an jera layi abun gwanin burgewa ashe ba iya shigar su
Fatuu bace wasu bak'ak'e suka sa Matan na sanye da fararen gown wasu marron suit Matan na sanye da
gown golden brown da sauran shiga kala kala sosae suka tsaru duk masu shiga iri d'aya sun jera wuri
guda ga makad'an su na gargajiya sunyi shigar su suna irin kid'an su suna ma ango da Amaryar shi kirari
bayan komae ya tsaru yadda ake so aka nufi cikin Hall d'in, Wow wow just wow don bansan ma ta ya zan
fara bayyana tsaruwar wurin ba don duk iya hasashen mai hasashe ba zai iya k'iyasta ainihin nawa aka
kashe ba wurin tsara wurin don wurin ya fitinu abun ba'a Magana suna shiga duk na ciki aka mik'e tsaye
police bands suka d'auka busar sarewa kake ji ta ko ina ga kid'an su da ke sa mutum ya tausaya ba tare
da yama sani ba wuri fa ya kacame da kid'e kid'e ga yan rawar gargajiya ma na nasu jikin Fatuu har
tsuma yake sai faman sakin murmushi take ji take ina ma anzo da Fauzy tazo taga sha'ani da ya amsa
sunan sha'ani, saida suka je suka zauna a high table sannan sauran Mutane duk aka zazzauna aka
dakatar da kide kiden don fara gabatar da abunda aka zo yi, bayan MC yay welcoming kowa wani abokin
ango ma yazo tare da budurwar shi ce ko matar shi oho yay ma kowa sannu da zuwa da gabatar da
abunda aka taru yi bayan ya gama babban Abokin Ango da Amarya inyamurai suka fito suka bada tarihin
Ango da Amarya bayan suma sun gama aka buk'aci Bride and Groom suka fito don taka rawa zo kaga
yadda suke cashewa abunsu cike da nuna ma juna kauna abun sai yama ba Fatuu kunya sai faman
sunnar da kai take yayin da ake ta masu ruwan lik'i masu lik'a dollars nayi masu lik'a Naira nayi manyan
mutane masu sanye da shigar su ta gargajiya ta ko ina sai tasowa suke suna lik'i daga baya aka bukaci
kowa ya koma Abokan Ango da Amarya inyamurai suka fito aka fara casu mai sunan casu Fatuu sai
dariya take haka ma su Abbas ji take kaman tay tsuntsuwa ta ganta a cikin filin itama tayi rawar saidae
ba dama, bayan duk an gama abubuwan da ya dangance su aka dawo kan hausawa shi Angon da kanshi
ya fara bayanin irin alak'ar shi da mutanen Katsina da irin karar da suka yi masu tun bayan da suka tsinci
kan su a cikin garin ba tare da nuna k'yama ko tsangwama ba Saboda bambancin Addini ya tabbatar ma
Mutane da musulunci addinin zaman lafiya ne sa6anin wasun su da suke masu kallon yan ta'adda yace
shi shaida ne game da Mutuncin hausawa don sun nuna masu k'auna ta yadda har sun zama daga cikin
Family d'in shi a k'arshe yay godiya ga musulman da suka zo wurin ya nuna hakan ba k'aramin abu ne a
wurin shi ba yay fatan Allah ya k'ara had'a kan su suci gaba da zama da juna da Amana yay Addu'ar
samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata ga K'asar mu Nigeria sannan yay godiya ga
Governor d'in Katsina da Sarakunan D'aura da Katsina da sauran manyan mutane Mutane nata amsawa
da Ameen bayan ya gama itama Amaryar aka bata tayi godiyar bayan duk sun gama aka buk'aci babban
Abokin Ango bahaushe da ya fito ya bada tarihin Ango na nan garin irin alak'ar shi da mutane da sauran
su MC ya tambayi angon waye zai fito ya nuna mashi Haisam duk ido ya dawo kan shi a nutse ya mik'e
ganin zai fito shi kadae MC yace the equation isn't balanced nan take duk aka gane abunda yake nufi da
yake d'an barkwanci ne duk aka sa dariya dakatawa Haisam yay ba wai fita da Fatun ne bazai yi ba sam
shigar ta bata dace da wurin ba a matsayinta na Musulma Abbas ne ya kalli Fatuu yace ta tashi suje
ganin Haisam d'in bai ce komae ba yasa ta mik'e ta fito suka jera wohoho all eyes on them ita kanta
Fatuu duk sai ta ji ta takura, tunda suka fara saukkowa daga kan steps d'in MC ya saki baki galala kamar
rainon sakarai yana bin su da kallo tun daga sama har k'asa, lokacin da suka k'araso gaban shi suka tsaya
fuskar Haisam dai ba wata walwala don duk ji yake wurin ya fice mashi a rai maimakon MC d'in ya bashi
loudspeaker d'in sai yace mashi wait ya juya kan Mutanen wurin yace "People are u seeing what am
seeing???" gaba d'aya aka sa dariya ya sake juyawa kan angon harda d'an rankwafawa alamar
girmamawa cikin harshen turanci da yake dashi ake Magana a wurin yace ya gafarce shi amman abokin
shi bahaushe ya tambaya ba Arab ba ko Indian gaba d'aya wurin aka kwashe da wata irin dariya har dai
shi Haisam d'in saida ya d'an dara Fatuu ma haka daga inda Angon yake zaune yace ma MC ya ba
Haisam d'in speaker ya tambaye shi tarihin shi da Hausa anan zai gane wanene shi ya juyo kan Haisam
yace suna rok'on Alfarmar jin tarihinshi da hausa farko kafin ya fad'i abunda aka bukace shi ya fito yi,
shiru ya d'anyi MC d'in nata fad'in please can ya kai hannu ya amshi speaker d'in cikin cool voice d'in shi
ya fara bada tarihinshi a tak'aice cikin harshen hausa aikuwa masu jin hausa a wurin aka hau tafi da sowa
Haisam d'in na d'an murmushi MC sai faman jinjina kai yake baki bud'e alamar mamaki bayan ya gama
ya canza harshe zuwa turanci ya fara bada tarihin Ango da mu'amalar shi da mutane anan sai ka rantse
ba shine ya gama Magana da Hausa ba gaba d'aya ya gama tafiya da mutane sai faman sakin murmushi
ake bayan ya gama ya mik'a ma MC d'in speaker d'in amman sai yak'i amsa yace yana son yay mashi few
questions ba yadda Haisam d'in ya iya dole yace mashi yana jin shi farko tambayar shi yay miye alak'ar
shi da Fatuu har saida gabanta ya fad'i Haisam d'in yay d'an shiru kamar mai nazari Abbas kuwa mi zaiyi
in ba Dariyar mugunta ba can ya nisa yace mashi girlfriend d'in ce da sauri Fatuu ta kalle shi sai kuma ta
kauda kanta gudun kada a gane ba gaskiya ya fad'a ba saidae bata yin zaton zai boye gaskiya ba,
tambayar shi yadda akai suka had'u ya k'ara yi anan bai 6oye ba yace mashi Neighbor d'in shi ce daga
baya ya koma kan Fatuu itama ya tambayeta tsakanin su waya fara cewa yana son wani shiru tay ta rasa
amsar da zata bashi kawae sai ji tay Haisam d'in yace mashi shi ya fara MC d'in ya k'ara tambayarta ya
taji da ya furta yana sonta tace taji dad'i sosae har bata san yadda zata bayyana ba tana fad'in hakan ta
sunnar da kai, haka dae yaci gaba da yi mata tambayoyi daga baya Haisam yace ya d'an yi excusing nasu
yay ma Fatuu alamar su je suka juya MC nata kod'a su yana fad'in "What a match, What a perfect
Match......." Maimakon su koma high table d'in sai gani tay ya nufi hanyar fita daga hall d'in hakan yasa
ta bi bayan shi suka fice, inda Motar su take ya nufa tay tsaye tana kallon shi ya bud'e ya kalleta yace ta
shiga cikin rashin fahimtar dalilin fitowar su ta kai hannu ta bud'e ta shiga tana ta kallon shi har yay ma
Motar Key ya fara yin reverse tana dae ta kallon shi da alamun mamaki har ya juya Motar suka tunkari
gate d'in fita, suna hawa hanya sai ga kiran Abbas yana yin picking tun kafin Abbas yace wani abu yace
mashi yaba Prince hak'uri he has an urgent call ya tafi daga haka yay cutting call d'in yaci gaba da driving
baki bud'e Fatuu ke kallon shi sam bata yarda da Maganar da yay ba a yaushe aka kira shin, d'an juyawa
yay ya kalleta yace mata lafiya fuska a tur6une tace mashi ya akai suka baro wurin daga farawa shiru yay
kaman ba zai ce komai ba sai kuma yace mata gida zai maida ta kamar zatai kuka murya na rawa tace "to
Saboda me, duka fa bamu wani dad'e da zuwa ba" nan ma shirun yay tana ta k'unk'uni sai da ya d'an
d'auki lokaci sannan yace "ban ce in akwae wani problem da kayan ba u shall inform me a canzo?" tura
baki tay yanzu ta gano dalilin kaman zatay kuka tace "to ai naga ta shige ni ne" banza ya mata taci gaba
da k'una k'uni da jan majina alamar zatai kuka can ya juya ya kalleta sai kuma ya maida idon kan hanya
calmly yace "ai mun je ko miye na damuwar?" kallon shi tay kaman bazata tanka ba ta d'aure fuska a
shagwa6e tace "to wannan zuwa ne, kofa Abinci bamu ci ba gashi serve ur self za'ai harda bank'ararrun
raguna mutum yaci iya cin shi ga wannan yar giyar ma da aka aje mana saman table ko sha bamu yi ba"
Haisam baisan lokacin da yay dariyar da har hak'oran sa suka bayyana ba jin wani shirmen ta wai giya
d'an juyawa yay still yana dariyar yace "Har yanzu baki daina ganin lemu kice giya ba ko" tana tura baki
tace "to ai giyar ce wannan ko ga kwalaben nan manya manya masu duhu kuma dama ai su suna shan
ta" d'an shaking kan shi yay yana d'an murmushi yace "to wannan ba giya bane is non Alcoholic suna
respecting addinin mu bazasu bamu giya ba saidae in mutum na sha yay Magana a bashi ko nama ma
musulmai suke ba suyi processing nashi" shiru kawae tay still bakinta a ture yake can ya d'age gira yace
"da giyan ne sai ki sha kenan?" Kikkafta ido tay tace "to ai in a rashin sani na sha ba wani abu ko" yace
"to waya kai ki inda za'a bakin balle har kisha?" Shiru ta d'an yi kafin tace "kai ka kai ni kuma kasan za'a
banin" yana murmushi yace "in nasan za'a baki bazan kai ki ba" shiru tay shima yaci gaba da driving d'in
shi yana yi yana d'an kallonta still da murmushi a kan face d'in shi ganin yadda ta 6ata rai ita ala dole an
mata laifi, a gaban wani babban soya spot ya parker Motar gefen titi ya fita part d'in gasasshen rago mai
yawa yasa aka yanko mashi had'i da gasasshar kaza bayan ya biyasu ya dawo a back seat ya bud'e ya
saka ya rufe ya koma driver seat d'in suka tafi, a gaban wani Cafe ya k'ara tsayawa ya fita bada jimawa
sosae ba ya dawo ruk'e da k'atuwar leda mai tambarin wurin ya shiga suka tafi har lokacin bata washe ba
sai fushi take, ganin sun bi wata hanya wadda ba ita suka biyo ba da zasu zo yasa ta d'an juya ta kalle shi
yanata driving bata ce komae ba ta maida kan ta jikin seat har suka k'araso wata unguwa suka shiga
Fatuu ta bi manyan gidajen da suke wucewa da ido lokaci guda mamakin ina ne suka zo ya cika ta tana
niyyar juyawa ta tambayi ina suka zo idonta suka sauka agaban wani d'an sign board mai d'auke da
sunan road d'in da Unguwar nan take ta gane G.r.a ne da mamaki ta juya ta kalle shi tace mi zasu yi a
Gra kamar bazai tanka ba sai kuma taji yace saida ita zai yi ta tura baki, suna hawa wani titi ya tunkari
wani tangamemen gate na wani katafaren gida ya tsaya yana latsa horn sau biyu wani mutum mai sanye
da kayan yan sanda ya d'an manyanta ya lek'o ta k'aramar kopa yana ganin Motar ya koma da sauri ya
zuge masu gate d'in Haisam ya shige, bai nufi k'aton parking space d'in ba sai ya parker ta gaban ginin
gidan wanda mansion ne na Gaske ya kalli Fatuu yace ta fito ya kai hannu ya bud'e kopar ya fita itama ta
bud'e ta fito baki bude take k'are ma gidan kallo duk da ba bene bane amman yana da girma sosae ga
ginin kan shi abun mutum ya saki baki yana kallo ne ga had'addun shuke shuken da suka zagaye ko ina
sun k'ara k'awata harabar sosae ta ko ina k'awatattun fitilu ne sun haske gidan security d'in ne ya iso
gaban Haisam yana washe baki yay mashi sannu da zuwa ya amsa mashi kafin ya kai idon shi kan Fatuu
itama ya gaidata duk sai ta ji wani iri hakanan ta amsa, bud'e back door yay ya fiddo da ledojin ciki
security d'in ya mik'a mashi hannu yace ya kawo ya rage mashi Haisam d'in yace ya bashshi bayan ya
rufe kopar yana shirin wucewa security d'in yace "Yalla6ai mai gyaran nan ya dawo yace abun nan sai ya
kai zuwa gobe dole sai a Kano aka samu goben za'a kawo sai ya idasa gyaran" kai ya jinjina sai kuma ya
tambaye shi tun yaushe aka maido wuta yace mashi ai duk yau akwae wuta gaskiya Haisam d'in ya amsa
da Ok ya juya shima security d'in ya koma gate kallon Fatuu yay bayan ya zagaya side d'in da take yace
suje tay tsaye tana kallon shi har zai juya ya dakata yace bata ji bane d'an yamutsa fuska tay tace ina ne
nan d'in wani kallo yay mata kafin ya bata amsa da inda zai sayar da ita ne ta d'an zaro ido ganin bata da
niyyar tahowa yasa shi cewa shi ya shiga ciki tay ta tsayuwa har azo a tafi da ita aikuwa tun kan ya rufe
baki tabi shi da sauri tana yi tana waiwayen bayanta ita duk sai ta tsorata da gidan ma da yayi Maganar,
Wani jigunannan Parlor suka shiga mai d'auke da Sofas set biyu ya tsaru iya tsaruwa ya bi wani Corridor
dake gefe Fatuu na bin shi a baya sai waige waige take har suka iso bakin wata babbar kopa ya tura suka
shiga Fatuu tay tsaye tana bin d'akin da kallo wanda Bedroom ne amman mai girman gaske daga can
gado yake da bedside drawers d'in shi sannan daga gaban shi inda table d'in gaban gado yake set d'in
leather Sofas ne ta yadda sun sa gadon a gaba daga tsakiyar su lallausan carpet ne a bangon da suke
facing k'atuwar plasma TV ce manne sai can gefe kuma dressing mirror yake daga d'an gaban shi wata
budaddar kopa ce ta corridor a gabanta kuma akwae k'atuwar window a wurin kayan motsa jiki ne sai
dae basu da yawa harda irin mai sa gudun nan wanda Fatuu ta hau sanyin Ac ta koina, suna shiga taja ta
tsaya har ya nufi ciki ya dakata ya juya ya kalleta ganin tayi tsaye ya nuna mata inda kujeru suke yace
taje ta zauna bata motsa ba ta bishi da ido hakan yasa ya dawo d'an gabanta ya tsaya yana kallonta ta
sadda kai can ta d'an d'ago ganin ya kafeta da ido yasa a marairaice tace "baka gaya man ina bane nan
d'in da muka zo" d'an kauda idon shi yay tana ta kallon shi ya juyo yace bata yarda dashi bane da sauri
tace "a'a kawai dae ina son sani ne" sigh yay yace "gidan Dad d'ina ne a G.r.a" kai ta d'aga har zai juya ta
k'ara cewa "to mi muka zo yi bazamu koma gida ba?" Idon shi a Kanta yay d'an murmushin gefe yace
"zaki ida abunda na hanaki ne kike fushi sai mu koma" d'an tura baki tay yace taje ta zauna ta shige
shima ya wuce saida ya aje ledojin kan Carpet yace mata yana zuwa ya nufi Corridor d'in cikin d'akin tabi
shi da kallo har ya shige kafin ta maido su tana k'are ma d'akin kallo ya dae tsaru sosae sam ba hayaniya
ga katafaren gadon yasha farin bedsheet gwanin burgewa, sanye da milk jallabiya mai gajeran hannu ya
fito ya nufi hanyar da suka shigo ya fita Fatuu dae tayi tsuru a saman kujera bai dad'e ba ya dawo
hannun shi ruke da plates harda yar wuka da glass cups ya nufi wurin kujeru ya d'aura akan Carpet ya
d'ago ya kalleta yace ta saukko ta taso tazo wurin ta zauna, da kan shi ya shiga fiddo abubuwan da ya
siyo yana sawa a plate d'in harda take away d'in Fried rice da irin lemun da tace ma giya yana fiddo shi
ya d'aga ido ya kalleta yana d'an murmushi ta tura baki ta kauda fuskarta, bayan ya gama yace ta ci ya
d'auki wasu da ya rage a cikin leda yace mata yana zuwa ya nufi hanyar fita don kai ma security, bata
fara ci ba har ya dawo ya zauna kan kujera yana kallonta yace taci mana tana d'an kikkafta ido tace to shi
fa yace zai ci ta gama tana d'an yamutsa fuska tace wato ita acici ko in dae bazai ci ba itama ta k'oshi
d'an murmushin gefen baki yay yana kallonta itama kallon shi take can ya tashi ya sauka kan Carpet d'in
ya lankwasa kafafun shi saida taga ya fara ci sannan itama ta sa hannu tun dai bata saki jiki ba har ta saki
suna ci suna kallon Tv sai gashi sun ci sosae harda k'arawa bayan sun gama yace in bata k'oshi ba ta k'ara
tace itama ta k'oshi ya bud'e mata lemun ya tsiyaya mata yana d'an murmushi yace ta d'auka ta kai
hannu ta d'auka ta d'an sha sai taji shi lafiya lau lemu ne yana murmushi yace saura ta k'ara gani tace
giya ce tay d'an murmushi taci gaba da sha a hankali, wayarshi ce ta fara ringing ya mik'e ya nufi gaban
dressing mirror ya d'auka da turanci yake magana bayan ya gama ya aje wayar ya juya ya nufi daga can
gefen inda kayan Motsa jiki suke saman wani desk ya d'aukko laptop dake a sama ya dawo wurin
kujerun ya zauna saman 3 seater ya aje laptop d'in a gabanshi bayan ya bud'eta ya fara operating nata
Fatuu da itama ta koma saman one seater ta zauna tana kallon Tv bayan wani lokaci ta kalleshi ta kira
sunan shi ya juyo ya kalleta tace ba yanzu zasu tafi bane gently yace ta d'an yi hak'uri ya k'arasa abu ana
jiranshi ne tace to ta maida idon kan Tv can ta tuna da bata yi sallar isha'i ba da yake tayi wankan tsarki
jiya zumud'in zuwa dinner ya hana ta tsaya tayi Sallar kallon shi tay tace tana son tayi salla ya d'ago ya
nuna mata corridor d'in da ya shiga ya canzo kaya yace in ta shiga akwae kopa mai kallonta anan toilet
yake tace to ta mik'e, lokacin data k'arasa ta tura kopar tasha mamaki don tayi zaton toilet d'in zata gani
amman sai taga laundry room irin nashi na gidan Hajiya amman wannan yafi kayatuwa don aciki press
d'in kayan shi take wadda ta glass ce kana kallon kan ka a jiki ga kuma wall cabinet a ciki su kayan wanka
suke sosae wurin ya burgeta don ita bata san yana dashi a can d'in ba tunda ko bedroom d'in shi bata
ta6a shiga ba, kopar da ta gani a cikin wurin tay tunanin nan ne toilet d'in ta nufeta ta tura aikuwa toilet
d'in ne wanda ya amsa sunan toilet, bayan tayo Alwalar ta fito tsaye tay a bakin corridor d'in tana
tunanin to da mima zatay sallar d'an gyalen data nad'a iya kafad'ar ta yake tana tsayen ya d'ago ya
kalleta ya tambaye ta da matsala ne tace eh ba hijab yace ina jallabiyar ta tace ta baro ta a Mota
mik'ewa yay yace yana zuwa bada jimawa ba ya dawo ya kawo mata tay mashi godiya ya d'aukko mata
prayer mat ta tambayi inda gabas take ya nuna mata kafin ya koma yaci gaba da aikin shi, bayan ta gama
sallar komawa tay wurin kujerun ta zauna kan 2 seater taci gaba da kallon a hankali kuma ta fara
gyangyad'i tun tana yi tana bud'e ido har takai ta d'an kwanta ta fara baccin sosae can ya d'ago ya ganta
tana baccin don bai ma san tayi ba juyawa yay yaci gaba da aikin da yake bayan wani lokaci Fatun ta
bud'e ido da sauri kuma ta tashi zaune tana d'an murza ido tace "Ya Haisam yakamata mu tafi dare yayi
sosae" kallon agogon jikin laptop d'in yayi yaga sha biyu saura saukko da d'ayar kafar shi yay ya mik'e
yace suje itama ta mik'e ganin bai kashe laptop d'in ba yasa tayi mashi magana yace zai dawo ne in ya
kai ta ta d'aga kai ta d'auki purse d'inta ta fita daga wurin kujerun shi kuma ya nufi gaban dressing mirror
ya d'aukko cay key yana nufo ta kwatsam aka d'auke wuta aikuwa Fatuu ta saki k'ara tana fad'in "Wayyo
ya Haisam kana ina don Allah ka kunna haske wllh ban ganin komae" shi Maganar tata ma dariya ta
bashi sai kace wata yar k'aramar yarinya wai tsoron duhu ya lura da ita abunda bai kai ya kawo ba shi
take ji ma tsoro jin baiyi magana ba yasa ta k'ara kware murya tana fad'in ta bani don Allah yayi magana
abun ma shi nishad'i ya saka shi sai kawae yay shiru aikuwa ta k'ara rud'ewa dama ta tsorata da gidan
tun farko cigaba da fad'in yana ina tay tana lalube duk ta firgice a haka har ta k'araso gabanshi tana kai
hannu ta ta6a chest d'in shi ga k'amshin jikinshi kuma aikuwa ta fad'a mashi ta fashe da matsanancin
kuka tana fad'in shine yana jinta zai yi banza da ita sosae ta k'ank'ame shi jikinta sai kerma yake sai kuma
duk bai ji dad'i ba baiyi zaton ta tsorata haka sosae ba slowly ya kai hannu bayanta alamar rarrashi ya
shiga furta mata "am sorry" lamo tay a hankali rawar da jikinta keyi ta fara raguwa cikin muryar kuka
tace ya kunna haske su tafi ya furta Ok bari ya duba wayan bai san takamaimai inda take ba aikuwa ta
k'ara rikeshi gam ganin haka yasa ya fara moving da ita a kokarin shi na su koma inda kujerun suke don
yafi tunanin anan ya aje wayar bayan da aka kira shi cikin rashin sani ashe ta bayan kujerun suka bi har
baisan sun zo bakin gado ba kawae sai jin su sukae sun fad'a saman shi rikica gaba d'aya hankalin su ya
tashi don abu ne da basu tsammaci faruwar shi ba tsit kake ji kowa na maida numfashi ba kamar Fatuu
da yake a samanta sun dan d'auki lokaci a haka kowa ya kasa yin kwakkwaran motsi tamkar anyi glueing
nasu da k'yar Fatuu cikin rawar murya ta ambaci sunan shi shiru bai amsa ba ta kai hannu da niyyar ta
d'aga shi hannun ya nutse acikin sumar kanshi wani irin shock yaji a jikin shi da sauri Fatuu ta janye
hannun tana breathing rapidly wannan d'agawa da saukar da chest d'inta keyi ya fara turning nashi on
slowly ya d'ago face d'in shi ta yadda numfashin su ke had'uwa gaba d'aya kasala ta lullube Fatuu da
k'yar ta iya k'ara bud'e baki tace "Ya Haisam ka......" Cak ta tsaya tana zare ido jin abunda bata ta6a zato
ba lips d'in Haisam a saman nata a rud'e ta fara kokarin k'ara yi mashi magana kawae sai jin tongue d'in
shi tay cikin bakinta bata ankare ba sai ji tay ya fara mata hot French kiss lokaci guda Fatuu ta rud'e ta
kidi'me ta gigice, gaba d'aya Haisam ya gama gigita yar Mutane har bata san ta zura hannunta acikin
sumar shi ba tana squeezing nata hakan da take ya k'ara turning nashi completely on hot romances ya
shiga yi mata tamkar yana operating laptop d'in shi to Fatuu dae ba k'arfe bace cikakkar mace ce da jini
ke yawo a jikinta tana cin mai kyau ta sha kuma mai kyau dole kota k'i ko taso jikinta na buk'atar abunda
ke faruwa da ita hakan yasa kwata kwata ta kasa hana shi abun har ya kai wani mataki da ita kanta bata
ankare da an kai ba ba abunda take sai sakin numfashi da k'arfi had'i da nannauyar ajiyar zuciya a wata
kalar duniya take jin ta da babu gwaggo babu Kawu Amadu ba Hajiyar sanata ba ba....., Fatuu bata tashi
dawowa hayyacin ta ba saida taji wani rikitaccen Al'amari dake shirin faruwa da ita wanda sam bata san
an kawo nan ba aikuwa a gigice ta kai hannu ta kama damtsen shi tana girgiza mashi kai tana fad'in ya
bari ba kyau abunda suke Allah zai kama su kada ya cutar da ita, da alama Haisam fa ya rasa control
kokarin penetrating d'in ta yake ta k'arfi ganin haka yasa Fatuu ta fara k'ok'arin kwatar kanta ta hanyar
kai mashi bugu da yakushi amman sam kamar bai jinta ma abunda yasa gaba kawai yake as if his life
depends on it cikin k'araji Fatuu ke fad'in "Don Allah Ya Haisam na rok'e ka in kana k'aunar iyayen ka
kana k'aunar Hajiyar Sanata ka k'yale ni kada ka cutar dani ni fa kanwarka ce......" bata k'arasa Maganar
ba ta saki wata irin razanannniyar k'ara koma in ce kururuwa........... innalillahi Wa'inna ilaihir raji'un!
Jama'a miya hwaru ne😳
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2044*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

...........tun bayan daya dawo hayyacin shi ya k'ank'ame ta sosae jin yadda jikinta keta kerma gashi an kai
wata ga6a da bata ma iya yin kukan mai sauti sai na zuciya k'walla nata gangaro mata ga zazza6i daya
rufeta ruf lokaci guda, to shima dae kermar nashi jikin yake duk ya rud'e yanata bata hak'uri cikin wata
irin murya mai nuna tsantsar tashin hankali gaba d'aya jin jikinshi yake tamkar ba nashi ba ga zazzabi
dake neman rufe shi shima a haka bacci ya d'auke su su duka saidae Fatuu bana dad'i bane don sai sakin
ajiyar zuciya take had'i da d'an firgita, suna haka aka maido da wuta sanyin Ac ya karad'e bedroom d'in
kermar jikin Fatuu ta k'aro ba kamar da yake ba kaya a jikinta iya duvet ne da ya rufa masu, da k'yar ta
bud'e idanunta da sukae mata wani irin nauyi jikinta na cigaba da yin kerma ga wasu kwalla masu zafi na
gangaro mata a gefe da gefen idanunta sam ta kasa wani kwakkwaran motsi don duk ilahirin jikinta ciwo
yake ga rad'ad'in azaba dake ratsa cikin jikinta ga kanta dake wani irin Sara mata ta k'ura ma ceiling ido
idanuwanta a d'an lumshe she wishes what happened was a dream ba gaske ba saidae koda ga yanayin
da take jin jikinta tasan gaske ne ya farun cikin ranta ta fara ayyana wannan wane irin bala'e ne miyasa
Ya Haisam ya akaita mata hakan anya kuwa da gaske ne ba mafarkin ba, a hankali ta fara tariyo abunda
ya faru tun daga farko ita dae tasan zata iya tuna lokacin daya kai hannu ya zuge mata zip dama rigar
nada dogon zip har kusan k'ugu kuma bata sa bra ba sakamakon kamata da rigar tayi sosae sai tasa yar
half vest kawae tunda kuma ya kai kan su ta fita hayyacin ta bazata iya tuna ga abubuwan da suka cigaba
da faruwa ba sai lokacin da taji yana kokarin penetrating d'inta, hannu tasa ta rufe bakinta tana wani irin
kuka mai cin rai miyasa hakan ta faru ya akai suka aikata hakan wata Zuciya ta raya mata sharrin shaid'an
dama duk in mace da namiji suka ke6e ai na ukkun su shaidan ne ta k'ara ayyana to amman miyasa da
tana rok'on shi kada ya aikata mata hakan yak'i sauraron ta mi zai sa ya cutar da ita har haka yanzu
shikenan ya rabata da budurcin ta ya Haisam ya cuceta bai tunanin abunda zai je ya dawo ba Saboda son
zuciya ya keta mata haddi wannan wace irin Masifa ce mutumin da ko a mafarki bata ta6a tunanin zai
mata haka ba balle a zahiri mutumin da shine ya bata kariya hakan bai faru da ita ba a baya amman shi
da kan shi ya aikata mata hakan mutumin da kowa nata ya yarda dashi ba kamar gwaggo har take iya
barinta ta fita da shi da daddare sosae shine ya aikata mata wannan d'anyen aikin da tasan in gwaggo
taji har zuciyarta na iya bugawa, innalillahi Wa'inna ilaihir raji'un! haka take ta maimaitawa tana juya
kanta tafin hannunta guda dafe da goshinta tana haka taji fitsari ya matseta ta fara kokarin janye jikinta
don ta tashi sai faman nishi take da k'arfi sai lokacin ta gane ba kaya jikinta ta k'ara sakin wani Sabon
kukan da K'yar taja jiki ta matsa can gefe inda ta hango jallabiyar ta ta d'auka daga zaunen ta zurata don
bata ma ga jar rigar ba da dubara ta isa k'arshen gadon a hankali ta zura kafafun ta k'asa saida ta
daddafe gefen gadon da hannunta sannan cike da k'arfin hali ta yunk'ura ta mik'e har wani Jiri ke dibarta
tasa hannu ta dafe kai tana d'aga k'afarta don ta fara tafiya ba shiri ta koma da6ar ta zauna har saida ta
saki yar k'ara Saboda wani rad'ad'in azaba da ta ratsata, hannu tasa ta rufe baki ta fashe da wani sabon
kukan jin fitsarin na niyyar zubowa yasa dubara ta fad'o mata ta duk'e k'asa ta fara yin rarrafe tana
cigaba da yin kuka a haka ta nufi Toilet d'in baiwar Allah duk wannan abun Haisam bacci yake ta shara
sai kace matacce, a wahalce ta isa toilet d'in da K'yar ta shiga cikin bathtub don ma tana da k'arfin hali
lokacin da fitsarin ya fara zubowa wata zabura tay a gigice tace "Wayyo Allah na!!!" ta k'ara fashewa da
kuka Saboda azaba da kyar ta gama tana ta gunji ta kai hannu ta kunna fanfon ruwan zafi ko da tai
tsarkin sai taji wani dad'i ya ratsata aikuwa taci gaba da yi ta bar fanfon a kunne tana tayi har bayan wani
lokaci sannan ta kashe sai gashi ta samu relieve sosae bata sha wahala ba wurin fitowa kamar da zata
shiga, da k'afafunta ta fito sai dae da K'yar take tafiyar tana yi tana dafa bango ga k'afafun sun d'an
bud'e bata iya had'e su a haka har ta fito cikin d'akin idanunta suka sauka akan Haisam dake ta bacci
sumar shi duk ta yamutse wani irin haushin shi taji ya turnuk'e ta ya aikata mata wannan aika aikar
amman baccin shi ma yake sha nan da nan ta ayyana dama da niyya yay mata hakan k'walla ne suka
cigaba da zubo mata tana sharewa wata zuciyar ta raya mata kawai ta tafi gida tunda ko ta zauna in ya
tashi bai wuce yace zai bata hak'uri tunda ba iya dawo mata da abunda ya rabata da shi zai yi ba da
wannan tunanin ta lalla6a ta d'auki gyalen rigar kota kan jar rigar bata bi ba dama tashi ce ta bar mashi
kayan shi a hankali take tafiyar ta nufi kofa akan hanya ta ga purse d'inta yashe a k'asa ta d'auka bayan
ta fita a bakin k'opa dama ta aje takalmanta saidae tasan bata iya tafiya dasu hakan yasa ta ruk'e su a
hannunta, ta d'auki lokaci kafin ta k'araso bakin gate d'in tsit kake ji da alama dare ya tsala sosai a bakin
kopar security ta tsaya ta kai hannu tana kwankwasa wa sai gashi ya fito hannun shi ruk'e da bindiga ya
bita da kallo ta d'an kauda fuskar ta ya ganeta hakan yasa shi cewa "Madam lafiya kuwa" kaman bazata
yi Magana ba k'asa k'asa tace ya bud'e mata kopa zata tafi ne da alamun mamaki yace "tafiya kuma cikin
daren nan ina shi yalla6an yake" nan ma shirun ta k'ara yi ta rasa mi zata ce mashi don kar ya zargi wani
abu can dubara ta fad'o mata tace "wani aiki yake a computer shine yace in jira ya gama mu tafi to sai
bacci ya d'auke ni yanzu bayan na farka kuma sai naga shima yayi baccin ban son in tashe shi ka bud'e
man zan iya tafiya" daga jin yadda take Maganar zaka fahimci ba daidai take ba sai faman nishi take ga
Maganar a wawware shiru Officer yay yanata kallonta ya lura da har jikinta ma kerma yake hakan yasa
shi ce mata kamar ma bata lafiya ko tace mashi eh zazzabi ne ya rufeta shine ma yasa ta farka yace to
bari shi yaje yay mashi magana sai yazo ya kaita don dare yayi sosae k'arfe d'aya saura da kyar ma in
bata wuce ba da sauri tace ba sai ya kira shi ba zata iya yace "Madam bari dae in mashi magana don a
irin wannan lokacin ba'a fita da k'afafu don karnuka keda akwae ta ko ina da sun ganta zasu yi mata tara
tara su aikata mata d'anyen aiki yana gama fad'in hakan ya nufi cikin gidan Fatuu na k'walla ta ayyana
d'anyen aiki ya wuce wanda aka aikata mata yanzu, kasa cigaba da tsayuwar tayi da K'yar ta zauna kan
saman wurin k'afafunta na a k'asa ta takure jikinta dake ta rawar sanyi wani irin fayau take jin ta, yana
shiga corridor d'in d'akin Haisam ya tunkari kopar ya tsaya yasa hannu yana kwankwasa wa tun yana yi a
hankali har ya kai ya k'ara sautin bugun amman shiru kake ji ba alamun za'a tanka kuma dae ba zai yuwu
ya kutsa kai ba, cigaba da kwankwasawa yay can cikin bacci bugun ya kai ma Haisam da K'yar ya fara
bud'e idanun shi da sukai wani irin nauyi gashi har kala sun canza sun d'an yi ja d'ago kan shi yay da
mamaki yake kallon kopar da ake bugawar can ya tambayi waye da kasalalliyar murya saida ya tambaya
sau biyu sannan k'asa k'asa Officer ya jiyo shi da d'an k'arfi yace Officer ne cikin ranshi ya maimaita
sunan Officer d'in kafin ya kai hannu ya yaye duvet d'in wani irin bugu gabanshi yay lokacin da idanun shi
sukai tozali da jinin da ke a jiki kallon jinin yake with mouth agape can ya furta "ZARAAH!!!" aikuwa cikin
zafin nama ya saukko da sauri ya nufi hanyar corridor ya nufi toilet don ganin ko tana ciki yaga wayam da
sauri ya juyo lokacin idanun shi suka sauka kan milk d'in jallabiyar shi da itama ke d'auke da stains na jini
ta cikin mirror d'in jikin press d'in shi k'ara rud'ewa yay ya nufi hanyar fita yazo bakin kopar ba tare da ya
bud'e ba sosae ya d'an lek'a kanshi ya tambayi Officer ko lafiya anan ya fad'i mashi dama Madam ce da
suka zo tare gata can bakin gate ta matsa sai ya bud'e mata ta tafi kuma ma bata lafiya don sai kerma
take da sauri Haisam d'in yace mashi yaje gashi nan zuwa ya koma cikin Corridor d'in yana wani irin sauri
da shi kanshi bazai iya tuna ga ranar da yayi irinshi ba wata jallabiyar ya zuro wuya a jirkice ya fito tun
kafin ya k'arasa ya hangota raku6e a jikin pillar yana k'arasawa ya tsaya akanta ya kira sunanta shiru bata
amsa ba bata kuma kalleshi ba sai ajiyar zuciya take yi da gani kukan zuci take Slowly ya duk'a a gabanta
Officer na ganin haka ya juya ya koma cikin d'akin shi, k'ara kiran sunanta yay still bata amsa ba ya kai
hannu ya kamo hannunta aikuwa ta fusge zafin da yaji a hannun ne ya k'ara tada mashi hankali cikin
trembling voice yace "am so sorry Zaraah mu koma ciki sai muyi magana" banza tay mashi ganin bata da
niyyar tashi yasa shi mik'ewa ya kai duka hannuwanshi zai d'auketa aikuwa ta fashe mashi da kuka mai
sauti tana fad'in ita ya kyaleta yasa a bud'e mata gate ta tafi, fasa d'aukar tata yay ya mik'e tsaye don bai
son Officer ya ji har ya zargi wani abu can ya sake duk'awa gabanta a hankali yace "kin ga yanzu dare yayi
sosae kiyi hakuri mu koma ciki zan kira Uncle d'in ki sai in sanar mashi dare yayi mana sosae matar Abbas
ta wuce dake gidanta in mun shiga ciki zamu yi magana kiyi hak'uri kinga ma baki lafiya sai kisha magani"
da ga voice d'in shi zaka fahimce shima a rud'e yake har wani d'an nishi yake don shima zazzabi ne a
jikinshi, duk yadda yay da ita su koma ciki tak'i sai ma ta kife kanta tana ta kuka har cikin ran shi yake jin
kukan don yasan shine silar shigarta halin da take ciki yama rasa tunanin da zai yi cikin ranshi yanata
ayyana miya faru dashi ne ya akai ya aikata wannan d'anyen aikin ina hankalin shi ya tafi ne, yasan tunda
ta kafe to bazata koma ban hakan yasa shi ce mata to bari ya maida ita gidan cikin fushi tace ita bata so a
bud'e mata gate kawae bai yi mamakin yadda tay mashi Maganar ba don yasan girman shi ya gama
fad'uwa a wurin ta rarrashin ta ya shiga yi yana nuna mata illar fitar ta a wannan lokacin in dai bata bari
ya kaita ba to saidae su kwana anan ala bashshi sai ya kira Amadun ya fad'a mashi abunda yace zai fad'i
mashin, shiru tay saida aka d'an d'auki lokaci sannan tace suje ya kaita ya mik'e da sauri kai kace ba
Haisam ba da alama bai ma san ina yake wurga k'afarshi ba dama Motar ba'a parking space take ba yana
d'aukko makullin ya shiga ya tada bayan ya juyata ya iso gaban gate d'in ya bud'e ya fito ya koma
wurinta yace ta taso suje ganin yadda take kokarin mik'ewa yasa shi kai hannu ya taimaka mata tana ta
k'ok'arin kwacewa bai biye mata ba saida ta mik'e sannan ya saketa da k'yar taja k'afa ganin ta nufi
kopar baya ya je ya bud'e mata saida dubara ta shiga ya rufe shima ya shige driver seat yay ma Officer
horn sai gashi da sauri ya fito yaje ya zuge masu gate d'in Haisam yaja suka fice, bayan officer ya rufe
gate d'in tsaye yay da alamun tunani yake saidai ya kasa hasashu komae k'arshe ya gyad'a kai ya koma
cikin d'aki, tunda suka taho taci gaba da kukan da take k'asa k'asa tana sheshsheka shiru bai ce mata
komai ba tunanin yadda zai maida ta gida acikin wannan halin yake can wata zuciyar ta raya mashi
yakamata ma ya kaita Asibiti don da alama akwae matsala Saboda jinin da ya gani duk da first night
dinsu da Fanan itama tay shedding blood d'in amman nata d'an kadan ne bai kai yawan na Fatuu ba da
wannan tunanin ya yanke wucewa da ita Asibiti kawai, kanta na duk'e har suka iso jin an tsaya yasa ta
d'ago lokaci guda ta gane Asibiti ne bayan ya kashe Motar ya bud'e ya fita saida ya rufe ta da Makulli
sannan ya nufi ciki Fatun na mashi wani kallo ta cikin glass wa zai yi tunanin zai iya aikata mata haka ta
raya a ranta, yana shiga reception sai ga wata Nurse zata wuce da sauri yay mata magana ta dakata
baiwar Allah har saida ta saci kallon k'afafun shi don taga in ba kofato bayan yay mata ya aiki tace
Alhamdulillah yace don Allah Doctor mace yake son gani tace mashi gaskiya ba mace duk maza ne shiru
yay kawai yana tunanin bai kamata ace namiji ne zai duba ta ba ganin haka yasa tace mashi dole sai
mace yace eh yafi son haka har zai juya tace "Yalla6ai akwae wata Mama tsohuwar nurse ce ba likita ba
amman kusan ma kamar likitan ake d'aukarta don ta san abubuwa sosae in kana so tana nan sai ka
ganta" da sauri ya kalle ta yace Ok tana ina tace suje ta juya hanyar da ta fito yana biye da ita har suka
isa wata kwana a bakin wata k'opa ta tsaya ta juya tace mashi tana zuwa ya d'aga mata kai, lokacin data
shiga mamar wadda dattijuwa ce tana kwance a saman gadon da ake duba mara lafiya ta d'age kai baki
bud'e tana bacci ga gilashin fuskarta ya zame a gabanta nurse d'in ta tsaya ta kira sunanta har sau biyu
bata farka ba hakan yasa ta d'an matsa ta kai hannu ta d'an bubbuga gefen kanta aikuwa sai gashi ta
bud'e ido kaman an latsa mata remote ta k'ura ma nurse d'in ido ita kuma tana mata murmushi can ta
yunk'ura ta tada kanta cikin fushi tace "Nurse Bilki ke wace irin muguwa ce ne?" D'an bud'a ido bilkin tay
tace "Mama nice muguwa kuma" tsuke fuska tay tace "eh mana in ba mugunta da rashin tausayi ba duka
fa ban dad'e dana samu na kwanta ba bayan gama kacaniyar Labour room shine kuma zaki zo ki katse
man bacci?" Sanin halin ta na mita yasa bilkin cewa "to yi hakuri Mama dama bak'o kika yi ne shiyasa na
tashe ki" d'an yamutsa baki tay tace bak'o kuma da tsakan daren nan waye shi bilkin ta fad'i mata yadda
sukai da Haisam wata uwar harara ta zabga mata tace "to in banda iskanci baki ji likiciya yake son gani ba
zaki tada ni ni likita ce?" d'an murmushi bilki tay tace "ai kema mama kaman likitan kike kuma don naga
kaman yana cikin tashin hankali ne yasa nace bari in maki Magana k'ila wata matsalar ce yake son fad'i
maki" cigaba da harararta tay kafin can ta yunk'ura ta saukko tana d'aure da zanin Atamfa saman farar
doguwar rigar aikinta tambayarta tay yana ina tace yana nan bakin kopa ta nufi kopar tana mita bilkin na
dariya a ranta tana ayyana dama ina ma'aikacin Asibiti yaga wata damar yin bacci mai yawa, Mama na
bud'e kopar idonta suka sauka kan Haisam dake jingine da bangon dake opposite da Office d'in har saida
tasa hannu ta gyara gilashin ta yadda zata gan shi da kyau ta bishi da kallo tun daga sama har k'asa ganin
yana kallonta yasa tace shine mai neman ta yace eh yana kokarin matsowa gabanta tace tana d'an zuwa
to yace Ok ta koma ciki suka had'a ido da bilki dake murmushi tace "Ke kin tabbatar wannan mutum ne
kuwa ba Aljani ba nifa ban yarda da shi ba don kwanakin nan dama ina yan gane gane" Bilki mi zatayi ba
dariya ba ganin yadda mama tayi zuru zuru da alama dae ta tsorata da Haisam d'in cikin dariya tace
"Wllh mama nima dana gan shi har saida na kalli k'afafun shi dama banga lokacin da ya shigo ba sai dae
naji anyi man Magana kawae ga abu na dare" turo baki Mama tay tace mata yanzu ya zasu yi bilkin tace
ita tana ganin lafiya lou Mutum ne in ba haka ba mi zai sa yazo wurin su har yace yana son ganin likita
Mama tace "Bilki raba kan ki da sharrin Mutanen 6oye" juyawa tay tace suje tare koma mi zai faru ya
faru dasu duka bilkin ta bita tana fad'in kai Mama kefa dama kin tsufa ni kuma yanzu nike kuruciya ta a
tare suka fita bawan Allah Haisam yana jingine da bango duk yayi zuru zuru bayan ta fito tace mashi tana
ji miye matsalar yake son ganinta ba tare daya ji komae ba ya shiga yi mata bayani bayan ya d'an
daidaita natsuwar shi tana ta jinjina kai ta d'an ta6e baki har ya gama saidae a yadda yay mata bayanin
nuna mata yay matarshi ce, tambayar shi tay yanzu ina take yace tana Mota ta tambaye shi tana iya
tafiya yace eh amman ba sosae ba ta kalli Bilki tace taje ta d'auki Wheelchair ta taho da ita su fara
tsayawa Nurses room a turo ta tace to ta kalli Haisam tace suje, da taimakon Bilki Fatuu ta fito ta
taimaka mata ta hau wheelchair d'in kafin ta tura ta tana biye da ita suka shiga saida ta tsaya aka tura
sunanta ta computer sannan suka wuce wurin Mamar da zasu shiga tace ma Haisam ya jira ta nuna
mashi waiting seats dake gefe alamar ya zauna yace ok, bayan an shiga da ita tare da Mamar aka
taimaka mata ta hau gadon ta sanya hand gloves ta fara dubata tana yi tana yamutsa baki can ta fara
mita tana fad'in "ni wllh irin wannan duk nafi ganin laifin iyayen ku su same ku suyi ta yi maku banke
banken magungunan mata to su mazajen naku duwatsu ne da bazasu rikice har suyi maku aika aika ba,
kamar ke yanzu ai baki wani bukatan magunguna iya lafiyayyen Abinci ma ya Wadatar kuma da gani ana
ci sai abu ya faru kuzo kuyi ta ma Mutane jan ido" bilki dai na tsaye daga can gefe tana k'umshe dariya
sosae ta duba ta bayan wani lokaci ta gama ta fara cire safar ta jefar a cikin dust bin kafin ta juyo ta kalli
Fatuu tace "Allah ya taimaka baki buk'atar stitches kin samu rauni ne a farko wurin shiga da alamu ansa
ma wurin k'arfi ne halan hana shi hakkin shi kika so yi ya nuna maki k'arfi haka?" sunnar da kai Fatuu tay
idanunta suka ciko da k'walla da tasan halin da take ciki da batai mata wannan Maganar ba kallon bilki
tay tace ta kamata su shiga toilet d'in cikin Office d'in ta taimaka mata da ruwan zafi ta zauna ta d'an
samu relieve tace to ita kuma ta juya ta fita Haisam na ganin ta lek'o ya mik'e yaje gabanta tayi mashi
bayanin komae tace yanzu dole ta dage da zauna ruwan zafi amman ba mai zafi ba sosae da d'an gishiri
sai magungunan da za'a bata ta rink'a sha in tana haka zata samu sauki yace to d'an zare mashi ido tay
tace "Amman fa ka k'yaleta ta huta sosae har ta warke garas kafin ka k'ara tunanin yin wani abu" jinjina
mata kai kawae yay tace ya jira zata tura magani yaje Pharmacy yace to tana niyyar juyawa ya dakatar da
ita ta hanyar rok'on ta ko ya samo mata wani abu a bata taci sai in ya amso magungunan a bata ta fara
sha daga nan d'an kya6e baki Mama tayi tace halan fushi take dashi yasan in ya bata bazata ci ba d'an
guntun murmushi kawae yay tace yaje ya kawo ya amsa da Ok ya wuce, bada jimawa ba ya dawo Cake
da lemu ya samo a shop d'in cikin Asibitin su kadae ne yake tunanin zata d'an ci don ba Abinci a wurin
bayan ya kwankwasa Nurse Bilki ce ta fito ta amsa kafin ya juya ya nufi Pharmacy d'in aka tura kud'in
yaje ya biya kafin ya amsa magungunan suma ya kai masu ya koma ya zauna, saida Mama ta matsa mata
ta cinye duka har lemun tana yamutsa fuska alamar bata so bayan ta gama suka rakota waje ba laifi
tafiyarta ta d'an k'ara warwarewa yana ganin ta fito ya mik'e ta kauda kai gefe Mama tace to gatanan sai
a kiyaye ya amsa da Ok yay mata godiya kafin ya rok'eta ta d'an bashi Account details nata farko kaman
bazata bashi ba tace ai ba sai ya bata wani abu ba ai aikinta ne yace ya sani just kyauta ce sannan ta fad'i
mashi nan take yay mata transfer d'in 70k yace taba Nurse Bilki 20k suka hau godiya har tana zolayar shi
tana in Amarya ta haihu a sanar masu ya d'an dai yi murmushin yak'e kawae suka tafi yana ruk'e da
ledan magungunan da bilki ta bashi, a hankali take tafiyar yana biye da ita a haka har suka fito shi ya
bud'e mata back door d'in kaman bazata shiga ba yanata kallon ta ita kuma ta juyar da fuskarta gefe
saida ta ga dama sannan ta shiga ya rufe kopar koda ya zagaya maimakon ya shiga driver seat d'in sai
shima ya bud'e bayan ya shiga tana ganin ya shigo ta juya mashi k'eya shiru yay yana kallon bayan kan
nata Magana yake so suyi saidae ya rasa ta inama zai fara can ya nisa yace "Zaraah" shiru bata amsa ba
balle ta kalle shi cigaba yay "I know i ave wronged u dat sorry isn't enough to make u forgive me but I
will still use it to apologize for what I have done am very sorry Zaraah" banza ta mashi yaci gaba "nasan
na cutar dake saidae billahi bada nufi hakan ya faru ba ni kaina I don't know what came over me da har
hakan ya faru amman koma miye laifi na ne cos am the one who took u there" nan ma dae tsit tay sai
yar sheshsheka da take yi a hankali shiru yay yana ta kallonta a cikin ranshi kuwa bai mamakin duk
abunda tay mashi ba don yasan dole ma girman shi ya fad'i a idonta sigh yay yace "in sha Allah zan gyara
laifin da na aikata gobe zamu yi Magana da ke but before then pls don't disclose what happened to
anyone" cikin fushi ta juyo fuskarta jage jage da hawaye tace "ai in ban fad'a ma kowa ba Allah shi ya
sani miyasa zaka man haka ka cutar dani bayan laifin da kasa muka aikata hakan bai isa ba har sai ka
cutar da rayuwata....." Fashewa tay da matsanancin kuka still yay yana kallon ta komae ya gama kwance
mashi ya rasa ta ina zai taro matsalan ta gyaru gashi shi kanshi ba lafiya gareshi ba don zazza6i tuni ya
gama rufe shi k'arfin hali kawae yake k'arshe dai hak'urin yaci gaba da bata yana zasu yi Magana gobe da
k'yar ya samu ta d'an tsagaita da kukan ya bud'e Motar ya fita bayan ya rufe ya bud'e driver seat ya
zauna kafin ya rufe yaja suka tafi...........

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2045*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


........lokacin da suka iso kopar gidan k'arfe d'aya da rabi na dare Unguwar tayi tsit ba kowa sai hasken
fitilu da yake akwae wuta, yana parker Motar ta kai hannu don ta bud'e ta fita amman sai taji kopar a
rufe cikin muryar fushi tace ya bud'e mata ta fita bai ce komae ba wayar shi na a hannun shi yana
kokarin kiran Amadu dama tun suna Asibitin bayan an shiga da Fatuu yay tunanin kiran shi cikin sa'a ya
d'aga kiran anan ya sanar dashi cewa ayi hak'uri sun yi dare ne da yake ba'a fara program d'in da wuri ba
amman gasu nan dawowa in ba damuwa kada yay bacci sai ya bud'e mata k'opa, yanzu ma da ya kira
shin bayan yay picking yace mashi gasu nan k'opar gida ya amsa da to ya katse kiran ya aje wayar a gefe
sannan ya d'auki wayarta dake aje kan seat ashe anan ciki ta barta tun bayan da ya kirata a wurin dinner
yace ta fito, bud'e k'opopin Motar yay Fatuu na jin ya bud'e ta kai hannu ta bud'e shima bud'e ta side
d'in shi yay ya fito ya zagayo inda take lokacin har ta zuro k'afafun ta hannu ya kai don ya taimaka mata
tak'i 6ari ya ta6ata dole ya k'yaleta yana ta kallon ta cike da tausayawa har ta fito hannunta ruk'e da
takalmanta ya duk'a cikin Motar ya d'aukko purse d'inta da ledan magungunan har ta fara tafiya ya bita
ya tsaya a gefenta ta kauda fuskar ta tana niyyar cigaba da tafiya cikin wata irin murya ya kira sunanta
shiru bata amsa shi ba sai dai ta tsaya bai damu ba yaci gaba da fad'in "am so sorry pls kiyi hak'uri nasan
ban kyauta maki ba amman kamar yadda nace zan gyara laifi na in sha Allah zamu yi Magana kinji?"
Shiru dae bata tanka ba ya mik'a mata ledan da purse yace "ga drugs en ki ki d'aure ki sha....and sun...ce
ki rink'a sit bath with lukewarm water da d'an salt nasan baki rasa sanin hakan but kaman yadda nace
kar ki fad'a ma kowa abunda ya faru pls" a wawware yake Maganar duk muryar shi ta canza ga wani
nishi da yake yi in yana Maganar shiru dai tayi kanta na gefe jin k'arar ta6a k'opar gidan su alamar za'a
bud'e yasa ta kai hannu ba tare data kalle shi ba ta amshi purse da magungunan daidai lokacin Amadu ya
bud'e k'opar tunanin yadda zata cigaba da tafiya ta shiga yi tayi tsaye Haisam ya fahimci hakan sai ya kira
Amadun ya nufo shi ya juya ya koma Mota Amadun na biye dashi a jikin Motar ya jingina Amadu ya iso
ya tsaya gaban shi da murmushi ya gaishe da shi ya amsa yana kokarin daidaita voice d'in shi yace "am
sorry na hanaka yin bacci ko?" Murmushi Amadu yay yace "ai lokacin da ka kira ni d'azun ban ma kaiga
kwanciya ba ina chatting ne" jinjina kai Haisam yay ya d'an saci kallon Fatuu dake k'ok'arin shigewa cikin
gidan yace ma Amadu "kana zance kenan?" Yar dariya mai sauti Amadu yay don bai tsammaci jin irin
Maganar daga wurin Haisam ba yace mashi a'a, d'an yamutsa fuskar shi yay a kokarin shi na ya d'an yi
murmushi kafin yace "Ok in ka shiga pls ka basu hak'uri" Amadu yace "toh naga ma tayi bacci yanzu
d'azun ne da ta ga k'arfe 12 tayi naga kamar ta d'an damu tana cewa ko lpy shine har ta kira wayarta sau
biyu ba'a d'aga ba sai na nuna mata ba lalle in an fara da wuri ba don irin wannan ana yin African time
sai akai har tsakar dare wasu ma kwana ake" d'an lumshe ido Haisam yay ya bud'e yace mashi ya shiga
gida ya gode sosae yayi mashi saida safe ya juya idon Haisam akan shi har ya shiga gidan ya maido kopar
ya rufe, hannu Haisam yasa ya dafe forehead d'inshi gaba d'aya ran shi a cunkushe yake rashin
kwanciyar hankali ta hana yaji zafin zazza6in daya rufe shi ya d'an d'auki lokaci a haka shi kadae kaman
Aljani acikin tsohon dare daga baya ya cire hannun daya dafe goshin ya rufe kopar da Fatuu ta fito kafin
ya zagaya driver side ya bud'e ya shige bai yi tunanin zuwa gidan Hajiya ba duk da yasan ko ya koma Gra
ba iya k'arasa aikin da ada shine zai maida shi can d'in ba, bayan ya tashi Motar ya juyata ya koma Gra,
lokacin da Amadu ya shiga gidan har ta shige d'aki shima nashi ya shige tana shiga ta nufi gado ta aje
ledar maganin da purse a gefe tay zaune tana ta sakin ajiyar zuciya a hankali can ta kai kwance ta kife
fuskarta a jikin katifa kwalla suka fara gangaro mata abunda bata ta6a tunani zai faru da ita bane ya
farun wai Ya Haisam ne yay raping d'inta wani ma in yaji wannan Maganar ai ba zai ta6a yarda ba wllh ita
yanzu shikenan tasan ko aure tay mijinta bazai ta6a d'aukarta da daraja ba in ma ya zauna da ita kenan,
runtse idonta tay tasa kuka mai ta6a zuciya ta fara raya miyasa Ya Haisam zai mata haka miyasa Ya za6i
ya cutar da ita har hakane ko dai Khalid da kowa yasan halin shi ne bai cutar da ita kamar yadda Haisam
yay ba shi da ma yake da aure wata zuciyar ce ta fara kokarin k'are shi tana ayyana mata sharrin shaid'an
ne ba komae ba tunda shima ai tasan ba halin shi bane ko, wata zuciyar kuma tace koda ba halin shi
bane dama ya so ya aikata mata hakan tunda ai ta rok'e shi amman yak'i saurarenta kuma dama yana yi
mata wasu abubuwa da bai saba mata ba ko jiya a parlon shi ai saida ta gan shi yana kallon mata boobs
hakan na nufin sha'awarta yake! tana yin wannan tunanin ta k'ara sautin kukanta abun da ciwo Mutumin
da take tsananin k'auna amman shi sha'awarta yake ta yadda har ya kasa dannewa saida yay mata
wannan aika aikar saida tay mai isar ta kanta na kife kafin ta rarrashi kanta ta yanke a ranta bazata bari
kowa yasan abunda ya faru ba kuma ba ruwanta da Ya Haisam ta fita daga harkar shi daga yau wata
zuciyar ta raya mata kar tace haka ta bari ya zo suyi Maganar da yace goben ta raya koma yazo ai bai
wuce yace zai bata hak'uri ne ba wani abu ba, "in kuma yace zai aure ki fa??" ta sake raya mata shiru tay
tana kikkafta ido k'arshe ta yanke tasan hakan ma ba mai yuwu bane mutumin da duka shekara d'aya da
rabi kenan da auren shi koma ba haka ba taya Aunty Fanan zata amince ya aureta ta san hakan ba mai
yuwuwa bane, "in shi yaga zai auren ki duk abunda zai faru ya faru fa?" Wata zuciyar ta k'ara raya mata
wannan karon yunk'urawa tay ta tashi zaune fuskarta a tamke a fili tace "Bazan Aure shi ba wllh tunda
ba don yana sona zai aure ni ba sai don ya goge laifin da ya aikata man ba zan ta6a amincewa ba yaje
yaci gaba da zama da matar shi da yake so" idanunta ne suka sauka akan ledar magungunanta ta kai
hannu ta d'aukko ta tana kallo ta raya yakamata ta 6oyeta can kuma tay tunanin dole fa sai tayi wankan
tsarki kuma, shiru tay zuciyarta ta fara tariyo mata farkon yadda abun ya faru a hankali ta lumshe ido
tana ta tuno lokacin kafin ta fita hayyacinta ji take inama ace da aure suka aikata hakan cike da so da
k'aunar juna wasu kwalla ne masu zafi suka fara gangaro mata tunowa da haramun suka aikata da sauri
tasa tafin hannunta cikin kuka take fad'in "Ya Allah ka yafe man na tuba bazan k'ara ba ba hali na bane
sharrin shaid'an ne" can ta mik'e tana tafiya a hankali ta nufi wardrobe ta aje ledar magungunan bayan
ta rufe tsaye tay tana tunanin yadda zata yi wankan in tace ta bari saida safe to saidai fa ta bari har gari
ya waye bata yi sallar Asuba ba tunda ba yadda za'ai ta yi da Asuba sanin lokacin gwaggo ma ta tashi
wata zuciyar ce ta ayyana mata kawae tayi yanzu tay tsaye tana jin tsoron kar ta je tana yi gwaggo kuma
ta fito taga tana yin wanka cikin tsakar daren nan wata zuciyar ce ta raya mata in ma ta kamata sai tace
sun dawo ne jikinta ba dad'i ta kasa yin bacci shine ta fito ta watsa ruwa still kaman hakan bai kwanta
mata ba don gani take kaman duk da haka zata gane can dae tay shahada ta nufi wajen kitchen taje don
tasan ana aje ruwan zafi a Electric kettle koda yaushe cikin sa'a kuwa akwai ruwan ta d'aukko butar gaba
d'aya cikin fad'uwar gaba ta fito ta nufi Toilet har ta shige ba wanda ya fito, a ciki ta had'a ruwan tay
wankan ta d'an zauna wasu duk da bata sa gishiri ba bata d'auki lokaci ba Saboda tsoron kada wani yazo
ya ganta doguwar rigar ta maida ta d'aukko butar ta fito saida ta cikata da ruwa ta lalla6a ta maida ta
kitchen d'in ta jona ta fito don tasan in ya tafasa zata mutu, har saida ta saki ajiyar zuciya ganin ta shige
d'akinta ba tare da wani ya ganta ba wardrobe ta nufa ta fiddo doguwar rigar bacci ta cire ta jikinta tasa
ta duk'unk'une wadda ta cire ta cusa ta a cikin Wardrobe d'in daga haka ta nufi switch ta kashe hasken
d'akin kafin ta nufi gado ta haye taja bargo ta lullu6e ba laifi sosae rad'ad'in da take ji ya rago sai dae
k'afafunta ne bata iya rufe su ba kamar in tana tafiya, lamo tay idanunta a waje tana kallon sama ta shiga
ayyana yanzu da ace aure tay hakan ta faru tasan da yanzu mijinta na nan yana tarairayar ta amman
yanzu gata tamkar mara galihu iya cuta dae ya Haisam ya cuceta wllh, a hankali take goge kwallan dake
zubo mata ba laifi zazza6in ya sauka saidae jikinne duk ba dad'i take jin shi.........

Lokacin da ya isa bakin gate d'in yana yin horn sau biyu Security yazo ya bud'e mashi ya shige, inda ya
parker ta d'azun da suka zo anan ya k'ara parker ta bayan ya kashe d'an jimm yay kaman ba zai fito ba
can ya kai hannu ya bud'e ya d'auki wayar shi dake gefe ya fita ya nufi cikin gidan, yana shiga Bedroom
d'in idanun shi suka sauka kan gadon ya nufe shi a bakin gadon ya zauna idanun shi akan blood stains
d'in dake jikin Farin bedsheet d'in tunanin yadda zai yi da shi ya fara zuciyar shi ta raya mashi wankewa
yakamata yayi ya mik'e ya kai hannu ya fara cire bedsheet d'in bayan ya cire yana ruk'e da shi ya nufi
hanyar corridor ya shiga laundry room ya bud'e Washing machine ya saka ya fara wankewa bayan ya
gama koda ya fiddo shi sai yaga stain d'in na nan amman dai ya d'an rage zuciyar shi ta bashi ba lalle ya
fita ba don ya bushe a jiki tunanin ko ya sa hannu ya wanke yaga in zai fita yay saidae shi bai iya wankin
hannu ba don iya underwear d'in shi dana Fanan yake wankewa suma kuma a washing machine can dae
ya yanke gwada wankewa da hannu ya juya yana tunanin a inda zai wanke don ba bucket a toilet d'in sai
dai ya tafi part d'in Mom d'in shi ya d'aukko kuma da akwae tazara, dubara ce ta fad'o mashi ta ya toshe
hanyar fitar ruwa ta bathtub d'in ciki sai ya wanke anan, bayan ya toshe a ciki ya k'ara wanke shi sam bai
sha wata wahala ba duk da ba yin wankin yake ba saidae shi ba rago bane don ma jikin yayi weak ga
zazza6in dake damun shi don har yanzu akwae shi a jikinshi cikin sa'a sai gashi ya fita don ma ba bleach a
toilet d'in duk da bai sha wahalan wankewa sosae ba tunda fari ne, bayan ya d'auraye shi tunanin inda
zai shanya shi yay ya yanke saidae ya fita can ta k'opar bayan gidan nan keda fence ta hanyar zuwa
swimming pool har zai tafi can idon shi ya sauka akan k'opar laundry d'in yaga lafiya lou zai iya d'aura shi
anan yay hakan sannan ya dawo ya wanke itama jallabiyar shi da ta 6aci, saida yay wanka ya tsarkake
jikin shi ya canzo wata jallabiyar sannan ya dawo cikin bedroom d'in ya nufi inda kujeru suke ya zauna ya
d'aura ha6ar shi kan hannuwan shi da ya dunkule tunanin halin da Zarah take ciki ya shiga yi gaba d'aya
tsananin tausayin ta ya gama mamaye mashi zuciya ba kamar in ya tuna yadda yay da Fanan a first night
d'in su nan da can ma sai ya d'auketa ya kaita ta dingi yi mashi rigima, gashi daga yadda Al'amarin ya
faru yasan Zarah ta fita jin jiki kawai don tana da k'arfin hali ne, slowly ya lumshe idonshi underneath his
breath ya furta "Am very sorry Zaraah I knew i hurt u..." tunanin ya kirata yaji halin da take ciki yay ya
bud'e idanun a hankali kafin ya yunk'ura ya mik'e ya nufi can gefen gado inda ya aje wayar shi Lokacin da
ya shigo saida ya kalli time biyu da rabi har ta wuce shiru yay yana tunanin ko ya kiratan can dae ya
bud'e wayar yay sending mata kira lokacin har bacci mai nauyi ya d'auketa hakan yasa har kiran ya yanke
ba'a d'aga ba ya sake wani kiran shima ba'a d'aga ba tunanin ko tayi bacci ko kuma fushin da take ne
yasa bata d'auka ba yay ya aje wayar akan mattress yai zugudum can ya mik'e ya nufi gaban mirror ya
jawo drawer chest ya fiddo wani d'an madaidaicin first aid box bayan ya d'aura saman mirror ya bud'e
Panadol ya d'aukko ya 6alli guda biyu ya maida bayan ya rufe box d'in ya maida shi inda ya d'aukko
wurin kujeru ya nufa walking very slowly ya zauna ya d'auki robar ruwa a cikin kayan Abincin da suka ci
ya bud'e ya sha maganin kafin ya rufe ya ajeta, maida bayan shi jikin kujeran yay ta d'age kai hannun shi
d'aya dafe da forehead d'inshi, ya d'an d'auki lokaci a haka can ya d'ago ya mik'e ya kwashe kayan ya fita
dasu daga d'akin bada jimawa ba ya dawo ya nufi Corridor toilet yaje ya d'auro Alwala bayan ya dawo ya
shimfid'a prayer mat ya kabbara sallar Nafila raka'a hud'u yay don k'arfin hali kawae yake bayan ya d'aga
hannu ya d'an jima yana Addu'oi kafin ya mik'e ya nufi gado har wani duhu duhu yake gani ko tunanin
shimfid'a wani bedsheet bai yi ba a haka ya hau kan mattress d'in yaja duvet ya lullu6e jikinshi har kan
shi nan da nan kuwa temperature d'in jikin shi yay high sosae numfashin shi ya fara fita da zafi a haka
bacci ya d'auke shi amman bana dad'i ba, gab da kiran sallar Asubar farko k'arar wayar shi ta tashe shi
alamar ana kiran shi ya bud'e fuskar shi duk ta canza kala da alamun mamakin mai kiran na shi a time
d'in, yunk'urawa yay ya tashi zaune ya kai hannu daga d'an gaban shi ya d'auki wayar yana kai idon shi
kan screen d'in ganin sunan mai kiran har saida gaban shi ya d'an Fad'i ya shiga tunanin ko lafiya jiki a
sanyaye yay picking kafin ya kara a kunne..,

Har aka gama Sallar Asuba Fatuu bata farka ba rashin jin motsinta yasa gwaggo bayan ta gama azkar ta
mik'e ta nufi d'akinta don tasan ta dawo lokacin da ake kiran sallar farko da ta fito ta d'aga labulan d'akin
ta ganta a kwance, lokacin da ta shiga tana a kudundune har sannan gwaggo ta tsaya a gaban gadon ta
fara kiran sunanta shiru har sau kusan ukku hakan yasa ta d'an duk'a ta kai hannu tana d'an bubbuga
jikinta can ta fara motsi a hankali ta cire bargon dake rufe da fuskarta ta d'an juyo da fuskar da yake taba
gwaggo baya ba saitin da take ba ta ke kallo koda tay arba da fuskarta da sauri tasa hannu ta dafe goshin
ta ta yarda har idanuwanta ta d'an rufe ganin ta farka yasa gwaggo ta zauna a bakin gadon tana kallonta
tace "Wane irin bacci kike ne haka baki san Asuba tayi ba ga gari har ya fara washewa baki tashi kin yi
salla ba" d'an yamutsa fuska tay murya k'asa k'asa tace mata bata san gari ya waye ba bari ta tashi, ganin
ta dafe kai yasa gwaggon tambayarta lafiya ta dafe kai haka wani irin bugu kirjinta ke yi tay k'ok'arin
daidaita Maganar ta tace "Wllh kan ne ke man wani irin ciwo" da d'an alamun mamaki gwaggon tace
"ciwon kai kuma to ya akai?" abu Fatuu ta had'iye ta fara tunanin abunda zata ce mata can tace "Wurin
ne hayaniya tayi yawa sosae sai faman kid'e kid'e ake harda yan police band fa ga masu irin kid'an su na
gargajiya in suka buga har tsakiyar kan Mutum wllh" yar dariya gwaggo tay tace to tunda shagali suke ai
dole suyi kafin ta kuma cewa "gashi kuma kun dad'e sosae don har sha biyu ta wuce fa idona biyu ina
dakon ki amman shiru ga wayar ki na kira ba'a d'aga ba........" Da sauri Fatuu ta tari numfashinta tace "a
cikin Mota na barta kuma ba'a fa fara ba da wuri anata jiran wasu manyan mutane da yake bikin fa d'an
sarkin inyamurai ne sai wurin sha d'aya in ma bata wuce ba aka fara da aka gama da Aunty Feenah ma
akace in bi gidanta wai in kwana ni kuma na matsa sai na dawo tunda ba haka mukae da ke ba" jinjina
kai gwaggo tay da d'an murmushi tace "Allah sarki ai da kin bitan ba wani abu dama dai aji shiru shine
matsala amman indai ansan inda ake ai ba komae" juyar da kai Fatuu tay gefe jin k'walla na son zubo
mata don wani irin tausayin gwaggon taji ta bala'en yarda da Haisam ta yadda ko kusa ranta bai bata
wani abu mara kyau a game dashi, kokarin mik'ewa ta fara yi tana fad'in ta tashi tay sallar in tayi
breakfast sai tasha magani akwae ruwan zafi a cikin flask a cikin kitchen da bread ita bari taje ta kwanta
ta huta tunda yau bazata aiki ba daga haka ta fuce, wani irin kuka mai cin zuciya Fatuu ta saki zuciyarta
ta raya mata yanzu fa ba kuka bane a gabanta ta fara tunanin yadda zatai jinyar kan ta ba tare da an
gane ba don a iya tafiyarta ma kawae da gwaggo ta gani to tabbas zata iya zargin wani abu koma ta gane
yin wannan tunanin yasa da sauri ta goge kwallan ta fara k'ok'arin sauka daga kan gadon a hankali ta fara
tafiya k'afafu a wawware tana d'an yamutsa fuska don wurin yay tsami tana buk'atar ruwan zafi, saida ta
d'an lek'a fuskarta ta labule ta kalli kopar d'akin gwaggo tsoro take kada ta fita itama ta fito su had'e ta
d'an d'auki lokaci a haka can dai tay Addu'a ta yaye labulen ta fita gabanta na wani irin bugu tamkar ana
mata luguden ta6are, kasa tafiya tay tayi tsaye a wurin can ranta ya bata ta lek'a taga mi gwaggo ke yi ta
nufi d'akin a yadda take tafiya har ta k'arasa without making any sound a hankali hannu na rawa ta d'an
d'aga labulan ta hangota saman gado ta lullube rabin jikinta har saida taji wani sanyi ta saki labulan ta
juya, sosae ta d'aure tana cije baki ta rink'a tafiya yadda zata d'an yi sauri ta nufi kitchen ta d'aukko
electric kettle ta nufi Toilet bayan ta fito, saida ta zauna ruwan zafi sannan ta d'auro Alwala, zaune tay
bayan ta gama sallan da k'yar ta shiga tunanin yadda zatai don yadda take tafiya tsab asirinta zai tonu
tana ta sak'e sak'e can dubara ta fad'o mata ta ta tafi Makaranta kawae kafin gwaggo ta tashi ko Kawu
Amadu don shima ta san yanzu bacci yake tunda weekend ne sai d'an anjima zai tashi ya bud'e shago da
wannan tunanin ta lalla6a da sauri ta tashi bayan ta d'auke abun sallan ta nufi Wardrobe ta fiddo wata
doguwar riga ta zumbula ta ciro yar madaidaiciyar hijab ta saka lokacin idanunta suka sauka kan ledan
magungunan ta d'aukko su bayan ta rufe ta d'aukko jakar goyonta da komae na karatun ta ke ciki ta
bud'e ta saka magungunan ta sake bud'e wardrobe ta d'auki k'ananun kaya kala biyu da undies don acan
tana da kaya bayan ta rufe wardrobe d'in ta d'auki wayarta dake ajiye gefen gado itama ta saka ta kauda
duk wani abu da zata kauda daga haka ta nufi hanyar fita hannunta ruk'e da jakar saida ta lek'a ta
tabbatar ba kowa sannan ta fita ba sai na fad'i yadda gabanta ke fad'uwa ba sai Addu'a take a cikin ranta
cikin sa'a har ta kai zaure bata ji motsin wani ya fito ba ta bud'e gidan wanda sakata ce kawae Amadu ya
sa da ya dawo daga sallar Asuba.

Lokacin da ta fito wajen kwalam ba mutane bata bi ta hanya ba ta lungun gidan Hajiya tabi tana yi tana
dafa bangon gidaje in ta gaji sai ta d'an tsaya ta huta kafin taci gaba tana cikin hakan tazo daidai kangon
da su goga suka so raping nata wanda yanzu gida ne masu shima har sun dawo yanayin fuskarta ne ya
canza ta shiga tuno yadda abun ya faru a lokacin har Haisam yazo ya ceceta da kuma lokacin da ta je part
d'in shi daga baya har yace mata dama ita yar iska ce, a hankali kwallan da suka taru suka fara gangaro
mata a fili ta furta "Ya Haisam yanzu ai kasan in ni yar iska ce ko....." Cigaba da lalla6awa tay tana yi tana
cigaba da goge kwalla ta d'auki lokaci kafin ta kai bakin hanya don ba ranar aiki bace sam bata ga wani
abun hawa a layin ba saida taje bakin hanya nan ma saida ta d'an yi jiran samun Napep don babu sai
masu mashin ne keta tsayawa tana girgiza masu kai don tasan ba iya hawa zata yi ba daga baya ta samu
Napep d'in ta fad'i mashi inda zata je suka tafi, lokacin da suka isa da kanta ta rok'i mai gadi kan ya bari a
shiga da ita ciki bata lafiya ne da yake sun saba sosai yace to amman yay sauri ya fito suka shige bayan
tayi mashi godiya, har bakin Hostel ya kaita bayan ta fito ta biya shi shima saida yay mata Allah ya
sawak'e tay mashi godiya sannan ya juya Napep d'in ya tafi, harta shige bata ga kowa ba anata baccin
weekend wad'anda suka rage a hostel d'in wanda ba yan gari ba don yan cikin gari da garuruwan kusa
duk weekend suke tafiya wani lokacin, data zo hawa bene nan abun ya zama aiki tana yi tana dafa bango
tana runtse ido had'i da cije baki a haka har ta haye ta nufi d'akin su a cikin bag d'inta ta fiddo makullin
da yake hannunta don Fauzy ma ta tafi gidan Aunty Mareeya Weekend, bayan ta bud'e ta shige ta turo
kopar ta nufi gado ta zauna ta aje jakar a gefenta har taji d'an sanyi yanzu sai tunanin abunda zata fad'a
ma gwaggo in ta kira ta shiga yi, tana ta zaune jugum ga wata irin yunwa da take ji tun a gida can ta
mik'e don ta samu abunda zata ci d'an gas d'insu ta kunna ta d'aura ruwa acikin yar babbar tukunya ta
koma gefen gado ta zauna har ya tafasa sannan ta tashi ta d'ibi wanda zata had'a tea cikin d'an Flask ta
saka Lipton kafin ta rufe sauran ruwan zafin ta juye a cikin bucket ta d'an sa gishiri sannan ta fita zuwa
toilet, sosae taji dad'i bayan ta fito saida ta soya k'wai sannan ta had'a tea d'in ta had'a da biscuit ta ci
data gama tasha magungunan ta haye gado ta kwanta ta lullu6e rabin jikinta tay ma bango k'uri
zuciyarta ce ta raya mata Ya Haisam yace zasu yi Magana gashi har yanzu bai kira ba balle ma yaji ya take
d'an ta6e baki tay ta raya ita tasan ba wata Magana data wuce ya bata hak'uri, a hankali ta fara lumshe
ido a haka har bacci Yay awon gaba da ita. Lokacin da gwaggo ta fito sam bata yi tunanin tashin Fatun ba
don tasan tace mata kanta na ciwo hakan yasa ta k'yaleta ta wuce kitchen koda ta shiga bata gane bata
yi breakfast ba don Amadu ya shiga ya d'iba sai tay tunanin ko Fatun ce itama had'a nata tay ta koma
d'aki, bayan ta gama ta fito da kayan ta maida kitchen kafin ta fara kokarin gyara gidan a haka har
lokacin d'aura Abincin rana yay ta d'aura tana cikin yin girkin tace bari ta duba Fatuu baccin yayi yawa ko
ciwon kan yayi tsanani ta nufi d'akin ta..........

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2046*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


..........Tana d'aga labulan d'akin ta sauke idanunta akan gadon dake wayam ba kowa da d'an mamaki ta
k'arasa shiga don ta tabbatar da abunda take gani, tabbas ba Fatuu kwance tsaye tay ta fara ayyana ina
taje ne acikin ranta can tace ko tana band'aki ne, sai kuma ta raya anya dae tana can tun d'azu fa tana
kitchen kuma bata ga fitowar ta ba in ba dai tun kafin ta fara aikin girkin ta shiga ba to amman mi zai sa
ta dad'e har haka ta jefa ma kanta tambaya, can dae ta juya ta fita daga d'akin ta nufi hanyar toilet don
ta tabbatar tun ma kafin ta k'arasa ta hango kopar shi a bud'e alamar ba mutum d'an tsayawa tay sai
kuma ta juya ta nufi hanyar fita daga gida, a bakin k'opa ta tsaya ta fara k'wala ma Amadu dake cikin
shago kira ya bud'e ya lek'o ganin itace yasa shi k'arasa fitowa ya nufo inda take ya tsaya yana kallonta
yace gashi tambayar shi tay ina Fatuu da d'an mamaki yace "bata ciki ne?" Gwaggon ta d'aga kai tace
mashi bata nan ta duba har toilet d'an jimm yay kafin yace "gaskiya ni banga ta fito ba tunda na bud'e
shagon" shiru gwaggon tay tana tunanin to ina ta shiga Amadu ya katseta da tambayar ta kira wayar ta
ta girgiza mashi kai alamar a'a yace to bari ya kirata ya juya ya koma shagon, bayan ya fito ruk'e da
wayar ya dawo gaban gwaggon ya fara k'ok'arin kiran Fatuu lokacin da kiran ya shiga tana ta sharar bacci
har kiran ya yanke bata ji ba sai da ya k'ara kira ne can a cikin bacci ringing d'in ya kai mata ta fara motsi
a hankali ta fara bud'e idanunta jin wayan nata k'ara yasa ta yunk'ura ta tashi zaune tana kai hannu zata
d'auka kiran ya katse, bayan ta d'auka ta duba mai kiran nata har saida gabanta ya fad'i ganin sunan
Kawu Amadu tana haka sai gashi ya sake kira tay shiru kaman bazata d'aga ba can dai tay picking ta kara
ta a kunne daga can bangaren Amadun ya kira sunanta ta amsa a hankali ya tambaye ta tana ina ne tace
mashi ta tafi Makaranta ya maimata abunda tace jin haka yasa ya mik'a ma gwaggo ta amsa ta kara a
kunne ta kira sunanta itama ta amsa mata had'i da gaishe da ita tace "naji kin ce kina Makaranta lafiya
kika tafi baki fad'a ma kowa ba?" Had'iyar abu tay ta fara tunanin k'aryar da zata mata cikin yar rawar
murya tace "d..dama na manta ban fad'a maki ba da yake jiya baki nan na dawo akwae wani malamin
mu to ba'a cika gane abunda yake koyawa ba ana ta mashi complaining shine ya ware mana lokaci a
cikin wannan weekend d'in da safe yace zai yi mana lesson tunda lokacin da yake dashi cikin ranakun aiki
bai isar shi ya rink'a yin bayani sosae yadda za'a gane" gwaggo dake sauraronta tace "to yanzu sai yaushe
zaki dawo?" shiru Fatuu ta d'anyi kafin tace "sai Allah ya kaimu Juma'a"

"Har sai Juma'a kuma ba da safe zaku rink'a yin lesson d'in ba in aka gama ai sai ki taho gida ko?" Fatuu
tace "eh amman da yamma ma zamu yi group Assignment" sauke yar ajiyar zuciya gwaggon tay tace "to
amman shi yayan ki fa daya maido ki yace zai rink'a kaiki baki tunanin zaiga kaman kin k'i jin Maganar shi
ko baki gode ba" d'an runtse ido Fatuu tay ta bud'e yanayin fuskar ta kaman zata yi kuka tace "Na fad'i
mashi ai" gwaggon tace Shikenan Allah ya bada sa'a Fatuu na gumshe kuka ta amsa da Amin da sauri ta
kife wayar akan katifa ta jingina da bango ta kifa fuskarta a tsakankanin cinyoyin ta wannan wace irin cin
Amana ce sukai ma gwaggo gaba d'aya ta yarda dasu ji yanzu daga fad'i mata hakan har ta amince, da
kanta ta rarrashi kanta bada jimawa ba aka kira sallar Azahar ta sauka daga kan gadon don tayi salla,
wasa wasa har dare bata ga kiran Haisam ba balle tasa ran zai zo suyi Maganar da yace bayan taci
indomie da ta dafa taje tay wanka ta zauna ruwa data dawo ta sha magungunanta ta kwanta saidae sam
ta kasa yin bacci abubuwa ne da yawa ke mata yawo a rai ba kamar rashin zuwan Haisam duk da ba wai
tana son zuwan nashi bane kawae sai take ganin kaman bai damu da halin da ya jefatan bane daga baya
ta dasa tunanin yadda rayuwarta zata kasance nan gaba ba kamar in tayi aure, "anya ma ni zan yi auren
kuwa?" ta ayyana a ranta sai dae itama tasan fad'a kawae take ba yadda za'ai ta rayu ba tare da ta yi
aure ba tasan ai baza'a ma ta6a k'yaleta ba, tana ta tunane tunane sai can dare bacci ya d'auketa, Washe
gari Lahadi haka taci gaba da jinyar kanta ranar ma har dare yayi Haisam d'in bai kira ba a lokacin Fatuu
har ta gama yankewa ranta dama dad'in baki ne kawae yay mata ba wani abu ba, bayan sallar isha sai ga
Fauzy ta dawo da mamaki ta shigo d'akin ganin kopar a bud'e idanunta suka sauka akan Fatuu dake
kwance saman gado hannunta ruk'e da waya tana ganinta ta fara mata murmushi ta nufi gadon da take
ta zauna a gefe surprisingly tace "wai da gaske ke ce?" Tana murmushi tace "a'a Aljana ce" gyara zama
Fauzy tay sosae tace "amman ya akai na ganki anan bacin kin koma gida?" d'an yamutsa fuska Fatuu tay
tace "to na dawo" waro ido Fauzy tay tace "Don Allah da gaske?" Kai ta d'aga mata alamar eh Fauzy tace
"to ina Ya Haisam d'in yake da kika dawo ko har ya tafi" d'an shiru tay idonta a kanta ta rasa wace amsa
ma zata bata can tace "Ya tafi Abuja" d'an tura baki Fauzy tay tace "to har kin siye mana zuciyar tashi ne
da kika bari ya tafi" d'an murmushi kawae Fatuu tay a cikin zuciyar ta ta raya in ni ban siye zuciyar shi ba
shi ai ya siye man Mutunci bin ta da ido Fauzy tay ta kalleta suka had'a ido duk sai ta tsargu can taji
Fauzyn tace "ya naga kamar wani abu na damun ki har face d'in ki ta nuna?" damm k'irjinta ya buga tasa
hannu tana d'an Sosa gefen kanta tace ba abunda ke damunta kawae bacci take ji kuma ta tsaya latse
latsen waya tay Maganar tana niyyar komawa ta kwanta bayan ta kwanta Fauzy dake kallonta tace
"amman yau kika dawo ne?" Kai ta d'aga mata alamar eh ta sake cewa taci Abinci ne Fatun tace eh taci
d'azun gyad'a kai tay ta mik'e tana fad'in ga wani Abincin ta taho dashi ta tashi su ci ta tambaye ta
minene tace tuwon shinkafa ne miyar d'anyen kubewa Fatuu tace to ta zuba masu, suna cikin ci Fauzy
tace bata ba ta labarin dinner d'in data fad'i mata a waya zasu da Ya Haisam, d'an yamutsa fuska tay
kafin ta d'an bata labarin sama sama bayan sun gama suka sha lemun data had'o masu dashi Fatuu na
son tasha magungunan ta amman ta rasa yadda zatayi don tasan da Fauzy ta gani sai ta tambaye ta
dalilin shan su tunda tasan magungunan na miye gashi ita ba wani rauni ke a jikinta da zata gani ba
shiyasa ma ta bar su a cikin bag d'inta bata fiddo su waje ba gudun hakan k'arshe kawae sai tay
kwanciyar ta Fauzy na ce mata bazata duba book d'inta ba tace mata bacci take ji. Washe gari Monday
suka cigaba da zuwa class kaman ko yaushe ba laifi tafiyarta ta d'an daidaita in dae ba kallon k'urulla kai
mata ba bazaka gane ba daidai take tafiya ba don sosae ta d'aure take tafiya yadda ba za'a zargi wani
abu ba musamman Fauzy, wasa wasa sai gashi har Friday tayi ba Haisam ba dalilin shi balle kiran wayar
shi bayan sallan juma'a suka fito tare don tafiya weekend saida aka fara sauke Fauzy Fatuu ta rok'i mai
Napep zata d'an shiga yace to suka shiga gidan tare ta gaisa da Aunty Mareeya itama saida ta tambayeta
Haisam tace mata ya koma kawae daga baya sukai sallama Fauzy ta rakota har bakin Napep suka k'ara
yin bankwana ta tafi, a k'opar gida suka tsaya bayan ta fito ta biya mai Napep d'in ta nufi ciki don shagon
Kawu Amadu a rufe yake, lokacin da ta shiga d'akin gwaggo ta nufa ta d'aga labule da yar sallama ta
hango gwaggon kwance tana bacci d'an murmushi tay har zata juya ta fita taji ta kira sunanta ta juya ta
kalleta suka had'a ido ta nufeta ta zauna a bakin gadon tana ta mata murmushi itama gwaggon tashi tay
zaune ta jingina bayanta da kan gadon tace mata an dawo Fatun tace eh ta gaishe da ita ta amsa kafin ta
tambaye ta Fauzy tace yanzu suka sauke ta a gidan Aunty Mareeya ta d'aga kai shiru ta biyo baya idon
gwaggo a kanta ita kuma ta sunkuyar da nata still murmushi take can taji gwaggon tace taje ta zuba
Abinci tace to ta mik'e ta nufi hanyar fita tana ruk'e da jakar goyon ta jikinta sanye da doguwar rigar
Atamfa A-shape ta yafa gyale dama ko ba don abunda ya faru da ita ba duk in ta san zata zo gida su
had'u da gwaggo bata sa matsattsun kaya don tasan da gwaggon ta gani sai tayi fad'a kuma dama tunda
abun nan ya faru da ita bata sa kayan da suka matse ta tafi zumbula doguwar rigar material, d'akinta ta
nufa bayan ta shiga ta aje jakar a gefe ta nufi bakin gadonta ta zauna duk yadda taso kar ta damu da
rashin kiranta da Haisam bai yi ba ta kasa abun ya matuk'ar d'aure mata kai tunaninta dama kenan
k'arya yake mata, ita dama tasan ba wani abun da zai iya yi ya gyara laifin shi kawae dae ya cuceta, jiki a
sanyaye ta mik'e tana kokarin maida k'wallan da suka tarun mata bayan ta fita kitchen ta nufa ta zubo
Abinci, da daddare bayan tayi sallar isha ta watso ruwa ta zura doguwar riga yar kanti mai gajeran hannu
ta saka hula akanta ta nufi d'akin gwaggo a zaune ta isketa akan kujera tana kokarin kunna Radio tana
ganinta ta sakar mata murmushi itama Fatuu shi take mata ta zauna daga gefenta tace "wai gwaggo
miyasa baki son zama a Parlor ne kullum indae kina gida kin fi son ki zauna a d'aki?" yar dariya tay tace
"nafi sabawa da d'akin ne ni mantawa ma nike da wani Parlor" d'an tura baki tay tace "ga kayan kallo
can maimakon kije ki kallo sai ki zauna kina ta faman jin radio sai kace wata tsohuwa" dariya sosae
gwaggo ke yi tace to ai tsohuwar ce ko Fatun tace "a'a da sauran ki Allah" murmushi kawae tay sai kuma
tana kallon Fatun tace "Oh ya mai jiki kuma" kallon rashin fahimta Fatuu ta bi ta da shi ganin haka yasa
gwaggon cewa "Senator Alee na Hajiya nike nufi, ni kwata kwata ban sani ba sai ranar Laraba nan data
wuce na shiga gaida Hajiyar anan Saude ke fad'a man wai ashe basu K'asar harda shi Haisam suna
Germany nace ai ban sani ba ke kuma baki fad'a man ba ko ta waya" zuru Fatuu tay zuciyarta ta ayyana
ashe bai K'asar muryar gwaggo ta katseta da fad'in "Bawan Allah, Allah ya bashi lafiya ya tashi kafadun
shi" a hankali Fatuu dake ta kallon ta tace Amin suka d'an yi shiru can tace ma gwaggon miya ke damun
shi ne, da d'an alamun mamaki tace ba dae bata san bai lafiyan ba Haisam bai fad'i mata ba a
dabarbarce Fatun tace "....a'a na san bai lafiyan amman ban san abunda yake damun shi bane" gyad'a
kai gwaggo tay da alamun damuwa tace "yanke jiki yay ya fad'i to an kaishi Asibiti nan Abujar daga baya
likitocin suka bada shawarar ayi saurin fita dashi don ya kusa samun stroke Saude tace a ranar Juma'ar
da ta wuce da Asuba aka kira Hajiyar ake sanar mata tun kafin gari ya waye suka tafi Kano ita da Haisam
d'in daga can suka hau jirgin Abuja" gyad'a kai Fatuu tay tace Allah ya bashi lpy mai dorewa gwaggo ta
amsa da Amin shiru tay da zuwa tayi taja gwaggon su je suyi kallo amman jin wannan Maganar yasa ta
fasa ta mik'e tace mata bari taje ta kwanta taji bacci take ji ta d'aga mata kai tace Allah ya tashe su lpy,
bayan ta koma d'aki zaune tay a gefen gado tama rasa tunanin da zatayi kenan wannan dalilin ya hana
shi zuwa suyi Maganar kaman yadda yace can ta ayyana to amman ai ko a waya dai ya kirata tunda
yanzu kwana takwas kenan da faruwar abun k'arshe dai ta yanke kawae bashi da abunda zai fad'a mata
ne shiyasa bai kiratan ba a hankali ta kai kwance ta lumshe ido. Washe gari Asabar tana gama yin
Breakfast ta gau gyara gidan tana cikin gyara d'akinta wayarta ta fara ringing ta aje bedsheet d'in da take
kakka6ewa ta d'aukko wayar daga kan dressing mirror tabi kiran da kallo ganin bak'uwar lamba kuma da
gani bata Nigeria bace bakin gadon ta nufa ta zauna ji take kaman kar ta d'aga kiran don tana tunanin ko
Haisam ne gab da kiran zai katse tay picking ta kara a kunne tun kafin tay magana taji ance "Hello
Kanwata kuma K'awata ya kike?" Zaro ido Fatuu tay ta washe baki jin muryar Haulat tace "Na'am Haulat
ashe kece naga ba number d'in ki bace wannan" tace mata eh ta mijinta ce tana ta washe baki tace "to
ya kike ya Nijar d'in?" itama Haulat bakin ta a washe yake tace mata nijar lafiya lou Fatun tace "kwana
biyu sai inta trying layin ki bai shiga gashi tunda ki kai nauyi kin daina chat saboda ragwonci" tana jiyo
dariyar Haulat d'in kafin tace "ashe ma ragwonci ne ba zan ce maki komai ba yanzu sai kema kin samu na
Ya Haisam zan rama don nasan ke k'ilan ma ko wayar bazaki iya ta6awa ba" d'an yamutsa fuska Fatuu
tay bata ce mata komae ba Haulat d'in ta tambaye ta Haisam tace mata yana nan bai dad'e da zuwa ba
amman ya koma daga baya tace mata dama ta kira ne ta sanar da ita tayi D'iya Fatuu ta k'ara zaro ido ta
rufe bakinta da hannu guda kafin tace "Don Allah Haulat da gaske kike ko wasa" tana jiyo dariyar ta tace
Wllh ba wasa take ba ta haihu ran Alhamis da tsakar dare jiya aka sallamota yanzu haka ga babyn nan a
hannunta da tsananin mamaki Fatuu tace "ikon Allah abun ba wuya ni wllh banyi zaton kin kusa haihuwa
ba" Haulat na dariya tace "ashe abun ba wuya ki bari in lokacin da kema zaki haihun yayi zan tuna maki
sai ki tantance" Fatuu na dariya tace ai ita haihuwar ne kawai bata yi ba amman tasan komai su da ke
shiga Labour room kawae dae taga saurin abun ne daga lokacin da sukai wayar k'arshe, fira suka cigaba
da yi har Fatuu na rok'onta ta turo mata picture d'in baby tace in suka gama zata sa ya turo mata ta
tambaye ta zata dawo gida wanka ne tace mata eh amman sai an yi suna Fatun tace aikuwa dole su zo
suna amman sai Haulat d'in ta hau rok'onta kan su barshi ba sai sun zo ba ai da anyi sunan zata dawo
daga baya Fatun tace Shikenan tunda haka take so sukai sallama tace ta gaida mata gwaggo da Kawu
Amadu, suna gama wayar cike da zumud'i taje d'akin gwaggo tana ta washe baki ta sanar mata zancen
Haihuwar Haulat itama gwaggo tayi murna sosae tayi masu Addu'oi, bayan ta fito daga d'akin gwaggo
hanyar waje ta nufa dama d'an gyale ne d'aure a kanta ta ciro shi ta yafa shagon Amadu taje shima ta
sanar mashi yay murna sosae yayi mata Allah ya raya tayi D'iya sai faman washe baki take, saida ta
amshi sweets da chocolate Amadun na fad'in komi take so ba zai hanata ba kar shima in tazo da kayan
dad'i ta hanashi ta nufi gida tana dariya, da daddare bayan sallar Magrib ita da gwaggo suka tafi yin
barka gidan su Haulat d'in, Ranar Monday da safe ta gama shirin ta tsab na tafiya Makaranta bayan tayi
breakfast data fito d'akin gwaggo ta shiga tayi mata sallama tace mata sai yaushe tace Friday tasan zuwa
lokacin k'ilan Haulat ta dawo tana murmushi tace mata to Allah ya kaimu ta amsa da Amin ta tafi, bayan
taje Makarantar saida akai break take sanar ma Fauzy zancen Haihuwar Haulat ta hau murna tana fad'in
zuwa suna Nijar ya kama su kenan Fatuu na dariya tace to murnar ta koma ciki da anyi suna zata dawo
saidae su isketa gida tsuke fuska Fauzy tay tace ita gaskiya ba haka taso ba ta so zuwa Nijar don bata
ta6a zuwa ba Fatuu nata mata dariya, a ranar da daddare suna cikin fira Fauzy ta kalli Fatuu tace "wai ni
Zarah ina Ya Haisam ne kwana biyu ban ji kinyi Maganar shi ba?" bin ta da ido Fatuu dake zaune saman
gadon tay tana tunanin abunda zata fad'i mata can ta sauke ajiyar zuciya ta fad'i mata halin rashin lafiyar
da mahaifin shi ke ciki yanayin fuskar Fauzy ne ya canza cike da jajantawa ta yi mashi Addu'ar samun
lafiya, Ranar Laraba da yamma Fatuu na zaune tana yin Assignment Fauzy kuma ta fita wayarta dake
ajiye gefe tay k'ara alamar shigowar sak'o kallon wayar tay sai kuma ta aje biron hannunta ta d'aukko
wayar ta shiga cikin messages d'in lokacin data bud'e sakon da ya shigon wani irin bugu k'irjinta yay da
tsananin mamaki take kallon alert d'in 500k daga wurin Haisam lokaci guda yanayin fuskarta ya sauya
zuwa 6acin rai a ranta ta fara raya lalle ma Ya Haisam wato zai iya turo mata kud'i amman ba zai iya
kiranta ba ita ga uwar son kud'i ko a tunanin shi zai siyeta da kud'i ne, a yadda take ji da tasan yadda zata
maida mashi dasu da kuwa ta maida ranta ne ya bata ko ta kira Abbas ta tura mashi tace ya tura ma
Haisam d'in sai kuma tay tunanin zai zargi wani abu tunda ai ba yau ya fara turo mata kud'i ba kuma har
ta Account d'in Abbas d'in yana turowa cikin fushi ta fita daga cikin messages d'in ta wurga wayar gefe
taci gaba da abunda take tana yi tana jan tsoki koda Fauzy ta shigo bata fad'i mata zancen kud'in ba don
ta sa aranta bazata ta6a mashi kud'i ba, da daddare wuraren k'arfe goma saura sai gashi ya kira hakan
kuma ba k'aramin tunzura ta yay ba wato ya turo kud'i shine ya samu k'warin gwuiwar kiranta k'in d'aga
kiran tay har ya yanke wani ya sake shigowa k'arshe ma sai ta saka wayar a silent kawae, Ranar Friday da
safe suna yin breakfast jikinsu sanye da Uniform ba tare da sun saka Hijab ba Fatuu ta fara kokarin tashi
tana fad'in ta k'oshi Fauzy tay sauri ta gama su tafi, tana mik'ewa wani irin jiri ya kwashe ta da sauri tasa
tafin hannunta na dama ta dafe goshinta tana yin salati hakan ya ja hankalin Fauzy ta kalleta ganin halin
da take ciki yasa ta mik'e da sauri ta kamata tana tambayar ta lafiya, a gefen gado suka zauna Fatun na
maida numfashi da d'an sauri Fauzy dake kallonta tace "What's happening Zarah?" Sai lokacin ta cire
tafin hannun tace mata ba komae kawae data mik'e ne taji jiri ya kwashe ta amman yanzu lafiya lau,
d'aga kai Fauzy tay tace "Sannu Allah yasa ba Malaria ke son kama ki ba don kinsan yanzu haka take tai
ta sa mutum jin jiri ga matsanancin ciwon kai" shiru kawae Fatuu tay tace mata ta k'arasa su tafi yau
Friday yanzu sun makara tace to tama k'oshi bari su saka Hijab kawai su tafi, a saman gadonta ta
d'aukko masu hijaban ta mik'a ma Fatuu ta ta itama ta sa ta nufi wurin kayan shafan su dake jere saman
table ta d'aukko turare ta shiga fesawa bayan ta gama ta nufi Fatuu itama ta fesa mata koda k'amshin
turaren ya d'aki hancinta da sauri ta kauda kanta Saboda wani irin tashin zuciya da taji, bayan Fauzy ta
kauda komae da sukae amfani ta goya jakarta ta mik'a ma Fatun tata ta yunk'ura ta mik'e suka tafi,
sosae k'amshin turaren da Fauzy ta fesa mata ke damunta ji take kamar zata yi amai a haka har suka
k'arasa class d'in suna shiga Malamin su na Farko na shigowa, tunda ta zauna take yan juye juye tana
yamutsa fuska sam ta kasa natsuwa wani irin tashin zuciya ne ke addabarta can malamin na cikin bayani
taji wani irin yunkurin amai ya taho mata da sauri ta mik'e hannunta rufe da bakinta ta d'an bubbuga
shoulder d'in Fauzy alamar ta bata hanya koda ta kalleta ganin yadda take yasa da sauri ta mik'e Fatun
ta fita daga cikin seat d'in da gudu ta nufi hanyar fita gaba d'aya idanun yan class d'in ya koma kanta
harda malamin nasu dakatawa yay ya bita da ido gaba d'aya Fauzy ta rud'e sai zare ido take can ta kalli
malamin tace "Sir pls let me help her" kai ya jinjina mata da sauri ta nufi hanyar fita ta bi bayan
Fatuu................

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2047*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

..........A can k'arshen barandar Classes d'in su Fauzy ta hangota tsugunne bayan ta fito ta nufeta da sauri
tana zuwa ta duk'a ta dafa Shoulder d'inta tana kallon yadda take faman maida numfashi gaba d'aya ta
amayar da breakfast d'in da ta ci cike da damuwa Fauzy tace "Sannu Zarah abun har ya kai haka" shiru
tay tana cigaba da yin nishi ta d'age kai sama Fauzy ta sake cewa "to ko cikin ki ne ya 6aci?" a hankali ta
girgiza mata kai alamar a'a Fauzyn tace "to gaskiya ina tunanin Malaria d'in ce dai muje famfo ki wanke
Fuskar ki sai mu wuce cikin Asibiti kiga Doctor" sauke ajiyar zuciya tay tana kokarin daidaita natsuwar ta
a sanyaye tace "ba sai mun je ba Fauzy nasan Malaria d'in ce ma kawae in mun koma Hostel zan sha
magani" cike da damuwa Fauzy tace "to amman ai bamu da maganin Malaria d'in iya paracetamol ne sai
na ciwon ciki" tace "shikenan bari muga zuwa a tashi in ban samu sauk'i ba sai mu siya in mun fita" shiru
Fauzy tay ganin Fatun na kokarin tashi yasa ta kai hannu da sauri ta taimaka mata suka nufi famfo ta
wanke face d'inta sosae da bakinta ta sha ruwan kafin suka nufi Class, lokacin da suka shiga gaba d'aya
aka maido idanu kan su Malamin su dake tsaye yay mata sannu ta amsa kafin ya tambayi abunda ke
damunta Fauzy ta bashi amsa da Malaria ce ya jinjina kai suka nufi seat, tunda ta zauna ta kife fuskarta
akan desk nan da nan bacci ya kwasheta har akayi break sannan Fauzy ta tada ta ta tambayeta mi take
so ta siyo mata tay d'an shiru don ji take bata son komae can tace mata ta amso mata youghort kawae ta
amsa da to ta tafi, bada jimawa ba sosae ta dawo lokacin har taci gaba da yin baccin Fauzy ta tashe ta ta
bata bayan ta bud'e mata ta amsa a hankali ta fara kur6a Fauzy na mata sannu tana d'aga kai sai gashi
har ta shanye kuma bata ji zuciyar na tashi ba, sosae Fauzy taji dad'in ganin ta d'an warware har tana
dariya da suna magana koda malamin su ya shigo bata koma ta kife kan ba ta tsaya ta saurari abunda
yake koya masu, cikin sa'a har aka tashi bata sake yin aman ba suka nufi Hostel suna zuwa suka fara
shirin tafiya Weekend Fatun tace ma Fauzyn tazo suje gidan su tayi weekend d'in acan in Haulat ta dawo
sai suje tace to bari ta tambayi Aunty Mareeya, koda ta kirata ce mata tay Fatun ce bata lafiya zata kaita
gida daganan za tay weekend d'in a can Aunty Mareeyar tace Subhanallahi miya sameta tace mata ba
ciwo bane Sosae Malaria ce harda amai ta sata tayi mata Addu'ar samun sauk'i tace taje dama itama
gobe Daura zata je sosae Fauzy taji dad'i tayi mata godiya da Allah ya kiyaye hanya Fatuu ma nata
murmushin jin dad'i, gaba d'aya riga da skirt na lace suka sa sukai d'an makeup kowacce ta rataya jakar
goyonta bayan sun yafa gyalensu sun yi kyau sosae abun ka da farare a tare suka fita suka rufe d'akin
kafin suka tafi Lokacin k'arfe ukku na rana, lokacin da suka isa gidan gwaggon bata nan sai kawu Amadu
shima bacci yake a d'akin shi, a d'akin Fatun suka sauka wannan ne zuwan Fauzy tayi Weekend a gidan
na biyu don lokacin da Suke aji d'aya ta ta6a zuwa, bayan Fatuu ta aje jakar ta ta cire mayafi ta fito ta
nufi kitchen don ta zubo masu Abinci waina da miya taga anyi ga kuma tuwon dare shima anyi
murmushin jin dad'i Fatuu tay a ranta ta ayyana gwaggo ba dae kokari ba har tayi Abinci haka kafin ta
tafi, wainar ta zuba masu ta nufi d'aki itama Fauzy tana ganin wainar ta washe baki don ta kwana biyu
bata ci ta ba sosae suka ci Fatuu harda sud'e plate, saida akai sallar la'asar sun fito yin Alwala suka had'e
da Kawu Amadu shima ya fito yin Alwalar yana ganin Fatun yace mata yaushe suka zo tace mashi yanata
sharar bacci lokacin da suka zo gashi ya bar ma Mutane gida a bud'e salon a shigo ai masu sata ya wurga
mata harara yace ta bar ganin fa ta girma har yanzu bata wuce bugu a wurin shi ba Fatun tay wata yar
iskar dariya tace "ni yanzu Kawu Amadu ai mai buguna sai dae ko ruwan sama amman ko gwaggo ai na
mata girma da bugo balle kai" jinjina kai yay ya d'an cije leben shi na k'asa yace "kawai dae kawae
shikenan..." Fatuu ta katse shi tace ya fad'a mana kawai dai mi yana yar dariya yace "kawae dai bazan
buge ki ba don kada Romeo yasa a kama ni don naga shima kaman ya shigo hannu" ya k'arasa yana tik'ar
dariya ba kamar da ya ga yadda ta tamke Fuska Fauzy ma sai dariya take ganin yadda suke drama sai
kace ba kawunta ba sai lokacin ta gaishe da shi yana murmushi ya amsa yay mata ya Makaranta tace
lafiya lau daga haka ya wuce ya d'ibi ruwan ya nufi hanyar waje yana cigaba da yi ma Fatuu dariya, sai
bayan sallar isha gwaggo ta dawo suka tare ta tana ganin Fauzy ta washe baki tana amsa mata sannu da
zuwan da take mata tay mata ya Makaranta da Auntyn ta tace lafiya lau daga baya ta wuce d'akinta
Fatuu tace ma Fauzy tazo su zuba Abinci suka nufi kitchen tare bayan ta zuba suka kai cikin parlor ta fito
ta nufi d'akin gwaggo lokacin ta gama cire kayan aikin Fatuu tace mata ta taho Parlor suci Abinci tana yar
dariya tace to a bari tayi wanka sai tazo ta mak'e mata kafad'a sai kace wata k'aramar yarinya gwaggon
nata dariya saida ta tasata gaba suka tafi parlon a tare ta zuba masu tuwon alkamar da miyar karkashi
mai kyau gwanin yauk'i taji kifi tarwad'a da suka fara ci sosae tuwon yay ma Fatuu dad'i don har wani
lumshe idanu take wasa wasa sai gashi har suka k'oshi amman ita bata k'oshi ba saida ta k'ara gwaggo na
fad'in bari cikinta ya fashe duk sukai dariya bayan sun gama suka fita da kayan gwaggo ma ta fita don
yin wanka tana fitowa tay sallar isha ta haye gado su kuwa suna a parlon suna yin kallo saida dare yay
sosae Fatuu ta kashe kayan kallon suka nufi d'aki don su kwanta, Washe gari a tare suka gyare gidan tsab
bayan sun gama suka d'aura girkin rana koda gwaggo ta fito don ta kama masu ce mata sukae sun yafe
taje ta huta tana dariya ta shi masu Albarka cike da farinciki suka amsa ta koma d'akin, bayan sun gama
suka zuba mata Fauzy ta kai mata d'akin ta Kawu Amadu ma aka zuba mashi su kuma suka yanke su fara
yin wanka sai su ci, bayan duk sun yi wankan lokacin gwaggo ta tafi aiki saida sukai sallar Azahar sannan
suka zuba abincin suka shiga Parlor akan Carpet suka zauna, Fatuu na fara cin Abincin wanda shinkafa da
wake da miya ne taji zuciyarta ta fara tashi hakan yasa ta d'an dakata ta gumtse baki kwata kwata Fauzy
bata lura ba don tana ci tana kallon Tv gaba d'aya hankalin ta ya tafi saida ta d'an d'auki lokaci jin tashin
zuciyar ya lafa yasa taci gaba da ci can wani irin yunkurin amai ya taso mata ta tashi da sauri ta nufi
hanyar waje hakan ya maido hankalin Fauzy kanta ta bita da ido can ta jiyo ta tana ta Kwara amai da
sauri ta mik'e ta fita ta nufi inda take a duk'e ta tsaya kanta tana ta mata sannu sai ga Kawu Amadu ya
fito ya nufo inda suke ya tsaya da d'an alamun razana ya tambayi Fauzy miya faru take amai haka itama
duk damuwa ce akan fuskarta tace mashi tana tunanin Malaria ce ke damunta dama jiya a School ma
saida tayi yace to bata je taga likita ba Fauzyn tace eh da yake tunda tayi bata k'ara yi ba kuma duk
alamu sun nuna malaria d'in ce don harda jiri tace tana ji da yake yanzu haka take ma Mutane, jinjina kai
yay ya kalli Fatun dake k'ok'arin mik'ewa yay mata sannu ta d'aga mashi kai ta nufi famfo ta kunna tana
wanke fuskarta da bakinta ta kora aman, Amadu dake kallonta yace inta gama ta duba d'akin gwaggo
yasan ba'a rasa maganin Malaria d'in ta d'aga mashi kai yace mata Allah ya sawak'e ya juya, bayan ta
gama kama hannunta Fauzy tay zasu koma Parlor Fatuu tace mata bari taje d'aki kwanciya take son yi
tace to taje ta d'aukko maganin sai ta sha bari ta kawo mata ruwa ta saki hannunta ta nufi Parlor don
d'aukko ruwan, a d'akinta ta iske ta bayan ta d'aukko ruwan tana ruk'e da Maganin data d'aukko ta
bud'e mata ruwan ta bata ta sha maganin bayan ta gama ta mik'a mata robar ita kuma ta kwanta
gefenta Fauzy ta zauna cike da damuwa tace mata to yanzu mi zata ci tunda ta amayar da wanda ta ci da
sauri ta girgiza mata kai alamar bazata ci komae ba kafin ta lumshe ido nan da nan bacci ya d'auketa duk
sai Fauzy taji Abincin ma ya fitar mata a rai ta mik'e ta koma Falon ta kwashe kayan ta kai Kitchen bayan
ta fito ta nufi d'akin a gefen Fatun itama ta kwanta bada Jimawa ba itama bacci ya kwasheta, sai bayan
da akai sallar la'asar Amadu ya shigo ya tashe su don suyi salla tun Fatuu na cikin yin sallan ta ji wani irin
kwad'ayin shawarma ya kamata bayan sun sallame ta kalli Fauzy tace mata bakinta ba dad'i ta zo suje su
siyo shawarma daga nan sai su biya shagon Aunty Zee su siyo ma Babyn Haulat kaya tunda tana hanya
tace to, gaba d'aya jallabiya suka sa sukai rolling veil d'in kowacce ta rataya yar side bag lokacin da suka
fito Amadu na ganinsu yace ma Fatuu yo har ta warke tana d'an murmushi tace mashi eh da sauki bata
son ta kwanta ne ciwon ya rufeta zasu je su dawo ya tambayeta ina zasu tace bakinta ba dad'i shawarma
zasu siyo yana murmushi yace "to ta Romeo a had'o dani" tura mashi baki tay taja hannun Fauzy dake
murmushi suka tafi, shagon Zee suka fara zuwa sosae tay farincikin zuwan su ta kar6e su hannu bibbiyu
suka gaida ta bayan sun zauna tay masu ya karatu daga baya suka fad'i mata abunda suke so cike da
zolaya tace ma Fatuu ko tayi aure har zata Haifa masu baby bata sani ba ta d'an waro ido tana dariya
tace "ai in nayi Aunty zee zaki sani don zan fad'a maki" jinjina kai tay tace "hakane nima ina wasa ne ai in
sha Allahu tuwo na mai na za'ai kinga mune k'irjin biki kenan" yanayin fuskar Fatun ne ya sauya still da
d'an guntun murmushi ta d'an sunkuyar da kai anan Zee ke mata zancen rashin lafiyar Senator tace su
Jidderh ne suka fad'a mata Fatuu da ta d'ago tace mata eh yana Germany aka ce tace eh haka aka fad'i
mata Addu'ar Allah ya bashi lpy tayi duk suka amsa da Amin ta mik'e tace su shiga sai su za6i kayan da
suke so, bayan sun shigan kaya sosae suka siya tarkacen kayan jarirai harda su mayukan su sannan ta
siya ma Haulat itama atampa mai kyau da harda lace ma taso ta siya mata to bata da isassun kud'i gashi
tasa ma ranta bazata ta6a wanda Haisam ya turo ba, saida suka baro shagon sannan suka biya wani Cafe
suka sayi shawarmar harda ice cream da youghort kafin suka wuce gida, da daddare bayan gwaggo ta
dawo ta gama kintsawa suka kai mata kayan don ta gani sosae ta yaba kyawun su tana fad'in su Fatuu fa
anyi D'iya dole a gwangwaje ta duk suka yi dariya har suka baro d'akin ba wanda yay zancen ciwon Fatuu
don ta gyagije baka cewa ma itace tay amai d'azun, a ranar sai wurin goma ta wuce su Haulat suka iso ita
da wasu yan uwansu lokacin data kira Fatuu ta sanar mata ta iso sha d'aya tayi cike da zumud'i Fatuu
tace in Allah ya kaimu tana nan zuwa a shafa mata kan Baby ace Mamanta na mata sannu da zuwa
Haulat na dariya ta amsa da to Maman Baby, Washe suna gama gyara gidan suka shirya don tafiya gidan
su Haulat da yake gwaggo bazata je aiki ba ita zatayi Abincin rana ta basu sak'on suyi ma Haulat barka da
zuwa sai ta shigo anjima suka amsa da to suka tafi, Lokacin da suka shiga gidan a tsakar guda suka iske
innarsu da fara'a tay masu sannu da zuwa duk suka gaidata ta amsa tana fad'in "Fatima yan Makaranta
karatu ya 6oye mana ke" d'an murmushi kawai Fatun tay tace Allah ya bada sa'a suka amsa da Amin
kafin sukai mata barka d'an murmushi tay tace ai ita za'a ma barka su shiga Haulat d'in na cikin d'akinta
suka amsa da to had'i da nufar d'akin, da sallama Fatuu ta shiga idonta suka sauka akan Haulat dake
zaune saman gado tayi wanka tana sanye da riga da zani na atampa tana rungume da babyn itama an yi
mata wanka an shiryata tana Feeding d'inta d'akin sai k'amshin jego yake suna had'a ido suka sakar ma
juna murmushi Fatuu ta nufe da sauri ta d'an yi mata side hug tana fad'in "Allah sarki Aminiyata nayi
missing d'inki over wllh" dariya Haulat tay tana fad'in itama haka Fatuu ta zauna gefen gadon Haulat ta
kalli Fauzy dake tsaye tana murmushi tace mata ga wuri ta zauna mana ta nufi wurin daga gefen Fatuu ta
zauna, k'ura ma Babyn ido Fatuu tay yadda take ta shan nono abunta ta bud'e ido mamaki kawae Fatuu
ke yi wai Haulat ce da D'iya Haulat dake ta kallon Fatuu ganin yadda take kallon babyn yasa tace "halan
mamaki kike?" Da sauri ta kalli Haulat tace "wllh abun ba wuya da anyi aure sai kiga an haihu" Haulat
dake dariya tace "Uhm dama ai yanzu haka zaki gani sai zaki haifa ma Ya Haisam tukunna zaki gane inda
wuyar ko babu" d'an 6ata fuska tay had'i da ta6e baki Haulat d'in tace "ko an daina yayin shi ne anyi new
catch?" Kafin tace wani abu Fauzy dake murmushi tace "yana nan daram a cikin zuciyar don ta shi ce ba
sauran space da wani zai samu" Haulat dake kallonta tana yar dariya tace "Fauzy bamu gaisa bama ya
karatu?" tace "Alhamdulillah barka mun samu karuwa Allah ya raya mana ya Albarka ci rayuwar ta"
Haulat ta amsa da Amin da sauri Fatuu ta kai hannu ta d'an bugi gefen hannunta tace ba'a amsawa fa
rashin kunya ne dariya kawae Haulat ke yi Fauzy tace "barta ta amsa abunta wllh ita tasan kwakwar da
ta ci kafin ta same ta sai kuma ayi Addu'a tak'i amsawa, ko ni da zan yi aure in haihu duk wanda yay ma
babyn Addu'a sai na amsa" Haulat dake dariya tace "ai zaki yin in sha Allah da lokaci yayi" d'an girgiza kai
tay tace ta yafe ba sai tayi ba Haulat dae murmushi kawae take don tasan labarinta tun bayan da suka
had'u da Fatuu ta bata labarin ta can Fatuu ta kai hannu tace ita dae gaskiya ta gaji da jira duk ta k'osa ta
d'auketa Haulat ta mik'o mata ita ta kai hannu ta amshi babyn, Fatuu na murmushi take kallon yarinyar
Tubarkallah kyakkyawa da ita gata fara hasken babanta ta d'aukko don yafi Haulat d'in haske amman
fuskarta tana kama da Haulat sosae, kallon Haulat tay ta tambayi sunanta tace Umma Salma Fatuu ta
d'an 6ata fuska tace maimakon a saka mata sunanta duk suka yi dariya Haulat ta kalli Fauzy tace "Fauzy
ya fama da k'awar nan ta ki" tana dariya tace "ai ke kika sha fama ni yanzu da Sauk'i ta girma tayi
hankali" juyawa Fatuu tay ta d'an harareta tace da bata da hankali kafin Fauzy ta bata amsa Haulat tace
da Sauk'i dai hankalin nan gaba d'aya suka kwashe da dariya, hira suka cigaba da yi Haulat nata ba Fauzy
labarin kuruciyar Fatuu tana ta tik'ar dariya suna haka har Azahar tayi suka tashi sukae salla bayan sun
gama ne k'anwar Haulat ta kawo masu abinci a cikin yar babbar kula ta koma ta kawo plates da ruwa
daga baya ta kawo ma Haulat nata ganin sun k'i fara ci tay masu magana tace ma Fauzy don Allah taci
itace bak'uwa tana murmushi tace itama ai yanzu ta zama yar gida Haulat tace hakane, hannu ta kai ta
bud'e warmer d'in dafa dukan shinkafa da taliya ne a ciki ta fara zubawa a cikin plate bayan ta gama ta
rufe ta kalli Fatuu tace suci kowa ta d'auki spoon suka fara ci, d'an kad'an Fatuu taci jin zuciyarta ta fara
tashi yasa ta aje spoon d'in Fauzy dake kallonta tace har ta k'oshi ta d'aga mata kai alamar eh, sai bayan
da suka gama suka ba Haulat kayan da suka kawo mata sosae tay farin ciki ta hau yin godiya har da
k'wala ma innar su kira ta shigo itama ta ga kayan tay godiya sosae tana fad'in lalle Mama Fatima ta fito
da d'iyarta wannan kaya haka k'arshe tay Addu'ar Allah yasa suma su ga yaran su kowa ta sunnar da kai
suna d'an murmushi Haulat na fad'in su Fatuu ashe yanzu an san kunya innarsu dake dariya tace ai
daman can da kunyarta daga baya ta fita, har akai la'asar suna gidan bayan an gama salla gwaggo tazo
itama harda kayan ta kawo masu sosae suka ji dad'i sai bayan Magrib sukai masu sallama Haulat na
tambayar Fatun yanzu Makarantar zata koma tace eh amman zata dawo cikin satin ta k'ara ganin Baby
tace to Allah ya bada sa'a suka amsa da Amin kafin su tafi aka basu naman suna mai uban yawa har
gwaggo na fad'in kar su kwashe ma mai jego fa innar su tace a'a bakomae godiya sukai suka tafi.
Washe gari da safe sukai shirin tafiya bayan sun gama yin breakfast suka je d'akin gwaggo sukai mata
sallama tay ma Fauzy godiyar ziyara harda kud'i ta basu ta rako su har bakin zaure Kawu Amadu ma ya
fito sukai sallama, Lokacin da suka isa Class kawae suka wuce don duk suna tare da jakunkunan su da
akayi break suka fita, tun bayan da suka dawo zuciyar Fatuu ta fara tashi ga wani ciwon kai daya far mata
lokaci guda daurewa kawai take bayan da malamin su ya shigo yana cikin yi masu bayani yau ma kamar
rannan amai ya taso mata ta fita da gudu Fauzy ta d'auki excuse ta bi bayanta, saida ta gama ta kamata
suka je bakin famfo ta wanke fuskarta da bakinta bayan ta gama Fauzy dake kallonta cike da damuwa
tace gaskiya suje taga likita ciwon ya fara yin yawa Fatun ta d'aga mata kai don itama abun ya fara
damunta class Fauzy ta koma ta fad'i ma malamin zata kaita taga likita ya bata izini ta d'aukar masu
jakun kunan su, lokacin da suka isa Opd office d'in wani Doctor Madugu suka nufa don sun san shi son
Fatuu yake ita kuma tak'i saurarar shi ba kamar da yake tasan halin shi ya cika son mata, saida suka jira
patient d'in dake ciki ta fito sannan suka shiga yana ganin su ya sakar masu murmushi suka zauna a kan
kujerun gaban table d'in shi yabi Fatuu da wani kallo yana sakin k'ayataccen murmushi ta d'an d'aure
fuska Fauzy ce ta fara gaishe dashi sannan Fatun kaman an mata dole yace ba zai amsa ba in bazata saki
face en ta ba k'ara tamke fuskar tay Fauzy ce tace mashi bata lafiya ne d'age gira yay ya tambayi abunda
ke damunta har Fauzy zata bashi amsa yace ita yake son yaji daga bakinta d'an shiru fatun tay kafin ta
fara mashi bayanin abunda ke damunta bayan ta gama yana d'an murmushi yace "kinga da mun yi aure
sai in yi tunanin ko mun samu rabo ne" a d'an harzuk'e ta kalle shi bata dae ce komai ba ya fara rubutu a
Computer d'in gabanshi can ya d'ago yace suje lab ya tura test ayi mata suka mik'e yabi bayanta da kallo
har suka fice, suna zuwa lab d'in ba 6ata lokaci akai mata awon don sun san masu yi awon Malaria da
typhoid ne aka mata bayan an tura ma likitan suka koma Opd d'in lokacin daya duba result d'in akwae
malaria d'in amman ba typhoid ya fad'i masu kafin ya tura masu magunguna yace suje pharmacy bayan
sun mik'e ya kira Fauzy ya bata kud'i yace su biya tay mashi godiya suka tafi, bayan sun amshi
magungunan suka tafi ganin an kusa tashi Fauzy tace su wuce hostel kawae sai ta sha magungunan ta
d'aga mata kai, bayan ta fara shan magungunan sosae ta samu sauk'i ta daina yin aman saidae bata da
appetite ba komae take iya ci ba tafi shan youghort sai kuma lemu Fanta sai abu mai d'an tsami ko yaji a
haka har Friday tayi suka tafi weekend, lokacin data koma gidan gwaggo bata nan bata dawo ba sai dare
Fatun ta fito tsakar gida ta tareta tay mata sannu da zuwa tana niyyar zuwa kitchen don ta kawo mata
Abinci tace mata ta barshi in tayi wanka zata ci ta ce to ta koma d'aki, washe gari bayan ta gama gyara
gidan tay wanka ta shirya cikin doguwar rigar material tay rolling veil d'in ta shiga d'akin gwaggo lokacin
tana kishingid'e saman gado amman ba bacci take ba a bakin gadon Fatuu ta zauna suna kallon juna da
gwaggon da ta d'ago kanta tana kallon Fatun sosae tana murmushi ta gaishe da ita ta amsa tace mata
zatace gidan su Haulat shiru gwaggon tayi tana ta kallonta saida Fatun ta maimaita mata sannan ta d'aga
mata kai alamar to har ta mik'e ta nufi kopa tana fad'in sai ta dawo taji gwaggon ta kirata ta dakata ta
juya da kai tay mata alamar ta zo ta koma ta tsaya daga d'an gabanta tace gata gwaggon ta yunk'ura ta
tashi zaune sosae tana kallonta tace "wani abu na damun ki ne??" Cikin rashin fahimta Fatuu ta
tambayeta wani abu tace tana nufin bata lafiya ne d'an murmushi Fatuu tay tace "Eh ciwo nayi har ma
naje naga likita ya tura ni aka man test aka ga malaria ce ke damuna sosae ya rubuta man magunguna
yanzu haka cikin shan su nike amman na samu sauk'i ai sosae" shiru gwaggo tay kafin tace mata basu
saka net ne in zasu wanta tace suna sawa wllh kawae ciwon ya kamata ne kuma kafin su shiga net d'in
saurayen na cizon su ko in sun fita class da daddare,jinjina kai gwaggon tay tace taje Allah ya sawak'e
amman dole su k'ara kulawa tace to ta tafi, tunda tazo gidan wani ikon Allah lafiya lou take cin Abinci
washe gari lahadi harda cin cin tayi masu ranar Monday da safe ta tafi.

tun bayan da ta koma sai ciwon ya k'ara dawowa sosae ga yawan amai da take yi kusan kullum sai tayi
amai a class wani lokaci in Malam na ciki ko kuma da break haka a Hostel ma in ya taso mata ta window
take zura kanta tai tayi ga magani tana ta sha amman abun yak'i lafawa har fuskarta ta d'an rame tayi
wani fayau da ita ranar laraba Fauzy tace mata kodae ta rakata gida amman sai tace tunda har anzo
ranar ta bari Friday ta je tace to kodae ta saka mata drip ko taji k'arfin jikinta Fatun tace eh, da kanta ta
fita taje ta siyo drip d'in bayan ta dawo ta saka mata shi lokacin daya k'are sosae ta samu k'arfin jikinta
washe gari Alhamis taje class lpy lou har aka tashi, da yamma Fauzy taje siyo abu a shop bayan ta dawo
ta nufo Hostel hannunta ruk'e da leda taji ana k'wala mata kira ta bayanta ta tsaya da ta juya sai taga
wata yar class d'in su ce mai suna Zainab Muhammadu wadda ake ce ma suda (sarkin labari) tana ta
sauri ta k'araso ta tsaya gaban Fauzy tace "dama tambayar ki nike son yi ya jikin Fatima Ard'o?" Wani
kallo Fauzy tay mata tace bata ganta bane yau a class da sauri tace ta ganta taga ma duk ta rame Fauzy
tace eh ai ciwo take ko daga haka ta fara kokarin wucewa Zainab d'in tace "wai kinsan abunda ake fad'a
kuwa game da ciwon da take?" Cakk Fauzy ta tsaya tana kallonta tace mi ake fad'an yar in ina ta fara
tace "j....ji nayi ana cewa wai kamar ciki ne da ita don ciwon da take yayi kama da laulayin ciki" rassss
gaban Fauzy ya fad'i ta zaro ido waje gaba d'aya hannunta guda dafe da bakinta can ta cire cikin bacin rai
tace "uban wa yace ciki gareta dama mara aure na samun ciki ne ko kuwa ana sha a ruwa ne ban sani
ba???" Yarfa hannu Zainab d'in tay tace "nima fa bani nace ba abunda aketa fad'a ne nagaya maki don
ku sani" daga haka ta wuce tay tafiyarta Fauzy tabi bayanta da kallo fuska a matuk'ar d'aure can ta wuce
fuuu itama ta shige cikin hostel d'in idonta har rufewa yake Saboda tsabar bacin rai da bibbiyu ta rink'a
hawa staircases d'in ta nufi d'akin su, lokacin data shiga Fatuu na kwance saman gado tana jiranta ta
kawo mata Fanta gado ta nufa ta aje ledar hannunta gefe ta zauna fuska a d'aure ta kumbura baki ganin
yanayinta yasa Fatuu yunk'urawa ta tashi zaune ta fara tambayarta lafiya bin ta da ido kawae tay kaman
bazata tanka ba can cikin bacin rai tace "wllh magulmaci bai ji dad'i ba yaji haushin asara!!" A d'an rud'e
Fatuu ta hau cewa ta fad'i mata gulamar mi akayi don Allah tace "wai shikenan mutum bazai yi ciwon
Allah da Annabi ba sai an ja mashi sharri yanzun nan da zan shigo wai Zainab Muhammadu ta tsaida ni
take fad'a man maganar da ake tayi game da ciwon ki.." a rud'e Fatuu tace mi ciwon nata yayi kaman
bazata fad'i mata ba ganin yadda take mata Magiya yasa tace "ke wai ciwon da kike wai kaman ciki gare
ki don ciwon yayi kama da laulayi Kiji jan sharri don Allah kawae don aja maki, ta ina zaki samu ciki tunda
ba aure gare ki ba!!" Zaro ido waje Fatuu tay tasa hannu guda ta dafe kirjinta a kidi'me ta maimaita "ciki
kuma!" Wani uban tsoki Fauzy taja jikin Fatuu har ya fara rawa kaman zata yi kuka tace "ni a ina zan
samu ciki bacin kowa yasan ba aure gare ni ba!" Wani tsokin Fauzy taja tace "dalla rabu dasu
magulmantan banza kawae an fad'a ne tunda kika ji Zainab Muhammadu ta fad'a don in dae tace abu to
tabbas an yi ne ki k'yale su ta Allah ba tasu ba duk mai neman ki da sharri saidae ya koma mashi wllh"
tana k'arasa Maganar ta fiddo mata Fanta d'in ta mik'a mata hannun Fatuu sai rawa yake ta amsa sai ta
aje ta a gefenta kawae tsananin tsoro da fargaba ne suka kamata jin abunda zuciyarta ke ayyana mata
na kada ace daga abunda Ya Haisam yayi mata ta samu ciki sosae kirjinta ke bugawa tunanin yaushe
yakamata tayi period ta shiga yi a lissafin ta gobe Juma'a wata guda kenan da abun ya faru kuma tayi
wanka da kwana d'aya hakan ta faru kenan yanzu kusan kwananta talatin da yin wanccan tasan kuma
bayan kwana ishirin da d'aya wato sati ukku koda biyu take yin sabon period yanzu kenan lokacin ya
wuce kuma ko alamun zata yi bata fara ji ba wani abu ta had'iya Kutt lokaci guda zufa ta fara tsattsafo
mata ta koma tamkar an dasa ta a wurin ko kwakkwaran motsi ta kasa yi kallonta Fauzy tay ganin halin
da take ciki da alama ta rude yasa tace mata wllh kada ta sake ta wani damu da zancen munafurcin su
tunda ita dae ai tasan ba shi gare ta ba ko, zuru da ido kawae tay ma Fauzy k'arshe Fanta d'in ma kasa
sha tay don ko kallonta ma bata k'ara yi ba Fauzy ta hau lallashin ta tana don Allah ta d'auka tasha kada
ta tada hankalin ta a banza ita data san haka zata shiga damuwa da bata fad'a mata bama, a wannan
daren yadda Fatuu taga rana haka ta ganshi sam bacci ya k'aurace ma idanunta sai juyi take tana
zullumin kada ace da gaske ciki ne da ita don duk alamu sun nuna kaman laulayi take yin da gaske yin
wannan tunanin har saida tasa hannu ta rufe bakinta, akan kunnanta aka kira sallar Asuba da k'yar ta iya
yin salla tana gamawa ko Addu'a kasa yi tay ta koma gado ta kudundune lokacin da gari ya waye Fauzy ta
d'an bubbuga ta tace ta tashi ta shirya kada su makara tana a kudundunen tace mata ta shirya ta tafi ita
bazata je ba jin hakan yasa Fauzy zama a gefen gadon da take tace "kamar ya bazaki class ba kuma, ko
don Maganar jiya to ke miye abun wai damuwa har haka ne tunda kin san kina da gaskiya ki tashi kawae
ki shirya mu tafi in mutum ya isa ya tunkare mu yayi mana Maganar mu mana" duk yadda tayi da ita ta
kafe kan bazata je class ba har ran Fauzyn ya 6aci tace "to ko dae Zarah da gaske cikin ne da ke???" shiru
Fatun tay bata bud'e fuskarta ba kirjinta na wani irin bugu can Fauzy ta kai hannu ta yakice bargon data
lullu6a Fatun ta kalleta da sauri suka zuba ma juna ido baiwar Allah duk ta firgice sai numfashi take da
k'arfi wani irin kallon tuhuma Fauzy ta fara yi mata ganin haka yasa Fatun sunkuyar da kai cikin
d'aurewar kai Fauzy tace "Zarah na tambaye ki baki ban amsa ba ki fad'a man gaskiya ko dae Maganar da
ake gaskiya ce??" Girgiza kai ta fara yi da k'yar ta d'ago ta kalleta idanunta sun ciko da Kwalla tace "Fauzy
ya zaki fad'i hakan kema bacin kin fi kowa sanin wacece ni kuma kin san ba aure ke gare ni ba" sauke
Ajiyar zuciya tay tace "to don mi zaki k'i zuwa class??" Cikin rawar murya tace "h.... hakanan kawae,
hankali na ya tashi sosae da jin Maganar ban so inje class haka su k'ara tabbatar da Maganar su gara in
tafi gida kawae in fad'i ma gwaggo halin ciwon da nike ciki a nema man maganin hausa" da k'yar ta kai
Maganar, shiru Fauzy tay tana nazarin Maganar can tace mata shikenan ta fahimta amman ta bari a tashi
sai ta rakata gidan tace mata to kawai, saida ta matsa mata sosae sannan ta d'an sha ruwan tea da yar
wainar kwae, tun bayan da Fauzy ta shirya ta tafi class take ta faman kai da kawowa a cikin d'akin gaba
d'aya ta gama firgicewa kanta ko kallabi babu ta rasa tunanin da zata yi tsoron ta ace da gaske tana da
ciki duk in tayi wannan tunanin sai yan hanjinta sun juya can wata Zuciyar ta raya mata taje ta siyo Pt
strip ta auna in shine tun wuri ta d'auki matakin daya dace, yin wannan tunanin yasa da sauri ta nufi
kayan su ta d'auki hijab ta bud'e jakarta ta d'auki kud'i har zata fita tay tunanin ta saka nikab d'in Fauzy
ta tafi dashi ta juya ta d'aukko shi ko sakawa daidai bata yi ba a haka ta tafi.......
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2048*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

...........Tafiya take bata san inda take wurga k'afafunta ba don sam bata cikin hayyacin ta a haka har Allah
yasa ta fito cikin Asibitin tasan in taje pharmacy d'in asibitin ba za'a bata ba tunda ba Doctor ya turo ba
hakan yasa ta yanke zuwa d'aya daga cikin pharmacies d'in dake wajen Asibitin tana ta tafiya gani take
tafiyar ma bata sauri tamkar maidota baya ake hakan yasa ta yanke hawa Napep duk da ba wani nesa
bane tama kusa isa, bayan ta tsaida ta fad'i mashi inda zai kaita shima mai Napep d'in har saida ya d'anyi
mamaki yace mata nan wajen gate tace eh amman zai jira zata siyo abu ne sai ya maido ta makaranta
yace nan school of nursing tace mashi eh yace to ta hau, bayan sun tsaya ta nufi cikin pharmacy d'in
gabanta sai fad'uwa yake har ta kusa rubzawa k'atuwar kwalbatin dake wurin batare da ta ankare da
slab din ya fashe ba mai Napep d'in ne ya d'an d'aga murya yace tabi a hankali don ya lura duk a firgice
take ta d'aga mashi kai kawae, bayan ta shiga ta fad'i abunda za'a bata ba 6ata lokaci aka d'aukko mata
ta je wurin biya ta bada d'ari biyar ta juyo saida cashier d'in yace mata canjin ta fa sannan ta juya ya bata
ta amsa ta fito bayan ta hau Napep d'in suka komo Asibitin, a bakin gate ya aje ta ta mik'a mashi duka
sauran canjin dake hannunta ta juya, ganin a rud'e take yasa yay tunanin ko bata san nawa ta bashi ba ya
tsaidata yace kud'in sun yi yawa tazo ta amshi canji hannu kawae ta d'an girgiza mashi alamar ya bassu
ta nufi ciki yana ta kallonta gashi dai baisan wacece ba don ta rufe face d'inta amman dae ta bashi
tausayi don tabbas da gani akwai abunda ke damunta k'arshe yay mata Addu'a yaja napep din ya tafi,
nan da nan ta iso d'akin su ta shige bayan ta cire nik'ab d'in zaune tay a gefen gado tana ta zare ido wani
irin tashin hankali take ciki tsoronta ta gwada taga cikin ne can wata Zuciyar ta bata shawarar ta daure ta
gwadan in ma shine tunda wuri ba sai taje ta siyo allurar zubda ciki ba tay ma kanta, sosae hakan yay
mata ba tare da tayi tunanin wata matsala ba ta mik'e saida ta samu wani d'an murfi sannan ta fita zuwa
toilet d'in su bada jimawa ba ta fito ko kallabi babu a kanta haka taje tayo fitsarin, a bakin windown
d'akin ta tsaya ta d'aura robar fitsarin ta koma bakin gado ta d'aukko ledar pt d'in ta dawo, tsaye tay cike
da fargaba take kallon fitsarin ba don komai sai Allah ya k'addara ba da iya tashin hankalin da take ciki ya
isa yasa in ma cikin ne ya zube, can zuciyarta ta raya mata time fa na tafiya gashi yau Friday tayi abunda
yakamata da sauri tasa hannu ta cizge ledan hannu na rawa ta fiddo tsinken gwajin ta tsoma shi a cikin
fitsarin kaman yadda ake yi bayan ta fiddo ta aje ledar data fiddo shi a ciki ta d'aura tsinken flat
hannunta nata k'akkarwa, a hankali ya fara washewa idonta akan shi tun ma kafin ya gama ta fara girgiza
kai had'i da gumtse baki a haka har ya gama jajayen layuka biyu suka bayyana daro daro alamar akwae
cikin, kwata kwata ta kasa yin kuka sai faman girgiza kai take tana fitar da numfashi da k'arfi da karfi ga
jikinta dake ta kerma da k'yar ta kai jikin bango kusa da window d'in ta jingina bayanta sai lokacin kwalla
suka fara zubo mata masu d'umi cikin wata irin murya ta fara fad'in "ciki ne da ni! Ciki....Na shiga ukku na
lalace na bani! Mi maye ni Fatuu na mutu, Ya Haisam ka cuce ni, kaci amanata na shiga ukkuna in
gwaggo taji wannan Maganar nasan mutuwa zatayi wllh..." tana Maganar tana Jujjuya kai, tana cikin
wannan halin taji motsin kaman ana tunkaro d'akin bata gama gasgatawa ba taji muryar wata tana fad'in
"Fauzy kema kin dawo kenan" Fauzyn ta bata amsa da "Eh wllh Maryam toilet ya koro ni" ta k'arasa
Maganar tana dariya jin muryar Fauzy yasa a firgice Fatuu ta kai hannu ta rarumi ledar strip d'in da
tsinken gwajin ta nufi gado a sukwane taja bargo ta lullu6e har kan ta, tana gama rufe jikin Fauzy na
shigowa ta bita da ido sam bata kawo idonta biyu ba ta duk'a ta d'aukko bucket ta fita don flushing d'in
su bai yi saidae mutum ya cika bucket da ruwa ya shek'a, tana jin lokacin data fita amman bata bud'e
jikinta ba don tasan da ta ga fuskarta zata zargi wani abu tay lamo tafin hannunta toshe da bakinta, after
some minutes saiga Fauzyn ta dawo ta maida bucket d'in k'ark'ashin bed tana kokarin mik'ewa kwatsam
idanunta suka sauka akan pt strip d'in dake yashe a k'asa wanda sam Fatuu bata san ya fad'i ba iya ledar
ce a hannunta, slowly Fauzy ta kai hannu ta d'aukko shi ganin abunda ke a jikin shi yasa ba shiri ta mik'e
idanunta still na akan shi tana kallo da tsananin Al'ajabi had'i da mamaki ta d'an gyad'a kai cikin ranta ta
ayyana pt strip kuma a d'akinsu mai nuna akwae ciki to waya kawo shi??? A wani irin slow ta d'ago ta
kalli Fatuu dake kudundune lokaci guda kirjinta ya buga jin zuciyarta na raya mata kodae itace tunda ai
ba kowa a d'akin sai ita kuma duk sauran students na Class hannu ta kai ta rufe bakinta gabanta na
cigaba da fad'uwa can kuma ta cire hannun murya na rawa ta kira sunan Fatun amman bata amsa ba
bata kuma nuna idonta biyu ba hakan yasa ta k'ara kiran sunan da k'arfi nan ma still bata amsa ba nan
take Fauzy ta shiga girgiza kai cikin murya mai nuni da tashin hankali tace "Zarah I know u'r not asleep
idonki biyu to ki tashi don na riga nasan abunda kike 6oyewa gashi ma a hannuna!!" runtse ido Fatuu tay
sosae ta kasa gane mi Fauzy ke magana akai tana haka taji Muryata tana fad'in "Ki tashi Zarah ina son
sanin wannan abun na waye!" Jin haka yasa a kidi'me ta yaye bargon tana juyowa idanunta suka sauka
akan abunda Fauzy ta d'aga tana nuna mata wani abu Fatuu ta had'iye Kutt sai zare idanunta da sukae
jawur take yanayin fuskar ta kadae ya tabbatar ma da Fauzy abunda take zargi, ganin irin kallon da take
mata ne yasa cikin rawar murya Fatuu tace "m....miye wannan d'in...?" Wani d'an murmushin takaici
Fauzy tay kafin tace "abun ki ne da kikai amfani dashi, yanzu ashe da gaske ciki ne da ke Zarah!!" A
razane Fatuu ta hau girgiza mata kai tana fad'in ita fa bata san mi take magana ba akai ya za'ai wannan
ya zama nata ita da tasan ba aure ne da ita ba, Fauzy tace "Yes Zarah ba aure ne dake ba amman kina da
ciki ai ba dole sai ta aure ake samun shi ba ko" Fatuu na jin haka ta saka mata kuka tana fad'in sharri zata
ja mata ita data san halinta ko samari bata saurara, duk yadda Fauzy ta so ta fad'a mata gaskiya abun
yaci tura k'arshe ma sai cewa tay ta sani ko sharri ake son ja mata tunda dama anata fad'in ciki ne da ita
jin wannan Maganar yasa Fauzy ta d'an sauko ta fara tunanin zai iya yuwuwa hakan ne to amman abun
da d'aure kai mi ta tsare ma wani da har za'a mata sharri irin wannan ita da take zaune da kowa lafiya
sannan kuma ana k'aruwa da ita sosae Saboda k'ok'arin ta, kan Fauzy ya gama d'aurewa ta rasa tunanin
da zatai sai kallon Fatuu da ta duk'e kanta tana kuka take can ta juya gefe idanunta suka sauka akan
hijab da nikab d'in da Fatuu ta ajiye slowly ta nufe su tasa hannu ta d'aga nikab d'in wanda nata ne kuma
a cikin Akwatin kayanta tasan ta ajiye shi to miya fiddo shi? bata kaiga ba kanta amsa ba idanunta suka
sake sauka a kan robar fitsarin da Fatuu tay amfani da shi harda sauran fitsarin ganin shi ya tabbatar ma
da Fauzy gaskiyar Al'amari cike da tashin hankali ta juyo tana kallon Fatuu yayin da acikin ranta ta furta
innalillahi Wa'inna ilaihir raji'un! Kiran sunan Fatuu tay ta d'ago da jajayen idanunta ta kalleta jiki a mace
ta nuna mata robar fitsarin tace itama kawo ta akai? Wani abu Fatuu ta had'iya cikin kuka ta hau rantse
rantsen itafa ba ita tay amfani dasu ba k'ilan tana cikin bacci wata ta shigo d'akin don kar a kamata tayi
amfani dasu anan still Fauzy tay tana kallonta kawae jin wata magana ta rashin hankali duk wuraren
dake da akwae a Hostel d'in sai wata tazo d'akinsu duk da ga Fatun kwance tay hakan, ta lura in ba da
gaske tay ma Fatuu ba bazata fad'i mata gaskiya ba duk da ta riga ta gama yarda itace tay amfani dasu
kawae tana son taji daga bakinta ne, sauke nannauyar ajiyar zuciya tay tace "Ok fine tunda kince bake
kika yi amfani dashi ba kin k'i ki fad'a man gaskiya I know what to do" tana gama Maganar ta juya zata
fita da sauri Fatuu ta mik'e ta sha gabanta fuskarta jage jage cikin rawar murya tace mi zatayi d'an
murmushi Fauzy tay tace ina ruwanta ta bata hanya, k'in kaucewa Fatun tay duk tay zuru zuru sai motsa
baki take ta rasa abunda zata ce ganin haka yasa Fauzy cewa "tunda kina son ki sani to bari in fad'a maki,
daga nan in na fita gidan ku zan wuce zan je in kai ma gwaggo wannan pt strip d'in in mata bayanin
komae harda ciwon da kike tayi ba tare da saninta ba kin fake da baki son hankalinta ya tashi alhali ba
haka bane sai yanzu na gano dalili" tana k'arasawa ta fara kokarin ra6awa ta gefen Fatun ta wuce da
sauri ta kamata tana girgiza mata kai cikin kuka tace "Fauzy don't do dis to me na fad'a maki bani nayi
amfani dashi ba nan fa Hostel room ne kowa zai iya shigowa kuma ai bani kad'ai ce a d'akin ba ko" ita
kanta Fatun bata san mi take fad'a ba, d'an murmushin takaici Fauzy tay tace "Yess Zarah u'r not d only
one a cikin d'akin ni dake ne so in kina tunanin ko sharri zan maki duk abun mai sauk'i ne yanzu ki sako
Hijab d'in ki mu fara zuwa gidan Aunty Mareeya akai mata pt strip d'in sannan mu wuce gidan ku akai
ma gwaggo kin ga duk sai a taru a tuhume mu baki d'aya" zuru Fatuu tay tana ta motsa baki cikin d'aure
Fuska Fauzy tace taje ta sako Hijab d'in su tafi mana, yarfa hannu Fatuu ta fara yi ta shiga fad'in ta shiga
ukku ta lalace karta yi mata haka don Allah ganin zata 6ata mata lokaci yasa Fauzy tureta gefe ta wuce
har ta kai kopa taji muryar Fatun tace "ki dawo zan fad'a maki gaskiya to" cakk Fauzy ta tsaya ta runtse
ido wani irin tashi hankalinta ya k'ara yi jiki a mace ta juyo ta kalli Fatuu dake tsaye bayanta tana ta kuka
cike da Al'ajabi tace "so it's true Zarah u'r pregnant?" Jinjina mata kai tay alamar eh wani irin jiri ne ya
kwashi Fauzy da sauri ta dafe kanta tana salati kafin da k'yar ta nufi gadonta ta zaune idonta akan Fatuu
dake tsaye can itama ta lalla6a ta koma gefen nata gadon ta zauna suna facing juna, sun d'an d'auki
lokaci a haka kwata kwata Fauzy ta kasa magana Saboda tsabar rud'ewa baki bud'e take kallon Fatuu
abun ya matuk'ar tada mata hankali wai Zarah data sani bata ko kula samari bare ayi zancen soyayya ko
aure itace da ciki, how on earth?" Fatuu dae sai kuka take ta sadda kai can Fauzy ta sauke ajiyar zuciya
rai a 6ace ta kira sunan Fatun ta d'ago ta kalleta a kausashe tace "am highly disappointed in you Zarah,
ina hankalin ki da na sani ina tunanin ki ya tafi, duk irin kamun kan ki da na sani har kika iya ba wani
dama ya ku sance ki ba tare da kinyi tunanin girman zunubin hakan ba, to ko dama kina aikatawa mu
kika lullu6e...." Da sauri Fatuu tace "Don girman Allah Fauzy ki daina fad'in hakan wallahi tallahi
billahillazi ba hali na bane yadda kika d'auke ni haka nike, Fauzy k'addara ce ta fad'a man nima ba da son
rai na ba hakan ta faru wllh fyad'e aka man" zaro ido Fauzy tay baki bud'e ta maimaita fyade aka mata da
sauri Fatuu ta d'aga mata kai alamar eh salati Fauzy ta shiga yi hannunta dafe da goshinta can ta cire
tace "amman ke ya akai har kika bari hakan ta faru ina kika je har aka maki hakan kuma waye yay raping
en ki??" yarfa hannu Fatuu tay ta langa6ar da kai tace "Don Allah Fauzy kada ki man wannan tambayar
nasan kin yarda dani to ki yadda wllh raping ne bada son raina bane" jinjina kai Fauzy tay tace "tabbas na
yarda dake Zarah amman taya daga kin fad'i man rape in ki akai sai in kama bacin baki fad'i man yadda
akai ba" Magiya Fatuu ta shiga yi mata kan ba sai taji yadda akai ba kawae ta taimaka mata ta san yadda
zata rabu da shi amman fir Fauzy ta k'i amincewa tace lallae fa sai ta fad'i mata yadda akai har a kai
raping inta in ba haka ba to da son ranta a kai kuma ba makawa sai taje gidan su ta fad'a, kuka wiwi
Fatuu ta ke yi hakanan bata son ta fad'i mata wanda yay mata hakan don duk da haushin shi da take ji
sai taji bata son Mutuncin shi ya zube a idon mutane gwara ta rufa mashi Asiri, k'arshe da Fauzy taga ta
kafe tak'i fad'i sai ran ta ya 6aci sosae ta mik'e Fatuu na ganin haka itama ta mik'e da sauri ta nufeta ta
kama hannunta guda tana kuka tana mata Magiya a fusace Fauzy tace "Wllh tllh Zarah ko kukan jini zaki
indae baki fad'i man wanda yay maki hakan ba Allah a yau d'innan sai gwaggo tasan halin da ake ciki
wato shi baiji komae ba yay maki hakan sai kece zaki kare shi da alama dae magana ta na akan hanya da
son ran ki komae ya faru" tana rufe baki ta fara k'ok'arin k'wace hannunta daga ruk'on da Fatun tay mata
cikin k'araji Fatuu ta fara fad'in "to don Allah Fauzy ki tsaya zan fad'i maki" bin ta tay da wani kallo kafin
tace to ta sakar mata hannu bayan ta saki ta koma gadonta ta zauna itama ta zauna a bakin nata ganin
yadda Fauzy ta kafeta da ido yasa ta fara motsa baki tana d'an nishin kuka ta rasa ta ina ma zata fara
Fauzy dake kallonta tace "am listening Zarah, tell me who impregnated u??" Ba alamar wasa a fuskarta
tay Maganar saida Fatuu ta had'iyi wani wahalallan yawu kafin da k'yar ta bud'e baki tace "zan fad'a
maki Fauzy amman don Allah don son Annabi ki man alk'awarin bazaki fad'a ma kowa ba koda gwaggo
ce kuma zaki taimaka man" kai Fauzy ta d'aga mata alamar eh hakanan taji gabanta ya fara fad'uwa tun
bata ji wanene ba don ta gane Fatun na jin nauyin ta fad'i ko waye, ce mata tay ta fad'i tayi alk'awarin da
bakinta Fauzyn ta bud'e baki tace tayi mata alk'awarin hakan suka zuba ma juna ido da k'yar murya na
rawa Fatuu tace "Y....YA HAISAM NE!!!" Kaman saukan aradu haka Fauzy taji Maganar gaba d'aya ta zaro
ido waje baki bud'e k'irjinta ya fara wani irin bugu k'arshe ta mik'e da sauri ta nufi kopar d'akin ta d'aga
labulan ta d'an lek'a wajen ta tabbatar ba kowa sannan ta maido kan ta ciki tasa hannu ta tura kopar
cikin tashin Hankali ta dawo ta zauna inda ta tashi a kidi'me tace "Zarah kina da hankali kuwa? have u
gone mad! Saboda na matsa maki sai kin fad'a mani wanda yay maki hakan shine zaki raina man hankali
don ki kare kan ki, mi Ya Haisam yay maki da ya cancanci wannan bak'in k'azafi daga gare ki???" Jujjuya
kai Fatuu ta shiga yi ita dama tasan zai yi wuya duk wanda yaji Maganar nan ya yarda da ita tana
sheshsheka tace "Wllh Fauzy da gaske nike shine yay rapi...." Tun kan ta k'arasa Fauzy tay mata yar
tsawa tace "Enough Zarah, enough pls wannan Maganar taki ba abu bane da hankali zai d'auka wllh
haba how on earth ace mutum kaman ya Haisam wai shine yay raping d'in ki, kawae na gane kina mashi
sharri ne don ai saurin barin Maganar amman wllh kin ban mamaki mi ya Haisam yay maki da zaki mashi
bak'in k'azafi?" Cikin kuka tace "Fauzy akan wane dalili zan mashi k'azafi miya man tunda nike dashi in ba
Alkhairi ba ba abunda yake shiga tsakanin mu sai yanzu da yay man wannan mummunan abun shiyasa
tun farko kika ga na kasa fad'i maki wanda yay man d'in Wallahi tallahi kinji na rantse shine kuma in zaki
lura ke kan ki rannan ba sai da kika tambaye ni wai lafiya kika ga ban ciki Maganar shi ba yanzu kuma ko
waya baki ganin muna yi kaman da har nace maki hankalin shi ne ba kwance ba tunda jinyar mahaifin shi
yake to kawae na fad'a maki ne don abar Maganar wllh" da alama mutuwar zaune Fauzy tay ko idonta
bai motsi ba k'aramar razana tay da jin zancen ba k'irjinta kai kace ana mata daka a wurin, ba wai bata
yarda da zancen Fatun bane kawae ta kasa believing Haisam zai iya aikata wannan d'anyen aikin ga wata
ma ba Fatuu ba, ta d'auki lokaci bata ce uffan ba sai da aka d'an jima sannan ta sauke nannauyar ajiyar
zuciya idonta akan Fatuu tace ta fad'a mata ya akai hakan ta faru nan Fatun ta shiga bata labari tiryan
tiryan bata 6oye mata komae ba har yadda ta kasa hanashi da farko da kuma yadda har ya aikata mata
hakan tana gamawa ta fashe da matsanancin kuka tana Fad'in ya cuceta ya gama da rayuwarta gashi
yanzu yaja mata abun kunya, itama Fauzy kuka ta saka suka taru sukai tayi aka rasa mai rarrashin wani
da k'yar Fauzy ta mik'e ya nufi gadon Fatun ta hau ta jawota jikinta ta shiga rarrashinta tana cewa ta
daina fad'in abunda take fad'i akan shi daga jin yadda abun ya faru bada niyya bane kawae kaddara ce
da sharrin shaid'an jin hakan yasa Fatuu d'agowa cikin kuka tace "duk da hakan harda son zuciya Fauzy
dama yanzu na fahimci yana man wasu abubuwa da bai saba ba rannan fa a parlorn shi kama shi nay
yana kallon man boobs ena gashi yay ta yawan ta6a ni bai jin komae ranar da zai koma wancan zuwan da
yayi harda hugging ena fa yayi kawae na fahimci ya fara sha'awata ne shiyasa ya kasa daurewa duk da
magiyar da na rink'a mashi amman saida ya cutar da ni" shiru Fauzy tay kaman tana nazarin wani abu
Fatun ta maida kanta jikinta don wani irin Sara mata yake can bayan wani lokaci Fauzy tace "Yanzu miye
abun yi don ni wllh kaina ya riga ya k'ulle saboda wannan ba k'aramin Al'amari bane ba kowace zuciya
zata iya d'auka ba" da sauri Fatuu ta d'ago ta kama hannuwanta cikin muryar kuka tace "mu zubar da shi
kawae Fauzy ba tare da kowa ya ji ba" waro ido Fauzy tay a razane tace "abortion kuma keda kan ki kike
fad'ar hakan sai kace baki san tarin illolin shi ba......" Katseta Fatuu tay "Eh nasani Fauzy amman shi
kadae ne mafita wllh in ba haka ba ba k'aramar matsala cikin nan zai jawo ba na farko kinga da an sani
za'a kore ni daga school d'in nan kuma bazan k'ara samun damar yin karatu anan ba ga suna na da zai
6aci, duk ba ma wannan ba gwaggo nafi ji wllh taji zancen nan zuciyarta na iya bugawa ta mutu kinga
Saboda fa wanda za'a aura man d'in nan ba shiryayye bane yana neman mata ta kasa natsuwa har da su
ciwo to ina ga yanzu in taji ina d'auke da cikin shege...." tana kai k'arshen Maganar ta fad'a jikin Fauzy
tana cigaba da yin kukan, shiru Fauzy tay ita dae har ga Allah tsoron abortion take can tace "ni gaskiya
Zarah ban goyon bayan ki abortion Saboda abunda kan iya faruwa duk da ba fata ake ba za'a iya samun
matsalar da asirin mu kuma zai zo ya tonu kinga anyi ba ai ba kenan ga laifin kisan kai kuma a wurin
Ubangiji gaskiya dae muyi tunanin wata mafitar ba wannan ba",

Fatuu da ta d'ago daga jikinta tace "wace mafita kike tunani data fi wannan Fauzy, in ba hakan muka yi
ba duk abunda zamuyi asirinmu tonuwa zai yi ni kuma abunda ban so kenan kar ki manta akwae aminci
mai k'arfi tsakanin Gwaggo da Hajiyar su shekaru masu yawa suna zumunci na tabbatar in wannan abun
ya bayyana sai zumuncin nan ya lalace abubuwa da yawa Al'amarin nan zai shafa don Allah Fauzy ki bani
goyon baya in sha Allahu ba wata matsala da za'a samu kuma Allah zai yafe man tunda yasan ba da son
raina hakan ta faru ba sannan cikin kinga k'arami ne ko kwana arba'in bai yi ba duka watan shi guda"
shiru kawae Fauzy tay tana bin ta da ido ita dae hakanan hankalin ta bai kwanta da a zubar da cikin ba ba
kamar wasu abubuwa da take nazari, magiya Fatuu ta shiga yi mata kan azubar d'in can ta nisa tace "kin
gane Zarah ni wllh raina bai kwanta da a zubar da shi ba ba kamar dana yi la'akari da wasu abubuwa shin
Ya Haisam ya ta6a kai ki gidan tunda kuke dashi?" a hankali ta girgiza mata kai alamar a'a shiru Fauzy tay
tana sake yin nazari tsawon shekara biyar da suka san juna amman bai ta6a kaita gidan ba sai yanzu
sannan tace yana yawan ta6a ta ba tare daya ji komae ba wanda a yadda ta bata labari a da sam bai
mata haka hasali ma bai son su ke6e su biyu to miyasa yanzu yake mata hakan? wata Zuciyar ta raya
mata k'ilan don yanzu ta girma ta zama cikakkar budurwa shiyasa ya fara jin sha'awarta kamar yadda
itama Fatun take tunani can kuma nazarinta ya gangaro kan Alkhairin da yake mata wanda harda su
wayar miliyan hakanan ba dangin iya bana baba nan ma wata zuciyar ta sake raya mata wannan ai
daman ya saba yi mata Alkhairin kuma zai iya yuwuwa ko ya fara son ta ne shiyasa har Yay mata irin
kyautar, k'arshe dae kan Fauzy ya k'ulle tamau ta kasa yin tunanin wani kwakkwaran dalili don komae a
bud'e yake amman tana jin kaman something is amissing k'arshe dole ta bar ma ranta kawae kaddarar
su ce a hakan, kallon Fatuu tay tace "zan amince a zubar kamar yadda kike so amman da sharad'i guda"
da sauri Fatuu tace miye sharad'in Fauzy taci gaba "Dole Ya Haisam yasan da cikin nan kafin mu zubar
d'in" wani kallo Fatuu tay mata a marairaice tace "miyasa za'a sanar mashi Fauzy abunda shi baima
damu da abun da yay man ba kina gani tunda hakan ya faru sau biyu ya kirani ban d'aga ba daga nan fa
bai sake kira ba dama shima kiran sai kusan da akai 2 weeks sannan don Allah mu rabu dashi kawae ni
nasan ba wani abunda zai yi" d'an girgiza kai Fauzy tay tace "karda idon ki ya rufe Zarah zubda ciki fa ba
k'aramin abu bane da za'a ce ayi ba tare da mai shi ya sani ba yanzu ba fata nike ba azo Asiri ya tonu
wurin zubarwar taya zamu kare kan mu tunda shi ba sanin da cikin yay ba think about it Zarah" d'an
shiru Fatuu tay duk ranta bai so ba tace mata ita tana ganin in sha Allahu ba abunda zai faru ai cikin
k'arami ne they should just go ahead and do d abortion ba tare da ya sani ba amman Fauzyn ta kafe kan
ita dae a sanar mashi don bata tunanin hakanan yak'i kiranta dole da dalili Fatun tace to taya zata sanar
mashi shi da bai nan kuma dae ai bai dace ta kira shi yana can wurin jinyar ba, d'an jimm Fauzy tay sai
kuma tace "mi zai hana ki kira Kawu Amadu ki tambayi ko sun dawo baki sani ba" gyad'a kai tay ta juya
can kusa da pillow ta d'aukko wayar ta fara k'ok'arin kiran Amadun ringing biyu ya d'aga ta gaishe shi ya
amsa ya tambayeta ta dawo gida ne don shi yana Makaranta tace mashi a'a sai anjima d'an shiru tay jin
hakan yasa ya tambayeta da wani abu ne tace a'a kawae tana son ta tambaye shi ko Hajiyar Sanata ta
dawo ne, yar dariya yay yace "ke dai fad'i gaskia kodae ran ki ne ya baki Romeo d'in ki ya dawo shine
kike son ki tabbatar" d'an yamutsa fuska tay tace "kai Kawu Amadu ni don Allah ka fad'a man ai Hajiya
dae na tambaye ka ba wani ba ko" tana jiyo dariyar shi kafin yace mata eh ta dawo jiya da yamma harda
ma Romeo d'in nata, ko sallama bata yi mashi ba ta katse kiran da ta kalli Fauzy har bata san tayi d'an
murmushi ba tace mata ya dawo jiya itama murmushin tayi tace "yauwa kinga Allah ya taimake mu
komae zai zo da Sauk'i in sha Allah" cike da farinciki Fatuu ta fad'a jikinta tana Fad'in "Thank u so much
Fauzy u'r more like my blood sis than Friend, Nagode ma Allah da yake had'a ni da k'awaye Nagari
wanda duk in ina cikin damuwa suma suke shiga damuwa har su bani shawara mai kyau da zata fitar
dani" d'agota Fauzy tay tana murmushi tace "What are Friends for, haka yakamata aboki na gaskiya ya
kasance wani lokacin in kai dacen aboki sai kaji ma har yafi maka wani dan'uwan naka na jini hakan nake
ji a tattare dake Zarah" k'ara fad'awa tay jikinta tana murmushi can taji Fauzyn tace "How I wish ace cikin
nan na halak ne lokacin da zamu gama makaranta kuna da d'an yaron ku ko yaranku in twins ne lokacin
nasan har sun d'an tasa ma, wai za'a ga ruwan kyau dae wllh amman ba komae komi Allah yay mai kyau
ne fatana dae ya shige mana gaba a duk abunda zamu yi" Fatun ta amsa mata da Amin a hankali Fauzyn
tace mata to ta tashi tay wanka ta shirya sai taje ita kuma zata jirata har ta dawo bazata tafi weekend ba,
sosae Fatuu taji dad'i ta mik'e, ba'a d'au wani lokaci ba tayo wankan ta zura doguwar riga bak'a ta yafa
gyalenta Saboda zumud'i har ta ma manta da ita mara lafiya ce, tare suka fito har wajen gate cikin sa'a
suka samu Napep da Fatuu zata shiga Fauzy ta kama hannunta tace "kiyi man alk'awari nima zaki same
shi kiyi mashi Maganar" kai ta d'aga mata tace "nayi maki Alk'awari kuma in zan dawo zan taho da
allurar sai kiyi man" d'an jimm Fauzy tay kafin ta gyad'a mata kai tace shikenan amman dae ta tabbatar
sun fara yin Magana da shi daga haka ta shige Fauzy na d'aga mata hannu suka tafi.

Tunda suka shigo Unguwar gabanta ke fad'uwa har d'an rufe fuskarta take don kada gwaggo ko Kawu
Amadu wani ya ganta Saboda bazata shiga gidan su ba don kada gwaggon ta gano halin da take ciki ba
kamar da ta tuna Maganar data yi mata rannan, har bakin gate mai Napep d'in ya kai ta bayan ta biya shi
tana ruk'e da yar purse d'inta ta tunkari gate d'in Office yay mata ya Makaranta ta amsa bayan ta gaishe
da shi ta shige, part d'in Hajiya tay tunanin fara zuwa don tayi mata ya mai jiki kuma k'ilan ma ta iske
Haisam d'in a can tunda yau Friday, lokacin data shiga Hajiyar na zaune a parlor tayi gayun Juma'a bak'i
tayi bayan ta dawo daga Masallaci basu dad'e da tafiya ba ta zauna tana kallo idanunta sanye da medical
glasses d'inta, tunda Fatuu tay sallama ta maido idanunta kanta tana kallonta har ta k'araso cikin parlon
ta zauna kujerar dake opposite da ita da d'an murmushi tace "Hajiya ina wuni an dawo lafiya" still
kallonta take fuska a sake ta amsa mata, Fatun ta sake cewa Ya mai jiki, d'an girgiza kai Hajiya tay tace
"mai jiki sai dae mu ce Alhamdulillah don an sha jiki kam amman cikin hukuncin Allah ya warke garas
abunda ake gudu Allah ya tak'aita faruwar shi" itama Fatun Alhamdulillah tace kafin tay Addu'ar Allah ya
k'ara mashi lafiya Hajiya ta amsa, d'an shiru sukae Fatun ta lura da Hajiyar sai kallonta take hakan yasa
tasha jinin jikinta ta sadda kai tana wasa da yatsunta can ta d'ago tace ma Hajiyar Ya Haisam na part d'in
shi ne zata mashi ya mai jiki d'an girgiza kai ta k'ara yi tace "bai nan tun jiya da muka dawo yana G.r.a da
yake har yanzu shi kaman jikin nashi bai idasa warwarewa ba" shiru Fatuu tay tana maimaita abunda
tace a cikin ranta can ta tambaye ta bai lafiya ne, Hajiyar ta ruk'e ha6a tace "ai ciwo yasha shima a can
jinya biyu akai wllh dama dae tun da muka bar nan zamu Kano na lura da yanayin shi har na tambaye shi
sai yace man fever ke damun shi to da yake mutum ne mai k'arfin hali a hakan har suka fita da Mahaifin
na su da yake mu sai daga baya muka bi bayan su Germany d'in, to a can ma bai samu ya huta ba bayan
sun je aikuwa sai ciwo ya buge shi wani irin zazza6i mai zafi da ciwon kai suka taru suka rufe shi dama
kuma shi yana dad'ewa bai yi ciwo ba, amman fa duk randa ya kwanta yana jin jiki wllh don ni bazan iya
tuna ma yaushe yay irin wannan ciwon ba amman dae Alhamdulillah ya samu sauk'i sosae nayi ma
tunanin zai wuce can U.s d'in da yake suma su Fanan d'in sun zo nan Germany kusan ita tay jinyar mijin
nata har ya samu sauk'i to da zamu dawo ne ita ta wuce can shi kuma muka dawo dashi" duk sai jikin
Fatuu yay d'an sanyi a hankali tace Allah ya k'ara basu lafiya Hajiyar ta amsa har zata mik'e taji tace
"amman kema dae Fateema kaman baki lafiyar ko?" Damm gabanta ya fadi a dabarbarce tace mata eh
itama malaria ke damunta, Hajiyar tace to taga likita ko don fuskarta ta fad'a da yawa gashi tayi fayau
kamar mara jini da sauri tace mata eh taje taga likita har test an yi mata an kuma bata magunguna yanzu
haka tana cikin sha ma Hajiya tace to Allah ya k'ara lafiya ta amsa da Amin had'i da mik'ewa zata tafi
Hajiyar tace ba ta bari taci Abinci tace a'a ta k'oshi taci Abinci daga haka sukai sallama ta nufi hanyar fita,
lokacin data fito har saida ta saki yar ajiyar zuciya bayan ta fito wajen gate sai taji dama ta san bai nan da
bata bari mai Napep d'in ya tafi ba, ta bayan gidan Hajiyar ta bi saida ta kusa bakin titi sannan ta samu
mai Napep ta fad'i mashi G.r.a zai kaita yace to ta hau suka tafi, bayan sun iso ya tambayeta road d'in da
zai kaita tace bata san sunan road d'in ba da yake sau d'aya ta ta6a zuwa kuma da daddare ne amman
zata rink'a nuna mashi hanya yace to, da yake G.r.a ba kaman geto bace sam Fatuu ta kasa gane gidan
sai faman uban zagaye layuka suke a kokarin ta na ta gano, sun d'auki lokaci tana dudduba gidajen
Unguwar har dae mai Napep d'in ya gaji ya parker a gefen hanya yace mata gaskiya fa ba lallae su gane
gidan ba tunda bata san sunan layin da yake ba k'arshe zasu yi ta yin wahala ne, shiru tay da alamun
damuwa bata son ta koma ba tare data gano gidan ba don ta san k'arshe ba lalle Fauzy ta bata goyon
baya ba ganin yadda ta damu yasa mai Napep d'in tambayarta bata san sunan mai gidan bane d'an Jim
tay ta tuno da Haisam yace ai gidan baban shi ne hakan yasa tace ta sani gidan Senator Alee Adamu
Zakee ne yace to bari yaga in za'a samu wanda za'a tambaya da sauri tace to ya fita daga cikin Napep d'in
yana duba hanya can saiga wata Mota ta taho ya d'aga ma mai Motar hannu cikin sa'a ya tsaya daga
d'an gaban Napep d'in ya nufi Motar da sauri, slowly glass d'in driver side ya sauka wani Alhaji ne a ciki
mai Napep d'in ya gaishe da shi bayan ya amsa yace don Allah tambaya suke yace to Allah yasa ya sani
mai Napep d'in yace "dama wani gida ne muke ta nema mun kasa ganewa gidan wani Senator Alee....."
kakarewa yay yana niyyar d'aga kai ya tambayi Fatuu yaji Alhajin yace gidan Senator Alee Adamu Zakee
da sauri mai Napep d'in yace yauwa eh nan, kwatance yay mashi mai Napep d'in ya gane yay mashi
godiya yaja Motar shi kuma ya koma Napep d'in Fatuu ta tambaye shi an gane gidan yace eh sosae taji
dad'i duk da fargabar da ta cika ta, suna shiga titin layin da aka masu kwatance Fatuu ta hango gidan ta
nuna ma mai Napep d'in ya tunkare shi, a gaban tangamemen gate d'in ya parker ta fito su Officer na
zaune a saman benci ta nufe su idanun su a kanta har ta k'arasa ta tsaya daga d'an gaban su, bayan ta
gaishe dasu tace don Allah ko Ya Haisam na nan d'ayan Officern da tunda ya ganta ya ganeta yace mata
eh yana nan, d'an shiru tay ganin haka yasa shi ce mata ba wurin shi tazo bane tace eh yace to ta shiga,
juyawa tay ta koma wurin mai Keke Napep d'in tace don Allah ya jirata ba dad'ewa zatay ba sai su koma
yace ba matsala hajjaju a fito lafiya harda ce mata wai ta taho mashi da lemu mai sanyi mak'oshin shi ya
bushe Saboda yawon da suka sha ta d'aga mashi kai kawae, ta k'aramar kopa ta bi ta shiga gidan tunda
ta tunkari ginin gabanta ke fad'uwa abubuwan da suka faru rannan suka shiga dawo mata, saida tay yar
tafiya mai d'an tsawo ta isa ginin gidan ta shiga Parlon kafin ta bi ta Corridor ta nufi kopar Bedroom d'in
shi.........

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2049*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.........tsaye tay a bakin kopar k'irjinta na ci gaba da bugawa da sauri da sauri ga tsoro da ya kamata ta
d'an d'auki lokaci a haka kafin tay k'arfin halin kai hannu yana d'an rawa ta d'an kwankwasa shiru bata ji
an yi magana ba hakan yasa ta k'ara d'an kwankwasawa da d'an k'arfi k'asa k'asa ta jiyo Muryar shi yace
"Who is dat" shiru tay har saida ya sake tambaya amman ta kasa bud'e baki tace itace jiyo shi tay yace a
shigo kopan a bud'e take da turanci d'an jimm tay kaman bazata shiga ba can ta d'an runtse ido kafin ta
bud'e fuska a d'aure slowly ta tura kopar, tana shiga suka had'a ido da shi yana zauna akan kujera 3
seater yana operating system jikin shi sanye da jar armless gabanta anyi bak'in rubutu sai bak'in wando
3-quater abu dae sai dae ace Tubarkallah daga gefen shi c-table ne a saman table d'in kwalin lemu ne
aje sai tumbler daga gefe kuma ledar take away ce mai d'auke da tambarin wani Eatery, bin ta da ido yay
ya yi matuk'ar mamakin ganinta duk da fuskar shi bata nuna hakan ba itama tsaye tay tana mashi wani
irin kallo cike da 6acin rai don bata tsammaci ganin shi haka ba wato dae zargin ta ya tabbata na bai
damu da abunda ya aikata mata ba tunda gashi zaune ya warke har yana latse latsen computer ba tare
daya nemeta ba tunda suka dawo,

"Come inside" taji cool voice d'in shi ta fad'a kaman bazata shigan ba ta d'aure fuska tamau can dae ta
nufi cikin a gefen shiga inda kujerun suke ta ja ta tsaya tana kallon gefe kallonta kawae yake ya lura da
yadda ta d'aure Fuska can yace "come and have a seat" banza ta mashi kuma bata kalle shi ba har saida
ya k'ara mata magana kan taje ta zauna a d'an fusace ta kalle shi tace "ba shi ya kawo ni ba" still idon shi
na a kanta ita kuma ta k'ara juyar da fuskarta can yay sigh yace "am listening miya kawo ki?" d'an
yamutsa baki tay alamun mamakin jin yadda ya tambayeta seemed he doesn't care at all aikuwa sosae
ranta ya k'ara 6aci idanun ta suka ciko da k'walla ta juya cikin rawar murya ta fara magana "Zuwa nai in
fad'a maka ka cuce ni, ka zalunce ni Ya Haisam, an yarda da kai amman kaci Amana kayi man abunda
wani ma ban tunanin zai man hakan balle kai, kace ni matsayin k'anwar ka ta jini ka d'auke ni amman
abunda kai man ya tabbatar da k'arya ne don in hakan ka d'auke ni baza ka ta6a son wani yayi man
hakan ba balle kuma kai da kan ka, kowa nawa ya amince maka amman duk da haka ka ha'ince su kai
man abunda na tabbatar ba kuskure bane da niyya ne tunda sai da na rok'e ka amman ka k'i saurare na
Saboda dama kana neman dama ne don ka fara nuna alamomin kana son ta6a jikina...." dakatawa tay
tana goge kwalla shidae sai kallonta kawae yake bazaka gane yanayin da yake ciki ba, tsayawa tay da
goge kwallan cikin muryar kuka tace "..gashi nan sakamakon abunda kai man ka jawo mana abun kunya
wanda na tabbatar gwaggo in taji zuciyarta na iya bugawa ta mutu...." dakatawa tay tana sheshsheka sai
lokacin yanayin fuskar shi ya canza ya d'an k'ank'ance ido alamar tunani kan abunda ta fad'a kan shi ne
ya d'aure gashi tak'i cigaba da Maganar sai kuka take faman yi tsam ya mik'e ya nufo ta ya tsaya gabanta
Slowly ya furta "What is it?" d'ago kai tay ta kalle shi cikin kuka tace "CIKI gare ni!!!" yanayin kallon da
yake mata ne ya sauya with surprise written boldly al over his face ya furta "U'r pregnant???" Kai ta
d'aga mashi alamar eh kan shi ya d'aure ya ayyana taya hakan zai faru sai kallonta kawai yake ita kuma
tana cigaba da yin kuka ta juyar da face d'inta gefe can taji yace "how did you know dat u'r pregnant?"
shiru tay mashi don sai taji tambayar ma ta rainin wayau ce tunda ai yasan karatun da take, "am asking
you Zarah" ya k'ara fad'a ba tare da ta kalli face d'in shi ba ta fara gaya mashi ciwon da take da yadda
aka fara gulman ciwon da take a school har zuwa yadda taje ta siyo Pt strip ta auna tana gama fad'i
mashi ta kai hannu ta bud'e yar purse d'in dake ruk'e a hannunta ta fiddo shi dama bayan ta shirya Fauzy
ta saka mata shi tace in tazo ta nuna mashi mik'a mashi tay ya kai hannu ya amsa ya fara dubawa nan
take ya tabbatar ma kan sa da gaske cikin gareta, d'agowa yay mamaki shimfid'e akan fuskar tashi ya
kafeta da ido sai lokacin ma ya lura da canzar da tayi tay wani fayau dama gashi bak'ak'en kayane a
jikinta, shiru ya rasa mi ma zaice abun ya matuk'ar bashi mamaki abun da akai just once amman ace har
ciki ya shiga jin yayi shiru yak'i yace Komae yasata cewa "Dama nasan bazaka iya cewa komae ba, iya
cuta dae ka cuce ni Ya Haisam yanzu da an san da wannan abun kunyan shikenan Mutuncin mu ni da
gwaggota ya gama zubewa a idon mutane ga school ma da an sani korata za'ai ga dangin Baffana su
bansan iya abunda zai faru ba in suka ji zasu ce dama abunda gwaggo ke sani ina aikatawa kenan shiyasa
tai duk yadda zatayi ta hana in auri wanda suka za6a man Saboda manemin mata ne to gashi nan nima
ashe abunda nike aikatawa kenan, wllh Ya Haisam ka zalunce mu kayi amfani da son zuciya wajen
tarwatsa mana farinciki ko wanda a da za'a aura man da yake halin shi bai cutar da ni har haka ba don
nasan Ya Abbas ya fad'a maka dalilin fasa auren mu sai kai da aka amince mawa kai da nake kallo
matsayin Yayana uwa d'aya uba d'aya...." Kuka sosae take shi kam zuba mata ido kawae yay don a
rayuwar shi wani bai ta6a tutsiye shi haka ba itace mutum ta farko, d'an tsagaitawa tayi tace "zuwa nayi
dama in fad'a maka game da shi sannan in sanar da kai zubar dashi zan yi don bazan bar wannan abun
kunyar a tare da ni ba ko don gwaggota da sauran dangi na kuma kai ma hakan zai rufa maka asiri duk da
kai ka za6i zubar man da Mutunci to ni bazan so in zubar maka da naka ba don har yanzu kana da girma
a idona sai dae ina k'ara tunasar da kai ka cuce ni ka ci amanar yarda" tana kai k'arshen Maganar tay
gaba abunta fuu bai juya ya kalleta ba har ta fuce ya zuba ma abun hannun shi ido jikinshi yay weak
sosae slowly ya d'an matsa ya zauna akan hannun kujera ya d'aura ha6ar shi akan hannun shi guda da ya
dungule ya rasa ma murna zai yi ko kuwa don tunda yake bai ta6a jin fargabar wani abu ba irin wannan
sosae kuma yay mamaki bai ta6a kawowa hakan Zai faru ba runtse ido yay ya shiga tariyo kalaman Fatuu
har zuwa k'arshe da tayi zancen zubar da cikin tunanin abunda yakamata yayi ya fara zuciyar shi ta raya
mashi yakamata yay saurin dakatar da ita fa don zata iya aikatawa wani abun kuma yazo ya sameta.....
Tana ta faman goge k'walla ta fito daga cikin gidan ko kallon inda su Officer suke zaune bata yi ba ta nufi
Keke Napep d'in bayan ta shige tace mashi su tafi bai tanka mata Maganar lemun da ya ce ta fito mashi
da shi ba ganin halin da take ciki, bayan ya ja Napep d'in sun bar wurin d'ayan Officer wanda bai san
Fatun ba ya kalli abokin aikin nashi yace "ita waccan d'in wacece naga kaman kasan ta" yana murmushi
yace "nima ban san wacece ba kwanaki ne Yalla6ai yazo tare da ita" da alamun mamaki yace "nan gidan
suka zo?" Kai ya d'aga yace "eh da daddare inaga wurin k'arfe 11 ma" jinjina kai d'ayan ya hau yi alamar
mamaki kafin yace "wato ya fara kawo mata kenan amman nayi mamaki koda yake dama irin Mutanen
nan sun fi bada mamaki" yar dariya d'ayan yay yace "nidae ban ce maka ya fara kawo mata ba ka sani ko
yar uwarsu ce"

"Kai tunda kake aiki a gidan nan ka ta6a ganinta koda in masu gidan na nan kuma koda yar uwarsu ce mi
zaisa ya zo da ita a wannan lokacin tunda yasan gidan ba kowa kai dai Allah ya kyauta kawae gata ma ta
fito tana goge fuska da gani kuka take" da alamun mamaki d'ayan yace "na gani wllh kasan ko rannan ma
haka ta fito tana kukan wurin d'ayan dare....." Katse shi yay ya maimaita lokacin da ya fad'an had'i da
ruk'e ha6a d'ayan yace "wllh amman dae tace ya tsaya yin wani aiki ne a computer sai bacci ya kwashe
ta lokacin da ta farka kuma shima ya riga yay bacci" d'ayan yace "to in haka ne miye na ta fito tana
kukan?" Still da murmushi yace "zazza6i ne ya rufeta tace dalilin farkawar tata kenan amman
dae.....kawai muyi mashi kyakkyawan zato kaman ko yaushe" dan ta6e baki d'ayan yay yana wani
murmushi.

Tana cikin Napep d'in wayarta ta fara ringing duk a tunanin ta Fauzy ce ta bud'e purse d'inta ta fiddo
wayar tana kallon screen d'in taga sunan Haisam ya bayyana wani irin tamke Fuska tay tak'i yin picking ta
d'aura wayar a kan laps d'inta har ta katse can sai ga wani kiran ya sake shigowa still tak'i d'auka saida ya
kira na ukku mai Napep d'in yace mata ana waya cikin disasshiyar murya tace mashi tana ji ya jinjina kai
yana kallonta ta side mirror ganin tana ta goge kwalla yasa shi ce mata tayi hakuri ta d'aga mashi kai
kawae. Tsaye yake wayar shi ruk'e a hannu ganin ya kira har sau ukku bata d'aga ba yasa shi yin shiru
kaman mai yin tunani can ya juya ya nufi inda bed d'in shi yake ya zauna a edge d'in gadon ya kai hannu
ya d'auki wayar landline dake aje a saman bedside ya kira gate saidae har ta tsinke itama ba'a d'aga ba
don su Officer d'in na wajen gate maidawa yay ya aje ya fara k'ok'arin kiran shi ta wayar dake hannun shi
ringing biyu Officer d'in ya d'aga tun kafin yace wani abu Haisam yace mashi akwae wata da ta fita yanzu
ya bita ya tsaidata gashi nan fitowa Officer na jin haka ya gane wadda yake magana akai yace mashi ai
tare da mai Keke Napep take kuma tana fitowa suka tafi yanzu ma yasan sun yi nisa tun kafin ma ya
k'arasa Haisam ya katse kiran yay zaune jigum ya rasa miya kamata ma yayi gaba d'aya ya shiga damuwa
har fuskar shi ta nuna sanin abortion ba k'aramin hadari ne dashi ba komai zai iya faruwa gashi yasan
halinta har yanzu she's stubborn tunda ta fad'a abunda zatai kenan, k'ara kiranta yay still ba ta d'aga ba
bayan kiran ya yanke d'an shiru yay can kuma sai ya shiga cikin messages ya tura mata sak'o kamar haka,

Don't do anything Zarah, pick my call now.


Bayan ya tura da yan mintuna ya sake kira still bata d'aga ba tafin hannun shi ya kai ya rufe daga hancin
shi zuwa ha6arshi yana breathing heavily yasan shi yay mata laifi amman bai yi tunanin zata iya mashi
haka ba, lokacin da sak'on ya shigo wayar ta ta duba d'an ta6e baki tay a ranta tace ko na d'auka ba
abunda zaka fad'a man k'arshe kace kar na zubar tunda ba kai ne a matsala ba dama ance komi namiji
yay ado ne to wllh sai na zubar dashi k'arshe ma sai ta saka wayar a silent kawae, suna hawa titi mai
Napep d'in ya tambayeta ina zai kaita ta ce babban Asibiti suka d'auki hanya,

Yanata zaune can ya yanke yabi bayanta ya mik'e da sauri ya nufi cikin Corridor bada Jimawa ba ya fito
ya canza kaya zuwa jeans da t-shirt bayan ya d'auki wayar shi da car key ya fice da sauri, parking space
ya nufa ya bud'e Motar da zai hau ya shiga bayan yayi mata key ya fito ya tunkari gate yana sakin horn
da k'arfi tuni su Officer suka mik'e aka zuge mashi Gate d'in ya fice ko ta kan d'aga mashi hannun da suke
bai bi ba, bayan wanda ya bud'e gate d'in ya rufe ya dawo yace ma abokin aikin ka lura da yadda ya fita
kaman akwae abunda ke faruwa yace mashi eh shima ya lura kuma yana tunanin game da yarinyar nan
ne da ta zo tunda ya kira yana a tsaidata d'ayan ya d'an jinjina kai yace Allah ya kyauta to ya amsa mashi
da Amin, Har ya fito daga Unguwar bai ganta ba dama bai yi tunanin zai gantan ba tunda ance a Napep
take tunanin inda yakamata ya nufa ya shiga yi ganin ranar Juma'a ce yasan tana komawa gida Weekend
yasa ya yanke zuwa can,

Suna zuwa gab da Asibitin tace ma mai Keke Napep d'in ya d'an tsaya wanccan Pharmacy d'in zata amshi
abu yace to ta ciro gyalen jallabiyar ta ta nad'a shi kaman nikab ta yadda ba za'a gane face d'in ta ba
bayan ta gama ta bud'e purse ta fiddo yar takardar data rubuta sunan allurar da zata siyan dama tun
kafin ta fito ta rubuta ko Fauzy bata sani ba, nufar cikin pharmacy d'in tay mai Keke Napep d'in nata
kallonta cikin d'aurewar kai ganin tayi basaja wanda da ba haka take ba, bayan ta shiga ta mik'a ma d'aya
daga cikin yan shagon takardar tace ita take so in akwae ya amsa yana dubawa can ya d'ago ya kalleta
yace akwae amman basu yi ma Mutane da sauri tace Owk dama ba yi mata za'ai ba ya juya bayan ya
d'aukko yace taje ta biya ta nufi cashier d'in ta biya aka bata receipt ta dawo ta amshi allurar ta juya
yana ta kallonta har ta fice k'arshe ya d'an girgiza kai kawae, bayan ta koma cikin Napep d'in yaja suka
nufi cikin asibitin, a daidai gate d'in School d'in su ya tsaya bayan ta fito ta bud'e purse d'inta ta fiddo
1500 ta mik'a mashi ya amsa ya duba da mamaki ya kalleta ganin kud'in sunyi yawa tun kafin yace wani
abu tace yasha lemun da bata d'aukko mashi ba da sauran ta juya ta nufi ciki yana ta washe baki yana
mata godiya, tana shigewa tasa hannu ta kwance gyalen ta nufi Hostel. Sosae yay gudu nan da nan ya iso
kopar gidan su bayan ya parker ya bud'e ya fito lokacin Amadu na cikin shago yana hango shi da sauri ya
bud'e ya fito ya nufo shi suka had'e ya gaishe dashi bayan ya amsa mashi yace "Zaraah na ciki?" d'an
shiru Amadu yay alamar tunani can yace "gaskiya kaman bata nan don tunda na dawo daga school ban
ganta ba kuma da ina cikin shago ban ga ta zo ba, shiru Haisam d'in yayi Amadu ya lura yanayin shi ya
canza hakan yasa yace mashi bari dae yaje ya tambaya ko ta dawo da bai nan ta fita kai kawae Haisam ya
d'aga mashi ya juya da sauri ya nufi cikin gidan, d'akin gwaggo ya nufa lokacin tana kwance kan gado
tana bacci tayi wankan juma'a wurin kanta ya tsaya ya fara kiran sunanta a hankali ta ware idonta akan
shi tana ganin shi ta yunk'ura ta tashi zaune tace mashi lafiya tambayarta yay Fatuu ta dawo ne tace "a'a
lafiya?" Yace "dama Ya Haisam ne yazo yana tambayarta yana waje" tace "ba ta kaiga dawowa ba har
yanzu kace mashi tana Makaranta k'ilan zuwa zai ya d'aukko ta" d'an shiru Amadu yay sai kuma yace
mata k'ilan to daga haka ya juya yana fad'in bari ya fad'i mashi, bayan ya fito ya sanar dashi har yanzu
bata dawo ba kai kawae ya d'aga mashi ya juya ya koma Motar bayan ya juyata ya koma ta hanyar da ya
biyo da gudu.

Lokacin da ta shiga d'akin nasu Fauzy na kwance tana bacci ta yi wanka tasa kaya a bakin gadon da take
Fatuu ta zauna ji tay kamar karta tasheta ta bari sai ta tashi amman kuma bata iya hakuri don ta k'osa ai
komae a gama hannu ta kai ta fara dan bubbuga jikinta a hankali ta fara motsawa kafin ta bud'e idonta
tana ganin Fatuu da sauri ta yunk'ura tana murza ido ta jingina da bango cikin muryar wanda ya tashi
daga bacci tace "kin dawo Zarah" kai Fatuu ta d'aga mata d'an shiru Fauzy tay tana ta kallonta can tace
"kin gan shi?" nan ma kan ta sake daga mata ta k'ara cewa "to ya ku kai dashi?" d'an ta6e baki tay
yanayin fuskar ta ya canza cikin bacin rai tace "bai ce komai ba sai faman bi na da ido kawae, ni dama
nasan fa ba abunda zai iya cewa shi kanshi daga yanayin fuskar shi na fahimce ya rud'e da jin zancen
cikin ba kamar dana nuna mashi pt strip d'in" shiru Fauzy tay saidae a ranta ta matuk'ar yin mamakin jin
wai bai ce komae ba can tace "to da ya ji Maganar zaki zubar da shi miya ce??" tace "dana fad'a mashi
shima tsaye yay man yana bina da ido har na baro mashi d'akin saida ina kan hanya ne naga ya kira ni ni
kuma ban d'aga ba" Fauzy tace "to Saboda mi Zarah ba sai Kiji mi zai ce ba" yamutsa fuska ta fara yi
idanunta suka ciko da k'walla cikin rawar murya tace "Fauzy da akwae abunda zai fad'a man tun ina can
da ya fad'i man kawai nasan bai wuce yace kar in zubar ba zai handling komae kuma wllh wannan ba yar
k'aramar matsala zai jawo ba ni gwaggota nafi ji Fauzy tun ina k'arama take bani labarin wata d'iyar yar
wajen aikin su da tay cikin shege a koda yaushe tana man misali da ita in tana gargad'i na koda na fara
period saida tay ta gargade ni akan kada na bari wani ko hannuna ya kama in ba haka ba zan samu ciki
Fauzy ki taimake ni ko don ita da karatu na da kuma kallon da za'a koma yi man ba kamar dangin mu har
ma dashi Ya Haisam d'in gara mu kawo k'arshen komai ba tare da kowa ya sani ba" ta k'arasa hawaye na
zuba daga idanunta had'i da kai hannu ta kamo hannun Fauzy shiru tay tana bin ta da ido wani irin
fad'uwa gabanta ke yi hakanan ita dae bata son a zubar da cikin ga fargabar mi zai iya zuwa ya dawo
magiya Fatuu taci gaba da yi mata can ta ja dogon numfashi cikin karyayyar murya tace "Zarah tsoro nike
wllh kada wani abu ya faru sakamakon yin allurar nan kinsan tana da illa fa" da sauri Fatuu tace "in sha
Allahu ba abunda zai faru raina na bani hakan kuma nayi maki Alk'awarin koda wani abun ma ya faru
bazan mentioning d'in ki ba zan d'aura ma kaina alhakin duk abunda zai faru pls k'awata wadda bata son
damuwata ki taimaka man" hannu Fauzy ta kai baki ta d'an cije yatsun ta tana nazari Fatun na cigaba da
kallon ta a marairaice can ta cire hannun cikin disashewar murya tace mata ta had'a allurar nan da nan
Fatuu tay d'an murmushin farin ciki ta fara kokarin had'a allurar.........

Sosae yake gudu yana driving d'in yana kai hannu bakin shi ya d'an ciza had'i da d'an bugun steering d'in
cikin lokaci kankani ya iso bakin gate d'in Makarantar su ya Parker sai lokacin ya fara tunanin yadda za'ai
ya samu ganinta in ma tana a cikin school d'in hannu ya kai gefe ya d'auki phone d'in shi ya fara kiranta
sai dae har ta katse bata d'aga ba haka saida ya kira sau biyar amman bata d'aga ba cikin tashin hankali
ya kai hannu ya d'aki steering d'in da k'arfi ya furta "ZARAH....!!!" shiru yay yana numfashi da sauri da
sauri kan shi ya gama k'ullewa bai san taya zai gan ta ba gashi bai san number d'in Fauzy ba balle ya
kirata zuciyarshi ce ta raya mashi the more yake 6ata lokaci the more rayuwar ta ke shiga hadari he has
to do something quickly hannu ya kai da sauri ya tashi Motar bayan ya juya ta ya jata da gudu ya tafi,
yana ta sak'e sak'en abunda yakamata yayi a ranshi k'arshe zuciyar shi ta yanke mashi kawae yaje ya
sanar ma Hajiya, bai d'au tsawon lokaci ba duk da da yar tazara ya iso Unguwar taso tun da ya karya
kwanar gate ya fara latsa horn wani na bin wani Officer na jin hakan ya tashi da sauri ya zuge mashi Gate
d'in ya shige fuuu bai nufi parking space ba ya wuce da Motar har kusa da part d'in Hajiya sannan ya
parker ta ya fito ko rufe kopar bai yi ba ya wuce ciki, lokacin da ya shiga Parlon kwalam ba kowa da sauri
ya nufi Bedroom d'in Hajiya yana shiga nan ma ya ga ba kowa har toilet ya nufa yay knocking tsit bai ji
anyi alamun da mutum ba hakan yasa ya juyo da sauri ya fito Parlor ya nufi hanyar fita har ya kusa kaiwa
k'opar fitan yaji motsi a bayan shi ya juya da sauri Amarya Saude ce don an d'aura mata aure da Officer
tarewa ce kawai ta rage, daga kopar baya ta shigo hannunta ruk'e da yar roba mai fad'i Haisam na
ganinta ya tunkare ta yana tambayarta Hajiya ko amsa gaisuwar da take mashi bai yi ba da hannu tay
mashi nuni da inda ta fito tace mashi tana baya wurin su d'awisu ya amsa da Ok ya nufi kopar ita kaita
saida tay mamakin ganin yanayin shi, yana fita bayan ya hango ta can a zaune akan kujera a gefen wurin
Aku da alama fira suke hannunta d'aya ruk'e da sandar ta ta alfarma da take amfani da ita yanzu wurin
yin tafiya, tun kan ya isa Aku yace ma Hajiya wai ga d'an ta nan jin haka yasa ta juya ta kalli Haisam dake
tunkaro ta kafin ta juyo tana dariya tace ma Akun bata fad'a mashi jikan ta bane ba d'anta ba Akun ya
dae yi shiru tamkar bai fahimci mi take nufi ba lokacin Haisam ya iso ya tsaya gefenta ta d'aga kai ta kalle
shi sai yama kasa ko gaida ita sai d'an motsa baki yake lokaci guda ta gane akwai abunda ke damun shi
tace mashi miya faru d'an shiru yay har saida ta maimaita sannan yace yana son yin Magana da ita ne
tace to ta taso ne ko anan zasu yi yace suje Parlor tace Ok ta fara kokarin mik'ewa Aku na fad'in sai kin
dawo Hajiyata tace to ya jirata suka nufi parlon tana gaba Haisam na bin ta a baya, bayan sun iso wurin
kujeru akan 3 seater ta zauna shima ya zauna daga can gefenta idanunta akan shi yay shiru yana kallon
carpet ganin haka yasa tace mashi shi take sauraro ya akai, shirun dae yaci gaba da yi ya rasa ta ina ma
zai fara tunda yake bai ta6a jin fargabar gaya ma wani magana ba irin yau saida Hajiya ta k'ara tambayar
shi da d'an k'arfi tace "miye wai ka fad'a in wani abu ya faru kayi man shiru zaka tada man hankali!"
Sauke ajiyar zuciya yay ya d'an kalleta idanun shi har sun canza sai kuma ya maida su yana kallon gefe
cikin raunanniyar murya ya fara cewa "...I want to tell u dat Zarah is pregnant and a.....am responsible
for it" daga haka ya dakata wani kallo Hajiya ke bin shi dashi baki bud'e cikin rashin fahimta tace "Fanan
nada ciki shine abun damuwa kai da zaka yi farinciki kiran ka tay ta sanar maka?" Tayi tambayar tana
murmushi ya fahimci bata fahimci sunan da ya fad'i ba gashi ta kafe shi da ido alamar tana jiran amsa
juyawa yay yayi facing d'in ta sosae cike da k'arfin hali yace "I said Zarah Not Fanan" lokaci guda yanayin
fuskarta ya canza ta tsuketa cikin d'aurewar kai tace "Wace zarar?" Jimm yay sosae yake jin fargaba can
dae ya dake yace "Zarah our neighbor I impregnated her yanzu haka tana d'auke da ciki na a jikinta" da
alama mutuwar zaune Hajiya tay baki bud'e take kallon shi shima kallon nata yake sun dan d'auki lokaci
a haka kafin ta kai hannu ta gyara zaman gilashin ta wai taga in shi ne da kyau a rud'e tace "Haisam kana
da hankali kuwa kasan mi kake fad'a kuwa dama ashe ciwon da kake ba wani abu bane shaye shaye ka
koya wurin turawan shine yanzu ka shawo abunda ya fi k'arfin ka kazo kana man zancen hauka to Allah
ubangiji ya tsare mu da irin wannan abun kunyan ka bari muji dana shaye shayen da ka fara, yanzu kai
Haisam duk yadda muke d'aukar ka mai hankali kowa na yaba halin ka nagari shine har ka bari turawa
sukai galaba a kan ka wannan wane irin abun kunya ne ni Hauwa!" tana k'arasawa ta kai hannu ta ruk'e
ha6a tay mashi zugudum tana mashi kallon bak'on mutum ba Haisam ba still yana ta kallon ta yasan
dama bazata fahimta ba cikin sauk'i d'an matsawa yay kusa da ita yace "ni fa ba wani abu da nake sha ko
kuma na sha yafi k'arfi na what am telling u is true Zarah da kika sani tana da ciki 1 month and nawa ne
yanzu taje G.r.a ta sanar mani don nima ban san tana dashi ba...." Nan ya kwashe yadda sukai da Fatuu
data same shi yanzu harda K'in d'aukar wayar shi da tayi da neman ta daya zo da kuma makarantar su da
ya je duk ya fad'a mata, tana ta kallon shi har ya gama mata bayani tay shiru kawae, zuciyarta ta fara
gasgata mata zancen shi Saboda yanayin da ta ga Fatun a d'azun tabbas yanayin ta ya nuna kaman na
mai d'auke da yaron ciki iya girgiza Hajiya ta girgiza cikin tsananin tashin hankali murya na rawa tace "K..
kenan kana nufin raping d'in yar mutane kai???" d'an cije lips d'in shi yay ya d'aga mata kai alamar eh ta
zabga uban salati tana tafa hannuwa ta shiga fad'in ".....Wannan wace irin musiba ce Haisam ya jawo
mana, duk yadda nike Addu'ar Allah ya raba mu da mugun ji da mugun gani ashe kai ne zaka jawo hakan
Haisam, miya faru da kai ne ka aikata ma Yarinyar Mutane wannan d'anyen aikin yarinyar da take tamkar
k'anwa a gare ka, mika sha ne ka aikata mata hakan, ka fad'a man ko don ance matar ka nada matsala
shi ne kai tunanin samun d'a ta wannan hanyar kasan mi ka aikata kuwa???" Sigh yay ya kai hannu ya
dafa goshin shi kafin ya cire yace "I ave told you ba wani abu dana sha fa abunda ya faru wasn't
intentionally kema kin san bazan aikata hakan da wani niyya ba ko don wai Fanan na da matsala nasan
nayi kuskure na biye ma son zuciya wannan dalilin ne ma yasa na kasa natsuwa har na dawo nan ban
wuce Us ba" kallon dae kawai take bin shi dashi tsananin tashin hankali yasa ko kuka ta kasa yi ganin shi
take a matsayin wanda ba daidai yake ba don kuwa da alama ya manta girman laifin da ya akaita da
wadda ya aikata mawa, cigaba yay "Yanzu dae isn't the right time da zamu cigaba da Maganan ya
kamata ai stopping nata daga aikata abunda tace zata yi u know abortion nada matsala and nayi
k'ok'arin in tsaidata but she refused to pick my calls kuma kinsan tunda karatun ta ne zata iya aikatawa
pls do something in ya kama ko gidansu ne muje sai a fad'a ma Grandma d'inta" wannan karon kallon
mahaukaci Hajiya ta koma yi mashi mahaukacin ma mai hauka tuburan don Maganar k'arshe da yayi a
wurinta ta mara hankali ko miskala zarratin ce kaman yasan mi take ayyanawa yasa shi fad'in "nasan
abun nada tashin hankali but bai kai na in aka samu Matsala ba don she may lose her life fa in hakan ya
faru kuma ya tashin hankalin zai kasance so is better a sanar mata ta dakatar da ita and I will take
responsible of everything" bakin Hajiya dai ya gama mutuwa sai ido kawae can ta yunk'ura ta mik'e
shima ya mik'e ta nufi kopar fita daga parlon ganin zata fita haka yasa shi cewa veil d'in ta fa banza tay
mashi tana dogara sandar ta har ta fice daga parlon shima haka...........

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
*ASM Bk2050*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

..........tana fitowa ta nufi hanyar gate shi kuma Haisam ya nufi Motar shi dake a bakin part d'in dama a
bud'e ya barta ya shige yay reverse kafin ya juyata ya nufi hanyar gate d'in a daidai saitin Hajiya ya tsaya
ya sauke glass yace mata ta shigo, banza tay mashi tana cigaba da dogara sandar ta ganin haka yasa shi
bud'e Motar ya fito ya sha gabanta tay mashi wani kallo kafin tace ya jaye ya bata wuri kawae sai ya
kama hannunta ya nufi Motar da ita tana ya k'yaleta amman yak'i sakin ta har saida ya bud'e kopar baya
ta shiga sannan ya koma gaban ya shige tuni Officer ya zuge mashi gate ya fice yabi Motar da kallo a ran
shi yana tunanin ko lafiya, A daidai gaban gidan su ya parker da sauri ya fito ya bud'e ma Hajiya kopar
bayan ta zuro sandar ta kafin ta fito ya maida duka kopopin ya rufe suka nufi gidan tana gaba yana biye
da ita Amadu dake cikin shago yana ganin su ya bud'e ya fito yazo gaban Hajiya ya gaishe da ita ta amsa
mashi kafin ta tambaye shi Dijen na ciki yace eh ta wuce ya k'ara gaishe da Haisam ya jinjina mashi kai
kawae, bin su da ido Amadu yay lokaci guda hankalin shi ya tashi don ya fahimci akwae abunda ke
faruwa tun ma d'azun da Haisam d'in ya zo neman Fatuu Addu'ar Allah yasa dae lafiya yay kafin jiki a
sanyaye ya koma cikin shagon, suna shiga zauren gidan Haisam yaja ya tsaya Hajiya har ta shiga ciki ta
juyo ganin bai shigo ba yasa ta tamke fuska tace "Wato ka d'auke ni mutuniyar banza ko ni ce zan shiga
in sanar da aika aikar da kayi?" Yana kallonta yace "No just to ask for permission first" wata uwar harara
ta zabga mashi tace "kai a tunanin ka yanzu kana da wata kamala ne wanda ya aikata abunda ka aikata ai
bai buk'atar a bashi izinin shiga gidan mutane ba kamar Mutanen da ya za6i zubar ma da Mutunci ka
shigo muje" wani kallo yake mata ya d'an girgiza kai yay mata alamar suje da hannu ta juya lokacin ta
fara yin sallama saida tayi sau biyu sannan gwaggon ta amsa ta lek'o don ganin waye koda ta gansu da
sauri ta k'arasa fitowa tana washe baki jikinta sanye da riga umbrella da zani na atamfa ta d'aura kallabi
nufo su tay tana masu maraba Hajiya dake bin ta da ido ganin yadda take ta washe baki yasa nan da nan
tausayinta ya mamaye zuciyar ta don ta tabbatar da ta san abun da ke tafe da su to tabbas manta yadda
ake dariya ma zata yi balle har tayi, gaida Hajiyar tay ta amsa mata tana kokarin daidaita natsuwar ta ta
kalli Haisam still da fara'a tace "d'ana Haisam barka da juma'a ya k'arfin jikin?" Slowly ya amsa mata da
Alhamdulillah Hajiya ta kya6e baki tana girgiza kai gwaggon tace su shigo cikin parlor, bayan sun shiga a
kan one seater Haisam ya zauna Hajiya ta nufi 3 seater gwaggo kuma ta zauna akan 2 seater ta shiga
k'ara gaida Hajiyar tana mata barka da juma'a ta amsa fuska a kwa6e shi kam Haisam tunda ya zauna ya
sadda kan shi k'asa, shiru duk suka yi gwaggo sai d'an murmushi take sai dae a cikin ranta ta lura kaman
akwae abunda ke faruwa ba kamar Hajiya data gani ba ko mayafi saida aka d'an d'auki lokaci sannan
Hajiya ta sauke nannauyar ajiyar zuciya idonta akan Gwaggo ta fara magana "Dije gamu mun zo saidae
ba irin zuwan da aka saba bane zuwa ne mara dad'i mun zo maki da Al'amari wanda ban tunanin ya ta6a
faruwa a kaf dangin ku...." Dakatawa tay sakamakon kukan da ya taho mata nan fa hankalin gwaggo ya
tashi haik'am ba kamar da ta ga Hajiyar na kuka ga Haisam ya sadda kai baida alamar d'agowa bare tasa
ran jin bayani daga gare shi a rud'e ta hau ba Hajiya hak'ura tana had'ata da Allah ta daina kuka k'arshe
ma sai ta tashi ta koma kusa da ita tasa hannu tana goge mata kwallan tana cigaba da bata hakurin can
ta shanye kukan tace "Dije nasan ki ke mace ce mai tsananin k'arfin hali ba k'aramin abu bane ke ta6a
maki zuciya don Allah ina rok'on ki da ki k'ara kan wanda ke gare ki don Al'amarin da muka zo da shi zai
iya tarwatsa maki zuciya wllh ni kaina da nake maki Maganar nan tuni zuciyar tawa ta tarwatsa Allah ne
kawae ke bani iko nake yin komae" tuni jikin gwaggo ya fara rawa duk ta bi ta rud'e a kidi'me ta hau ce
ma Hajiyar to tana ji in sha Allahu ba abunda zai faru da ita ta sanar mata abunda ke faruwa cigaba
Hajiya tay "Dije kin san duk inda ake zaman lafiya Shaid'an bai da sukuni har sai yaga ya tarwatsa ni dake
zumunci ne mai k'arfi a tsakanin mu tsawon lokaci Saboda dage wa da Addu'oi da su Azkhar yasa tsawon
lokaci bai yi nasara akan mu ba sai yanzu, dije sai yanzu....." Share k'walla taci gaba da yi hankalin
gwaggo in yayi dubu ya gama tashi a lokacin ta rasa ma hasashen da zata yi kan abunda ke faruwa ganin
Hajiyan tak'i fad'a mata abunda ke faruwa yasa ta juya kan Haisam tace "d'ana Haisam don Allah ka
sanar dani abunda ke faruwa in sha Allahu zan fahimta ai ni musulma ce...." Tun kan ta k'arasa Hajiya ta
katse ta da Fad'in "k'yale wannan Dije dashi shaid'an yay amfani yayi galaba yake son ganin ya tarwatsa
mana farinciki zan sanar maki abunda ke faruwa amman ina rok'on ki da girman Allah ki fahimce ni" da
sauri gwaggo ta hau jinjina mata kai alamar zata fahimtan Hajiya tace mata ina Fateema gwaggon tace
mata bata kai ga dawowa ba har yanzu amman dae yau zata dawo Hajiyar tace mata ta kirata a waya
yanzu ta ce mata duk abunda take ta bari ta taho gida da sauri baiwar Allah gwaggo ta mik'e ta nufi
hanyar fita tana Fad'in bari ta d'aukko wayar to, bada jimawa ba ta dawo hannunta ruk'e da wayar ta
fara kiran Fatuu ba tare da ta koma ta zauna ba saidai har ta yanke bata d'aga ba wasa wasa sai da ta
kirata sau kusan goma amman ba'a d'aga ba Hajiya dake ta kallonta tace "halan tak'i d'agawa?" Kai
gwaggo ta d'aga mata ta girgiza kai tace "dole ta k'i d'agawa don itama tana cikin tashin hankali" a
razane gwaggo dake kallon ta tace "kodae wani abu ya faru da Fatun ne ko tayi had'ari ne, don Allah
Hajiya ki sanar man!" ganin yadda ta rud'e yasa Hajiyar kwantar da murya ta na kokarin fahimtar da ita
ba abunda take tunani bane ya same ta kawai dae akwai dalilin da ya sa ba lalle ta d'aga kiran ba, ta
nuna mata lalle dole sai Fatun tazo zata ji abunda ke faruwa gwaggon tace to yanzu ya za'ai gashi ta k'i ta
d'aga kiran, tambayar ta Hajiya tay ko tasan d'akin da Fatun take a can Makarantar tace a'a ta dai san
Hostel d'in amman bata san d'akin su ba tunda bata ta6a zuwa ba Hajiyar ta sake tambayar ta bata san
wata k'awar Fatun ba ta kirata tace ta sani amman bata da lambar wayar ta don duk in zasu gaisa da
wayar Fatun suke gaisawa, shiru kowa yayi gwaggo dai na tsaye k'ik'am can Hajiya tace "ina ga tashi
zamu yi mu tafi Makarantar tasu kawae alabashshi sai mu nemi d'akin nasu in mun je" shiru gwaggo tay
fuskarta duk ta canza an barta a duhu sai faman sak'e sak'e take a ranta can tace ma Hajiyar "ina tunanin
Amadu bai rasa lambar k'awar tata bari in mashi magana" da sauri Hajiya tace to taje taji in akwai ta juya
har tana yin tuntu6e wurin fita daga parlon Hajiya na ta bi a sannu, bayan fitar ta ta maida idonta akan
Haisam da still kan shi na sadde ta hau jefa mashi wani mugun kallo fuska a kwa6e, Saboda tsabar
rud'ewa a yadda take ba lullu6i babu itama ta fita har bakin shagon Amadu yana ganinta ya bud'e ya fito
ya hau tambayar ta lafiya ba kamar yadda yaga yanayin fuskarta murya na rawa tace "ban san abunda ke
faruwa ba Amadu amman dai gaskiya da matsala gashi sun k'i sanar dani abunda ke faruwa wai sai Fatuu
ta zo Hajiya harda kuka fa gashi anata kiranta a waya tak'i d'agawa" zaro ido Amadu yay ba kamar daya ji
tace Hajiya harda kuka yama rasa mi zai ce Gwaggon ce ta tambaye shi ko yana da lambar Fauziyya da
sauri yace "eh akwae Fatuu na kira na da ita" tace to ina wayar ya d'aukko mata ita yace to had'i da
juyawa da sauri ya koma cikin shagon without wasting time ya dawo ruk'e da wayar ya fara kokarin kiran
Fauzy.........,

Tun bayan da ta yi mata allurar ta haye saman gadon ta ta jingina da bango duk ta takure a guri d'aya
har yanzu jikinta rawa yake d'an yi Saboda zullumin abunda zaije ya dawo idanunta akan Fatuu dake
kwance akan gadonta ta rufe ido bacci ne ya kwashe ta tana cikin jiran tsammani bayan da aka mata
allurar, duk in tayi motsi sai gaban Fauzy ya fad'i daramm! Tana haka wayarta dake gefe ta fara ringing
da sauri ta kalle ta kafin ta kai hannu ta d'aukko lokacin da tay arba da sunan Uncle Ahmad kamar yadda
tay saving no d'in shi har saida gabanta ya fad'i tabi kiran da kallo har ya kusa yankewa kafin hannu na
rawa tay picking yana jin ta d'aga da sauri ya mik'a ma gwaggo wayar ta karata a kunne ta rafka sallama
wani irin rassss Fauzy taji murya na rawa ta gaishe da ita ko amsawa gwaggo bata yi ba ta jefa mata
tambayar suna tare da Fatuu ne da sauri tace mata eh gata nan kwance tana bacci gwaggon tace "wani
abu ya samu wayarta ne inata kira bata d'aga ba kema kuma baki d'aga mata ba?" A rud'e Fauzy tace
"a....a'a banji kiran ba k'ilan ko wayar bata a tare da ita don ban ganta ba tun d'azun"

"To ki tasheta ki bata wayar taki ina son magana ne da ita" Fauzy ta amsa da to da sauri tana k'ok'arin
sauka daga kan gadonta ta nufi Fatuu ta sunkuya ta kai hannu tana tashin ta a hankali ta bud'e idanunta
da sauri don kada ta fad'i wani abun Fauzy ta kanga mata wayar a kunne tace "gwaggo ce ke son magana
da ke kiyi magana" waro ido Fatuu tay saida ta had'iya miyau Kutt kafin tayi sallama gwaggon bata amsa
mata sallamar ba tace "ina kika jefa wayar ki ne anata kira tana shiga amman ba'a d'agawa?" Kikkafta ido
ta fara yi a d'an razane jin yanayin voice d'in gwaggon tace mata wayar na a silent ne shiyasa ita kuma
bacci ya d'auketa cike da bada umarni tace "to duk abunda kike yi ki bari yanzu yanzun nan ki taho gida
ina jiran ki" zaro ido Fatuu tay sosae gabanta ya hau fad'uwa cikin inda inda tace "s..sai anjima da
daddare zan taho gwaggo zamu yi wani group......" Bata samu damar k'arasawa ba sakamakon tsawar da
gwaggon tayi mata tace yanzu take son ta taho ba sai anjima ba da sauri Fatun tace mata to gata nan
tahowa daga haka ta kashe kiran, kallon Fauzy Fatuu tay idanu waje itama kallon nata take a d'an
kid'ime ta tambaye ta abunda ke faruwa Fatun ta yarfa hannu tace "nima ban sani ba tace dai komi nake
yi in bari in tafi gida yanzu gashi a muryar ta kaman akwae alamun tashin hankali" wani kuka cikin Fauzy
yay tace "to kodae tasan da Maganar cikin ne?" tay Maganar hannunta guda ruk'e da ha6arta Fatuu
dake kallonta tace "taya za'ai ta sani baccin daga ni sai ke muka sani...." da sauri Fauzy tace "sai kuma Ya
Haisam ba" wani kallo Fatun tay mata tace "kina nufin shi zaije ya gaya mata?" Fauzy tace "Eh mana
shiyasa nace da kin d'auki kiran shi kin ji mi zai ce maki yana iya yin tunanin kar kije ki samu matsala
wurin yin abortion d'in ya yanke gwara yaje ya gaya ma gwaggon" wani kallon anya kina da hankali Fatun
ke bin Fauzy dashi tace "Saboda tsabar baida hankali ya aikata man hakan sannan yaje ya fad'i mata
haba da Allah kema Fauzy ai baya ma fara ba wllh k'ilan dae akwae abunda ya faru kawae ba wannan
ba" uhmm kawai Fauzyn tace,

"Ni tsoro na ma kada sai ina gidan cikin ya zube tunda har yanzu shiru, koda yake tunda ba wani babba
bane nasan ba wani jini zan zubda ba in sha Allahu in ma ta fuskanci wani abu sai in ce mata period d'ina
ne ya zo yau" tana k'arasawa tay d'an murmushin jin dad'in samun mafita ta mik'e Fauzy dae nata bin ta
da ido gaba d'aya a tsorace take, bayan ta had'a duk abunda zata d'auka a jakar goyonta ta yafa mayafin
jallabiyar jikinta tace ma Fauzy ta tafi jiki a mace tace bari ta rakata ta hau Napep, bayan sun fito daga
Hostel d'in sun nufi gate Fatuu ke tambayar ta sai yaushe zata tafi weekend d'in Fauzyn tace sai d'an
anjima bayan Magrib in ta gama kimtsawa, bayan sun fito suka samu Keke Napep Fatun ta shige Fauzy
tace mata duk abunda ake ciki don Allah ta kirata don a tsorace take wllh Fatun tace ta kwantar da
hankalin ta in sha Allahu ba game da wannan abun bane ta d'aga mata kai kawae suka tafi Fauzy ta juyo
sukuku da ita ta koma Hostel,

lokacin da suka iso layin gidan nasu tun kafin su tsaya a kopar gidan ta hango Motar Haisam dake fake
wani irin bugu k'irjinta ya shiga yi har Mai Napep d'in ya tsaya a gaban Motar ta fito da tsananin mamaki
take kallon Motar, bayan ta biya shi ta juya suka had'a ido da Kawu Amadu dake kallonta ta cikin shago
nan da nan ta sha jinin jikinta da k'yar ta d'aga k'afarta ta nufi wurin shi ta tsaya a gaban Shagon ta
gaishe da shi duk ta kame kanta ya amsa yanata kallonta don shi kan shi ya lura da canzawar da tayi
kafin yace mata ta shiga gwaggo na jiranta, a kid'ime ta tambaye shi Ya Haisam na ciki ne yace mata eh
tay jimm kaman bazata wuce ba har saida yay mata magana sannan ta nufi hanyar shiga gidan k'irjin ta
tamkar ana mata luguden ta6are kanta ya gama d'aurewa ta tabbata dae Ya Haisam d'in zuwa yay gidan
su ya fad'a, tunanin abunda yazo yace ta shiga yi ba kamar yadda taji gwaggon na mata Magana da ta
kira waya "ba dai kaina aka d'aura laifin ba!!!" ta raya a cikin zuciyar ta, lokacin data shiga zauren gidan
d'an jimm tay kaman bazata shiga ba can dae ta shiga cike da fargaba ta nufi Parlor ganin takalman su
anan tana zuwa bakin kopar parlon taja ta tsaya ido waje ganin Hajiya a zaune ita bata ma ganta ba saida
gwaggo tace mata ta shigo ciki sannan Hajiyar ta juya ta kalleta, a d'arare ta shiga ta k'ara togewa a
bakin kopar tana ta zare ido wani irin kallo gwaggo ke bin ta da shi Lokaci guda jikinta yay lakwas don ko
ba'a fad'a mata ba ta gane mike faruwa da Fatun Hajiya ce ta nuna mata gefenta tace tazo ta zauna ta
nufi wurin jikinta tamkar ana zare mata lakka, bayan ta zauna murya na rawa ta gaishe da ita kafin ta
d'an saci kallon Haisam da idanun shi ke akan Carpet itama ta sunkuyar da kan nata tana kallon yatsun
hannunta dake yin rawa ji take inama ta 6ace bat daga wurin Hajiya ce ta katse shirun da fad'in "Dije ga
Fateema ta zo yanzu zan sanar dake abunda ke faruwa amman kaman yadda na rok'e ki kafin yanzu ina
sake rok'on ki don girman Allah kiyi hakuri kiyi hakuri dije duk da wannan yayi kad'an ya hana zuciyar ki
girgiza amman dai ina rok'on ki kar ki tashi hankalin ki sosae ta yarda zaki cutu don aikin gama ya riga da
ya gama sai ayi tunanin mafita kawae tunda ko an tashi hankalin ba abunda zai canza...." d'agowa
gwaggo tay ta kalli Hajiyar fuska a kwa6e ta jinjina mata kai kawae, d'an jimm Hajiya tay ita kanta bazata
iya tuna ranar da taji fargabar sanar da wani abu irin yau ba gani take kamar zuciyar gwaggo zata iya
bugawa ita kanta Fatuu tuni kwalla sun fara gangaro mata tasa hannu ta rufe bakinta ji take kamar kar a
sanar ma da gwaggon don in dai wani abu ya sameta to bazata ta6a yafe na kan ta da kuma Haisam ba,
sosae kuma tay mamakin k'arfin halin shi da har ya iya zuwa ya sanar da abu irin wannan, jin Hajiyar
tak'i cigaba yasa gwaggo ce mata karta ji komae ta sanar mata kawae ita ai musulma ce ta yarda da
k'addara mai kyau da kuma Maras kyau jin haka yasa Hajiya d'an gyara zama ido cike da k'walla tace
"Dije Fateema dai.....CIKI ne da ita, kuma ba kowa ne yay mata ba sai wannan k'aton kawai d'in da bai
dubi girman zumunci ba bai dubi girman yarda ba ya iya cin Amana har haka ta hanyar biye ma son
zuciya...." Fashewa tay da matsanancin kuka Fatuu ma haka ita kuwa Gwaggo ta sadda kanta ta yadda
bazaka iya gane halin da take ciki ba can Hajiya ta d'ago taci gaba "Don girman Allah dije kiyi hak'uri a
taru a rufa ma juna Asiri tunda abun nan duk na gida ne iya cuta dae nasan an cuceku shiyasa ma ake
baku hakuri......." kallabin ta ta kwanto taci gaba da share hawaye da shi, duk da kasancewar ta tsufa kan
cike yake da gashi wanda rabin shi duk hurhura ce anyi mata kitso all back, duk abun nan sai yanzu
Haisam ya d'ago da kan shi ya kalli Hajiya kafin ya maida idon kan Fatuu da sadda kai tana ta kuka slowly
ya maido kallon kan Gwaggo cikin sa'a ta d'ago da fuskarta suka had'a ido d'an jinjina mata kai yay had'i
da d'an lumshe ido kafin ya mayar da kallon k'asa nan take ta fahimci abunda yake nufi, d'agowa Hajiya
tay ta kalli Fatuu dake ta kuka tace "Fateema ya akai kika biye mashi, ki ka bari ya cutar da ke har haka
keda nike ganin ki mai hankali da wayau baki tunanin ke zaki fi cutuwa ba a matsayin ki na yarinyar
budurwa shi kuwa yayi auren shi!" d'agowa Fatuu tay cikin kuka tace "Wllh Hajiya ba laifi na bane shine
yace zan raka shi dinner d'in abokin shi to da muka je bamu dad'e ba muka bar wurin...to da muka taho
shine nay fushi Saboda bai bari mun dad'e ba shine ya wuce dani G.r.a bayan ya siya abubuwan ci, koda
muka je ni ban so shiga cikin gidan ba hakanan na bi shi.....da muka je wani d'aki nan ma saida na
tambaye shi abunda muka zo yi shine yace wai zan k'arasa abunda bai bar ni nayi ba a wurin dinner d'in
har nike fushi......to bayan mun ci Abinci tare da shi sai aka kira shi a waya shine ya d'aukko laptop ya
fara latsawa da na ga dare yayi sosae nayi mashi magana akan yakamata mu tafi shi...shine yace in bari
zai d'an ida wani aiki ne to nan har nace bari in yi salla bayan na gama na koma kan kujera ina kallo sai
bacci ya fara d'aukata ina haka na farka nace mashi mu tafi dare yayi sosae yace to ya mik'e nima na
mik'e bayan na fita wurin kujeru shima ya tafi ya d'aukko makullin Mota kawae sai aka d'auke da wuta
shi......." Kafin ta k'arasa gwaggo ta daka mata wata irin tsawa tace "DUM HETSI FATUU!!!" a razane
Fatuu ta kalli gwaggon haka ma Hajiya da mamaki take kallon gwaggon jin yadda ta daka mata tsawa
bayan ita aka cutar idanun gwaggon ne suka ciko da kwalla gani take sam ba'a kyauta ma Haisam ba
wannan tonon sililin har ina ya muzanta, cikin harshen fulatanci murya na rawa ta hau yi ma Fatuu
Magana tana rufe baki a wani irin zabure Fatuu ta mik'e tana zare ido baki bud'e idonta akan Haisam da
still kan shi na k'asa, cikin d'aurewar kai Hajiya tace "a'a Dije, a'a, kada muyi haka dake ya za'a cuci
yarinya har haka sannan ki hau daka mata tsawa tamkar itace mai laifi bugunta za'ai kuma a hanata
kuka? to mi Haisam d'in yayi maki da har ya shanye ki haka??" rai 6ace take Maganar ita kuwa gwaggon
maida kan ta tay k'asa ba alamar zata yi magana Hajiya ta maida idonta kan Fatuu da ke tsaye cike da
tashin hankali jikinta sai 6ari yake tace "fad'a man mi tace maki ne Fateema? ba don ma na watsar ba ai
nima ina d'an jin fullancin za'a canza harshe a cuci yarinya" sake tambayar Fatuu tay kan ta fad'a mata
abunda tace mata a d'imauce Fatun tace "C...cewa cewa tay w...wai shi MIJINA NE!" sakin baki Hajiya tay
jin wata magana kamar ta wanda ya sha giya Haisam mijin Fateema ta ina!!! wani kallo Hajiya ke bin
gwaggo dashi cikin d'aurewar kai tace "Dije ko dae kema chemicals d'in da Kike amfani dasu a wurin aiki
suna bugar da ke ne da har yasa kike magana mara kan gado haka?" d'agowa gwaggo tay fuskarta share
share da hawaye ta girgiza kai tace "Hajiya da suna bugar da ni zuwa yanzu ai da ban tunanin za'a same
ni da cikakken hankali....." Da sauri Hajiya ta katse ta tace "ai Maganar da ki kai Dije ta nuna babu
cikakken hankali a tare dake kwata kwata Haisam fa kika ce wai mijin Fateema ne Saboda Allah har ki
tunanin kina da Hankali? A yaushe aka d'aura masu auren da har mu bamu sani ba???" Shiru gwaggo tay
ita kuwa Hajiyar ta kafeta da ido can ta juya ta kalli Haisam da still kan shi na k'asa ganin yadda bai ce
komae bane yasa jikin Hajiyar idasa mutuwa don da alamu da gaske ne kenan tunda gashi bai ce komae
ba cikin daka tsawa tace masu bazasu yi mata bayani ba ta ya akai Haisam ya auri Fateema?? Had'iye
abu gwaggo tay cikin rawar murya tace "tabbas akwae igiyar auren shi ukku akanta hakan ne ma yasa
aka fasa auren ta da wanda aka so aura mata bayan munje can ni da Abbas lokacin da ta gudo, saidae ita
Kanta bata san da hakan ba Saboda wani dalili Abbas ne zai yi maki bayanin komae" da alama Hajiya
mutuwar zaune tay don kuwa idanunta ko kyaftawa basa yi ita kuwa Fatuu jin wannan bayanin na
gwaggo ya k'ara jefa ta cikin matsanancin tashin hankali nan take taji mararta ta fara murd'a mata ta kai
hannu ta dafeta tana nishi da k'arfi, wani abu mai d'umi taji ya fara zubo mata ta k'afafun ta hannu na
rawa ta d'an d'aga jallabiyar nan take idanunta su kai tozali da jinin dake ta zubowa tamkar ana koro shi
a razane ta d'ago ta kai idon ta kan Haisam da shima idon shi ke akan jinin dake zubowar shi kadae ya
lura da abunda ke faruwa wani irin jiri ne ya kwasheta ta kai hannu ta dafe goshi kafin ta tafi gaba d'aya
zata kifa cikin zafin nama ya yunk'ura ya isa gareta ya tarbeta ta fad'a jikin shi..........

Yau akwae yak'i tsakanin team Fatuu da team Haisam🤣 Wllh yan team Haisam kada ku yarda ku bi mashi
hakkin shi gurin duk wanda ya zage shi ko ya muzan tashi da munanan kalamai☹️

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2051*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


.............A razane duk suka mik'e ganin abunda ke faruwa Hajiya ta fara fad'in" gashi nan ai zaku kashe
masu D'iya..." Gwaggo duk ta rud'e hannunta sai rawa yake daukarta Haisam d'in yayi yay hanyar fita
parlon da ita duk suka rufa mashi baya, yana fita ya kira Amadu da k'arfi ya fito daga cikin shagon da
sauri koda yaga abunda ke faruwa da gudu ya nufi Motar ya bud'e mashi baya ya sakata lokacin Hajiya ta
fito ta nufi Motar itama ta shige bayan ta d'aura kan Fatuu akan cinyoyinta sai ga gwaggo itama ta fito
tana kokarin sanya hijab hannunta ruk'e da wata hijabin da sauri Amadu ya tunkare ta cikin tashin
hankali ya fara tambayarta abunda ke faruwa idanu cike da k'walla tace "Maganar da tsawo ka kula da
gidan" daga haka ta nufi Motar Haisam yay mata nuni data shiga gaba tace to ta bud'e kopar ta shiga
shima ya shiga driver seat ya tashi Motar bayan ya juyata suka tafi Amadu na tsaye jikin shi gaba d'aya ya
mutu yabi Motar da kallo har ta 6ace ma ganin shi sannan jiki a mace ya koma shago, tunda suka hau
hanya Hajiya ke sababi tana Fad'in "Wllh idan wani abu ya samu yarinyar nan duk sai nayi k'arar ku
tunda kun d'auki aure abun wasa abu kamar a shirin film ko littafi ace wai Haisam ya auri Fateema ba
tare da sanin mu ba Saboda bamu da amfani ke Dije da nike gani mai hankali amman kika goyi baya...."
Dakatawa tay tayi k'wafa kafin ta maida idonta kan Haisam dake driving tace "ko ba abunda ya faru da
ita sai na bi mata hakkinta hakanan kusa yarinya tay ta yawo da aure a saman kanta ba tare da ta sani ba
kaman baku san darajar shi ba, sannan wllh kukan daka sani shima sai na bi hakki na hakanan kasa ni
kuka share share ko mahaifin ka daya kwanta ciwo bamma shi kuka haka ba don iskan ci kasan yarinyar
matar ka ce shine bazaka sanar dani ba da kazo sanar man da aika aikar da kayi mata ka nuna man
raping d'inta kai kana ganin kuma yadda hankali na ya tashi na d'imauce amman ko a jikin ka Saboda
shegen miskilanci wato in mutu ma kai ko a jikin ka ko bari dae Allah ya tashi Fateema dani kake zancen"
tsit kowa yay gwaggo kanta na k'asa shi kuma idon shi na akan hanya yanata driving bai ko kalleta ba ta
cikin mirror can ya kai hannu cikin aljihun jeans d'in shi ya fiddo wayar shi kokarin kiran Dr Habeeb
wanda ya ta6a duba Fatuu da ya kaita har yasan ta fara period ya shiga yi saidae layin nashi baya shiga
kusan 3 times yana jarabawa but isn't available Abbas ya koma kira ringing biyu ya d'aga tun kafin yace
wani abu Haisam d'in ya riga shi ta hanyar kiran sunan shi Abbas d'in ya amsa yace mashi Don Allah idan
yana da wani phone no d'in Dr Habeeb ya kira shi yaji in yana Hospital gasu nan kan hanya zasu kai Zarah
and is Emergency, hankalin Abbas d'in ne ya tashi ya hau tambayar shi abunda ya faru da ita yace mashi
yana driving ne zasu yi Magana pls ya kira Dr d'in yanzu daga haka ya katse Hajiya ta kya6e baki tace "ai
da sai kayi mashi bayani yarinyar mutane zaku kashe tunda shima da sa hannun shi" still bai tanka ta ba
sai dae ya d'an kalleta ta cikin mirror suka had'a ido ta wurga mashi uwar harara ya maida idon kan
hanya yana cigaba da driving.

YADDA HAISAM YA AURI FATUU,


A Lokacin da Alhaji Lawal yazo wurin Ard'o ya sanar da batun janye Maganar auran Khalid da Fatuu
Saboda yarinyar bata so tana da wanda take so kamar yadda Abbas ya sanar mashi firrr Ard'o yaki
amincewa yace sam baza'a fasa auren ba su Yaya suka harzuk'a suka hau tunzura shi kan baza'a fasan ba
nan Abbas ya shiga nuna masu da gaske ne tana da wanda take so baya K'asar ne shi Aminin sa ne kuma
da ya dawo zai zo a d'aura masu auren, lokacin Alhaji Lawal ya shiga nuna masu illolin dake tattare da
auren dole tunda har bata so to a kyaleta Ard'o fa ya hau sama ya tuma yace muddin yana raye hakan
bazai faru ba wllh dole abi Maganar shi ai ba itace ta farko da aka fara za6a ma miji ba lokacin Alhaji
Lawal ya k'ara nuna mashi ita baza'a had'a ta da yaran nan ba tunda a birni ta taso kuma a birni in
hukuma taji za'a ma yaro auran dole bai so to kuwa d'aukar kwakkwaran mataki suke don har kotu ake
zuwa mutumin k'auye da tsoron hukuma jin haka yasa Ard'o cewa yaji za'a fasan amman saidae a d'aura
mata auren da Wanda take so don tayi girma da yawa ba aure nan fa cikin Abbas ya d'uri ruwa a rud'e ya
shiga yi masu bayanin shi wanda take son baya K'asar ai yaje yin wani aiki ayi hakuri ya dawo amman
Ard'o ya kafe har da cewa ai ko miji bayanan za'a iya d'aura mashi aure kuma tunda shi yace Aminin sa
ne ba sai ya amsar masa ba sosae Abbas ya rud'e suka shiga kallon kallo shida gwaggo Alhaji Lawal yasa
baki yace ayi hak'uri ya dawon kafin nan sai ita yarinyar taci gaba da karatunta aifa zancen suke so shine
abunda Ard'on yace ya kafe kan ba'a isa yayi yadda ake so ba tunda daga yarinyar har uban nata shike
iko dasu, su Yaya aka hau Kumfar baki ana zuga Ard'o don ita bata ma so ya janye da Khalid d'in k'arshe
ma sai Ard'on ya fashe masu da kuka wiwi yana fad'in tunda yake nuna iko da ya'yan gidan ba wanda
suka ta6a watsa mashi k'asa a ido sai iyalan Muhammadu don haka in dae ba'a d'aura da wanda take
son ba to dama k'arya ne kawai so ake a yaudare shi to kuma Wallahi tallahi da kwarankwasa sai an
d'aura da wanda aka za6a mata in ba haka ba a yau d'in nan ba gobe ba saidae Muhammadu ya tattare
iyalin shi su bar mashi gida ya yafe su tunda basu da wani amfani a wurin shi sai saka shi jin kunya yana
rufe baki ya hau yin tari aikuwa kan kace mi fadar ta rikice aka hau fad'in Baffan Fatuu da Gwaggo zasu
kashe Ard'on hankalin gwaggo yayi matuk'ar tashi haka ma Abbas don yasan mutumin k'auye da iya jan
sharri a rud'e ya hau lalla6a su yace a d'an jira zai kira shi ya sanar mashi sai a d'aura masu auren sai
lokacin Ard'on ya d'an sassaukko yace ya bashi kafin gobe Juma'a Yaya ba haka taso ba tamkar zata
fashe nan ta kawo Maganar a ba Khalid d'in Mino Chairman ya nuna itama a barta tay karatun ta k'arshe
tasa aka fiddo masu da akwatunan lefen su, bayan an watse waje Abbas da gwaggo suka nufa suka tsaya
jikin Motar Abbas d'in fuskokin su d'auke da matsananciyar damuwa Abbas yama rasa mi zai ce Gwaggo
ce tay k'arfin halin cewa "d'ana Abbas ai da baka ce zaka yi ma wanda take son magana ba tunda dai
babu dama an tsara hakan ne don asamu mafita kawae" cike da damuwa yace "amman muddin ba'ai
yadda yake son ba saidae fa a d'aura mata waccan mutumin" yar ajiyar zuciya gwaggon ta sauke tace "in
hakan Allah ya k'addaro mu bamu isa mu hana ba kuma koma dae miya faru ai harda laifin ta tun farko
da anyi ma tufkar hanci tun da wuri ai kaga da ba'a ma kawo yanzu ba da lokaci ya riga da ya k'ure ni
dama nasan fasa wannan auren ba abu bane mai sauk'i a wurin wanccan kafaffen tsohon" hannu Abbas
yasa ya dafe fuskar shi yama rasa tunanin da zai yi can ya yanke kiran Haisam don ya sanar dashi halin da
ake ciki Saboda yasan da Maganar zuwan shi garin kallon gwaggo yay yace mata ta shiga ciki in sha
Allahu za'a samu mafita zai yi mata magana cike da damuwa tace mashi kar yace zai takura kan shi don
ba samun mafitar za'ai ba kawae suje a sanar da Ard'on wanda take son yace bai shirya ba sai a d'aura
mata da wanda suke so d'in kawae, girgiza mata kai Abbas yay yace a d'an dai jira ta shiga ciki tace mashi
to kawae ta nufi komawa cikin gidan a ranta tana tunanin taya za'a samu mafita bacin ita Fatun bata da
wani wanda take so da har za'a d'aura masu aure, bayan tafiyar gwaggon ya shiga kiran Haisam saidae
sam wayar tak'i shiga Saboda rashin Network mai kyau k'arshe dole ya yanke komawa Jimeta ya juya ya
bud'e Motar ya shige bayan ya tashe ta ya ja ya tafi, a can cikin gidan bayan gwaggo ta koma sukai zaune
jugum harda Baffan Fatuu cike da damuwa ya tambayi gwaggon dama da wanda Fatun suke son juna, ba
tare data 6oye mashi ba ta sanar mashi babu wani wanda suke soyayya don karatun ta tasa a gaba
kawae shi Abbas yasa a fad'i hakan ne don a samu mafita yanzu kuma ga yadda abu ya kasance Yadikko
dai sai bin su da ido kawae take ita tasan Fatun nada wanda take so to amman shi ba lalle in yana son ta
ba balle aje ga zancen aure bacin ma bai dad'e da yayi aure ba, k'arshe shima Baffan ce ma gwaggon yay
kawae ayi hakuri a k'yale shi ya aura mata wanda yake so sai su bita da Addu'a tace itama tayi ma Abbas
Maganar hakan amman yace a jira shi sai su jira suga abunda Allah zai yi duk suka ce Allah ya za6a
abunda yafi zama Alkhairi.

Cikin mintuna talatin ya isa jimetan bayan ya shiga gari ya samu wani ya tambaye shi ko akwae wani
Hotel mai kyau yace mashi eh yay mashi kwatance, bayan ya isa ya kama d'aki aka bashi makulli ya nufi
d'akin wanda d'an madaidaici ne akwae duk abun buk'ata na cikin bedroom da yake Hotel d'in ba wani
babba bane, toilet ya fara shiga ya watso ruwa daga baya ya fito daga shi sai singlet da d'an short ya aje
kayan daya cire a saman gadon shima ya zauna daga gefe ya kai hannu ya d'aukko wayarshi da ya aje
lokacin da ya shigo ya shiga kiran Haisam saidae duk iya kokarin da yayi layin nashi yak'i shiga har
mik'ewa yay ya d'an zagaye d'akin ko ya samu kiran ya shiga amman da yay dialing sai ya yanke k'arshe
dole ya dawo bakin gadon ya zauna had'i da cillar da wayar asaman gadon ya had'e hannuwan shi ya
d'aura ha6ar shi abun duniya duk ya dame shi yama rasa tunanin da zai yi, maida bayan shi yay saman
gadon ya kwanta yana kallon ceiling sai sak'e sak'e yake a haka bacci yay awon gaba dashi, ba shi ya
farka ba sai bayan Azahar lokacin har angama salla jiki a mace ya mik'e ya nufi toilet saida ya k'ara watsa
ruwa ya d'auro Alwala sannan ya fito ya zura wandon shi ya kabbara salla anan cikin d'akin, bayan ya
gama ya d'aga hannu yana Addu'a aciki ya rok'i Allah daya kawo masu mafita a Al'amarin nan ya za6a
abunda yafi zama Alkhairi, bayan ya gama ya mik'e ya koma kan gadon ya shiga duniyar tunani ga yunwa
ya fara ji can yaji wayar shi ta fara ringing ya juya ya kai hannu ya d'aukko ta yana kallon screen d'in yaga
sunan da ya saka ma Haisam ya bayyana har bai san lokacin da yay murmushin farinciki ba duk da baida
tabbacin za'a samu mafita a wurin shi, bayan ya d'aga suka gaisa yace mashi tun d'azun yake trying kiran
shi amman yak'i shiga Haisam d'in ya tambaye shi yadda suka k'are da Mutanen cike da damuwa Abbas
yace "Wllh H,Zakee bamuyi nasara ba k'arshe ma abun nema yay ya zama wani issue na daban" cikin
cool voice d'in shi ya tambaye shi abunda ya faru nan Abbas ya kwashe komae ya fad'i mashi tun daga
kan zuwa gidan Alhaji Lawal har zuwa zaman da akai d'azun a fadar Ard'o yace "Wllh kafaffen tsohon
nan ya kafe kan lalle sai dae a d'aura mata auren da wanda nace suna son juna and ni na fad'i hakan
thinking that za'a samu mafita ya amince kamar yadda shi Dad d'in yaron ya amince" shiru Haisam yay
can yayi sigh yace "So what's d way out now?" Yarfa hannu guda Abbas yay kan lap d'in shi yace "ban
sani ba H,Zakee cos am completely confused abunda nasani dae shine muddin ba wanda nace d'in to
tabbas wancan guy d'in zasu aura mata wllh don tsohon ya d'auki zafi da yawa nema ma yay ya suk'e
mana fa yaja aka mana caa wai in ya mutu mune and yace muddin ba'a d'aura mata da wanda aka ce
tana so ba kuma ba'a bari ya aura mata wanda ya batan ba to ya yafe Dad d'inta dole ya bar mashi gida a
yau d'in nan sosae ya shiga tashin hankali abun ba dad'i but he's in serious dilemma har ma da ita Zarah
wllh, ni tsorona ma aje a aura mata shi ba fata ake ba wani abun mara dad'i yazo ya faru tunda ta nuna
bata son shi ta tsane shi so everything can happen" shiru Haisam kaman ba zai ce komae ba saida ya
d'an d'auki lokaci har Abbas d'in na fad'in "H,Zakee are u there?" Yay sigh yace mashi "yeah" Abbas d'in
yaci gaba da fad'in "da akwae wanda take so sai a aura Matan kawae ba wani abu bane karatu ko a
d'akinta ne sai tayi wannan ba wani problem bane har haihuwa in suna so zasu iya dakatar wa har ta
gama karatunta to ni ta fad'a man ba wani wanda take so gaskiya Saboda karatu ta saka a gaba" still
shirun Haisam yay can Abbas yaji yace "I think u should just marry her Abbas" har saida Abbas ya d'an
zaro ido jin Maganar Haisam d'in yay d'an guntun murmushi a ranshi ya ayyana da ace ba wani a zuciyar
ta tabbas da zai yadda ya aureta to amman yanzu ba zai iya auren ta ba gaskiya don yasan zuciyarta na
wurin wani har saida Haisam ya k'ara mashi magana sannan yace "ba wai bazan iya auren ta ba H,Zakee
saidae gaskiya itama ba lalle ta amince ba Saboda akwae shakuwa mai k'arfi tsakanin ta da Feenah
hakan zai jawo babbar matsala azo a kasa samun kwanciyar hankali kuma" shiru Haisam yay yana
nazarin Maganar shi can yaji yace to ko Yayi ma Najeeb magana yasan zai amince tunda yana sonta
dama, yanayin fuskar Abbas d'in ne ya sauya da sauri yace "haba H,Zakee ban tunanin zaka yi wannan
Maganar ba duk don mi ake gudun wannan d'in da za'a aura mata ba Saboda halin shi ba to miye
marabar shi da Najeeb d'in duk abunda yake Najeeb ma nayi k'ilan ma ya take shi" sai lokacin ma shi
Haisam d'in ya tuna da wannan yace "gashi Saleem was already engaged da sai in mashi magana" wani
d'an guntun murmushi Abbas yay jin yadda Haisam d'in keta kawo mutane can yay ajiyar zuciya yace
"H,Zakee kai why not ka aureta kawae dama kaga ance wanda take so bai K'asar kaga kenan kai ka dace
matsayin wanda za'a aura mata" wani d'a murmushin gefen baki yay yama rasa wace amsa zai ba Abbas
d'in har saida ya sake mashi magana kan abunda ya fad'a sannan yace "I thought k'arfi kowa sanin
yaushe nay aure zaka k'ara man Maganar wani auren and Maganar shakuwa da kai itama Fanan d'in ai
sun shak'u" Abbas yace "amman ai hakan ban tunanin zai hana ka aureta matuk'ar kana so ko don ka
taimake ta duba da irin shak'uwar da ke tsakanin ku....." Tun kan ya k'arasa Haisam d'in ya girgiza kai
tamkar yana ganin shi yace "isn't possible Abbas bansan yadda zan kawo wannan issue d'in ba just 3
months da yin aure na so let think of another solution" Abbas yace "H,Zakee Maganar aure fa ba
magana bace mai sauk'i da kawae za'ai tunanin da anyi ma wani magana zai amince kuma yakamata ka
rink'a tuna dalilin son fasa wannan auren nata, ni ina ganin in dae zaka amince ba wani abu bane zaka
iya auranta ba tare da kowa ya sani ba just to help her ya zamana iya mu nan muka sani ko ita ba sai an
sanar da ita ba kaga bayan an d'aura maku auran zaka iya rabuwa da ita ba tare da idda ta hau kanta ba"
Haisam d'in yace "but baka tunanin still sunanta zai canza?" Da sauri Abbas jin kaman ya fara yin nasara
yace "No, ai kaga yanzu su nan dama an sanar dasu wanda take son bai K'asar to in aka d'aura auran
daga baya in tayi nisa a karatun ta sai a sanar masu ka warware auren don ba yanzu zaka dawo ba ita
kuma kar tay ta zama da aure a kanta ba miji" wani kalan murmushi Haisam yay yace "what if suka
maido Maganar auren wanccan din?" Abbas yace "ban tunanin hakan ai ba wai daka raba auren za'a
sanar masu ba sai an samu kaman 2 years haka lokacin kuma nasan yayi auren shi tunda ba yaro bane
kuma nasan ko don ya shirya da Dad d'in shi zai yi sauri yay aure in ma lokacin sun kawo zancen yi mata
wani auren nasan k'ila bata rasa wanda take so then" shiru Haisam yay yana nazarin Maganar Abbas sai
Addu'ar Allah yasa ya amince yake a cikin ranshi don yana da tabbacin ba lalle ya saketa ba in ya aureta
don ya fahimci kamar shima yana son Zarah d'in kawae bai gane bane bayan wani d'an lokaci yace mashi
shikenan in yana ganin hakan za'a samu mafita ba tare da wata matsala ba ayi hakan Abbas ya washe
bakin farin ciki yace in sha Allahu ba wata matsala da za'a samu Haisam d'in yana murmushi yace shi zai
zaman mashi Waliyyi kenan yace eh yana dariya ya tambaye shi nawa za'a bada sadaki Abbas yace ko
nawa yadda yaga yayi mashi yace zai turo mashi 1 million ya bada 500k sadakin sauran 500k d'in ai
abunda yakamata sosae Abbas yay mamaki jin sadakin daidai da na Fanan ya bada hakan ya k'ara
tabbatar mashi da zargin shi na yana son Fatuu kawae ya kasa ganewa ne nan take ya d'auki aniyar sai ya
yi yadda yay auren ya d'ore in sha Allah, suna gama wayar sai ga kud'in ya turo mashi murna a wurin
Abbas har saida ya d'an taka rawa kafin ya d'aga hannu yay ma Allah godiya ya rok'i yasa hakan yazama
Alkhairi, ba 6ata lokaci ya saka kayan shi ya d'auki wayarshi ya fice, ko ta kan ya nemi Abinci bai bi ba ya
hau Motar shi bayan ya fito ya nufi komawa rugar akan hanyar shi zuciyar shi ta raya mashi yakamata
yaje ya sanar ma da Alhaji Lawal don ya zame masu shaida sosae hakan yay mashi ya nufi hanyar zuwa
gidan cikin sa'a ya gane kuma ya same shi yana gida, bayan ya shiga Parlon shi suka gaisa Abbas ya
tambayi ko ya gane shi yana fara'a yace ya gane shi mana ba duka d'azun suka rabu ba shima Abbas
murmushi yake kafin ya sanar dashi yazo rok'on Alfarma ne yace to Allah yasa zai iya nan ya sanar dashi
wanda take son ya amince a d'aura masu auren har ma ya turo da sadaki shine yake son don Allah ya
shige masu gaba, sosae yaji dad'i yace ya taya Fatuu murna anan ya tambaye shi game da Haisam d'in
Abbas ya sanar dashi sunan shi da kuma waye Mahaifin shi sosae Alhaji Lawal yay mamakin jin d'an
Senator Alee Adamu Zakee ne wanda ba 6oyayyen d'an siyasa bane kusan ko ina an san shi ba kamar
daya kasance shine Senator d'in daya fi kowane Senator kud'i a Arewa ba 6ata lokaci yace ya tsaya ayi
sallar la'asar sai su koma rugar tare a shirya yadda za'a d'aura masu auren Abbas yace to nan Yasa aka
kawo mashi Abinci yaci ya k'oshi daga baya yace zai d'an je cikin gari ya dawo yace to, kud'i yaje ya fiddo
ana gama sallar la'asar ya dawo ba 6ata lokaci bayan Chairman ya dawo daga Masallaci suka tafi rugar
Abbas na a Motar shi shima yana a Jeep d'in shi driver na tuk'a shi, lokacin da suka isa Ard'on na a kopar
gida zaune da mutane suka nufi wurin su bayan sun zauna aka shiga gaisawa Ardon yace su shiga cikin
fada Alhaji Lawal yace a'a nan ma lafiya lau tunda dama abunda ke tafe dasu ana son mutane su shaida
nan Abbas yay ma Ard'on bayani game da amincewar da Haisam yay ya fiddo kud'i 500k ya aje a gaban
shi yace ga sadakin ta sannan ya k'ara fiddo 200k yace wannan kuma na su ne su raba inji Angon jama'a
zo kuga idanu baki bud'e kowa ke kallon kud'in Alhaji Lawal dae sai murmushi yake a rud'e Ardo ya hau
tambayar wai waye wanda zai aure tan ko dai d'an yankan kai ne wannan iyayen kud'i a sadaki Alhaji
Lawal ne yay masu bayanin ko wanene Angon Ardo daya gama rud'ewa harda cewa da tana da saurayi
irin wannan tuntuni bata kawo shi an d'aura masu aure ba, Kamalu da Amadu da tunda suka ga isowarsu
suka taso suka zo gefe don jin abunda zasu tattauna ai suna jin zancen Haisam ne za'a d'aura dashi suka
nufi cikin gida da hanzari har rige rigen shiga d'akin suke lokacin su gwaggo duk suna a parlon tun bayan
da suka gama sallar la'asar har saida su gwaggon suka tsorata ganin yadda suka fad'o masu Amadu na
washe baki ya hau yi mata bayanin abunda ke faruwa a waje cikin d'aurewar kai ta maimaita sunan
Haisam matsayin wanda za'a d'aura aure dashi yace mata eh wllh har sadaki ma an kawo Naira 500k
zaro ido gwaggo tay tama kasa cewa komae Yadikko ko bata san lokacin data fara sakin murmushi ba
Kamalu ne ya juya da sauri ya nufi d'akin baffan su ya sanar mashi lokacin yana kwance ya kasa fita
Saboda damuwa ai yana jin zancen ya mik'e ba shiri ya nufi wajen anan aka shirya d'aura auren gobe
Juma'a a Masallacin Juma'a dake Jimeta bayan gama Sallar juma'a Lokacin da Alhaji Lawal zai tafi har
kud'i Abbas ya basu don su sha mai amman yak'i amsa yace da Haisam da Fatuu duk ya'yan shi ne
k'arshe saidae yay ma driver d'in shi Alheri suka tafi kan sai goben, sam gwaggo ta rasa farin ciki zatai
komi gaba d'aya kanta ya gama d'aurewa ta yadda akai Al'amarin ya kasance haka, sai bayan sallar isha
sannan duk suka hallara a parlon Yadikko harda Abbas cike da damuwa gwaggo tace "d'ana Abbas ya
akai hakan ta faru Saboda mi zaku takura kan ku har haka shi Haisam bai ganin bai dad'e da yin aure ba
zai k'ara wani wanda nasan ba don yana so bane kawae k'arfin hali ne irin nashi shiyasa ya za6i cire mu a
matsala shi kuma ya jefa kan shi a matsalar aure ba ba k'aramin abu bane, gaskiya ni ban goyon bayan
auren nan kwata kwata shima nasan bai yi nazari yadda ya kamata ba kafin ya amince, gaskiya ban
amince ba kawae a k'yaleta ta auri wanda suke so hakan zai fi nima hankali na zai fi kwanciya fiye da ace
Haisam ta aura" ganin yadda duk ta damu yasa Abbas warware mata komae yace shi yana ganin hakan
zai fi kan ta auri wanccan da bata so kuma shima Haisam d'in hakan yayi mashi tunda ba takura shi yay
ba ta bari kawae ayi yadda suka tsaran Allah yasa haka yafi zama Alkhairi" Yadikko itama tace "nima ina
ganin hakan zai fi kawai ai dama Addu'ar abunda yafi zama Alkhairi duk muke tayi to hakan shi yafi
Alkhairin" Baffan Fatuu dae ya rasa ta cewa su Amadu da Kamalu ma duk suka goyi bayan yadda aka
tsaran gwaggo dae tay shiru fuskarta d'auke da damuwa duk da ta ragu sakamakon jin ba auren
dundundun bane nan Abbas yaba gwaggo sauran 300k d'in yace ayi abunda yakamata tace yaba Baffan
dama an bashi sadakin Fatun amman saida Ardo yasa aka bashi wani abu a ciki wai ai sun riga sun gama
mata komae, Yadikko ta zubo ma kowa Abinci bayan an gama ci duk akai sallama kowa ya nufi wurin
kwanciya Amadu har ya fita ya dawo yace ma gwaggo yana son magana da ita ta mik'e ta fito wajen jiki
sukuku acan gefe suka ke6e ganin yadda duk ta damu ya shiga kwantar mata da hankali yace shi yana jin
hakan wata hikima ce ta Ubangiji nan ya kwashe komae game da son da Fatuu kema Haisam d'in har
ciwon da tayi acan baya suka zata na Aljanun ta ne tsananin mamaki ne ya kama gwaggo har saida tasa
hannu ta ruk'e ha6arta baki bud'e ta shiga fad'in yanzu dama duk wannan halin data shiga Saboda
Haisam ne Amadun yace mata tabbas don da bakinta ta fadi mashi ya bata labarin lokacin d'aya isketa
cikin mawuyacin hali tana amai a d'aki har ta sanar mashi hakan tafa hannu gwaggo ta shiga yi tana
salati Amadun yace don haka ta bi su da Addu'a kawae k'ilan Allah ne ya cika mata burinta, a daren ranar
kasa runtsawa gwaggo tay sosae tausayin Fatuu ya mamaye mata zuciya biri yayi kama da Mutum ashe
shiyasa tak'i sake ma Fanan duk da hakan ji take ba yadda za'ai auren ya dore abunda za'ai iya su ba tare
da sanin dangin shi ba ita kanta bazata so Fanan taji zancen auren nan ba Saboda yadda ta d'auke su
gani take hakan zai zama tamkar cin Amana ne, Washe gari Juma'a aka fara shirye shiryen d'aurin aure
tunda safe Abbas da Baffan Fatuu suka tafi kasuwa suka yo siyayyar kayan Abincin da za'ai harda tunkiya
da za'a yanka bayan sun dawo dole gwaggo ta washe suka fara hidiman Abinci da soyen nama bayan
sallar Juma'a Mutane masu yawa suka shaida d'aurin auren Haisam da Fatuu sosae Alhaji Lawal yay
kokari don kuwa shi ya kawo take aways na abinciccikan da aka raba ma Mutane, bayan sun koma gida
aka ci gaba da hidiman biki saidae yawanci yaran gidan ba kowa ne yasan da Maganar auren ba sun dae
ga anyi Abinci ga nama kuma an soya Yaya ranar wuni tay a d'aki tana ciwon bakin ciki tun bayan da taji
da wanda aka d'aura ma Fatuu aure to ai dama ita Hassada ga mai rabo taki ce, Washe gari ana gama
sallar Asuba suka kamo hanya harda su Yadikko aka taho Katsina..........
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2052*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

............. Lokacin da suka iso Katsina wannan dalilin ne yasa lokacin da Fatuu ta tambayi Abbas da gaske
an fasa auranta yace mata eh amman an d'aura da shi haka da zata bi su Mino lokacin da Abbas yazo kai
su suga gari ta saka fitted gown Yadikko tay magana kan rashin dacewar ta fita da rigar da d'an k'aramin
gyale har gwaggo ta saka baki k'arshe dai saidae ta canza kaya haka lokacin da Haisam ya kirata vedio
call da tace fushi take dashi har bacci ya kwashe ta ya kai hannu yana zagaye lips d'in ta saman screen
lokacin duk matar shi ce ita, bayan an samu natsuwa su Yadikko sun koma aka fara shirin cigaba da
karatun Fatuu lokacin gwaggo ta nemi Abbas yazo suka zauna a parlor bayan sun gaisa ne ta fad'i mashi
dalilin kiran nashi dama kan Maganar sakin Fatuu ne don suna shirin cigaba da karatun ta kuma ga aure
akan ta shiyasa take so ya tuntu6i Haisam da Maganar dama sadakin shi na nan a wurin Baffan ta za'a
maido mashi amman sai yace shi yana ganin ba sai an yi mashi magana ba tunda ai yasan da auren shi a
Kanta kuma dole zata cigaba da karatu don haka a k'yale shi taci gaba kawae cike da damuwa gwaggo
tace "amman baka ganin akwae had'ari ace ta tafi wani gari karatu da auren da bata san dashi ba a kanta
ni ina ganin d'ana Abbas gara ai mashi Magana ya saki kaman yadda aka tsaran" Abbas d'in ya nuna
mata shi fatan da yake dama auren ya d'ore ba wai su rabu ba gwaggo ta hau girgiza kai tace "gaskiya ni
bana son hakan duk da zan yi matuk'ar farin ciki in ta samu miji kamar shi to amman ana barin halak ai
ko don kunya yanzu in matar shi tasan da Maganar auren da wane ido zan kalleta ita kanta zata ga an ci
Amanar ta ba kamar yadda ta d'auke ni tamkar itama ni kakarta ce" cikin kwantar da murya Abbas yace
"gwaggon mu wannan duk ba abun damuwa bane in dae Allah ya kaddaro dama zasu kasance miji da
mata ai mu bamu isa mu hana ba kuma duk abunda zamu yi yanzu wllh bamu isa mu raba ba don haka
mu bar ma Allah komae shi zai shige mana gaba kiga komae yazo da sauk'i" ba don taso ba tace mashi
shikenan amman dae gaskiya bai kamata ta tafi wani gari karatu da aure a kanta ba shine ya kawo mata
shawarar Fatuu ta fara yin School of Nursing tunda an kusa fara yin Medicine anan ko bayan ta gama ne
sai tayi k'arshe gwaggon ta amince ta kuma rok'e shi kan ya taimaka mata wurin kula da Fatun yace in
sha Allahu, tun daga wannan lokacin duk abu in ya shafi Fatuu sai gwaggo ta tuntu6i Abbas ko lokacin da
zasu bikin Haulat Nijar sai da tay mashi magana shi kuma ya kira Haisam don neman izini lokacin yace
mashi duk inda zasu suje ba sai an rink'a tambayar shi ba ya bada izini haka lokacin da taso zama a
Hostel farko gwaggo tak'i amincewa tace saidae in ya kama ko zasu yi wani abun kaman yadda ta fad'a
mata daga baya ta tuntu6i Abbas da Maganar yay ma Haisam Maganar shi da kan shi yace abarta in dae
tana so ta zauna shiyasa gwaggon ta k'yaleta take zama saidae duk da haka tana saka ido sosae a kanta
kaman wurin sa kaya da kuma tabbatar da tana a Makarantar duk da ta yarda da ita sosae.

***** ****** *****

Suna isa Abincin Haisam ya hango Dr Habeeb a bakin main Entrance gefen shi nurses ne guda biyu suna
ruk'e da gadon d'aukar mara lafiya ya nufi inda suke ya parker a gefe ko kashe Motar bai yi ba ya fito
lokacin itama Hajiya ta bud'e kopar bayan ta fara K'ok'arin fitowa, d'ayan side d'in Haisam ya nufa yaima
nurses d'in alamar su zo suka turo gadon zuwa inda yake bayan ya bud'e kopar ya duk'a ciki ya cicci6o
Fatuu da take a kwance ba numfashi ya juya ya d'aurata akan gadon Dr Habeeb ne ya basu umarnin su
nufi Amenity da ita ya juyo kan Haisam da Fuskar shi ta bayyana tashin hankali hakan yasa ko gaisawa
basu yi ba ya tambaye shi abunda ke faruwa nan yay mashi bayanin cikin da ke gareta da kuma yadda ta
fara zubda jini sakamakon razana da tayi saidae ya nuna mashi akwae yuwuwar tayi wani abu dama don
ta zubar da cikin da sauri yace mashi su je suka nufi ciki gwaggo da Hajiya ma suka rufa masu baya,
lokacin da suka isa har an shigar da ita d'aki an kwantar da ita Dr yaba d'aya daga cikin Nurses d'in
umarnin abubuwan da zata kawo mashi da sauri ta amsa ta juya da d'an gudu gudu ya kalli Haisam yace
su jira ya shige d'akin dama d'ayar Nurse din na ciki bada jimawa ba wadda ya aika ta dawo ta shige had'i
da maida kopar ta rufe, tsaye duk sukae kowa ya jingina da bango ga seats nan na zaman jira amman
duk sun kasa zaunawa Saboda fargaba da ta cika kowannan su Hajiya sai k'wafa take tana kai hannu tana
ruk'e ha6arta da bakin ta gwaggo dae tayi jugum sai ido kawae ita kadae tasan halin da take ciki sai
Addu'oi take a zuciyarta Haisam kuma ya d'age face d'in shi sama yana kallon ceiling yayin da hannuwan
shi ke zube a cikin Aljihunan jeans d'in shi, sai bayan kusan 15 minutes Dr ya bud'e kopar ya fito da sauri
Hajiya tace "Dr ya ya?" d'an murmushi yay yace mata lafiya lou in sha Allah ya juya kan Haisam da ya
sauke face d'in shi yana kallon shi yace mashi bari ya gan shi a Office aikuwa a harzuk'e Hajiya tace "Dr
kamar ya ka gan shi a Office baka ga yadda duk muka damu bane har ma mun fi shi shiga damuwa duk
abunda zaka fad'a mashi ai mu ya cancanta ka fad'a mawa ba shi da yayi silar jefata a halin da take ciki
ba saboda son zuciya har da ma wannan" ta kai Maganar tana nuna gwaggo da sandar hannunta sadda
kai k'asa gwaggo tay ita kanta ta k'osa taji halin da Fatun ke ciki ganin yayi shiru yasa Hajiya cewa suna
jin shi a wane hali take ciki ne gyara tsayuwar shi yay yace "ta razana sosae ne shiyasa tay doguwar suma
hakan kuma ya haddasa mata bleeding d'in da take don cikin dake jikinta ya fita amman akwae yuwuwar
dama anyi kokarin zubar dashi don bleeding d'in yayi yawa ace iya razanar tasata zubar da jini haka
sosae amman mun samu jinin ya rage ita kuma har yanzu bata farfado ba amman dae ba wani abu zata
farfado in sha Allah yanzu tana buk'atar Oxygen don level d'in nata yayi k'asa sosae sannan already an
samata drip yanzu tana buk'atar jini kusan leda biyu...." Tun kan ya rufe baki Hajiya ta shiga nuna mashi
Haisam da sandar hannunta tace "gashi nan ja shi ku tafi a de6i nashi in ma fiye da leda biyu ake so duk
shi zai bada su" Dr dake d'an murmushi yace "ai Hajiya sai in yayi daidai...." Katse shi tay da fad'in "ko ma
bai yi daidai ba ku d'iba sai kuyi ma canza ku bata wanda yay daidai da nata, amman in fad'a maka
gaskiya bai dad'e daya tashi daga jinya ba don haka ku binciki jinin in ba wata cuta kar aje a d'irka mata
wani abun ya faru a lik'a man sharri nima a saka ni cikin wad'anda suka cuceta" d'an ta6e baki Haisam
yay yayi ma Dr alamar suje da hannu yana murmushi suka tafi nurse dake ruk'e da jinin Fatuu da aka
d'iba tabi bayansu suka nufi Lab, bayan sun je aka d'ibi jinin Haisam d'in duk aka gwada aka ga zai iya
bata kuma cikin sa'a bai da ko malaria har Dr Habeeb na cewa da yake ba anan yake zaune ba shiyasa bai
da yar Malariar zamani shidae d'an murmushi kawae yay sai kuma yace mashi a ka'ida leda guda
yakamata ya bata Haisam d'in yace in dae za'a iya samun leda biyun a d'iba kawae Dr yace shikenan aka
fara shirin d'ibar jinin baida yadda zai yi duk irin kyankyamin shi haka ya kwanta akan gadon, ana gama
d'ibar leda guda wata irin juwa ta taso mashi har ya kasa jurewa saida ya kai hannu ya dafe forehead d'in
shi Dr Habeeb na ganin hakan ya tambaye shi halan bai ci Abinci ba sai lokacin ya tuna da baici Abincin
rana ba an dae siyo mashi bai kaiga ci ba Fatuu taje mashi da zancen cikin da ke gare ta, kai ya d'aga
mashi alamar eh Dr d'in yace yana zuwa ya fita bai d'au lokaci ba ya dawo ya kawo mashi Maltina da
cake yace bari aje a fara saka mata wanda aka d'iba ya d'aga mashi kai, Bayan an tafi a d'ibi jinin Haisam
d'in Hajiya da gwaggo suka shiga cikin d'akin gwaggo ta tsaya daga gefen gadon idonta akan Fatuu dake
kwance ido a rufe kanta ba kallabi gashinta ya tarwatse, a gefen gadon Hajiya ta zauna fuskarta cike da
tausayi ta kai hannu ta shafa fuskar Fatun tana Fad'in "Baiwar Allah Fateema hakanan an d'auki alhakin
ki ana neman asa ki rasa rayuwarki gashi ansa kin aikata babban laifi in ke kika zubar da cikin koda yake
su Allah zai kama da laifi ba ke ba...." Haka tay ta surutai gwaggo dae tay shiru, Dr na fitowa ya nufi
Amenity anan suka had'e da Abbas daya shigo ya nufe shi bayan sun gaisa fuskar shi d'auke da damuwa
ya tambayi Dr d'in abunda ke faruwa don yaga Motar Haisam a waje alamar suna Asibitin nan ya kwashe
komae ya fad'i mashi da tsananin mamaki Abbas ya maimaita Zarah ta samu ciki, jin yadda cikin ya zube
ne yasa bai nuna farinciki ba tare da Dr suka nufi Amenity d'in, bayan sun shiga d'akin wata uwar harara
Hajiya tabi shi da ita nan take yasha jinin jikin shi ya gaishe da gwaggo da ke zaune kan yar doguwar
kujerar da take cikin d'akin da d'an murmushi ta amsa yace ya mai jiki kafin ta bashi amsa Hajiya ta
amshe da fad'in "Mai jiki da kuka jefe halin da take ciki? to ai gata kana gani don haka sai ka ba kan ka
amsa ba sai ka tambayi wani ba" hannu ya kai ya d'an sosa k'eyar shi ya gaishe da ita tay banza da shi ta
kya6e baki Dr Habeeb ya wuce ya fara kokarin sama Fatuu jinin bayan ya gama zai fita Abbas na niyyar
bin bayan shi Hajiya tace ya tsaya zatai magana dashi yace to, bayan fitar Dr tana mashi wani mugun
kallo tace "Yanzu Abbas abunda ku kai kun kyauta, domin Allah kun kyauta ma Fateema dubi halin da
kuka jefa yar mutane kiri kiri kusa yarinya tay ta yawo da aure a kanta ba tare data sani ba taya zaku
aikata wannan d'anyen aiki haka??" d'an rankwafar da kai yay yace "Wllh hajjaju gaba d'aya hakan ya
faru ne Saboda samun mafita gudun jefa rayuwar ta a matsala......" Nan ya kwashe yadda komai ya faru
ya sanar da ita cikin fushi tace "to ai gashi nan matsalar da kuke gudan mata ku kun jefata a wata shi
kuma in bada niyyar rabuwa da ita ya aure taba ai sai ya fito ya bayyana ma Mutane duk abunda zai faru
ya faru yafi da ya kama baki yay shiru shi ga miskili sannan kuma yay kwance kwance ya d'irka ma yar
mutane ciki ba kunya ba tsoron Allah banda fyaden da yay mata, iya cuta dae wllh an cuci Fateema kuma
harda ku a cutar da ita don haka ku zauna da shirin in dae wani abu ya sameta ba fata nike ba sai an bi
mata hakkinta, a ina aka ce don yarinya matar ka ce ka afka mata hakan ai bashi da maraba da fyad'e"
kan Abbas na sadde k'asa haka ma gwaggo jin tayi shiru yasa ya d'an d'ago don duk kunya ta rufe shi ya
shiga bata hak'uri yana fadin sun yi kuskure ta ta6e baki tace su dae suka sani ita dae ai yanzu jiran
Fateema take sumi sumi ya juya ya nufi hanyar fita bayan ya fito ya nufi Lab duk ran shi ba dad'i, sosae
baiji dad'in yadda Al'amarin ya kasance ba kamar cikin da ya zube, lokacin da ya isa d'akin da Haisam
yake a lab yana shiga suka had'a ido dashi ya jingina da bango hannun shi ruk'e da abubuwan da Dr ya
kawo mashi yana ci a hankali Abbas ya shiga da yar sallama can k'asan mak'oshi ya amsa mashi ya nufi
inda yake ya zauna daga bakin gadon yana kallon shi da yar damuwa yace mashi sannu kai kawai Haisam
d'in ya d'aga mashi suka d'an yi shiru idon Abbas akan shi shi kuma ya maida nashi k'asa can Abbas yace
"ashe haka abu ya faru ba dad'i yanzu Hajiya ta tutsiye ni tana ta fad'a" ido kawae Haisam ya bi shi dashi
Abbas dake kallon shi yace "to wai ya akai hakan ta faru ba tare da ka warware mata komae ba, nasan da
kayi mata bayani duk hakan bazata faru ba" still idon ya bishi dashi ba alamar zai tanka mashi wata yar
dariya Abbas yay yace "look dude ba fa wata fuska da zaka man bayan ka aikata 6arna ka cuci yar
mutane kaja har muma ta shafe mu" shigar da lip d'in shi na k'asa yay ya d'an ciza suka bi juna da ido
Abbas nata sakin murmushin iskanci can ido a d'an lumshe slowly yace "What do u want me to say
Abbas? It was intentionally or what?" Abbas dake murmushi yace "kusan hakan mana in ba da niyya ba
mi zai sa ka aikata?" Still idon shi na akan shi ya d'an ta6e baki kafin yace "isn't as u think, it was
mistake" Abbas yace "to ya akai har kai irin wannan kuskuren, ni mamaki na a ina hakan ya faru ko a part
d'in naka" ya k'arasa yana yar dariyar iskanci d'an langa6ar da kai Haisam yay kaman bazai tanka shi ba
ganin haka yasa Abbas gumtse Dariyar yace ya bari don Allah ya fad'a mashi don kan shi ya daure sai da
yay d'an Jim kafin a nutse ya soma bashi labari tun daga barin su wurin dinner d'in Prince da dalilin kaita
G.r.a d'in har zuwa yadda Al'amarin ya fara cike da damuwa bayan yazo nan a bayanin yace "I don't
know what came over me and how everything happen dat way, i completely lost control as if my life
depends on it dat moment...." dakatawa yay ran shi a 6ace Abbas nata girgiza kai had'i da d'an
murmushi Haisam d'in ya cigaba "She said she was pleading me then I dont even heard her" yar Dariya
Abbas yay mai d'an sauti Haisam d'in ya jefa mashi wani kallo mai kaman Harara cikin dariyar yace "Da
alama akwae bambanci kenan?" Ya d'age ma Haisam d'in gira d'an guntun tsoki yay sai kuma yay d'an
murmushin gefe had'i da juyar da kan shi, hannu Abbas ya kai ya dafa k'afar shi guda da ya mik'ar a
saman gadon yace "Wllh H,Zakee ba wani abu bane face rabo Allah ya k'addara a wannan ranar a kuma
daidai wannan lokaci Mom Zarah sai ta samu cikin ka shine kawae kuma Allah ya kaddaro dama can ita
matar ka ce shiyasa wata kil hakan ya faru don asiri ya tonu" shiru bai ce komae ba dae Abbas ya dasa
"amman miyasa daga baya ba kai mata bayani ba har abun ta kasance haka" sigh yay yace "ranar da
hakan ya faru naso in mata hakan but tana cikin mawuyacin hali gashi ta matsa sai ta tafi gida don ni
bamma san lokacin da ta je gate ba saida security yazo ya sanar dani bayan na fita naso mu koma ciki a
lokacin I intend to explain myself but sai tak'i and banso muyi jayayya don dare yayi sosae ga security zai
iya tunani na daban shiyasa nai mata yadda take so sai ma dana fara kaita hospital don tay shedding
blood sosae" d'an bud'a ido Abbas yay fuskar shi tay yanayin tausayi ya hau girgiza kai can yace "to
amman daga baya fa, da kai mata bayani ko kuma ni kayi man magana nayi mata na tabbatar da bata yi
tunanin yin abortion ba in shi d'in tayi" hannu yasa ya d'an shafo forehead d'in shi kafin yace "a ranar
nima kwana nay ban lafiya dama tun da abun ya faru naji ni abnormal daga baya fever mai tsanani ya
rufe ni wurin Asuba sai ga kira daga Mom ta sanar dani halin da Dad ke ciki so I have no option dole in
tafi muna zuwa can nima ciwo ya rufe ni kuma harda abunda nay ma yarinyar ke damuna duk da nasan
mata ta ce amman nasan ban kyauta mata ba hakan ya k'ara worsen condition d'ina bayan na d'an samu
sauk'i na Kirata amman tak'i picking dama ko ranar da abun ya faru na kira bata yi picking ba, a lokacin
da ina can da ta d'auki wayan zan mata bayani ne in ma bata yarda ba zance taje ta tambayi grandma
d'inta so ganin bata d'auka ba I just decided in rabu da ita in na dawo sai in mata bayanin komae" Abbas
dake ta kallon shi jin ya dakata yasa shi cewa "to amman data gane tana da cikin bata sanar da kai
bane?" Yanayin face d'in shi ne ya k'ara canzawa yace "Yau d'in nan nasan da Maganan Abbas, ta same
ni can G.r.a lately anan take sanar man tana ta ciwo a School har an fara rumours d'in ciki ne da ita shine
ya ja hankalinta......" Nan ya kwashe yadda sukai da ita d'azun ya sanar mashi Abbas sai girgiza kai yake
har ya gama sannan cike da damuwa yace "Wllh harda rashin rabo Allah ya k'addaro dama ba za'a haife
shi ba saidae Al'amarin ya bayyana kawae" shima Haisam d'in ran shi a d'an 6ace yace "with her
stubbornness also, if she had listened to me this wouldn't hv happened......" Shiru yay bai k'arasa ba ya
juyar da fuskar shi ganin yanayin shi yasa Abbas cewa "Kayi hak'uri nasan dole kaji ba dad'i kaga tak'i jin
Maganar ka amman na tabbatar in ma zubar da shi d'in tay tayi hakan ne don Saboda ku duka bazata so
sunan ku ya 6aci ba tunda kallon da take ma cikin bana halal bane" shiru bai ce mashi komae ba kafin
Abbas ya k'ara cewa wani abu Dr Habeeb ya shigo ya nufo su da d'an murmushi kallon Haisam yay da
shima ya kalle shi yace ya gama ya d'ibi d'ayan kai ya d'aga mashi Abbas yay saurin tambayar wani jinin
za'a d'iba yace mashi eh cewa yay a d'ibi nashi in zai yi Dr yay yar dariya yace "Malam bari dae a diba
nashi d'in tunda akwae don na tabbatar ko naka yayi sai an samu Malaria a ciki" dariya sukae gaba d'aya
shidae Haisam d'an guntun murmushi kawae yay, bayan an fara d'ibar jinin Dr ke tambayar Abbas wai
mara lafiyan matar H,Zakee ce yace mashi eh ya sake cewa amman yaga kaman ba itace suka je bikinta
ba Abuja yace mashi eh wannan Amaryar shi ce da d'an murmushi yace "ai da yake su manya ne shiyasa
har ya k'ara, itama wanccan din ai Amaryar ce tunda duka yaushe akai bikin" Murmushi kawae Abbas
yayi bayan an gama d'iba saida ya zauna ya huta sosae lokacin Dr ya tafi daga baya suma suka mik'e
Abbas nata mashi sannu saidae ya d'aga kai kawae bayan ya tashi tsaye Abbas ke ce mashi yakamata
yaje yay wanka ya canza kaya don jini ya 6ata mashi gefen hannun shi da gefen rigar shi saima lokacin shi
Haisam d'in ya lura yace suje Office d'in Dr ya wanke hannun zuwa anjima yaje yayi wankan Abbas yace
to yasan in ba don ta kama dole ba ba yadda za'ai Haisam ya zauna da rigar nan, bayan sunje ya wanke
suka nufi d'akin da Fatuu take lokacin da suka shiga jinin da aka saka mata nata shiga jikinta tunda Hajiya
ta kalle su sau d'aya ta kauda kai Gwaggo ce tai mashi sannu ta mik'e tace suzo su zauna har yace tay
zamanta tace zata shiga toilet ne lokacin Magrib ya yi ta nufi toilet d'in su kuma suka zauna yana ta
kallon Fatun can suka had'a ido da Hajiya tana hararar shi ya sunkuyar da kan shi k'asa Abbas dae sai
d'an murmushi yake, fitowa gwaggo tay tana gyara hijab d'in jikinta bayan ta daidaita ta kalli Abbas tace
suje suyi salla kar lokaci ya shige ya amsa mata da to hannun shi ruk'e dana Haisam suka mik'e suka tafi
gwaggo ta kalli Hajiya tana son yi mata magana amman tana jin shakka can dae ta tay k'arfin halin ce
mata an fara kiran salla a fad'ace tace tana ji ai d'an murmushi gwaggo tay ta k'ara ce mata ga Hijab nan
a jikin kujera ta d'aukko mata tace bata so ai batasa ta ta d'aukko mata ba yadda take Maganar ta d'aure
fuska irin tayi fushin nan kwantar da Murya gwaggo tay ta shiga bata hak'uri har saida taga ta d'an saki
Fuska ta fara k'ok'arin mik'ewa sannan gwaggon ta nufi gefe ta kwanto kallabinta ta shimfid'a ta kabbara
salla, suna fita yace ma Abbas ya tsaya nan yay salla shi bari yaje yayi wanka sai ya dawo Abbas d'in yace
to suje tare mana yace No ya tsaya koda za'a buk'aci wani abu sannan yace Ok sukae sallama ya tafi, ana
gama sallar Abbas ya koma d'akin nan gwaggo tasa shi ya kira mata Amadu don ta baro wayarta a gida
har Hajiya ma bata zo da waya ba a gida ta baro ta tun lokacin da Haisam ya sanar mata zancen cikin
Fatuu, bayan ya kira ta fara ringing ya mik'a mata yana d'auka yaji muryar gwaggo ya hau tambayar ta ya
Fatuu ko gaida ita bay ba dama tunda suka tafi hankalin shi ba kwance yake ba k'arshe ma kulle shagon
yay ya koma gida bayan ya shiga kuma hankalin shi ya k'ara tashi haik'am ganin d'igo d'igon jini a tsakar
gidan har zuwa cikin Parlor, saida ya gyara duk inda ya 6aci sannan ya shige d'akin shi ya kwanta cike da
zullumi gashi duk yaga wayoyin su a Parlor balle ya kira yaji halin da ake ciki, jin yanayin muryar tashi
tace mashi ya kwantar da hankalin shi da Sauk'i sosae ana mata k'arin jini ne cike da damuwa yace mata
zasu iya yin Magana tace ai bata kaiga farkawa ba tukun, nan tace mashi ya zubo Abinci a Warmer da
plates ya kawo da ruwa sannan ya d'aukko abun salla da buta da kayanta kala d'aya sai bargo ya tambayi
Asibitin da suke sai lokacin ta tuna da bai sani ba ta fad'a mashi yace to, Haisam na barin Asibitin G.r.a ya
nufa bayan ya shiga Bedroom d'in shi dole wanka ya fara ya zura jallabiya kafin yay sallar Magrib anan
cikin dakin don lokacin ta ya shige, bayan ya sallame zaune yay jigum duk ya rasa mike mashi dad'i daka
kalle shi zaka fahimci yana cikin damuwa don fuskar shi ta nuna, ya d'an d'auki lokaci a haka kafin yay
Addu'a ya mik'e ya nufi cikin Corridor, sanye cikin wasu k'ananan kayan ya fito fess da shi ya d'auki Car
key da wayarshi ya fita, saida ya tsaya yay sayayya mai yawa su lemu da ruwan roba katan katan da uban
fruit harda gasassun kaji da balango mai yawa sannan ya wuce Asibitin, bayan ya isa ya parker Motar ya
fara d'aukar lemu da ruwan ya shiga dasu lokacin Amadu har ya k'araso yana zaune cikin d'akin yay
zugudum sai kallon Fatuu yake Haisam na shigowa ya mik'e da sauri yaje zai amshi abunda ya shigo dashi
yana gaishe shi amsawa yay yace ya bashshi yaje Mota akwae wasu ya d'aukko ya amsa da to da sauri ya
juya ya fita shima ya k'arasa ciki gwaggo na mashi sannu da zuwa cikin cool voice d'in shi ya amsa ya
gaishe da ita kafin ya gaishe da Hajiya dake zaune akan Carpet d'in da Amadu ya kawo gwaggo ta mik'e
ta koma gefen gado tace ya zauna, bayan ya zauna d'akin yay tsit Amadu ya dawo ruk'e da manyan ledoji
ya aje a gefen inda sauran kayan suke ganin yay tsaye Haisam yace yazo ya zauna mana ya nufi gefen shi
ya zauna shiru ta sake biyo baya har aka fara kiran sallar isha lokacin Haisam yace ma gwaggo ga kaya
nan nasu ne tay mashi godiya ya mik'e ya fita Amadu ma ya bi bayan shi, bayan sun gama sallar isha ta
bud'e ledojin ta d'aukko plate ta fara zuba ma Hajiya koda ta mik'a mata cewa tay bata ci da alama dae
ran ta ya 6aci sosae hak'uri ta shiga bata suna haka suka dawo daga Masallaci harda Abbas nan fa ya sa
baki aka cigaba da ba Hajiyar hak'uri sannan tace taji zata ci, k'ara zuba wani tay taba Amadu ya kai ma
su Abbas harda Fruit d'in shima Amadun ta zuba ma shi kowa ya fara ci banda Haisam da tunda aka kai
masu Abbas ya aje a tsakiyar su yay mashi magana sai yace ya fara ci yay zaune shiru idon shi na kallon
floor gwaggo ta lura da bai ci hakan yasa tay mashi magana tana lallashin shi kan yaci kar yunwa tay
mashi illa dama gashi bai warware sosae ba ga kuma jinin shi an d'iba da yawa jin haka yasa Hajiya ta
ta6e baki tace "ai itama wadda ya kwantar bata ci ba waya san ma ko duk yau bata ci komae ba don
haka ki rabu dashi" shiru gwaggo tayi shi kuma ya d'aga ido ya kalleta suka had'a ido tana ta tura baki
yanayin fuskar shi ne ya d'an canza kamar zai yi murmushi amman bai bayyana ba sai daga baya ya fara
ci a hankali don yana jin yunwa sosae kuma d'akin fess yake tamkar ba Asibiti ba ko d'azun gab da
Magrib saida aka shigo akai Mopping tiles d'in kasan da bazai ma ci ba, wurin k'arfe tara Dr Habeeb ya
shigo ya duba ta ya sanar masu da ta farfad'o don numfashin ta ya dawo bacci take yi yanzu ko wane
lokaci zata iya farkawa shi lokacin tashin shi yayi amman akwae Doctor da yazo in da wani abu sai ai
mashi Magana ga Nurse nan zata cigaba da kula da ita sukae mashi godiya Abbas da Haisam suka raka
shi ita kuma Nurse d'in ta gaishe dasu tay masu ya mai jiki duk suka amsa tace zata tafi amman zata
rink'a lek'owa in kuma da wani abu sai ai mata magana tana a Nurses station gwaggo ta amsa da to ta
juya ta tafi, bayan wasu mintuna Haisam ya dawo shi kadae ya tsaya a gefe cikin girmamawa yace ma
gwaggo su je Abbas na waje zai maida su gida tana jin haka tace mashi a'a Don Allah suje su ita zata
tsaya ta kwana tun kan ta rufe baki a harzuk'e Hajiya tace "Yau naga ikon Allah ni Hauwa, shin wai shi
d'in ba mijinta bane kuma shine sanadin kwanciyar ta to waya kamata yay jinyar ta dama bashi ba ko
kuwa ya ja ma yar Mutane wahala sai kuma yaje yay share share akan gado yana bacci to kuwa bai isa ba
shi zai zauna yay jinyar ta duk da kema bai kamata kiyi baccin ba shima Abbas d'in muje ya kaimun dole
ya dawo nan ai jinyar ta dashi" tana gama Magana ta fara k'ok'arin mik'ewa duk gwaggo bata ji dad'i ba
wllh don Haisam d'in na buk'atar isasshen bacci saidae ba yadda ta iya dole tabi Maganar Hajiyan itama
ta mik'e ta d'auki kayan da Amadu ya kawo mata na sawa amman banda su bargon dama Amadu a tsaye
yake sukai mashi sallama yana tsaye ya d'aga masu kai sai da ya raka su bakin k'opa yay tsaye har suka
bar wurin sannan ya koma ciki, bakin gadon ya nufa ya tsaya hannuwan shi zube cikin Aljihun jeans d'in
shi yanata kallonta bazaka iya karantar yanayin fuskar shi ba ya d'an d'auki lokaci a haka kafin yay yar
ajiyar zuciya ya kai hannu ya shafi forehead d'in shi kafin ya juya walking slowly ya koma kan kujera ya
zauna, suna hawa hanya Hajiya ta amshi wayar Amadu ta kira saude bayan ta d'aga ta gaishe da ita tace
mata taga bata ganta a gida ba ko abu ne na gaggawa ya taso shiyasa batai mata ko sallama ba ta fita
Sauden tay Addu'ar Allah ya maido ta lafiya tace ai gata nan ma a kan hanya so take tay sauri ta feraye
dankali tay Faten shi yaji Alaiyahu sai kuma ta d'ibi yan ciki tay d'an ferfesu karta 6ata lokaci don Allah da
sauri ta amsa mata da to ta kashe wayar, su gwaggo aka fara ajewa kopar gida sukai ma Hajiyar saida
safe ta amsa ba yabo babu fallasa aka wuce da ita su kuma jiki a sanyaye suka nufi cikin gida gwaggo
taso taga tashin Fatun, bayan sun isa gidan Hajiyan sawa tay dole Abbas ya tsaya har aka gama Abincin
don ma ba me d'aukar lokaci bane aka zuba a k'ayatattun Warmers Saude ta bi shi dasu har zai fita daga
parlon Hajiya ta tsaida shi tace ma Saude ta je ta daukko mosquito spray bayan ta kawo ta ba Abbas d'in
tace gashi nan a fesa a d'akin kar sauro ya ciji Fateema ya k'ara mata wata cutar banda wadda suka jaza
mata shi dae d'an murmushi kawae yay yasan harda don Haisam ta bada shi yay mata saida safe ya tafi
Saude na biye dashi ruk'e da basket d'in Warmers suka nufi Mota, yana shiga ciki sai ga kiran gwaggo
tace ya wuce ne yace mata a'a yanzu dae zai tafi tace to don Allah ya d'an tsaya zata bashi kayan Fatuu
akai mata in ta farka sai ta canza yace to, lokacin da ya tsaya horn yay Amadu ya fito ruk'e da yar jaka
mai d'auke da kayan Fatuu harda undies da pad bayan ya saka a back seat yay mashi saida safe ya juya
shi kuma yaja Motar ya tafi, lokacin da isa Asibitin k'arfe goma ta wuce bayan ya Parker ya fito ya bud'e
back door ya fiddo basket d'in kayan Abincin da jakar ya rufe ya nufi ciki, Haisam na zaune kan kujeran
ya d'an kishingid'a had'i da lumshe ido Abbas d'in ya shigo da yar sallama ya bud'e idon a hankali ya kalle
shi Abbas d'in ya d'an yi mashi murmushi ya nufi inda yake, a gaban kujeran ya aje kayan hannun shi ya
zauna gefe idon shi akan Haisam yace mashi sannu ya jinjina mashi kai nuna mashi kayan yay yace ga
Abinci nan da kayan matar shi an ce inta tashi ya bata ya kuma taimaka mata tay wanka ta canza kaya
wani kallo yay mashi Abbas d'in yay dariya kafin ya juya ya kalli Fatuu ya d'an girgiza kai ya juyo yace ma
Haisam wai har yanzu bata farka ba ya d'aga mashi kai yace "Allah sarki Mom Zarah wllh na tausaya
mata sosae Allah ya bata lafiya" shiru Haisam d'in yay Abbas yace "bazaka amsa ba ko baka so tay saurin
samun sauk'i ka maida bugu nan da nan asamo mana twins" still banza yay mashi fuska a d'aure Abbas
ya tuntsire da dariya yace "Serious kasan wani rabon na kore wani fa gashi Mom Zarah na fahimci ba ta
wasa bace da an bata take amsa" d'an k'ank'ance ido yay yana kallon shi Abbas d'in sai dariya yake can
slowly yace ya tashi ya tafi gida dare yayi Abbas d'in yace wato ya ishe shi kenan daga yana taya shi hira
ya rage kad'aici yace mashi ya gode bacci yake ji ne Abbas d'in ya fara kokarin mik'ewa yana fad'in ai
shikenan, tare suka fito saida ya raka shi har bakin Mota Abbas ya bud'e ya shige driver seat yay mashi
saida safe ya juya ya koma ciki, yana shiga d'akin ya k'ulle kopar ya nufi kujerar ya zauna idon shi akan
Fatuu can kuma ya kai hannu ya dauki wayar shi ya fara lallatsawa bayan wani lokaci ya ajeta don bacci
yake ji daurewa kawae yake mik'ewa yay ya d'auki bargo ya shimfid'a a saman kujerar kafin ya kwanta
saidae bata d'auke tsawon shi ba gaba d'aya a hankali ya fara lumshe ido yana yi yana bud'ewa har
baccin ya d'auke shi, Misalin k'arfe sha d'aya da yan mintuna ta fara mutsu mutsun farkawa slowly ta
fara bud'e idanuwan ta tana yi tana sake lumshe su a haka har ta bud'e su gaba d'aya akan ceiling d'in
d'akin ta k'ura ma Fanka ido tana kokarin gano a ina take, d'ago hannuwanta tay duka jin su kaman ba
daidai ba nan idonta ya sauka akan kanular dake a jikin kowanne nan take ta gane inda take, sauke su
tay ta fara juya kan ta a hankali tana bin d'akin da kallo har idanunta suka sauka akan Haisam da idanun
shi ke a rufe wani irin bugu kirjinta yay ta k'ura mashi ido lokaci guda abubuwan da suka faru suka fara
dawo mata har zuwa lokacin data san shi Mijinta ne ta shiga tunanin ashe duk abubuwan da yake mata
Saboda wannan dalilin ne ita bata sani ba tay wani tunani na daban a hankali ta saki d'an murmushi tana
cigaba da kallon shi zuciyar ta na raya mata yanzun nan shi Mijinta ne wani irin dad'i take ji a cikin ranta
can kuma ta tuno da Maganganun da ta gaggaya mashi a G.r.a nan take yanayin fuskar ta ya sauya
damuwa ta bayyana tamkar yaji ajikin shi tana kallon shi ya fara motsi yana kokarin bud'e ido sam ta
kasa janye idanunta kirjinta sai bugu yake da sauri da sauri a hankali ya bud'e idanun suka sauka akan ta
ya bita da kallo suka zuba ma juna ido...........

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2053*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


...........kasa jurewa tay a hankali ta maida idonta k'asa shima maida nashi yay ya lumshe bayan wani
lokaci ta d'ago ta sake kallon shi har lokacin bai bud'e idanun nashi ba hakanan sai taji wani iri don kallon
da ta ga yana yi mata ba kalan wanda yake mata bane a kwanakin baya kafin hakan ta faru, maida idon
tay tana kallon gaban ta cikin ran ta tana k'ara tariyo abubuwan da suka faru gaban ta ne ya fad'i tunowa
da jinin data gani nan ta fara kokonton anya cikin bai fita ba kuwa lokaci guda ta yanke ta san ma zai yi
wuya in yana nan, wani iri taji damuwa ta bayyana kan fuskar ta sai kuma ta hau yin tunanin halin da
gwaggo da Hajiya suke ciki tana haka taji fitsari ya matseta ta fara kokarin yunk'urawa ta tashi dama an
riga an cire mata k'arin jinin da aka saka mata na farko a can gefe ta hango gyalenta dama yana jikinta
aka zo da ita Saboda rolling d'in shi tay sai bayan an kawo ta d'akin ya kwance, bayan ta yafa gyalen
saman kanta zuro k'afafun ta tay a hankali ta saukko daga saman gadon wani irin fayau taji ta kwata
kwata ba k'arfi a jikinta ga juwa na niyyar kwasar ta ba shiri ta koma ta zauna tasa tafin hannun ta guda
ta dafe forehead d'inta duk Haisam na kallonta don tunda ta fara k'ok'arin saukkowa ya bud'e ido jin
mutsu mutsun da take, bin ta yay da kallo ba tare da ta sani ba can ya yunk'ura ya tashi tsaye walking
slowly ya nufe ta duk bata sani ba har saida taji k'amshin shi jikin shi ya cika mata hanci sannan ta d'ago
da fuskar ta da d'an sauri idanunta suka sauka a cikin nashi wani irin bugu kirjinta yay ta kafe shi da ido
had'i da d'an motsa baki kamar zata ce wani abu amman ta kasa furta komae Slowly taji cool voice d'in
shi ya furta "Let me Help" ya mik'a mata hannu duk tayi tsuru tsuru kamar mara gaskiya ta kai hannu a
d'arare ta kama santalelen hannun nashi jajir dashi ga taushi kai kace ba hannun babban namiji ba don
kuwa banda yanayin halittar fata shi kan shi hannun yana shan tsadaddun mayukan gyara masu saka
taushi, bayan ta mik'e tsaye zame hannun na shi yay ya zagaya dashi ya tallabo Shoulders d'in ta suka
fara tafiya fuskarta a k'asa gaban ta naci gaba bugawa har suka isa bakin kopar toilet d'in sannan ya
dakata ya zame hannun nashi ta d'an kalle shi sai taji yace "Can u....or I should call Nurse?" d'an girgiza
kai tay a hankali tace zata iya shiru bai ce komae ba ta juyar da fuskarta ta tura ta shige ta maido k'opar,
toilet d'in tsaf kai kace bana asibiti ba duk da ba bathtub amman har heater ta ruwan zafi akwai da
shower, butar data gani wadda gwaggo tasa Amadu ya kawo ta d'auka ta tari ruwan zafi daidai yadda
zafin zai mata, lokacin data tattare rigarta gabanta ne ya fad'i ganin cinyoyinta jage jage da jini bata yi
mamakin rashin ganin pant d'in data sa ba don tasan a ina take zai yuwu an cire shi ne, jiki a mace ta
duk'a ta fara yin fitsarin bayan ta gama tay amfani da ruwan wurin wanke k'asan nata sosae bayan ta
gama ta mik'e tsaye da k'yar, tunanin yakamata tay wanka ta shiga yi don tasan duk jini ne a jikin rigar
don ma tana bak'a saidae bata san kuma ko akwai wasu kayan da zata canza ba, matsawa tay ta jingina
da bango tay shiru sam ta kasa karantar yanayin da ta ga fuskar Haisam don sai take ganin kaman yana
d'aure fuska, tana ta tsaye ta rasa mike mata dad'i gashi bata san ya zata yi ba tana son yin wanka
amman bata san ko akwae kaya ba kuma sai take ta jin fargabar fita tana haka taji an yi knocking kopar
har saida kirjinta ya d'an buga damm da sauri ta kai ido kan kopar k'ara knocking d'in akai ta nufi kopar
cikin rashin k'arfin jiki tasa hannu a hankali ta bud'e tay arba da Fuskar shi, bin shi tay da ido ya mik'o
mata abun hannun shi wanda towel ne da soap dish ta kai hannu ta amsa murya k'asa k'asa tace mashi
ta gode bai ce komai ba ya juya itama ta koma ciki, yana bata kayan waje ya nufa yaje yay ma Nurse
Magana kan azo a gyara mata bed har ya dawo bata fito ba ya zauna kan kujera yana nan aka zo aka
gyara gadon aka canza Bedsheet can ya tuna da Magungunan da Dr Habeeb ya tura pharmacy don yace
akwae yuwuwar ba sai an yi mata wankin ciki ba don yana tunanin komae ya fito sakamakon jinin da ya
zuba sosae zuwa washe gari za'ai mata scanning don a tabbatar mik'ewa yay ya tafi ya amso, bayan ta
gama wankan tsaye tay ta kasa fita da towel d'in jikinta wanda iyakar shi tsakiyar cinyoyin ta, tana ta
tsayuwa gashi jiki ba kwari can dae ta nufi kopar saida tay d'an jimm kafin hannu na rawa ta kama
handle d'in ta bud'e sai dae tana sa kai taga d'akin wayam ba kowa wani sanyi taji ta shiga ta nufi gadon
da taga an gyara mata shi zaunawa tay tana ta yan kalle kalle ta hango jakar kayanta a gaban drawer d'in
gadon ta tashi ta d'aukko ta a gefen gadon ta d'aurata ta bud'e, hannu ta kai tana d'an d'aga kayan kafin
ta fiddo wata doguwar rigar material ta aje gefe ta ciro pant da pad data gani suma ta aje tunanin ko ta
koma toilet tasa kayan ta shiga yi wata zuciyar ta raya mata tunda ita kadae ce ta sa anan mana k'ilan
har ta gama bai shigo ba, yin wannan tunanin yasa da sauri ta bud'e pad d'in ta ciro wadda zatai amfani
da ita tasa a jikin pant d'in bayan ta gama ta saukko daga saman gadon ta zura pant d'in tana kokarin
sanyawa taji an turo kopar aikuwa da sauri ta d'ago ta kalli kopar ba tare da ta ankare ba kuma towel
d'in ya kwance Saboda d'agowar da tayi ba shiri nan take boobs d'in ta suka bayyana duk ta dabarbarce
don kuwa idon shi na akanta ganin haka yasa da sauri ya koma yaja mata kopar, ta d'ago da towel d'in da
sauri had'i da dafe k'irji tana kallon kopar kafin a kasalance ta duk'a taci gaba da sakawa bayan ta gama
ta zura doguwar rigar ta fiddo hula ta saka ta zuge jakar har ta koma ta zauna sai kuma ta mik'e ta d'auki
towel d'in da ledar da ta ciro pad da yan takardun ta nufi toilet da ganin yadda take tafiyar jikinta sam ba
kwari, bayan ta dawo still bai shigo ba ta koma bakin gadon ta zauna tana facing kopar tama rasa
tunanin da zatayi tay zuru sai kikkafta ido take tana haka ya turo kopar da yar sallama ya shigo suka
had'a ido a hankali ta amsa kafin ta maida idonta k'asa da sauri ta fara d'an wasa da yatsun ta, wurin
gadon ya nufa a saman yar drawer d'in gefe ya d'aura ledar drugs d'in ya juyo ya d'an kalle ta kan ta a
k'asa kaman yana son cewa wani abu ji tay a jikinta ita yake kallo ta d'an d'ago a hankali suka had'a ido
taji yace "How are u feeling?" a sanyaye tace "Alhamdulillah da Sauk'i" shiru bai ce komae ba can taji
yace "are u done with this?" jin tambayar yasa ta kai idon ta kan jakar kayan da ke gefen ta kafin ta kalle
shi ta d'aga kai alamar eh ta gama amfani da ita hannu ya kai ya d'auke ta ya maida ita inda take da,
duk'awa yay wurin kayan Abincin ya d'auki plate da spoon sai bottle water ya mik'e ya nufi window d'in
d'akin bayan ya zuge net d'in jiki ya fara d'auraye su Fatuu nata kallon shi har ya gama ya rufe ruwan
tana ganin zai juyo ta maida idonta k'asa ya dawo ya tsugunna gaban basket d'in Warmers masu d'auke
da abincin ya fara bud'ewa, Faten dankalin ya zuba ya saka spoon d'in kafin ya mik'e ya kai mata ta mik'a
hannu ta amsa nan ma saida ta furta mashi ta gode bai ce komae ba ya juya tabi shi da kallo, rufe
warmer d'in yay ya koma kan kujerar ya zauna had'i da jingina bayan shi ya d'an d'age kan shi, gaba
d'aya jikinta ya mutu Saboda canjin da ta gani a tattare da shi da k'yar ta d'auki spoon d'in ta fara ci duk
yadda Abincin yay mata kyau a fuska sam ta kasa jin dad'in shi a baki hakanan dae take ci kad'an kad'an
saida taci kaman rabi sannan ta tashi zata maida wurin kayan Abincin lokacin ya sauke fuskar idanun shi
suka sauka a kan ta wani kallo ya jefa mata ta sadda kanta k'asa cike da bada umarni taji yace mata ta
cinye shi duka d'agowa tay ta kalle shi still kallon dae yake mata jiki a sa6ule ta koma ta zauna don sai
taga kaman ma hararar ta yake, ba yadda ta iya haka ta dingi turawa ba don tana jin dad'in shi ba har ta
samu ta cinye tana niyyar mik'ewa taga ya taso yazo gabanta, amsar plate d'in yay ya maida ya k'ara
d'aukar wani yaje ya wanko shi bayan ya dawo ya zuba mata farfesun yan cikin shima ya mik'a mata ta
amsa yanzu bata ce mashi ta goden ba saidae ta d'an kalle shi, bayan ya juya plate d'in da ta 6ata ya
d'aukka yaje ya wanko shi ya maido, kujerar ya koma ya zauna ya k'ara d'age kan kaman d'azu, sosae
farfesun yay mata dad'i saidae damuwa ta hana taci shi sosae don gani take kaman dai da gaske fushin
yake, bayan ta d'an sha kawai sai ta aje spoon d'in tsam ta mik'e zata aje shima sai gashi ya sake juyowa
ya kalleta nan take tay pause tana kallon shi fuska a yamutse daga inda yake taji yace "Eat it up!" d'an
yamutsa fuska tay cikin rawar murya tace "na k'oshi" shiru bai ce komae ba idon shi akanta itama ta kasa
motsawa balle ta aje can ya mik'e ya nufo ta yazo daga gabanta ya tsaya suna facing juna abu ta rink'a
had'iya ta sak'a d'ayan hannun da bada shi ta ruk'e plate d'in ba gefen wuyanta tana d'an sosa wurin
kasa jure kallon shi tay ta maida idon t k'asa, hannu taga ya mik'o ya amshi plate d'in ta kalle shi da kai
yay mata alamar ta zauna ta koma gefen gadon kawae sai gani tay shima ya zauna a gefenta ya fara
d'ibowa zai bata ta yamutsa fuska idanunta har sun ciko tace mashi ta k'oshi wani kallo ya wurga mata
ba shiri ta bud'e bakin ya zuba mata ta fara taunawa tana kikkafta ido, haka yaci gaba da bata har ta dai
ta saki Fuska taci gaba da ci tana yi tana satar kallon shi wani lokacin su had'a ido sai tay saurin janye
idon ga k'amshin shi da ya gama cikata, saida ta cinye shi duka sannan ya mik'e ya maida plate d'in ya
d'aukko mata ruwa bayan ya bud'e mata ya mik'a mata ta amsa tasha da d'an yawa sannan ta cire robar
daga bakinta ta mik'a mashi ya amsa ya rufe, ledar fruit ya bud'e suma ya zuba a plate d'in ya mik'a mata
k'in amsa tay ya wani d'aure fuska kawae sai ta saka mashi kuka still yay yana kallon ta komi yay mata na
kuka shida ko tanka mata bai yi ba cike da shagwa6a duk da ita ba da niyyar shagwabar take yi ba nature
d'in ta ne haka taci gaba da yamutsa fuska tana d'an ta6e baki kalan yadda take kuka tun yarinta tana ta
faman kikkafta ido kwalla na gangaro mata shi dai kallon ta kawai yake ga abu ta barshi dashi a hannu
sigh yay ya d'age gira yace mata "na buge ki ne?" da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a ya sake cewa
"to wannan d'in na miye?" yay mata nuni da k'wallan dake zubawa da ido shiru tay ta sadda kanta k'asa
har saida yace ba magana yake mata bane sannan ta d'ago tana d'an share kwallan cikin muryar kuka
tace "ba komae" shiru bai ce komae ba sai ya koma gefen ta inda ya tashi ya sake zaunawa ya d'aukko
6ararrar ayaba zai bata tana ta goge kwalla ba tare data kalle shi ba hakan yasa bata san yana mik'o
mata ba saida taji yace "FATUU" damm k'irjinta ya buga a ranta ta maimaita sunan daya kira ta dashi
don tunda yasan sunanta bai ta6a kiran ta da hakan ba sai yau nan take jikinta yay lakwas tamkar an
watsa ma kaza gishiri a sa6ule ta kai idon ta gare shi taga ayabar da yake mik'o mata a hankali ta bud'e
baki ta d'an gutsira ta fara taunawa, haka yaci gaba da bata har saida ta shanye komae ya maida plate
d'in ya d'aukko ledan magungunan daya aje da ruwa ya sake zaunawa suma ya shiga 6aro mata yana
mik'a mata tana sha da ruwan har ta gama dama bata gudun magani allura ce wani lokacin ake fama da
ita shima kafin ta girma haka yanzu saidae in za'a yi mata ta cije baki da runtse ido, bayan ya maida
komae duk plates d'in ya wanko su ya bud'e warmer d'in ya zuba Abincin don shima yunwa yake ji bayan
ya saka spoon ya nufi kujera tana ta bin shi da ido har ya zauna a nutse ya soma ci, Allah sarki true love
sai kawae taji tausayin shi ya kamata ta shiga tunanin k'ilan ma ya dad'e bai ci Abincin ba tunda hakanan
ma tasan ba ci yake sosae ba, tana ta zaune tana kallon duk wani motsi da yake wurin cin Abincin kama
daga kai cokalin ya d'ebo zuwa kai wa bakin shi saida ya d'an d'auki lokaci da farawa tukunna ba tare
data ankare ba taga ya juyo sun had'a ido duk sai ta kame kanta sum sum kaman munafuka ta haye
gadon ta kwanta had'i da juya mashi baya, cigaba da cin Abincin yay har ya gama ya tashi ya d'ebo
farfesun bada yawa ba shima ya sha da ya gama ya je ya wanke abun da 6ata ya d'auki bottle water ya
koma kan kujeran ya bud'e yasha da d'an yawa bayan ya gama ya rufe murfin ya ajeta a gefe ya maida
bayan shi jikin kujerar ya kai idon shi kan Fatuu data duk'unk'une wuri d'aya ya d'an d'auki lokaci yana
kallon ta kafin ya janye idon ya kai hannu ya d'auki wayar shi ya fara latsawa can kuma ya aje ya mik'e
bargon daya shimfid'a ya d'auka ya nufeta yana zuwa bakin gadon ya bud'e shi ya lullu6a mata lokacin
idon ta biyu tay ma bango tsuru taji ya rufa mata, lumshe ido tay yana daga abunda ke k'ara mata
k'aunar Haisam wato sanin yakamata don kuwa kaman yasan sanyi take ji kuma ta rasa yadda zata sanar
mashi, yana gama rufa mata wayar shi ta fara ringing ya nufi inda take bayan ya zauna ya kai hannu ya
daukko sunan daya sa ma Fanan ya bayyana akan Screen yasan su can gari ya waye, picking yay ya kara
ta a kunne tun kafin tace wani abu yace mata "Good Morning" cikin sigar shagwa6a ta amsa mashi ta
tambaye shi ya akai bai yi bacci ba yace mata yayi farkawa yay da bud'ar bakinta sai cewa tay wai ba dae
yana soyayya da wata bane ta waya d'an guntun murmushi yay yace mata ai da taji yana waya ko tace ai
wai ko chat fuska a sake yace mata yana wani aiki ne tace mashi Ok, tambayar shi tay mai jiki yace mata
ya samu sauk'i sosae shima ta tambayi na shi yace ya warke cike da shagwa6a tace "so when are u
coming back, serious am missing my husband ina daurewa ne kawae" d'an murmushin da ta ji sautin shi
yay kawae tace "seems like u'r not missing me babe" sigh yay yace waya fad'i mata tace gashi nan ta
fad'a mashi tayi missing nashi but bai nuna shima yana nata ba, yana murmushi yace ai abunda ta sani
ne dole yayi so ba sai ya fad'a ba, d'an murmushi tay tace tama manta waye mijin nata, tambayarta yay
waye shi tana yar dariya tace wanda magana ke ma wuya d'an Murmushin gefe yay kawae,

"I asked when are coming back baka fad'a man ba" shiru ya d'an yi kafin yace mata ya kusa yanzu yana
Katsina ne da alamun mamaki ta tambayi mi yaje yi Katsina kuma yace ya rako Hajiya ne sai kuma wani
aiki ya rike shi a shagwa6e tace to yanzu har sai yaushe kenan yana murmushi yace "Don't worry I will
come back soon" da sauri tace "not soon babe soonest in ba haka ba zan zo ne nan" yar dariya yay har
hak'oran sa suka d'an bayyana yace mata aikin nata fa tace shima ai yana aikin ko yace ai shi yana da
strong reason Dad d'in shi ke bai lafiya,

"But tun kafin ya fara ciwo ka taho ai" yace ai wannan ya nemi permission ne sai kuma ya k'ara nema
yanzu Saboda ciwon kuma ko daga nan zai iya yin wani aikin tace itama sai ta nema ai tana da babban
dalili tunda wurin mijinta zata zo yace banda wanda aka bata taje Germany tana yar dariya tace zata
k'ara nema ne kaman yadda shima yay, nan yace mata kar ta damu zai dawo bada dad'ewa ba tace Ok,
suna cikin wayan ta tambaye shi Zarah har saida ya d'aga ido ya kallo Fatuu kafin ya bata amsa da tana
lafiya tace ai ta yada ita ko waya ta manta last da sukai itace ma ke mata magana ta WhatsApp wani
lokacin sigh yay yace mata tasan yanayin karatun da take may be bata samun isashshen time ne tace
hakane Allah ya bada sa'a slowly ya amsa da Ameen, tun dae yana wayan a zaune har ta kai ya d'an
kishin gida ya aje wayan a hannun kujera yasa speaker saidae ya rage volume dama baida juriyar ya kafa
waya a kunne yay tayi, duk wannan abun idon Fatuu biyu ta ji tun lokacin da ya fara yin wayan saidae
kwata kwata bata jin mi yake fad'a don dama bai d'aga murya ko a waya balle kuma da yake da
Sweetheart d'in shi yake wayar, duk da Fatuu bata gane da ita bane amman ran ta ya bata itace, runtse
idonta tay ta shiga jefa ma kan ta tambayoyin da bata da amsar su, tambayar farko wadda tafi d'aure
mata kai itace yanda akai Ya Haisam ya aureta ba kamar data ji gwaggo tace dalilin fasa aurenta da
Khalid kenan wanda ita dae tasan tun bayan data je ruga sau d'aya ma su kai waya da shi har sai bayan
da suka dawo nan ta ayyana ashe ranar da sukai Vedio call da yace zai ga fushin da take dashi ita matar
shi ce, tsananin mamaki ne ya cika ta sai kuma ta d'an yi murmushi, tambaya ta biyu data sake jefa ma
kanta itace ya matsayin auren yake tunda ba wanda ya bayyana mata har sai yanzu da Al'amarin nan ya
faru shin auren zai d'ore ko kuwa ba zai d'ore ba don ta fahimci kamar ba don hakan aka yi shi ba, gashi
kamar yana fushi da ita kuma tasan don abunda ya faru ne ga maganganun data je ta fad'a mashi har
tak'i d'aga wayar shi wanda tasan da ta d'aga kiran nashi da hakan bai faru ba, tambaya ta k'arshe da har
saida gaban ta ya fad'i sosae itace yanzu in auren zai d'ore ne ya Aunty Fanan zata ji anya zata amince da
ita matsayin KISHIYA tunda ta tabbatar itama ba ta san da auren ba kaman yadda ko Hajiya bata sani ba
wata zuciyar ta raya mata ga dangin su kuma suma ba lalle ma su amince ba, wani irin sanyi jikinta yay ta
raya ita dama ta dad'e da fahimtar Ya Haisam ya fi k'arfinta ba iya samun shi zatai matsayin miji ba
hakanan zuciyarta ke azabtar da ita da son shi duk kuwa yadda taso ta cire shi abun ya gagara duk aje a
dawo son shi na nan mak'ale a zuciyar, wasu siraran hawaye ne suka fara gangaro mata masu d'umi taci
gaba da tunane tunane a haka bacci ya d'auketa, shima tuni sukai sallama da Fanan d'in ya nuna mata
bacci yake ji, gaba d'aya kwanciyar bata mashi dad'i dama d'azun harda k'arin da bargo ne ya samu har
bacci ya d'auke shi yanzu kuwa ji yake ya takura ga kayan jikin shi daya kwanta dasu su kan su a takure
yake da su don bai saba kwana da kaya ba bai ma tunanin ya ta6a kwana da kaya haka, hakanan dae ya
d'aure yana ta faman gyara kwanciya akai akai, bai fesa maganin daya gani a cikin basket d'in ba don ba
sauro a d'akin tunda akwae Ac ga kuma fanka sannan windows d'in akwae Net, sai can dare ya raba ya
samu bacci ya d'auke shi,

A kan kunnan shi aka fara kiran farko na sallar Asuba hakan yasa ya tashi zaune ya kai idon shi kan Fatuu
dake ta bacci, d'auke idon yay ya shiga tunanin yadda zai yi salla don bai using wani toilet ba wanda ya
saba amfani ba balle kuma na Asibiti gashi bai yuwuwa yace zai tafi gida ya barta can yay deciding ya
shiga na cikin d'akin kawae ya mik'e ya nufi toilet d'in, after few minutes ya fito harda Alwala yayo ya
koma wurin kujeran ya ciro prayer mat dake jikin ta ya shimfid'a ya kabbara raka'atanil fajr bayan ya
sallame zaune yay yana tasbih ta hanyar yin amfani da wayar shi har lokacin salla yayi sannan ya mik'e
saida yay d'an jimm yana kallon gadon sai kuma ya juya ya tafi, har aka gama sallar ya dawo bata farka
ba ya koma kan kujerar ya zauna ya bud'e wayar shi ya fara yin Azkar bayan ya gama ya ajiye wayar ya
d'an zamo jikin shi daga kan Sofa d'in ya d'age kai had'i da lumshe ido yana haka yaji motsin ta slowly ya
sauke kan ya kai idon shi kan gadon lokacin ta tashi zaune suna had'a ido tay saurin maida kanta k'asa,

"Do u need anything?" taji cool voice d'in shi yana tambaya daga inda yake d'agowa tay ta kalle shi a
sanyaye tace toilet zata je d'an shiru yay sai kuma yace "Do u need Help?" Girgiza mashi kai tay alamar
a'a bai ce komae ba ta fara kokarin saukkowa daga kan gadon, ba laifi taji k'arfin jikin ba kaman jiya ba
idon shi a kan ta har ta shige cikin toilet d'in, bata d'au lokaci ba ta fito idon ta a k'asa ta nufi gadon ta
zauna a gefe kan ta a sadde, pad da pant take son ta d'auka don ta canza amman ta kasa d'auka tana
haka taji yace "U need to take bath" da sauri ta d'ago ta kalle shi suka had'a ido kaman yar k'adangaruwa
ta d'aga mashi kai sai kuma murya na rawa ta gaishe da shi ya amsa had'i da tambayar jikin ta tace da
Sauk'i sosae ya d'aga mata kai kawae ya janye idon shi daga kallon ta har yanzu dae canjin da ta gani a
fuskar tashi yana nan, mik'ewa tay ta nufi inda jakar kayan take ta duk'a bayan ta bud'e ta d'auki abunda
take buk'ata ta rufe jakar ta mik'e tana rungume da su ta nufi Toilet d'in still kallon ya bita dashi har ta
shige, saida ta gama kimtsawa a ciki sannan ta fito bata gan shi a cikin d'akin ba saidae attender dake
Mopping sarkin tsafta har yaje ya kira azo a goge suna had'a ido da matar Fatun ta gaishe da ita tana
murmushi ta amsa tay mata ya jiki tace da Sauk'i ta nufi gadon ta haye ita kuma bayan ta gama har
kujerar ta kakka6e ta nufi cikin toilet d'in don ta gyara shi tana shiga sai gata ta fito ruk'e da dustbin ta yi
hanyar fita, saida aka gama gyara d'akin fess sannan ya shigo lokacin Fatuu na zaune ta jingina da kan
gadon ta bishi da ido har ya zauna sannan ta janye idon, tsit kake ji sai kace ba mutane a d'akin ko kuma
kurame ne a ciki bayan d'an wani lokaci ya fara tunanin ya samo mata wani abu ta ci sai dai kuma yasan
yayi safiya da yawa ko ya fita ba lalle ya samo wani abu ba hakan yasa shi tunanin ya bari garin ya d'an
k'ara wayewa, suna ta zaune can ta d'an saci kallon shi karaf suka had'a ido kasa janyewa tay shima
kallon nata yake kawai sai ji tay yace "kina jin yunwa ne?" tambayar ma saida taso ta d'an bata dariya
amman ba halin yi da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a sai kuma kamar mara gaskiya ta zame ta
kwanta ta juya mashi baya don ta fahimci Saboda kallon data yi mashi ne yasa shi yi mata tambayar bin
bayan ta yay da kallo can kuma ya d'age kan had'i da lumshe ido, karfe bakwae saura yan mintuna aka
kwankwasa kopar ya sauke kan ya kai idon shi kan kopar saida aka k'ara knocking d'in sannan yace a
shigo kopan a bud'e take aka turo Amadu ne ya fara shigowa yana ruk'e da basket mai d'auke da kayan
abinci gwaggo na biye da shi itama tana ruk'e da wasu kayan harda bucket da kujera yar tsugunno ta
roba yana ganin su ya mik'e tsaye fuskar shi a sake yake kallon su suka nufo ciki suma duk suna yi mashi
murmushi, a gefen gadon ya aje basket d'in gwaggo dake gefe da murmushi tace "Sannu d'ana Haisam
ya kwanan Asibiti" d'an murmushi yay yace mata Alhamdulillah had'i da gaishe da ita bayan ta amsa tace
"Amman dae nasan baka samu yin bacci ba kwanan Asibiti akwae takura gashi ba'a shirya mashi ba" still
murmushin yake yace mata yayi bacci yar dariya tay tace ya dae fad'a ne Amadu ya gaishe dashi yayi
mashi ya mai jiki ya amsa, ganin yayi tsaye tace mashi yay zaman shi zata zauna a gefen gadon ya koma
yace ma Amadu yazo ya zauna itama gwaggo ta zauna idonta akan Fatuu dake ta bacci ta lullu6e tana
son ta tambayi ko ta farka amman ta kasa Saboda kunya can dae ta kalle shi tana murmushi tace "ya mai
jikin?" Kallonta yay calmly ya furta "da Sauk'i sosae tun jiyan around 11 ta farka yanzu bata dad'e data
koma ba" wani sanyi gwaggo taji cikin ranta Amadu ma har saida yay d'an murmushin jin dad'i gwaggon
tace Allah ya k'ara lafiya duk suka amsa da Amin shiru ta biyo baya, bayan d'an wani lokaci gwaggo tace
ma Haisam ko a had'a mashi breakfast taga safiya ce sosae bata san ko zai ci ba yace mata a'a tace to ko
tea ne a had'a mashi ya gasa cikin shi fuska a sake yace mata ba zai iya sha ba bai wanke baki ba tana
murmushi ta jinjina kai kawai don ta san shi sarkin tsafta ne da gaske ba zai iya cin ba, Shiru suka k'ara yi
Amadu na latsa waya ita kuma gwaggo kanta a k'asa tana yi tana d'an juyawa ta kalli Fatuu can ta juya ta
kalli Haisam daya had'e hannuwan shi ya kifa goshin shi tace "d'ana Haisam Don Allah ka tashi kaje gida
ko ka samu ka huta sosae" slowly ya d'ago ya d'an kalleta suka had'a ido sai kuma ya kawar da idon bai
ce mata komae ba dae hakan yasa ta k'ara ce mashi yaje ba wani abu ai tunda gasu sun zo, a hankali ya
furta to tare da yin godiya ya mik'e bayan ya d'auki wayar shi sukai sallama ya nufi kopa ya fita,

"Bawan Allah ni tausayi ma ya bani da gani bai samu isashshen bacci ba" Amadu ne yay Maganar
gwaggo tace "taya zai samu yin isashshen bacci a nan duk da dai kamawa take amman nasan da wuya in
ya ta6a jinyar wani haka suda suka saba kai mara lafiya K'asar waje shiyasa wllh ban so ya kwana ba don
dole zai takura to ba yadda zan yi da Hajiya" shiru Amadu yay can ta mik'e ta cire hijabin jikinta ta d'auki
bucket d'in da kujerar ta nufi toilet, bayan ta shiga fess ta gan shi dama niyyarta in yana buk'atar gyara
sai ta gyara anan taga rigar Fatuu data cire jiya da undi ta d'aukko su ta saka acikin bucket d'in don ta
wanke, Amadu na zaune ruk'e da wayar yana lallatsawa kaman daga sama yaji muryar Fatuu ta kira
sunan shi da sauri ya d'aga kai ya kalli gadon suka had'a ido da ita ta tashi zaune gaba d'aya hankalin shi
na akan wayar har baiji motsin tashin ta ba, mik'ewa yay ya nufi gadon yana washe baki ya zauna a gefe
itama murmushi take mashi cike da farin ciki yace "Sannu kin tashi?" Kai ta d'aga mashi a sanyaye ta
tambayi yaushe ya zo yace basu dad'e ba harda gwaggo tana cikin toilet ta d'aga mashi kai ya tambayi ya
jikin nata tace da Sauk'i sosae yanayin fuskar shi ne ya canza "ashe haka abu ya faru ni ban sani ba koda
nazo lokacin baki farka ba saida muka koma gida da daddare gwaggo ke sanar dani" shiru tay ta zuba
mashi ido can yaji tace "Kawu Amadu miyasa baka ta6a fad'a man zancen auren ba duk da kasan ni ban
6oye maka abu" yadda tay Maganar kaman zatai kuka shima yanayin fuskar tashi ne ya sauya zuwa
yanayin damuwa ya kai hannu ya kamo hannunta guda yace "ba hakanan na k'i fad'a maki ba gwaggo ce
ta hana tace kar in sake inyi maki Maganar shine dalili" d'an ta6e baki tay kwallan da suka taru suka zubo
sharr da sauri ya kai hannu yana goge mata yana bata hak'uri had'i da nuna mata komi ya faru haka Allah
ya k'addara suna haka gwaggo ta bud'e kopar toilet d'in ta fito............

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2054*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


...........Nufo cikin d'akin tay tana d'an yarfe ruwan fuskarta da alama wanke ta tay, a gefen gadon ta
tsaya idon ta akan Fatuu da itama ta kafeta da nata idanun, da d'an murmushi tace "sannu kin tashi"
itama murmushin take mata ta d'aga mata kai kafin ta gaishe da ita ta amsa tay mata ya jiki, shiru suka
d'an yi suna ta kallon juna Amadu na kallon su da murmushi yar ajiyar zuciya gwaggo tay tace mata ga
breakfast nan kai ta k'ara d'aga mata, kina iya saukkowa ne?" Gwaggo ta tambaya a hankali tace mata
eh ta fara matsowa zuwa bakin gadon ta zuro da kafafun ta har zata mik'e gwaggon ta dakatar da ita
tace yakamata a k'ulle gashin ta kai hannu ta fara tattara mata shi bayan ta gama ta juya cikin kayanta ta
d'aukko mata brush da toothpaste ta tambayeta zata iya zuwa toilet nan ma kai ta d'aga mata alamar
zata iya amman duk da haka saida ta kai hannu ta d'agota ta nufi toilet d'in da ita Amadu nata kallon su
cike da k'auna, Bayan da Haisam ya fito yana shiga reception zai nufi hanyar fita wata mata sanye da
farar doguwar rigar uniform kanta d'aure da kallabi ba hijab a jikinta ta sha gaban Haisam tana Fad'in
"wa nike gani kaman ango?" dakatawa yay ya kai idon shi kan ta nan take ya ganeta mama ce wadda ta
duba Fatuu lokacin da abun ya faru da d'an murmushi ya gaishe da ita yay mata ya aiki bayan ta amsa
fuska a d'age tana kallon shi ta cikin glasses d'inta tace "wani ke bai lafiya ko kai?" Fuska a sake yace
mata ita matar tashi ya kawo tambayar shi tay Mike damun ta kuma yace "She had a miscarriage" waro
ido mama tay "Subhanallahi yaushe hakan ya faru?" Ya bata amsa da jiya ta tambayi yanayin cikin yace
mata just 1month ne ruk'e ha6a tay "Oh kace dai tun wannan karan battan aka samu abu bai dad'i ba
kuwa" shi dae d'an murmushi kawae yay tambayar inda Fatun take tayi ya fad'i mata tana Amenity da
room no d'in ta jajanta mashi kafin sukai sallama ya tafi, tare suka fito bayan tayi brush d'in saida
Gwaggo tace ko zatai wanka tace tayi d'azun da asuba, bayan sun fito kan kujera gwaggo ta sata ta
zauna ta fara had'a mata breakfast, kakkauran tea da slice bread sai wainar k'wai ta had'o mata ta aje a
gefen ta tace ta ci ta k'oshi kallonta tay da d'an murmushi tace mata ta gode, kallon Amadu da har
lokacin yana a bakin gadon Gwaggo tay ta tambaye shi yanzu zai yi Karin kumallon ta had'a mashi yace
a'a ta bari sai d'an anjima gefen Fatuu ta koma ta zauna cikin sanyin murya Fatun tace ita ba yanzu zata
ci ba tana mata murmushi tace sai ta gama, a hankali take cin Abincin akai akai gwaggo ke kai idonta kan
ta tay mata sannu ita kuma sai tay d'an murmushi ta amsa suna haka aka turo k'opar Mama ce ta shigo
da sallama idonta akan su Gwaggo dake zaune ta amsa mata tunda Fatuu ta kalleta ta gane ta, k'arasowa
ciki tay gwaggo na kokarin mik'ewa tace tay zamanta su ai sun saba da tsayuwa, gaisawa suka shiga yi
Amadu ma ya gaishe da ita ta amsa kafin ta maido idonta kan Gwaggo tay mata ya mai jiki da fara'a tace
mata gata nan da Sauk'i ta maida kallon ta kan Fatuu cike da jajantawa tace "Sannu Amarya ai yanzu na
had'u da Angon naki zai fita shine yake sanar da ni kina nan kin samu miscarriage" wani abu Fatuu ta
had'iya tay mata zuru da ido Gwaggo kuwa kan ta ne ya kulle cikin ranta ta hau mamakin jin sunan data
kira Fatuu Saboda a tunanin ta iya su kadae suka san da Maganar auren to ya akai ita ta sani gashi ba
sanin ta ma tayi ba ko a yan'uwan Haisam d'in, kamar Mama tasan zancen zucin da Gwaggon ke yi ta
kalleta tace "ai bayan auren nan ya kawo mana ita magashiyan cikin mawuyacin hali hankalin shi a
tashe" wata irin kunya ce ta rufe Fatuu ta sadda kai gabanta na fad'uwa gwaggo ma d'an murmushin
yak'e tay ta maida idon ta gefe Amadu kuwa dama wayar shi na a hannun shi sai kawae yay kaman yana
kira ya mik'e ya nufi hanyar fita, cigaba Mama tay "ai har fad'a saida nay tayi kan yadda ake d'irka ma
yara magungunan da suka fi k'arfin su don harda hakan ke haddasa irin wannan aika aikar azo kuma aita
jan ido Allah ma yaso ita ba'a dangana da yin d'inki ba, ashe har an samu rabo sai kuma abu mara dad'i
ya faru" gwaggo dake ta murmushin yak'e a kunyan ce tace mata "Wllh kam" ta fahimci irin Mutanen ne
da bakin su a sake yake komi yazo fad'i suke ba tare da sun ji komae ba,
"To Allah ya maida mafi Alkhairi ai abun ba wuya yanzu kin ji an samu wani ba kamar yaran yanzu
fitinannu ne wllh jarabar tsiya gare su" Fatuu tamkar ta nutse a wurin haka taji ba ita kadae ba har
gwaggo wata irin kunya ce ta rufe ta saidae ta sadda kan ta k'asa ita kuwa Mama ko a jikin ta tambayar
gwaggo tay wai Fatuu d'iyarta ce ta d'ago da d'an murmushi tace mata a'a jikarta ce a wurin ta take nan
fa ta hau yi ma gwaggo tambayoyi sai kace yar jarida harda tambayar ta amma dae Haisam d'an manyan
mutane ne ko don taga ranar da ya kawo Amaryar tashi har kyautar dubu hamsin yay mata nurse da ta
kawo shi wurinta kuma dubu ashirin nan gwaggo ta sanar da ita ko d'an waye harda su ruk'e ha6a tace
koda taji ai biri yay kama da mutum sai kuma tace ma gwaggo wai kaman ta san fuskarta a wani wuri
tace mata ba mamaki ita attender ce a k'aramar Asibiti Mama tace ba shakka anan tasan fuskar sai k'ara
cewa ikon Allah wai su kaman masu d'an rufin asiri ne daga amsoshin da ta bata shi kuma gashi d'an
shahararran mai kud'i da aka sani a haka kuma ya auri ita Fatun don taga yanzu auren jari hujja ake ita
dae gwaggo sai murmushi take tace mata ai su ba irin wad'annan masu kud'in bane kud'in su basu sa
masu girman kai ba kowa na su ne ko mai kud'i ko talaka duk d'aya suka d'au kowa, sosae ta shiga yabon
su tana fad'in dama tana jin ana fad'in alkhairan mahaifin shi da kakar tashi ma har a tv tana ganin
aiyukan Alkhairin da suke yi harda ce ma Fatuu tayi dace ta k'ara gode ma Allah samun irin wad'annan
mazan a yanzu ba k'aramar baiwa bace don tsananin wahala gare su don haka ta rik'e shi gam ta bishi
sau da k'afa still kan Fatun na k'asa Gwaggo dae sai murmushi take daga baya ta hau yi ma Fatun
tambayoyi tace anyi mata wankin ciki ne gwaggo tace mata a'a jiya har suka bar asibitin da daddare ba'ai
ba da yake ta suma ne sai daga baya ta farfad'o Allah yaso bata tambayi dalilin suman nata ba sai ta kalli
Fatun tace "kina zubar da jini ne sosae har yanzu?" Kai ta girgiza mata ba tare data kalleta ba a hankali
tace "a'a ba sosae bane" tace "akwae gudaji gudaji?" d'an shiru Fatun tay alamar tunani sai kuma ta d'an
kalleta tace a'a babu, nufar gado mama tay tana fad'in k'ilan ma ba sai anyi Mata ba to da alama komae
ya fice tunda dama cikin k'arami ne sosae, a gaban drawer d'in gefen gadon ta tsaya ta kai hannu ta fara
duba magungunan dake sama tana yi tana d'age ido had'i da cuno baki da alama dae kaman bata gani
sosae sai da gilashin, bayan ta gama dubawa ta dawo wurin su tace tunda an bata wadancan
magungunan tasan za'ayi mata scanning in anga komae ya fita ai shikenan dama amfanin wankin cikin
don a fitar da komae koda wani abu ya mak'ale a mahaifar gwaggo ta d'aga mata kai daga baya tace bari
ta tafi tana shirin tafiya gida ne aikin kwana tayi zuwa da daddare in ta shigo zata shigo taji yadda sukai
da likita gwaggo ta mik'e tay mata rakiya har bakin k'opa tana mata godiya ta tafi, tunda gwaggo ta juyo
ta dawo kan Fatuu ke a k'asa inda ta tashi ta koma ta zauna d'akin yay tsit wata irin kunyar gwaggon ce
ta lullu6e Fatuu yayin da ita kuma Gwaggo ran ta yay mata wani iri sosae abun ya ta6a mata zuciya jin
Haisam har Asibiti ya kawo Fatun wato yanzu da ba aure a tsakanin su kuma Al'amarin cikin bai biyo
baya ba shikenan ita ba sanin an aikata zatay ba, sosae jikinta yay sanyi lalle mutum bai isa ya shiryar da
wani ba face Allah yaso kaidae kawae saidai kai iya bakin kokarin ka ka had'a da Addu'a amman wani
tsananin ka ko sa ido ko wani wayon ka ko dubara duk basu yi wllh tarbiyar yara yanzu sai an dage da
Addu'oi don duk yadda kake kaffa kaffa wllh bai hana yaro lalacewa ba tare da ka ankare ba Allah
Ubangiji ya shirya mana zuri'a ya tabbatar dasu akan daidai ya taya mu tarbiyyantar dasu kada yaba wani
abokin halitta damar canza su daga kan tarbiyyar da akai masu mai kyau ya shirye mu baki d'aya darajar
fiyayyen halitta Manzo (S.A.W).
Haisam na fita daga Asibitin gidan Hajiya ya nufa, bayan ya isa yay parking Motar part d'in shi ya nufa
yana zuwa Toilet ya shige don yin wanka, after some minutes ya fito k'ugun shi d'aure da Towel ga wani
short yana goge sumar shi da shi wata irin yunwa yake ji shiyasa bai tsaya busar da ita da dryer ba shi
kan shi saida yay mamakin yunwar don bai cika yin Breakfast da sassafe ba sai wurin 11 haka amman
yanzu duka k'arfe takwas da yan mintuna, gaban dressing mirror ya tsaya ya shafe jikin shi da body
cream d'in shi mai daddad'an k'amshi bayan ya gama ya shafa roll on ya feshe jikin shi da body spray
kala ukku har wani mai ya d'aukko ya matsa a tafin hannun shi ya kai kan kwantacciyar sumar chest d'in
shi ya shafe nan take ta k'ara kwanciya luff ya k'ara d'aukko hair spray ya feshe sumar kan kafin ta k'irjin
ma ya d'an fesa mata bayan ya gama yan shafe shafen closet ya nufa ya ciro jallabiya da short ya dawo
bakin gadon ya fara kokarin sawa, sanye cikin jallabiyar wadda coffee brown ce mai gajeran hannu ya
fito bayan ya zura takalma a cikin Corridor ya shigo cikin parlorn dake a gyare tsaf kaman ko yaushe ya
nufi kopar ya fita, part d'in Hajiya ya nufa lokacin da ya shiga Parlon ba kowa hakan yasa ya wuce
Bedroom d'inta ya turo kopar ya shiga da yar sallama, tsayawa yay a bakin kopar yana kallon Hajiyar
dake kwance tana ta sharar bacci ta rufe rabin jikin ta da lallausan bargo baki a wangame d'an murmushi
kawae yay ya juya ya bud'e kopar yana fitowa Saude ma ta fito daga cikin d'akin ta zata kitchen
dakatawa yay cikin girmamawa ta gaishe dashi ya amsa mata tay mashi ya mai jiki don jiya bayan Hajiya
ta dawo saida ta bata labari kaf tana ta fad'a tana fad'in Haisam bai d'auke su da mahimmanci ba bama
kamar ita yanzu ta gane bai damu da ita ba bai k'aunar ta shiyasa ya iya fad'i mata abunda hankalin ta zai
tashi harda uban kukan ta ko ta mutu ko tay rai shi ko ajikin shi nan fa Saude ta hau rarrashinta tana
bata hak'uri saidae a can k'asan ranta ta ji ma Fatuu dad'i sosae da Haisam ya kasance mijinta duk da
bata ji dad'in zubewa da cikin yay ba har Addu'a tay kan Allah yasa auren ya d'ore, umarnin ta kawo
mashi breakfast ya bata ta tambayi abunda zata kawo yace wanda ya samu daga haka ya wuce saida ya
fita daga cikin corridor d'in sannan itama ta wuce, a parlor ya zauna bai koma part d'in shi ba ta bishi da
shi can don yanzu yasan ita matar aure ce, ba'a d'au lokaci ba ta shigo cikin parlorn ruk'e da d'an babban
tray saida ta janyo c-table gaban shi sannan ta d'aura mashi tace aci lpy ya jinjina mata kai had'i da furta
thanks, kakkauran tea ne a cikin mug sai babban plate mai gidaje da marfi bayan ya bud'e soyayyar
plantain ce a gida d'aya sai chips a wani gidan na k'arshe kuma soyayyar wainar k'wai ce daga d'ayan
gefen tea d'in ledar biredi mai yanka yanka ce duk da komae d'an daidai ta zuba sun mashi yawa, fara ci
yay a nutse yana yi yana d'an kallon Tv a haka har ya gama ya rufe sauran da ya rage ya idasa hayewa
kan kujerar ya kwanta sosae yana ci gaba da yin kallon bada jimawa ba bacci ya kwashe shi. Sai wurin
karfe goma Hajiya ta fito jikinta sanye da doguwar riga cotton ta nufo cikin parlorn da sandar ta ta
alfarma tana zuwa bakin kujerun tay turus idon ta akan Haisam da ya d'aura hannun shi d'aya ya rufe
idon shi yana ta bacci, d'an ta6e baki tay ta wuce ciki a kujerar kusa da tashi ta zauna ta bishi da kallo
kaman yaji a jikin shi ya fara motsi ya sauke hannun slowly ya fara bud'e idanun shi suka sauka akan
Hajiya da ta tura baki tana bin shi da ido shima kallon ya bita dashi kafin ya yunk'ura ya tashi zaune ya
jingina da jikin kujerar cikin muryar wanda ya tashi daga bacci ya gaishe da ita "Gud morning
Sweetheart" wata uwar harara ta zabga mashi a d'an fusace tace "ai ka daina yaudara ta kaje can kai ma
wata dad'in baki ba dai ni ba" wani kalar kallo yake bin ta da shi idanu a d'an lumshe can yay sigh slowly
ya furta "am sorry" k'ara tura bakin tay ta kauda idon ta gefe ganin haka yasa shi jan jiki ya matsa can
k'arshen kujerar ya kai hannu ya kamo hannunta ta fara k'ok'arin kwacewa sai dae ta kasa a fad'ace tace
"ai tunda kaga zuciyata bata buga ba sai ka k'arasa ni ta hanyar k'arya man hannun" d'an guntun
murmushi yay remorsefully yace "I said am sorry I regret what I did, I dont know what came over me har
hakan ya faru" yana Magana yana wani lumshe mata idanu sai kace wata budurwar shi ko matar shi k'in
kallon shi tay tana cigaba da tura bakin had'i da kikkafta idanu d'an matsa hannun yay aikuwa ta juyo a
fusace tace "Ka gama raina ni Haisam, kai wato har kana da k'arfin halin yi man wannan iskan cin ko" har
sai da ya d'an yi yar dariya jin abunda tace cigaba tay "in ba don ka raina mu ba ka d'auke mu maras
amfani wai har kasa a d'aura maka aure ba tare da sanin mu ba" rai 6ace tay Maganar yace "kiyi hak'uri
Allah ne ya kaddara hakan zai faru ni kaina I never thought zan yi hakan" wani kallo take jefa mashi can
tace "uhmm kai ka sani" sakin hannun nata yayi ya maida bayan shi ya jingina da kujerar idon shi na
kallon gaban shi ita kuma Hajiyar idonta na akan shi can cikin d'aure fuska ta tambaye shi jikin Fateemar
ya kalleta fuska a sake yace mata da Sauk'i tace ta farka ne yace mata eh tun jiya tay shiru can kuma ta
sake cewa "ita waccan ta K'asar wajen kunyi magana da ita ne karta ji shiru tunda dae ba yadda za'ai ka
tafi kabar yar mutane da ciwo" d'aga mata kai yay sai kuma yace mata sun yi magana jiya tace "kadae
zabga mata k'arya tunda naga ka iya ta yanzu" bai ce komae ba ya d'age kan shi kawae yana facing
saman Parlon yaji tace in baccin zai cigaba ya tashi ya koma part d'in shi ko a gyara mata parlonta yazo
ya kama yi mata bacci ya hana a gyara, sauke kan yay suka had'a ido sai kuma ya mik'e ya nufi hanyar
fita yana tafiya a hankali tabi shi da ido har ya fita ta maida jikinta jikin kujerar tay shiru da alamun
damuwa akan fuskar ta ta, part d'in shi ya koma ya shige bedroom ya kwanta a kan gado nan da nan
wani baccin ya sake d'aukar shi.

Saida Amadu yaga fitar Mama sannan ya koma cikin d'akin yana niyyar komawa bakin gadon Gwaggo ta
mik'e tace yazo ya zauna bari ta had'a mashi breakfast d'in yaci yanzu in ba haka ba ba lalle ya samu
damar ci ba d'an anjima mutane zasu iya fara zuwa yace to, bayan ya fara ci Fatuu dake gefen shi ta
tambaye shi ko yaga wayarta kafin ya bata amsa gwaggo tace gata nan cikin Aljihun ta jiya ma bayan sun
koma Fauziyya ta kira ta d'aga ta fad'i mata tana Asibiti shiru Fatuu tay cikin ranta ta shiga raya da ta bi
Maganar Fauzy da yanzu cikin na nan ta tabbatar ma inda tasan kiran da Haisam yay mata a waya da
yawa ne harda text message bazata bari a zubar ba wani, wani irin sanyi jikinta yay nan take taji wata irin
nadama tazo mata da kanta ta zubar da cikinta na halak cikin mutumin da take tsananin k'auna, gaba
d'aya ji tay breakfast d'in ya fitar mata a rai ta mik'e ta tattara kayan ta nufi gefen gado dasu gwaggo na
ce mata har ta k'oshi tace eh ta tashi ta bata magungunan ta, bayan ta gama sha idasa hayewa gado tayi
tay lamo har gwaggo na tambayar ta ko jikin ne tace a'a bacci ne bai ishe ta ba tace ai sai taci gaba ta
lumshe ido kaman baccin zatai da gaske amman tunane tunane da zancen zuci kawae take a haka baccin
ya d'auketa ba, bayan Amadu ya gama yace ma gwaggo zai tafi sai anjima zai dawo tace to k'ilan ta kira
shi ya dafa Abinci ya zauna cikin shiri sukai sallama ta bashi kayan Abincin da aka gama dasu ya tafi.
Wuraren k'arfe sha d'aya Fatuu ta farka taga d'akin wayam ba kowa tana kwance aka turo k'opar sai ga
Fauzy ta shigo da yar sallama da sauri Fatuu ta yunk'ura ta tashi zaune tana kallonta itama Fauzy da sauri
ta nufi gadon ta zaune a gefe fuskarta d'auke da matsananciyar damuwa tayi mata sannu ta d'aga mata
kai d'an shiru sukai sunata kallon juna fuskar Fatuu a yamutse kaman zata saka kuka can Fauzy tace
"ashe haka abu ya faru harda kwanciya Asibiti tun bayan da muka rabu inata so in kira ki zullumi da
fargaba suka hana ganin har dare yayi baki kirani ba kin sanar da ni halin da ake ciki yasa nai k'arfin halin
kiran ki saidae kusan sau ukku ba'a d'aga ba tsoro ya kama ni sosae na shiga tunanin to ko lpy gashi na
kasa kiran ko Kawu Amadu, sai can dare wurin karfe 11 nace bari in k'ara jarabawa k'ilan ki d'aga tunda
lokacin kwanciya ne ina kira sai gwaggo ta d'auka nan take sanar dani wai an kwantar dake Asibiti wayar
na gida aka barta wllh sosae hankali na ya tashi bazan 6oye maki ba ko bacci ban yi ba saboda fargabar
abunda ya faru har aka kwantar da ke, Aunty Mareeya har ta gane ina cikin damuwa tanata tambayata
Mike damuna saidae in ce mata ban jin dad'i kawai don ban san taya zan mata bayani ba" dakatawa tay
ta kai idonta kan ledar Karin jinin dake rataye cike da damuwa tace "harda k'arin jini ma akai maki kenan,
cikin ne ya fita kika zubda jini sosae?" Kai Fatuu ta d'aga mata alamar eh, girgiza kai Fauzy tay "Sannu,
wllh irin abunda nake ta gudu kenan kinga ko a Makarantar hakan ta faru sai an san dalili, to yanzu da su
gwaggon suka sani miya faru?" Shiru kaman bazata ce komae idanunta suka ciko da k'walla a hankali
suka fara gangaro mata cikin muryar kuka tace "Fauzy na aikata babban kuskure wllh ashe cikin nan na
halak ne ba yadda na zata ba" waro ido Fauzy tay with mouth agape a rud'e tace "cikin halak! Kenan kina
son kice man Ya Haisam Mijin ki ne???" Cikin kuka ta d'aga mata kai k'ara zaro idon tay ta kai hannu ta
rufe baki kafin ta cire cike da Al'ajabi ta tambayeta yadda hakan ta faru nan ta shiga fad'i mata komae da
ya faru bayan ta dawo gidan har zuwa yanzu, salati Fauzy ta shiga yi tana yi tana kai hannu tana dafa
gaban kanta da kuma bakin ta cikin tsananin tashin hankali ta hau fad'in "ni wllh dama raina saida ya
bani anya ba wani abu a k'asa kwata kwata na kasa yadda Ya Haisam zai aikata maki hakan Saboda son
zuciya kawae dai bani da wata hujja ne, innalillahi abu dae bai yi dad'i ba wllh aka ce rashin sani yafi dare
duhu" sosae ta shiga damuwa har fuskar ta ta nuna idanun ta sun sauya kwalla ta kwanta cikin su sosae
Fatuu ke kuka tana fad'in "nayi danasani Fauzy duk da na d'aga wayar Ya Haisam bayan dana je na sanar
mashi da hakan bata faru ba, saida yay ta kira na harda message ya turo man yace kar in yi komae in
picking kiran nashi amman na k'iya k'in Fad'a maki nay don kar ki hana a zubar na nuna maki sau d'aya ya
kira, wllh ban yi zaton na halak bane tunda ni bansan komae ba ai gashi naga kaman ma yayi fushi
Saboda hakan " itama Fauzy k'wallan ne suka fara zubo mata suna cikin haka suka ji karar bud'e kopa
duk suka kai idon su kan kopar toilet sai ga gwaggo ta fito idon ta a kan su suma suka bita da ido cike da
rashin gaskiya...............

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2055*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

......Kauda idon ta tay daga kallon su ta nufo cikin d'akin cikin kame kai Fauzy ta gaishe da ita ta amsa
tare da d'an kallon ta tay mata ya mai jiki nan ma ta amsa kafin ta nufi kujera, a jikinta ta janyo Hijab
d'inta ta nufi hanyar fita daga d'akin tana kokarin sakawa, bayan ta fita Fauzy ta kalli Fatuu da yar
damuwa tace "ta san kin yi wani abu ne don zubar da cikin?" d'an shiru Fatun tay fuskar ta duk hawaye
tace bata sani ba ko likita ya gane ya sanar masu tunda ta dad'e bata farfad'o ba amman in ma ta sanin
to bata nuna mata ba, ajiyar zuciya Fauzy tay tace "to k'ilan bata sani ba amman yanzu kaman ma taji
abunda muke cewa" shiru kawae Fatun tay idon Fauzy akan ta wani irin tausayin ta ne ya kamata tasan
dole ta shiga matsananciyar damuwa yadda take son Ya Haisam bazata ji dad'i ba ace ta samu cikin shi
na halak kuma ta zubar da hannun ta gashi tace yayi Fushi, hannu Fauzy ta kai ta kamo nata ta fara
lallashin ta "ki kwantar da hankalin ki Zarah nasan dole Kiji ba dad'i amman kada kisa damuwa a ranki ki
d'auka komae rubutacce ne dama haka Allah ya k'addaro kuma shima Ya Haisam d'in na tabbatar zai
fahimce ki kawae dae dama dole ne ya nuna maki 6acin ran shi Saboda zai ga kin k'i jin Maganar shine
har hakan ta faru wanda nasan bai yi zaton hakan daga wurin ki ba a yadda kuke da shi amman dae
komai zai daidaita in sha Allahu, ki daina damuwa ko don halin da kike ciki kada ki samu wata matsalar
kuma" tana kai Maganar ta kai hannu tana goge mata kwalla daga baya tace bari ta sanar ma Aunty
Mareeya, bayan ta kirata ta sanar mata zancen kwantar da Fatun Asibiti salati ta saka hankali a tashe ta
hau tambayar Fauzy abunda ya samu Zarah nan ta kwashe komai ta fad'i mata tana jin yadda take zabga
salati a rud'e tace tana nan zuwa wane Asibitin take ta sanar mata, bayan sun gama wayar yar hira Fauzy
ta shiga yima Fatun duk don ta daina damuwa harda zancen irin shagalin da zasu yi in komae ya daidaita
da kalar su ankon da za'ai daga baya kuma yanayin fuskar ta ne ya canza tace tasan ma d'auke Fatun zai
yi su bar K'asar amman dae gaskiya a bari sai sun gama karatu lokacin tasan ta k'ara samun wani cikin
harma ta haihu, harda Addu'ar Allah yasa next cikin da zata samu na twins ne, tun dai Fatuu na d'an
murmushi sai gata harda su dariya, Bayan sallar Azahar sai ga su Feenah Abbas ya kawo su lokacin da
suka shigo su Fatun na Zaune akan gadon Fauzy na gefen ta Abdul na hango ta ya nufi gadon da gudu ya
fara k'ok'arin hawa Fauzy ta taimaka mashi yana hayewa ya fad'a jikin ta Feenah na fad'in bai ganin mara
lpy ce, a gefen gadon Feenah ta tsaya bayan ta aje basket d'in kayan Abincin data shigo da shi tana sanye
da doguwar rigar Atamfa tayi d'aurin kallabi mai steps ga gyale mahad'in kayan ta yafa a kafad'a hannun
ta na dama ruk'e da hannun Nasreen da itama tasha yan kanti, da alamun damuwa Abdul dake kallon
face d'in Fatuu yace "Aunty Fatuu ashe baki lpy" itama kallon shi take da d'an murmushi ta d'aga mashi
kai alamar eh ya juya ya kalli ledar K'arin jini fuskar shi kaman zai kuka idanun shi har sun kawo kwalla
yace mata sannu ta rungume shi ta gefe Feenah ma tayi mata ya jiki ta amsa mata kafin ta gaishe da ita
Nasreen ta fara rigimar itama a d'aurata kan gadon Feenah tace ya duk zasu haye gadon mara lafiya
Fatuu ta mik'o hannu tace ba wani abu ta d'auro ta Fauzy ta kai hannu ta d'aukko ta, ganin Feenah nata
tsayuwa yasa Fatuu ce mata "Aunty Feenah ga kujera can ki zauna" d'an murmushi tay tace "bari in
gama ganin ki to, ashe abu kuma haka ya faru jiya Dear ke fad'a man banji dad'i ba wllh nace da an sani
ai da an tari abun da wuri duk da hakan bai faru ba, shima yace man bai san abunda ke faruwa ba sai
jiyan" idanun Fatuu ne suka ciko da k'walla bata dae ce komae ba sai kikkafta idanu take don kada su
zubo suna haka Abbas ya shigo dama yana waje wurin gwaggo suna gaisawa, bakin gadon shima ya tsaya
Fauzy ta gaishe dashi ya amsa yay mata ya karatu ya maida kallon kan Fatuu cike da kulawa yace "Mom
Zarah ya jikin?" Kallon shi tay a sanyaye tace da Sauk'i,

"Allah ya baki lafiya ashe haka abu kuma ya faru?" Aikuwa kaman tana jira ta fashe masu da kuka dama
daurewa kawae take, girgiza kai Abbas ya shiga yi cike da tausayi Feenah ma Fuskarta kaman zata sa
kukan Fauzy kuwa tuni kwalla sun ciko mata, sosae Abdul ya rud'e ya d'ago yana fad'in "Aunty Fatuu don
Allah kibar kuka zaki samu lafiya in baki yi shiru ba nima zan yi kukan" k'ok'arin shanye kukan ta fara
tana girgiza ma Abdul kai alamar kada yayi ya kai hannu yana goge mata kowa jikin shi yayi sanyi Abbas
ne yace "Kiyi hakuri Mom Zarah nasan an maki ba daidai ba don da kin sani hakan ba zai faru ba to
amman komai ki ka ga ya faru dama rubutacce ne" kallon shi tay cikin muryar kuka tace "Amman Ya
Abbas Saboda mi aka 6oye man ko kai ba sai ka fad'i man ba tunda ni ban 6oye maka komai" da alamun
Damuwa kan face d'in shi yace "kiyi hak'uri don Allah haka aka tsara ne ba za'a sanar maki ba shiyasa..."
Katse shi tay "to Saboda mi?" Shiru yay don bai son yace mata auran tsarawa akai don a taimake ta ba
don ya d'ore ba, ba kamar kuma yanzu da abu ya shiga tsakanin su, Feenah ta fahimci Abbas bai son
sanar da ita game da auren hakan yasa ta kai hannu tana share mata hawayen dake zubowa tana fad'in
"Haba Mom Zarah d'in mu kefa nasan mai k'arfin hali ce kiyi hak'uri komae ya wuce ko ma samu ki warke
da wuri a k'ara samo mana cikin wani Baby d'in in sha Allahu ma twins za'a maida mana tunda da yawa
wani rabon ke kore wani" d'an murmushi Fauzy tay ta sadda kan ta haka ma Fatuu d'an juyar da fuskar
ta tay Abdul kuwa k'ura ma Feenah da tayi Maganar ido yay can ya kasa jurewa ya d'ago daga jikin Fatuu
yace "Momy Aunty Fatuu tayi aure ne?"

D'an shiru tay sai kuma tace mashi "Mi yasa ka tambaya?" yace "naji kin ce ta Warke ta haifo babies?"
shiru Feenah tay sham ta manta dashi a wurin tay Maganar tasan shi bai ji ya k'yale Abbas kuwa d'an
d'age gira yay yana kallon Feenah da murmushi alamar jiran yaji amsar da zata ba Abdul don ya kafeta
da ido can ta d'aga mashi kai tace eh tayi aure, waro ido yay alamun mamaki ya juya ya kalli Fatun ya
sake juyowa ya kalli Mom d'in tashi yace "Yaushe tay auren ni ban sani ba kuma waye ta aura?" ta biyun
ta amsa mashi tana d'an murmushi tace "Baban ka Zakee" har saida yay wata yar zabura ya tsuke fuska
cikin fushi yace "Kamm shine sukai auran ban sani ba kuma bani nace ma ya aure ta ba" a hak'ik'an ce
yay Maganar sai bin su yake da kallo ya kumburo baki sigh Abbas yay yace mashi "ai ba'a yi bikin ba
tukun an dai d'aura masu aure ne....." Katse shi yay kaman zai kuka "to ni miyasa ba'a je dani d'aurin
auren ba ba inada babban riga ba" har saida ya basu dariya su duka Fatun ma saida tay d'an murmushi
wato shi a tunanin shi saida babban riga ake zuwa d'aurin aure, kafin wani ya bashi amsa aka turo k'opar
da yar sallama k'asa k'asa ya shigo, Wow Tubarkallah Angon Fatuu shine abunda na fad'a, wankan bak'in
Voile yay ana d'an hango hasken vest d'in shi kad'an hannun shi d'aure da Agogo ta bak'ar fata haka
k'afafun shi dakakkun half cover ne masu kyau da tsada Sumar nan tasha gyara ta k'ara bak'i sai salk'i
take, sosae yay kyau tun ma kafin ya k'arasa shigowa k'amshin turaren shi ya baza d'akin kai kace shi
kadai kamfanonin turaren suke ma irin nashi don koda yaushe k'amshin shi na daban ne, tunda Fatuu
tay arba da Fuskar shi gaban ta ya fara wani irin bugu gaba d'ayan su idanun su na akan shi yayin da
Fauzy acikin ranta ta hau fad'in Tubarkallah sam bata ganin laifin Fatuu da take son shi ita a yadda take ji
ma da itace abu ya shiga tsakanin su har ta samu ciki wllh bazata zubar da shi ba bari zatai har ta haife
tunda tasan bazai ta6a wofintar da ita ba duk surutun da za'ai aje ai ta yi, Abdul na ganin shi ya saukko
daga kan gadon ya nufe shi da sauri lokacin har ya zo tsakiyar d'akin a gaban shi ya tsaya yana kallon shi
fuska a d'aure hakan yasa Haisam d'in tsayawa yana kallon shi Fuska a sake su Abbas nata murmushi
daga inda yake yace ma Haisam "Baba Zakee yau fa ka ta6o d'an gidan ka kay mashi laifi" d'an kallon
Abbas da yay Maganar yay sai kuma ya maido idon kan Abdul daya kumbura kamar zai fashe cikin cool
voice d'in shi yace "What's happening?" Ya kai hannu zai dafa kan Abdul d'in da sauri ya janye kan yasa
hannuwan shi duka ya ruk'e k'ugun shi alamar dai abun yau baram baram za'ai Abbas kau mi zai yi in ba
dariya ba haka ma su Fauzy still Haisam murmushi yake calmly ya furta "kaga dariya suke mana tell me
laifin mi nayi?" Yana tura baki yace "ashe dana ce ka auri Aunty Fatuu ka aureta ban sani ba kuma ko
d'aurin auren ba'a je dani ba!" Abbas ya amshe da fad'in "kuma dae yana da babban riga ato" duk sukai
dariya shima Haisam d'in yar dariyar yay ya kamo hannun shi yana fad'in yayi hak'uri to ya fara bubbuga
k'afa k'arshe Haisam d'in ya sunkuce shi ya d'aura shi a bayan shi sai k'unk'uni yake cike da shagwaba,
yana zuwa bakin gadon Fatuu ta sunkuyar da kanta Fauzy dake kallon shi ta gaida shi ya amsa tay mashi
ya mai jiki haka Feenah ma duk ya amsa Fauzy ta sauka daga kan gadon ta nufi Kujera Feenah ma ta bi
bayan ta ya rage daga shi sai Abbas tsaye a bakin gadon, kai idon shi yay kan ta kaman ance ta d'ago
suka had'a ido Slowly ya furta "Ya jiki?" a sanyaye tace da Sauk'i ya jinjina kai kawae still da canjin da
take gani akan Fuskar tashi, mai da kallon yay kan Abbas dake mashi wani kallo irin na wanda yay abu ba
daidai ba shi kuma ya maida mashi martani da nashi mai kaman harara suna haka Dr Habeeb ya shigo
cikin d'akin da sallama su Feenah suka amsa had'i da gaishe dashi yay masu ya mai jiki ya nufi su Abbas,
hannu ya basu suka gaisa gaba d'aya ya kalli Haisam yay mashi ya mai jiki k'asa k'asa yace da Sauk'i kafin
ya d'an matsa gaban gadon da murmushi yace ma Fatuu ya jiki tace da Sauk'i ta gaishe dashi ya amsa,
tambayarta yay tana jin wani ciwo ko a marar ta haka tace a'a bata jin komae ya k'ara tambayar yanayin
jinin da ke zuba da yanayin yawan shi a kunyance take bashi amsa tana yi tana d'an sadda kai don duk su
Abbas na ji,

"To ya kike jin yanayin jikin ki?" tace "kawae ba k'arfi ne sosae" jinjina kai yay "Ok sai a hankali k'arfin zai
dawo zuwa anjima sai a ida saka maki sauran jinin" kai ta d'aga ya juya kan Haisam yace "Yanzu ina ganin
muje ai mata Scanning d'in mu ga" kai Haisam ya d'aga ya juya ya kalleta suka had'a ido sai taga kaman
ma harararta yake da sauri ta sunkuyar da kan ta, Abbas ya yi ma Feenah magana kan tazo ta taimaka
mata suje wurin scanning tace to ta mik'e su kuma suka wuce tare da Dr d'in, bayan ta saukko daga kan
gadon Fauzy ma ta taso lokacin gwaggo ta shigo tazo wurin su tana fad'in bari a bata abunda zata yafa ta
wuce wurin jaka ta ciro mata d'an gyalen ta dama kan ta da hula suka tafi Feenah ta tallabo Shoulders
d'in ta, a kan hanyar su ne Fauzy ke yin Addu'ar Allah yasa aga cikin na nan Feenah tace ai gaskiya da
wuya ne Saboda Dear ya fad'a mata ta zubar da jini sosae gashi cikin dama d'an k'arami ne zai wuya ya
tsaya kuma already Dr ma yace masu ya fita, lokacin da suka isa a bakin wurin suka iske su Haisam tunda
ta kalle shi sau d'aya ta kauda idon ta Abbas ne yace mata ta shiga Dr d'in na ciki ta d'aga kai ta shiga
suma su Feenah suka tsaya a bakin kopar don su jirata daga baya Dr ya fito yace ma su Abbas suje Office,
sai bayan wasu mintuna Fatun ta fito Feenah ta tambayi an gama tace mata eh ance za'a tura ma Dr tace
Ok ta k'ara kamata suka tafi, Suna zaune a Office suna yar hira aka turo result d'in ya fad'a masu gashi an
turo ya fara dubawa bayan wani lokaci ya d'ago ya kalli Haisam yace "ya nuna ba sauran wani abu
mahaifar ta is empty so ina ganin kawae taci gaba da shan magungunan tunda tace jinin ma ba mai yawa
bane ke zuba yanzu a hankali zai d'auke, in kuma kun fi so ayi mata D&C d'in to wani lokacin yana
taimakawa wurin k'ara conceiving da wuri amman dama ciki k'asa da 10 weeks ba dole sai an yi ba indai
ba wata matsala haka" Wani kallo Abbas yay ma Haisam cike da shak'iyanci yace "H,Zakee ina ganin ayi
matan ko Saboda ai saurin k'ara samun wanin" banza yay ma shi cikin cool voice d'in shi yace ma Dr
shikenan ba sai anyi ba ya gode yana fad'in hakan ya mik'e Abbas ma ya tashi yana mashi dariyar iskanci
shima Dr Habeeb d'in mik'ewa yay yana yin dariyar don daga baya Abbas yay mashi bayani game da
auran da yadda aka samu cikin, saida ya rako su bakin Office d'in yace tayi duk abunda zata yi bada
jimawa ba zai zo ya sa mata jinin Haisam ya amsa da Ok kafin suka tafi, Bayan su Fatuu sun koma kan
kujera Feenah tasa ta zauna don taci Abinci cikin wanda ta kawo mata ta zubo mata tace ma Fauzy itama
ta zuba tana murmushi tace to, tasa Fatuu gaba tay wai sai ta ci shi sosae Abdul ma na gefen ta yana
fad'in taci ta k'oshi ta warke su tafi gida tare tay yar dariya suna haka Hajiya ta shigo harda Saude ruk'e
da k'aton Basket din kayan Abinci da kuma Tk, Feenah ta mik'e taba Hajiyar wuri don ta zauna, bayan ta
zauna idon ta akan Fatuu ta kai hannu ta dafa kafad'ar ta tace "Sannu Fateema kin ji an ja maki jinyar
dole" d'an murmushi kawai Fatuu tay ta gaisheta bayan ta amsa taci gaba "an gode ma Allah daya tashi
kafad'un ki, jiyan nan ai hankali na ya tashi sosae wllh yarinya tamkar ba rai ga uban jini da kika zubda, to
ya jikin naki yanzu?" tana d'an murmushi tace da Sauk'i sosae Hajiya tace "to Alhamdulillah Allah ya
k'aro sauk'in, su Dije sun auna Arziki don da wani abu ya same ki duk sai nayi k'arar su an bi maki hakk'in
ki wllh duk da haka ba k'yale su zan ba" kowa yay murmushi su Sauden sukai mata ya jiki ta amsa masu
ana haka gwaggo ta shigo cikin d'akin d'auke da plastic chairs guda biyu ta aje tace ma Saude su zauna,
bayan sun zauna duk suka gaishe da ita Sukae mata ya mai jiki ta amsa masu dama ta gaisa da Hajiya tun
a waje tana ta tura baki ta amsa mata, lokacin Abbas da Haisam suka shigo Hajiya ta bisu da wani wani
kallo fuska a tsuke Abbas ne kawae ya gaishe da ita ta amsa mashi ba yabo ba fallasa ya kalli gwaggo yay
mata bayanin da Dr yayi game da scanning d'in yace ba sai anyi Mata wankin cikin ba taci gaba da shan
magani gwaggon tace to in sha Allah Hajiya tace "ai gwara dae kada ayi matan a kyaleta da wahalan da
aka d'ora mata ba sai an k'ara mata wata Azabar ba" kowa dae murmushi kawae yake banda Haisam
dake tsaye can ya juya zai fita Abbas yabi bayan shi,

Sai da akayi la'asar Abbas ya kira Feenah ta fito su tafi lokacin an k'ara sama Fatuu jinin Abdul yasa
rigimar bazai tafi ba shi anan zai tsaya dama da yaga za'a saka mata jinin harda kukan shi da kyar gwaggo
ta lalla6a shi tace Asibitin ba'a barin yara su zauna da an ganshi za'a zo a tafi dashi ya bari in suka koma
gida sai yazo ya zauna har ta warke gaba d'aya yace to yaushe zasu koma gidan tace bada dad'ewa ba da
an sallame su zata kira daddy d'in shi ta gaya mashi sannan ya yarda suka tafi Fauzy tay masu rakiya har
bakin Mota, tana niyyar dawowa ciki sai ga Aunty Mareeya mai Keke Napep ya tsaya da ita Fauzy ta nufe
su tana murmushi tay mata sannu da zuwa ta amsa tace ta d'aukko basket a ciki tace to, bayan ta
d'aukko ta sallami mai Napep d'in suka nufi cikin Asibitin, lokacin da suka shiga d'akin Aunty Mareeya ta
gaida su Hajiya da Gwaggo tay masu ya mai jiki suka amsa sannan ta nufi gadon Fatuu na kwance jinin
nata shiga ta kalli Aunty Mareeyar da d'an murmushi ta gaishe da ita saida ta zauna a bakin gadon da
alamun damuwa tay mata sannu da jiki Fatun ta amsa bayan Fauzy ta aje basket d'in tazo daga d'ayan
gefen itama ta zauna Aunty Mareeya ta kalleta k'asa k'asa da murya tace "d'azun kina gaya man abun
Al'ajabi ashe duk abunan mutumin nan mijin Zarah ne" gyad'a kai Fauzy tay kawae ta sake cewa "amman
dai ni kun yi man rashin hankali wllh haba kaman baku san halin shi ba ai bai kamata kuyi saurin zubar da
shi ba" cike da damuwa Fauzy tace "wllh nima Aunty ban so akayi saurin zubar dashi ba..." Nan ta fad'i
mata yadda sukai da Fatuu kan zubar da cikin gaba d'aya k'asa k'asa suke Maganar yadda baza'a ji su ba,
bayan ta gama fad'i mata ta kalli Fatuu tace "na fahimci dalilin ki Zarah haka Allah ya k'addara amman
dae da kin bashi dama kin ji abunda zai ce wllh tunda mutumin nan kin fi kowa sanin halin shi bai kamata
ki k'i saurarar shi ba koda ace babu auran yayi maki haka na tabbatar zai yi abunda ya dace ya samar
maku mafita bazai ta6a bari ki wulakanta ba nasan k'arshe ma cewa zai ya aure ki kuma ai mu abunda
muke so kenan" shiru kawae Fatuu tay ita kanta yanzu dana sani kawae take ta rasa ya akai ta kasa yi ma
Ya Haisam uzuri amman tasan Saboda son da take mashi ne shi kuma sai taga kaman ya fara sha'awarta
ne can taji muryar Aunty Mareeya tana fad'in "ni wllh dana san da Maganar bazan bari a zubar ba, ni in
nice ma wllh bazan yi tunanin zubar dashi ba yaushe ma ai ko shi yace a zubar bazan yarda ba adai nemi
mafita kawae" hannu Fauzy tasa ta gumtse Dariya ta kai hannu ta bugi shoulder d'in ta tace "to uwar
gulma ai don kar a akaita laifi biyu na fad'i hakan" cire hannun Fauzy tay tana ta dariya Fatuu ma saida ta
d'an yi, Sai bayan Magrib duk suka tafi har da Fauzy tace nan zata kwana gwaggo tace a'a taje gida ta
huta tunda ta wuni, a daren Abinci saidae gwaggo ta ba wasu don yayi yawa sosae,

Misalin karfe tara na daren Fatuu na kwance jikinta sanye da english wears riga da skirt bayan tayi
wanka ta saka su gwaggo kuma na kishingid'e kan kujera ta kunna Radio d'in wayarta tana saurara aka
kwankwasa kopar d'akin gwaggo tace a shigo kopan a bud'e take, da sallama ya shigo bayan ya turo
kopar tana ganin shi ta yunk'ura ta tashi zaune tana murmushi ta hau yi mashi sannu da zuwa, shima
yayi wanka ya canza kaya zuwa jeans da t-shirt hannuwan shi ruk'e da manyan ledoji ya nufi daga can
wurin drawer ya aje ya juyo yana gaishe da gwaggo ta amsa tare da mik'ewa tace ya zauna ita kuma ta
koma gefen gadon ta zauna shiru ta biyo baya Fatuu dae tayi zuru can ya d'ago a nutse yace ma gwaggo
yanzu Abbas zai zo zasu koma gida da sauri ta tari numfashin shi tace "a'a baza'a yi Haka ba yau dae ni
zan kwana ka koma gida kai baccin ka zurga zurgar da ake ma ta isa tasa a gaji ai" d'an shiru yay yana
kallon gabanshi shi bai iya gardama ba can ya d'ago yace mata ba wani abu ai zai kwana da sauri ta sake
cewa "yau dae da wani abu gaskiya d'ana Haisam" har saida yay d'an guntun murmushi tace ya kira
Abbas d'in yace basai ya zo ba kar yay wahalar zuwa ya furta Ok sai kuma ta mik'e ta nufi hanyar fita,
bayan ta bud'e kopar ta fita suka rage su biyu d'akin yay tsit Fatuu dae na kwance lamo can ta d'an d'aga
ido ta saci kallon shi yana zaune idon shi na kallon gaban shi tana ta kallon shi can taga yana niyyar
juyowa da sauri ta maido idonta, gaban ta ne ya fara fad'uwa Jim k'amshin shi ya fara cika mata hanci
alamar kamar yana tunkaro ta har dai taji k'amshin ya gama cika ta gaba d'aya hakan yasa ta d'aga ido da
sauri ta ganshi tsaye a bakin gadon hannuwan shi zube a cikin Aljihunan jeans d'in shi gabanta ne ya hau
fad'uwa suka k'ura ma juna ido ta fara d'an motsa baki ganin irin kallon da yake mata a dabarbarce tace
mashi ina wuni shiru bai amsa ba hakan yasa ta sauke idanun ta k'asa cikin mutuwar jiki, saida ya mula
yasha iska sannan taji yace ya jikinta ba tare data d'ago ba ta amsa mashi da Sauk'i taji ya k'ara cewa ko
akwae abunda take buk'ata da turanci ta girgiza mashi kai alamar a'a still bata d'ago ta kalle shi ba,

"So this is d result of being stubborn" taji ya fad'a ba shiri ta d'ago suka had'a ido ya d'aure fuska kai
kace bashi yay Maganar ba, idanun ta ne suka ciko da k'walla kan kace mi suka fara zubowa shar cikin
raunanniyar murya ta furta "kayi hakuri" shiru bai ce komae ba idon shi akan ta itama kallon shi take
k'wallan na cigaba da zubowa can kawai sai ya juya ya nufi hanyar fita ta bi bayan shi da kallo yana
ficewa ta kife fuskar ta a jikin pillow ta saki kuka mai cin rai, sai bayan wani lokaci taji shigowar gwaggo
hakan yasa tay saurin shanye kukan ta gyara kwanciyar ta ta yadda taba gwaggon baya, ledojin da ya
kawo ta shiga bud'awa su Fruit ne da uban nama harda su shawarma da ice cream har saida gwaggo ta
d'an girgiza kai ta d'auki shawarma guda da ice cream ta nufi gadon, a gefe ta zauna ta kira sunan Fatun
shiru bata amsa ba har saida ta k'ara sannan ta amsa k'asa k'asa tace ta tashi ga shawarma da ice cream
tasan zata ji dad'in su ba tare data juyo ba tace mata ta k'oshi gwaggon tace "to ai in aka bar su lalacewa
zasu yi" daga yadda take tace mata ai akwae fridge ko sai a saka bazasu yi komae ba, shiru gwaggon tay
tana kallon ta kaman mai nazarin wani abu can ta kira sunanta ta amsa tace ta tashi zaune har saida
gabanta ya fad'i bata da yadda zatayi dole ta yunk'ura ta tashi kan ta a k'asa,

"Kuka kike yi ne?" Gwaggo ta tambaya da sauri ta girgiza mata kai tana k'ara d'ukar da kanta, d'an
jimm gwaggon tay kafin tace "miya faru ne ko kina jin wani ciwo ne?" Nan ma kai ta girgiza,

"in baki fad'a man damuwar ki ba wa zaki fad'a mawa ko kin fi son ki 6oye abu har wani ciwon ya kama
ki?" jin yadda tay Maganar a tausashe yasa ta d'ago ta kalleta idanunta cike da k'walla cikin karyayyar
Murya tace "Ya Haisam ne ke fushi kan abunda ya faru" d'an guntun murmushi gwaggon tay tace "to ba
dole yay fushi ba ko ke baki ga laifin da kika aikata mashi ba, ba d'azun nan naji kina fad'a ma Fauziyya
saida yay ta kiran ki harda sak'o ya tura maki amman kika k'i saurarar shi sai ke yanzu kike son ya saurare
ki kome?" Shiru bata ce komae ba k'walla na zubo mata gwaggo taci gaba "ni kaina da naji hakan in fad'a
maki gaskiya ban ji dad'i ba wllh nayi zaton zaki amfani da hankali kafin ki yanke hukunci" cikin muryar
kuka tace "Gwaggo ni ban sani bane nayi zaton hakanan hakan ya faru shiyasa naji tsoron abunda zai
biyo baya gashi Makaranta har an fara gulman ciwon da nike ina tsoron abun ya fito in samu matsala ga
kuma ke da kuma zumuncin dake tsakanin ku da Hajiya da kuma surutan mutane in aka sani shiyasa na
k'i saurarar shi don nasan yana iya cewa in bar shi" 6ata rai gwaggo tay sosae tace "wato kin fi tsoron
wad'annan abubuwan akan Mahalliccin ki? Ko baki san girman laifin zubar da ciki ba?" d'an yarfa hannu
tay "na sani gwaggo naga cikin k'arami ne sosae kuma bada son raina na same shi ba sannan in na barshi
zan fuskanci matsaloli da yawa shiyasa naga gara in zubar" d'an ta6e baki gwaggo tay "baki tunanin
matsalolin shi kuma zubar da cikin ba? Baki tunanin har ranki zaki iya rasawa ba?" shiru tay ta sadda kai
gwaggo taci gaba "nayi mamakin duk irin yardar dake tsakanina dake har kika iya 6oye man wannan
babban Al'amarin ashe zaki iya cutar dani har haka Fatuu??" A rud'e ta fara girgiza mata kai k'walla na
zuba ta kai hannu ta kamo hannunta guda tace "a'a gwaggota don Allah kar kice haka wllh tallahi kin ji
na rantse bada son raina nayi hakan ba saboda gudun matsalolin da zasu biyo baya ne kuma wllh ke na fi
ji ma Saboda ni bansan ya aure ni ba nayi tunanin in kika ji zaki shiga mawuyacin hali ne Saboda kina
yawan gargadi na da bani misali da yar wajen aikin ki gashi naga kuma shi an yarda dashi an amince
mashi hakan yasa naji tsoro don nayi tunanin zuciyar ki ma zata iya bugawa wllh wannan ne dalili
amman Allah ne shaida ta ban ta6a yunkurin aikata abu makamancin wannan ba, wllh gwaggo ko saurayi
bani dashi duk da ana yawan nuna ana so na amman ban saurarar su balle ta kai ni ga aikata wani abu ba
daidai ba shi kan shi koda muka je can G.r.a d'in raina bai so in shiga ba kawae don na yarda dashi nasan
bazai cutar dani ba yasa na bi shi" yar ajiyar zuciya gwaggon ta sauke tace "amman miyasa tunda abun
ya faru baki sanar da ni ba in har akwae yarda a tsakanin mu, washe garin ranar har d'akin ki nazo da
safe kika nuna man kan ki na ciwo miyasa baki fad'i man ba sai kika za6i ki 6oye man k'arshe ma kika
gudu Makaranta wannan abun ya ta6a ni Sosae bazan 6oye maki ba yasa na fara tunanin zaki iya cuta ta"
idanunta ne suka ciko hakan ya k'ara tada hankalin Fatuu ta k'ara k'ank'ame hannunta dake cikin nata a
rud'e tace "a'a gwaggota kar ki wannan tunanin a kai na don Allah wllh bansan taya zan fad'i maki abu
irin wannan ba ina tsoron wata matsala ta biyo baya ne banson in rasa ki kaman yadda na rasa
Mahaifiyata ke nike gani madad'in ta ban son rasa ki gwaggota ganin Al'amarin na da girma, ki yarda
dani Don Allah wllh ban taba munafuntar ki ba kinji na rantse" sosae take kuka itama gwaggon har
kwallan sun fara zubo mata can ta sa hannu ta fara goge ma Fatun k'wallan ta tace "shikenan ya isa kar
kija ma kan ki wani ciwon amman daga yanzu kar ki k'ara 6oye man koma miye da ya shafe ki zan
fahimce ki tunda ai ni musulma ce na yarda da k'addara mai kyau da kuma mara kyau komi ya faru da
bawa dama can an riga da an rubuta tuni alkalumma sun bushe ko wata matsala gare ki kar Kiji komae ki
fad'a man in inada iko sai in maki maganin ta in kuma ban iyawa sai in taya ki rok'on mai kowa da komae
tunda shi yace mu rok'e shi zai amsa mana wannan shine amfanin Mahaifiya daga inda ta gane kana
6oye mata abubuwa kana rushe yardar da ke tsakanin ku ne" da sauri Fatuu ta jinjina mata kai tace "in
sha Allahu bazan k'ara 6oye maki komai ba mahaifiyata" hannu gwaggon ta bud'e mata tana murmushi
ta fad'a jikinta ta rungume ta sosae wata irin natsuwa zukatan su suka samu sun d'an d'auki lokaci a haka
kafin gwaggo ta d'agota tana fad'in tasan halinta yanzu ta kama yin bacci Fatun tay murmushi, warware
mata shawarmar tay tace "ki saki jikin ki kici tunda dae shi ba sanin baki cin zai yi ba nasan kawae yana
maki hakan ne don ki gane kin yi mashi ba daidai ba amman nasan zai fahimce ki sai kuma muga abunda
Allah zai yi dangane da Al'amarin auran na ku" shiru Fatun tay ta mik'a mata shawarmar ta amsa ta fara
ci a hankali, tana cikin ci tace ma gwaggo itafa in ba wata shawarmar su ci tare tace akwae zata ci, matsa
mata tay saida ta d'aukko harda youghort ta k'aro ma Fatun, suna cikin ci Fatun ta tambaye ta yadda
akai Ya Haisam d'in ya aureta tana murmushi ta fara bata labari tiryan tiryan har ta gama, sosae Fatuu ta
jinjina abun a ranta wato ashe ma taimakon ta yay ita dama abun ya matuk'ar d'aure mata kai data ji wai
ya aureta gashi yanzu abunda ya k'ara bata mamaki irin kud'in da ya biya matsayin sadaki nan take taji
bata ji dad'i ba data 6ata mashi rai saidae ta wani bangaren kan ta ne ya kulle kan tunanin dalilin da ya
sa bai sake tan ba kamar yadda aka tsara har abu yazo ya shiga tsakanin su, kamar gwaggo tasan abunda
ke ranta taji tace "nayi zaton bayan auren zai sake ki to amman sai bai yi hakan ba k'arshe har Abbas na
tuntu6a don yay mashi Magana Saboda kar kici gaba da karatu ga auren da baki sani ba akan ki amman
sai ya nuna a k'yale shi kawae tunda ai yasan da hakan aka tsara k'arshe ma sai ya nuna shi dama yafi
son auran ya d'ore to farko dae ni gaskiya ban so ko don Saboda Matar shi ganin amincin dake tsakani to
amman kuma daga baya sai nay tunanin in hakan Allah ya k'addaro ba yadda za'ai" kallon Fatuu tay da
ke taunar abu a hankali tana saurarar ta wani murmushi tay tace mata "Ke ma kina son auren ya d'ore
ne??" Waro ido Fatun tay ta dakata da taunar abun bakin ta batay tunanin zata mata wannan tambayar
ba, ganin yadda ta kafeta da ido alamar jiran amsar ta yasa ta girgiza kai a hankali alamar a'a, wata
dariya taga gwaggon tayi har saida ta tsargu ta bita da ido can ta furta Allah ya za6a abunda yafi zama
Alkhairi daga haka ba wanda ya k'ara cewa komae suka cigaba da cin abubuwan da Suke ci har fruit da
naman gwaggo ta k'ara d'ebo masu saida suka ci suka k'oshi sauran ta saka acikin Fridge dake a d'akin,
bayan sun gama Fatuu taje tayo brush lokacin data fito har gwaggo ta gyara mata gadon ta maida brush
d'in ta haye gado ta kwanta gwaggo ma saida ta wanko bakin bayan ta fito ta d'aukko bargo ta rufa ma
Fatun kafin itama ta fiddo wani bedsheet ta nufi kujera tana fad'in tunda harda fruit suka sha tasan zai
taimaka wurin saurin narkar da abunda suka ci tunda ba'a son da an ci Abinci a kwanta gashi bacci take ji
ta haye kujerar bayan tayi Addu'oi ta tottofe a 6angarorin d'akin ta kwanta, lamo Fatuu tay tana tunanin
masoyinta ta ayyana tunda take dashi ba abunda ke shiga tsakanin su face Alkhairi amman bata ta6a
tunanin zai amince ya aureta ba don kawae ya taimaketa wani kalan son shi taji ya ratsa zuciyar ta har
saida ta lumshe ido Slowly ta furta "Am so sorry for my mistake Ya Haisam and my beloved husband
also" wani irin murmushin dad'i ta saki nan ta fara tariyo abunda ya faru tsakanin su a G.r.a tun farko da
suka fad'a saman gadon da lokacin da tay mashi magana taji shiru bai ce komai ba ta kai hannu ya nutse
cikin sumar shi mai taushi ga santsi wani irin dad'in ta6awa ne da ita, a hankali ta gangaro kan lokacin da
ta bud'e baki don sake yi mashi magana bata samu damar k'arasawa ba ya had'e lips d'in su wannan
karon kankame jikinta tay tunowa da yadda ya rink'a bata hot and deep French kisses the way she felt at
dat moment was like her breathing would cease, haka tay ta tunano abubuwan da suka faru wani
lokacin tay murmushi wani ta tsuke fuska wani ta kankame jiki a haka har bata san lokacin da bacci yay
awon gaba da ita ba...........

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2056*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

........Washe gari lahadi tun wurin karfe 8:30 Tk ya kawo masu Breakfast daga gidan Hajiya haka wurin 9
ma sai ga Fauzy itama ta kawo masu tace ma Fatun zata je ta dawo Aunty ta aiketa Kasuwa, da har
gwaggo ta kira Amadu kan ya had'o masu abun karin kumallo ganin sun kakkawo yasa ta kira shi tace ya
barshi, wurin karfe 12 na rana saiga Haulat harda innar su sunzo gaida Fatun take ce mata ita bata san
tana Asibiti ba sai da k'anwar ta taje siyayya shagon Kawu Amadu yake fad'a mata, cike da nuna damuwa
ta tambayi Fatun wai miyake damunta da har ya kaita ga kwanciya Asibiti tana rungume da Babyn Haulat
d'in da ta k'ara girma Tubarkallah ta bata labarin sanadin ciwon, sosae ita ma Haulat ta girgiza da jin
zancen Aurenta da Ya Haisam tace Allah kenan mai yin yadda yaso a kuma lokacin da ya so cike da
farinciki duk da bata ji dad'in rasa cikin ba tace "K'awata kinga abun Allah ko gashi har kin ci ribar hakurin
da ki kai, muna ta ganin kaman shi ba rabon ki bane ashe da rabon a kusa ma" ta k'arasa tana murmushi
shiru Fatuu tay da damuwa akan face d'in ta Haulat da ta lura da hakan tace "ko baki farinciki ne Allah ya
cika maki burin ki, ko kuwa Saboda rasa cikin ne, kiyi hak'uri duk rashin sani ne ya jawo haka Allah ya
k'addara hakan sai ya faru" yar ajiyar zuciya Fatun tay a sanyaye tace "haka ne Haulat na sani kawae dae
ina ganin auren ba zai d'ore ba tunda ga dalilin yin shi" da sauri tace "in sha Allahu zai d'ore mutu ka
raba keda ya Haisam bi'iznillahi ki kwantar da hankalin ki ni ina ganin hakan hikima ce ta Ubangiji dama
ya kaddaro shine mijin ki shiyasa komae ya faru, baki ga da akai auran ba duk da ga yadda aka tsara
amman kuma sai bai sake ki d'in ba k'arshe ma ga abu har ya shiga tsakanin ku harda rabo ni na tabbatar
auran nan zai d'ore ke yama d'ore kawae" ta k'arasa tana yar dariyar farinciki still da yanayin damuwa
Fatuu tace "amman fa Haulat Ya Haisam d'in Fushi yake dani kan wannan abun daya faru yana ganin nayi
mashi taurin kai Saboda nak'i in saurare shi naje na zubar da cikin" itama yanayin fuskar ta ne ya sauya
ta kai hannu ta kamo hannun Fatun guda tace "kinga wannan ma kadae ya isa yasa ki gane ya Haisam ba
don ya sake ki ba ya aure ki in ma farko da wannan niyyar ne to daga baya ya canza ra'ayi tunda gashi
har bai ji dad'in zubewar cikin ba wanda da yana da niyyar rabuwa dake ai shi dad'i zai ji koma da kan shi
yasa a zubar Saboda kar abun da ya shiga tsakanin ku ya bayyana, nasan shi mutum ne mai fahimta
sosae zai fahimci dalilin ki yay maki uzuri tunda ai sun san ke baki san da auren ba kuma Saboda ku duka
kika aikata hakan, don haka ki kwantar da hankalin ki ba abunda zai faru kawae yana fushin ne don ya
nuna maki kin mashi laifi kuma ki gane bai ji dad'i ba ko don Saboda gaba, keda ma kike yar gidan shi
dama ko kin 6ata mashi rai da kin bashi hakuri yake hak'ura ki tuna fa tun farkon sanin shi kafin ku saba
ma babbar asara kikae mashi harta kud'in shanu goma kuma kina sane kika aikata mashi amman kina
zuwa kika bashi hakuri ya hak'ura balle kuma yanzu da kuka zama abu d'aya ya kuma san abunda kika yi
kuskure ne sakamakon rashin sani da Kin san komae baza ki aikata hakan ba kuma yanzu da ya baki
dama zaki gyara laifin ta hanyar biyan shi abunda ya rasa ba kamar na shanu ba" ta k'arasa tana dariya
itama Fatun yar dariyar tayi ba kamar da ta tuno mata da can baya, kwantar mata da hankali taci gaba
da yi har saida taga ta washe bayan sallar Azahar suka tafi, wurin k'arfe ukku Fauzy ta dawo harda
Abincin rana ta kawo masu Gwaggo tay ta godiya tana fad'in ba'a gajiya da d'awainiya Fauzy na
murmushi tace ai an zama d'aya gwaggon tace hakane tay Addu'ar Allah ya bar zumunci, Fauzy da kanta
ta zuba ma Fatun ta kai mata saman gado tana ci suna yar fira nan take fad'i mata zancen zuwan Haulat
ta nuna bata ji dad'i ba da basu had'u ba amman in suka koma gida zata je ta k'ara ganin Baby d'in su,
bayan ta gama cin Abincin Fauzy ta d'aukko mata drugs d'in ta tare da bottle water ta sha, gab da la'asar
sai ga su Feenah sun k'ara zuwa yau ma harda Abinci, da Abbas ne zai kawo amman Abdul ya sa rigimar
sai anzo aikuwa tunda suka zo ya haye gadon suka kankame juna shida Fatun daga baya Abbas ya shigo
ya gaishe da ita tana ta murmushi ta amsa har yana fad'in "Alhamdulillah da alamu Amaryar mu da wuri
zata warware ta biya mu abunda muka rasa" murmushi Fauzy da Feenah sukai ita dai d'an sadda kai
kawai tay tana d'an murmushi ya tambayi ta ci Abinci tasha magungunan ta Fauzy tace eh, sai bayan
la'asar suka tafi da daddare bayan isha Haisam yazo yau ma kaman jiya da manyan ledoji yana sanye da
k'ananun kaya yana shigowa Fauzy da har lokacin tana nan don tace yau a nan zata kwana ta mik'e daga
kan kujera da suke zaune tare da gwaggo taje ta amshi ledojin tana mashi sannu da Zuwa ya d'aga mata
kai ya juya suka gaisa da gwaggo ganin tana niyyar mik'ewa don ta bashi wuri yasa shi ce mata ta zauna
zai wuce ne tace to ta koma Fauzy ma bayan ta aje ta dawo kusa da gwaggon ta zauna, slowly ya nufi
gadon Fatuu na zaune jikinta sanye da doguwar rigar Atamfa ta jingina da bango kanta sanye da hula ta
kallabin rigar tayi wani fayau da ita ta k'ara haske sosae saidae ta rame ba kamar Fuskarta har idanunta
sun fad'a, a gefen gadon ya tsaya tunda ya shigo ta sadda kai k'asa saida taji tsayawar shi a wurin ta d'an
d'ago suka had'a ido ta gaishe da shi jinjina mata kai yay slowly ya tambayi jikinta ta bashi amsa da
Sauk'i, shiru yay idon shi akanta itama shi take kallo tana yi tana d'an maida idon k'asa tana sake
d'agowa da su duk ta kame kan ta can ya d'an ta6e baki ya juya ya nufi hanyar fita su gwaggo su kai
mashi saida safe ya amsa, tunda ya tafi tay zugudum Fauzy ta taso ta zo gefen gadon ta zauna ganin
yanayin Fatun ta tambaye ta har yanzu fushin yake cikin raunanniyar murya tace mata eh Fauzyn tace "ki
daina damuwa k'ilan ma fa ba wani fushin da yake tunda irin su dama gane masu yana da wuya kawai
k'ila yana canza maki fuska ne don ki gane kin mashi laifi" shiru kawai tay amma ita ai ta karance shi
sosae tana gane yanayin shi, yau ma dai kaman jiya suka sha shagalin su da abubuwan da ya kawo
gwaggo ta zubo masu itama ta zuba ta koma kan kujera da Fatuu tak'i ta ci Fauzy ta tursasa mata harda
yin k'asa k'asa da murya tace "ki saki jiki ki ci ki k'oshi ta hakane zaki samu sauk'i sosae cikin d'an lokaci
ko Kya yi sauri ki biya shi abunda kika sa ya rasa ya daina fushin in ma shi yake yi" wani kallo mai kaman
harara tay mata Fauzyn ta sa dariya tana d'an gumtse baki daga baya Fatun ta fara ci suna cikin ci cikin
rad'a Fauzy tace "akwae wata mai magunguna da Aunty ke siye jiya dana koma muke Maganar da ita
tace yakamata a amsar maki su don suna da mugun kyau wllh tunda ita tana amfani dasu ta shaida
ingancin su, haka tace su maza ta haka ake kama su Aunty harda cewa wai ba kamar irin wad'annan
miskilan mazan an fi kama su ta nan wai har zaucewa suke kaita mamaki kaman basu ba kinsan mijinta
shima miskili ne duk da bai kai Ya Haisam ba" cikin rashin fahimta Fatuu da tayi sototo tace mata wai
wane irin magunguna ne Fauzy tay mata wani kallo tasa hannu ta ruk'e ha6a tace "yanzu nan wai ke baki
gane inda aka dosa ba sai kace wata yar primary magungunan mata fa ake nufi wanda mata ke sha don
gyara jikin su Saboda su kama mazajen su badai wai baki san su ba?" Shiru Fatuu tay kaman mai tunani
can tace mata ta san su taga ana tallan su a Tv kuma da suna secondary school lokacin da suka kusa
gamawa wad'anda zasuyi aure da sun gama suna zuwa da su suyi ta sha harma su samma su har da wani
mai kaman chocolate da kwakwa a ciki tana son shi yana da dad'i don Haulat har badawa tay aka siyo
mata da yawa suna sha, da sauri Fauzy tace "Chocolate gumba kenan akwae ma ta kwakwa da dabino
d'an banzan dad'i ne da ita wllh duk ni ke sace ta Aunty Mareeya tay ta fad'a harma ta gaji yanzu in aka
kawo mata sai ta d'ibar man a yar roba ta bani tace in na satar mata nata wuta bal bal" gaba d'aya suka
sa dariya Fauzy ta k'ara cewa "kinsan akwae su fa da yawa wasu gari ne da Madara ake sha wasu da
Zuma wasu na ruwa ne ke harda itatuwan tsarki tarkace ne sosae ake had'o ma mutum, kuma fa wai
kinsan kaman gumbar nan da kika ce kina son ta tana da dad'i wai fa haka suke ji mazan in ku kai
Meeting" waro ido Fatuu tay don ta gane meeting d'in da take nufi Fauzy tasa hannu ta gumtse dariya
Fatun ta girgiza kai a hankali tace "Allah ya shirye ki Fauzy nidai ba ruwana" da sauri tace "ke kau keda
ruwa wllh don ba k'aramin gyara zaki sha ba Aunty tace duk sai an sauke mashi miskilancin da Matarshi
ta kasa sauke mashi wai sai an sa duk inda ya zauna sai ya ambaci sunan ki nace mata Aunty kaman wani
zautacce tace ai haka zai koma a kan ki" gaba d'aya suka saka dariya har saida suka ja hankalin gwaggo
dake cin abu tana saurarar radio ta juyo ta kalle su Fauzy data lura ta wutsiyar ido ta zaro ido had'i da
rufe baki da ido tay ma Fatuu nuni da gwaggo itama ta gumtse dariyar, suna haka Amadu ya shigo dama
gwaggo ta kira shi don ya kawo mata abun shimfid'a ta kwanta k'asa ita kuma Fauzy sai ta kwanta kan
kujerar da fara'a ya shigo ya nufi gwaggo ya kai mata kayan suka gaisa ya juya ya nufi gadon ya tsaya a
bakin gadon yana fad'in "kuce kuna nan kuna shagalin ku wannan to jinya kuke ko party" duk dariya su
kai Fauzy ta gaishe dashi ya amsa Fatuu ma haka ya tambayi jikinta tace mashi ta samu sauki yace ai
gashi nan kam ya gani suka k'ara sa dariya Fauzy tay mashi bismilla yace suci gaba da shagalin su ya juya
ya koma wurin gwaggo ya tambaye ta yaushe za'a sallame su ne yaga ai ta samu sauk'i sosae tace to
suna dae jiran Dr har yanzu bai ce komae game da sallamar, da zai tafi ta k'ulle mashi sauran abubuwan
da suka rage tace in yaje sai yaci ya amsa yay godiya sukai sallama ya tafi, Washe gari wurin k'arfe tara
da yan mintuna Dr ya shigo lokacin Fauzy ta tafi tuni Saboda zata makaranta Fatuu tayi wanka tana
zaune gefen gado tana yin Breakfast da Tk ya kawo masu bayan sun gaisa da gwaggo dake zaune kan
kujera tana shan tea yay mata ya mai jiki ta amsa ya nufi Fatuu ya tsaya bakin gadon itama ta gaishe shi
da murmushi ya amsa yay mata ya jiki tace ta samu sauk'i yace Alhamdulillah haka ake so ya tambayi
tana cin Abinci sosae ko tace mashi eh, jinjina kai yay daga nan ya shiga yi mata wasu tambayoyin tana
bashi amsa daga baya yace bari ya duba bp d'inta ta maida kayan breakfast d'in kan drawer ya fara
gwada ta harda idon ta ya bud'e ya duba bayan ya gama yace zata iya cigaba da yin Breakfast d'inta tace
to, juyowa yay ya dawo wurin gwaggo yace mata yana ganin tunda komae lpy lou za'a sallame su yanzu
sai taci gaba da shan magungunan ta a gida tana murmushi ta amsa da to had'i da yin godiya ya juya ya
tafi, bayan ya koma Office ya kira Haisam ya fad'i mashi za'ai discharge d'in su yace mashi gashi nan
zuwa yana kan hanya, bayan ya iso Office d'in Dr ya nufa yana sanye da jallabiya bayan sun gama
tattaunawa ya fito ya nufi Amenity, kwankwasa kopar yay aka bashi izinin shiga sannan ya tura da yar
sallama gwaggo da har ta fara packing kayan su ta juyo tana kallon shi da murmushi ta amsa sallamar tay
mashi sannu da zuwa bayan ya gaishe da ita ya fad'i mata Dr ya sallame su tace to Alhamdulillah Allah ya
k'ara mata lafiya ya kyauta gaba a hankali ya amsa da Amin kafin ya tambayi ko akwae kayan da za'a fitar
tace eh ga wasu nan ta juya ta d'aukko mashi jakar kayan Fatuu da Basket ya amsa yana shirin juyawa
Fatuu tace mashi ina kwana ya dakata ya kai idon shi kan ta bai amsa ba slowly yace mata ya jiki ta amsa
sannan ya juya tabi bayan shi da kallo, bayan ya fita gwaggo ma ta d'auki su bargo da wani basket d'in
tabi bayan shi, bayan an kai komae Mota Fatuu ta saukko daga saman gadon ta yafa gyalenta suka tafi
bayan sun fito saida gwaggo ta lek'a d'akunan dake kusa da nasu tay masu sallama da Addu'ar samun
lafiya sannan suka wuce, lokacin da suka isa Motar Haisam d'in bai ciki gwaggo ta bud'e mata gaba ta
shiga itama ta bud'e kopar baya ta shige basu dad'e da shiga ba sai gashi ya fito hannun shi ruk'e da
ledar magunguna da Dr ya sake rubutawa bayan ya iso ya bud'e driver seat ya zauna ya rufe kopar a
gefen shi ya aje ledar ya tashi Motar suka tafi, tunda suka taho idon Fatuu na gefe tana kallon hanya har
suka iso Amadu dake cikin shago yana ganin Motar ta parker da sauri ya bud'e ya fito ya nufo Motar
yana washe baki shi ya bud'e ma Fatuu kopar ta fito lokacin itama gwaggo ta fito yana ta washe baki
alamar yaji dad'i yace ma gwaggo ashe yau za'a sallame su tace eh suma basu sani ba saida safen nan da
likita yazo, kallon Fatuu dake tsaye yay yayi mata sannu ta d'aga kai ya juya ya nufi Haisam da ya fito
yana kokarin bud'e boot ya gaishe dashi, tare suka fiddo kayan ciki Amadu ya d'auki wasu ya nufi gida
Haisam d'in na niyyar d'auka gwaggo tace mashi don Allah ya barshi za'a kwashe hakan yasa ya dakata,
godiya ta shiga yi mashi had'i da Addu'oi a hankali yake amsawa ta d'auki wasu kayan ta juya Fatuu dake
tsaye ta bita suka nufi gidan tana tafiya a hankali har ta kusa shiga ta juyo ta kalle shi suka had'a ido har
lokacin yana tsaye a bakin boot d'in jiki a sanyaye ta juya ta shige, suna shiga gidan tsaf da gani ma da
safen nan an share shi anyi Mopping dama Amadu baida ganda ya iya komai na cikin gida, d'aki Fatuu ta
nufa gwaggo tace ta shiga parlor bari ta canza mata zanin gado tace to, bayan ta d'aukko wankakke a
d'akinta ta shiga ta canza mata sannan Fatun ta koma d'akin tana shiga ta nufi gado ta hau ta kwanta,
bayan gwaggo ta koma d'akinta ta kira Hajiya a waya ta sanar mata an sallamo su tay mata barka tace sai
ta shigo tare da tambayar jikin Fatun suna gama wayar gwaggo ta cire kayan jikinta ta fito don yin wanka
dama ita bata yi ba a Asibitin sosae taji dad'in sallamo sun da akai don komi dad'in wuri naka yafi ba
kamar kuma wuri irin Asibiti da sam baida dad'in zama sai dole, tana kwance lamo can ta tuna da bata
fad'i ma Fauzy an sallamo su ba kuma tasan yanzu an isa yin break hakan yasa ta kai hannu ta d'aukko
wayarta dake a gabanta ta kira ta, sosae taji dad'in jin an sallame su tace in aka tashi tana nan zuwa
sukai sallama, bayan ta gama wayar ta aje shiru tay tana tunanin Mijinta ta rasa gane mashi yanzu ada in
tayi mashi abu ba daidai ba da ta bashi hak'uri yake hak'ura amman yanzu ta lura kaman bai hak'ura ba
koda ta bashi hakurin gashi kuma ita a ganinta in ma tana da laifi ai shima yana da shi miyasa tun da
abun ya faru bai sanar mata shi mijinta bane koda lokacin da suka je Asibiti ne bayan an gama dubata da
suka dawo Mota ya shigo baya yana bata hak'uri har yana fadin zai gyara laifin shi ai tun lokacin ya
kamata ya sanar mata, sannan ko da bai K'asar da ya turo mata kud'i har ya kirata daga baya da bata
d'auka ba ai ko message ba sai ya turo mata ba yayi mata bayani haka tay ta raya abubuwa a ranta har
bacci ya kwasheta, gwaggo na fitowa daga wankan ta sa yar doguwar rigar shan iska ta haye gado don
tana da bashin bacci aikuwa nan da nan ya kwasheta, ba ita ta farka ba sai wurin sha biyu ta fito don
d'aura girki ta lek'a d'akin Fatuu da har lokacin bacci take sakin labulan tay tana niyyar shiga kitchen ta
jiyo wayarta na ringing ta koma d'aki ganin Hajiya ce yasa ta d'aga da sauri bayan ta gaishe da ita tace
mata ba sai sun yi Abinci ba gashi nan Saude nayi ta kira d'azun ba'a d'aga ba tasan bai wuce bacci suke
gwaggon tace eh wllh tay mata godiya bayan sun gama wayar sosae ta ji dad'in hakan a ranta dama
baccin bai ishe ta ba ta koma ta kwanta cikin ranta tana jinjina kirki irin nasu shiyasa sam bata ji dad'in
Al'amarin nan da ya faru ba don gaba d'ayan su sun shiga tashin hankali ba kamar Hajiya data sha kuka,
Bayan sallar Azahar Saude ta kawo Abincin lokacin Fatuu ta farka saida ta shiga d'akin tay mata ya jiki
sannan ta tafi gwaggo ta zubo ma Fatuu Abincin da aka kawo wanda lafiyayyar sakwara ce miyar egusi
da tasha ganyen ugu ga ganda da kuma nama sai farfesun yan ciki wanda hanta tafi yawa a ciki sai uban
k'amshi ke tashi ta kai mata d'aki itama Abincin ya burgeta tun bata ci ba, saida ta wanko bakin ta
sannan ta fara ci, bayan gwaggo ta zuba ma Amadu ta mik'a mashi itama ta zuba ta koma d'akin Fatun ta
zauna kan Carpet tana ci suna d'an yin fira da Fatun dake zaune a bakin gado tana cin Abincin, wurin
la'asar Fauzy tazo harda Abinci ta kawo masu bayan ta shiga sun gaisa da gwaggo ta aje mata basket d'in
tana ta mata godiya ita kuma tana murmushi tana cewa ba komai ta fito ta nufi d'akin Fatuu lokacin tana
kwance tayi wanka ta canza kaya zuwa doguwar rigar material itama Fauzy ita ce a jikinta tayi rolling veil
tana rataye da side bag suna had'a ido suka sakar ma juna murmushi ta nufi gadon Fatuu ma ta tashi
zaune, hayewa gadon Fauzy tay ta yadda suke facing juna tace "sannu Amaryar mu ya k'arfin jiki?" Yar
harararta Fatuu tay Fauzyn tana dariya tace "ai dai ba k'arya nayi ba ko kuma wasa da gaske amaryar ce
ke, kinsan kuwa a Makaranta dana fad'a cewa ke matar aure ce akaita mamaki" Fatun tace miyasa ta
fad'a tace "to ai kinga dama anata gulma gashi yau baki je ba sai tambayata ake wai badai jikin naki bane
yay tsanani shine nace masu miscarriage ki kai dama ke matar aure ce mijin naki ne ba zaune yake a
K'asar ba yana dai zuwa, aikuwa kinga yadda akaita mamaki kuma wllh nan da nan suka yarda har wasu
na cewa wai shiyasa wani lokacin kike zama hostel wani lokacin kuma kiyi day nace masu eh har na
bud'e pictute d'in ki wanda kikae tare dashi na nuna masu wasu suka ce sun ta6a gani ya kawo ki wasu
kuma ya zo d'aukar ki Zainab Muhammadu ma cewa tay tabbas ta ta6a ganin shi har sukai ta yaba
kyawun shi ita da su Sa'adatu nan fa ta hau shela harda hawa saman Desk tana fad'in to masu gulmar
Fatima Ard'o na da ciki tabbas tana da shi kuma na halal ne don da auren ta kuma gashi nan sun ja
sakamakon gulmar da suke cikin ya zube sai Allah ya saka mata bak'in k'azafin da akai tay mata, sosae ta
bani dariya wllh" d'an murmushi Fatuu tay ta d'an ta6e baki tace "Auran dake lilo" da sauri Fauzy tace
"in sha Allahu ba wani lilon da yake komai zai daidaita mu sha biki...." Katseta Fatuu tay "har yanzu fa
Fauzy fushi yake" Fauzy tace "zai yi ya gama ne amman ni na tabbatar ya riga ya gama shigowa hannu
tunda abunnan ya faru kin ma tuna man ga sak'o Aunty Mareeya ta bani in kawo maki" tana kai Maganar
tasa hannu ta ciro side bag d'inta ta bud'e wata kullin bak'ar leda ta fiddo bayan ta bud'e ta ciro wata yar
kwalba madaidaiciya ta mik'a ma Fatun ta amsa ta fara karanta sunan maganin da bayanin yadda ake
amfani dashi ba Arzik'i tasa hannu ta rufe baki Fauzy ta kyalkyace da dariya tace "Wllh nima sunan
maganin ya ban dariya lokacin da zata bani sak'on fa hana ni tay in duba aikuwa ina hawa Napep na
bud'e nima saida na rufe baki nace Ya Haisam ya bani ana shirya mashi makaman da zasu tarwatsa
miskilancin shi" yar dariya Fatuu tay tare da d'an girgiza kai Fauzy ta shiga fiddo sauran tana mata bayani
wani da Madara zata sha wani da nama haka tay ta mata bayani ita dae tayi zuru saida ta gama sannan
tace "Dama sana'ar kika fara yi kinga yadda kike bayani sai kace kece mai maganin" Fauzy ta kyalkyace
da dariya Fatun ta k'ara cewa "kema yakamata Fauzy ki manta da abunda ya faru ki fara saurarar samari
ko Kya samu miji kema kiyi auranki, lokaci tafiya yake muna k'ara shekaru gashi mutuwa ake yakamata
muyi auren ko don mu samu masu yi mana Addu'a" idanun Fauzy ne suka ciko da k'walla cikin
raunanniyar murya tace "Wllh Zarah na kasa mantawa da Mujaheed duk da irin abunda yay man ba
kuma wai ace in ya dawo gare ni zan iya auran shi ba wllh tllh ko da ace misali dole sai shi zan aura to
saidai in mutu ban auren ba, kawae zuciyata ce sam bata man Adalci data kasa cire man shi a rai",
Fatuu tace "matsalar daga wurin ki ne Fauzy kin k'i ba wani namiji dama da zaki daure ki ba wani da
yake son ki dama a hankali zaki ga kin fara cire shi a ran ki, ki daure Pls" ta kai hannu ta kama hannunta
guda, d'an murmushin yak'e Fauzy tay tace "zan jaraba in sha Allahu duk da a yanzu ba wani da zan ba
damar amman k'ilan ko da bikin ki kinsan ance a bikin wata wata ke samun miji" ta k'arasa tana d'an
murmushi haka Fatun ma tace "wai wane biki abunda an riga da an d'aura tuni" da sauri tace "aikuwa
dole in komae ya daidaita mu sha shagali sai kace wani auren mak'iya za'a yi shi lami dole musha anko
mu cashe bikin d'an Senator guda" dan ta6e baki Fatun tay can tace "Don Kawu Amadu bai had'u ba
dana had'a ku" yar harara Fauzy ta wurga mata "Kawu Amadun ne zaki ce bai had'u ba santalelen
saurayi dashi ga tsawo gashi fari ga kyau daidai gwargwado" dariya Fatuu tay tace "ai ba wannan
had'uwar nike nufi ba ta kud'i nike nufi shi baida kud'i ke kuma na fi son ki auri wanda Mujaheed zai
girgiza in yaji" d'an murmushi Fauzyn tay "Allah ya za6a mana abunda yafi zama Alkhairi a gare mu"
Fatuu ta amsa da Amin suka cigaba da hira har Fauzy na ce mata ta tashi ta 6oye magungunan kada
gwaggo ta shigo ta gani tace to tana k'ok'arin sauka daga gadon.

Tun bayan da Haisam ya maido su G.r.a ya wuce don yin wani aiki a computer sai da akai Azahar sannan
ya dawo gidan Hajiya ya kwanta bacci, saida aka fara kiran sallar la'asar sannan ya tashi yay wanka ya
shirya ya wuce Masallaci, bayan ya fito daga Masallacin parlon Hajiya ya wuce lokacin da ya shiga ba
kowa ya nufi ciki ya zauna kan 2 seater ya d'auki remote yana canza channel, bai dad'e da zama ba
Hajiya ta fito jikinta sanye da doguwar riga da mayafinta hannunta ruke da sandar ta haka idanunta na
saye cikin medical glasses d'inta hango shi da tay yasa ta nufi cikin parlon don da gidan su Fatuu ta fito
zata, tana zuwa cikin parlon ya d'aga ido yana bin ta da kallo har ta zauna a kan one seater d'in dake
gefen shi itama kallon shi take bayan ta zauna tace "ashe ka tashi" kai ya d'aga mata,

"ai tun d'azu nike dakon ka bansan ma ka dawo gidan ba saida Saude ta dawo daga gidan su Fateema

nike tambayarta ko taga Motar ka a parking space tace man eh" shiru kaman bazai ce komae ba sai
kuma yace "ba sai ki kira ba" d'an ta6e baki tay tace ai na kira ka sau biyu ko, farko landline na kira ba'a
d'aga ba na kira wayar ka itama baka d'aga ba nan nagane bacci kake" yana ta kallonta har ta gama
sannan ya d'an d'age gira yace "Wani abu?" tace "kaci Abinci ne?" Kai ya girgiza mata alamar a'a, "to sai
kai zaune da yunwa baka iya shiga kaman magana" tay Maganar tana d'an hararar shi d'an guntun
murmushi yay "ban jin shi sosae ne" tace "uhmm kai dai ka sani wa zai zauna yay ta fama da kai kan
abunda amfanin kan ka ne alhali kai ba damuwa kai da halin da mutum zai shiga ba ya mutu ko yay rai ba
abunda ya dame ka" d'an murmushi yay kawae ya fahimci kan zancen ciki daya zo yay mata take
Magana da alama dae abun yay mata zafi,
"Am all ears da wani abu ne?" Fuska a kwa6e tace ya ci Abinci tukun ta juya tana k'wala ma Saude kira
bayan ta fito ta bata umarnin kawo mashi Abincin, akan c-table ta d'aura tray d'in kayan Abincin tana
kokarin yin serving nashi ya d'aga mata hannu alamar ta bashshi ta mik'e tace aci lafiya ya jinjina mata
kai, a nutse ya fara cin Abincin yana yi yana kallon channel d'in daya kamo Hajiya ma idonta na akan Tv
d'in tana kallon American film d'in da ake yi tana yi tana d'age kai had'i da yamutsa fuska wani lokacin
har hannu take d'an d'agawa in anyi abun tashin hankali, bai d'auki lokaci mai tsawo ba ya gama ya yago
tissue yana goge baki, kallon Hajiya yay bayan ya gama yace mata "am done" ta maido idonta kan shi
saida ta gyara zama ta fara magana "dama game da Fateema ne tunda an sallamo ta ina son in ji miye
matsayin ta tunda bai yuwuwa a barta tay ta zama da aure a kanta ba kamar yanzu da tasan da shi"
shiru yay yana kallon gaban shi har saida tace mashi kar ya 6ata mata lokaci ya bud'e baki yay mata
magana don fita take son yi, sigh yay ba tare da ya kalleta ba yace "I will divorce her" wani kallo Hajiya ta
bishi da shi jin bata ce komae ba yasa ya juya ya kalleta ganin kallon da take mashi yace "dama haka aka
tsara ai ba Abbas ya fad'a maki ba?" a k'ufule tace "eh ya fad'a man hakan aka tsara amman bai ce acikin
tsarin anyi da kai zaka rabata da budurcin ta ba" yana jin haka ya juyar da fuskar shi daga barin kallon ta
taci gaba "Yanzu kai irin Adalcin ka kenan? Sai da ka raba yarinya da pride d'inta sannan zaka ce ka
saketa wato k'aramar bazawara kake son mayar da ita kenan, idan k'anwar ka ce zaka so ai mata haka?"
Shiru bai ce komai ba bai kuma kalleta ba a fad'ace tace "ba tambayar ka nike ba Haisam! idan Jidderh ce
Fateema zaka so ai mata haka?" Sai lokacin ya d'an juyo slowly ya furta "am sorry for dat" daga haka yay
shiru itama bata k'ara cewa komae ba sai da aka d'an d'auki lokaci sannan ta dasa fad'in "ko kusa ban
amince wai kace zaka saketa ba yanzu ta riga ta zama Matar ka dole kaci gaba da zama da ita don haka
yanzu dole ta baro gidan su akawo ta part d'in ka nan zata cigaba da zama kafin muga abunda Allah zai yi
sai kasan yadda in ka koma zaka sanar ma Matar ka ni kuma daga baya zan kira iyayenka su zo harda ita
ta Lagos din sai in sanar masu su kuma ganta ko don Saboda halin rayuwa bai kamata ace duk basu san
da Maganar ba auren ba" shiru yay can ya kalleta yace "is dat all?" Kai ta d'aga mashi ganin yana
K'ok'arin mik'ewa yasa da alamun mamaki tace "au tashi za kai bazaka ce komae ba?" Dakatawa yay
yace "So What do you want me to say ba kin tsara komae ba kiyi yadda yay maki" wannan karon bud'e
baki tay galala tana kallon shi ganin hakan yasa shi d'an d'age gira "ba haka ya yi maki ba so just go
ahead do as u wish" ta6e baki tay tana mashi wani kallo tace "to yalla6ai shikenan" mik'ewa yay ya nufi
hanyar barin parlon walking majestically Hajiya ta saki baki tana bin bayan shi da kallo har ya fuce,
hannu ta kai ta ruk'e ha6a a fili tace "tabbas Yau na shaida Miskili yafi mahaukaci ban haushi kaji fa
yaron nan don Allah wai ni zai ma duniyanci, in da farko ya aure ta don ya taimaketa wannan na yarda
don zai iya yin hakan amman na tabbatar yana son zama da Fateema shiyasa bai saketa ba kamar yadda
suka tsara" ta kai Maganar tana ta6e baki had'i da yin k'wafa tana niyyar mik'ewa Saude ta kawo mata
wayarta data baro d'aki tace anata kira ta amsa ta duba mai kiran kafin ta d'aga suka hau yin wayar, sun
d'auki lokaci suna wayar kafin sukai sallama ganin yamma tayi sosae yasa ta yanke barin zuwa gidan su
Fatun sai da daddare.............
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2057*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

............. Bayan gama sallar Magrib Hajiya ta nufi gidan su Fatuu lokacin da ta zo daidai shagon Amadu ta
d'an d'aga Murya tace "Ahmad ya kasuwa" jin haka yasa ya kallo wajen yana ganinta da yake akwae
wuta da sauri ya fito lokacin har ta karya kwanar shiga suka had'e da fara'a ya gaishe da ita ta amsa ta
k'ara ce mashi ya kasuwa yace Alhamdulillah, ganin yana k'ok'arin bin ta su shiga gidan tace ya koma
wurin sana'ar shi ta gode yay mata a fito lafiya ya juya, tana shiga cikin gidan tay sallama jin ba'a amsa
ba yasa ta k'arasa wurin kopar parlon ta k'ara yin wata sallamar da d'an d'aga murya lokacin gwaggo
dake cikin d'aki ta ji ta amsa, tana lek'owa ganin mai yin sallamar yasa ta k'arasa fitowa da sauri ta
nufeta jikinta sanye da hijab tun bayan da ta gama sallar Magrib bata Mik'e ba zaune take tana yin tasbih
ta jiyo sallamar, sannu da zuwa tay mata ta gaishe da ita tana d'an murmushi Hajiyar ta amsa ta nufi
cikin parlon tun ma kafin gwaggon tace mata ta shiga, bayan ta shige tabi bayanta daga d'an can gefen
kujerar da Hajiya ta zauna itama ta zauna tana k'ara gaishe da ita bayan ta amsa tace "Barka an dawo"
gwaggo tace "Yauwa eh wllh",

"to Allah ya kyauta gaba ya k'ara mata lafiya, ai kun auna Arziki da Allah ya tashi k'afadun ta ba tare da
wata matsala ba" yadda tay Maganar fuskar ta a d'an d'aure cike da girmamawa Gwaggo ta hau bata
hak'uri tace ai hak'uri ya zama dole tunda aikin gama ya riga da ya gama wanda aka cuta an cuce shi"
d'an murmushi kawae gwaggon tay Hajiyar tace "Ya jikin Fateemar?" tace mata da Sauk'i bari a kira ta
tana d'akinta,
"In tana bacci ne ki rabu da ita",

tace "ban tunanin shi take yi kawae dai tana kwance ne tun bayan da muka dawo sai da dalili take
fitowa" tana k'arasawa ta mik'e ta nufi hanyar fita Hajiya na fad'in ai dole tay ta kwanciya wannan uban
jini da ta kwararar, lokacin da ta d'aga labulan a kwance ta same ta idanunta a rufe tana sanye da
doguwar rigar bacci kanta sanye da hula, nufar ta gwaggo tay ta tsaya a bakin gadon ta kira sunanta jin
shiru bata amsa ba yasa ta gane bacci take ta sunkuya ta kai hannu ta d'an bubbuga shoulder d'inta, a
hankali ta bud'e idanun suka sauka akan gwaggo tace mata "Sannu ya k'arfin jikin?" hannu ta kai tana
muttsike idanun tace mata da Sauk'i gwaggon tace "ba abunda ke maki ciwo?" Kai ta d'aga kafin tace
"kawae jikin ne ba k'wari" kai ta jinjina "Wannan dama sai a hankali, ga Hajiya nan tazo ganin ki ki taso"
amsa mata tay da to ta fara kokarin saukkowa, a tare suka tafi gwaggon na gaba tana biye da ita suka
nufi parlon, bayan gwaggo ta shige da yar sallama itama ta shiga idon Hajiya a kanta ta mik'a hannu tana
ce mata tazo ta zauna kusa da ita da yake a saman 2 seater take zaune, a gefenta Fatun ta zauna a
hankali ta gaishe da ita ta amsa kafin ta kai hannu ta dafa Shoulder d'inta tana tambayar ta ya jikin tace
mata ta samu sauk'i sosae,

"To Ya jinin yana zuba sosae ne?" ta tambaya sunkuyar da kai Fatuu tay tace "a'a kad'an ne kaman zai
d'auke" jinjina kai tay tace "ai kin zubar da jini dole yay saurin d'aukewa" shiru Fatun bata ce komae ba
Still kanta na k'asa, "Yanzu akwae abunda ke damun ki a jikin?" d'an girgiza kai tay tace "a'a kawae k'arfi
ne babu sosae" tace "Wannan sai a hankali zai dawo kina dae cin Abinci sosae ko?" Kai ta d'aga mata
alamar eh tace yayi kyau kafin ta sake tambayar tana shan suma magungunan da aka bata tace mata eh,
shiru ta d'anyi kafin ta dasa "Fateema ina son tambayar ki kuma gaskiya nike son ki fito ki fad'a man kin ji
ko?" d'agowa tay ta kalleta ta d'aga mata kai alamar to,

"Ina son inji shin zaki cigaba da zama da Yayan ki matsayin mijin ki ko kuwa baki so in raba ku?"
Dammm! gaban Fatuu yay wani irin bugu ta kasa d'agowa balle tace wani abu ganin haka yasa Hajiya
cewa ba shiru zata yi ba ta bud'e baki tay Magana a hankali ta saci kallon gwaggo suka had'a ido tana
ganin haka ta juyar da fuskar ta daga barin kallon Fatun ta koma kallon gefe Hajiya tace "ki daina kallon
ta ba abunda zata ce maki tunda ai ba ita zata zauna da shi ba dole kece zaki yanke kar Kiji wani abu ki
fad'i man ra'ayin ki kan hakan" wani abu Fatuu ta had'iya ta rasa ma wace amsa zata bata duk ta rud'e
kanta a k'asa sai zare ido take tana motsa hannuwan ta da bakin ta, da d'an d'aga Murya Hajiya tace
mata dare nayi tayi magana d'agowa tay duk ta dabarbarce murya na rawa tace ".....Duk abunda...kuka
za6a man yayi man" d'an murmushi Hajiya tay tace "To Fateema in muka za6a maki abunda bai maki ba
fa tunda mu ba sanin abunda ranki zai fi so mukai ba kuma dae baso muke mu takura maki ba shiyasa
aka baki dama ki fad'i abunda ranki ke so, kinga mu bamu zamu zauna da shi ba don haka kar Kiji komae
ki fad'i kina son cigaba da zama dashi matsayin miji ko kuwa a raba ku" k'ara kallon gwaggo tay taga bata
kallonta ta maida idon k'asa abu biyu ne suka hanata magana na farko kunya na biyu kuma tana
kokonton amincewa ba kamar yanayin da take gani tattare da Haisam d'in,
"Shikenan tunda baza kiyi Magana ba bari in tashi in tafi, ni dae bazan yanke hukunci ba yazo kuma bai
maki dad'i ba tunda ai harda irin hakan tasa aka fasa wanccan auren ko an za6a maki wanda baki so duk
da harda k'arin halin shi" ganin tana k'ok'arin mik'ewa yasa gwaggo ta canza harshe tay ma Fatun
Magana da d'an d'aga murya tace bazata bud'e baki tay magana ba, tana yamutsa fuska kaman zata saka
kuka itama ta juya harshen tace mata tana so amman kunya take ji ta fad'i mata hakan, Hajiya da ta fasa
mik'ewa ta kya6e baki tana bin su da ido har suka gama sannan tace "wato matsalar ka zauna cikin
wad'anda ke yin yaren da baka iya ba kenan har gulmar ka sai ayi a kuma zage ka tass ba tare da ka sani
ba k'arshe ma har kai ta washe baki kana tunanin abun kirki ake fad'a kaiga sakarai" murmushi kawae
gwaggon tay Hajiya dake kallonta tace to mi suka ce a fad'i mata gwaggo tay mata bayani, wata irin
kunya ce ta lullu6e Fatuu kan ta a sadde, d'an murmushi Hajiya tay tace "ina ruwan Fateema to miye
abun jin kunya mutumin da dama Mijin ki ne kawae amsa zaki bada, shikenan Allah Ubangiji ya shige
mana a Al'amarin tashi kije Allah yay maki Albarka ya k'ara maki lafiya damu baki d'aya, a hankali ta
amsa da Amin ta mik'e ta nufi hanyar fita sumi sumi har lokacin bata d'ago fuskar ta ba, Bayan fitar ta
Hajiya ta kalli gwaggo tace "Sai ku fara shiri ran Juma'a in Allah ya kaimu zata tare a d'akin mijinta nan
part d'in shi" rasss kirjin gwaggo yay bata yi tunanin haka da wuri ba a d'an rud'e tace "to..Amman Hajiya
bai yi wuri ba kuwa har a shirya ta tare a ranar?" Hajiya dake kallon ta ta cikin glasses tace "to Dije wane
irin shiri ne za'ai da har nan da Juma'a bai isa a gama ba?" Cikin yar inda inda tace "dama wai Saboda
kayan d'aki tunda wanccan wanda suka yi su sun fanshe su yanzu dole sai nayi ma Mahaifin nata Magana
sai a siya wasu koda anan ne sai kuma sauran dae abubuwa" tana Maganar tare da yin nuni da
hannuwan ta har ta k'arasa Hajiya da ta ta6e baki tana saurarar ta tace "To wane kayan d'aki kuma, ina
ce a part d'in nashi akwae su kuma ba abunda sukai yanzu in an siya mata wasun su wanccan ya za'ai da
su, ki bar zancen wasu kayan d'aki tay amfani da wanda ke akwae acan abunda ma nasan zaman na d'an
lokaci ne Saboda karatun ta data gama ai dole ta bi shi inda yake zaune tunda ba yadda za'ai tay zaune
nan mijin ta na wata uwa duniya, kuma ko bayan ta taren kina iya ganin ma ya canza mata wasu kayan
d'akin tunda wanda ke akwae yanzun ma ai daga can K'asar wajen ya siyo su don haka ki bar zancen su
kiyi sauran yan shirye shirye da ba'a rasa ba suma kada kice zaki wani takura kan ki tunda an riga an
d'aura ba wani abu da ake buk'ata kawae ki sanar ma makwabta da Abokan Arzik'i don a shaida auren
tunda abun surutu bai ma Mutane wuya kuma ma dai wani surutun dole ayi tunda yanzu tazo ta samu
ciki kuma tazo daga baya ta haihu duk mutane basu san da auren ba ai kinga dole ayi surutu ko, in da
wata matsala kiyi magana ina sauraren ki" godiya gwaggon tay mata daga baya tace "akwai kayan
kitchen da ya siya mata na waccan auren suna nan ajiye ban san ko za'a iya kai mata ba tayi amfani
dasu" tace "Eh to bai kamata aita ajiye su ba, bari muga tunda akwae d'ayan d'akin da yake aikin
injiniyan cin nashi kuma an kwashe komae tunda yanzu ba'a nan yake ba sai abunda ba'a rasa ba inaga
sai a jera mata kayan a cikin shi ya zama kaman kitchen dama kuma zagaye yake da table sai a k'ara
gyarawa yadda zai yi Sosae, shikenan ko in kuma da wani abun sai ki fad'a don nafi son mu gama
Maganar da ta danganci tarewar yanzu" d'an shiru gwaggo tay akwae abunda ke damunta a rai saidae ta
rasa ta yadda zata yi mata Maganar Hajiya ta lura hakan yasa tace mata tayi magana inda wani abu ta
kalleta cikin yar in ina tace "d...dama wai naga su can sauran dangin nashi da Matar shi basu san da
Maganar auren ba shi ne nace...to ba matsala ta taren?" Hannu Hajiya tasa ta ruk'e ha6a "Oni Dije kin fi
ni sanin abunda ya dace ne ko kuwa tsoro kike in sun sani za'a cinye maki Fateemar?" da sauri gwaggo ta
girgiza kai alamar a'a ta hau bata hak'ura Hajiya ta dasa fad'in "ki bita da Addu'a kawae in sha Allahu
komae zai zo da Sauk'i tunda shi ya k'addaro komae nasan hakan duk cikin hikimar sane shiyasa nima na
d'auki Al'amarin da Sauk'i" kai gwaggo ta jinjina tay Addu'a tare da k'ara yi mata godiya daga haka ta fara
k'ok'arin mik'ewa gwaggo ma ta tashi don tay mata rakiya,

Fatuu na komawa d'aki ta nufi gadonta ta haye can k'arshe ta zauna had'i da jingina bayanta a jikin
bango sai zare ido take tama rasa shin murna ya kamata tayi ko mi, canjin da take gani a wurin Haisam
duk shi ya Sagar mata da gwuiwa har take jin shakku game da zaman su tare gani take kaman shi bazai
so hakan ba saboda in don laifin da ta yi ne ai ta bashi hak'uri, gani take da yana son ta ko yana son
cigaba da zama da ita ai da ya hak'uri ya sake mata, tana haka Gwaggo ta shigo bayan ta dawo daga raka
Hajiya, gadon ta nufa ta zauna a baki idonta a kan Fatuu da itama ta k'walalo ido tana kallon ta can tay
yar ajiyar zuciya ta fara Magana "Sai ki fara shiri ranar Juma'a in Allah ya kaimu zaki koma gidan Hajiya
can part d'in Yayan naki" dadamm! k'irjin Fatuu yay wata irin Fad'uwa ta zaro ido kaman zasu Fad'o a
razane take kallon gwaggo jin abunda ta fad'a wanda kwata kwata bata zaci jin hakan ba, ko da ta
amince ba tay tunanin da wurwuri haka ba, jin bata ce komae ba yasa gwaggo cewa bata ji abunda tace
bane ta d'an yamutsa fuska kaman zatai kuka tace "Gwaggo da wuri haka kuma ya za'ai hakan bacin ba
wanda ya sani a dangin shi ko ita fa Aunty Fanan bata sani ba" da alamun damuwa akan fuskar gwaggo
tace "to nima nayi ma Hajiya Maganar hakan amman tace ayi Addu'a kawae Allah ya shige mana gaba"
idanun ta ne suka ciko da k'walla ita tasan hakan ba k'aramar matsala za'a iya samu ba can suka fara
zubowa sharr gwaggo dake kallonta tace mata ai ba kuka yakamata tayi ba suyi Addu'a kaman yadda
Hajiyan tace komai sai aga yazo da Sauk'i cikin kuka tace "amman gwaggo ni ina tsoron kada azo a samu
matsala fa in daga baya suka sani suka ce basu yarda bafa basu son auren tunda kinga Aunty Fanan
yar'uwar su ce" shiru gwaggo tay ta sauke idanun ta k'asa ita kanta abunda yafi damunta kenan a cikin
rai can ta d'ago tace "Addu'ar dae kawai zamuyi tunda ba abunda yafi k'arfin ta, koda nayi mata magana
kan hakan nuna wa tay ban fi ta sanin abunda ya dace ba kin ga ai bazan yi jayayya da ita ba ko" shiru
Fatuu tay tana goge kwallan dake zubo mata ana haka Amadu ya d'aga labulan d'akin ganin gwaggo yasa
shi shigowa yana fad'in ashe tana nan yaje d'aki bai sameta ba hannun shi ruk'e da k'atuwar leda ya nufo
su a bakin gadon ya aje ledar yace gashi nan in ji Ya Haisam yana gaida mai jiki kai gwaggo ta d'aga, ganin
yanayin fuskar ta yasa shi tambayar ta lafiya ya juya kan Fatuu dake ta goge k'walla ba shiri ya kai zaune
yana tambayar gwaggo jikin nata ne ta girgiza mashi kai alamar a'a,

"To miya ke faruwa ne naga kunyi jugum jugum ga damuwa akan fuskokin ku ita harda kuka don Allah
ku fad'a man?" Shima har yanayin fuskar ta shi ya sauya yar ajiyar zuciya gwaggo ta sauke ta fad'a mashi
zancen da Hajiya tazo tayi, d'an bud'a ido yay alamar mamaki sai kuma ya washe baki yace "to shine
abunda yasa maku damuwa ku da zaku yi farinciki auren zai d'ore wanda mu hakan dama muke fata"
d'an murmushin yak'e gwaggon tay tace "ba wai ba'a farincikin bane kawae damuwar tamu game da
dangin nashi ne da basu san da zancen auren ba ita gudun ta kar daga baya kuma azo a samu matsala
suce basu amince ba" da sauri yace "ku ma cire wannan tunanin in sha Allahu ba wata matsala da za'a
samu koda ma an samu Allah zai kawota da Sauk'i don haka mu mik'a komae gare shi ayi Addu'a kaman
yadda Hajiyan tace, kuma kun manta ne gaba d'aya dangin na shi da matar ta shi duk tana da iko da su
don haka ayi yadda tace kawae" jinjina kai gwaggo tay ya juya kan Fatuu yana murmushi ya d'an kwanta
kan gadon ya kai hannu ya kamo hannun Fatuu guda yana fad'in "u should be happy Allah ya amince
Romeo ya zama naki ba kuka ba" tura mashi baki tay yasa dariya gwaggo ma murmushi ta bisu da shi,
sakin hannun Fatun yay ya koma ya zauna yana kallon gwaggo yace "to yanzu ya za'ai Maganar kayan
d'aki gashi an sa k'urarren lokaci ko da yake ai indai da kud'i har a siya ko?" Fad'i mashi yadda sukai da
Hajiyar game da hakan tay yace "shikenan ma an hutar da mu naji dad'i wllh in akwai buk'atar ayin ko
nan gaba sai ayi matan in kuma zai tafi da Ita can d'in ne bama sai an yin ba" juyawa yay kan Fatuu dake
ta bin su da ido yana dariya yace "Waya ga su yar fillo a jirgi za dai asha hauka nasan" k'ara tura mashi
baki tay ta d'an harare shi yace "ni kike harara, kifa bar ganin wai ke matar aure ce baki fi k'arfin in kikai
man ba daidai ba in zane ki ko da kin bar gidan nan ne zan iya bin ki har can gidan in maki hukunci"
gwaggo dake dariya tace "shi kuma mijin nata sai ya bika da ido kai ta dokar mai mata ko",

"Wllh yadda yake tubarkallan nan ma sha Allah yace zai rama mata ai sai ya karairaya ni nasan" ya
k'arasa yanata dariya itama gwaggon dariyar take Fatun dai sunkuyar da kai tay tana d'an murmushi
yayin da zuciyar ta ke suffanto mata surar Haisam,

"To yanzu shikenan sai dae a jira ranar akaita ko akwae abunda zaki?" Amadu ya tambaya tace "Eh zan
bada ayi mata su cin cin tunda za'a sanar da makwabta zancen Auren nasan daga baya za'a shishshiga sai
ranar Juma'a d'in ayi Abinci Saboda wanda zasu zo" kai ya jinjina "hakan yayi amman fa kar kiyi su da
yawa ayi daidai daidai, to su yan Adamawa fa za'a sanar masu ne naga kaman lokaci ya k'ure ko?" d'an
jimm tay kafin tace "zan kira Baffanta in sanar mashi komai amman zance mashi ba sai sun zo ba su bari
sai daga baya in an samu natsuwa" kai ya jinjina yace hakan yayi sai kuma yace "Yanzu shikenan haka
za'ai bikin Romeo da Juliet d'in lami ba wani d'an cashewa gaskiya yakamata a d'anyi mana ko yar dinner
ce mu shaida muna biki" gwaggo dake murmushi tace "aikuwa dai haka zaku yi hak'uri don ba wani abu
da za'ai" gyad'a kai yay "shikenan amman fa mun biyo bashi ko daga baya ne dole ayi mana in komae ya
daidaita dangin shi sun sani" ta6e baki gwaggo tay "tunda ibada ne ya zama Farilla dole sai an yi ko"
k'ok'arin mik'ewa ya fara yi yana fad'in bari ya d'aukko plates su yi shagalin abun farinciki ya nufi hanyar
fita, plate guda biyu ya d'aukko babba da k'arami ya duk'a ya bud'e ledar abubuwan daya saba kawo wa
ne a ciki ya zuzzuba a plate d'in ya mik'a ma gwaggo ta kar6a shima ya d'auki wanda ya zuba a k'aramin
plate ya mik'e idon shi akan Fatuu data takure a guri guda yace "ki saki jiki Amaryarmu dis is worth
celebrating don haka ki saki ran ki kici ki k'oshi" ya nufi hanyar fita yana fad'in dole ma ya d'inka sabuwar
shaddar kai Amarya daga haka ya fice gwaggo ta d'an girgiza kai da d'an murmushi ta juya kan Fatuu da
tay zuru tace ga abu nan taci, girgiza mata kai tay alamar a'a ganin ta damu sosae yasa ta shiga kwantar
mata da hankali tace ta saki jiki taci don jikinta na buk'atar su ko kuzarin ta ya dawo cike da tsokana tace
mata ko so take a kaita d'akin miji haka sukuku da ita Amarya da ake son ta da kuzari Fatun ta duk'ar da
kan ta gwaggon nata murmushi, daga baya ta d'ago suka fara ci tare da gwaggon lokacin take ce mata ta
kira Fauzy ta fad'a mata don su fara shirye shiryen su k'unshi da gyaran kai har tana cewa yakamata ma
in an gyara kan ai kitso ita dae Fatun shiru tay, bata wani ci sosai ba tace ta k'oshi amman gwaggo ta
matsa mata saida ta k'ara ci daga baya ta bar d'akin da sauran da suka rage, tun bayan da gwaggo ta fita
tay zaune zugudum ta rasa Mike mata dad'i ita dai har ga Allah zallumin zama part d'in nashi take ba tare
da dangin su sun san da auren ba sam hankalinta bai kwanta da hakan ba, tana haka Gwaggo ta k'ara
shigowa hannunta ruk'e da cup mai d'an girma a bakin gadon ta tsaya ta mik'a mata ta ce ta shanye
abun ciki maganin sanyi ne ba tare data ce komai ba ta amsa ta kafa baki nan da nan ta shanye shi tass
don dama ta saba bata tun kwanakin baya harda itatuwan tsarki da na sha duk ce mata take na sanyi ne,
bayan ta shanye ta mik'a mata Cup d'in ta amsa ta juya Fatun ta bita da kallo don a yanzu ta gane ko
magungunan miye take bata da sunan na sanyi, can wata zuciyar ta raya mata ko shiyasa ma lokacin da
abun ya faru Ya Haisam d'in ya rikice mata tamkar bashi ba duk da rok'on shi da ta rink'a yi amman a
banza, tuno lokacin yasa ta saki d'an murmushi tasa tafin hannunta ta rufe idanunta alamar kunya tana
haka ta tuno da magungunan da Fauzy ta kawo mata na yar kwalbar inserting d'in shi ake bayan wasu
mintuna sai a wanke da ruwan d'umi wata zuciyar ta raya mata tay amfani dashi yanzu sai kuma ta tuna
da jinin da take hakan yasa ta bari sai ya d'auke sai wanda ake ci da nama gashi yanzu ta gama cin
naman saidae ba dama ta sa a gaban gwaggo d'ayan kuma da peak milk tunanin ko taje shagon Kawu
Amadu ta amso Madarar tay amman kuma ta k'oshi sosae gashi yanzu gwaggo ta bata wani k'arshe ta
yanke gobe tayi amfani dasu kawae ta sauka don taje ta wanko hannu ta sha ruwa, tun bayan da ta
kwanta bacci ya k'aurace ma idanunta sai juye juye take tana tunanin wane irin zama za tay da Ya
Haisam matsayin miji kuma ta koma part d'in shi ganin abun take kaman wasa wllh, can kuma ta koma
tunanin ya Aunty Fanan zata ji in taji Maganar auran na su ita da yan gidansu har saida gabanta ya fad'i
tunowa da Mahaifiyar Fanan d'in wato Hajiya Maryam jikinta ne yay wani mugun sanyi don ta santa tana
da kirki amman fa jarababbiya ce ta gaske a hankali tunanin ta ya koma kan yan gidan su Haisam su
wannan bazata iya yanke hukunci a kan su ba kawai dae tasan suna da kirki sosae kuma tana Mutunci da
wasu daga cikin yan gidan kaman Nameer, Jidderh dasu twins wannan sun ma maidata tamkar yar'uwar
su haka Mahaifiyar Haisam d'in ta san ta sosae kuma duk in tazo tana zuwa ta gaishe da ita cikin sakin
fuska take amsa mata bata san in suka ji zancen auren ko zasu amince ba, damuwa ce kwance akan
fuskar ta haka taci gaba da tunane tunane har bata san lokacin da bacci ya kwashe ta ba, Washe gari da
niyyar zuwa Makaranta ta tashi ta hau shiri ba 6ata lokaci gwaggo na cikin Kitchen ta iske ta bayan ta
amsa mata gaisuwar ta ta bita da kallo ganin ta sanye da Uniform yasa tace mata ba dai Makaranta wai
zata je ba tace eh ai ta samu sauk'i, girgiza kai gwaggo tay "koda kin samu sauk'i bazaki je ba gaskiya har
sai shi Mijin naki ya baki izini tukun kar ai rashin hankali" yamutsa fuska tay kaman za tai kuka tace
"amman gwaggo ko da ai da auren nike zuwa ko har ma in zauna a can" gwaggo dake kallon ta ta d'an
d'aure fuska tace "da kika ce lokacin baki san da auren ba yanzu kuma kin sani don haka duk abunda zaki
sai da izinin shi" idanunta cike da k'walla tace "to gwaggo in kika ce sai ya bada izini har sai yaushe kenan
zan ci gaba da zuwa kina gani fa ko jiya bai shigo ba Kawu Amadu ya ba sak'o" tace "ba kina da waya ba
ki kira shi mana ki fad'i mashi" tura baki tay tana cigaba da yamutsa fuska had'i da kikkafta idanu
gwaggon ta mik'o mata abun breakfast tace taje tayi yadda sukai da shi to ta amsa ta juya, tana komawa
d'aki ta aje kayan Breakfast d'in akan Carpet ta koma bakin gado ta zauna sai k'unci take ita sam bata
son ta kira shi don bata san mi zata ce mashi ba da sunan neman wani izini shi da ko kiranta bai yi ba tun
bayan da suka dawo har yanzu sai ita ce zata kira shi, tana ta zaune cikin 6acin rai can dubara ta fad'o
mata da sauri ta kai hannu ta d'aukko jakar goyonta ta bud'e wayarta ta fiddo ta fara kiran Abbas tana
fara yin ringing ya d'auka bayan ta gaishe da shi yay mata ya jikin ta amsa daga nan tay shiru jin haka
yasa shi tambayar ta da wani abu ne murya kaman zata yi kuka ta fad'i mashi makaranta take son zuwa
amman gwaggo ta hana wai har sai Ya Haisam ya bada izini kuma tun jiya daya maido su ma ita bata
k'ara ganin shi ba tambayar ta yay har ta samu sauk'in da zata iya cigaba da zuwa School tace mashi eh
har yana cewa kodae ta bari ta k'ara warwarewa amman ta kafe kan ta samu sauk'i ko ta zauna ba
abunda take sai kwanciya kuma can ana ta wuce ta, sigh yay jin haka yace ta bashi wasu mintuna zai
sake kira tace to, bayan sun gama wayar ta saukko ta fara yin breakfast don ranta ya bata zata je
Makarantar tana cikin yi sai gashi ya sake kira bayan tayi picking yace ta zama cikin shiri ga Mijin nata
nan zai zo ya kaita ya k'arasa yana yar dariya tace ta gode, cire wayar tay ta bita da kallo jikinta ne yay
sanyi jin shi zai kaita aje wayar tay taci gaba da yin Breakfast d'in, tana gamawa ta jiyo horn d'in shi har
saida gabanta ya fad'i ta d'an yi jimm lokacin taji ya k'ara yin wani ta yunk'ura ta mik'e, gado ta nufa ta
goya jakar ta ta sa hijab dake aje saman gadon bayan tasa fararen takalman ta na makaranta ta d'auki
tray d'in kayan breakfast d'in ta fita, kitchen taje ta aje su ganin gwaggo bata ciki yasa ta fito ta nufi
d'akinta tana zaune kan carpet itama tana yin breakfast d'in ta shiga ta d'aura idonta a kanta Fatun tace
mata gashi nan yazo zata tafi gwaggon tace "to a dawo lafiya kinga ai hakan yafi da ai abu kai tsaye" bata
ce komai ba tana shirin juyawa gwaggo ta sake cewa "amman fa gida zaki dawo don zama a Makaranta
ya k'are in ma kina da kaya ki kwaso su yau kin ji ni?" Kai ta d'aga mata kawai ta juya ta fita, bayan ta fito
ta nufi d'ayan side d'in Motar ta kai hannu ta bud'e lokacin da ta shiga idonta ya sauka akan shi har saida
gaban ta ya d'an fad'i tay saurin d'auke idon ta ta rufo kopar, juyawa tay ta d'an kalle shi yana sanye da
jallabiya ta gaishe dashi ya amsa ba tare da ya kalleta ba yaja Motar suka fara tafiya ta juyar da fuskar ta
gefe wani abu taji ya tokare mata k'irji wai ita Ya Haisam ke sharewa haka idanunta ne suka ciko da
k'walla da sauri ta fara K'ok'arin maida su don bata son su zubo mata, har suka isa fuskar ta na gefe ya
parker inda ya saba aje ta tace mashi an gode ba tare da ta kalle shi ba tana niyyar juyawa don ta bud'e
kopar taji yace mata "Wait" dakatawa tay still bata kalle shi ba saida taji yace mata ta amsa sannan ta
juya ta kalli kud'in da yake mik'o mata yan dubu duba bin kud'in tay da ido kafin ta d'ago a raunane ta
kalle shi suka had'a ido da sauri ta kawar da nata ta furta "ka bar su" shiru bai tanka mata ba bai kuma
janye kud'in ba yamutsa fuska ta fara yi tana d'an kikkafta ido a K'ok'arin ta na kada tay kuka ta sake
juyawa still kallonta yake fuskar shi ba yabo ba fallasa ta sake ce mashi tana da kud'i nan ma bai tanka ba
bai kuma janye kud'in ba bata da yadda zatay ba don ta so ba tasa hannu ta kar6a wani irin bak'in ciki ne
ya turnuk'e ta ta shiga ayyana wato ita ga mayyar kud'i, ko tambayar ta ya jiki bai yi ba sai wasu kud'i zai
bata, can k'asan mak'oshi ta furta mashi ta gode tana shirin juyawa ta bud'e taji yace mata ya jikinta har
bata san lokacin data juya ta kalle shi ba kaman mai jin zancen zuci, d'auke idon tay ta ce mashi ta samu
sauk'i daga haka ta juya ta bud'e Motar ta fice, saida taji ya juya Motar ya tafi sannan ta tsaya da tafiya
ta juyo tana kallon Motar idanun ta cike da k'walla sharr suka fara zubowa tasa hannu tana gogewa kafin
ta juya ta nufi aji, tana shiga suka had'a ido da Fauzy aikuwa ta taso da gudu ta nufo ta tana fad'in Oyoyo
Bestie nah, tana zuwa ta kankame ta gaba d'aya hankalin yan ajin ya dawo kan su, sakin ta tay tana
kallonta da murmushi da alamun mamaki tace mata wai har ta warke ta d'aga mata kai, kama hannuta
tay suka nufo cikin ajin ana ta mata sannu da jiki tana amsawa, koda suka zauna akan seat d'in su haka a
kaita tasowa ana zuwa yi mata ya jiki harda Zainab Muhammadu nan ta hau ce ma Mutane wllh su zo su
nemi yafiyar ta zargin ta da sukai na tana da ciki bada aure ba aikuwa wasu sukai ta ce mata ta yafe
masu su basu san ita matar aure bace tace ta yafe suna haka malamin su ya shigo kowa ya koma seat
d'in shi, gaba d'aya damuwa tay mata yawa har ta kasa tsaida hankalin ta kan abunda ake koya masu
saidae ta sunkuyar da kai kota kai hannu ta dafe goshi ko ta d'an cije baki Fauzy duk tana lura da ita
saidae ba damar tayi mata magana, basu samu damar yin Magana ba don malamin na fita wani na
shigowa har saida akai break sannan Fauzy ta tambaye ta wai mi yake damunta ne ta lura tana cikin
damuwa nan ta kwashe zancen tarewar ta ta fad'a mata har Fauzy bata san lokacin data saka yar k'arar
murna ba cike da farinciki tace "to keda zaki farinciki ma Allah ya cika maki burin ki Aure ya d'ore Ya
Haisam ya zama naki sai kita damuwa" d'an yarfa hannu tay ta cije baki tace "Fauzy bazaki gane ba ne
ina hango gagarumar matsala a tattare da hakan dangin shi fa basu sani ba haka ma Matar shi Hajiya ce
kadae ta sani yanzu in suka zo daga baya suka ce basu amince da auren bafa?" Da sauri Fauzy tace "ni
wllh ban ganin za'a samu wata matsala, karfa ki manta gaba dayan su Hajiya na iko dasu tunda kuma ta
amince ai ta zauna na tabbatar bazata bari a raba auren ba kawae muci gaba da Addu'a" shiru kawae tay
idanunta sun cika da k'walla can suka zubo sharr da sauri Fauzy ta dafa Shoulder d'in ta ta shiga bata
hak'uri cikin kuka tace "Fauzy abunda yafi damu na Ya Haisam ya canza man yanzu da nike ganin ya
zama mallaki na, in don laifin dana yi mashi ne na bashi hak'uri duk da in zai man Adalci ai bani kadae
keda laifi ba ko, ni ina ganin gaskiya kaman gara in hak'ura da auren shi tunda na fahimci bai sona
kawae nasan zai amince ya zauna da ni ne k'ilan don Hajiya tay mashi dole kinga to wane irin zaman aure
zamu yi haka, koda nike son shi nafi son shima ace yana sona ko d'an yaya ne" yar ajiyar zuciya Fauzy ta
sauke tace "ni gaskiya ina tunanin k'ilan akwae wani dalili da ya sa ya canza maki amman ba wannan ba
kuma da dukkan alamu yana son ki shiyasa tun farko bai sake ki ba kaman yadda aka tsara, kuma in ma
fushin yake Saboda rasa cikin kinga hakan ya tabbatar da yana son kine shiyasa yake son cikin har yay
fushi da kika zubar, kuma da bai son ki gaskiya a ganina bazai amince yaci gaba da zama da ke ba tunda
shi fa namiji ba'ai mashi dole irin wannan" shiru tay kaman mai nazarin wani abu can tace "ina ganin
kaman hakurin da kika bashi bai isa ba mi zai hana ki same shi ki bashi hak'uri sosae, da kaman ki k'ara
iske shi can G.r.a d'in nike gani" d'an waro ido Fatuu tay tace "in je in k'ara bashi hak'uri kuma, gaskiya ni
bazan je ba Fauzy hakanan ya wulakanta ni ai na bashi hakurin ko" hannu Fauzy ta kai ta dafa Shoulder
d'inta tace "k'ilan abun yay mashi ciwo ne sosae, kinsan su irin su gane masu yana da wuya amman
tunda har kika ga ya nuna to tabbas bai ji dad'in abun bane kije ki same shi ki bashi hak'uri sosae ba
fad'uwa bane wllh karki manta shi Mijin ki Aljannar ki na a tafin kafar shi kuskurene ace yana fushi dake
haka indae fushin yake da gaske Saboda abunda kika aikata don haka nidai a gani na kije ki bashi hak'uri
tun kafin ranar Juma'ar tayi" shiru Fatuu tay tana juya zancen zuwa bashi hakurin a cikin ranta can wata
zuciyar ta tuno mata da lokacin data fasa mashi glass har Haulat ta bata shawarar taje ta bashi hak'uri
kuma shawarar tayi mata amfani wanda itace silar komae a tsakanin su, yin wannan tunanin yasa ta kalli
Fauzy tace "shikenan zan je d'in amman bansan lokacin da yake can ba gashi in na koma gida bansan
yadda zan ce ma Gwaggo ba har ta barni in fito" Fauzyn ta tambaye ta yana zuwa aiki ne tace mata a'a
ya bar aiki nan tunda ya bar K'asar, sake tambayar ta tay yaushe rabon data gan shi tace mata shi ya
kawo ta tace "kinga da ace can ya tafi sai kiyi sauri tunda anyi break duk da ma an kusa dawowa sai kije
ki dawo mai Napep d'in da ya kai ki sai ya jira ki ku dawo" d'an jimm Fatun tay kaman mai yin tunani can
tace bari ta gwada zuwa k'ilan can ya wuce in kuma bai can sai ta dawo ta mik'e Fauzy ma ta mik'e tace
bari ta rakata, suna fitowa waje suka samu Keke Napep Fatuu har zata shiga ta dakata takai hannu cikin
aljihun rigarta ta fiddo kud'i cikin wanda ya bata ta mik'a mata tace tay break ta shige cikin Napep d'in
Fauzy ta d'aga hannu tana mata sai ta dawo da fatan Allah yasa ta iske shi ta amsa da Amin yaja suka tafi
ita kuma ta juya...............
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2058*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.........Tunda suka taho take ta faman zullumin abunda zai biyo baya in ta iske shi, wannan karon bata
wani sha Wahalar gano gidan ba da suka iso don ta rik'e sunan Road d'in, a bakin tangamemen gate d'in
tace ma mai Napep d'in ya tsaya bayan ta fito tace zai jirata ne su koma yace to ba matsala ta juya ta
nufi k'aramar kopar a d'arare, Officer dake zaune shi kadae yana ganin ta ya hau washe baki harda
mik'ewa yana mata sannu da zuwa abun har saida ya bata mamaki a hankali ta amsa mashi ta tambaye
shi ko Ya Haisam na ciki da sauri ya d'aga mata kai yace eh yana nan tace zata gan shi ne yace mata ba
Komai ta fito lafiya ta wuce, tunda ta shiga harabar gidan gabanta ke ta fad'uwa tana tafiya tana yan
waige waige har ta isa bakin mai entrance na gidan ta turo kopar ta shige, ba kowa a cikin parlon farko ta
wuce Corridor d'in da zata kaita d'akin nashi cike da fargaba har ta iso bakin dakakkar kopar dake a rufe,
tsaye tay ta kasa kwankwasawa sai faman wasi wasi take a cikin ranta ta had'e hannawun ta tana
cakud'a su, can dae ta kai hannu yana d'an rawa ta fara knocking a hankali, kusan sau biyar ta
kwankwasa amman shiru bata ji an yi magana ba, dakatawa tay da knocking d'in tay jimm tana tunanin
ko dae bai nan wata zuciyar ta ayyana mata amman ai Officer yace yana nan kuma da ya fita bazai ce
mata haka ba ta raya to ko bacci yake yin Wannan tunanin yasa ta yanke ko dae ta tafi, har zata juya sai
kuma ta dakata tay tunanin k'ara d'an kwankwasawa k'ilan tay sa'a yay Magana, can cikin bacci yaji
knocking d'in sama sama har dai yaji shi sosae ya fara motsa idanuwan shi kafin slowly ya bud'e su dai
dai lokacin ya k'ara jin anyi knocking d'in cikin disasshiyar murya irin ta wanda ya tashi daga bacci ya
tambayi wanene shiru ba'a amsa ba saima k'ara yin knocking d'in da akai ya k'ara tambaya nan ma shiru,
tunani yay k'ilan Officer ne ko ya kira landline bai ji ba hakan yasa ya yaye lallausan duvet d'in daya rufe
rabin jikin shi da shi ya saukko da k'afafun shi kafin ya idasa mik'ewa daga shi sai farar singlet fara kal sai
short da iyakar shi rabin cinyoyin shi, saida ya zura takalman da ke a bakin gadon sannan ya nufi kopar,
ganin ta k'ara kwankwasa har sau ukku ba'a bud'e ba yasa ta hak'ura tana shirin juyawa ya bud'e kopar
da sauri ta kai idon ta kan shi suka had'a ido, wani irin bugu kirjinta yay ta d'an zaro ido tana kallon shi
shima irin kallon baka tsammaci ganin mutum ba ya bita dashi, gaba d'aya ta kame kanta ba kamar a
yadda ta ganshi hannuwan ta da ta had'e sai d'an rawa suke, sakin kopar yay ya juya ba tare da ya ce
mata komae ba, d'an jimm tay kaman bazata shiga ba sai kuma ta shiga ta maido kopar wani irin
ni'imtaccen sanyin Ac had'i da daddad'an k'amshi mai ratsa zuciya suka tarbeta har saida ta d'an lumshe
ido taja numfashi, in da kujeru suke ya nufa ya zauna kan 2 seater ta nufi can walking slowly gaba d'aya a
d'arare take, a gefen wurin ta tsaya tana kallon shi ya sa duka tafukan hannayen shi ya dafe goshi alamar
baccin bai ishe shi ba aka katse mashi, saida ya d'an d'auki lokaci sannan ya cire ba tare daya kalleta ba
da hannu yay mata nuni da kujera alamar ta zauna jiki a sa6ule ta nufi cikin wurin ta zauna akan one
seater tana facing d'in shi, gaba d'aya ta tsorata da yadda ta ganshi don bata ta6a ganin shi haka ba duk
ilahirin jikin shi inda gashi ke fitowa suma ce a kwance liya liya ga farin shi gaba d'aya ya tafi bai d'aya
skin d'in shi sumul da ita ba ko d'an ta6o ko bambancin kala harta gwuiwar shi ba bak'i ko tabo kamar
bai yi rarrafe ba da yana yaro kawae dae skin d'in wurin jan ta ya d'an fi cizawa ga suffar k'arfin shi ta
bayyana muraran gaba d'aya a murde yake, tana cikin k'are mashi kallon ya kai idon shi kanta suka had'a
ido ta fara motsa baki da k'yar ta k'ak'alo Kalmar ina kwana tace mashi kaman ba zai amsa ba sai kuma
ya amsa can k'asan makoshi ganin yana mata kallon da take ganin na fushi ne yasa ta sunkuyar da kanta
yaci gaba da kallon ta,

"Why are u here not in School?" Bayan wasu sakanni taji cool voice d'in shi ya fad'i hakan, d'ago kanta
tay ta kalle shi ta fara motsa baki tama rasa ta ina zata fara mi zata ce mashi duk ta dabarbarce ba
kaman da ya kafeta da kaifafan idanuwan shi masu k'ara mashi kwarjini gathering much courage ta fara
magana cikin yar rawar murya "d...dama zuwa nayi in baka hak'uri kan abunda ya faru....nasan nayi
maka laifi amman ni bansan komai bane shiyasa na aikata wannan kuskuren....don Allah Ya Haisam kayi
Hakuri" da k'yar ta k'arasa Saboda idon shi dake a kanta tana yi tana maida kan ta k'asa tana d'agowa,
bin ta kawae yake da ido kaman ma bashi da niyyar tanka mata duk tasha jinin jikinta sai yan kame kame
take,

"Ba zan yi hakurin ba!" Kaman saukar aradu haka taji Maganar da sauri ta tsaida idanunta akan shi ta
zaro su don bata ta6a tunanin zata ji ya fad'i haka ba, d'agowa yay daga jinginar da yayi da kujeran a
kausashe yace "da baki san komae ba banyi k'ok'arin sa ki sani ba? Tell me how many times did I call u to
explain everything amman Saboda taurin kai kika k'i picking all my calls har message na tura maki
warning u not to do anything amman Saboda abu ya faru bani da sauran girma da mutunci a wurin ki
shiyasa bazaki bi umarni na ba, ni da kika zo nan I gave u chance kin fad'i duk abunda kike so u even
shouted at me kin kira ni Azzalumi, macuci, maci Amana which I never expect to heard from u and dat's
d worst thing that ever happened to me....." Dakatawa yay yana d'an girgiza kai fuskar shi d'auke da
tsantsar 6acin rai ya d'an cije baki Fatuu ko tunda ya fara magana ta kid'ime don bata ta6a ganin irin
yanayin da yake Maganar ba tunda suke da shi sai zare ido take tana sakin numfashi da k'arfi ta had'e
hannuwan ta akan k'irji tama kasa bud'e baki tace wani abu,

"Nayi tunanin koda ace hakan ya faru ne kuma ba aure tsakanin mu zaki man uzuri, for how long muna
tare dake na ta6a maki wani abu makamancin wannan? duk wani dama da zan iya aikata maki hakan na
samu amman ban ta6a jin ina sha'awan hakan ba kaman yadda kika fad'a man wai ina son jikin ki God
forbid! ban ta6a jin hakan ga wata wadda ba halal d'ina ba, kallon da nike ma siblings d'ina shi nike maki
before aure ya shiga tsakaninmu amman kin yanke man mummunan hukunci har kin nuna guy d'in da
aka so aura maki yafi ni duk da halin shi da aka fad'a man Saboda shi bai cutar dake ba sai ni right?" rai
6ace yake Maganar yana jinjina kai da alama maganganun nata sun tsaya mashi a rai, a rud'e Fatuu ta
taso tazo daga d'an gaban shi ta duk'a tana girgiza mashi kai ya bita da ido cikin kuka tace "Don girman
Allah ya Haisam kai hak'uri nasan nayi maka ba daidai ba sharrin zuciya ne, wllh ita tasa na kasa maka
uzuri duk da nasan halin ka ta raya abubuwa ba daidai ba akan ka, kuma wllh ni ban daina ganin girman
ka ba kawae dai nak'i d'aga wayan ka ne Saboda ina tunanin zaka hana ni aiwatar da abunda nai niyya ni
kuma ina tsoron matsalolin da zasu biyo baya don bansan da aure a tsakanin mu ba shiyasa naga yin
hakan yafi kuma wllh harda k'arin don kada k'imar ka da Mutuncin ka su zube kaji na rantse maka,
amman don Allah kayi hak'uri na gane kuskurena ba zan k'ara ba" ta k'arasa fuskarta jage jage da
hawaye tana yi tana gogewa wasu na sake zubowa, shiru yay ya jingina da kujerar yana ta kallon ta ita
kuma sai motsa baki take ta marairaice fuska can yay sigh yace "is Ok,ai ke zan ba hak'uri na aure ki bada
sanin ki ba daga baya kuma na cutar dake am really for dat" da sauri tace "a'a ai ni taimako na kayi kuma
ba cutar dani kayi ba don ban sani bane nace haka kuma da na saurare ka da na san komai kayi Hakuri da
abunda nayi" ta k'arasa tana ta6e baki yadda ta saba kuka tun yarinta still idon shi na akan ta sai yan
kame kame take taji ya sake cewa "I know kinsan girman zunubin laifin da kika aikata amman kika za6i ki
aikata and kinsan had'arin da ke tattare dashi but still kika aikata kawae don gudun matsaloli, baki ji
tsoron sa6a ma Ubangiji ba?" hannu ta kai tana d'an sosa gefen wuyanta tana kikkafta ido ganin ya kafe
ta da nashi idon yasa tace "Sharrin zuciya ne, kuma har yanzu banda cikakken hankali tunda ban girma
ba sosae amman na rok'i Allah ya yafe man" bin ta kawae yay da ido ita kuma tsakani da Allah tay
Maganar ta, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yace "shikenan kawae you can go back to School nayi
hak'urin" kallo ta bi shi dashi har saida yace bata ji bane sannan ta fara k'ok'arin mik'ewa tace mashi ta
gode ta juya, har ta fita daga wurin idon shi na akan ta sannan ya maido su yana kallon gaban shi kaman
mai tunanin wani abu lokacin yaji k'arar rufe kopar ya mik'e ya nufi hanyar corridor, bada jimawa ba ya
fito sanye da jallabiya ya nufi gaban mirror ya d'auki Car key ya fice, lokacin daya fito a harabar gidan ya
hangota ta tunkari gate tana tafiya tana goge fuskarta da hannu, parking space ya nufa sai lokacin ta lura
da shi ya d'aga hannu yay mata alamar ta tsaya, bayan ya fiddo Motar ya nufo gate d'in a saitin inda take
ya tsaya ta zagaya d'ayan side d'in ta bud'e kopar gaba ta shiga, sai da suka fito sannan ta tuna da mai
Keke Napep dake ta faman jiranta sam bai ji ya gaji da jira ba don yana sa ran zai samu biya mai kyau ba
kamar da ya ga gidan da ta shiga, Haisam na ganin Napep d'in tun kafin ma tayi magana ya tambaye ta
tare suke tace mashi eh ya tsaya gefen shi ya kai hannu ya bud'e glove box ya k'irgo 5k ya bata yace ta
kai mashi tace to ta amsa ta bud'e kopar, lokacin data ba mai Keke Napep d'in washe baki yay ya shiga
yin godiya harda biyo ta bayan ta bud'e kopar ya duk'o da kai yana mashi godiya ya d'aga mashi kai
kawae bayan ta shiga yaja suka tafi,

A daidai inda ya aje ta da safe ya parker tuni an koma break ba kowa a wajen ta juya ta kalle shi idon shi
na kallon gaban shi a sanyaye ta furta ta gode ya d'aga mata kai ta juya zata bud'e kopar lokacin taji
muryar shi yace in an tashi ta jira zai zo ya d'auketa, d'an juyawa tay suka had'a ido a hankali tace mashi
to kafin ta sake juyawa ta bud'e kopar, bayan ta fita ya juya Motar ya tafi tabi bayan Motar da kallo har
ta daina ganinta sannan ta juya jiki ba kwari ta nufi class, tana zuwa bakin barandar benen da ajin su
yake kawae sai ta zauna a wurin ta jingina da pillar ta d'an d'age kanta sama kwalla suka fara gangaro
mata wani irin dana sani take yi ta rasa ya akai ta kasa yi ma Ya Haisam uzuri kaman yadda ya fad'a
yakamata ace tunda tasan halin shi bata yi mashi yadda tay mashi ba, amman tasan harda bak'in
abubuwan da taga ya fara yi mata ne yasa tay tunani na daban akan shi, tuno yadda ya rink'a yi mata
Magana da tsantsar 6acin rai ta shiga yi dama Fauzy tace k'ilan abun yay mashi ciwo sosae ashe hakane
ta fahimci bai so ta zubar da cikin ba, girgiza kai ta fara yi a fili ta shiga fad'in "am sorry my husband
nasan na aikata kuskure amman cikin rashin sani ne bazan k'ara ba..." haka tay ta sambatu k'walla na
zuba, Sa'adatu ce ta fito daga cikin class d'in su zata je toilet ta hango ta saida taje ta dawo sannan ta
nufi Fatun ta tsaya gefen ta ta kira sunanta har sau biyu sannan tay d'an firgigit ta sauke kai ta kalleta,
ganin hawaye a fuskar ta yasa tay saurin zama a gefen ta kai hannu ta dafa Shoulder d'inta tana
tambayar ta lafiya Fatun tay shiru, ta k'ara tambayar ta ko jikin nata ne sai lokacin ta d'aga mata kai
alamar eh cike da tausayawa ta hau yi mata sannu ta tambayi to ta sha magani ne ko suje ta rakata
Asibiti tace mata daga can take tace to ta taso su tafi aji amman sai tace taje kawae tafi jin dad'in zama
anan ta ce to, ta k'ara yi mata sannu tare da mik'ewa ta nufi komawa aji, da yake akwae malami cikin
class d'in hakan yasa bata fad'i ma Fauzy game da Fatun ba har saida ya fita sannan ta tashi da sauri taje
seat d'in su ta fad'i ma Fauzy aikuwa tun kafin ta gama fad'i matan ta mik'e zumbur tay hanyar fita, tana
hangota ta nufe ta da sauri, tana zuwa ta zauna gefenta hankali tashe ta kai hannu ta dafa Shoulder d'in
ta ta hau tambayar ta miya faru, tace ta iske Ya Haisam d'in kai Fatuu ta d'aga mata alamar eh, tace to ya
sukai dashi, cikin muryar kuka ta shiga fad'i mata Fauzyn nata girgiza kai itama har idanunta sun kawo
kwalla bayan ta gama fad'i mata yadda sukai dashi tace "ashe abun ya mashi ciwo ne sosae kaman yadda
kika ce Fauzy, ban ji dad'i ba da na kasa yi mashi uzuri har komai ya faru if I had known I would have
listened to him da komai bai faru ba nayi dana sani sosae" janyo ta Fauzy tay ta rungume ta ita kanta
bata ji dad'in abubuwa data fad'i ma Ya Haisam din ba wanda ta 6oye mata hak'ik'anin yadda sukai dashi
lokacin data dawo, jin tana ta kuka yasa tace "shikenan kukan nan ya isa hakanan kinga ba ki idasa
warwarewa sosae ba kada kuma wani ciwon ya kama ki, tunda yace ya hak'ura ai shikenan sai a kiyaye
gaba" d'ago kai tay ta kalleta tace "ni gani nike kaman bai hakuran ba ya dae fad'a ne kawae tunda har
yanzu yanayin da nike gani bai canza ba" Fauzyn tace "kar ki damu tunda yace ya hak'ura to ya hak'uran
kin dae san ai ba zai magana biyu ba daga baya yace bai hak'ura ba wannan ai k'aranta ne, dama burin
mu ya hak'uran naji dad'i sosae abunda kuma ya rasa in sha Allahu bada jimawa ba za'a biya shi wani"
wani kallo Fatun ta d'aga kai tay mata Fauzy tasa dariya,
"Yanzu kinga sai muji dad'in fara shirye shiryen duk da banji dad'i ba da ba wani shagali da za'ai amman
mun biyo bashi koda in kika haihu ne sai mun yi shagali sosae, yanzu yaushe kike ganin zamu je ai maki
k'unshi da gyaran kan?" d'agowa tay daga jikinta ta zauna sosae tace mata itama bata sani ba Fauzy tace
"tun yau yakamata a fara maki gyaran jiki gobe ma a k'ara sai a gyara maki gashi jibi in Allah ya kaimu sai
ayi maki k'unshi bari in aka tashi zan je gida sai in sanar ma Aunty Mareeya zuwa da la'asar sai muje
wurin gyaran jikin" kai Fatun ta d'aga mata alamar to Fauzy ta kai hannu taja kumatun ta tana fad'in ta
saki ranta Amarya da farinciki aka santa ta d'anyi murmushi kawai ta kama hannunta tace ta tashi su
koma aji suka mik'e, Bayan an tashi Hostel suka wuce ta tattara kayan ta da suke a nan kaman yadda
gwaggo ta bata umarni Fauzy nata fad'in zatai missing d'inta kad'aici zai dameta amman tana farinciki da
abun Alheri ne yasa zata bar zama hostel d'in, Fatun nata murmushi itama duk wani iri take ji tasan dole
ta damu da tafiyar ta, indomie Fauzy ta dafa masu harda kifi sardine suna cikin ci Haisam ya kirata yace
yazo ta fad'i mashi suna cin Abinci ne amman sun kusa gamawa yace ba wani abu ta gama, bayan sun
gama Fatuu tace mata to tazo ba sai a ajeta a gidan ba kawae, cike da tsokana Fauzy tace a'a wai kada ta
shiga tsakanin Masoya ta hana su sakewa inta gama kimtsawa zata tafi Fatun ta harareta ta saka dariya,
tare suka fito Fauzy ta kamo mata trolley d'inta dama iya shi kadae ne sauran abubuwa kaman
provisions wannan ta bar ma Fauzy, lokacin da suka iso inda ya parker Motar back door ta bud'e ta saka
akwatin bayan ta rufe ta bud'e kopar gaba ta shiga yana sanye da k'ananun kaya Fauzy ta lek'o ta gaishe
da shi fuska a sake ya amsa yay mata ya karatu daga baya ta k'ara yi ma Fatuu sallama tace sai ta zo
anjima ta rufo mata k'opar, saida ya ja Motar ta gaishe dashi ya amsa idon shi a kan hanya ta juyar da kai
tana kallon gefen hanya har suka iso kopar gidan su ya parker, d'an kallon shi tay tace ta gode ya jinjina
mata kai still bai kalleta ba ta juya ta bud'e kopar bayan ta fita har zata rufe sai kuma ta tuna da fitar da
zasu yi anjima da Fauzy tasan in ta fad'i ma gwaggo sai tace ta tambaye shi hakan yasa ta duk'ar da kan
ta ciki a sanyaye ta fad'i mashi sai lokacin ya juyo suka had'a ido, jinjina mata kai yay tay mashi godiya
bayan ta janye kan ta rufo mashi kopar ta bud'e back door ta fiddo trolley din, har saida ta shige gida
sannan yaja Motar, tana shiga d'akin gwaggo ta nufa ta d'aga labulan taga bata ciki ta saki ta nufi
d'akinta, tana shiga ta aje trolley d'in a bakin gado ta aje jakarta saman gadon ta cire Hijab d'in itama ta
d'aura ta saman gadon, tana juyawa zata nufi hanyar fita taji wayar ta tayi k'ara alamar shigowar
message ta koma bakin gadon bayan ta bud'e jakar ta ta fiddo wayar ta fara dubawa, alert ne na 500k
daga Haisam har saida ta d'an zaro ido dama wanccan da ya turo mata suna nan bata ta6a ko sisi ba
yanzu ga wasu sun kama 1 million kenan d'an jinjina kai tay ta ayyana in gwaggo ta dawo sai ta nuna
mata, har zata aje wayar wata zuciya ta raya mata yakamata tay mashi godiya d'an jimm tay tana yin
wasi wasi na ta kira ko kar ta kiran, can dae ta kira saidae har ta yanke bai d'aga ba jikinta ne yay sanyi
lakwas ta ji dama bata kira ba don a tunanin ta yana tare da wayar tunda yanzu ya turo mata sak'o, har
zata ajeta kan gado sai gashi ya kira tabi kiran da kallo kaman bazata d'aga ba can dae tay picking ta kara
a kunne bai tanka ba cikin yar inda inda tace taga sak'o ta gode sai lokacin ya furta Ok tay shiru can taji
ya furta "da wani matsala ne?" da sauri tace a'a ta katse kiran, bin wayar tay da kallo a ranta ta ayyana
halin Ya Haisam sai shi ta d'an ta6e baki sai kuma tay d'an murmushi ta aje wayar ta juya, d'akin Kawu
Amadu ta nufa ta iske shi yana ta bacci hakan yasa ta juyo ta koma d'akin ta, a bakin gado ta zauna ta
d'auki wayar tana kokarin kiran gwaggo, tana fara ringing ta d'aga bayan ta gaishe da ita ta tambayeta ta
dawo ne tace mata eh ta iske bata nan ko ta tafi aiki ne tace a'a taje inda zata kai aikin su dublan ne, ta
tambayi taci Abinci ko tace mata taci a Makaranta bata jin yunwa amman duk da haka saida tace mata ta
k'ara taci ta k'oshi tace to, daga baya ta sanar da ita zancen zuwa gyaran jikin da zasu yi da Fauzy a
kunyace gwaggon tace mata to amman ta kira shi ta sanar da shi har saida ta d'an yi murmushi dama
saida ranta ya bata ta fad'i mata ta tambaye shi daya kawo ta harma da kud'in daya turo da wanccan
daya fara turowa itama gwaggo saida ta jinjina yawan kud'in tace saidae ta dawo tay amfani dasu suyi
duk abunda zasu yi tace to, bayan sun gama wayar ta mik'e ta nufi kitchen ba laifi taji damuwar da take
game da yanayin Ya Haisam ta ragu,

Saida Fauzy tay wanka ta shirya sannan ta fito don tafiya gida, bayan ta isa bata iske kowa a parlor ba
yaran Aunty Mareeyar basu kaiga dawowa daga School ba don suna tsayawa extra lesson, Bedroom d'in
ta ta nufa tay knocking ta jiyo Muryar ta tana a shigo sannan ta tura kopar da sallama ta shiga, tana
kwance saman gado tayi wanka jikinta sanye da doguwar rigar Atamfa kallabin ta aje a gefe kanta yasha
kitso yar yar Tubarkallah dama akwae gashin kitson ya zubo gefe da gefen wuyanta tana ruk'e da wayar
ta, tana ganin Fauzy tace lafiya dai ko ta dawo don jiya ta tafi, a bakin gadon Fauzy ta zauna tana kallon
ta da murmushi tace mata lafiya lau, Aunty Mareeyar tace "kenan hakanan kika dawo, ko missing d'ina
kike shine kika zo ki gan ni?" Yar dariya tay tace mata eh amman harda Albishir tazo yi mata, tana jin
hakan ta aje wayar ta maido hankalin ta gaba d'aya kan Fauzy tana fad'in ta bata ta sha, cike da tsokana
Fauzy tace "Dama Daddyn su Hanif ne na gani ya kai wata Makarantar mu amman shi bai ganni ba saida
ya sauketa ya tafi naje muka gaisa nike tambayarta inda ta san shi take ce man wanda zata Aura ne har
an sa masu rana shine nace bari in zo in fad'i maki kin kusa yin k'anwa mu kuma zamu yi sabuwar
Aunt......" bata k'arasa ba Aunty Mareeya ta kai hannu ta janyo ta ta daddage ta d'uma mata dundu tana
fad'in bari ta fara ta kanta ita yar zuwa ta fad'i, wata irin gantsarewa Fauzy tay sosae taji zafin dundun
har saida ta saki k'ara tana fad'in "Aunty Mareeya so kike ki kashe ni kika buga man wannan k'aton
hannun naki tubarkallah" sakin ta tay tana dariya tace gobe ma ta k'ara fad'i mata irin wannan
mummunan labarin Fauzyn ta tashi zaune tana yamutsa fuska kaman zatai kuka har kallabinta ya cire
Aunty Mareeya dake ta dariya tace mata tana jin ta wane Albishir ne zata mata, tana tura baki tace ta
fasa fad'i mata ta fara k'ok'arin mik'ewa da sauri ta janyo ta ta fad'a saman gadon ta rungume ta tana
bata hak'uri sannan ta shiga fad'i mata zancen tarewar Fatuu, har saida Aunty Mareeya ta rangad'a
gud'a ta shiga washe baki tana fad'in Alhamdulillah an zo daidai inda take so, ta bata labarin zuwa da
tayi d'azun bashi hak'uri da yadda sukai dashi, yamutsa baki Auntyn tay tace "in ma bai hak'uran ba ta
lalama zai hak'ura ne don dole, wllh ni dama fatana auren dai ya d'ore duk wannan miskilancin sai an
sauke mashi shi sai ya rasa sukuni duk in bai ji Zarah a gefen shi ba, shiri za'ai mata na musamman ba
boka ba Malam amman fa sai ya susuce a kanta mu da muke da AUNTY BEE KAYAN MATA AND
SUPPLEMENTS ai zance kuma ya k'are, mu mata da Allah yay mu masu daraja ai duk kika ga mace bata
da k'ima da daraja a wurin mijinta wllh ita taso, macen data san kanta wllh bata zama ba tare da gyara
kan ta ba musamman da kaya masu tsananin inganci na Aunty Bee, ai ance ko kana da kyau to ka k'ara
da wanka" Fauzy da tay sototo tana sauraren ta tace "Aunty su kayan Aunty Bee d'in nada kyau sosae
kenan" hannu Aunty Mareeya tasa ta ruk'e ha6a tace "Uhmm bazaki gane ba yarinya tunda baki san
yadda karatun yake ba, amman wllh kin ji na rantse kayan ta Kat ne ingancin su ba'a magana sai mutum
yayi amfani dasu zai shaida don sha yanzu ne magani yanzu, gashi abun burgewa abubuwan mune na
gargajiya ake sarrafawa ayi magungunan sam basu da wata illa sa6anin wasu magungunan ke da kinji kin
san harda surkulle" Fauzy ta tambayeta a ina Aunty Bee d'in take tace "a Kano take nima yadda akai na
santa nan Neighbor d'ina Maman taufiq taji ina complain kan sai aita zuzuta magani amman in na siya
sai inji ba haka ba k'arshe ma na daina siya nace gwara in cigaba da shan su Fruit dasu Fresh milk shine
fa tace ai in jaraba kayan Aunty Bee d'in, farko k'iyawa nay nace kowane Magani haka ake cewa amman
ta matsa man ta bani wasu in gwada....."

Hannu tasa ta ruk'e ha6a tace "Fauziyya...." Itama Fauzyn ruk'e ha6ar tay tana gumtse dariya tace
"Aunty..." ajiyar zuciya Aunty Mareeya ta sauke tace "naga abun Al'ajabi wllh, amman mu bar Maganar
daga nan bari in kira ta in mata zancen Zarah" tana rufe baki Fauzy ta kyalkyace da dariya itama Aunty
Mareeyar dariyar take ta fara k'ok'arin kiran layin Aunty Bee kamar haka, 08144224934 wayar na fara
yin ringing Aunty Mareeya ta d'aga ma Fauzy gira tace "yanzu zata d'auka ta bala'in iya haba haba da
customer da kin kirata ko kika tura mata sak'o ta WhatsApp ba 6ata lokaci zaki ji ta d'auka saidae in wani
babban uzurin ya hanata d'agawa da wuri amman data gani ko daga baya ne zatay ma mutum
magana..." Jin Aunty Bee d'in ta d'aga kiran yasa tay shiru suka shiga gaisawa cike da mutunta juna daga
baya ta shiga yi mata bayanin K'anwarta take so a gyare mata sosae kaman yadda aka saba harda cewa
mijin miskili ne na gaske so take asa ya magantu ba tare daya shirya ba Aunty Bee d'in tay dariya irin ta
mata da suka amsa sunan su tace mata karta damu wannan ba matsala bane saidae in bata yi amfani da
magungunan ba amman tabbas zai magantu, gaba d'aya suka saka dariya Aunty Mareeya tace tana son
ta turo mata hotunan packages na magungunan zata tura ma Mamar Amaryar tace ba matsala ta duba
WhatsApp yanzu zata turo mata in sha Allahu sukai sallama, suna gama wayar ta shiga WhatsApp d'in
dama anan take Fauzy ta shigo, ba 6ata lokaci sai ga hotunan ta turo Aunty Mareeya tay ma Fauzy
alamar ta matso ta gani ta k'arasa hayewa kan gadon, baki bud'e take ganin hotunan magunguna ba
kamar package na Amaren ya burge Fauzy sosae tun ma a ido, magunguna ne sosae Aunty ta shiga fad'i
mata sunayen su, su Zakaran mak'alemata, kazar gadali, zabuwa, cicci6i, tsumi kala kala masu wanke
mara suyi maganin sanyi, gumba ma kala kala ga garirrrika wato daka akwae d'akan yar gata, k'orama,
green emergency, bata gaban kishiya , a ciji kunne....." Aunty bata k'arasa fad'in sauran ba Fauzy ta
kwashe da dariya harda tuntsirawa ta d'ago tana fad'in Aunty badai kunnan Zarah za'a cije ba da sauri
Aunty Mareeya ta kai mata bugu tana fad'in mara kunya kawae ita tana nuna mata ne don in za'a ma
k'awayen ta aure ta taimake su ta tallata masu don su gyara kansu, k'arshe sai ta fita daga cikin hotunan
Fauzy nata rok'on ta taci gaba da mata bayani tace bata yi,

"To amman Aunty kince a Kano take yanzu yaushe har aka kawo su Zarah tai amfani dasu saura fa kwana
ukku ta taren" murmushi Aunty Mareeya tay tace "ai wannan ba matsala bane Aunty Bee bata da wasa a
kasuwarta in yanzu nace duk ana son wannan kayan a gobe insha Allahu zaki ga ta turo su ke ko Lagos
kike kika ce kina son kayanta cikin kwana biyu zasu iso maki kuma abun mamakin kayanta basu lalacewa
yadda ta turo su haka zaki amshe su ba cuta ba cutarwa, kuma koda yan kud'i k'alilan zaki samu kayanta,
kai ai Allah yaba Aunty Bee gaskiya ba k'aramin taimakon mata take ba shiyasa a koda yaushe Allah ke
k'ara ma kasuwarta Albarka wllh" Fauzy tace "to yanzu tura ma Zarah za'ai ta gani in mata bayani?" Yar
harara Aunty ta wurga mata "wata Zarah can, kenan ita zata gyara kanta sai kace mara gata gwaggon
zaki kira man in mata bayani kina da no d'inta?" tace mata ba'a rasawa ta ciro wayarta a cikin jaka ta fara
dubawa cikin sa'a akwae lambar tace ta kirata, tana fara ringing ta d'auka Aunty ta amsa cikin
girmamawa ta gaishe da ita tay mata Allah yasa alheri Fauzy ta fad'i mata zancen tarewar Zarah, daga
baya ta shiga yi mata bayanin magungunan sosae gwaggo taji dad'i tay ta godiya tana shi Albarka tace
duk kud'in da ake buk'ata tay ma Fatun Magana zata turo sai a kawo tace to, daga baya sukai sallama
suna gama wayar gwaggo ta kira Fatuu tace mata Auntyn Fauziyya zata kira inta fad'i mata kud'i ta tura
mata tace to, ba tare da 6ata lokaci ba bayan ta kira Fatuu ta tura mata kud'in ita kuma nan take ta tura
account d'in Aunty Bee daga baya ta kirata tace ta tura mata receipt ta duba, bayan ta gani ta tabbatar
mata gobe in Allah ya kaimu wurin k'arfe 10 na safe magungunan zasu iso tace harda gudummawarta ta
k'ara aba Amarya, dama haka take da wuya kai siyayya bata k'ara maka ba Aunty tay mata godiya sosae
sukai sallama har Fauzy na yamutsa fuska tana ita baza'a siyar mata koda kazar bace Aunty tace asarar
kud'i kenan, ana yin sallar la'asar Fauzy tay ma Aunty Mareeya sallama ta tafi gidan su Fatuu don zuwa
gyaran jikin...........

(Aunty Bee Kayan Mata And Supplements TESTED AND TRUSTED duk abunda Aunty Mareeya ta fad'a
game da kayanta gaskiya ne ni shaida ce don haka kar ki bari a barki a baya wllh ki zama tauraruwa a
idon oga ta hanyar amfani da kayan Aunty Bee, Mace mai gyara bata boranci)

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2059*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


.............Fauzy na zuwa ba 6ata lokaci suka tafi don itama Fatun ta gama shiryawa, sai Magrib ta dawo
Fauzy an sauketa a School, daka kalli fuskarta ma zaka gane tasha gyara ga wani k'amshi da jikinta ke
fitarwa, lokacin data shiga gidan d'akin gwaggo ta nufa ta isketa ta dawo tana yin salla hakan yasa ta juya
ta nufi d'akin ta, a gaban dressing mirror ta tsaya bayan ta cire veil d'in da tayi rolling ta fara k'are ma
kanta kallo tana sakin murmushi, hannu ta kai tana shafa kumatun ta da har wani glowing suke, skin d'in
ta ta k'ara yin sumul gwanin taushi dama a mulke take Saboda tsadaddun mayukan da take amfani dasu,
bayan wani lokaci ta d'auki gyalen ta da ta ajiye a gefen mirror ta fita, d'akin gwaggo ta koma ta iske ta
gama Sallar tana zaune kan darduma tana tasbihi, gefen ta Fatuu ta nufa ta zauna suka had'a ido ta sakar
mata murmushi saida ta shafa sannan itama ta mayar mata da murmushin tace "Auta ta ta fara fitowa
sak Amarya" murmushi kawae Fatun ke yi ta gaishe da ita bayan ta amsa ta tambaye ta Fauzy tace mata
an aje ta a Makaranta ta d'aga kai, d'an shiru su kai suna ta yi ma juna murmushi daga baya Fatuu tay
mata Maganar kud'in d'azu da aka turo da wanccan da tay mata Maganar su gwaggon ta tambaye ta ta
tura ma Aunty Mareeya tace mata eh, tace to ai nata ne ba zatay amfani dasu bane, d'an shiru Fatun tay
kafin tace "ni ba abunda zan yi dasu kawae dae ina tunanin zuwa shagon Aunty Zee in siyo wasu kaya"
gwaggo dake kallonta ta tambaye ta wane irin kaya ko na sawa tace mata eh, tace "Yanzu duk kayan da
ke gare ki sai kin k'ara,wasu ma fa baki ta6a sakawa ba sai aita tara kaya don ma ana bayarwa, duka
yaushe Chairman ya baki akwati biyu na kaya ga shima Yayan naki da zai tafi yay maki akwatunan kaya
ga wad'anda kike siya duk basu isa ba ki tattara abun ki ki tafi dasu sai kin k'ara wasu" da d'an alamun
kunya Fatun tace "d...dama wai ko wanda zan sa ranar Juma'a d'in ne da yan underwear" da k'yar ta
k'arasa Maganar had'i da sunkuyar da kai gwaggon tace "ni ina ganin tunda lokaci ya riga ya k'ure kawae
ki bar shi yanzu yaushe har aka d'inka ma tunda kina da sababbin kayan da baki ta6a sawa ba ko cikin su
ne ki za6i d'aya sai ki saka, nasan ma ko daga bayane zai maki suturar tunda hakanan ma yayi bare kuma
yanzu, kawae don lokaci ya k'ure ne amman su underwear d'in zaki iya siyowa" kai ta d'aga mata alamar
to, "to wai ma kin had'a kayan naki ko kuwa baki had'a ba?" a hankali ta girgiza mata kai alamar a'a, tace
"to har sai yaushe ko sai lokaci ya k'ure kizo Kita faman duminiya" d'an yamutsa fuska Fatuu tayi kaman
zatai kuka tace "ni wllh gani nike kaman wasa ba gaske ba wai zan bar gidan nan" yar dariya gwaggo tay
tace "ki bari sai ranar zaki shaida in wasa ne ko gaske, in Allah ya kaimu ranar Juma'a kaman yanzu ai ina
sa ran kin ma bar gidan nan" cike da shagwaba tace "Wayyo Allah, wllh gwaggo ban jin dad'i zan rabu
daku zan koma wani wuri" tana rufe baki k'walla suka zubo mata sharr gwaggo dake ta dariya tace "ni
kuma kinga dad'i nike ji..." Katse ta tay da fad'in "kai gwaggo dama ashe kin gaji dani" tace "ai abun
farinciki ne yanzu ka ga naka yayi aure ba kamar da auren yay wuya yan mata da dama nata neman mijin
aure babu, gashi ke kin samu d'aya tamkar da miliyan don wannan wuce dubu, in na ce banji dad'i ba ai
na zama butulu ban gode ma Allah ba daya amsa man Addu'ar da nike maki koda yaushe ta ya baki miji
na gari" d'an murmushi Fatun tay ta sunkuyar da kai can ta d'ago tace "nama ji dad'i daba nesa bane zan
rink'a zuwa koda yaushe...." Da sauri gwaggo ta tari numfashin ta "ki rink'a zuwa ina? aikuwa dana sa6a
maki wllh mi kika d'auki aure ne, abun wasa ko mi to a hir d'in ki kika ce zaki rink'a yin sunturi kina zuwa
sai na sa6a maki kuwa, Mutuncin mace ta zauna a d'akinta sai ta kama ta fito" tana ta yamutsa fuska
tace "kaman ma ke bazaki missing d'ina ba" tana yar dariya tace "ba kuwa zan yi ba tunda na samu
madadin ki, Mino zan d'aukko ta dawo nan dama nayi mata alk'awarin zata dawo" d'an waro ido Fatuu
tay ta fara sakin murmushi cike da farinciki tace "Yanzu Mino nan zata dawo kenan?" Kai ta d'aga mata,
"amman kuma ai bata gama Secondary d'in ba" gwaggo tace "Eh aji biyar ta shiga in ta dawo nan sai ta
k'arasa ai" sosae Fatuu taji dad'i sai faman washe baki take, tana matuk'ar son yan'uwan ta don kuwa
mahaifiyar su itama tana son ta suma kuma haka don in ba ka sani bama baka cewa ba uwar su d'aya
uban su d'aya ba ba kamar dae Mino d'in bala'en kama take da Fatuu, tana zaune a d'akin akai sallar isha
gwaggo ta tashi tayi ita kuma ta koma d'akin ta, bayan gwaggo ta gama d'akin Fatun ta nufa tana shiga
ta iske ta a kan gado tana latsa wayarta tace mata ta tashi ta taya ta su had'a kayan nata tace to, saukko
da akwatunan ta sukai daga saman wardrobe gwaggo ta bud'e wardrobe d'in ta fara za6o mata wanda
zata tafi dasu ita kuma tana jerawa, suna cikin haka taci karo da k'umshin ledar magungunan da Aunty
Mareeya ta fara aiko mata ta fiddo tana fad'in miye aciki, d'an zaro ido Fatuu tay ganin gwaggon na
kokarin kwancewa yasa gabanta ya hau fad'uwa ta sadda kanta k'asa, bayan ta bud'e k'ura ma abunda
ke ciki ido gwaggo tay ta kai hannu ta fiddo da yar kwalbar ciki ta d'aga tana duba takardar jiki lokacin
Fatuu ta d'an d'ago gwaggon ta jefa mata wani mugun kallo ba shiri murya na rawa tun ma kafin ta
tambaye ta ta hau yi mata bayanin wadda ta bata, har saida gwaggo taji d'an sanyi don da hankalin ta
har ya tashi ta maida kwalbar ciki kafin ta kalleta sai yan kame kame take ta tambayeta ta yi amfani dasu
ne tace mata a'a gwaggon tace to Saboda mi ba bata akai don tayi amfani da su ba, cikin yar in ina ta ce
mata na kwalbar dole sai jinin ya d'auke su kuma sauran wani da nama ake cin shi wani kuma da peak
milk tana Maganar tana sussune kai, yar ajiyar zuciya gwaggon tay tace mata taje wurin Amadu ta amso
Madarar da sauri tace to ta juya gwaggon ta bita da ido har ta fita, bayan ta amso tasa ta d'aukko Kofi da
cokali a Kitchen ta tambayeta yadda aka ce a had'a ta fad'i mata da kanta ta shiga had'a mata bayan ta
gama ta bata ta shanye daga baya suka cigaba da abunda suke.

Washe gari wurin Misalin k'arfe sha d'aya saura na safe aka kira Aunty Mareeya daga tasha cewa ga
sak'o an kawo mata daga Kano tace to suka fad'i mata tashar da suke, kiran Daddyn su Hanif tay ta sanar
dashi zata je ta dawo, ba 6ata lokaci dama tana ta dakon isowar kayan ta tafi, bayan ta amshi sak'on
magungunan direct gidan su Fatuu ta nufa lokacin tana Makaranta sai gwaggo ta tarbeta tana ta fara'a
suka shiga Parlor, gaisawa suka shiga yi daga baya Aunty Mareeya ta warware kwalin da aka sako sak'on
ciki ta shiga firfito dasu tana yi tana ma gwaggo bayanin kowanne ta shiga yabawa tana sa Albarka ita
kanta taga sauk'in kayan gasu da yawa, bayan ta gama fiddo su ta nuna mata wanda yakamata a fara ba
Fatun zuwa ranar tarewar sauran kuma sai ta tafi dasu taci gaba da amfani dasu a can gwaggon tace to
da ta dawo sai a fara batan, sosae tay ma Aunty Mareeya godiya tana Allah ya bar zumunci daga baya ta
tambaye ta ko akwae wani abu gwaggon tace ehh kayan k'amshi take so an mata kwatancen in da zata
samu to ita kuma ba sanin kan su tay ba Aunty Mareeya tace wannan ba matsala bane akwae inda za'a
same su masu kyau jera mata kawai za'ai don already a kwalaben su masu kyau suke nan ma godiya
gwaggon tay mata ta tambayi kaman nawa zasu isa ta fad'i mata, bayan sun gama Maganar kayan
k'amshin suka shiga Maganar Abinci da za'ai ranar Juma'ar, saida suka gama tsara komae Gwaggon ta
bata kud'in abubuwan da zata siyo sannan ta tafi. Tun Aunty Mareeya na kan hanya ta kira Fauzy ta
sanar mata zancen isowar sak'on Magungunan taji dad'i sosae ta sanar ma Fatuu ita dae d'an guntun
murmushi kawai tay, bayan an tashi Hostel suka wuce Fauzy ta had'a kayanta a cikin d'an trolley zata bi
Fatun kaman yadda suka tsara a aji ita da dawowa cikin Makaranta sai bayan ta tare daga baya Haisam
yazo d'aukar su, tun bayan da suka shiga Motar suka gaida shi ba wanda ya k'ara cewa uffan har suka isa
gida, suna shiga d'akin gwaggo suka wuce tana ta fara'a tay masu sannu da dawowa suka gaishe da ita
tace in sun kimtsa su zuba Abinci yana Kitchen suka ce to suka nufi d'akin Fatuu, suna cikin cin Abincin
gwaggo ta k'wala ma Fatun kira bayan taje ta bata wasu daga cikin Magungunan da aka kawo kaza da
cicci6i da kuma zabuwa duk ta d'ibar mata tace taje ta cinye su duka harda romon su tace mata to ta
koma d'aki Fauzy na zaune tana cin Abincin ta shigo ta koma inda ta tashi ta zauna, koda Fauzy taga
abunda ta shigo dashi nan take ta gane na maganin ne tunda taga hotunan su jiya ta hau yin murmushi
Fatuu ta aje tace su ci Fauzy ta zaro ido tace ta rufa mata Asiri wannan yafi k'arfin ta saidae itan tay d'an
murmushi kawae ta kai hannu ta yago naman kazar ta kai baki koda taji taste d'in ta ba Arziki ta d'an
yamutsa baki da k'yar ta had'iye na bakinta a tunanin ta ko kazar ce kad'ai haka sai ta d'ibi cicci6i shima
tana kaiwa baki taji shi salaf sai kaifin magani bayan ta had'iye ta kalli Fauzy tace don Allah ta ci da dad'i
sosae jin haka yasa ta cewa tunda ta matsa mata bari ta d'an ci ta kai hannu ta yagi kazar Fatuu nata
gumtse dariya gaba d'aya ta kai naman baki ba Arziki itama ta tsaya cak ta kasa taunawa ta d'an zaro ido
Fatuu kau mi zata yi in ba dariya ba, da k'yar Fauzy ta had'iye tana d'an yamutsa fuska ta kai hannu ta
d'auki ruwa ta kwankwad'a bayan ta aje tace "tabb, ni fa koda na ganta na zata Normal farfesun kaza ne
ashe ashe duk farfesun magani ne wannan dole ma tay aiki a jiki kam" koda Fatuu tace mata ta k'ara don
Allah cewa tay wllh in ta ganta a lahira kaita akai hakanan taja ma kanta bala'e ta kasa zaman lafiya ita
dae daya zamar ma dole taci Fatuu tay ta mata dariya, daurewa tay taci gaba da ci daga baya ma lafiya
lau ta rink'a ci har ta cinye ta shanye romon kaman yadda gwaggon tace, bayan sun gama suka hau
shirin tafiya gyaran jiki da wankin kai don gwaggo tace kitso za'a yi mata, da daddare bayan sun dawo
sun ci Abinci gwaggo ta kara kiran Fatuu ta bata tsumi kusan kala ukku ta sha harda na magarya mai
wanko mara yay maganin sanyi aikuwa sosae yay ma Fatuu aiki don duk wani sauran jini daya rage saida
ya fito a daren,

Washe gari Alhamis da safe bayan sun yi breakfast suka hau shirin tafiya Makaranta Haisam ne yazo ya
d'auke su, Bayan an tashi ya d'aukko su suna dawowa Abinci kawae suka ci suka hau shirin tafiya k'unshi
lokacin da Fatuu ta shiga toilet yin wanka har saida ta d'an yi mamaki ganin Pad d'in data sa da safe
Kandas ba jini alamar dae ya d'auke hakan yasa bayan ta gama wanka ta had'a dana tsarki tayi sannan ta
fito, tana komawa d'aki ta zura doguwar riga don yin salla Fauzy na ganin haka tay yar shewa ta hau
tsokanar ta tana fad'in an yi a daidai abun ya mata dad'i wllh, ita dai d'an murmushi kawai tay ta girgiza
kai, bayan duk sun shirya suka tafi, Ana gama sallar la'asar sai ga Saude tare da Tk rike da wasu
jakunkuna masu shegen kyau guda ukku Gwaggo ta tarbe su suka shiga cikin parlor, bayan sun gaisa
Saude tace mata gashi in ji Hajiya tace Fateema ta fara amfani da kayan ciki gwaggo ta hau godiya Saude
ta k'ara cewa da Mota suka zo tace a kwaso kayan kitchen da sauri gwaggo tace to ta mik'e suma suka
mik'e gaba d'aya suka fita, saida ta lek'a waje ta kira Amadu ya shigo aka fara kwashe na cikin d'akin shi
ana kaiwa cikin Hilux d'in da suka zo da ita daga baya aka kwashe na cikin d'akin Fatuu, sai bayan da suka
tafi ne gwaggo ta koma parlor ta bud'e jakunkunan ta fara dubawa, kaya ne ciki dinkakku lace kala biyu
atampa kala ukku sai shadda data sha uban aiki itama kala biyu sai lifaya da dogayen riguna suma kala
bibbiyu a cikin d'ayar jakar mahad'in sune wato takalma da mayafai harda hijab da jakunkuna sai cikin ta
k'arshen underwear ne harda rigunan bacci dasu sark'ok'i da kuma kayan shafa duk da kayan basu da
yawa amman fa da ka gani kasan masu kud'ine ba k'ananun kaya bane, bayan gwaggon ta gama dubawa
ta hau jinjina kai cikin ranta take raya ita dama ranta ya bata da wuya ba'ai ma Fatun kaya ba, maida
komai tay ta mik'e ta fita, d'akin ta ta koma tana zuwa ta kira Hajiyar a waya tay mata godiya ta
tambayeta ba wata matsala tace mata eh ta k'ara yin godiya sosae da Addu'oi. Bayan su Tk sun kai kayan
ta k'aramar kopa suka rink'a shiga dasu shida Amadu da gwaggo tasa ya bisu Saude ma ta fara d'auka
Officer ya taso yace ta barshi ya kama aka rink'a shigar dasu tare da shi ita kuma ta nufi cikin part d'in
don ta fara jerawa kaman yadda Hajiya ta bada umarni har aka shigar da komae. Yau ma sai bayan
Magrib suka dawo har Fauzy ma anyi mata k'unshi gwaggo na gani ta hau yabawa don ba k'aramin kyau
yay ba ya zanu rad'am abun ka da farare kuma gashi ja da bak'i ne yay gwanin burgewa gwaggo ta nuna
masu kayan da aka kawo suka fara dubawa Fauzy nata santi ita dae Fatuu murmushi kawai take.

JUMA'AT BABBAN RANA

Washe gari da wani irin yanayi Fatuu ta tashi ta kasa gane farinciki take ko damuwa gaba d'aya kasala ta
baibaiye ta har Fauzy ta fahimci hakan ta tambayi Mike damunta tace ita dae gatanan ta rasa Mike mata
dad'i ma yar dariya Fauzy tay tace zullumin barin gida ne, Bayan sun yi breakfast suka yi shirin tafiya
Makaranta, koda Fatuu taje yima gwaggo sallama cewa tay ai tayi zaton zasu hak'ura da zuwa yau Fatun
da tay sukuku tace ai ko sun zauna ba abunda zasu yi gara su tafi gwaggon tace shikenan itama ta lura da
yanayin ta har saida ta tambayeta wani abu ke damunta ne tace mata ba Komai ta juya zata fita
gwaggon ta bita da kallo tana d'an murmushi, tana komawa d'aki ta jiyo horn d'in Haisam suka fito,
Bayan tafiyar su makwabta suka fara shigowa don gwaggo duk ta sanar dasu zancen auren da tarewar
kowa yaji sai ya taya ta murna har innar su Haulat ma tazo nan aka fara shirin d'aura girki duk da ba
wani abu za'ai ba miyar waina ce da sinasar da ta bada ayo mata sai Fried rice itama Aunty Mareeya ta
amsa zata bada ayo harda su coleslaw, bayan an d'aura miyar aka fara had'a kunun Aya da zobo lokacin
wasu daga cikin Abokan aikin gwaggon suka zo har an taho da su dublan d'in data bada aikin su nan aka
cigaba da hidima, lokacin da su Fatuu suka dawo wurin k'arfe d'aya saura mutane sun d'an taru a gidan
ba laifi harda Zaliha d'iyar kishiyar gwaggon da iyalanta da kuma iyalan baba shehu suna shigowa aka
hau ce ma Fatuu Amarya Amarya ita dae d'an murmushi kawae take tana gaishe dasu suka wuce d'aki,
suna shiga Fatuu ta nufi gado ta zauna dabar Fauzy dake k'ok'arin cire Hijab tace ba zama yakamata tay
ba ta tashi taje tay wanka ta shirya kar aita ganin Amarya kamar an koro ta kallo kawae ta bita dashi bata
da niyyar mik'ewa, suna haka gwaggo ta shigo ruk'e da plate d'in Abinci da kuma na sobo da kunun aya
ta aje masu akan Carpet tace gashi nan su ci in sun gama taje tay wanka ta d'aga mata kai, bayan sun
fara ci bata ci wani mai yawa ba ta cire hannunta Fauzy na tambayar ta badae har ta k'oshi ba tace eh
rarrashin ta ta shiga yi kan ta k'ara tace mata bata jin dad'in bakin ta ne dole ta rabu da ita tace to taje
tayo wankan, bayan tayo wankan itama Fauzy taje tayi suka fara shiryawa doguwar rigar shadda ta fiddo
mata a cikin kayan da Hajiya ta aiko ta taimaka mata ta d'an yi make up ta koma saman gado ta zauna
Fauzy ma ta hau shiryawa lokacin Haulat ma tazo bayan ta gaisa da gwaggo ta bata gudunmawar data
kawo tana ta godiya ta koma d'akin Fatuu, a bakin gado ta zauna ganin yanayin ta yasa ta hau
tambayarta lafiya ita da za'a gani tana farinciki Fauzy na yar dariya tace fargaba ce itama Haulat dariyar
tayi.

Ana gama sallar Juma'a su Feenah suka iso sun ci gayu Abdul harda babbar riga tunda bai sa yaje daurin
aure ba yasa yazo tarewa, harda katan katan d'in lemu da ruwa suka kawo da kwalin Warmers masu
kyau harda na had'addan glass jug ga kuma kud'i gwaggo tay murna sosae sai godiya take, daga baya ta
koma d'akin Fatuu tana zaune saman gado ta rungume Abdul da tunda suka shigo gidan ya nufi d'akin,
bakin gadon Feenah ta zauna ta kalli Fatun da murmushi tace "Amaryar mu kin sha kyau" d'an murmushi
kawai tay ta gaishe da ita aka kawo masu Abinci, su Feenah basu dad'e da zuwa ba Aunty Mareeya ta iso
tare da k'atuwar kular Fried rice da trays d'in coleslaw anyi sealing, su Amadu ne suka shigo da su tare da
Tk da wani abokin su ita kuma suka kamo k'aton kwalin kayan k'amshi ita da Maman taufiq makwabciyar
ta da suka taho tare, gwaggo tay farinciki sosae har ta kasa rufe baki sai faman godiya take tana shi
Albarka daga baya wasu daga cikin k'awayen su na makaranta da Fauzy ta gayyata suka zo ciki harda
Zainab Muhammadu da wadda zatayi ma Fatuu make up dama sana'ar ta ce ba 6ata lokaci aka fara yi
mata, lokacin da aka gama baka jin komai sai Tubarkallah da kowa ke fad'a don ba k'aramin kyau
kwalliyar tay mata ba ba kamar da yake ba'a ta6a yi mata irin ta ba,nan fa aka shiga yi mata hotuna daga
baya aka sa ta canza kaya tasa lace shima akai mata hotunan, haka aka ci gaba da hidima aka ci aka sha
abun sai godiyar Allah, Bayan sallar la'asar Haisam na Zaune a Bedroom d'in shi na G.r.a tare da Abbas
da Saleem da yasan da zancen auren daga baya Najeeb dae bai sani ba don bai K'asar yana Canada, basu
dad'e da gama cin Abinci ba da Abbas ya kawo daga gidan Hajiya don anan ya iske su bayan ya kai su
Feenah, gaba d'ayan su kowa na ruk'e da wayar shi yana latsawa jefi jefi suke yin Magana, can Abbas ya
mik'e daga kan kujerar da yake ya nufi Haisam dake kishingid'e jikin shi sanye da ash d'in shadda ya
zauna daga gefen shi yana fad'in "gafa Amaryar ka ta fito ma sha Allah" d'aga ido yay ya kalli wayar,
Abbas yaci gaba da bud'e mashi sauran dama Feenah ce ta d'aura su a status

har saida suka k'are sannan Haisam d'in ya janye idon shi ba tare da yace komai ba, Abbas ya mik'e ya
nufi Saleem dake sanye da farar shadda yana latsa waya shima ya shiga nuna mashi d'an guntun
murmushi yay cikin cool voice d'in shi tamkar Haisam yace wai yarinyar nan ce har ta girma Abbas na
dariya yace mashi eh mana gashi ma har ta d'auke nauyin H,zakee Haisam din na jin shi bai ko kalle su ba
Saleem d'in ya k'ara yin d'an guntun murmushi kawai, suna nan har aka yi sallar Magrib suka tafi
Masallaci suna can har akai isha ana gamawa Hajiya ta kira Abbas tace mashi ya taho suje su d'aukko
Fateema yace to bayan sun gama ya kira Feenah ya tambaye ta akwae Mutane ne da yawa tace mashi
ba laifi, Saleem yay ma Magana da yake da Jeep ya zo kan suje su d'aukke su yace ok, kallon Haisam
Abbas yayy yana murmushi yace ya taso suje ya d'an girgiza mashi kai alamar ba zai je ba ya juya yace
ma Saleem su je ya mik'e har zasu tafi Haisam ya dakatar dasu Abbas ya juyo yana kallon shi ya mik'e
yace yana zuwa, dressing mirror ya nufa ya jawo drawer chest ta tsakiya ya fiddo wani makulli, bayan ya
rufe ya dawo wurin su ya mik'a ma Abbas yace yay amfani da Motar duba makullin yay ya d'ago da d'an
bud'a ido yace "Lalle kana ji da Amaryar nan a Jeep d'in Dad d'in za'a d'auketa" shiru yay mashi ya nufi
komawa kan kujera yace ma Saleem suje suka nufi hanyar fita daga Bedroom d'in, Bayan Hajiya ta kira
Abbas tay mashi Magana ta kira gwaggo tace mata a shirya Fateema za'a zo a d'auketa tace to, d'akin ta
ta nufa su Aunty Mareeya da Feenah da sauran k'awayenta duk suna ciki anata hira Aunty Mareeya sai
basu dariya take gwaggo ta shiga ta sanar dasu, wani irin bugu k'irjin Fatuu yay gabanta yaci gaba da
Fad'uwa Aunty Mareeya kau harda gud'a ta rafka ta mik'e tana fad'in Fatuu ta tashi ta canza kaya, Wani
farin dankareren lace mai adon golden cikin kayan da aka kawo mata ta fiddo mata da gyalen shi golden
da takalman shi half cover masu tsini suma golden harda purse d'in su dama barin su akai sai za'a kaita
ta saka su, ba 6ata lokaci aka gama shiryata abun saidae ace Tubarkallah tayi kyau har ta gaji sai yi mata
hotuna ake ba'a dad'e da gama shiryata ba Hajiya da Saude suka zo Hajiya na fadin gasu sun zo biko tana
sanye da lifaya Saude ma tasha doguwar rigar lace da mayafi, nan aka shiga gaishe gaishe Gwaggo tace
ma Hajiyar su shiga tace a'a basai sun shiga ba dare nayi a fiddo ta su tafi tace to ta nufi d'akin, tunda taji
zancen an zo tafiya da ita ta saka kuka da duk ganin abun take kaman wasa sai yanzu ta tabbatar gaske
ne, nan aka shiga rarrashin ta Aunty Mareeya data ruk'ota cike da zolaya take ce mata waya fad'i mata
amare na kuka yanzu k'auyanci ne, bayan sun fito aka kaita gaban Hajiya dake tsaye tana jira tace akaita
Mota duk aka firfita ta kalli gwaggo dake tsaye jikinta duk yayi sanyi tace itama tazo aje da ita ta rakata
d'akinta tace to ta juya don d'aukko Hijab bayan ta dawo suka fita tare da Hajiya.............

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2060*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


......... Lokacin da su Hajiya suka fito Abbas na tsaye bakin Jeep d'in da ya zo da ita har an shiga da Fatuu,
Aunty Mareeya da Feenah da inna Zaliha da Matar Baba shehu duk suka shiga ya juya kan sauran
k'awayen Fatuu da suka rage don wasu sun tafi ya nuna masu Jeep d'in Saleem yace su je su shiga harda
Fauzy ita ta shiga gaba sai Haulat, sauran wad'anda suka rage Abokan aikin gwaggo Hajiya ta nuna masu
Motar da Tk ya zo da ita suka shiga Amadu na a Front seat, kowa ya samu wuri sai wasu daga cikin
Makwabta ne basu samu ba Hajiya tace su taka a k'asa itama a k'asan zata duk akai dariya ta kira Abbas
yazo gaban su tace mashi su d'an zagayo da su Fateemar ita ma ta shaida an yi mata d'aukar Amare yana
murmushi yace to ya juya, Motar Saleem ya nufa ya zagaya driver side ya bud'e yana zauna ya d'an d'age
kan shi jikin headrest ya sanar dashi zasu d'an zagayo dasu roundabout ya jinjina mashi kai ya rufe mashi
kopar, saida yaje ya sanar ma Tk shima sannan ya dawo Motar tashi, lokaci guda gaba d'aya suka kunna
motacin sai lokacin gwaggo dake tsaye ta tuna da kayan Fatuu ta yi ma Hajiya Maganar ko a d'aukko
kafin su tafi tace ta bari in suka dawo sai Tukur yazo ya d'auka tace to, Tk ne ya fara jan tashi dama shine
a gaba lokacin da suka baro gidan Hajiya da zasu zo ya mik'i hanya Abbas ne a tsakiya sai ta Saleem
k'arshe suka tafi,

Bayan tafiyar su Hajiya tace masu su tafi su jira su acan gidan, har zasu tafi ganin an bar gidan a bud'e
yasa Hajiya cema gwaggo akwai sauran mutane ne a gidan za a bar shi a bud'e, sai lokacin ta ankare da
sauri ta juya tana fad'in ta manta Hajiya na cewa ko duk tafiyar Fateemar ce tasa ta rikicewa, bayan ta
shiga ta d'aukko wayar ta da makulli ta fito ta rufe gidan suka tafi, ta k'aramar kopa suka shiga suka nufi
part d'in Haisam, lokacin da suka shiga a gyare harabar take tsaf an gyare shukokin flowers d'in wurin
gwanin sha'awa suka nufi kopar shiga parlon, suna shiga makwabtan da aka je da su suka saki baki galala
suna bin parlon da kallo ga wani ni'imtaccen sanyin Ac had'i da fitinannan k'amshi da ya karad'e cikin
parlon, gwaggo dae sai d'an murmushi take itama tana k'are ma parlon kallo, parlon yana nan yadda
yake amman an k'ara wasu abubuwa kaman daga bayan L-shape ansa dining table mai kujeru hud'u
suma leather ne bak'ak'e sai daga gaba bangon dake kallon su an sa wani jigunannan console mai jan
hankali golden haka saman kujera L-shape an canza throw pillows an sake wasu masu design mai kyau
da d'aukar hankali, Carpet d'in k'asa ma an canza wani sabo wanda ke akwae da an maida shi wurin
dining table, haka flowers d'in dake a angles d'in parlon an k'ara wasu, d'an madaidaicin Fridge d'in dake
parlon an maida shi cikin kitchen sai sabon freezer da aka siya mata a cikin kayan kitchen aka aje shi a
parlon daga can wurin dining table, a jikin bangon parlon an manna manyan Frames harda mai Ayatul
kursiyyu, blinds d'in jikin Windows ma an canza su zuwa manyan labulaye wanda daka kalla ba sai an
fad'a maka ba zaka shaida masu kud'i ne Saboda had'uwar da sukai kuma sun hau da parlon sosae,
komae ya hau daidai nan aka shiga yabawa ana sa Albarka tare da Addu'oi, Hajiya tace masu su shiga
suga sauran d'akunan suka ce to suka nufi hanyar corridor, Bedroom d'in ma tsab dashi sai k'amshi ke
tashi nan ma an canza labulayen ciki haka gadon ma yasha babban bedsheet mai pillows da yawa ko a
ido ka kalle shi kasan zai yi mugun taushi, nan ma sosae suka yaba daga baya Hajiya tace suje su ga
Kitchen ta juya gaba suka bi bayanta, d'ayan d'akin da yake matsayin Lab d'in shi a da shine aka maida
mata kitchen d'in, bayan sun shiga ciki sosae shima suka yaba komae an tsara shi har a sama anyi
cabinet haka k'asan ma cikin kankanin lokaci an maida d'akin Kitchen na yan gayu, bayan sun gama gani
suka nufi Parlor sai faman yabo da san barka ake, duk suka zazzauna suna dakon isowar su Fatuu
farinciki Fal cikin zuciyar gwaggo har fuskar ta ta kasa 6oyewa sai d'an murmushi take ganin wai autar ta
ce zata rayu a cikin wurin, sai godiya take ga Allah acikin ran ta,

Tun da suka tafi Fatuu ke ta faman kuka har Abbas saida yay mata Magana yace gidan fa Ya Handsome
d'inta za'a kaita ba wani wurin ba ai farinciki yakamata tayi ba tay ta yin kuka ba sai kace za'a kaita inda
za'a cuta mata, Aunty Mareeya itama tace abun ya bata mamaki wannan kuka haka sai kace za'a kaita
gidan makiyinta Feenah ce tace "ai dole duk da hakan sai taji ba dad'i barin gidan da ka saba rayuwa a
ciki ka koma wani wuri ba abu bane da ba za'a ji komai ba", inna Zaliha tace gaskiya ne ba kamar yadda
suka shak'u da gwaggon ta,

Aunty Mareeya tace "hakane, amman dae kukan yayi yawa bai kamata ta sama kanta damuwa ba tunda
dai ga baki ga hanci ba nisa tayi da gida ba, muda aka d'aukko daga wani gari sai an dad'e kafin muje gida
ita kuwa data fito fa zata ga gidan koda bata shiga ba zata ji dad'i, gani ma zatayi tamkar ba ta bar gidan
ba tunda duk unguwa d'aya ne kuma in taso ma kullum taje nasan ba zai hana ba" inna Zaliha dake d'an
murmushi tace "hakane amman dai kar ace kullum sai anje d'in hakan bai kamata ba, ita mace ta zauna a
d'akinta shi yafi mutunci ba kullum ai ta ganinta tana sunturi a waje ba hakan bai dace ba" gaba d'aya
suka ce gaskiya ne harda Abbas, saida suka shawo roundabout na Barhim sannan suka koma. A cikin
kwanar gate suka parker Motocin bayan sun iso duk aka firfito Aunty Mareeya na ruk'e da Fatun gefenta
Abdul ne ruk'e da hannunta guda suka shiga ta k'aramar k'opa da sauran Mutane, lokacin da suka
k'araso bakin kopar shiga parlon Aunty Mareeya ta tsaya da ita tace tayi Addu'a sannan ta shiga da k'afar
dama wad'anda ke a bayan su duk suka tsaya saida ta gama sannan suka shige sauran suka bi bayan su,
suna shiga d'aya daga cikin makwabtan dake zaune suna jiran isowar su ta mik'e ta rangad'a gud'a mai
sautin gaske su Hajiya suka shiga sakin murmushi itama ta mik'e ta nuna masu inda zasu shiga da ita
kowa ya baza ido yana k'are ma parlon kallo, hardae Aunty Mareeya da Feenah bin parlon suke da kallo
don ba k'aramin had'uwa yay ba ya matuk'ar burge kowa ga wani irin k'amshi mai had'e da sanyin Ac da
ya baza ko ina na parlon, Fauzy ma ta jinjina had'uwar wurin har d'an jinjina kai take haka sauran
k'awayen su Zainab Muhammadu ma baki bud'e take k'are mashi kallo, ba wanda ma yay tunanin kayan
ciki wai ba sababbi bane don kana kallon su zaka ga sabunta a tattare dasu tunda dama iya Haisam d'in
kadae ne ke amfani dasu kuma masu matuk'ar inganci ne hakan yasa sam basu canza daga yanayin da
aka siyo su ba, Saude ce tay masu jagora zuwa Bedroom d'in nan ma saida aka sa Fatun tayi Addu'a a
bakin kopar shiga sannan ta shiga da k'afar dama aka wuce ciki da ita wurin gado, nan ma dae sosae
Mutane suka yaba anata Addu'oi, a can tsakiyar gadon aka sa ta haye ta zauna ta jingina da headboard
kanta na sadde cikin gyale Fauzy ma ta hau ta zauna gefen ta haka Abdul ma har lokacin yana ruk'e da
hannunta duk ya damu tun da yaga tana kuka shima a Mota har kukan yayi yana fad'in ta daina kuka,
bayan an gama ganin Bedroom d'in har Laundary room da toilet saida mutane suka shiga suka gani
harda su Aunty Mareeya, bayan sun gama dubawa suka fita zuwa Kitchen ya rage daga Fauzy sai sauran
k'awayen su, su Zainab dake zaune a bakin gadon sai faman santi suke suna Allah ya maida su damshin
Fatuu Fauzy na dariya take amsa masu Zainab tace suje suga sauran wuraren suma duk suka mik'e suka
nufi laundry Fauzy ta juya ta kalli Fatuu da har lokacin bata d'ago ba ta kai hannu ta d'an d'aga gyalen ta
lek'a fuskar ta suka had'a ido idanun nata sun yi jawur Fauzy ta jawota jikinta tana Fad'in "Haba Amaryar
Ya Haisam kukan ya isa hakanan, keda zaki murna ki farinciki Allah ya cika maki burin ki yau gaki a gidan
shi a d'akin ki mallakin ku keda shi, don Allah kiyi hakuri kar kija ma kan ki wani ciwon a wannan daren
mai daraja da zaku idasa dunk'ulewa ku zama abu d'aya" d'aga idanunta da suka sauya kala tay ta d'an
kalli Fauzyn dake ta sakin murmushi wanda da gani da biyu take yin shi, yar harara Fatuu ta jefa mata ta
maida kan ta k'asa Abdul dake a jikinta shima yace "Aunty Fatuu kar ki k'ara yin kuka don Allah, Baba
Zakee ba zai cuce ki ba kuma zai rink'a siya maki kayan dad'i da yawa harda Computer ki rink'a yin game"
d'an murmushi tay ta d'aga mashi kai kafin ta kai hannunta da ya sha k'unshi da had'add'un awarwaro
yan manya guda hud'u sai zobba guda biyu ta shafi fuskar Abdul d'in yaron yana k'aunar ta sosae, d'aga
ido Fauzy tay tana k'ara kallon d'akin tace yakamata a k'ara sa turaren wuta cikin wanda Aunty Mareeya
ta kawo tace bari tay mata magana ta sauka daga saman gadon ta nufi kopar fita, tana fita parlon taga
ba kowa a ciki tun bayan da suka gama dudduba ko'ina Hajiya tace atafi part d'in ta a ci Abinci kar a 6ata
ma Amarya nata shine aka d'unguma aka tafi can, wayar ta ta fiddo daga cikin side bag d'inta ta fara
k'ok'arin kiran Auntyn bayan tayi picking ta tambaye ta suna ina ta fad'i mata tace gata nan zuwa, fita
tay daga cikin parlon bayan ta fito part d'in duk da bata san in da part d'in Hajiyar yake ba bata sha
wuyar gane hanyar da zata bi ba saboda ko ina fayau yake da haske tamkar da rana, tana shigowa
harabar ta hango part d'in ta nufe shi, bayan fitar Fauzy a hankali Fatuu tasa hannu ta yaye gyalen kanta
yadda fuskar ta ta fito sosae, d'aga kai tay ta fara bin bedroom d'in da kallo har yanzu ganin abun take
tamkar ba gaske ba kaman mafarki ne, wai yau itace a cikin bedroom d'in Ya Haisam a saman gadon shi
kuma ma a matsayin matar shi Allah kenan buwayi gagara misali acikin ikon sa komai mai yuwuwa ne
cikin sauki, cigaba da k'are ma d'akin kallo tay iya fentin shi abun burgewa ne balle kuma rantsattsun
tsadaddun furniture d'in ciki, sam d'akin baida hayaniya ga wasu jigunannan labulaye, bedsheet d'in
saman gadon cikin wanda Hajiya ta siya mata ne lokacin da za'ai mata aure da kayan kitchen har saida ta
kai hannunta ta d'an ta6a jikin shi gwanin taushi, tana haka ta shiga tunano can baya tun daga kan
farkon ganin shi lokacin da ya raba su fad'a da Jameela mai awara, a nutse taci gaba da tunanin baya sai
faman sakin murmushi take lokacin ta tuno da ran da tazo kawo mashi takardar list d'in littattafan da
yace taje ta d'aukko bata gan shi a parlon ba ta zo bakin corridor ta tsaya tana yin sallama tace ga
takardan, jin shiru bai amsa ba yasa tace ko ta shigo ne ta kawo mashi ya bata amsa da tunda d'akin ta
ne ai sai ta shiga daga bayanta ashe bai a cikin d'akin, wani irin murmushi ta saki har fararen hak'oran ta
suka d'an bayyana a ranta ta ayyana yanzu gashi ya zama nawa d'in gani ma zaune a saman gadon ka,
k'ara tunano lokacin da zai kaita makaranta tay da tace don dai ita k'arama ce da sun yi soyayya kuma in
ta gama Secondary School cigaba zatai da karatu yace to ko ya jirata ne tace ai lokacin ita ta zama
babbar budurwa shi ya kuma ya tsufa, tace in yana so zata had'a shi da yar ajin su sofiya moussa yace bai
sata ba daga baya kuma ta hau yi ma safiyar sharri har tana ba ma lalle ya so ta ba don k'aton baki gare
ta hak'oranta kuma sun d'an turo kuma bata da jiki kamar sandar suluka take, tunano hakan har saida
tay dariya mai d'an sauti, ita kanta tasan tayi ma Haisam hauka iri iri kafin ta girma amman bai ta6a yin
fushi da ita ba ko ya canza mata, in ma tayi abunda ya nuna ta 6ata mashi rai da ta bashi hak'uri yake
hak'ura, tabbas dole ne ka ra6i Haisam sai ya burge ka don komai nashi na musamman ne samun irin shi
wanda ya had'a abubuwan da ya had'a zai matuk'ar wahala, ga tsantsar kyau, ga kud'i, ga kirki, ga hali
mai kyau, ga ilimi, ita kam ko iya haka ta gode ma Allah don ya gama mata komai samun Haisam a
matsayin miji ba k'aramar baiwa bace wllh, wata zuciyar ce ta raya mata in kuma bai son ta fa kuma
dangin shi suka k'i amincewa da ita, sosae jikinta yay sanyi lakwas yin wannan tunanin, tasan koda bai
son ta bazai cutar da ita ba tana da tabbacin hakan inda za'a samu matsala wurin dangin nashi ne in basu
amince da ita ba ga kuma matar shi Fanan, sosae Fatuu ke jin zullumin abunda zai je ya dawo in ta samu
labarin auren nasu don ita shaida ta kan irin son da take ma Ya Haisam ga hirar da ta ta6a ji yana yi da
Abbas da ta tabbatar da cewa Fanan d'in ce ta fara son shi da ya nuna baiso shine har ta kwanta gadon
Asibiti, tsayawa tay da yin tunane tunanen Saboda gaba d'aya jikinta ya mutu ta zuba ma bangon da take
facing ido a ranta ta shiga ayyana ita bazata so Ya Haisam ya shiga matsala Saboda ita ba, in dae bai son
ta da bai cigaba da zama da ita ba, wata zuciyar tace ki ka sani ko yana son ki kaman yadda ake hasashe
tunda har abu ya shiga tsakani kuma ya nuna rashin jin dad'i da kika zubar da cikin, shiru tay don a
wannan ga6ar baza ta iya yanke hukunci ba duk da a yanzu tasan gaba d'aya abunda ya farun bada niyya
bane kuma da ya nuna yayi fushi kan abunda tay k'ilan don aikata hakan laifi ne kaman yadda ya fad'a
mata da taje bashi hak'uri da kuma gudun kar wani abu ya faru da ita ba wai don yana son cikin ba ko ita,
haka tay ta sak'e sak'e, jin Abdul yay tsit yasa ta kai idonta kan shi taga ashe yayi bacci ta fara k'ok'arin
gyara mashi kwanciya a gefen ta tana cikin haka taji an turo kopar Bedroom d'in ta kai idonta da sauri,
Kawu Amadu ne ya shigo yana sanye da sabuwar shadda light blue da ya d'inka musamman Saboda
ranar, suna had'a ido suka sakar ma juna murmushi ya iso bakin gadon ya zauna sai faman murmushi
take mashi ta kasa yi mashi magana,

"Amarya, Allah dai ya amince Romeo ya zama naki" ya fad'a yanata murmushi still itama murmushin
take ta k'i cewa komae,

"Ko duk Farin ciki ne ya hana ki magana?" Ya fad'a yana murmushi da sauri tasa tafukan hannuwanta
da suka sha k'unshi ta rufe fuskar ta, bayan ta cire tana kallon shi yace "kinga ikon Allah ko?" Kai ta d'aga
mashi alamar eh, "zaki iya tuna abunda na fad'a maki a can baya lokacin dana iske ki a d'aki cikin
mawuyacin hali har kika fad'a man Saboda Ya Haisam ne?" Shiru bata ce mashi komae ba ta maida
idanun ta k'asa, yaci gaba "lokacin na fad'i maki in Ya Haisam rabon ki ne kina zaune ba tare da wata
wahala ba za ki ga yazo ya Aure ki har kita mamakin yadda akai hakan, kin tuna?" d'agowa tay ta kalle shi
tare da d'aga mashi kai, yaci gaba "kin ga maganata ta tabbata, Wannan kad'an ne daga cikin ikon Allah,
in dae zaka dogara gare shi to tabbas zaka samu biyan buk'ata ba kamar in ka had'a da hakuri da kuma
Addu'a, in kika ga duk kin yi wannan amman bukatan ki bata biya ba to abun ba Alkhairi bane gare ki sai
ya musanya maki da wanda yake Alkhairin, shi yasa ake son bawa ya kasance mai yawan godiya ga Allah,
in ka samu ka gode mashi haka in ka rasa, a koda yaushe in zaka yi Addu'a to ka rok'i abunda yafi zama
Alkhairi a gare ka, duk abunda kaga kasamu to shine yafi Alkhairi, Allah ubangiji da kan shi acikin suratul
baqara yace zaku so wani Al'amari alhali ba Alkhairi bane a gare ku, haka zaku K'i wani Al'amari alhali
Alkhairi ne a gare ku, Allah ne mafi sani ko baku sani ba, to kinga ba buk'atan ka matsa ma kan ka akan
dole sai ka samu wani abu tunda ga mai badawa wanda ya san abun Alkhairi ne a tare da kai ko sharri
sai ka mik'a komai a Wurin shi ka dage da Addu'a, a k'arshe ina taya ki murnar samun abunda ran ki ke
so ina fatan kuma ku zame ma juna Alkhairi, Allah ubangiji ya bashi ikon ruk'e ki da Amana ya kauda
dukkan wata fitina, kema Allah ya baki ikon yi mashi biyayya ya albarkace ku da zuria d'ayyiba Amin"
idon shi a Kanta ya k'arasa fuskar ta da d'an murmushi take kallon shi ba tare da ta ce komae ba, d'an
tsuke fuska yay yace "ba zaki ce Amin ba" d'an yamutsa fuska tay ta d'an sa hannu ta rufe wurin idanun
ta alamar kunya, yace "ke ni zaki wani nuna ma ke mai kunya ce, miye abun kunya an roka maka abun
Alkhairi ba sai ka amsa ba" jin haka yasa ta ce Amin a hankali tare da d'an kallon k'asa, kafin ya kara
cewa wani abu aka turo k'opar bedroom d'in gaba d'aya suka kai idanun su wurin Tk ne ya shigo shima
yana sanye da irin shaddar Amadun da alama anko su kai suna had'a ido da Fatuu ya washe baki ya
tunkaro su yana fad'in "Amaryar mu, amaryar mu" yadda ya furta sautin kaman Wak'a Fatun tana ta
murmushi ya k'araso bakin gadon shima ya zauna kusa da Amadu ya k'ara ce ma Fatuu dake kallon shi
Amaryar su ta gaida shi, da sauri yace "ah ai yanzu ni ne yakamata in rink'a gaishe dake tunda kin koma
Aunty na" bata ce komae ba tana dae ta murmushi ya juya kan Amadu yace "kaga ikon Allah ko, yanzu fa
dole in rink'a girmama ta tunda ta zama Matar Yayana kuma uban gidana" yar dariya Amadu yayi Tk d'in
ya juya kan Fatuu yace "Aunty Amarya Allah yasa dae a rink'a rangwanta man, a da daba k'ark'ashin ikon
ki nike ba ma baki d'aga man k'afa ba balle kuma yanzu da kike da cikakken iko dani...." Maida kallon shi
yay kan Amadu yace "AA (Ahmad Abdullahi) ka tuna can baya lokacin da aka sa in kaita yawon salla ta
maida ni kaman yaron ta tay ta wahalar dani?"

"na tuna mana har saida kay ciwon k'arya" ya k'arasa yana dariya shima Tk tuntsirewa yay da dariya
tunowa da lokacin, Fatuu ma dariyar take dama lokacin daga baya ta gane ciwon k'arya ne har ta fad'i
ma Haisam bayan ya dawo tace bata gama yawon ba har ta rok'e shi ya idasa kai ta hakan ne silar farkon
zuwan ta gidan Abbas, Amadu dake kallon shi yace "har ka kai Yayar Fauziyyar ta d'aukko sauran kayan?"
d'an girgiza kai Tk yay "No tace in bata makullin Motar ta iya sai

su d'aukko ni in huta shine na bata" kai Amadu ya d'aga Tk ya juya kan Fatuu dake kallon su, da
murmushi yace "na taya ki murna yar k'anwar mu yanzu kuma Auntyn mu, Allah ubangiji yasa Alkhairi ya
baku zaman lpy, wllh baki ji dad'in dana ji maki ba lokacin dana samu labarin auren, Ya Haisam cikakken
mutum ne harda ma rabi, samun shi matsayin abokin rayuwa abun a taya mutum murna ne sam bani da
shakku a kan shi don yayi 100% kuma kun bala'en dacewa wllh, zaku ji dad'in yin rayuwa tare don kun
riga da kun gama fahimtar juna, shine zai iya maki don ma yanzu naga kin natsu....au tuba nike Hajiya
tah su6ul da baka ne" gaba d'aya suka sa dariya ya k'ara cewa "dama ni ne mai kula da part d'in nan
wurin gyara shi, to yanzu Aunty zan ci gaba da aiki na ne ko yaya?" Yay tambayar idon shi akan Fatuu
dake ta faman sakin murmushi ta kasa ce mashi komae,

Amadu ne yace "ah dama ai don ba mata ne, yanzu kuma tunda gata na me kaci gaba ita zata rink'a
gyarawa" da sauri Tk yace "No ka bar Hajiyata ta yanke hukunci don itama tana da iko dani yanzu" ya
juya kan Fatuu yana fad'in ta yanke yadda za'ai sai Faman dariya take, da k'yar tace mashi ai ba ita zata
yanke hukunci ba Ya Haisam ne yace shikenan, ya juya kan Amadu yace "gaskiya AA yakamata muma fa
mu fara haramar shigewa daga ciki, ko da yake k'ilan ma sai na riga ka kai da ko budurwa nasan baka da
ita, ko kayi ta Yanzu?" Amadu dake murmushi ya girgiza mashi kai alamar a'a,

"Gaskiya yakamata ace by now kana da budurwa ko kuma ka tsaida wadda zaka aura tunda nasan ba'a
rasa masu son ka kaine kawae baka basu dama" Amadu dake yar dariya yace "No k'yale budurwar nan
bari dae in nemi kud'i su taru tukunna in lokacin auren yayi zaka ga bazan sha wahalan samu ba tunda na
gama had'uwa" dariya sosae Tk yasa bayan ya tsagaita yace "kuma wllh in dae kana da kud'i bazaka sha
wata wahalan samun irin Matar da kake so ba, wai ni yanzu yan mata na soyayya tsakani da Allah kuwa?
Ni kaina nan wai d'an ganin da ake ina fantamawa da motoci aka kuma ji gidan da nike kar kaso kaga
yadda yan mata suke lik'e man, nan basu san Almajiri bane" gaba d'aya sukai dariya Amadu yace ai
yanzu yafi k'arfin a ce mashi Almajiri shima ya zama dangin Senator d'in, suna haka aka turo k'opar duk
suka kai idanun su kan masu shigowar, Abbas ne da Saleem da k'yar Abbas ya matsa mashi suka shigo
don ya k'iya yace mi zai shigo ya yi, su Amadu na ganin su suka mik'e suna gaishe dasu kafin suka nufi
kopar fita su kuma suka k'arasa shigowa ciki idanun su akan Fatuu da itama kallon su take da d'an
murmushi haka Abbas ma murmushin yake mata, a gaban gadon suka tsaya yana kallon ta yace "Mom
Zarah Amaryar mu, an daina kukan ko?" Kai ta d'an d'aga mashi alamar eh kafin a Sanyaye ta gaishe dasu
suka amsa,

"haka yakamata ai kar ya haddasa maki wani ciwon muda muke so a biya mu abunda muka rasa a
yau......", bai rufe baki ba daga bayan shi yaji an ce "mi kake ci na baka na zuba ai kunsan dai ita d'in bata
wasa bace da kun bata zata biya ku" Aunty Mareeya ce da ta shigo ruk'e da kwalin kwalaben kayan
k'amshi tay Maganar duk suka juya har da Saleem suka kalleta Fatuu kuwa wata irin kunya ce ta rufe ta
da sauri ta sadda kan ta k'asa, shigowa tay cikin d'akin ta nufi wurin dressing mirror Abbas ya bita da
murmushi don sai ya d'an ji kunya duk da tun a Mota wurin kawo Fatuu ya fahimci bakin ta a sake yake
itama, Saleem ne ya kalli Fatuu cikin cool voice d'in shi yace mata Allah yasa Alkhairi bata amsa ba sai
d'an murmushi kawae tay mashi Aunty Mareeya ce ta amsa tare da juyowa ta kalle shi kafin ta maida
idon kan Abbas dake ta murmushi itama ta yi had'i da d'an girgiza kai tana a gaban dressing mirror, ta
fiddo wasu had'add'un kwalaben humra da turaren wuta tana jerawa a wurin a parlor ma ta jera wasu a
cikin gidajen da su tv suke sosae suka k'ara k'awata wurin, Saleem ne ya juya zai tafi Abbas dake kallon
Fatuu yace mata bari su je sai ya kawo mata Angonta Aunty Mareeya tay carab tace suna jiran shi yazo
ya siya bakin Amarya a wurin su tay Maganar tana dariya shima Abbas d'in dariyar yake ya juya suka fita,

bayan fitar su Fauzy ta shigo ruk'e da burner data gama turara parlor ta jona ta anan aka zuba turare
Bedroom d'in ya fara turaruwa shima Aunty Mareeya da ta gama ta shiga yi ma Fatuu bayanin yadda
zatay amfani da wasu daga cikin kayan kamshin ita dae kai kawai take d'aga mata, bayan an gama turara
d'akin Fauzy ta hau gyara bedroom d'in duk da ba wani 6aci yay ba tana cikin gyaran Aunty Mareeya ta
sake shigowa hannunta ruk'e da cup ta nufi side d'in da Fatuu take ta zauna a bakin gadon ta bata tace
ta shanye abun ciki, ba musu ta amsa ta kafa baki saida ta shanyen ta mik'a mata Cup d'in tace ta taso
zata nuna mata abu a kitchen tace mata to ta zuro da k'afafun ta ta mik'e suka nufi hanyar fita Fauzy
nata sakin wani kalan murmushi wanda da gani da biyu take yin shi, bayan sun je kitchen d'in bin d'akin
Fatuu tay da kallo an tsara shi ya koma babban Kitchen a ranta ta shiga tuna lokacin da ta fara shigowa
cikin shi yin fitsari da ta zo ba Haisam hak'uri da kuma lokacin da yay mata Assignment d'in maths tuna
lokacin har saida ta saki murmushi, waya ta6a tunanin wai d'akin zai zama kitchen d'inta gaba d'aya part
d'in ma, wata drawer Aunty Mareeya ta jawo ta ce ta matso, nuna mata abubuwan dake ciki tay wanda
sauran magungunan ta ne da aka siya mata a wurin Aunty Bee ta shiga yi mata bayanin yadda zata rinka
amfani da kowanne Fatun na d'aga mata kai har ta gama, tambayarta tay ko a cikin kitchen d'in akwae
abunda bata iya amfani da shi ba ta gwada mata, a sanyaye tace duk ta iya tana ganin yadda Aunty
Saude mai aikin nan gidan ke amfani da su Aunty Mareeyar tace da kyau daga haka suka fito suka koma
Bedroom d'in, suna komawa Feenah ta shigo tace ma Aunty Mareeya ance su fito za'a maida kowa gida
tace to dama sun gama mata komae ai, ta kalli Fatuu da tay zuru jin zancen zasu tafin ta tambaye ta
akwai wani abu ta girgiza mata kai sukuku da ita ta juya ta nufi wurin k'atuwar wardrobe d'in d'akin, a
gefenta ta d'aukko jakar ta ta dawo bakin gadon Feenah na tsaye, zuge zip d'in jakar tay ta kai hannu ta
ciro wata farar shopping bag mai d'auke da tambari ta d'aura ta akan cinyoyin Fatuu tace "Yar k'anwata
Amarya ga tawa gudunmawar nan saura kuma kice zaki k'i yin amfani dasu Saboda wai kunya, ke da shi
yanzu ba sauran wata kunya don kun riga kun zama abu d'aya, an san kunya abu ce mai kyau amman
yanzu a wani wurin in kika ce zaki saka kunya to zaki k'wari kan ki ne da kuma shi Mijin naki don haka ba
a komai zaki rink'a nuna kunya ba....." Katse ta Feenah tay da fad'in "ba kamar yadda take da kishiya
kuma ma baturiya, gaskiya dole sai kin zage wllh don su ba wata kunya gare su ba don ma ita tana ruwa
biyu....." Aunty Mareeya ta kar6e "kin ji dai ko, wannan nasan har yawo daga ita sai d'an pant in ma tasa
kenan tana iya yi a gaban shi, don haka ki zage wllh balle ke da ma kike da surar jan hankali Tubarkallah,
ki kuma dage da gyara jikin ki ciki da waje, duk magungunan da nayi maki bayani kada ki wasa da shan su
sannan kuma kada ki k'asa a guiwa wurin faranta mashi irin su ta nan wajan aka fi kama su, ki sashi ya
susuce ta yadda duk in zaiyi Magana sai ya ambaci sunan ki alamar kece a ran shi koda yaushe" gaba
d'aya suka sa dariya harda Fauzy dake can d'ayan side d'in gadon raku6e,

Feenah ta d'aura da fad'in "Bayan wad'annan kuma sai a had'a da biyayya don itace zata k'ara
taimakawa wurin siye zuciyar shi duk da nasan ke mai biyayya ce a gare shi tun ba yanzu ba, to ki k'ara
akan wadda kike mashi don yanzu ne zata fi yin aiki kuma zaki fi cin ribar yin ta, a k'arshe ina Addu'ar
Allah yasa Alkhairi a zaman ku ya had'a kawunan ku gaba d'aya da abokiyar zaman taki ya kauda fitina ya
bashi ikon yin Adalci a tsakanin ku, ya albarkace ku da zuria d'ayyiba" su Aunty Mareeya ne suka amsa
ita kuma Fatun kan ta na a k'asa, lokacin Abbas ya lek'o cikin d'akin yace su suke jira fa duk suka mik'e ya
d'aga murya yana ma Fatuu sai da safe, yana shirin juyawa Feenah tace don Allah ya taimaka mata da
Abdul yadda yay baccin nan ba iya d'aukar shi zatay ba ya k'arasa shigowa cikin d'akin ta kinkimo mashi
Abdul d'in ya kar6e shi ya sa6a a Shoulder yana fad'in Allah ma ya taimake su da yayi baccin ai da ba
k'aramar rigima za'ai dashi ba don yana iya cewa nan zai kwana ba kamar yana ganin gidan Baban shi da
Momy d'in shi ne duk sukai dariya ya juya ya nufi kopa suma suka bi bayan shi Fatuu ta fara k'ok'arin
saukkowa daga saman gadon Fauzy dake kallonta tace ina zata, jin haka yasa su Aunty Mareeya juyowa
suma suka tambayi inda zata fuskar ta kaman zatai kuka murya na d'an rawa tace raka su zatai, waro ido
tay tace a ina ta ta6a ganin Amarya tayi rakiya ta koma ta zauna kafin Angon ta ya zo, ba yadda ta iya
dole ta koma ta zauna suka tafi banda Fauzy da tay tsaye ta kasa tafiya yanayin fuskar ta ya sauya itama
kaman zata saka kukan, bin juna da ido sukai can k'walla suka zubo ma Fatuu sharrr Fauzy ta d'an girgiza
mata kai daga inda take tsaye tace "ki daina kuka Zarah lokacin farinciki ne yanzu, Allah yasa Alkhairi ya
baku zaman lafiya sai mun had'u School" da k'yar ta k'arasa Maganar, jin kuka na niyyar k'wace mata
yasa ta juya da sauri ta fita, tana fita Fatuu ta d'age k'afafunta ta kife fuskar ta tana kuka a
hankali.................

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2060*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


......... Lokacin da su Hajiya suka fito Abbas na tsaye bakin Jeep d'in da ya zo da ita har an shiga da Fatuu,
Aunty Mareeya da Feenah da inna Zaliha da Matar Baba shehu duk suka shiga ya juya kan sauran
k'awayen Fatuu da suka rage don wasu sun tafi ya nuna masu Jeep d'in Saleem yace su je su shiga harda
Fauzy ita ta shiga gaba sai Haulat, sauran wad'anda suka rage Abokan aikin gwaggo Hajiya ta nuna masu
Motar da Tk ya zo da ita suka shiga Amadu na a Front seat, kowa ya samu wuri sai wasu daga cikin
Makwabta ne basu samu ba Hajiya tace su taka a k'asa itama a k'asan zata duk akai dariya ta kira Abbas
yazo gaban su tace mashi su d'an zagayo da su Fateemar ita ma ta shaida an yi mata d'aukar Amare yana
murmushi yace to ya juya, Motar Saleem ya nufa ya zagaya driver side ya bud'e yana zauna ya d'an d'age
kan shi jikin headrest ya sanar dashi zasu d'an zagayo dasu roundabout ya jinjina mashi kai ya rufe mashi
kopar, saida yaje ya sanar ma Tk shima sannan ya dawo Motar tashi, lokaci guda gaba d'aya suka kunna
motacin sai lokacin gwaggo dake tsaye ta tuna da kayan Fatuu ta yi ma Hajiya Maganar ko a d'aukko
kafin su tafi tace ta bari in suka dawo sai Tukur yazo ya d'auka tace to, Tk ne ya fara jan tashi dama shine
a gaba lokacin da suka baro gidan Hajiya da zasu zo ya mik'i hanya Abbas ne a tsakiya sai ta Saleem
k'arshe suka tafi,

Bayan tafiyar su Hajiya tace masu su tafi su jira su acan gidan, har zasu tafi ganin an bar gidan a bud'e
yasa Hajiya cema gwaggo akwai sauran mutane ne a gidan za a bar shi a bud'e, sai lokacin ta ankare da
sauri ta juya tana fad'in ta manta Hajiya na cewa ko duk tafiyar Fateemar ce tasa ta rikicewa, bayan ta
shiga ta d'aukko wayar ta da makulli ta fito ta rufe gidan suka tafi, ta k'aramar kopa suka shiga suka nufi
part d'in Haisam, lokacin da suka shiga a gyare harabar take tsaf an gyare shukokin flowers d'in wurin
gwanin sha'awa suka nufi kopar shiga parlon, suna shiga makwabtan da aka je da su suka saki baki galala
suna bin parlon da kallo ga wani ni'imtaccen sanyin Ac had'i da fitinannan k'amshi da ya karad'e cikin
parlon, gwaggo dae sai d'an murmushi take itama tana k'are ma parlon kallo, parlon yana nan yadda
yake amman an k'ara wasu abubuwa kaman daga bayan L-shape ansa dining table mai kujeru hud'u
suma leather ne bak'ak'e sai daga gaba bangon dake kallon su an sa wani jigunannan console mai jan
hankali golden haka saman kujera L-shape an canza throw pillows an sake wasu masu design mai kyau
da d'aukar hankali, Carpet d'in k'asa ma an canza wani sabo wanda ke akwae da an maida shi wurin
dining table, haka flowers d'in dake a angles d'in parlon an k'ara wasu, d'an madaidaicin Fridge d'in dake
parlon an maida shi cikin kitchen sai sabon freezer da aka siya mata a cikin kayan kitchen aka aje shi a
parlon daga can wurin dining table, a jikin bangon parlon an manna manyan Frames harda mai Ayatul
kursiyyu, blinds d'in jikin Windows ma an canza su zuwa manyan labulaye wanda daka kalla ba sai an
fad'a maka ba zaka shaida masu kud'i ne Saboda had'uwar da sukai kuma sun hau da parlon sosae,
komae ya hau daidai nan aka shiga yabawa ana sa Albarka tare da Addu'oi, Hajiya tace masu su shiga
suga sauran d'akunan suka ce to suka nufi hanyar corridor, Bedroom d'in ma tsab dashi sai k'amshi ke
tashi nan ma an canza labulayen ciki haka gadon ma yasha babban bedsheet mai pillows da yawa ko a
ido ka kalle shi kasan zai yi mugun taushi, nan ma sosae suka yaba daga baya Hajiya tace suje su ga
Kitchen ta juya gaba suka bi bayanta, d'ayan d'akin da yake matsayin Lab d'in shi a da shine aka maida
mata kitchen d'in, bayan sun shiga ciki sosae shima suka yaba komae an tsara shi har a sama anyi
cabinet haka k'asan ma cikin kankanin lokaci an maida d'akin Kitchen na yan gayu, bayan sun gama gani
suka nufi Parlor sai faman yabo da san barka ake, duk suka zazzauna suna dakon isowar su Fatuu
farinciki Fal cikin zuciyar gwaggo har fuskar ta ta kasa 6oyewa sai d'an murmushi take ganin wai autar ta
ce zata rayu a cikin wurin, sai godiya take ga Allah acikin ran ta,

Tun da suka tafi Fatuu ke ta faman kuka har Abbas saida yay mata Magana yace gidan fa Ya Handsome
d'inta za'a kaita ba wani wurin ba ai farinciki yakamata tayi ba tay ta yin kuka ba sai kace za'a kaita inda
za'a cuta mata, Aunty Mareeya itama tace abun ya bata mamaki wannan kuka haka sai kace za'a kaita
gidan makiyinta Feenah ce tace "ai dole duk da hakan sai taji ba dad'i barin gidan da ka saba rayuwa a
ciki ka koma wani wuri ba abu bane da ba za'a ji komai ba", inna Zaliha tace gaskiya ne ba kamar yadda
suka shak'u da gwaggon ta,

Aunty Mareeya tace "hakane, amman dae kukan yayi yawa bai kamata ta sama kanta damuwa ba tunda
dai ga baki ga hanci ba nisa tayi da gida ba, muda aka d'aukko daga wani gari sai an dad'e kafin muje gida
ita kuwa data fito fa zata ga gidan koda bata shiga ba zata ji dad'i, gani ma zatayi tamkar ba ta bar gidan
ba tunda duk unguwa d'aya ne kuma in taso ma kullum taje nasan ba zai hana ba" inna Zaliha dake d'an
murmushi tace "hakane amman dai kar ace kullum sai anje d'in hakan bai kamata ba, ita mace ta zauna a
d'akinta shi yafi mutunci ba kullum ai ta ganinta tana sunturi a waje ba hakan bai dace ba" gaba d'aya
suka ce gaskiya ne harda Abbas, saida suka shawo roundabout na Barhim sannan suka koma. A cikin
kwanar gate suka parker Motocin bayan sun iso duk aka firfito Aunty Mareeya na ruk'e da Fatun gefenta
Abdul ne ruk'e da hannunta guda suka shiga ta k'aramar k'opa da sauran Mutane, lokacin da suka
k'araso bakin kopar shiga parlon Aunty Mareeya ta tsaya da ita tace tayi Addu'a sannan ta shiga da k'afar
dama wad'anda ke a bayan su duk suka tsaya saida ta gama sannan suka shige sauran suka bi bayan su,
suna shiga d'aya daga cikin makwabtan dake zaune suna jiran isowar su ta mik'e ta rangad'a gud'a mai
sautin gaske su Hajiya suka shiga sakin murmushi itama ta mik'e ta nuna masu inda zasu shiga da ita
kowa ya baza ido yana k'are ma parlon kallo, hardae Aunty Mareeya da Feenah bin parlon suke da kallo
don ba k'aramin had'uwa yay ba ya matuk'ar burge kowa ga wani irin k'amshi mai had'e da sanyin Ac da
ya baza ko ina na parlon, Fauzy ma ta jinjina had'uwar wurin har d'an jinjina kai take haka sauran
k'awayen su Zainab Muhammadu ma baki bud'e take k'are mashi kallo, ba wanda ma yay tunanin kayan
ciki wai ba sababbi bane don kana kallon su zaka ga sabunta a tattare dasu tunda dama iya Haisam d'in
kadae ne ke amfani dasu kuma masu matuk'ar inganci ne hakan yasa sam basu canza daga yanayin da
aka siyo su ba, Saude ce tay masu jagora zuwa Bedroom d'in nan ma saida aka sa Fatun tayi Addu'a a
bakin kopar shiga sannan ta shiga da k'afar dama aka wuce ciki da ita wurin gado, nan ma dae sosae
Mutane suka yaba anata Addu'oi, a can tsakiyar gadon aka sa ta haye ta zauna ta jingina da headboard
kanta na sadde cikin gyale Fauzy ma ta hau ta zauna gefen ta haka Abdul ma har lokacin yana ruk'e da
hannunta duk ya damu tun da yaga tana kuka shima a Mota har kukan yayi yana fad'in ta daina kuka,
bayan an gama ganin Bedroom d'in har Laundary room da toilet saida mutane suka shiga suka gani
harda su Aunty Mareeya, bayan sun gama dubawa suka fita zuwa Kitchen ya rage daga Fauzy sai sauran
k'awayen su, su Zainab dake zaune a bakin gadon sai faman santi suke suna Allah ya maida su damshin
Fatuu Fauzy na dariya take amsa masu Zainab tace suje suga sauran wuraren suma duk suka mik'e suka
nufi laundry Fauzy ta juya ta kalli Fatuu da har lokacin bata d'ago ba ta kai hannu ta d'an d'aga gyalen ta
lek'a fuskar ta suka had'a ido idanun nata sun yi jawur Fauzy ta jawota jikinta tana Fad'in "Haba Amaryar
Ya Haisam kukan ya isa hakanan, keda zaki murna ki farinciki Allah ya cika maki burin ki yau gaki a gidan
shi a d'akin ki mallakin ku keda shi, don Allah kiyi hakuri kar kija ma kan ki wani ciwon a wannan daren
mai daraja da zaku idasa dunk'ulewa ku zama abu d'aya" d'aga idanunta da suka sauya kala tay ta d'an
kalli Fauzyn dake ta sakin murmushi wanda da gani da biyu take yin shi, yar harara Fatuu ta jefa mata ta
maida kan ta k'asa Abdul dake a jikinta shima yace "Aunty Fatuu kar ki k'ara yin kuka don Allah, Baba
Zakee ba zai cuce ki ba kuma zai rink'a siya maki kayan dad'i da yawa harda Computer ki rink'a yin game"
d'an murmushi tay ta d'aga mashi kai kafin ta kai hannunta da ya sha k'unshi da had'add'un awarwaro
yan manya guda hud'u sai zobba guda biyu ta shafi fuskar Abdul d'in yaron yana k'aunar ta sosae, d'aga
ido Fauzy tay tana k'ara kallon d'akin tace yakamata a k'ara sa turaren wuta cikin wanda Aunty Mareeya
ta kawo tace bari tay mata magana ta sauka daga saman gadon ta nufi kopar fita, tana fita parlon taga
ba kowa a ciki tun bayan da suka gama dudduba ko'ina Hajiya tace atafi part d'in ta a ci Abinci kar a 6ata
ma Amarya nata shine aka d'unguma aka tafi can, wayar ta ta fiddo daga cikin side bag d'inta ta fara
k'ok'arin kiran Auntyn bayan tayi picking ta tambaye ta suna ina ta fad'i mata tace gata nan zuwa, fita
tay daga cikin parlon bayan ta fito part d'in duk da bata san in da part d'in Hajiyar yake ba bata sha
wuyar gane hanyar da zata bi ba saboda ko ina fayau yake da haske tamkar da rana, tana shigowa
harabar ta hango part d'in ta nufe shi, bayan fitar Fauzy a hankali Fatuu tasa hannu ta yaye gyalen kanta
yadda fuskar ta ta fito sosae, d'aga kai tay ta fara bin bedroom d'in da kallo har yanzu ganin abun take
tamkar ba gaske ba kaman mafarki ne, wai yau itace a cikin bedroom d'in Ya Haisam a saman gadon shi
kuma ma a matsayin matar shi Allah kenan buwayi gagara misali acikin ikon sa komai mai yuwuwa ne
cikin sauki, cigaba da k'are ma d'akin kallo tay iya fentin shi abun burgewa ne balle kuma rantsattsun
tsadaddun furniture d'in ciki, sam d'akin baida hayaniya ga wasu jigunannan labulaye, bedsheet d'in
saman gadon cikin wanda Hajiya ta siya mata ne lokacin da za'ai mata aure da kayan kitchen har saida ta
kai hannunta ta d'an ta6a jikin shi gwanin taushi, tana haka ta shiga tunano can baya tun daga kan
farkon ganin shi lokacin da ya raba su fad'a da Jameela mai awara, a nutse taci gaba da tunanin baya sai
faman sakin murmushi take lokacin ta tuno da ran da tazo kawo mashi takardar list d'in littattafan da
yace taje ta d'aukko bata gan shi a parlon ba ta zo bakin corridor ta tsaya tana yin sallama tace ga
takardan, jin shiru bai amsa ba yasa tace ko ta shigo ne ta kawo mashi ya bata amsa da tunda d'akin ta
ne ai sai ta shiga daga bayanta ashe bai a cikin d'akin, wani irin murmushi ta saki har fararen hak'oran ta
suka d'an bayyana a ranta ta ayyana yanzu gashi ya zama nawa d'in gani ma zaune a saman gadon ka,
k'ara tunano lokacin da zai kaita makaranta tay da tace don dai ita k'arama ce da sun yi soyayya kuma in
ta gama Secondary School cigaba zatai da karatu yace to ko ya jirata ne tace ai lokacin ita ta zama
babbar budurwa shi ya kuma ya tsufa, tace in yana so zata had'a shi da yar ajin su sofiya moussa yace bai
sata ba daga baya kuma ta hau yi ma safiyar sharri har tana ba ma lalle ya so ta ba don k'aton baki gare
ta hak'oranta kuma sun d'an turo kuma bata da jiki kamar sandar suluka take, tunano hakan har saida
tay dariya mai d'an sauti, ita kanta tasan tayi ma Haisam hauka iri iri kafin ta girma amman bai ta6a yin
fushi da ita ba ko ya canza mata, in ma tayi abunda ya nuna ta 6ata mashi rai da ta bashi hak'uri yake
hak'ura, tabbas dole ne ka ra6i Haisam sai ya burge ka don komai nashi na musamman ne samun irin shi
wanda ya had'a abubuwan da ya had'a zai matuk'ar wahala, ga tsantsar kyau, ga kud'i, ga kirki, ga hali
mai kyau, ga ilimi, ita kam ko iya haka ta gode ma Allah don ya gama mata komai samun Haisam a
matsayin miji ba k'aramar baiwa bace wllh, wata zuciyar ce ta raya mata in kuma bai son ta fa kuma
dangin shi suka k'i amincewa da ita, sosae jikinta yay sanyi lakwas yin wannan tunanin, tasan koda bai
son ta bazai cutar da ita ba tana da tabbacin hakan inda za'a samu matsala wurin dangin nashi ne in basu
amince da ita ba ga kuma matar shi Fanan, sosae Fatuu ke jin zullumin abunda zai je ya dawo in ta samu
labarin auren nasu don ita shaida ta kan irin son da take ma Ya Haisam ga hirar da ta ta6a ji yana yi da
Abbas da ta tabbatar da cewa Fanan d'in ce ta fara son shi da ya nuna baiso shine har ta kwanta gadon
Asibiti, tsayawa tay da yin tunane tunanen Saboda gaba d'aya jikinta ya mutu ta zuba ma bangon da take
facing ido a ranta ta shiga ayyana ita bazata so Ya Haisam ya shiga matsala Saboda ita ba, in dae bai son
ta da bai cigaba da zama da ita ba, wata zuciyar tace ki ka sani ko yana son ki kaman yadda ake hasashe
tunda har abu ya shiga tsakani kuma ya nuna rashin jin dad'i da kika zubar da cikin, shiru tay don a
wannan ga6ar baza ta iya yanke hukunci ba duk da a yanzu tasan gaba d'aya abunda ya farun bada niyya
bane kuma da ya nuna yayi fushi kan abunda tay k'ilan don aikata hakan laifi ne kaman yadda ya fad'a
mata da taje bashi hak'uri da kuma gudun kar wani abu ya faru da ita ba wai don yana son cikin ba ko ita,
haka tay ta sak'e sak'e, jin Abdul yay tsit yasa ta kai idonta kan shi taga ashe yayi bacci ta fara k'ok'arin
gyara mashi kwanciya a gefen ta tana cikin haka taji an turo kopar Bedroom d'in ta kai idonta da sauri,
Kawu Amadu ne ya shigo yana sanye da sabuwar shadda light blue da ya d'inka musamman Saboda
ranar, suna had'a ido suka sakar ma juna murmushi ya iso bakin gadon ya zauna sai faman murmushi
take mashi ta kasa yi mashi magana,

"Amarya, Allah dai ya amince Romeo ya zama naki" ya fad'a yanata murmushi still itama murmushin
take ta k'i cewa komae,

"Ko duk Farin ciki ne ya hana ki magana?" Ya fad'a yana murmushi da sauri tasa tafukan hannuwanta
da suka sha k'unshi ta rufe fuskar ta, bayan ta cire tana kallon shi yace "kinga ikon Allah ko?" Kai ta d'aga
mashi alamar eh, "zaki iya tuna abunda na fad'a maki a can baya lokacin dana iske ki a d'aki cikin
mawuyacin hali har kika fad'a man Saboda Ya Haisam ne?" Shiru bata ce mashi komae ba ta maida
idanun ta k'asa, yaci gaba "lokacin na fad'i maki in Ya Haisam rabon ki ne kina zaune ba tare da wata
wahala ba za ki ga yazo ya Aure ki har kita mamakin yadda akai hakan, kin tuna?" d'agowa tay ta kalle shi
tare da d'aga mashi kai, yaci gaba "kin ga maganata ta tabbata, Wannan kad'an ne daga cikin ikon Allah,
in dae zaka dogara gare shi to tabbas zaka samu biyan buk'ata ba kamar in ka had'a da hakuri da kuma
Addu'a, in kika ga duk kin yi wannan amman bukatan ki bata biya ba to abun ba Alkhairi bane gare ki sai
ya musanya maki da wanda yake Alkhairin, shi yasa ake son bawa ya kasance mai yawan godiya ga Allah,
in ka samu ka gode mashi haka in ka rasa, a koda yaushe in zaka yi Addu'a to ka rok'i abunda yafi zama
Alkhairi a gare ka, duk abunda kaga kasamu to shine yafi Alkhairi, Allah ubangiji da kan shi acikin suratul
baqara yace zaku so wani Al'amari alhali ba Alkhairi bane a gare ku, haka zaku K'i wani Al'amari alhali
Alkhairi ne a gare ku, Allah ne mafi sani ko baku sani ba, to kinga ba buk'atan ka matsa ma kan ka akan
dole sai ka samu wani abu tunda ga mai badawa wanda ya san abun Alkhairi ne a tare da kai ko sharri
sai ka mik'a komai a Wurin shi ka dage da Addu'a, a k'arshe ina taya ki murnar samun abunda ran ki ke
so ina fatan kuma ku zame ma juna Alkhairi, Allah ubangiji ya bashi ikon ruk'e ki da Amana ya kauda
dukkan wata fitina, kema Allah ya baki ikon yi mashi biyayya ya albarkace ku da zuria d'ayyiba Amin"
idon shi a Kanta ya k'arasa fuskar ta da d'an murmushi take kallon shi ba tare da ta ce komae ba, d'an
tsuke fuska yay yace "ba zaki ce Amin ba" d'an yamutsa fuska tay ta d'an sa hannu ta rufe wurin idanun
ta alamar kunya, yace "ke ni zaki wani nuna ma ke mai kunya ce, miye abun kunya an roka maka abun
Alkhairi ba sai ka amsa ba" jin haka yasa ta ce Amin a hankali tare da d'an kallon k'asa, kafin ya kara
cewa wani abu aka turo k'opar bedroom d'in gaba d'aya suka kai idanun su wurin Tk ne ya shigo shima
yana sanye da irin shaddar Amadun da alama anko su kai suna had'a ido da Fatuu ya washe baki ya
tunkaro su yana fad'in "Amaryar mu, amaryar mu" yadda ya furta sautin kaman Wak'a Fatun tana ta
murmushi ya k'araso bakin gadon shima ya zauna kusa da Amadu ya k'ara ce ma Fatuu dake kallon shi
Amaryar su ta gaida shi, da sauri yace "ah ai yanzu ni ne yakamata in rink'a gaishe dake tunda kin koma
Aunty na" bata ce komae ba tana dae ta murmushi ya juya kan Amadu yace "kaga ikon Allah ko, yanzu fa
dole in rink'a girmama ta tunda ta zama Matar Yayana kuma uban gidana" yar dariya Amadu yayi Tk d'in
ya juya kan Fatuu yace "Aunty Amarya Allah yasa dae a rink'a rangwanta man, a da daba k'ark'ashin ikon
ki nike ba ma baki d'aga man k'afa ba balle kuma yanzu da kike da cikakken iko dani...." Maida kallon shi
yay kan Amadu yace "AA (Ahmad Abdullahi) ka tuna can baya lokacin da aka sa in kaita yawon salla ta
maida ni kaman yaron ta tay ta wahalar dani?"

"na tuna mana har saida kay ciwon k'arya" ya k'arasa yana dariya shima Tk tuntsirewa yay da dariya
tunowa da lokacin, Fatuu ma dariyar take dama lokacin daga baya ta gane ciwon k'arya ne har ta fad'i
ma Haisam bayan ya dawo tace bata gama yawon ba har ta rok'e shi ya idasa kai ta hakan ne silar farkon
zuwan ta gidan Abbas, Amadu dake kallon shi yace "har ka kai Yayar Fauziyyar ta d'aukko sauran kayan?"
d'an girgiza kai Tk yay "No tace in bata makullin Motar ta iya sai

su d'aukko ni in huta shine na bata" kai Amadu ya d'aga Tk ya juya kan Fatuu dake kallon su, da
murmushi yace "na taya ki murna yar k'anwar mu yanzu kuma Auntyn mu, Allah ubangiji yasa Alkhairi ya
baku zaman lpy, wllh baki ji dad'in dana ji maki ba lokacin dana samu labarin auren, Ya Haisam cikakken
mutum ne harda ma rabi, samun shi matsayin abokin rayuwa abun a taya mutum murna ne sam bani da
shakku a kan shi don yayi 100% kuma kun bala'en dacewa wllh, zaku ji dad'in yin rayuwa tare don kun
riga da kun gama fahimtar juna, shine zai iya maki don ma yanzu naga kin natsu....au tuba nike Hajiya
tah su6ul da baka ne" gaba d'aya suka sa dariya ya k'ara cewa "dama ni ne mai kula da part d'in nan
wurin gyara shi, to yanzu Aunty zan ci gaba da aiki na ne ko yaya?" Yay tambayar idon shi akan Fatuu
dake ta faman sakin murmushi ta kasa ce mashi komae,

Amadu ne yace "ah dama ai don ba mata ne, yanzu kuma tunda gata na me kaci gaba ita zata rink'a
gyarawa" da sauri Tk yace "No ka bar Hajiyata ta yanke hukunci don itama tana da iko dani yanzu" ya
juya kan Fatuu yana fad'in ta yanke yadda za'ai sai Faman dariya take, da k'yar tace mashi ai ba ita zata
yanke hukunci ba Ya Haisam ne yace shikenan, ya juya kan Amadu yace "gaskiya AA yakamata muma fa
mu fara haramar shigewa daga ciki, ko da yake k'ilan ma sai na riga ka kai da ko budurwa nasan baka da
ita, ko kayi ta Yanzu?" Amadu dake murmushi ya girgiza mashi kai alamar a'a,

"Gaskiya yakamata ace by now kana da budurwa ko kuma ka tsaida wadda zaka aura tunda nasan ba'a
rasa masu son ka kaine kawae baka basu dama" Amadu dake yar dariya yace "No k'yale budurwar nan
bari dae in nemi kud'i su taru tukunna in lokacin auren yayi zaka ga bazan sha wahalan samu ba tunda na
gama had'uwa" dariya sosae Tk yasa bayan ya tsagaita yace "kuma wllh in dae kana da kud'i bazaka sha
wata wahalan samun irin Matar da kake so ba, wai ni yanzu yan mata na soyayya tsakani da Allah kuwa?
Ni kaina nan wai d'an ganin da ake ina fantamawa da motoci aka kuma ji gidan da nike kar kaso kaga
yadda yan mata suke lik'e man, nan basu san Almajiri bane" gaba d'aya sukai dariya Amadu yace ai
yanzu yafi k'arfin a ce mashi Almajiri shima ya zama dangin Senator d'in, suna haka aka turo k'opar duk
suka kai idanun su kan masu shigowar, Abbas ne da Saleem da k'yar Abbas ya matsa mashi suka shigo
don ya k'iya yace mi zai shigo ya yi, su Amadu na ganin su suka mik'e suna gaishe dasu kafin suka nufi
kopar fita su kuma suka k'arasa shigowa ciki idanun su akan Fatuu da itama kallon su take da d'an
murmushi haka Abbas ma murmushin yake mata, a gaban gadon suka tsaya yana kallon ta yace "Mom
Zarah Amaryar mu, an daina kukan ko?" Kai ta d'an d'aga mashi alamar eh kafin a Sanyaye ta gaishe dasu
suka amsa,

"haka yakamata ai kar ya haddasa maki wani ciwon muda muke so a biya mu abunda muka rasa a
yau......", bai rufe baki ba daga bayan shi yaji an ce "mi kake ci na baka na zuba ai kunsan dai ita d'in bata
wasa bace da kun bata zata biya ku" Aunty Mareeya ce da ta shigo ruk'e da kwalin kwalaben kayan
k'amshi tay Maganar duk suka juya har da Saleem suka kalleta Fatuu kuwa wata irin kunya ce ta rufe ta
da sauri ta sadda kan ta k'asa, shigowa tay cikin d'akin ta nufi wurin dressing mirror Abbas ya bita da
murmushi don sai ya d'an ji kunya duk da tun a Mota wurin kawo Fatuu ya fahimci bakin ta a sake yake
itama, Saleem ne ya kalli Fatuu cikin cool voice d'in shi yace mata Allah yasa Alkhairi bata amsa ba sai
d'an murmushi kawae tay mashi Aunty Mareeya ce ta amsa tare da juyowa ta kalle shi kafin ta maida
idon kan Abbas dake ta murmushi itama ta yi had'i da d'an girgiza kai tana a gaban dressing mirror, ta
fiddo wasu had'add'un kwalaben humra da turaren wuta tana jerawa a wurin a parlor ma ta jera wasu a
cikin gidajen da su tv suke sosae suka k'ara k'awata wurin, Saleem ne ya juya zai tafi Abbas dake kallon
Fatuu yace mata bari su je sai ya kawo mata Angonta Aunty Mareeya tay carab tace suna jiran shi yazo
ya siya bakin Amarya a wurin su tay Maganar tana dariya shima Abbas d'in dariyar yake ya juya suka fita,

bayan fitar su Fauzy ta shigo ruk'e da burner data gama turara parlor ta jona ta anan aka zuba turare
Bedroom d'in ya fara turaruwa shima Aunty Mareeya da ta gama ta shiga yi ma Fatuu bayanin yadda
zatay amfani da wasu daga cikin kayan kamshin ita dae kai kawai take d'aga mata, bayan an gama turara
d'akin Fauzy ta hau gyara bedroom d'in duk da ba wani 6aci yay ba tana cikin gyaran Aunty Mareeya ta
sake shigowa hannunta ruk'e da cup ta nufi side d'in da Fatuu take ta zauna a bakin gadon ta bata tace
ta shanye abun ciki, ba musu ta amsa ta kafa baki saida ta shanyen ta mik'a mata Cup d'in tace ta taso
zata nuna mata abu a kitchen tace mata to ta zuro da k'afafun ta ta mik'e suka nufi hanyar fita Fauzy
nata sakin wani kalan murmushi wanda da gani da biyu take yin shi, bayan sun je kitchen d'in bin d'akin
Fatuu tay da kallo an tsara shi ya koma babban Kitchen a ranta ta shiga tuna lokacin da ta fara shigowa
cikin shi yin fitsari da ta zo ba Haisam hak'uri da kuma lokacin da yay mata Assignment d'in maths tuna
lokacin har saida ta saki murmushi, waya ta6a tunanin wai d'akin zai zama kitchen d'inta gaba d'aya part
d'in ma, wata drawer Aunty Mareeya ta jawo ta ce ta matso, nuna mata abubuwan dake ciki tay wanda
sauran magungunan ta ne da aka siya mata a wurin Aunty Bee ta shiga yi mata bayanin yadda zata rinka
amfani da kowanne Fatun na d'aga mata kai har ta gama, tambayarta tay ko a cikin kitchen d'in akwae
abunda bata iya amfani da shi ba ta gwada mata, a sanyaye tace duk ta iya tana ganin yadda Aunty
Saude mai aikin nan gidan ke amfani da su Aunty Mareeyar tace da kyau daga haka suka fito suka koma
Bedroom d'in, suna komawa Feenah ta shigo tace ma Aunty Mareeya ance su fito za'a maida kowa gida
tace to dama sun gama mata komae ai, ta kalli Fatuu da tay zuru jin zancen zasu tafin ta tambaye ta
akwai wani abu ta girgiza mata kai sukuku da ita ta juya ta nufi wurin k'atuwar wardrobe d'in d'akin, a
gefenta ta d'aukko jakar ta ta dawo bakin gadon Feenah na tsaye, zuge zip d'in jakar tay ta kai hannu ta
ciro wata farar shopping bag mai d'auke da tambari ta d'aura ta akan cinyoyin Fatuu tace "Yar k'anwata
Amarya ga tawa gudunmawar nan saura kuma kice zaki k'i yin amfani dasu Saboda wai kunya, ke da shi
yanzu ba sauran wata kunya don kun riga kun zama abu d'aya, an san kunya abu ce mai kyau amman
yanzu a wani wurin in kika ce zaki saka kunya to zaki k'wari kan ki ne da kuma shi Mijin naki don haka ba
a komai zaki rink'a nuna kunya ba....." Katse ta Feenah tay da fad'in "ba kamar yadda take da kishiya
kuma ma baturiya, gaskiya dole sai kin zage wllh don su ba wata kunya gare su ba don ma ita tana ruwa
biyu....." Aunty Mareeya ta kar6e "kin ji dai ko, wannan nasan har yawo daga ita sai d'an pant in ma tasa
kenan tana iya yi a gaban shi, don haka ki zage wllh balle ke da ma kike da surar jan hankali Tubarkallah,
ki kuma dage da gyara jikin ki ciki da waje, duk magungunan da nayi maki bayani kada ki wasa da shan su
sannan kuma kada ki k'asa a guiwa wurin faranta mashi irin su ta nan wajan aka fi kama su, ki sashi ya
susuce ta yadda duk in zaiyi Magana sai ya ambaci sunan ki alamar kece a ran shi koda yaushe" gaba
d'aya suka sa dariya harda Fauzy dake can d'ayan side d'in gadon raku6e,

Feenah ta d'aura da fad'in "Bayan wad'annan kuma sai a had'a da biyayya don itace zata k'ara
taimakawa wurin siye zuciyar shi duk da nasan ke mai biyayya ce a gare shi tun ba yanzu ba, to ki k'ara
akan wadda kike mashi don yanzu ne zata fi yin aiki kuma zaki fi cin ribar yin ta, a k'arshe ina Addu'ar
Allah yasa Alkhairi a zaman ku ya had'a kawunan ku gaba d'aya da abokiyar zaman taki ya kauda fitina ya
bashi ikon yin Adalci a tsakanin ku, ya albarkace ku da zuria d'ayyiba" su Aunty Mareeya ne suka amsa
ita kuma Fatun kan ta na a k'asa, lokacin Abbas ya lek'o cikin d'akin yace su suke jira fa duk suka mik'e ya
d'aga murya yana ma Fatuu sai da safe, yana shirin juyawa Feenah tace don Allah ya taimaka mata da
Abdul yadda yay baccin nan ba iya d'aukar shi zatay ba ya k'arasa shigowa cikin d'akin ta kinkimo mashi
Abdul d'in ya kar6e shi ya sa6a a Shoulder yana fad'in Allah ma ya taimake su da yayi baccin ai da ba
k'aramar rigima za'ai dashi ba don yana iya cewa nan zai kwana ba kamar yana ganin gidan Baban shi da
Momy d'in shi ne duk sukai dariya ya juya ya nufi kopa suma suka bi bayan shi Fatuu ta fara k'ok'arin
saukkowa daga saman gadon Fauzy dake kallonta tace ina zata, jin haka yasa su Aunty Mareeya juyowa
suma suka tambayi inda zata fuskar ta kaman zatai kuka murya na d'an rawa tace raka su zatai, waro ido
tay tace a ina ta ta6a ganin Amarya tayi rakiya ta koma ta zauna kafin Angon ta ya zo, ba yadda ta iya
dole ta koma ta zauna suka tafi banda Fauzy da tay tsaye ta kasa tafiya yanayin fuskar ta ya sauya itama
kaman zata saka kukan, bin juna da ido sukai can k'walla suka zubo ma Fatuu sharrr Fauzy ta d'an girgiza
mata kai daga inda take tsaye tace "ki daina kuka Zarah lokacin farinciki ne yanzu, Allah yasa Alkhairi ya
baku zaman lafiya sai mun had'u School" da k'yar ta k'arasa Maganar, jin kuka na niyyar k'wace mata
yasa ta juya da sauri ta fita, tana fita Fatuu ta d'age k'afafunta ta kife fuskar ta tana kuka a
hankali.................

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2061*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.......bayan su Aunty Mareeya sun fito saida suka koma part d'in Hajiya suka k'ara yi mata Allah yasa
Alkhairi sannan sukai mata sallama tana ta godiya duk aka fito harda su inna Zaliha da tun d'azu suka so
tafiya Hajiya tace su bari za'a maida su gwaggo ta biyo su tace suje gida don Allah zata basu kayan biki,
Motar Saleem Abbas yace su Aunty Mareeya da Feenah su shiga gwaggo ma ta shiga shi kuma ya d'auki
su inna Zaliha da iyalan baba shehu sai wasu abokan aikin gwaggo da suka rage su biyu, a daidai kopar
gidan su Fatuu suka tsaya gwaggon ta shiga ta d'ebo ma kowannensu su cin cin harda man shanu, bayan
ta kawo masu suka yi sallama tana ta godiya tace ma Fauzy saura ta daina ganin ta tunda k'awar ta ta
bar gidan tana yar dariya tace a'a zata rink'a zuwa har weekend ma zata rink'a zuwan mata, sosae
gwaggo taji dad'i tace to Allah ya bada iko suka tafi tana ta k'ara godiya tare da d'aga masu hannu, saida
sukai nisa sannan ta koma ta kullo gidan ta nufi gidan Hajiya don bata yi mata sallama ba ta taho, tana
tafiya tana tunanin autar ta sai murmushi take wani lokacin ta d'an girgiza kai, har ta fara jin kewar ta
tana son ta gan ta saidae ba dama don bazata iya zuwa part d'in ba a yanzu.

Feenah aka fara ajewa gida don tafi kusa tay ma Saleem d'in godiya sukai sallama dasu Aunty Mareeya
har tana fad'in taga gida zasu rink'a zumunci in sha Allahu tace to shikenan ta gode, dama sun yi
musayar lambar waya tun a gidan su Fatuu kafin akai ta, daga nan Goriba road suka nufa aka kai Aunty
Mareeya, bayan ta nuna mashi gidan ya parker tay mashi godiya ya jinjina mata kai ba tare da ya ce
komae ba ta bud'e kopar ta fita Fauzy dake a gaba ma ta fito bayan sun rufe mashi kopopin yaja ya tafi,
tsaye Aunty Mareeya tay baki bud'e tabi bayan Motar da kallo kafin tace "da alama shima wannan
lalurar gare shi" kallon bayan Motar da har tayi nisa Fauzy tay kafin ta juyo ta kalli Aunty Mareeya cikin
rashin fahimta ta tambayi wace irin lalura gare shi, tace "irin ta mijin Zarah mana, daga gani shima miskili
ne na gaske" yar dariya Fauzy tay "na lura da hakan don ko d'azun da za'a kai Zarah da muka hau Motar
shi bai ce ma kowa uffan ba sai d'an Music da ya kunna sama sama" Aunty Mareeya dake kallon ta tace
"da gani dai wani shege ne ko kuma d'an wani shegen shiyasa harda rufe lambar Mota, baice yana son ki
ba?" ta kafe Fauzy da ido alamar jiran amsa, dariya Fauzy tay "taya zai ce yana sona na fad'i maki tunda
muka hau Motar shi bai ce mana uffan ba, kema ba gashi kin gani ba har kin fad'a" k'wafa tay tace
"Allah ya yabawa aya zak'in ta, ai da ya sake yace yana son ki har abun ya kai ga aure da an taimaka
mashi an sashi ya rink'a magana shima yadda za'a sa abokin shi, Allah sarki Zarah...." Murmushi tay
kawae bata ida abunda zata ce ba ta nufi gate Fauzy tabi bayanta acikin ranta tana tuna k'awarta Fatuu
dama tunda suka baro ta ta tsaya mata a rai, a yanzu kuwa sai taji ta fara sha'awar yin aure itama.

Gwaggo na isa part d'in Hajiya a parlor ta same su kaman yadda ta barsu ita da Saude sai dae ita Sauden
tana kitchen tana yin girki musamman don su Fatuu kaman yadda Hajiya ta bata umarni, zama gwaggon
tay Hajiya tace har ta sallame su tace mata eh suka d'an ci gaba da yin hira suna kallo, can gwaggo tace
bari ta tafi sai Allah ya kaimu ta k'ara yi mata godiya da Addu'oi, tana k'ok'arin mik'ewa Hajiya tace ta
tsaya zasu je wurin Zarah yanzu sai suje tare tasan dae bata rasa mararin son ganin ta, cike da Zolaya tay
Maganar gwaggo dai d'an murmushi kawai tay ta sadda kai, bada jimawa ba Saude ta shigo cikin parlon
hannunta ruk'e da wani had'add'an basket mai d'auke da k'awatattun Warmers, a gefen kujera ta tsaya
cike da girmamawa tace ma Hajiya an gama, kokarin mik'ewa ta fara yi tace ma gwaggo suje itama ta
mik'e, har zasu tafi tace ma Saude taje saman gadon ta towels na nan da aka manta ba'a saka mata a
kaya ba ta d'aukko a kai mata tace to, bayan ta dawo ta d'auki basket d'in d'ayan hannun rungume da
towels d'in da ta d'aukko suka tafi. Tun bayan da su Fauzy suka tafi ta kife fuska tana kuka sai da ta d'an
d'auki lokaci a haka sannan ta d'ago idanunta duk kwalla tay zuru tana d'an kalle kallen d'akin, can ta kai
hannu ta cikin ledan da Aunty Mareeya ta bata ta fiddo abun da ke ciki, bata gane ko miye ba saida tasa
d'ayan hannun ta bud'e sannan ta ga ashe rigar bacci ce orange colour ta dai had'u ba karya yadin ta
gwanin santsi irin mai bin jiki d'in nan kuma bazata wuce guiwa ba tana da d'an fingilallan pant mak'ale a
jikinta, ajeta tay gefe ta zazzago sauran da ke ciki guda biyu, d'aya baby pink ce shara shara wannan da
k'yar ta wuce mazaunan mutum irin wadda in aka sa a naked za'a ga mutum har saida Fatuu ta d'an
bud'a ido ganin rigar, d'ayar ta karshe cream ce yadinta cotton ne mai dad'in tabawa gwanin taushi daga
wurin wuyanta da k'arshen hannun ta da zai iya wuce guiwar hannu duk gashi gashi ne gazar gazar yana
d'an walwali harda ribbom gareta, itama tana da pant sai dai gabanta a bud'e yake kawai yan igiyoyi
gareta wuri ukku da zaka daure, har saida Fatuu ta d'an sauke ajiyar zuciya fuskarta a d'an kwa6e take
bin rigunan da kallo ita kam bata jin zata iya amfani dasu a yanzu gani take zai iya mata kallon mara
kunya, maida su tay cikin ledan ta d'an yi jimm can kuma ta mik'e ta nufi wardrobe don ta 6oye su a ciki,
saidai duk yadda tay ta bud'e wardrobe d'in ta kasa ta rasa ta ya ake bud'eta don bata ga wani handle da
zaka kama ka bud'e ba a jikinta, k'arshe d'aya daga cikin jakunkunan ta dake a gefen wardrobe d'in ta
duk'a ta bud'e, a can k'asa ta tura ledan bayan ta rufe ta mik'e, a gaban dressing mirror ta tsaya tana
kallon kanta, ita kan ta taga had'uwar da tayi don lace d'in ba k'aramin had'uwa yayi ba kuma ko ba'a
fad'a ba da ka kalle shi zaka gane ba mai k'ananun kud'i bane, ga sark'a da yan hannun ta suma tamkar
gold sun yi ma hannunta da ya sha k'unshi kyau ba kad'an ba, zuciyarta ce ta fara hasasho mata Haisam
tsaye a bayanta har bata san lokacin da ta d'an yi murmushi ba, bayan ta gama kallon kan nata juyawa
tay jiki a sanyaye ta koma bakin gadon ta zauna ta jingina da headboard, bada jimawa ba aka turo kopar
ta kai idonta da sauri kan mai shigowar, Saude ce ta fara shigowa suka had'a ido tay ma Fatun murmushi
itama tana niyyar mayar mata Gwaggo ta shigo aikuwa zumbur tay ta mik'e da sauri gudu gudu ta nufo
kopar tana zuwa ta fad'a jikinta ta fashe da kuka lokacin Hajiya ma ta shigo tana dogara sandar ta idanun
ta sanye da glasses har lokacin lifaya d'in ce nad'e a jikinta, sosae ta k'ank'ame gwaggon sai kace zata
shige cikin jikinta sai faman kuka take har kallabinta ya fad'i haka gyalen ma ya zamo daga saman kan ta
gashinta da ya sha gyara baki wuluk sai salk'i yake an yi parking d'in shi ya bayyana, har cikin ran gwaggo
take jin kukan hakan ya karya mata zuciya daurewa kawai take tasa hannu guda ta d'an dafa bayan ta,

"To wannan kukan shagwa6a ne ko na me, sai kace wadda zaku rabu kwata kwata, duka yaushe kika
baro gidan kuma gashi har kin gan ta to miye abun kuka Fateema" Hajiya dake tsaye gefe tay Maganar
Saude nata kallon su gwanin ban tausayi, d'ago da ita Gwaggo tay suka had'a ido Fuskar ta duk tayi jage
jage da hawaye a sanyaye tace mata ya isa hakanan ta kamata suka nufi gado ta zaunar da ita, Hajiya ta
kalli Saude tace ta kai towels d'in saman jakunkunan dake gefen Wardrobe in ta tashi ta canza masu wuri
tace to, tsaye gwaggo tay a gaban Fatun tana d'an murmushi Hajiya ma ta maido idon ta kan Fatun tace
"Fuskar Amarya duk tayi jage jage haka, kar kija Angon naki yazo yay tunanin wani abun mukai maki ya
d'auki mataki a kan mu" cike da zolaya tay Maganar Fatun ta sunkuyar da kan ta k'asa,

"Amman Dije ya akai aka bar mata kai haka ba'ai kitso ba" Hajiya dake kallon kan Fatun ta fad'a,
gwaggon tace "Wllh naso ai mata shafa'a nayi gashi yau anata hidima ban ko tuna ba" jinjina kai tay tace
"shikenan bari in Allah ya kaimu gobe sai a kira Balaraba tazo tay mata" gwaggo tace to cike da
girmamawa, sake kallon Fatuu tay "Fateema ga Abinci can a saman Dining table in zaki ci in kuma zaki
jira Angon naki ne sai ku ci tare dama can baya ke kike sa shi yaci da yawa yanzu ma sai ki dasa don har
yanzu ba wani cin Abincin kirki yake ba" gaba d'aya d'an murmushi sukai banda Fatuu da ta sadda kai
Hajiya ta kalli Saude tace suje, ganin gwaggo na niyyar bin su yasa tace in bata gama da ita ba ta tsaya
zasu jirata a parlor cike da jin nauyi tace to, don dama bata samu yi ma Fatuu Nasiha ba, bayan fitar su
Fatuu ta kalli gwaggon ta kamo hannunta cikin muryar kuka tace ta zauna sai ta girgiza mata kai alamar
a'a, magiya Fatun ta hau yi mata kan ta zauna tace bazata zauna a gadon suruki ba tay Maganar da yar
dariya dole Fatuu ta k'yale ta sai kuma ta nuna mata bedside drawer tace to ta zauna saman ta, bata
musa ba ta nufi inda take ta zauna Fatun taja jiki ta matsa kusa da ita ta k'ara kama hannunta tana yar
ajiyar zuciya irin ta wanda yay kuka, bin juna sukai da ido Fuskar gwaggo da d'an murmushi ita kuma
Fatun ta d'an kwa6e fuska idanunta sunyi raurau kaman zata cigaba da kukan, nannauyar ajiyar zuciya
gwaggo ta sauke ta fara Magana a nutse,

"Ina matuk'ar godiya ga Allah daya nuna man wannan ranar gaki a cikin d'akin ki na aure hakan ba
k'aramin abun farinciki bane, dad'in dad'awa kuma wanda ya kasance a matsayin mijin naki mutum ne
da kowacce uwa zatay Alfahari in d'iyar ta ta samu irin shi a matsayin miji, bani haufi akan yadda zaki
gudanar da rayuwar gidan auren ki don nasan wacece ke fiye da kowa, duk yadda ake son Mace ta
kasance a gidan aurenta na tabbatar zaki kasance, saidai ina so in k'ara jan hankalin ki, a yanzu kin baro
shek'ar da kika taso cikinta kika saba rayuwa kin dawo wata sabuwa da baki saba ba, dole zaki ga
yanayin rayuwar ya bambanta sosae, kada kiga ai kinsan abokin rayuwar naki kun saba dole wasu
abubuwan zasu canza, ki k'ara wasu ki kuma rage wasu don yadda kuke dashi a da da kuma a yanzu ba
d'aya bane, yanzu shi Mijin ki ne wanda Aljannar ki na a tafin k'afar shi dole ki k'ara girmama shi kiyi
mashi biyayya fiye da yadda kike mashi, ki bishi sau da k'afa sannan ki zama mai wadatuwa da duk
abunda yay maki kada kiga yanzu kina da hakki akan shi kice zaki rink'a rainuwa kan abunda yay maki,
duk abunda yayi maki ki zama mai godiya had'i da Addu'ar k'arin budi a gare shi, sannan kada kice zaki
rink'a yawan kai mashi buk'atu kiga ai yana da halin yi maki in dai abu ba ya zama dole ba to ki hak'ura
don yawan tambayar abu na sa ka gundiri mutum koda bai fito ya nuna ba, na tabbatar zai tsare maki
dukkan hakk'in ki don haka sai ki zama mai kauda kai, sannan 6angaren tsafta nasan baki da kyuwa ko
ganda, ki k'ara dagewa wurin gyara jikin ki da Mahallin ku ki hana idon shi ganin abunda zai munana
mashi haka ki hana hancin shi shak'ar abunda zai 6ata mashi...." D'an dakatawa tay idanun Fatuu akan ta
sun yi rau rau, bayan ta d'an nisa taci gaba "a zaman farkon nan da zakuyi anan zaki k'ok'ari ki fahimci
miye yake so da kuma miye bai so ma'ana miye in kinyi zai ji dad'i ya faranta mashi rai miye kuma in kinyi
ba zai ji dad'i ba ko zai bakanta mashi, in kin fahimci hakan sai ki kiyaye sai kiga kun zauna lafiya har in
kin ji wasu na korafin tsakanin su da mazajen su kita mamaki, a k'arshe inason in ja hankalin ki game da
abokiyar zaman ki, ki sani ku biyu keda shi Saboda haka kada ki zamo mai son kai, duk abunda baza ki so
ya faru dake ba to itama kada ki so mata haka duk abunda kika so ma kan ki itama ki so mata, ki zauna
da ita tsakani da Allah, nasan in Maganar auren ku ta bayyana rai zai iya 6aci kiyi hakuri da duk abunda
zai biyo baya ba kamar daga gareta don tabbas an mata ba daidai ba, in Allah ya daidaita tsakanin ku ki ci
gaba da daukarta tamkar Yayarki uwa d'aya uba d'aya kar kiyi mata kallon kishiya balle har zuciyar ki ta
samu damar sak'a maki wani abu ba daidai ba game da ita, in abun farinciki ya faru da ita ki taya ta
murna in na jajantawa ne ki taya ta jajantawa kada ki sake ki bari shaidan yay galaba a kanki game da ita
in ma zaki kishi da ita to akan kyautata ma mijin ku ne, haka dangin shi ma ki d'auke su tamkar naki ki
zauna da kowa lafiya sannan ki dage da yin ibada don neman dacewa, a K'arshe ina Addu'ar Allah
ubangiji ya sanya Alkhairi a zaman ku gaba d'aya Amin,(Wannan Nasiha ce ba ga Fatuu kadai ba ga duk
wata Amarya da ke karanta Novel d'in nan, duk abun da kika ji mai muhimmanci ki aiki da shi zai maki
amfani in sha Allah).

A tare suka fito parlon Hajiya da Saude na zaune suna kallo, tana ganin su ta fara k'ok'arin mik'ewa
Saude ma haka, Hajiya tay ma Fatuu saida safe tace taje ta jira Mijinta yazo daga haka ta nufi k'opa,
kallon juna sukai ita da gwaggo ganin idanunta sun ciko yasata girgiza mata kai alamar kada tay kukan
had'i da yi mata d'an murmushi da k'yar itama ta d'an yi mata gwaggon ta nufi kopa har zata fita ta juya
ta kalli Fatuu da tay tsaye tay mata alamar ta koma ciki a sanyaye ta d'aga hannu ta d'an yi mata bye bye
ta jinjina mata kai daga haka ta fuce, bin parlon ta shiga yi da kallo har ta kai idanunta sama kan
chandelier taga an canza wata da ta fi ta da k'awatuwa, d'an murmushi tay ta sauke idanunta ta juya har
zata shiga corridor sai kuma ta juya ta nufi Dining Area tana tafiya kaman mai yin sand'a, tsaye tay tana
bin wurin da kallo ya burgeta sosae can ta nufi wurin table d'in ta kai hannu ta fiddo Warmer guda ta
bud'e farfesun yan ciki ne sai zuba uban k'amshi yake, fiddo d'ayar tayi wadda tafi girma itama ta bud'e
taga Fried Spaghetti ce da tay brown tasha vegetables daga gefe manyan soyayyun tsokokin nama ne a
jere, maida murfin tay ta rufe ta jera su kan table d'in kafin ta d'auki basket d'in ta wuce, Kitchen ta shiga
don ta aje nan ma ba k'aramin burgeta yay ba fuskarta d'auke da d'an murmushi take k'are mashi kallo,
daga baya ta juyo ta fito ta koma Bedroom.

***** *****

Bayan Abbas ya aje su inna Zaliha direct G.r.a ya wuce, Haisam zaune acikin Bedroom d'in shi saman 3
seater ya d'an kishingid'a ya cire rigar shaddar jikin shi daga shi sai farar singlet da wandon shaddar,
Video call yake da Fanan ta cikin computer d'in dake ajiye saman c-table sai faman zabga mashi
shagwa6a take kan ya koma tana missing d'in shi sosae shi kuma yana rarrashin ta kan ta kwantar da
hankalin ta ya kusa komowa, daga ita sai wasu yan fingilallun half vest da wandon ta wanda da kad'an ya
d'ara ma pant sai faman yin abubuwan jan hankali take yanata d'an murmushi don ya gane mata sam
bata da Sauk'i ta wannan 6angaren don in dai yana a kusa da ita hana mashi sakat take, suna cikin haka
Abbas ya turo kopar Bedroom d'in ya d'an juya ya kalli wurin kafin ya juyo kan screen Fanan d'in ta
tambaye shi waye can k'asan makoshi ya furta Abbas aikuwa da sauri ta tashi ta sauka daga saman
gadon da take kwance tayi ruf da ciki ta nufi closet, Zama Abbas yay gefen shi yana sakin murmushi ya
tambayi da wa yake Video call ne slowly ya furta mashi Fanan,

fad'ad'a murmushi Abbas yay yace "kace da uwar gida kake ganawa, to in ka gama ga Amaryar ka can
mun kai maka tana jiran ka" wani kallo Haisam d'in yay mashi mai kaman harara, ba don Fanan d'in ta
mik'e ba da tabbas sai taji abunda Abbas d'in yace, dariya sosae Abbas ke yi yana fad'in ya gama boye
boyen shi dole asiri ya tonu, Haisam d'in bai tanka mashi ba saima ya maida idon shi kan Screen, lokacin
Fanan d'in ta dawo ta zura doguwar riga kanta tasa hula sa6anin da babu hulan sai brown sumar ta da ta
zuba gefe da gefen fuskarta duk da haka yanzun ma ta fito daga gefen wuyanta, tambayar ina Abbas d'in
yake tay Haisam ya juya laptop d'in ta kalli Abbas dake dariya yace "gani nan uwar gida",

itama yar dariya take tace "uwar gida and also Amarya" wata yar iskar dariya Abbas yasa har saida
haisam yay mashi wani kallo suka had'a ido hakan ya k'ara bashi dariyar da k'yar ya tsagaita Fanan d'in
tace mashi ko ta fad'i ba daidai bane da sauri yace "No, no daidai kika fad'a kawae yanayin yadda kikai
Maganar ne naga kaman akwae son kai a ciki, da sai ki tsaya a uwargidan ita kuma Amaryar sai tazo"
wani kallo ta watsa mashi ta had'e giran sama da ta k'asa tace ashe bai k'aunar ta har haka bata sani ba,
da sauri ya d'aga hannu yana fad'in tuba yake, cikin d'an d'aure fuska tace to ya daina mata irin wannan
mummunan fatan ita kad'ai ce ba k'ari wannan Alk'awari ne Until death do them part itama d'in tare
zata d'auke su, jinjina kai Abbas ya hau yi yana k'ok'arin danne dariyar dake ciyo shi yace to ya bari Allah
ya bada ikon ruk'e Alkawari tace Amin ai yasan waye mijinta tunda ya d'auka zai ruk'e da sauri Abbas
yace gaskiya ne,

"To amman wai ya akai kika k'yale shi yay zaune anan ne naga ma kaman bai da niyyar dawowa nan"
d'an 6ata fuska tay "nima na k'osa ya dawo bana jin dad'in rashin shi a kusa dani duk na takura, amman
yace man wani aiki ne ya ruk'e shi ya kusa dawowa" d'an ta6e baki Abbas yay ya jinjina kai yace "Tabbas
hakane na manta, ko yau ma ya k'ara samun wani babban aikin mai cike da Alkhairi don haka sai kin d'an
k'ara hakuri kin d'aga mashi k'afa" d'an rausayar da kai tay tace shikenan ya zata yi tana yi mashi fatan
nasara, da sauri Abbas yace "Yauwa, haka ake son matar kwarae duk in mijinta yazo mata da wani
Al'amari ta fahimce shi ta yiwu Alkhairi ne" murmushi tay kawai tace bari ta k'yale su suyi hira yace ok,
juyo da Laptop d'in Haisam yay sukai sallama cike da nuna kauna kafin ya katse, maida idon shi yay kan
Abbas dake dariya ya hau jinjina kai yace "Wato har na fara tausaya maka wllh, waya fad'a maka ana ma
mata irin wannan Alk'awarin? Ai koda baka da ra'ayin k'ara Aure bai kamata kai mata Alk'awari ba don
bamu ke da iko da kan mu ba komai na iya canza wa just like it happens now, yanzu in tazo ta san da
zancen wane kallo kake tunanin zata maka in ma ta saurare ka kenan" bin shi da ido kawae Haisam d'in
yay kaman ba zai ce komae ba, can yay sigh slowly ya furta "she was already my wife then" Abbas yace
"amman ai ita bata sani ba ko" d'an d'age gira yay yace zai fahimtar da ita in buk'atan hakan ya ta so,
d'age kafad'a Abbas yay yana murmushi yace Allah ya taimaka bai amsa mashi ba saima ya juyar da idon
shi,

"Yanzu ka tashi muje in kai ka an bar yar mutane ita kad'ai kuma kasan ba sabawa tay ba" ba tare daya
kalle shi ba yace yaje kawai, still dariya Abbas ke yi can ya mik'e ya nufi hanyar fita sai lokacin ya juyo ya
kalle shi, bayan wani lokaci Abbas d'in ya dawo abunka da wanda yasan gidan hannun shi ruk'e da mug
d'an tiriri na fitowa alamar abunda ke ciki mai zafi ne, wurin kujerun ya nufa ya koma inda ya tashi ya
zauna ya kai hannu ya kama igiyan tea bag d'in data lek'o waje yana dan tsoma ta ciki yadda zai yi Sosae,
bayan wani lokaci ya mik'a ma Haisam dake kallon shi yana murmushi yace ga shi ya sha, wani kallo ya bi
shi da shi kafin ya maida kallon kan cup d'in baida niyyar amsa, k'ara kallon Abbas yay ganin irin
murmushin da yake yi yasa ya fahimci ko na minene tunda ko da bikin su da Fanan ya bashi irin su, d'an
girgiza mashi kai yay slowly ya furta "No need" Abbas d'in yace "kai dai ka amsa don kuwa kana buk'atar
shi ko an gaya maka ita ma hakanan za'a kawo maka ita ba tare da an gyara taba ba kamar yadda kai
mata aika aika" kallon shi kawai Haisam d'in ke yi baida niyyar amsa, duk yadda Abbas yay dashi kan ya
amsa ya sha ya k'i k'arshe dole ya k'yale shi yace yayi ma kansa shi bari yasha Allah yaso zai mashi
amfani, bayan ya shanye ya mik'e yace bari ya maida mug d'in daga can zai wuce, mik'ewa Haisam yay ya
taka mashi suna zuwa bakin k'opa Abbas yace yaje ya shirya ya tafi gun yar mutane tana can ita kadae,
tsaye yay yana kallon shi ya fita yana murmushi har zai rufe kopar sai kuma ya dakata yace "saura ka
k'ara bari ka zama uncontrollable kazo kana fad'a man k'auli da ba'adin u feel like ur life depends on it"
sai lokacin Haisam ya saki murmushin da har hak'oran shi suka d'an bayyana Abbas d'in ma dariya yake
yi yace makullin Motan na nan a wurin da ya zauna ya d'aga mashi kai daga haka sukai sallama ya tafi,

Wurin kujerun ya koma ya zauna kan ta farko ya d'aura kafa d'aya akan d'aya ya zuba ma gaban shi ido
da alama tunani yake yi, ya d'an d'auki lokaci a haka can ya mik'e ya fita daga wurin ya nufi hanyar
corridor, saida ya d'auki kusan 30 minutes sannan ya fito da alama wanka ma yayi don ya canza kaya
zuwa farar shadda Sol sai salk'i take da alama sabuwa ce bata ga ruwa ba, hannun shi d'aure da agogon
diamond k'afafun shi na sanye da fararan half cover, kan shi ba hula sai nad'add'ar bak'ar sumar shi da
gani an gyara ta don sai shining take yana janye da d'an madaidaicin trolley, saida yaje ya kauda laptop
d'in dake saman c-table sannan ya dawo bakin dressing mirror ya d'auki Car Key ya kai hannu ya kama
trolley d'in da ya aje, bayan ya latsa switch hasken d'akin ya d'auke ya bud'e kopar ya fita,

Wani irin tsoro ne ya fara kama Fatuu ganin dare yayi sosae don sha d'aya ta kusa, duk ta takure kanta a
saman gadon sai wuwwurga ido take ga wata irin yunwa da take ji, lokaci bayan lokaci take duba time a
jikin wayar ta dake a gabanta har ta fara fidda ran zuwan Haisam d'in ta shiga tunanin yadda zata kwana
ita kadae a part d'in, can bayan wani lokaci taji ana k'ok'arin bud'e kopar aikuwa a tsorace ta tashi zaune
jikinta har ya fara yar rawa kanta ba kallabi ta zaro idanu tana kallon kopar, a hankali ya turo k'opar ya
shigo da yar sallamar da ko Fatun bata ma ji ba, yana shigowa idanun shi suka sauka cikin nata da ta zaro
ya dakata suka bi juna da kallo, ya lura da a tsorace take hakan yasa shi k'ara yin sallama a hankali sai
lokacin taji ta amsa tare da sauke nata idanun saman gadon shiru ta biyo baya, jin bai k'ara cewa komai
ba yasa ta d'ago ta kalle shi, still yana tsayen suka k'ara had'a idanu cikin yar rawar murya tace "Sannu
da zuwa" kai ya d'aga mata kawai ya juya ya nufi wardrobe yana janye da trolley d'in ta bishi da kallo, aje
trolley d'in yay ya kai hannu gefenta ya latsa sai gashi ta fara zugewa da kanta sai lokacin Fatuu ta gane
yadda ake bud'e ta, bayan ta gama bud'ewa ya kai hannu ya zuge trolley d'in ya fara k'ok'arin fiddo
kayan ciki tana ta kallon shi, bayan ya saka na farko ta kai hannu ta d'auki kallabinta ta yafa saman kai ta
sauka daga saman gadon a d'arare ta nufe shi, lokacin data isa ya saka na biyu yana juyowa ya ganta a
gefen shi ya bita da ido, saida ta had'iyi abu sannan cikin yar in ina tace "b....bari in saka.." bai ce mata
komai ba sai kawai ya juya ya tafi tabi bayan shi da kallo, Laundry room ya nufa ya tura kopar ya shige, a
sanyaye ta kai hannu taci gaba da fiddo kayan tana jerawa har da su underwear d'in shi, har ta gama bai
fito ba ta zuge trolley d'in ta maida shi gefe wurin jakunkunan ta ta aje, komawa tay wurin gado tana
niyyar zama ya bud'e kopar ya fito fuskar shi da alamun ruwa haka k'asan hannun rigar shi mai links,
tsaye tay ta kasa zaman tana kallon shi tana yi tana maida idon k'asa, tsayawa yay daga d'ayan bangaren
gadon yana kallon ta kaman zai yi magana, sai da ya d'an d'auki lokaci sannan taji yayi Maganar saidae
bata ji mi ya ce ba ta bishi da kallon rashin fahimta, ya gane bata ji mi yace ba ya d'an maida idon shi
k'asa sai kuma ya d'ago slowly da turanci yace ta samu tsarki, kai ta d'aga mashi alamar eh tare da maida
idon ta k'asa taji yace taje tayo Alwala tace to, ba tare da ta kalle shi ba ta nufi hanyar Laundry room d'in
sumi sumi, lokacin data fito har ya shimfid'a prayer mat guda biyu a saman lallausan carpet d'in dake a
gaban gadon yana zaune a bakin gado, wurin jakunkunan ta nufa ta bud'e ta curo Hijab ta fara k'ok'arin
saka wa ya mik'e ya daidaita kan abun sallar gaba ita kuma ta hau kan ta baya ya kabbara salla, Nafila
raka'a biyu sukai sam Fatuu batayi mamakin jin yadda yake sakin kira'a ba don ba yau ta fara jin shi yana
karatun Qur'ani ba yana yawan yi ta cikin wayar shi, gaba d'aya Allah ya bashi ilimin boko dana Addini
abun saidae ace ma sha Allah, zama sukai suna lazimi tana ta kallon sumar bayan kan shi ba zato sai gani
tay ya juyo har saida gabanta ya fad'i don sun yi gab da juna, had'a ido sukai ta d'an waro nata yay mata
alamar ta matso da kan shi, matsawa tay dab da shi ya kai hannu ya dafa kanta ta d'an sunkuyar da kan
tana kallon k'asa gaba d'aya k'amshin shi ya gama cikata, Addu'ar da Manzo (S.A.W) ya koyar mutum
yayi in yay Amarya ya shiga yi bayan ya gama ya sauke hannun nashi ta d'ago suka k'ara had'a ido, bai yi
tunanin tambayar ta wani abu ba don duk abunda yake son sani game da ita ya sani, juyawa yay ya d'aga
hannu ya fara jero Addu'oi da sauti kad'an itama ta d'aga nata hannuwan bayan ya gama a tare suka
shafa ya yunk'ura ya mik'e tana dai ta bin shi da ido, har yayi taku d'aya zuwa biyu ya dakata ya juyo ya
furta akwai abu akan dining table daga haka ya juya ya nufi kopar ya fita, zugudum tay ta bi k'opar da ido
tama rasa tunanin da zata yi, gaba d'aya ta kasa gane mashi duk ya canza mata sai kace ba Ya Haisam
d'in da ta sani bane, in don abun da tayi ne ai taje ta bashi hak'uri kuma ya nuna ya hak'ura to miyasa
taci gaba da ganin shi haka wanda ada da ta bashi hak'uri yake hak'ura kuma bata ganin canji a tattare
dashi kamar yanzu, gaba d'aya jikinta ne ya k'ara yin sanyi, tunowa da Abincin da su Hajiya suka kawo
yasa ta yunk'ura ta mik'e, cire Hijab d'in tayi ta linke ta mayar ta dawo ta kwashe abubuwan sallan suma
ta linke ta je ta ajiye ta d'auki kallabin ta dake a saman gadon ta yafa saman kan nata ta nufi hanyar fita,
d'an jimm tay a bakin k'opar tana zullumin fita can dai ta kama handle d'in ta ja kopar ta bud'e a d'arare
ta fita,

Tana zuwa bakin corridor d'in ta hango shi zaune akan L-shape ya d'an kishingid'a yana kallo, had'a ido
sukai da sauri ta kawar da nata sum sum ta nufi hanyar dining d'in, tana zuwa taga manyan ledoji guda
biyu ta fahimci sune yay mata magana akai ta kai hannu ta fara bubbud'a su taga miye a ciki, d'aya su ice
cream da Youghort da kuma snacks d'ayar kuma fruit ne, shiru ta d'anyi tana tunanin yadda zata yi dasu
can ta d'auki guda ta nufi freezer ta bud'e ta saka, dawowa tayi ta d'auki d'ayar ma taje ta kai ba tare
data d'au komai ba don ta ci, bayan ta dawo tsaye tay gaban table d'in tana tunanin ko zai ci Abincin ma,
wata zuciyar ta bata taje ta fara tambayar shi, kamar bazata je ba sai kuma ta tafi tana tafiya kamar
wadda k'wai ya fashe mawa a ciki, bata zagaya cikin parlon ba sai ta bi ta bayan kujeru ta tsaya a d'an
gefen bayan kujerar da yake zaune ta bi shi da ido ta kasa cewa komai, kamar yaji ajikin shi da mutum a
wurin ya d'an juyo da kan shi suka had'a ido, d'an kikkafta idanu ta shiga yi da k'yar tace mashi dama
Abinci ne aka kawo daga part d'in Hajiya, shiru ya d'anyi still idon shi na akan ta sai kuma ya d'an girgiza
mata kai alamar bazai ci ba, maimakon ta tafi sai tay tsaye tana kallon shi ganin haka yasa shi cewa "Dare
yayi" saida ta had'iyi abu kafin a sanyaye tace "ai Abincin ba mai nauyi bane" yanayin kallon da yake
mata ne ya sauya da sauri ta maida nata idon k'asa tana haka taji ya mik'e ta d'ago tana kallon shi, saida
taga ya zagayo sannan itama ta nufi Dining d'in ta d'ayan side d'in da ba ta nan ya bi ba.............

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2062*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

......... Zama yay akan d'aya daga cikin chairs d'in sai lokacin ta tuno da bata d'aukko plates ba da d'an
hanzari ta juya ta nufi hanyar corridor Slowly ya juya yana kallonta har ta shige sannan ya janye idon,
bada Jimawa ba ta dawo hannuwanta ruk'e da plates da bowl sai serving spoon da kuma spoons da forks
duk ta d'aurayo su don da alamun lemar ruwa a jikin su, bayan ta aje ta bud'e babbar warmer d'in ta fara
zuba mashi tana sa kaman rabin plate taga ya d'an d'aga hannu alamar ya isa ta d'aukko k'atuwar tsokar
nama ta d'aura tana niyyar k'ara wata nan ma ya k'ara dakatar da ita ta hanyar k'ara d'aga mata hannu
ta tsaya, saka mashi fork tay ta tura gaban shi ta bud'e Warmer d'in farfesun ta zuba mashi kad'an ta
tura mashi, Fridge ta nufa ta d'aukko bottle water da lemu ta dawo ta aje daga gaban shi ta sake juyawa
ta koma ta d'aukko glass cups daga cikin fridge d'in ta dawo, tana niyyar bud'e robar lemu ya dakatar da
ita a hankali ya furta ruwa kawae yake buk'ata ganin zata bud'e nan ma yace sai ya gama a hankali ta
furta to, zuba nata abincin tayi bada yawa ba tasa fork ta d'auka tana niyyar juyawa ya d'ago ya kalleta
suka had'a ido ta kasa tafiya,

"zaki je ina ki ci Abinci?" taji cool voice d'in shi ya tambaya, shiru kaman bazata ce komai ba ganin ya
kafe ta da ido yasa tace d'aki zata je, still yay yana kallon ta can taji yace "shi nan don me aka yi shi?"
Shiru bata ce komae ba ta maida idon ta k'asa, "Sit!" cike da bada umarni taji ya fad'a, ba yadda ta iya
dole ta aje Abincin ta zauna, duk da tana jin yunwa ta kasa cin Abincin sosae don duk sai taji ya fitar
mata a rai sai d'an tsakura take tana yi tana satar kallon shi yanata cin nashi a nutse, bata wani ci da
yawa ba ta mik'e ta d'auki Abincin yana kallonta tun kan yace wani abu tace mashi ta k'oshi zata kai
kitchen ne ya d'an d'age mata gira "da kika ci mi?" yanayin Fuskar ta ne ya sauya idanuwan ta sukai rau
rau kaman zatai kuka yace ta zauna ta cinye shi, komawa tay jiki a sanyaye taci gaba da ci ba don tana jin
dad'in shi ba don ta rasa mike mata dad'i kamar ta fashe da kuka take ji, ya rigata gamawa amman sai
yay zaune ya kafe ta da ido har saida itama ta cinye sannan ya mik'e ta bi shi da ido, Fridge ya nufa ya
bud'e ya d'aukko babbar robar ice cream da wasu daga cikin Snacks ya dawo, aje mata yay gabanta da
sauri ta kalle shi ba tare da ya kalle ta ba yace suma ta cinye aikuwa kaman jira take ta fashe mashi da
kuka ta kife kanta a kan table d'in kallabin ta ya zamo ya baro saman kan ta, bin ta da ido yay yana kallon
ta da alamun mamaki ita kan ta kawai ji tay kukan yazo mata, d'an kwankwasa saman glass table d'in yay
ta d'ago fuskar ta jage jage da hawaye ta kalle shi,

"na buge ki ne?" Ya tambaya had'i da d'age mata gira ta girgiza mashi kai alamar a'a, "then miye abun
kuka?" cikin muryar kuka tace "ni na k'oshi" bin ta da ido yay can yace "shine na kuka, ko akwai abunda
ke damun ki ne?" Da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a, "Ok, kin ci wani abu ne before I came?" Kai ta
sake girgiza mashi, "kuma shine har kin k'oshi?" tana d'an tura baki tace to ba ta ci Abinci ba yanzu,
yanayin fuskar shi ne ya sauya kaman zai d'an yi murmushi "ai baki k'oshi ba so ki k'ara da wannan"
kallon shi tay ba dama tay mashi musu don kuwa yasan yanayin yadda take cin Abinci, ganin ya kafeta da
ido yasa da sigar shagwa6a ta d'an juya kai tana yamutsa fuska tace to ai sunyi mata yawa dare yayi
sosae bazata ci Abinci da yawa ba tunda kwanciya zata yi, ganin yadda yake kallon ta tana Maganar yasa
ta juyar da fuskar ta gefe can taji yay sigh ya furta Ok, komawa yay ya zauna duk abunda ya d'aukko ya
raba biyu saidae d'aya yafi d'aya girma ya bata wanda suka fi girman shi kuma ya fara cin sauran itama ta
fara ci tana yi tana d'an kallon shi har lokacin ba kallabi a kanta, kusan a tare suka gama ya bud'e mata
robar ice cream d'in ya tura mata ganin yana niyyar mik'ewa da sauri tace to shi bai rage ba ai yayi mata
yawa shi ma, wani kallo ya jefa mata sai taga kaman ya harareta ta d'an tura baki ta sauke idon ta k'asa,
d'an guntun murmushin da iyakar shi lips d'in sa yay taji yace in ta rage tasa a fridge daga haka ya juya ta
d'ago ta bi shi da ido, dakatawa yay ya juyo yace in ta gama yana buk'atar fruit bada yawa ba ta d'aga
mashi kai ya juya ya tafi, sai gashi ta shanye ice cream d'in duka dama harda rashin sake mata fuska da
ta ga baiyi ba yasa taji komae ya fitar mata a rai, bayan ta gama ta nufi Fridge ta fiddo ledar fruit d'in
tunanin ko ta had'a mashi fruit salad tay tasan zai fi jin dad'in sha tayi ta juya tana ruk'e da ledar ta nufi
hanyar corridor yana zaune a inda yake da kafin ya tashi ya d'an kai idon shi kanta kafin ya maida su kan
tv, ba 6ata lokaci ta had'a mashi ba mai yawa ba sosae a cikin d'an bowl mai kyau ta bud'e fridge d'in
cikin kitchen ta d'aukko k'ank'ara ta d'an kwankwatsa ta a ciki ba mai yawa ba don tasan bai son abu mai
sanyi sosae, saka ledar fruit d'in tay a cikin fridge d'in nan ta d'auki bowl d'in ta nufi parlon, tunda ta fito
ya maido idon shi kanta itama kallon nashi take tana isa ta d'aura saman c-table ta ja shi gaban shi ta
d'ago suka had'a ido tace gashi nan da d'an murmushi ya jinjina kai tare da furta thanks, juyawa tay ta
koma Dining Area ta fara kwashe kayan Abincin, wanda zata saka a fridge ta saka tay clearing wurin,
saida ta wanke duk abunda suka 6ata a cikin kitchen ta maida su ma'adanar kowanne sannan ta fito ta
nufi bedroom, tana shiga ta koma can bakin gado inda ta zauna d'azun ta zauna tay shiru kaman mai
tunanin wani abu, gajiya tay da zaman ta kai kwance amman k'afafun ta na a k'asa, har bayan wani
lokaci tana a hakan can taji an bud'e kopar da sauri ta tashi zaune suka had'a ido, rufe kopar yay ya nufo
ciki ya tsaya gaban dressing mirror ya fara k'ok'arin cire Diamond Watch d'in wrist d'in shi, bayan ya cire
a saman wurin ya aje ta ya juyo idanunshi suka sauka cikin nata da take ta faman bin shi dasu taga ya
nufi hanyar Laundry room tana ta kallon shi har ya shige sannan ta juyo, komawa tay yadda take kafin ya
shigo taci gaba da wurga ido tana tunane tunane, kusan Mintuna 15 ya d'auka sannan taji ya turo kopar
ya fito tana kwancen ya zagayo wurin gadon, wani irin bugu k'irjinta yay mata don kuwa daga shi sai
towel d'aure a k'ugun shi ya fito, tunda take bata ta6a ganin namiji haka ba balle shi da yake
Tubarkallah, a rud'e ta juya ta yadda ta bashi baya yana jin mutsu mutsun ta bai ko kalle ta ba ya nufi
gaban dressing mirror, duk mayuka da turarurrukan da yake amfani dasu suna a wurin saidae an k'ara
wasu dasu kwalaben humra da turaren wuta, mai din shi ya d'an shafa sama sama bayan ya gama ya hau
feshe jikin shi da turare Fatuu da tay lamo tana ta kikkifta idanu tana jin yadda yake fesa turarurruka ta
d'an lumshe ido had'i da d'an yin murmushi, yana da son k'amshi sosae har da hakan ke k'ara mata
k'aunar shi gashi koda yaushe zaka ji k'amshin shi na daban ne, bayan ya gama closet ya nufa ya bud'e
bayan ta zuge ya fiddo sleeping dress riga da wando ya juya ya k'ara nufar laundry idon shi akan Fatuu
da ta takure guri guda ya d'an ta6e baki da yanayin murmushi kan face d'in shi ya wuce, jin k'arar k'opa
yasa ta d'ago da sauri ta kalli kopar Bedroom d'in sai dai bata ga alamar ita aka bud'e ba nan ta gane
laundry ya shiga, bada jimawa ba taji motsin zai fito aikuwa da sauri ta maida kan yadda take da, fitowa
yay ya saka kayan baccin ya nufi k'opar fita, har ya kama handle d'in sai kuma ya dakata ya juyo yana
kallon ta, ta ji lokacin da ya kama k'opar amman bata ji ya rufe ba hakan yasa ta d'an d'ago zata saci
kallon shi karaf suka had'a ido nan take ta kama kanta ta k'arasa d'agowa ta tashi zaune sai waro ido
take tana d'an motsa baki,

"Zaki kwanta haka ne?" taji ya fad'a, shiru tay tana kallon shi ba tare da ta ce komai ba, d'age mata gira
yay "am I not talking?" abu ta d'an had'iya a hankali tace "a'a",

"U should go and take bath" kai ta d'aga mashi alamar to ta mik'e sumimi sumimi ta nufi wurin
wardrobe, towel d'in da ta gani saman jakunkuna ta d'auki wani light blue ta juyo idanun ta suka sauka
cikin nashi yana tsaye har lokacin da sauri ta sauke kanta k'asa ta wuce, tana kaiwa bakin k'opar zata
shiga taji k'arar bud'e kopar shi ta juya lokacin ya fita, After some minutes ta fito tana d'aure da towel
d'in a k'irji da yake yana da d'an girma ya saukko mata ta yafo kallabin lace d'in da ta cire, nufar wurin
jakunkuna tay ta duk'a ta bud'e wadda ke d'auke da kayan bacci, wata doguwar riga cotton ta fiddo cikin
kayan da Hajiya ta aiko jikinta gwanin taushi ta bud'e cikin Akwatunan ta ta d'aukko hula ta mik'e ta
koma bakin gado, saida ta d'an shafa mai sannan ta shafe jikinta da wata humra mai Masifar k'amshi don
kuwa nan da nan k'amshin ta ya karad'e d'akin ta d'aukko roll on ta goggoga a hammata, bayan ta gama
yan shafe shafen da goge gogen ta dawo bakin gado ta saka rigar, komawa tay gaban dressing mirror
d'in ta hau feshe jikin rigar da turare saida ta fesa kaman kala ukku sannan ta dawo bakin gadon ta
d'auki towel d'in ta nufi laundry don ta baza shi ya bushe, bayan ta fito zama tay a bakin gado tay shiru
gaba d'aya bata jin bacci gashi dare yayi sosae don tuni k'arfe 12 tayi ko don Saboda bak'unta ne oho,
tana ta zaune can ta idasa hayewa gadon ta kwanta tay k'uri tana kallon bangon da k'opa take, bata
dad'e da kwanciyar ba ya turo k'opar ya shigo suka had'a ido ya tunkaro gadon har saida gabanta ya
fad'i, yana isa bakin gadon ya kai hannu ya d'aukko babban pillow guda ya d'ago idon shi a Kanta ya furta
mata "Gud nyt" kai ta jinjina mashi kaman yar k'adangaruwa, har zai juya sai kuma ya kai hannu jikin
lamb dake gefen gadon ya kunna sannan ya juya Fatuu dai nata kallon shi, saida ya kashe switch hasken
d'akin ya d'auke sai na fitilar da ya kunna sannan ya bud'e kopar ya fita, zuru Fatuu tay a ranta ta fara
tunanin kenan a parlor zai kwana Saboda ita, sam ran ta bai mata dad'i ba ba kuma don wani abu ba sai
don kwanan da zai yi a parlon tasan ba lalle yaji dad'in kwanciyar ba duk da kujerar nada taushi sosae
amman zai iya takura, tana ta zancen zuci can zuciyar ta ta raya mata wani abu tay d'an jimm tana
tunanin tayi ko kuwa, tashi tay zaune ta saukko daga saman gadon ta nufi hanyar fita har ta kusa kaiwa
kopa sai kuma ta dakata ta juyo ta koma wurin kayanta, golden gyalen da ta cire ta d'auko ta yafa
sannan ta nufi kopar fita.

Lokacin da ta fito cikin Corridor d'in tsayawa tay tana kallon cikin parlon ya kashe hasken cikin shi sai na
wasu da ya bari na gidajen wurin su Tv sune suka d'an haska parlon, nufar cikin parlon tay sai kace mai
yin sand'a ta hango shi kwance kan L-shape side d'in da ya fi zama, tunda ta bud'e k'opa ta fito ya
hangota ya zuba mata ido yana ta kallon ta har ta k'araso, daga bakin kujerar taja ta tsaya tana kallon shi
ta gane kallon ta yake shima, kasa isa wurin shi tay tayi tsaye sai d'an wasa take da yatsun hannunta
tana d'an kikkafta ido had'i da motsa baki alamar tana son fad'in wani abu, yunk'urawa yay ya tashi
zaune idon shi akanta yay mata alamar ta zo da hannu ta matsa a d'ayan side d'in ta tsaya ya k'ara mata
alamar ta zauna a hankali ta d'an d'osana ta zauna,

"Any problem?" Ya tambaya, cikin yar inda inda tace "D...dama cewa nay kaje ka kwanta ciki ni zan
kwanta anan" da k'yar ta k'arasa Maganar Saboda kallon da yake jefa mata mai wuyar fassaruwa ba
Arzik'i ta sunnar da kan ta bayan tayi Maganar, maida bayan shi yay jikin kujeran still idon shi na akanta
kaman bazai ce komae, jin shirun yayi yawa yasata d'an d'agowa suka had'a ido, sigh yay "ba wani abu
kije ki kwanta" yanayin fuskar ta ne ya sauya hakanan taji kaman idanunta na son tara k'walla da sauri ta
maida fuskarta gefe tana kikkafta idanu don kar su tarun,
"Fatuuh" ya kira sunanta ta d'an yamutsa fuska had'i da d'an cije lower lip d'inta ba tare da ta juya ba,
hakanan bata son Fatuu da yake kiranta duk da sunan ta ne kuma yafi kowa iya fad'ar shi don a gayance
yake furta shi amman duk da haka bata so sai take ganin kaman bai huce bane yasa yake kiran ta haka
ko kuma matsayin da take dashi a wurin shi da yanzu ya ragu, k'ara kiran ta yay sai lokacin ta juya suka
had'a ido fuskar shi a d'an sake yace "Don't worry am comfortable here kije ki kwanta it's already late"
ba tare da ta ce mashi komai ba ta mik'e ta nufi hanyar corridor walking very slowly don duk jikinta ya
mutu, idon shi na kanta still yana zaune bai kwanta ba har ta shige cikin Corridor d'in yana ji ta bud'e
kopar Bedroom d'in ta shige, maida kanshi yay jikin kujera ya d'age shi yana facing sama had'i da lumshe
ido ba zaka iya karantar yanayin shi ba a lokacin, ya d'an d'auki lokaci a haka kafin ya maido kan k'asa ya
koma ya kwanta.

Tana shiga d'akin ta nufi bakin gado ta zauna ta zuba ma wuri guda ido, ta d'an d'auki lokaci a hakan can
ta idasa hayewa saman gadon ta kwanta ba tare da ta cire gyalen ba, kwata kwata bacci ya k'aurace ma
idanuwan ta sai juye juye take ba kuma wai don tana son wani abu ya kasance tsakanin su ba kawae dai
ta rasa mike mata dad'i ne, sam ta kasa gane mashi har ta fara kokonton anya yana son Auren ba Hajiya
ce ta matsa ba kuwa, haka tay ta tunane tunane zuciyar ta na sak'a mata abubuwa har dare ya tsala da
k'yar bacci ya d'auketa shima kuma ba mai nauyi ba,

Akan kunnanta aka fara kiraye kirayen farko na sallar Asuba ta bud'e ido saidae bata tashi ba tay zuru,
ba'a dad'e da gama kiran sallar ba taji an turo kopar ta kai idanun ta wurin tana ganin shi ya shigo da
sauri ta rufe ido, saida ya kalleta sannan ya wuce wurin closet ya bud'e, jallabiya ya fiddo yana ruk'e da
ita ya nufi laudary room jin k'arar bud'e kopar yasa ta bud'e idon nata, bayan few minutes ya fito ta sake
rufe idon nata, saida taji k'arar bud'e kopar Bedroom d'in sannan ta d'an bud'e idon taga ya saka
jallabiyar ya fita da alamun Alwala yayi, bayan fitar shi bada jimawa ba itama ta tashi ta saukko ta nufi
laundry room d'in, Alwala tayo bayan ta fito ta wuce wurin jakunkunan ta ta ciro wata doguwar riga tare
da hijab d'in da sukai salla da Haisam ta dawo bakin gado don ta saka, bayan ta gama ta shimfid'a prayer
mat ta kabbara raka'atanil fajr, tana zaune tana ta tasbih har lokacin sallar Asuba yayi ta mik'e don tayi,
bayan ta gama tayi Addu'oi ta shafa, zaune tay a wurin kaman an dasa ta ta kasa tashi can sai ma ta
kwanta a wurin cikin sa'a bacci ya d'auke ta. Bayan an gama salla saida gari ya d'an fara washewa ya
dawo daga Masallaci, a bakin kopar parlon ya cire takalman shi ya nufi kujera ya zauna, had'e hannuwan
shi yay ya d'aura ha6ar shi yana kallon wuri guda ya d'an d'auki lokaci a hakan can ya mik'e ya nufi
hanyar corridor, Slowly ya tura kopar Bedroom d'in ya shiga idanuwan shi suka sauka akan ta kwance
kan Carpet ta takure cikin Hijab d'in kaman mai jin sanyi, tsaye yay a bakin kopar yana ta kallon ta can ya
idasa shiga ciki wurin Ac ya nufa ya rage mata ita sannan ya dawo inda take, kiran sunanta yay shiru bata
motsa ba ya k'ara nan ma bata farka ba, d'an jimm yay sai kuma ya rankwafa ya kai hannu ya d'an
bubbuga shoulder d'in ta nan ta fara motsi ya d'ago, a hankali ta bud'e idanun ta ta d'an d'ago suka
had'a ido da sauri ta k'arasa d'agowa ta tashi zaune tana gyara hijab, kallon shi ta d'an yi k'asa k'asa tace
mashi ina kwana ya d'aga mata kai,
"taya zaki ji dad'in bacci anan, ki koma kan bed mana" taji cool voice d'in shi ya fad'a, bata ce komae ba
ta mik'e ta d'auke abun sallar ta maida sannan ta nufi gadon idon shi akanta, ganin zata hau ba tare da ta
cire k'atuwar hijab d'in ba yasa shi k'ara yi mata magana kan taya zata kwanta da ita zai iya shak'e ta nan
ma ba tace komai ba tasa hannu ta cire, saida ta linke ta ta mayar wurin kayan ta sannan ta dawo still
yana a inda yake ta hau saman gadon sannan ya juya ya fita, da k'yar ta koma baccin shima parlon ya
koma ya kwanta, ba laifi ta d'an yi baccin don sai k'arfe tara saura ta farka ta tashi zaune tana yin yar
mik'a da hamma, sosae ta ji dad'in baccin da tayi jin jikinta ba k'arfi yasa ta saukko daga kan gadon ta
wuce laundry don ta shiga toilet tay wanka, d'aure da towel a k'irji kanta sanye da hular wanka ta yafo
wani short a kafad'arta ta fito, gaban dressing mirror ta tsaya tana k'ara goge ruwan jikinta bayan ta
gama ta aje short towel d'in ta fara shafa mai cike da fargabar kar ya shigo ya iske ta haka, bayan ta
gama ta shafa su humra nan da nan k'amshin su ya karad'e Bedroom d'in, wurin jakunkunan kayan ta ta
nufa bayan ta gama ta duk'a ta janyo babbar mai d'auke da kayan sawa ta bud'e nan ta fara tunanin
kayan da zata saka tsakanin lace shadda da kuma atamfa ga kuma jallabiyu, ta d'an d'auki lokaci tana
ruwan ido can dae ta fiddo wata hadaddar atamfa mai red flowers riga ce da straight skirt tana ganin
kayan ta gane kb ne ya d'inka su don yasan kalan d'inkin da tafi so kuma dama ba'a amshi ko
measurement d'in ta ba tunda yana dashi, maida jakar tay ta bud'e mai d'auke da undies ta fiddo wanda
zata saka, bayan ta fiddo komae da take buk'ata ta maida jakunkunan ta dawo bakin gado, d'aura kayan
tay ta fara k'ok'arin sakawa gabanta na d'an fad'uwa don kar a maimaita na Asibiti, har ta gama bai shigo
ba ta koma gaban mirror tana kallon kanta abun saidae ace Tubarkallah, sosae kayan suka amshe ta
shape d'inta ya fita kamar an zana ta gashi straight skirt d'in irin mai tsaga ta gaba ne rigar ma tayi mata
k'yam k'yam daga wurin hips d'in ta ya bud'e sosae kaman zai fashe yadda ya kamata, d'an jujjuyawa tay
tana k'are ma kanta kallo har saida ta d'an yi murmushi don ita kanta taga yadda kayan suka mata kyau,
yar light make up tayi tasa red janbaki wow just Ma sha Allah, gashinta ta warware ta sharce shi har zata
kulle wata zuciyar ta bata ta bar shi haka a sake tay d'an jimm tana tunanin yin hakan don bata yi mashi
haka, can ta yanke barin nashi taga in zata yi kyau ta d'aukko k'aton kallabin atamfar ta lankwasa shi ta
gaba ta kashe d'auri gaban sai yay kaman daurin Zarah buhari duk da bata sa komae ba ciki amman ya yi
sosae da yake atamfar sabuwa ce, Jama'a ku zo kuga Fatuu ta fito sak Amarya ita kanta sai d'an sakin
murmushi take wani irin kyau da bata ta6a ganin tayi ba taga yau tayi ga bak'in gashinta mai santsi yay
mata rumfa a k'afadun ta abun dai sai wanda ya gani, turarurruka ta feffesa bayan ta gama ta nufi gefen
gado ta kwashe towels d'in da tay amfani da hulan wanka ta wuce laundry don ta kai su, baza su tayi
yadda zasu sha iska ta nufi hanyar fita, daidai tana fitowa Haisam ya turo kopar Bedroom d'in ya shigo
idanun shi suka sauka cikin nata tay tsaye cak kaman an dasa ta da alamun yar razana take kallon shi
shima yanayin kallon da yake Mata irin na baka tsammaci ganin mutum ba balle kuma a yadda take,
sakin fuska yay yanayin d'an murmushi ya bayyana itama d'an murmushin tay da hannu yay mata alamar
ta wuce ta tafi a nutse, saida ta wuce sannan shima ya wuto ya shiga laundry room d'in, a gefen gado ta
zauna a ranta tana raya kar fa yace Saboda wata manufar tay kwalliyar wata zuciyar ta sake raya mata
amman dama can ai yasan dai tana yin gayun ta ko, yin wannan tunanin yasa ta kauda wanccan tunanin
sai kuma ta k'ara yin tunanin k'ilan wanka zai yi yakamata ta fita ta bashi wuri in ya fito ya shirya koma ta
je ta had'a masu Breakfast, mik'ewa tay har zata nufi kopa sai kuma ta wuce wurin kayanta ta bud'e inda
takalma suke ta curo wasu flat shoe da suka hau da kayan jikinta ta saka su sannan ta tunkari kopar fita
don zuwa Kitchen.

Bayan da ta shiga cikin Kitchen d'in duk iya dubawar da tayi bata ga wasu kayan abinci ba da zata yi
amfani da su sai iya su cincin da dublan kawae, tsaye tay ta jingina da drawer tana k'are ma Kitchen d'in
kallo a ranta tana k'ara yaba kyan shi ganin abun take har yanzu kaman al'mara wai nan Kitchen d'in ta
ne, idanunta ne suka sauka akan drawer d'in da Aunty Mareeya ta nuna mata da ta zuba mata
magungunan ta, a yadda ta fad'a mata yakamata da safen nan ta sha amman sai taji kaman bazata sha
d'in ba tunda tasan dalilin shan magungunan, tana ta tsaye k'arshe ma sai tay d'an tsalle ta haye saman
drawer d'in ta zauna sai yan kalle kalle da yan tunane tunane take, ta d'auki kusan minti talatin a haka ta
jiyo k'amshin Haisam cikin hancin ta da sauri ta kalli kopar shigowa daidai lokacin ya sawo kai cikin wurin
wato tun ma kafin ya shiga wuri Kamshin shi ke sanar da isowar shi, ya yi wanka ya shirya cikin k'ananun
kaya bak'in jeans da farar t-shirt daga gabanta an d'anyi style d'in bak'in rubutu, sosae kayan suka amshi
jikin shi yay wani Fresh sumar nan sai kyalli take tasha gyara haka sajen shi ya kwanta luf, daga can bakin
kopar ya tsaya tana ganin shi ta diro k'asa tana kallon shi, tambayar ta yay mi take yi a nan ba ga parlor
ba,

"Dama na shigo inyi breakfast ne amman na duba banga kayan Abinci ba" a sanyaye tay Maganar sai
faman bin bakin ta da ya sha jan jambaki yake da kallo har ta gama, ganin yadda yake ta kallon ta kaman
ba zai ce komae ba yasa ta d'an sunkuyar da kan ta, "Ba sai kin yi ba za'a kawo" taji ya fad'a, d'agowa tay
ta d'aga mashi kai alamar to suka ci gaba da kallon juna tana yi tana d'an maida idanunta k'asa da d'an
motsa baki,

"ko kina buk'atar wani abu ne?" da sauri ta girgiza mashi kai ta nufi inda yake don ta fita ta gefen shi ta
wuce, bin bayanta yay shima ya fito ganin zata shiga bedroom yasa shi ce mata taje ta zauna a parlor
mana, juyowa tay ta kalle shi tace zata gyara d'akin ne ya d'aga mata kai ya wuce cikin parlon ta bi bayan
shi da kallo yana tafiyar shi mai cike da k'asaita, d'an murmushi tay ta tura Kopar ta shige..............

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
*ASM Bk2063*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

...........Bayan shigarta tsayawa tayi daga gaban gado tana tunanin abunda zatai ma d'akin don fes yake,
can dai ta fara gyaran gadon ta kakka6e abunda zata kakka6e bayan ta gama da gadon laundry ta nufa ta
d'aukko floor wiper ta dawo ta fara gyara tsakar d'akin, bata d'au wani dogon lokaci ba ta gama ta maida
ta ta dawo da d'an towel mai taushi ta goge furniture d'in, bayan duk ta gama ta kunna burner dake jone
jikin socket ta zuba turaren wuta nan da nan daddad'an k'amshi ya fara karad'e d'akin, bayan d'akin ya
turaru ta cire burner d'in ta nufi Parlor don shima ta turara shi, yana zaune a inda ya saba zama ya d'an
kishingid'a Tv nata aiki wayar shi ruk'e a hannun shi yana lallatsawa, tana fitowa ya d'aga ido ya d'an
kalle ta kafin ya maida su kan wayar, anan wurin kayan kallon ta jona ta tsaya tana jira ya gama
turaruwa, tana cikin tsayuwar aka k'wank'wasa kopar parlon Haisam ya bada izinin a shigo, Saude ce ta
shigo hannun ta ruk'e da d'an babban basket mai d'auke da kayan Breakfast ta tsaya daga bakin kujerun
tana gaishe da shi ya amsa tare da d'an kallon ta ta nufi c-table zata d'aura yace ta kai dining area ta
amsa da to ta wuce, Fatuu na tsaye tana kallon ta da murmushi tun da ta shigo itama murmushin take
mata ta nufo in da take, tana zuwa Fatuu ta amshi basket d'in tana gaishe da ita ta fad'ad'a murmushin
ta tana amsawa, godiya Fatun tayi mata k'asa k'asa da murya tace "Yayi kyau Amaryar mu, naji dad'in
ganin ki haka sosae" yar kunya ce ta kama Fatun tana ta murmushi ta d'an sadda kan ta, tambayar ta tay
mi take so a dafa masu da rana ta d'ago tace mata ko mi ta dafa tana ta murmushi tace in dai akwae
abunda take so ta fad'i kar ta ji nauyi Fatun tace mata da gaske duk abunda ta dafa yayi tace to shikenan
sukai sallama ta juya, kan Dining table ta kai basket d'in ta d'aura sama, juyowa tay ta nufi Kitchen plates
da cups da sauran abun da zata buk'ata ta d'aukko saida ta d'auraye su tare da hannuwan ta da tay aikin
sa turaren wuta sannan ta fito ta koma dining d'in, wata babbar Warmer a cikin kayan ta fiddo ta bud'e
nan take wani irin k'amshi ya bugi hancin ta, Kaza ce guda d'aya babba ta gasu tasha kayan yaji da spices
sun manne a jikinta daga k'asanta kuma a tsage yake tasa spoon ta juyata ta bud'e wurin nan take taga
ashe Chicken and Chips ne ta ta6a gani Sauden tayi ba dai dad'i ba soyayyen dankalin turawa da dafaffen
kwai ake cusawa a cikin Kazar bayan an tafasa ta sai a d'inketa a shafe ta da butter a bad'a kayan yaji da
spices sai a gasa su tare a Oven, gani tay in ta yaga zata 6ata ta hakan yasa ta k'yale ta fiddo ledan sliced
bread dake ciki ta aje kan table d'in sannan ta fiddo kayan tea da Flask mai d'auke da ruwan Lipton da ya
sha kayan k'amshi sai wani bowl mai murfi ta bud'e shi nan kuma wainar k'wai ce murtuka murtuka,
tunanin ta fara mashi magana kafin ta had'a tay hakan yasa ta nufi cikin parlon tana tafiya a hankali kai
kace yanga take saidai kamata da kayan sukai ne yasa hakan, tana zuwa bakin kujeru kafin ta k'arasa
taga ya mik'e ya tunkaro inda take yana zuwa saitin ta yay mata wani kallo ya wuce abun shi ta juya ta bi
bayan shi, bayan ya zauna ta fara had'a mashi tea d'in tana yi tana tambayar yadda zata saka mashi
komai har ta gama ta tura gaban shi ta fiddo kazar ta d'aura akan plate itama ta tura mashi ta curo waina
d'aya daga cikin bowl d'in tasa a wani plate ta tura mashi sauran dake a cikin bowl d'in duka sannan ta
d'aukko ledan biredi ta bud'e ta curo yanka biyar ta d'aura a gefen wainar k'wan da ta d'auka ta tura
mashi ledan itama yana dai ta kallon ikon Allah, har ta gama had'a tea d'in ta ta zauna bai ta6a komae
ba, hannu ya kai ya ciro slice na bread ya yagi wainar kwai ya had'e sannan ya d'auki cup d'in tea ya fara
sha a nutse, kallon shi tay bayan wani lokaci ganin bai ta6a kazar ba yasa a hankali tace "gashi nan ka ci
while it's still hot kar ta huce" shiru bai ce Komai ba bai kuma kalleta ba saida ya k'ara sipping tea kaman
sau biyu sannan ya d'aga ido suka sauka cikin nata, da hannu tay mashi nuni da kazar ya kai idon shi kan
ta kafin ya sake maido su a kanta "miye wannan d'in?" d'an waro ido tay jin wata tambaya kenan ma bai
gane shi ta aje mawa ba, cikin yar inda inda tace "C... chicken and Chips ne" hannu ya kai ya d'an ruk'e
ha6ar shi taji yace "mi za'ai dashi?"

"Kai na aje mawa ka ci" tay Maganar tana d'an kikkafta idanu,

"Na zama ke kenan?" ya tambaya had'i da d'an d'age mata gira ta d'an zaro ido sai kuma ta d'an tura
baki "ai ba ina nufin ka cinye shi ba duka kawae naga in na 6ara ta zan 6ata ne shiyasa na bar maka in ka
ci ka rage sai in ci, kuma ma ai nima ba iya cinye ta zan yi ba ko" yadda tay Maganar cike da shagwa6a
saidae ita matsayin lafiya lou take Maganar ta, d'an guntun murmushi taga yayi gashi ya kafeta da ido ita
kuma sai faman kikkafta nata take tana d'an juyar da fuskar, wani plate ya d'auka ya rufe kazar ya kai
hannu ya d'auki cup d'in shayin ya cigaba da sha, bayan ya cinye waina d'aya ya tura mata bowl d'in ta
d'an kalle shi, saida ya k'arasa shanye tea d'in ya bud'e kazar ya d'aukko fork ya fara k'ok'arin 6alla sai dai
kuma tak'i 6alluwa ta dad'i, aje fork d'in yayi ya kai hannu wurin cutlery set d'in dake a tsakiyar table d'in
ya curo yar wuk'a, d'an jim yay bai sata jikin Kazar ba ganin tana buk'atar a wanke ta tunda anan suke aje
lokaci guda Fatuu ta fahimci dalilin dakatawar tashi ta mik'e ta mik'a hannu alamar ya bata ya d'aga ido
ya kalleta kafin ya bata, bayan ya mik'a mata ta fita daga cikin kujerar ta nufi hanyar kitchen ya bi bayan
ta da kallo har ta shige Corridor sannan ya juya da wani irin yanayi akan Face d'in shi, had'e hannuwan
shi yay ya d'aura ha6ar shi a ranshi ya raya yakamata a sa washbasin a wurin Saboda zaryar da yaga tana
yi, bada jimawa ba ta dawo ta wanko wuk'ar ta mik'a mashi amman sai bai amsa ba yay mata alamar ta
zuba mashi, ganin kazar ta d'an mata nisa yasa ta zagaya daga gefen shi ta jawo plate d'in ta fara yankar
mashi, gaba d'aya sun cika juna da fitinannan k'amshin jikin su Haisam har d'an lumshe ido yay slowly ya
bud'e ba tare da ta gani ba, tana yanko wurin cinye ta d'aura mashi a plate zata k'ara ya d'aga mata
hannu alamar ya isa ta kai idon ta kan shi suka had'a ido, d'an tura baki tay ta marairaice fuska a hankali
ta furta mashi gaskiya bai isa ba yayi kad'an, ido ya bita dashi da alama ya kasa ce mata komai ta k'ara
yanko wani ta d'aura, kallon shi tay ta d'an bud'a ido ta tambayi ta k'ara ya d'an wurga mata harara ta
saki murmushi tace to bari a zuba mashi mahad'in kazar ta d'ebo dankalin ta zuba tana shirin sake
d'ebowa ya kai hannu ya ja plate d'in ba tare da ya ce komae ba ta k'ara yin murmushi, tana shirin
komawa wurinta taga ya kai hannu ya tura plate d'in kazar wurin da ta zauna, bayan ta koma ta zauna a
nutse suka cigaba da yin Breakfast d'in tana yi tana d'an satar kallon shi, saida ya cinye wanda ta zuba
mashin ya yago tissue ya goge bakin shi, mik'ewa yay zai bar wurin ya juya suka had'a ido taji yace ya
bata space ta cinye komai ta d'an bud'a ido ya juya ya tafi tay d'an murmushi had'i da d'an girgiza kai, ba
laifi ta d'an ci sosae bayan ta gama ta mik'e ta fara kwashe kayan tana kaiwa kitchen, saida ta wanke
abubuwan da suka 6ata kazar da ta rage ta saka ta fridge wainar k'wan kuma da ledan biredin ta ajiye su
saman counter, bayan ta gama fitowa tay ta wuce Bedroom saida ta d'aukko wayar ta daga cikin purse
ta koma gefen gado ta zauna, bayan ta bud'eta tunanin wa zata kira ta shiga yi can ta kira Fauzy tana
fara ringing ta d'aga,

yar shewar farinciki tay tace "K'awata Amarya ai ban tsammaci ganin kiran ki ba don banyi tunanin zaki
tuna da wata Fauzy ba da wuri haka" d'an murmushi mai sauti Fatun tay ta tambayi ya suke da Aunty
Mareeya tace mata duk suna lafiya ta k'ara ce mata ya gajiya had'i da yi mata godiya, tana dariya tace ai
ita ke tattare da gajiya su tasu tabi jiki tuni har saida Fatun ta d'an girgiza kai, tambayar ta Ya Haisam
Ango tayi tace mata yana parlor, hiran School suka shiga yi ta tambayi yaushe zata dawo Fatun tace
mata jibi in Allah ya kaimu,

"ah haba dae jibi, ki bari sai kin gama cin Amarci kaman after a week sai ki dawo" tana murmushi tace
mata so take ta samu matsala kenan Fauzyn tace to ta bari sai kaman Wednesday tazo amman ba jibi ba,
tuna mata tay tace kar Amarci yasa ta manta da Assignment d'in da aka basu ran Friday dai, Fatun tace
to zata yi jakarta ma na gida amman yanzu zata kira Kawu Amadu ya kawo mata, daga baya sukai
sallama tana ce mata ta gaishe mata da Ango tana murmushi tace zai ji,

Bayan sun gama wayar Kawu Amadu ta kira har saida ta kusa yankewa sannan ya d'aga ta gaishe dashi
yana yar dariya yace "Amaryar mu kun tashi lafiya" amsa mashi tay da lafiya lou suma ta tambayi ya suka
tashi yace mata lafiya, jin ta d'an yi shiru yasa shi tambayar ta lafiya dai ko cikin yar in ina tace mashi
dama don Allah so take ta rok'e shi ya kawo mata jakarta ta makaranta, farko cewa yay shi ba zai kawo
ba ta marairaice tana rok'on shi k'arshe sai cewa tay shikenan bari tazo ta d'auka da kanta yana dariya
yace ai dama yana cikin shago ya sake ya ganta sai ya zane ta kuma da tsallan kwad'o zai maida ta, itama
dariyar take a hankali tace mashi ai yanzu ta wuce wannan a wurin shi yace eh lalle ta isa shi take gaya
ma haka ko to ta gwada fitowar zata sha mamaki, rok'on shi ta k'ara yi yace bari ya kawo mata tay mashi
godiya ta tambayi gwaggo yace ta na cikin gida, bayan sun gama wayar d'an jimm tay tana son kiran
gwaggo amman kunya take ji, can dai tay dialing lambar ta ta fara ringing, bayan ta d'aga a kunyace ta
gaishe da ita tana murmushi ta amsa tay mata sun tashi lafiya da tambayar d'anta Haisam Fatun tace
mata yana parlor tace to ta gaishe mata da shi tace to, d'an shiru sukai can gwaggon ta ce badai wata
matsala ko da sauri tace mata eh ba komai, tambayar ta tay wai ta fad'a ma baffanta zancen gwaggon
tay yar dariya tace ta fad'a mashi mana yayi farinciki sosae ma, cikin yar shagwa6a tace amman shine bai
kirata ba tace k'ilan ya bari sai an samu natsuwa ne, bayan sun gama ta shiga kiran Baffan nata cikin sa'a
ta shiga ya d'aga ta gaishe da shi yana murmushi ya amsa ya tambayi ya take ita da maigidan nata, cike
da shagwa6a tace "Baffa shine kasani amman baka kira ni ba gaba d'aya ma ka manta dani" yar dariya
yayi "haba ni na isa in manta da inna wuro gaba d'aya, dama zan kira na bari a nutsu tukun, na matuk'ar
yin farin ciki da jin abun Alkhairi wllh har bazan iya kwatanta maki ba ashe dai rabon shine mijin naki
yasa komae ya faru, kinga sakamakon yi ma iyaye biyayya Allah ya juya komai, Nagode inna wuro ina
matuk'ar Alfahari dake matsayin jinina, ina rok'on Allah ya k'ara ma rayuwar ku Albarka ya jikan
Mahaifiyar ku" har k'walla sun taru a idanun ta ta amsa mashi da Amin, tambayar ya karatun ta yay tace
mashi Alhamdulillah yace Allah ya bada sa'a, bayan ta amsa ta tambaye shi Yadikko yace tana d'aki bari
ya mik'a mata tace to, bayan ya kai ma Yadikkon cike da Farinciki tana washe baki suka gaisa tana fad'in
Amaryar su, tambayar ya gida da Angon ta tay Fatun ta amsa mata ta shiga yi mata Allah yasa Alkhairi da
nuna yadda tay murna da Al'amarin tace Addu'ar da suke tayi ce Allah ya amsa taji mata dad'i sosae wllh
da Al'amarin ya juye haka dama haka take ta fata, daga jin yadda take Maganar Fatuu ta fahimci ba
k'aramin farinciki take ba, tambayar ta su Mino tay tace basu kaiga dawowa daga islamiyya ba tace to in
sun dawo zata kira ta tambayi yaushe zasu zo tace suna nan zuwa in ta Haihu, a shagwa6e tace a'a ita
dae bata yarda ba wllh tana dariya tace suna nan zuwa bada dad'ewa ba, bayan sun gama Magana da
Yadikkon ta ba Baffan wayan suka cigaba nan yake tambayar ta Haisam yace bai da Lambar shi yana son
yi mashi godiya tace ai yana nan ko a kai mashi yace to, mik'ewa tay da sauri ta nufi hanyar fita, Yana
kishingid'e kan kujera ta tunkaro shi Wayar kare a kunnanta, tana zuwa daga gefe ta tsaya ta cire wayar
daga kunnan ta a hankali tace mashi Baffan ta ne yake son Magana da shi ya d'an d'aga mata kai ta mik'a
mashi wayar ya amsa, gyara zama yay a nutse ya gaisa da shi nan ya hau yi mashi godiya sosae da
Addu'oi, k'asa k'asa yake amsa wasu wasu kuma yay shiru daga baya sukai sallama ya mik'a mata phone
d'in idon shi cikin nata da d'an murmushi ta amsa ta maida ta kunnan ta, har ta juya kaman zata tafi sai
kuma ta dakata tana tambayar Baffan yaushe zasu zo to jin yana mata sallama yace mata ba yanzu ba sai
an d'an jima, aikuwa cike da shagwa6a ta hau Jujjuya jiki tana ita dae bata yarda ba don Allah su zo
kwanan nan kai kace da gayya take juya jikin saidae ita bata ma san tana yi ba kuma da alama ma ta
manta da a gaban Haisam d'in take, shi kuwa kafe bayan nata yay da ido da wani kalan expression mai
wuyar fassaruwa yake kallon nata, bayan sun yi sallama ta juyo suka had'a ido ta sakar mashi d'an
murmushi shima ya d'an yi mata, juyawa tay zata tafi taji yace in ta gama abunda take zasu gaishe da
Hajiya ta juyo tace mashi to sannan ta tafi, tana komawa Bedroom d'in bada jimawa ba akai knocking
kopar ya bada izinin shigowa, Amadu ne ya shigo ruk'e da jakar Fatun da d'an murmushi ya nufi cikin
parlon ya tsaya daga gefe yana gaishe da Haisam d'in, bayan ya amsa ya nuna mashi armchair yace ya
zauna mana, mik'ewa yay ya nufi hanyar Bedroom d'in da alama kiran ta zai yi, yana tura kopar daidai ta
kawo bakin kopar zata bud'e ta yafo mayafi golden da ta sa jiya da yake a atamfar akwae golden brown
harda takalman da ta saka jiyan mahad'in gyalen half cover masu tsini sun k'ara mata tsawo ta tattara
gashin ta a baya ta sa red ribbom sai yayi kaman ta saka hular gashi don ya rufe gefe da gefen fuskar,
tura kopar da yay ta buge mata goshi da sauri taja baya had'i da sa hannu guda ta dafe wurin da ta
bugen, bai yi zaton tana a bakin kopar ba yay moving zuwa inda take tsaye ya kai hannu ya cire hannun
ta da ta dafe goshin wurin har ya d'an canza kala, bin wurin yay da kallo ya kasa furta komae don gaba
d'aya wata irin kasala yaji ta fara saukar mashi sakamakon K'amshin ta da ya cika mashi hanci, jin yayi
shiru yasa ta d'aga ido ta kalle shi suka sauka cikin nashi nan take gabanta ya fad'i ganin irin kallon da
yake mata da sauri ta sauke idon ta k'asa, d'ayan hannun nashi slowly ya zagaya dashi bayan ta ya matso
da ita suka had'e da juna nan take wutar Fatuu ta d'auke ta fara shiga wani irin yanayi dama kuma a
tsume take har saida ta d'an runtse ido, jikinta ne ya canza wata irin kasala ta baibaiye ta wani abu ya
fara mata yawo a jiki ga k'afafuwan ta na neman kasa d'aukarta, sauke gudan hannun shi da ke ruk'e da
natan yay k'asa ya d'an sunkuyar da face d'in shi Slowly ya d'an fara matsawa da ita saitin tata, jin saukar
breathing d'in shi a gab da Fuskar ta yasata d'agowa da sauri har saida gabanta yay wani irin bugu ganin
fuskar shi kusan saura kad'an ta had'e da tata, wani irin kallo mai wuyar fassarawa suka shiga bin juna da
shi, da k'yar Fatuu ke daurewa gudun kada ta zaqe don ta kai wata ga6a da take neman rasa control
idanun ta har sun fara lumshewa sai k'ok'arin daidaita su take amman abun yaci tura kawae sai ta rufe
su gaba d'aya, bin dogayen eye lashes d'in ta yay da kallo sai d'an far far suke sakamakon idanun nata
dake motsi, numfashin ta ne ya nemi tsayawa jin ya had'e faces d'in su nan take jikinta ya fara d'an rawa
ta koma yin numfashi da sauri da sauri shima nashi da d'an k'arfi yake fita yana had'uwa da nata, sun
d'an d'auki lokaci a haka suna ta shak'ar scent d'in juna, can ya janye fuskar ta shi a hankali ya maidata
gefen tata ta yadda kwantaccen sajen shi ya had'e da gefen tata fuskar cikin wata irin murya mai fuzgar
mai sauraro ya furta "am sorry, bansan kina a wurin ba...." Kasa ko d'aga mashi kai Fatuu tay idonta still
na a rufe taji ya k'ara furta "Uncle d'in ki na jiran ki a parlor" yana yin Maganar ya d'ago ya cire hannun
shi dake tallabe da ita ya juya ya nufi hanyar Laundry ba tare da ya ko kalleta ba, da k'yar ta d'an bud'e
idanun ta da suka gama canza kala tabi bayan shi da kallo kar ya shige ya rufe kopar, kasa cigaba da
tsayuwar tay don gaba d'aya jikinta ya gama mutuwa da k'yar ta ja jiki zuwa bakin gado ta zauna dabas
still breathing heavily, hannu tasa ta dafe goshin ta ta d'an sadda kai, ita kad'ai tasan mi take ji a jikinta,
da k'yar ta fara k'ok'arin daidaita kanta tunowa da yace Kawu Amadu na a parlor, mik'ewa tay jiki a mace
ta nufi kopar ta bud'e, bayan ta fito saida ta k'ara tsayawa a cikin Corridor ta k'ara daidaita natsuwar ta
sannan ta nufo cikin parlon, tana shiga suka had'a ido ta fara mashi murmushi wanda yafi kama dana
yak'e shima d'an murmushin yake mata ta nufi inda yake, a d'ayar armchair d'in ta zauna ta gaishe da shi
ya amsa shiru ta biyo baya don sai taji kaman muryar ta ba a daidai take ba, hannu ya kai ya d'aukko bag
pack d'in daga k'asa ya d'auro ta kan hannun kujera yace mata ga ta nan da k'yar tace mashi ta gode,
ganin ya mik'e alamar tafiya zai yi yasa cikin yar rawar murya tace don Allah ya tsaya yay breakfast yay
mata wani kallo mai kaman harara ya juya ya tafi ta k'ara ce mashi ta gode ya d'aga mata kai kawae
lokacin ya bud'e kopar ya fita, zaune tay turus tama rasa mi yake mata dad'i a hankali ta d'aga ido ta
kallo kopar Bedroom d'in ta shiga tunanin zuwa zatai tay mashi magana su tafi ko kuwa, ji tay bazata iya
zuwan ba tay zaune zuciyar ta na tariyo mata abunda ya faru a tsakanin su, tana haka bayan wani lokaci
taji k'arar bud'e kopar Bedroom d'in aikuwa da sauri ta sunkuyar da kanta k'asa, nufo cikin parlon yay
idon shi akanta ya tsaya daga gefen ta taji yace zasu iya tafiya sai lokacin ta d'ago ta kalle shi ta d'an
d'aga mashi kai, mik'ewa tay har zai juya sai kuma ya dakata ya juyo yana kallon ta ta d'an kawar da
fuskar ta, "How are feeling, ko wurin na ciwo muje Hospital?" D'an kallon shi tay had'i da girgiza kai a
hankali tace a'a yama daina zafin ya jinjina kai yay gaba ta bi bayan shi a ranta ta shiga raya kenan duk
abunda yay mata d'azun ban hak'uri ne Saboda ya buge ta, yana gaba tana biye dashi suka shigo harabar
gidan, suna cikin tafiyar ta kai idon ta can gefe wurin parking space ta hangi d'awisu ya bud'e jikin shi
yana kuka gwanin burgewa, murmushi Fatuu ta saki tunowa da can baya lokacin da ta kawo ma shi Fruit
na karin ciwo ta iske zashi Masallaci har suka fito tare ta tsaya a harabar tana ma d'awisun wasa shi
kuma ya nufi hanyar Masallacin yana d'an d'angyasa k'afa Saboda raunin da yaji da kwalba, gab da zai
shiga ta kware murya tace Ya Handsome kayi man Addu'a Allah yasa in zama likita ya d'aga mata kai ba
tare da ya juyowa ba, fad'ad'a murmushi tay bata ta6a kawo wa a ranta wai zasu yi aure ba don ita
auren ma bai gabanta a lokacin duk da kuruciya, ko ba aure a tsakanin su Haisam nada daraja a wurinta
ta silar shi ne ta san kanta ko lokacin da ta kasa mashi uzuri da abu ya Faru tsakanin su harda girman da
yake da shi yasa duk da tana tunanin laifi yayi mata amman bata son girman shi ya fad'i ne gashi hakan
ba K'aramin karya mata zuciya yay ba don tana ganin ita tana k'aunar shi shi kuma sha'awar ta yake ashe
duk ba haka bane, Kallon bayan shi taci gaba da yi wata irin k'aunar shi na ratsa mata zuciya har tana
d'an yin murmushi a haka har suka k'araso part d'in suka shiga,

lokacin da suka shiga basu samu kowa a cikin parlon ba an dai gyara shi fess sai k'amshi ke tashi, Hanyar
Bedroom d'in ta ya nufa ta bi bayan shi, knocking kopar ya d'an yi daga ciki ta bada izinin a shiga ya tura
da yar sallama ya shiga, tana zaune a bakin gado idanunta sanye cikin glasses hannunta ruk'e da Littafin
Addini tana dubawa bata dad'e da komawa cikin d'akin ba bayan ta yi Breakfast, d'ago ido tay ta kalle shi
tana niyyar yin Magana Fatuu ma ta shigo da sallama Hajiya ta saki murmushi tana amsa mata kafin tace
"Maraba da Amaryar mu" d'an sadda kai tay Hajiyar ta nuna mata gefen ta da hannu alamar tazo ta
zauna, tsaye Haisam yay daga gaban gadon bai zauna ba ya gaishe da ita ta amsa tay mashi an tashi
lafiya, kai idon ta tay kan Fatuu da ta d'an sunnar da kai da murmushi tace "Amarya an tashi lafiya ya
bak'unta kuma?" a hankali tace Lafiya lou,

"Ba dai yar kunya muka fara dake ba" Hajiya ta tambaya tana murmushi hakan yasa Fatun d'agowa
itama murmushin ne akan fuskar ta a hankali tace mata a'a, "Yauwa to, ni ba surukar ki bace Kakar kice a
hakan zaki cigaba da kallo na muci gaba da wasa da dariya kaman da, don ma yanzu anyi hankali
natsuwa tazo an rage sani nishad'i" yar dariya Fatuu tay ba tace komai ba, kallon Haisam tay "Kai kayi
tsaye kaman wani Security ka samu wuri mana ka zauna, ko gadin Matar taka kake?" Fuskar shi a sake
kaman zai murmushi ya kalleta ta nuna mashi Stool a gaban mirror tace ya d'aukko shi sai ya zauna, yin
yadda tace yayi suka d'an yi shiru kafin ta fara magana,

"Alhamdulillah, duk abunda Allah yayi mai kyau ne, a koda yaushe muna rok'on Alkhairi so duk abunda
muka ga ya faru damu in ma mai kyau ko akasin hakan Alkhairi ne, Fateema ina maki barka da shigowa
wannan Family don a yanzu kin zamo wani 6angare nashi, ina fata zaki d'auke mu a matsayin dangin ki,
ki rungumi kowa matsayin dan'uwan ki duk da bani da shakku akan ki nasan ki farin sani nasan baki da
matsala to sai kinyi hak'uri don shi mataki ne nasara ba kamar a yadda Auren naku ya kasance, dole daga
baya za'a iya fuskantan yan matsaloli bama fata in sha Allahu muna fatan Allah zai shige mana gaba,
sannan ina son ki saki jikin ki kada wai ko don kiga ga yadda akai auren naki ki takura kanki Ki k'i yin
walwala, duk aure aure ne duk kuwa yadda aka yi shi ki walwala ki farinciki ki Alfahari da Auren, gidan
mijin ki naki ne so ba buk'atar takura kai, duk yadda bani da haufi akan mijin ki ance wai zo mu zauna zo
mu sa6a, so a duk lokacin da yay maki wani abu da baki ji dad'in shi ba ki k'ok'arin yi mashi Magana kada
kice zaki bar abun a ranki duk d'an Adam ajizi ne zai iya yi maki laifi ba tare da ya ankare ba, ta hanyar yi
mashi magana ne zai gane har ya gyara laifin shi, in kuma bai gyaran ba wanda bana tunanin hakan ni
kizo ki sanar dani kar kiji wani abu, duk yay maki wani abun da kike tunanin fad'i ma wani don neman
mafita ko shawara kizo wuri na kar kice zaki kai k'ara gidan ku hakan ba komai yake jazawa ba face
matsala, zai iya maki abu kije ki fad'a daga baya ku shirya ki manta ma amman su kuma abun na nan a
ran su watak'il su k'ullace shi ko makamancin hakan, don haka k'opa ta a bud'e take duk in kina da wata
matsala kizo gun Hajiyar Sanata ki fad'a mata ni kuma in sha Allahu zanyi k'ok'arin ganin na daidaita
komai, ina Fatan zaki cigaba da yi mashi biyayyar dana san kina mashi kada don ya zama mijin ki kice zaki
rage kan hakan a'a a yanzu k'arawa ya kamata kiyi don muhimmancin shi a yanzu yafi na da ya tashi daga
Yayan ki Handsome ya koma Mijin ki wanda Aljannar ki ke a tafin kafar shi" d'an dakatawa tay kan Fatuu
a k'asa haka Haisam d'in Fuskar shi na a gefe,

"Na dawo gare ka Zakee manyan dawa, ga Fateema nan Amana ce a wurin ka duk da nasan kasan da
hakan amman ina fad'a maka ne don kada ya zama ba wanda ya fad'a maka hakan, ka ruk'e ta Amana
dama can kai kamar guardian ne a gare ta to yanzu matsayin ka ya koma biyu don haka sai ka linka
komae, kuma don ta zama taka ba yana nufin ta zama baiwar ka ba duk kyautatawar da zaka yi mata
lada zaka samu haka in har kaci zarafin ta ka munana mata tabbas zaka samu zunubi don haka ta zama
taka ne don ka kyautata rayuwar ta, sannan ina son jan hankalin ka kayi k'ok'arin zama adali ga matan ka
nasan ba sai nayi maka bayanin yadda zaka zama adali ba kasan miye yin Adalci tsakanin mutane, idan
har ka za6i yin rashin Adalci to ka bud'e ma kanka da kanka kopar matsalolin da zasu hana maka
kwanciyar hankali ga kuma zunubi a wurin ubangiji, a k'arshe ina Addu'ar Allah yasa Albarka a Auren ku
ya kauda duk wata fitina, yasa ya zame maku silar shiga Aljanna gaba d'ayan ku, Amin ya Rabbi" a
hankali Haisam ya amsa da Amin Fatuu kuma a cikin rai ta amsa Hajiya ta kai hannu ta d'an bugi shoulder
d'in ta tace ita bazata amsa ba ta d'ago tana yar dariya tace ai ta amsa,

"Oh Fateema ni wannan in nayi sakaci ban yi da gaske ba yar gaisuwar da nike samu yana zuwa ma ai sai
ki hana shi ya tattara ni ya zuba a dustbin" cikin rashin Fahimta Fatun ta d'an waro ido Hajiya taci gaba
"eh mana, kina irin wannan kwalliyar ina zai rink'a tunawa da wata tsohuwar matar shi..." Tun kan ta
rufe baki Fatun tasa tafukan hannuwan ta ta rufe fuska Hajiyar nata dariya, a hankali Haisam ya d'ago ya
kalli Fatun suka had'a ido da Hajiya ta d'an harare shi cikin wasa yay d'an guntun murmushi ya juyar da
fuskar shi gefe,

"Yanzu dae ki bani cin hanci sai in yafe maki shi in kuma fad'a maki abubuwan da zasu sa ki kama shi a
hannu" cire tafukan hannuwan tay tana murmushi bata ce komai ba, mik'ewa yay yace ma Hajiyar zai
d'an je G.r.a tace a dawo lafiya ya nufi hanyar fita, kallon Fatuu Hajiya tay ta d'an kai mata bugu tace
bazaki tashi ki raka shi ba yaran zamani duk baku san abunda ke sa ana kama miji ba, mik'ewa tay a
kunyace ta nufi hanyar fita Hajiya ta bita da ido tana murmushi a ranta ta ayyana Allah kenan gwanin
hikima, wasu mutanen na shigowa rayuwar mu ne in ma su amfane mu ko mu mu amfane su, wasu su
tsaya wasu kuma su tafi bayan sun taka rawar da zasu taka, a fili ta furta "Allah kasa Mudace", tana
fitowa har ya kusan fita daga parlon taja ta tsaya a bakin corridor, kamar yaji a jikin shi ya juyo suka
had'a ido, dakatawa yay ganin haka yasa ta nufe shi walking slowly, a d'an gaban shi ta tsaya tana bin shi
da kallo ganin ya kafeta da ido yasa cikin yar inda inda tace "D...dama Hajiya ce tace in rako ka" da k'yar
ta kai Maganar Saboda kallon da yake bin ta dashi ba Arzik'i ta sunkuyar da kanta,
"Ok thanks, ki koma" taji yace ta d'ago, kai ta d'an d'aga mashi yana shirin juyawa tace "Sai ka dawo
Allah ya tsare" dakatawa ya sake yi ganin yanayin fuskar shi kaman zai murmushi yasa itama ta d'an yi
mashi, "Do you need something?" da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a ya d'aga kai ya wuce, saida
taga fitar shi sannan ta juyo tana d'an sakin Murmushi ta nufi komawa Bedroom d'in Hajiya..............

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2064*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

..........tana shiga tace mata ya tafi ta d'aga mata kai kafin tace eh a hankali , a inda ta tashi ta koma ta
zauna Hajiya ta fara magana "irin nuna kulawa haka yana k'ara dank'on k'auna tsakanin ma'aurata,
yanzu kinga kece abu na k'arshe da ya gani kafin ya fita to zaki ga kin tsaya mashi a ran shi yana tafiya
yana tunanin ki har ma kiga yana d'an murmushi kaman ta6a66e, ba kamar yadda kika ci gayun nan"
Dariya Fatuu ta saki ba kaman da tace kaman ta6a66e ta bata dariya sai Maganar ta tuno mata da
Maganar Aunty Mareeya, itama hajiyar Dariyar take taci gaba "naji dad'i dana gan ki haka tsaf kin sha
gayu wannan ma zai taimaka wurin siye zuciyar shi don shi mutum ne mai tsananin son tsafta nasan kin
san da hakan, ga son k'amshi don haka ki dage da tsafta, amman fa kuma kar tay yawan da zaki janye
man hankalin shi gaba d'aya" ta d'an ta6e baki, sosae Fatuu ta saka dariya, cigaba tay bayan ta d'an
murmusa,

"Komai nashi Sak kakan shi wllh, yana tuna man dashi a koda yaushe shiyasa bazan 6oye ba a duk
jikokina nafi jin shi a raina kowa ma ya sani, hatta y'ay'an cikina ban jin su kaman yadda nake jin shi, Duk
irin halayen shi na kakan shi ne, koda ake ganin Sojoji kaman basu da kirki basu da tausayi ba haka bane
kowa da irin halin shi kaman dae a sauran mutane....." D'an dakatawa tay tana kallon hoton Gen. Adamu
Zakee dake a jikin bango cikin shiga ta Alfarma, da gani akwae k'auna mai k'arfi a tsakanin su kuma
rashin shi ba k'aramin ta6a mata zuciya yay ba,

"Shima haka yake da son K'amshi, ko 6ata mashi rai kikai in dae zaki je bashi hak'uri ya kasance kina
sakin k'amshi to Magana ta k'are tuni zai yafe maki, koda ma ba ke kika 6ata ran ba in dae zaki rarrashe
shi kina k'amshi yanzu ya saukko" idonta akan hoton take Maganar, tausayin ta ne ya kama Fatuu itama
ta kai idon ta kan hoton ta d'an girgiza kai, bayan d'an wani lokaci Hajiya ta sauke idon ta tare da ajiyar
zuciya, kallon ta Fatuu tay da d'an murmushi tace "Allah ubangiji ya jik'an shi da rahama yasa ya huta,
Allah ya h....had'a ku a Aljanna" tana murmushi ta amsa da Amin sai kuma tace "muci gaba da soyewa
acan ko?" Dariya Fatuu tay suka d'an yi shiru, can ta kalle ta tace bari taje wurin Aunty Saude ta taya ta
aiki,

"to ke waya fad'a maki Amarya na wani aiki, ki zaman ki ki huta, ki k'yale ta tayi aikin ta lokacin yin aikin
zai zo sai kita yi" shiru tay ta maida kanta k'asa, "in kina son zuwa kije k'yama k'ara koyon wasu
abubuwan tunda Saude ba daga baya ba wurin iya girki tasan hannun ta, sai ki dage ki k'ara koya duk da
ma Mijin naki ba gwanin cin Abinci bane, amman k'ilan ya rink'a cin na Matan shi" tana d'an murmushi
ta mik'e zata tafi, har ta juya Hajiya ta dakatar da ita, "Yauwa na tuna, Maganar gyaran part d'in naku
Tukur ne ke yi, to tun kafin ki tare yayi man magana kan zai cigaba ne ko a'a nace ya bari ki zo duk da dai
shi Namiji ne ina ganin baida Matsala, amman ke ya kike so" d'an jimm Fatun tay ta rasa mi zata ce
Hajiyan tace ta bud'e baki tay magana, a sanyaye tace duk yadda ta yanke yayi,

"Shi d'in ne ya nuna yana so, tun farko ma ni ba shi naso yayi aikin ba bayan Haisam d'in ya dawo sawa
nayi ya nemo wani amman ya matsa, kwanaki har zaunar dashi nayi nai mashi Magana kan hakan tunda
ko ni bai bari akai kayana wurin wanki ga Karatu lokacin amman sai cewa yay wai baida abunda zai saka
mana sai dai hakan kawai, nace to mu duk abunda ya ga an yi masa ai don Allah ne ba wai don ya saka
mana ba, dama can Allah ya k'addaro akwae rabon shi a tare da mu" ta k'arasa tana murmushi itama
Fatun shi take yi, "Yanzu tunda naga ya nuna yana so ke ki rink'a gyara Bedroom da Kitchen ala bashshi
shi sai ya rink'a gyara maki parlon tunda dama yana da girma ko in kin tafi Makaranta sai ya shiga ya
gyara, Wankin k'ananun kayan mijin naki kuma kyaci gaba in zai mashi na manyan kaya sai yazo nan yay
amfani da injin d'in nan, koma kawae bari na mashi magana tunda ga naki sun k'aru ya bari a rink'a
kaiwa dry cleaning kawai", kallon Fatun tay "lafiya lou zaki rink'a gyara Bedroom d'in da Kitchen d'in ba
takura tunda naga karatu kike?" Da sauri tace mata eh, a ranta ta raya ita da ke yin fin wannan aikin a
gida wannan ai ba wani aiki bane, ce mata tay taje tayi mata godiya ta juya ta fita, Kitchen ta nufa a ciki
ta iske Saude na shirye shiryen d'aura girkin rana, da yar sallama ta shiga ta juyo tana murmushi ta amsa
mata ta nufi gefenta gaban drawer ta jingina fuskar ta da murmushi tace "Sannu da aiki Aunty Saude",

"Yauwa Amaryar mu kun shigo" kai ta d'aga mata suka d'an yi shiru,

"Aunty Saude aiki na zo taya ki" d'an waro ido tay "aiki kuma Fateema keda kike Amarya, ki rufa man
Asiri kar nayi laifi" tana murmushi tace "kai Aunty Saude daga taya aiki sai yin laifi ai na fad'i ma Hajiya
zan zo in taya kin" tace "to amman ai ina iya yin laifi wurin Angon naki yaga duka daga kawo mashi
Amaryar shi jiya yanzu na saka ta aiki" d'an tura mata baki tay tana murmushi "Kai Aunty Saude shi ina
ruwan shi kuma ma ai ya fita bai gidan"

"Ya kamata dai kije ki huta don kina buk'atar shi ansha hidima" still tura bakin ta k'ara tana kallon ta
itama Sauden kallon ta tay tana yar dariya, Fatuu tace "ni dae na huta har na gaji ma" kafewa tay kan sai
ta taya ta aikin girkin tace ai ta k'ara koya ma Sauden tace shikenan tunda ta kafe,

"Mi kike so a dafa tunda ban kaiga d'aura komai ba sai ayi gaba d'aya kawai" d'an bud'a ido tay alamar
mamaki tace "Aunty Saude ni zan fad'i mi za'a dafa" yar dariya tayi "Eh mana ki fad'i abunda kike so a
dafa maku keda Angon naki" d'an jim tay ta maida idon ta k'asa alamar kunya, ganin ta tsaya tana kallon
ta alamar amsa take jira yasa ta d'ago tana d'an far far da ido tace "Aunty Saude kiyi abunda kikai niyya
kawai" tace "to ko shi ki fad'i abunda yake so sai ayi" d'an jimm ta k'ara yi sai kuma tace "to ai kin fi ni
sanin abunda yake so ni dai kawai nasan bai son tuwo da miyan yauk'i"

"Eh bai cin tuwon masara ko dawa da miyar yauk'i sai na shinkafa da yake yana son Abinci irin haka su
sakwara har teba ma yana ci" Fatuu dake kallon ta tace "to ko ayi ebar?" Dariya tay "haba Fateema ya
za'a had'a ango da teba kuma" itama Fatun dariyar tay bata ma san ya akai ta furta hakan ba, "ina ganin
ko ayi sakwara don gaskiya yana son ta" Saude ta fad'a, da d'an sauri ta d'aga kai tace to ayi, amsar
gyalenta tayi ta kai mata d'akinta bayan ta dawo suka fara aikin Pounded Yam d'in ba 6ata lokaci, Fatuu
na tsaye tana yanka su alaiyyahu da Albasa harda ganyen ugu tace "Aunty Saude wai sai yaushe zaki
tare?" tana juya miya tay yar dariya "ai na riga na tare Fateema" da alamun mamaki "kin tare, amman
kuma yanzu ba d'akin ki na cikin nan kika kai man gyale na ba?"
"Eh ai ban bar d'akin ba har yanzu matsayin nawa yake inna shigo ina aiki kinga ba sai nata zarya zuwa
baya ba, kuma ma in ya tafi garin su wurin d'ayar matar shi a nan zan cigaba da kwana" kai Fatun ta
d'aga alamar gamsuwa sai kuma tace "Amman Aunty Saude tarewa ba sanarwa balle ai mana d'an
shagali" tana yar dariya ta k'arasa, itama dariyar tayi "Kai Fateema har kin bani dariya wane shagali kuma
tsofe tsofe dani wannan ai sai ku, kema kawai nasan don ga yadda Al'amarin ya kasance ne da ba
k'aramin shagali za'ai ba duk da haka kina iya ganin anyi daga baya" murmushi kawai Fatun tay tana
fad'in ba wani tsufan da tayi wllh ai da ko yar Walima an yi masu, Sauden tace Hajiya ma taso tayi itace
ta nuna bata so, cigaba da aikin sukai har Sauden na tambayar Fatuu turaren da ta shafa k'amshin yayi
mata dad'i in ba tsada zata siya irin shi tace mata ai Humra ce duk da ta shafa turaren kad'an amman dai
k'amshin na Humra ne, ta fad'i mata wadda ta siyo mata tace aikuwa tana so gaskiya zata bada a siyo
mata Fatun tace ta bari zata d'ibo mata, nan fa suka hau yin yar jayayya Saude na fad'in a'a karta kwashe
abunta ta bari a siyo mata kawai tace to ai kafin a siyo mata sai ta fara amfani da wadda zata batan
tunda akwai da yawa, basu d'au wani lokaci mai tsawo ba suka gama had'a komai saura k'arashe, bayan
an kwashe Fatuu tace bari ta nik'a cikin Food processor Sauden tace ta bari ta daka a turmi tafi dad'i
Hajiya ma tafi son a daka, bayan ta fiddo turmin ta wanke ta fara d'akan sakwara Fatuu ta kafe kan sai
itama ta daka farko Sauden ta k'i bata k'arshe da ta matsa ta bata tana faman fad'in tabi a Hankali don
Allah kada tsautsayin Amarci ya gifta Fatun sai dariya take, kan kace mi daddad'an k'amshi ya karad'e
Kitchen d'in har cikin Parlor, bayan an kammala hada miyan egusi da ta sha ganye ga ganda da kuma
nama tayi wani irin kitif bata ko juya jikinta sai an juya ta, a tare suka nannad'a sakwarar a farar leda,
bayan sun gama a wasu jigunannun luxury Warmers aka zuba tasu Fatun,

"Ban taho da Warmers d'in jiya da kuma kayan breakfast d'in da aka kai yau ba da yake duk akwae
sauran Abinci na saka a fridge, sai dai inna koma sai in kawo ko Almajirai in suna zuwa sai a basu kada ya
lalace" Fatuu tayi Maganar tana kallon Saude, tace "ai Almajiran ma sun zo tun d'azu da safe na tattara
masu wanda za'a basu, amman Abincin nada yawa ne?" d'an jimm Fatuu tay alamar tunani "Eh gaskiya
da d'an yawa don na jiyan bamu ci sosae ba sai breakfast d'in yau shima bread d'in da saura sosae sai
itama kazar wurin rabi ce don shi cinya kawae yaci ma sai chips d'in shima ba sosae ba" Jinjina kai Saude
tay sai kuma tace "amman mi zai hana ki aika dasu gida kawae kinga itama gwaggo ta huta da yin girki
tunda daga ita sai Amadu" d'an waro ido Fatuu tay "Aunty Saude in aika dasu gida kuma, in aka gani fa
zai zama kaman fa nayi rashin gaskiya ne", yar dariya tay ganin yanayin fuskar fatun tace "to miye abun
rashin gaskiya fita da Abinci gidan nan ai ba wani abu bane, kullum cikin fita ake dashi ba wanda zai
maida kai ya ga kinyi wani rashin gaskiya" shiru tay kaman tana nazarin Maganar tata can ta kalleta
"amman Aunty Saude ba ance ba kyau ka d'auki abinci bada izini ba ka bayar" Saude ta fahimci abunda
take nufi wato bada izinin miji ba tace "Wannan ai ana nufin d'anyen Abinci Fateema, amman dafaffe ba
laifi in ka bada gudun kada ya lalace ya zama anyi Almubazzaranci kuma kai laifi" d'an gyad'a kai tay
alamar ta fahimta, saida suka had'a kunun Aya mai shegen dad'i kafin a tare suka kai wanda za a kai
dining table, bayan sun gama Fatuu cikin d'an jin kunya tace mata bari taje tana son tayi wanka Saude na
dariya tace ai haka yakamata, da kanta taje d'akinta ta d'aukko gyalenta bayan ta fito ta shiga Bedroom
d'in Hajiya don yi mata sallama, bayan ta shiga ta iske ta kwance akan gado tana bacci hakan yasa ta juya
zata tafi sai kuma taji muryarta ta kira sunanta ta juyo ta ga ta d'ago da kanta tana kallonta, nufar gadon
tay tana niyyar duk'awa kan Carpet da hannu tay mata alamun ta zauna a bakin gadon, cikin Muryar
wanda ya tashi daga bacci tace "Bacci ne ya d'auke ni halan Azahar ma tayi tuni?" tace "A'a an dai fara
kiran sallar" ta fad'a tana d'an kallon gefe, jinjina kai tay suka d'an yi shiru sai kuma ta sake cewa"har an
gama aikin girkin ne" kai ta d'aga "Eh mun gama zan koma can ne" kanta a k'asa tay Maganar, "Ok, sai ki
tafin maku da naku ma" amsawa tay da to tana k'ok'arin mik'ewa Hajiya ta dakatar da ita da fad'in "kinga
na manta jiya nace zan sa a kirawo balaraba tay maki kitso ko a bari sai yamma kawai" shiru Fatun tay
kanta a sadde tana d'an wasa da yatsun hannunta, ganin bata ce komai ba yasa Hajiya tambayar ko bata
son kitson ne ta d'ago ta d'an kalleta fuskar ta da d'an murmushi ta d'aga mata kai alamar eh, yar harara
Hajiya ta wurga mata "ashe har yanzu halin ki na rashin son kitso na nan Fateema?" Shiru bata ce komai
ba Hajiya tace "yanzu in baki yin kitson zaki takura ne, in gayun Amarci kike son kiyi na k'yale ki aita gayu
lafiya, amman dole ki rink'a yin kitso, amsa mata tayi da to a kunya ce tace mata taje ta mik'e tay mata
sallama.

Bayan ta fito Kitchen ta nufa don ta d'aukko Basket d'in Abincin su ta taras da Saude na gyara Kitchen
d'in, bayan ta d'aukka tay mata sallama ta fito, tana isa part d'in nasu bayan ta shiga parlon ta nufi
Dining Area, a saman table ta d'aura Basket d'in ta shiga fiddo da warmers d'in tana jerawa, bayan ta
gama d'aukar Basket d'in tay ta wuce Kitchen don ta aje, tsaye tay a gaban drawer bayan ta aje ta shiga
tunanin Maganar Aunty Saude tana wasi wasin ta aikata yadda tace ko a'a, can ta yanke yin yadda tace
d'in ta bud'e fridge ta fiddo sauran Kazar da Abincin jiya ta fara k'ok'arin dumama su a cikin Oven, bayan
ta gama ta d'aukko kwalin Warmers masu kyau ta bud'e, mai d'an girma a ciki ta d'auka bayan ta wanke
ta juye Abincin, sake d'aukko wata tayi itama bayan ta wanke ta juye Kazar, shiru ta d'an yi tana tunanin
yakamata ta samu leda ta saka su ba ta aika dasu haka ba can ta tuno da ledar kayan baccin da Aunty
Mareeya ta bata tana da girma Warmers d'in zasu shiga ciki, da sauri ta juya ta fita ta nufi Bedroom,
bada jimawa ba ta dawo ruk'e da ledar ta fara saka Warmers d'in ciki hannun ta har d'an rawa yake,
gaba d'aya sun shiga harda sauran wuri ma nan ta tuno dasu Snacks da ice cream d'in dake a Fridge d'in
parlor ta juya da sauri ta fita daga cikin Kitchen d'in, d'ebo su tay ta saka harda robobin yoghurt da ice
cream guda guda, bayan ta had'a komai tay tunanin kiran kawu Amadu don ya turo mata yaro da sauri
ta juya ta fito ta shiga Bedroom, Wayar ta ta d'aukka ta kira shi yana d'agawa tunkan tayi magana yace
mata miye kuma, yar dariya tay tace ba komai don Allah yaro take son in akwae wanda yazo siyayya ya
turo mata shi yace to, aje wayar tayi ta juya ta fita tay tsaye bakin corridor tana dakon isowar wanda za'a
turon, bada Jimawa ba akai knocking da sauri ta nufi kopar ta bud'e, wani yaro ne d'an unguwar ya turo
tana ganin shi tace mashi tana zuwa ta juyo, ledar ta d'aukko harda dublan ta d'ebo mashi bayan ta
kawo tace gwaggo zai kai mawa ta bashi ta dublan d'in tace gashinan ya ci yana washe baki yay mata
godiya da Allah yasa Alkhairi ta amsa, juyawa tay da sauri ta koma Bedroom ta nufi gaban mirror bayan
ta cire su sark'a da yankunnan ta ta cire kayan jikinta ta d'aura towel ta nufi laundry room, after some
minutes ta fito jikinta sanye da bathrobe da ta gan su cikin cabinet d'in laudary ta d'auka, bayan ta fito
doguwar riga tasa da hijab ta shimfid'a abun salla ta kabbara sallar Azahar da har angama ta a Masallacin
gidan, bayan ta gama ta cire kayan ta linke da abun sallan ta maida kowanne wurin shi ta d'auki towel ta
d'aura sannan ta nufi gaban mirror ta fara shafa, tana cikin yi wayarta ta fara ringing ta nufi gefen gado
ta d'auka har saida gabanta ya fad'i ganin gwaggo ce mai kiran, bayan tayi picking ta gaidata nan tace
mata mi ta aikata haka da sauri ta tari numfashin ta ba kamar yadda taji tayi Maganar cikin yar rawar
murya ta fad'i mata duk yadda sukai da Saude, yar ajiyar zuciya ta sauke tace mata duk da haka yayi wuri
da yawa ta fara hakan tace to zata kiyaye daga baya sukai sallama, bayan ta gama shafe shafen da goge
gogen ta nufi wurin jakunkunan kayanta ta duk'a, tunanin kayan da yakamata tasa ta shiga yi, tana son
saka k'ananun kaya don ko a gida tafi saka su ba kamar in ba inda zata je saidae tana gudun yay wani
tunanin na daban, d'aya daga cikin Akwatunan kayan ta na gida ta bud'e ta fara ruwan ido can dae ta
fiddo wata fitted gown d'in lace yellow da touches d'in dark ash bayan ta rufe akwatin ta bud'e na
Undies ta d'auki wanda zatai amfani dasu, bakin gado ta nufa ta fara k'ok'arin sakawa bayan ta gama ta
koma gaban mirror tana k'ara gyara kwalliyar da tayi yar light, sosae rigar ta amshe ta dama ita duk
kayanta suna amsar jikinta Saboda irin d'inkin da ake yi mata dake fiddo dirin ta sosae, irin d'aurin
kallabin d'azun tayi ta k'ara zubo da gashin gaba can kuma sai ta raba gashin na 6arin hagu ta maida shi
baya na 6arin dama ta barshi a gaba, sosae hakan da tayi ya k'ara mata kyau sai kace wadda zata gasar
kyau, bayan ta feshe jikinta da turare ta gyara komai ta maida bathrobe d'in, a gefen gado ta zauna ta
fara tunanin ko akwae abunda yakamata tayi can ta mik'e ta nufi dressing mirror ta d'aukki robar Air
Freshener ta shiga feshe Bedroom d'in Bayan ta gama ta juya ta nufi kopar fita, parlor tazo nan ma ta
shiga feshe ko ina tana haka taji an turo kopar parlon ta kai idanun ta da sauri, Haisam ne ya shigo shima
da alama wanka yayi don ya canza kaya zuwa farin jeans sai yellow polo shirt daga jikin tsayayyar collar
d'in akwae ratsin fari haka a k'asan hannuwan ma sannan daga gaba 6angaren dama akwae farin
tambarin polo d'in, yadda yasa Yellow d'in riga abun kaman had'in baki da itama tasa kaya Yellow, Cikin
parlon ya shigo ya nufi inda ya saba zama ya zauna, slowly ta nufi inda yake hannunta ruk'e da robar
freshener d'in, daga d'an gefe ta tsaya tayi mashi sannu da zuwa ya jinjina mata kai tay tsaye suka bi
juna da ido tana d'an motsa baki, "Ya gida?" taji ya tambaya har saida taji mamakin tambayar ganin ya
kafe ta da ido fuska a sake yasa ta yin d'an murmushi tace mashi lafiya lau ya d'aga kai,

"Sit" ganin tana ta tsayuwa yasa shi ce mata haka, zama tay a bangaren inda take shiru ta biyo baya da
d'an murmushi take kallon shi tana yi tana maida idanun k'asa, "Kin yi kyau" kaman daga sama taji
Maganar ta kalle shi had'i da d'an waro ido mamaki kwance akan fuskar tata, ya fahimci hakan sai kawai
yay d'an guntun murmushin gefe idon shi a Kanta ya maida bayan shi ya jingina da jikin kujerar, Maganar
sai ta tuno mashi da Fanan ita ta koya mashi cewa hakan duk in tayi kwalliya bai yaba ba sai tay ta k'orafi
daga nan ya fahimci mata basu son suyi kwalliya a k'i yabawa, da k'yar ta furta mashi ta gode bai ce mata
komae ba sai ma ya maida idanun shi kan wayar shi dake a hannun shi ya fara latsa ta, "k..Kai ma kayi
kyau" da k'yar ta tattaro kalmomin muryar ta na d'an rawa ta furta mashi, shiru kaman ba zai ce komai
ba can taga yay mata kallon k'asan ido fuskar shi a sake ya furta thanks kafin ya maida idon kan Screen,
bin shi da ido tay ta ayyana sam baka ta6a gane mashi, tana cikin kallon shi ya d'ago suka had'a ido,
d'age mata gira yay ya tambayi da wani abu da sauri ta girgiza mashi kai sai kuma tace ga Abinci can kan
table ya jinjina kai, saida ya d'an k'ara lallatsa wayar kafin ya aje ta a gefe ya mik'e ganin haka yasa itama
ta mik'e ta bi bayan shi, Kitchen ta wuce anan ta aje Freshener d'in ta wanke hannuwan ta sannan ta
d'auki duk abunda zata buk'ata na cin Abinci ta fita, bayan ta iso dining d'in ta fara zuba mashi tana sa
sakwara guda d'aya ya d'aga mata hannu alamar ta isa kawai sai gani yay ta k'ara d'aukko guda ya d'ago
ya kalleta ta d'an tura baki ta fara k'unk'uni a shagwa6e tace "ya za'ai abu d'aya ya ishe ka" wani kalan
kallo ya ke bin ta da shi ya d'an d'age gira,

"Ba zai isheka ka k'oshi ba sai dae ko biyu" tana gama Maganar ta k'ara mashi d'ayar tana yi tana kallon
shi, yanayin fuskar shi ne ya sauya taga kaman ya d'aureta ta fara d'an kikkafta idanu a marairaice tace
"har yanzu fa in baka cin Abinci sosae Ulcer zai iya kama ka" still yay yana bin ta da ido without saying
anything, jikinta ne yay sanyi ta kai hannu da niyyar ta cire wadda ta k'aran taji yace "in ya kama ni I have
got married now" da sauri ta kalle shi taga ya d'an d'age mata gira kuma ya saki fuskar lokaci guda ta saki
murmushi jin bai manta da Maganar data ta6a yi mashi ba, bayan ta gama serving nashi itama ta zuba ta
fara ci tana yi tana satar kallon shi yana cin nashi a nutse, sunyi nisa da farawa ta dakata idon ta a kan shi
tana d'an murmushi slowly ya d'aga ido ya kalleta don yaji kallon shi take, "ya yi dad'i Abincin?" ta
tambaya, bai bata amsa ba ya maida idon shi kan Abincin, saida ya k'ara ci sannan taji yace miye na
tambaya tunda ba ita tayi ba, a hak'ik'an ce tace ai tare fa suka yi kuma ko ita kad'ai zata iya yin shi, d'an
guntun murmushi kawae yay yaci gaba da ci, sai ga shi ya take duka sakwarar cikin wasa ta tambayi ta
k'ara mashi ya d'an wurga mata harara, bayan ya sha kunun ayar ya yago tissue ya goge mouth d'in sa
sannan ya mik'e zai bar wurin idon Fatuu a kan shi, dakatawa yay ya kalleta suka had'a ido Slowly taji ya
furta "the empty plate is ur answer for d question u asked" daga haka ya juya yana tafiyar shi ya nufi
cikin parlon tabi bayan shi da kallo tana Murmushi shi komai nashi na daban ne, saida taci ta k'oshi don
ita kanta Abincin yayi mata dad'i sosae, bayan ta gama ta fara kwashe kayan da sukai amfani ta kai
Kitchen, saida ta gyara Dining table d'in sannan ta koma Kitchen ta wanke komae da suka 6ata ta maida
shi a wurin shi, bayan ta gama har zata fita idanunta suka sauka akan bokitan su cin cin a ranta ta raya
tunda aka yi su bata ci ba wata zuciyar ta ayyana shi k'ilan ma baya cin su, tunanin ta d'iba ta kai mashi
taga in yana ci tay ta d'aukko plate mai kyau ta bud'e ta d'ebo kowanne bada yawa ba harda alkaki,
bayan ta zuba ta nufi hanyar fita yana kishingid'e kan kujera idon shi akan Tv yana kallon American film
ta nufo shi tana tafiya a nutse sai kace mai yin yanga, tunda ta tunkaro cikin parlon ya maida idanun shi
kanta har ta k'araso ta d'aura plate d'in kan c-table ta k'ara matsar dashi kusa dashi ta d'ago tana
murmushi suka had'a ido tace mashi gashi nan ya ci, maida idon yay kan abunda take maganan kafin ya
d'ago ya kalleta tana tsaye still Murmushin take tana d'an wasa da yatsun hannunta da ta had'e, ji tay
yace a ina zai saka wannan d'in da sigar shagwa6a tace ai su ba Abinci bane,

"Who told u ba Abinci bane, yanzu kaci wannan kasha ruwa bazaka k'oshi ba?" Ya tambaya had'i da
d'age gira, d'an tura baki tay "Ya za'ai su kosar da Mutum, saidae in da yawa aka ci kuma ai kai kad'an ne
na kawo maka ko" tana Maganar ya kafe bakinta da kallo, sigh yay ya d'an shaking kan shi "bansan ina
zan sa shi ba as am stuffed, I couldn't eat another bite" bin juna sukai da kallo na d'an wani lokaci can ta
kai hannu a sanyaye ta d'auki plate tana shirin juyawa taji yace zai ci wani lokacin ta juyo suka had'a ido
ya d'an bud'a mata ido alamar taji abunda yace ta d'aga mashi kai daga haka ta wuce ya bita da kallo,
bayan ta maida su ta fito ta wuce Bedroom, bada jimawa ba ta fito hannunta ruk'e da laptop d'inta da
babban hardcover ta nufo cikin parlon ya maido idon shi kanta, a gefen shi ta tsaya a d'an marairaice
tace "please, could you help me with this Assignment, ta email malamin yace mu tura mashi gashi harda
drawing nayi k'ok'arin in d'aukko in saka na kasa" shiru yay just staring at her har saida tasha jinin jikinta
ta d'an juyar da fuskar ta, tana haka taji cool voice d'in shi yace ta kawo ya gani ta matsa, akan c-table ta
d'aura ta shiga nuna mashi yadda Assignment d'in yake bayan ta gama ta d'ago ya kai hannu ya fara latsa
Computer din, can bayan d'an wani lokaci ya d'ago suka had'a ido yace mata sai ya d'aukko abu a G.r.a
za'a iya tura mashi zuwa dare zai nuna mata, murmushi ta shiga yi tayi mashi godiya bai ce mata komai
ba ya koma ya jingina bayan shi jikin kujerar, hannu ta kai zata d'auki laptop d'in slowly taji yace an hana
ta zama a parlor ne, kallon shi ta d'an yi still da murmushi ta fasa d'aukar laptop da littafin ta koma
d'ayan side d'in kujeran ta zauna, remote ya d'auka ya canza daga channel d'in da yake kallo zuwa Arewa
24 lokacin suna cikin yin maimaicin shirin dad'in kowa da yake k'arfe ukku yayi, d'an juyawa tay ta kalle
shi ta d'an yamutsa baki nan take ya gane mi hakan ke nufi ya k'ara canza channel zuwa tauraruwa ganin
suna yin wak'ok'i yasa ta d'an yi murmushi, voice d'in shi taji yana tambayar yayi mata ta juya ta d'aga
mashi kai ya aje remote d'in dama ta dalilin ta ya san channels d'in hausa, tana kallon wakokin tana d'an
bi wani lokacin har d'an juya kai take akwae wata da ya lura tana mata dad'i don sosae take bin wak'ar
tana juya kai, still yay yana ta kallon ta kai kace ita ta raira wak'ar saidae kuma kunnan shi na akan
wak'ar yana sauraro can kaman taji kallon ta yake ta juya suka had'a ido yar dariya tayi mashi shi kuma
ya d'an yi mata guntun murmushi, ana yin wakokin kaman guda biyar suka datse suka sako tallar
magunguna, juyowa tay tace mashi ya maida channel d'in da yake kallo sun gama fuskar shi a sake
kaman zai murmushi ya kalle ta, tambayar ta yay ba wani da ake irin shi, ta gane wakokin yake nufi tace
mashi ko an canza ba lalle ana yi ba dama nan an fi sa su, shiru yay can ya kai hannu ya d'auki remote
d'in ya canza channel d'in da yake kallo farko suka cigaba da kallon American film d'in tare, gaba d'aya
Fatuu ta takura don sai yin abubuwan sa kunya suke, suna cikin kallon aka nuno jarumin Film d'in da
budurwar shi suna romancing juna ji Fatuu tay kaman ta nutse a wurin don abun bana Arziki bane, can
abun ya kai ga an sa6ule rigar budurwar har boobs d'inta sun bayyana Fatuu na ganin hakan ta mik'e
zumbur ta nufi hanyar corridor without even looking at him ya bi bayanta da kallo shi sai ma ta so bashi
dariya yadda tayi, tana shiga Bedroom d'in ta nufi gado ta zauna a baki ta d'an waro ido tay shiru kaman
mai tunanin wani abu, a hankali ta kwanta ta takure a guri guda tana cigaba da tunanin da take yi, bata
dad'e da kwanciyar ba aka kira sallar la'asar, har tayo Alwala ta zo ta kabbara sallar bai shigo ba, bayan
ta gama zaune tay kan abun sallar ta jingina da gado tana haka taji wayar ta na ringing ta mik'e ta nufi
bedside drawer inda wayar take ajiye, d'an jimm tay ganin shine ke kiran kafin ta d'auka a hankali tayi
sallama amsa mata yay yace mata ya je ya dawo ta yi mashi adawo lpy, tambayar ta yay akwae abunda
take so tace mashi a'a daga haka yay cutting kiran, bin wayar tay da kallo bayan ta cire ta daga kunnan ta
a ranta ta shiga raya shi d'in ba dai kula ba duk zai fita sai ya tambayi ko tana son wani abu, d'an
murmushi tay tana jin k'aunar shi na k'ara ninkuwa a cikin ranta, tunanin tafiya part d'in Hajiya tay ta
taya Saude girkin dare tunda ko ta zauna ba abunda zata yi ta mik'e, bayan ta d'aukko gyale da takalma
ta k'ara gyara fuskar ta a gaban mirror sannan ta tafi, saida ta tsaya Kitchen ta d'aukko wasu daga cikin
kayan da aka kawo masu Abinci don ta maida sannan ta tafi, tare sukai aikin Abincin daren kaman da
rana a nan tayi sallar Magrib da isha'i sannan ta baro part d'in tare da Abincin su ta dawo part d'in su har
lokacin Haisam d'in bai dawo ba, bayan ta aje kayan Abincin kan table ta wuce Bedroom, har ta zauna
bakin gado zata fara latsa wayar ta Zuciyar ta ta ayyana mata yakamata tayi wanka ta mik'e bayan ta aje
wayar ta nufi gaban dressing mirror ta cire jewellery d'in jikinta ta maida komai ma'ajiyar shi sannan ta
wuce laundry room, after some minutes ta fito sanye da bathrobe kanta ba kallabi sai short towel tana
goge fuskar ta da gefen gashin ta, gaban dressing mirror ta tsaya ta shafa mai da su humra bayan ta
gama ta wuce wurin kayanta a ranta ta ayyana yakamata ta jera kayan a cikin closet ta yanke gobe tunda
ba Makaranta zata je ba tayi hakan, ruwan idon kayan da zata sa ta shiga yi daga k'arshe ta yanke ta saka
sleeping dress kawai tunda dare ne kwanciya zatayi ta bud'e jakar da suke ta fiddo wasu riga da wando
silk cikin wanda aka kai mata rigar gajeran hannu gare ta ta d'an saukko zata kai cinyoyin ta, gefen gado
ta koma ta fara saka su ba tare da ta d'aukko undies ba tunda dare ne, gaban mirror ta koma ta k'ara
gyara parking d'in gashinta, bayan ta gama ta maida su bathrobe d'in ta d'aukko phone d'inta ta haye
gado ta fara latsa ta, bata dad'e da hawa ba taji an turo kopar da sauri ta kai idonta suka had'a ido dashi
ya shigo da yar sallama tana d'an murmushi ta amsa mashi, a gaban gadon ya tsaya tayi mashi sannu da
zuwa ya d'aga mata kai, mik'a mata ledar daya shigo da ita yay ta matso ta amsa tana kallon shi kafin ta
maida kallon kan ledar shi kuma ya nufi gaban mirror ya fara cire Wrist watch d'in shi, bud'e ledar tay ta
lek'a sai kuma ta kai hannu ta fara fiddo abubuwan dake ciki nan taga Pop corn ne da tuwan Madara
harda gullisuwa sai Chocolates manya manya with surprise written on her face ta d'ago tana kallon shi
don bata tsammaci ganin su ba tunda bata ce mashi tana so ba, hanyar laudary room ya nufa ba tare da
ya kalle ta ba da d'an d'aga murya tace "Thank u so much, Allah ya k'ara bud'i na Alkhairi" d'an juyowa
yay ya kalleta fuskar shi a sake ba tare da ya ce komae ba ya juya yaci gaba da tafiya har ya shige, tana ta
sakin murmushi da alama taji dad'in kawo mata su da yay ta bud'e ledar tuwon madara ta fara sha nan
take wani dad'i ya ratsa ta harda lumshe ido lokaci guda zuciyar ta ta tariyo mata can baya irin su ne
kyauta ta farko da ya fara mata da hannun shi ta dingi zuba mashi santi harda bashi labarin irin Pop corn
d'in da ake kawo masu a Makaranta duk tsakuwowi da gishiri don an raina masu wayau, tunowa da
lokacin yasa tay ta dariya can tay tunanin yakamata ta bashi wuri tasan wanka yake in ya fito ya shirya ta
saukko daga kan gadon ruk'e da ledar ta nufi hanyar fita, tana zaune a parlor tana cigaba da cin
abubuwan ta tana yi tana kallon sabon shirin dad'in kowa ya fito shima ya shirya cikin sleeping dress riga
da wando tun kafin ya k'arasa shigowa k'amshin shi ya karad'e parlon, tana ganin shi ta mik'e da hannu
tay mashi alama da Dining area ya nufi can ta bi bayan shi, ba wani Abinci sosae yaci ba ya dawo cikin
parlon, bayan ta gama ta gyare wurin ta had'o mashi Fruit salad, a kan c-table ta d'aura mashi tace gashi
nan ya sha ya furta mata thanks tay d'an murmushi ta koma inda ta taso ta zauna taci gaba da kallon ta,
bayan an gama ta juyo suka had'a ido lokacin har ya gama sha tay mashi d'an murmushi taji yace zasu
iya yin Assignment d'in yanzu tace eh, bud'e Computer d'in yay dama tana nan ba'a d'auke ba ya fara
operating nata tana ta kallon shi can taga yay mata alamar tazo da hannun shi ba tare daya d'ago ba ta
mik'e ta nufe shi, a gefen shi ta ja ta tsaya ya k'ara mata alamar ta zauna a kusa da shi still bai kalleta ba,
a d'arare kaman mai jin tsoro ta raku6a gefen nashi ta zauna ya shiga nuna mata yadda zatai, tun dai
bata saki jiki ba har ta washe suka cigaba da yi har ta kai ya kama hannunta yana koya mata yadda zata
d'aukko zanen, tuni jikin su ya had'e da na juna gaba d'aya sun cika juna da fitinannan k'amshi, ba'a d'au
wani dogon lokaci ba suka gama har an tura ma malamin tana ta murmushin jin dad'i ta hau yi mashi
godiya, d'an murmushi kawae yake ba tare daya ce komai ba ta mik'e ta kai hannu ta d'auki book d'in
tana shirin juyawa ta tafi kwatsam tay tuntu6e da kafar shi ta tafi gaba d'aya zata kifa aikuwa cikin zafin
nama ya jawo ta tayo baya ta fad'o jikin shi gaba d'aya, tsit kake ji Wutar Fatuu ta d'auke don ba
k'aramar razana tayi ba gaba d'aya ta runtse idanunta gam jikinta sai d'an rawa yake tana fitar da
numfashi da sauri da sauri, still yay yana bin fuskar ta da kallo ya kasa cewa wani abu idanunta sai rawa
suke, bayan wani lokaci natsuwar ta ta daidai ta a hankali ta fara bud'e idanun ta, bayan ta ware su gaba
d'aya suka sauka akan face d'in shi dake gab da ta ta, sam kowa ya kasa yin kwakkwaran motsi sunyi tsit
gazing in to each other's eye and inhaling each other's sweet scent, Fatuu ce tay k'arfin halin ce mashi ta
gode da taimaka da yay ta fara k'ok'arin d'agowa sai dae ta kasa don ya ruk'e ta tightly, slowly ya d'ago
da fuskar ta ta yadda saura kad'an su had'e Fatuu na ganin haka da sauri ta runtse idonta breathing d'in
su ya fara had'uwa zuciyarta ta fara beating da sauri da sauri, numfashin ta ne ya nemi tsayawa jin ya
had'e bakunan su.........

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2065*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

........... Kissing d'in ta ya shiga yi deeply a nutse hannun shi duka biyun talla6e da kanta da ba kallabi
gashinta dake fake yayi k'asa, Fatuu kam tuni ta k'ame ta kasa ko d'aga hannunta don abun yazo mata
unexpected sai numfashin ta da ke fita rapidly kirjinta na hawa da sauka da sauri da sauri, sun d'auki
lokaci a haka kafin slowly ya kwantar da ita akan kujeran tayi Flat still idanunta na a rufe, had'e fuskokin
su yayi ta yadda tsinin hancin shi ya had'e da nata inhaling each other's breathe wanda gaba d'aya yake
fita da k'arfi, sun d'an d'auki lokaci a haka kafin slowly ya janye fuskar ya fara Moving dinta around her
neck yana inhaling scent d'in jikinta, a wannan lokacin a wata irin duniya ta daban Fatuu take jinta the
world around her faded away, sai faman sakin nishi take ta kai har saida ta d'an bud'e bakinta don ji take
numfashin ta na neman katsewa, wani irin salo yake mata mai rikita kwakwalwa a nutse cike da
gwanancewa, suna cikin haka ya kai hannu ta k'asa a hankali ya fara tattare rigar ta, Fatuu na jin haka
bugun zuciyar ta ya k'aru, dakatawa yay da shak'ar K'amshin wuyan ta da yake ya fara jawo fuskar k'asa
har ta sauka kan flat tummy d'in ta daya bayyana sakamakon dama iya rigar baccin ce ta rufe shi, har
saida Fatuu ta d'an gantsare lokacin da taji ya kai nan jikinta ya fara d'an rawa ta fara mommotsa
k'afafun ta, bin cikin nata ya fara yi yana cigaba da shak'ar Scent d'in da jikinta ke saki giving her soft
kisses at the same time, she's savoring every touch and every kiss ji take tamkar zata suk'e, cigaba da
moving face d'in shi yay yana yi mata abunda yake mata, a haka har ya rage da ya k'ara janye rigar boobs
d'in ta zasu bayyana a lokacin numfashin Fatuu kusan d'aukewa yay, yana k'ok'arin k'ara janye rigar
hannun shi ya gogi boob d'in ta, dakatawa yay da abunda yake matan tamkar an latsa mashi pause yay
d'an jimm can kuma sai ya d'ago daga jikin nata, dakatawar da yay yasa da k'yar ta d'an bud'e idanun ta
da sukai mata wani irin nauyi ta hango shi zaune daga gefe kan shi a k'asa yasa hannu guda ya dafe
gefen fuskar tashi, k'arasa bud'e idanun ta da tuni sun canza daga ainihin kalar su da yanayin su tayi ta bi
shi da kallo har lokacin numfashin ta da d'an k'arfi yake fita, sun d'an d'auki lokaci a haka can wata
zuciyar ta raya mata zaman me take ta tashi ta tafi d'aki, da k'yar ta yunk'ura ta tashi zaune ta saukko da
k'afafawun ta k'asa kafin ta mik'e, ko ta kan littafin ta da laptop d'in bata bi ba ta nufi hanyar corridor
tana tafiya a harhard'e gaba d'aya jikinta jin shi take kaman ba nata ba sai kace na wadda ta tashi daga
ciwo sam ba k'arfi a jikin nata kwata kwata, Slowly ya d'aga idon shi da suka sauya daga yanayin su yana
kallon ta har ta shige d'aki sannan ya maida kan nashi k'asa yasa dukkan hannuwan shi ya talla6e shi,
tana shiga ta nufi bakin gado ta zauna dabas ta kankame jikinta da har lokacin yana d'an yin rawa, gaba
d'aya ji take kamar har lokacin yana cigaba da yi mata abubuwan da suka wakana tsakanin su, gaba d'aya
ya tado mata da urge d'in ta dama kuma a tsume take a yadda take ji ma sai tayi wanka, ta d'an d'auki
lokaci a haka can ta kai kwance k'afafunta na a k'asa tay tsuru tana ta imagination hakan ya k'ara kashe
mata jiki sosae, zuciyar ta ce ta fara raya mata anya Ya Haisam na son ta kuwa, inda yana son ta bata
tunanin yadda suka kai wani mataki haka zai k'yale ta, wata zuciyar ta k'ara raya mata da bai son ta zai yi
mata abubuwan da yayi mata ne sai kuma ta sake raya ai k'ilan bada niyya bane kaman yadda ya faru a
G.r.a dalili ne ya sa komai ya faru to k'ilan yanzu ma haka ne tunda ita ta fad'a mashi, idanunta ne suka
ciko da k'walla ita kad'ai tasan abunda take ji a jikinta can ta runtse idanun ta suka fara gangaro mata, ta
d'an d'auki lokaci a haka saida taji ta d'an samu sassaucin abunda take ji a jikinta sannan ta yunk'ura ta
tashi zaune sai kuma ta mik'e tana tafiya a hankali ta nufi wurin kayanta ta d'aukko hula tasa, gaban
dressing mirror ta tsaya tana kallon kanta kwalla na ci gaba da zubo mata daga baya ta sa hannu ta goge
ta juya ta nufi hanyar laundry, d'aure da towel ta fito ta koma wurin kayanta ta curo doguwar riga ta
zumbula daga haka ta nufo gado ta kwanta ta ja duvet ta lullube har kanta. Tun bayan da ta shige yake
zaune a yadda yake tsawon lokaci sai daga baya ya mik'e ya nufi hanyar fita daga cikin parlon walking
slowly, not too long da fitar shi ya dawo hannun shi ruk'e da wani abu har ya zauna sai kuma ya mik'e
bayan ya aje abunda ya d'aukko a kan kujerar ya nufi hanyar Dining, bottle water ya d'aukko daga cikin
freezer ya dawo, zaunawa yayi ya shiga bud'e ruwan bayan ya bud'e ya aje shi akan c-table ya kai hannu
gefen shi ya d'aukko abunda ya aje wanda d'an kwali ne kamar na magani ya bud'e, ciro abunda ke ciki
yay ya 6allo guda d'aya ya saka cikin bakin shi ya kai hannu ya d'aukko robar ruwan, bayan ya shanye ya
rufe robar ya aje ya maida abun cikin kwalin wanda kaman magani ne, bayan ya rufe kwalin ya sake
mikewa ya nufi hanyar fita, bada jimawa ba ya dawo ya nufi wurin Switch ya kashe hasken Parlon ya bar
na wasu k'ananun fitilu kaman yadda yake yi ya koma wurin Kujerar, Zaune yay idon shi akan Corridor
kaman mai tunanin wani abu, ya d'an d'auki lokaci a haka kafin ya kwanta yau ko pillow d'in babu saidae
ya tada kan shi da hannun kujera yasa tafin hannun shi d'aya ya rufe fuskar shi, ta dad'e bacci bai d'auke
ta ba sai tunane tunane take tana juye juye har dare ya yi sosae tana a haka, har Addu'a tay a cikin ranta
kan Allah yasa tayi baccin, sai bayan wani lokaci sannan baccin ya d'auketa cike da mafarkan abunda ya
faru.
Sai da gari ya fara wayewa sannan ta farka lokacin har anyi sallar Asuba tuni, bayan tayo Alwala tazo ta
kabbara salla, zaune tay da ta gama cikin ranta tana ayyana Ya Haisam bai shigo bane yin Alwala da bai
tashe ta ba, haka tay ta zancen zuci ita kad'ai sai bayan wani lokaci sannan ta mik'e ta cire Hijab d'in data
yi sallar ta ninke ta d'auke prayer mat duk ta maida su wurin da suke, komawa tay gado ta kwanta ta
kudundune taci gaba da yin sak'e sak'e a ranta, tsawon lokaci tana a hakan bacci yak'i d'aukar ta har taji
ta gaji da kwanciyar ta mik'e don ta gyara d'akin, bayan ta gama gyaran d'akin tasa turaren wuta toilet ta
wuce tayo wanka, bata canza kaya ba doguwar rigar jikinta ta bari haka jikinta ma iya mai kawai ta shafa
sai turare data fesa ta koma bakin gado ta zauna, hakanan rashin shigowar Haisam d'in ta tsaya mata ta
raya k'ilan don abunda ya faru ne k'ilan kuma ya shigo tana bacci, gaba d'aya ta rasa mike mata dad'i har
wayarta ta daukka don tayi ko chatting ne amman k'arshe sai dai ta aje ta ta haye gado tay shiru, tana
kwancen taji anyi knocking kopar d'akin ta tashi zaune da alamun mamaki, jin an k'ara kwankwasawa
yasa ta mik'e ta nufi kopar, tana bud'ewa taga Saude ce tayi mata murmushi itama ta d'an yi mata ta
gaishe da ita, bayan ta amsa tace mata dama Breakfast ne ta kawo to bata iske kowa a parlon ba kar ta
aje ta tafi kuma ba'a san ta kawo ba yasa tace bari tayi mata magana, Fatuu ta d'an yi mamakin jin tace
ba kowa a parlon kenan ma baya nan godiya tay mata har Sauden zata juya ta tafi sai kuma ta dakata
idon ta akan Fatun tace "amman ko baki lafiya ne?" d'an fad'uwa gaban ta yay tayi d'an murmushi tace
mata a'a lafiyar ta lau, Sauden tace "amman Fateema naga idanunki sun canza kaman ma kuka kikai ko?"
da sauri ta girgiza mata kai "a'a Aunty Saude" tana kai Maganar ta sunkuyar da kanta k'asa don sai taji
idanunta na tara k'walla, hakan da tayi yasa Saude zargin da wani abu ta kai hannu ta dafa Shoulder
d'inta tace "in wani abu ke damun ki Fateema ki fad'a man in da taimakon da zan maki, barin damuwa
ba abunda yake ma mutum sai haddasa mashi ciwo" da k'yar ta maida k'wallan ta kalle ta da d'an
murmushin yak'e ta girgiza mata kai tace "ba abunda ke damuna Aunty Saude kawai na tashi da ciwon
kai ne" kai Sauden ta jinjina ta yarda da abunda tace ta tambayi to tasha magani tace mata eh tun jiya da
daddare,

"to yanzu ai yakamata ki k'ara sha tunda ga Abinci nan na kawo ki zo ki ci sai ki sha maganin in kuma kinji
bai daina ba gara kiyi magana akai ki Asibiti, kinsan yanzu haka malaria ke sa mutane suyi ta ciwon kai
mai tsanani" kai ta d'aga mata tace ta zo tayi breakfast d'in, ba musu ta fito suka shigo parlon tare
Sauden tace suje tay serving nata da sauri tana murmushi tace mata lafiya lau zata yi ai ba wani ciwo
yake mata sosae ba tay mata godiya ita kuma tay mata Allah ya sawak'e ta tafi, zaune tay a dining d'in ta
kasa yin Breakfast sai tunanin inda Haisam d'in ya tafi take wata zuciyar ta raya mata k'ilan ma ba gidan
ya kwana ba k'arshe ta yanke watak'il yana G.r.a, ta d'auki lokaci a haka kafin ta fara yin Breakfast din,
bata wani ci da yawa ba ta mik'e ta koma d'aki, ji tay duk zaman bai mata dad'i ta yanke tafiya part d'in
Hajiya bayan ta d'aukko gyale ta yafa ta fita, tana kaiwa bakin k'opar parlon zata bud'e taga an turo ta
kalli mai shigowar da sauri, Haisam ne ya shigo jikin shi sanye da k'ananun kaya da gani wanka yayi sai
sakin uban k'amshi yake, suna had'a ido ta sadda kanta k'asa da sauri, k'arasa shigowa yay idon shi a
kanta ya tsaya daga gefe, kirjinta ne ya fara bugu da sauri sauri da k'yar ta bud'e baki ta gaishe dashi ba
tare data kalle shi ba ya amsa, shiru ba wanda ya k'ara tanka wa balle ya motsa still idon ta na k'asa shi
kuma ya kafeta da nashi idon wata irin kunyar shi taji ta rufe ta, jin bai k'ara cewa komae ba kuma yayi
tsaye yasa ta d'an d'ago ta kalle shi suka k'ara had'a ido da sauri ta juyar da face d'in ta gefe ta fara
motsa baki murya na d'an rawa ta fad'i mashi zata part d'in Hajiya ne, shiru bai ce komae ba hakan yasa
ta d'an juyo still kallon ta yake sai kace mai nazarin wani abu, tambayar ta yay bata lafiya ne ta d'aga ido
ta kalle shi sai kuma ta girgiza mashi kai had'i da maida idon k'asa, ji tay ya k'ara cewa in bata lafiya ne su
je Hospital ba tare da ta kalle shi ba a sanyaye tace mashi lafiyar ta lau k'asa k'asa ya furta Ok ya fara
k'ok'arin wucewa ciki, har zata fita sai kuma ta tuna da breakfast d'in da aka kawo ta juya ta koma ciki
daga gefe ta tsaya ta d'an kalle shi yana zaune kan kujera tace mashi ga breakfast can an kawo ya jinjina
kai yana kallonta, ganin tayi tsaye yace taje in da zata tace zatay serving nashi ne yace no problem zai yi
da kan shi ta je, kallon shi ta sake yi idon su ya k'ara had'uwa da sauri ta juya ta nufi kopa ta fita, Tana
tafe tana zancen zuci gaba d'aya ta kasa gane ma wannan auren nasu, tasan ana aure ne in ana son juna
to su ita ce ke sonshi shi ba son ta yake ba kawae ya aure ta ne don ya taimaka mata ba don suyi
rayuwar Aure ba abun kuma turns out this way, yanzu haka zasu cigaba da yin tasu rayuwar auren? Ta
jefa ma kan ta tambaya, ta so ace shima yana jin son ta ya kuma nuna mata tasan da ba k'aramar
rayuwar Aure mai dad'i zasu yi ba, idanun ta ne suka ciko da k'walla daga baya suka fara zubowa, saida
ta iso bakin part d'in sannan tasa gefen gyalenta ta goge Fuskar sosae sannan ta shiga, ganin ba kowa a
parlon yasa ta wuce Bedroom d'in Hajiya nan ta iske ta tana bacci ta fito ta nufi Kitchen ba kowa a ciki ta
juyo ta nufi d'akin Saude, ciki ta isketa tana ganinta ta washe mata baki tana fad'in har ta samu sauk'i da
ta fito, a gefen Katifarta ta zauna tana murmushi tace mata ai fa dama ba sosae yake mata ciwon ba
yanzu ma ta samu sauk'i ta zo ta taya ta aikin Abinci Sauden tace a'a yau dae ta huta ko ta k'ara samun
sauk'i Sosae tay murmushi kawae, kwanciya tay akan Katifar Sauden don tak'i yarda ta taya ta aikin bada
jimawa ba kuma bacci yay awon gaba da ita, saida akai sallar Azahar Saude tazo ta tashe ta don tayi
salla, bayan ta gama sallar ta nufi Bedroom d'in Hajiya ta isketa zaune akan prayer mat tun bayan da ta
gama salla bata tashi ba ta nufi gefen ta ta zauna tana gaishe da ita da murmushi ta amsa tana tambayar
ina Angonta ta sanar da ita ai tun d'azun tazo ta iske tana bacci shine ta wuce d'akin Aunty Saude nan
bacci ya kwashe ta, tana zaune a d'akin Hajiyar sai ga Haisam ya shigo tunda suka had'a ido ta maida
kanta k'asa ya zauna a bakin gado bayan ya gaida Hajiyar suka shiga d'an yin fira jefi jefi daga baya Saude
ta shigo ta sanar da ita an shirya table tace ai sai su tashi suje suci gaba d'aya tunda suna nan, Fatuu ce
tay Serving d'in su bayan itama ta zuba nata ta zauna saidai kasa sakin jiki tay taci sosae sai faman
Jujjuya cokali take har Hajiya ta gane ta tambaye ta ko bata son Abincin ne da sauri tace mata a'a tace to
taga tak'i sakin jiki taci sosae in bata son shi tayi Magana sai a samar mata wani abun tace a'a tana so
dole ta daure ta rink'a turawa, bayan sun gama Haisam ya tafi dama shi ya fara tashi su kuma suka koma
Parlor suna kallo, sai bayan la'asar sannan Fatuu ta koma part d'in su tana zuwa ta wuce toilet don tayi
wanka, bayan ta fito ta shirya cikin doguwar rigar Atamfa A shape ta d'an shafa powder da lip glow ta
fesa turarurruka, wayarta ta d'auka ta haye gado ta fara yin Azkar bayan ta gama tay tunanin kiran
Haulat don tun ranar tarewar ta rabon ta da ita, ta dai san da ita aka kawo ta amman bata san lokacin
data tafi ba, sai bayan isha Haisam ya dawo yau ma harda ledar su ice cream ya kawo mata tayi mashi
godiya daga baya suka wuce dining area don cin Abinci, bayan Fatuu ta gama duk abunda zata yi na
shirin kwanciya ta d'aukko Al'qur'ani ta zauna a saman gado tana karantawa lokacin Haisam ya shigo
shima tuni yayi shirin kwanciya, dakatawa tay da karatun ta kalle shi ba laifi ta rage jin kunyar tashi
Fuskar shi a sake ya nufo gadon ya d'auki pillow yace mata "Gud night" kai ta d'aga mashi ya juya ta
bishi da ido har ya fita sannan taci gaba da karatun, Washe gari ana kiran sallar Asuba ta farka, tana
gama yin sallar ta wuce toilet tayo wanka, bayan ta fito ta fara shirin zuwa Makaranta, Yana kwance kan
kujera idanun shi a rufe ta fito sanye da Uniform ta nufo cikin parlon, daga gefen shi ta tsaya tana kallon
fuskar shi ta fara tunanin ko bacci yake yi, slowly taga ya fara bud'e idon suka sauka a kanta, gaishe da
shi tayi ya jinjina mata kai cikin yar inda inda tace mashi dama Makaranta take son zuwa, kafeta yay da
ido ba tare da yace komai ba hakan yasa ta maida nata k'asa, tana haka taji yace tayi breakfast ne ta
girgiza mashi kai alamar a'a, shiru yay ta d'ago ta kalle shi yace to zata tafi School d'in ne ba tare da tayi
breakfast d'in ba tace mashi eh,

"Dama kina yin haka?" taji ya tambaya, ta gane yana nufin dama tana zuwa Makarantar ba tare da tayi
breakfast d'in ba, a hankali tace "a'a, amman in na tsaya jira zan iya makara, nasan bata san da zanje
Makarantar bane yasa bata yi da wuri ba" tana Maganar ya kafeta da ido, sigh yay taji yace sai tayi
breakfast zata je ta kalle shi yanayin fuskar ta ya sauya, tunawa tay da ice cream d'in daya kawo mata ko
roba d'aya bata sha ba tace mashi bari tasha ice cream da cin cin to, wani kallo yay mata ya d'an
yamutsa fuska yace ya zata sha abu mai sanyi da safe ta yamutsa fuska a shagwa6e tace to ai lafiya lau in
ta tsaya jira sai an kawo zata makara ne fa, shiru yay kaman bazai ce komai ba can yay mata alamar ta
zauna da hannu, bayan ta zauna ya yunk'ura ya mik'e tana ta kallon shi ya nufi kopa ya fita, bayan fitar
shi tana zaunen idanunta suka sauka akan pillow tay tunanin ta d'auke tunda tasan shi zai kai ta School
d'in kuma daga can ba lalle ya dawo nan ba, mik'ewa tay ta nufi kujerar ta kai hannu ta d'aukko filon,
wani abu ta ji ya fad'o akan k'afarta ta kai idanunta k'asa don taga minene, duk'awa tay ta kai hannu ta
d'aukko abun, k'aramin kwali ne wanda ya d'aukko jiya ta bishi da kallo, daga yanayin sunan dake jiki da
hotunan jiki ya nuna magani ne saidae ta kasa gane maganin ko na miye daga sunan shi amman daga
yanayin hoton jiki ya nuna kaman na ciwon ciki ne don wani mutum ne a jiki ya daddafe cikin shi ya d'an
duk'e sai kuma daga gaba gashi nan bayan yasha maganin a kwance yanata bacci harda d'an murmushi
akan fuskar shi, jujjuya kwalin ta shiga yi a ranta tana raya Ya Haisam bai lafiya ne amman bata ga alama
ba wane irin ciwon ciki yake yi, ranta ne ya bata ta bud'e k'ilan akwae leaflet a ciki sai ta duba k'ilan ta
gane na ko wane irin ciwon ciki ne, har zata bud'en sai kuma wata zuciyar tace mata bafa kyau yin
bincike hakan yasa ta fasa sai ma ta maida pillow d'in kawae ta tura maganin a karkashi don tana
tunanin anan yake ya fad'o, bata dad'e sosae ba da komawa ta zauna sai gashi ya shigo hannun shi ruk'e
da d'an babban tray ta bi shi da ido har yazo ya aje akan c-table, matsar mata yay da table d'in yace
gashi nan ta kalli tray d'in sai kuma ta kalle shi ya koma ya zauna, hannu ta kai ta bud'e plate d'in da aka
rufe wani plate nan take k'amshi ya bugi hancin ta taga indomie ce tasha vegetables harda soyayyun
cinyoyin kaza guda biyu tayi gwanin kyau a ido daga gefe kuma Cup d'in tea ne an had'a shima an rufo
shi, da alamun mamaki ta d'aga ido ta kalle shi ya jingina bayan shi yana kallon ta mamaki ta shiga yi a
cikin ranta na badai shi ya dafa ta ba, hannu ta kai ta d'auki fork ta fara ci sosae tay mata dad'i, kasa
jurewa tay tana cikin ci ta dakata ta kalle shi yana ta latsa wayar shi,

"Amman kai ka dafa ta ne?" da k'yar ta tattaro kalmomin ta tambaye shi, shiru kaman bai ji tambayar
da tayi ba har ta fidda ran zai amsa taga ya d'ago ido ya kalle ta taji yace ta tambayi Abincin mana, d'an
tura mashi baki tay ta maida idon ta kan Abincin, tana cikin ci taji yace shi ya dafa akwai matsala ne, har
saida ta maimaita Maganar tsabar mamaki ba wai don ya dafa matan ba sai don bata ta6a tunanin ya iya
girki ba koda dafa tea ne, saida ta cinye ta duka farko ta rage yace mata wa zata bar mawa tana d'an
murmushi tace shi d'an murmushi yay kawai ya gane wasa take mashi tunowa da can baya, naman ne ta
rage ta kwashe kayan ta kai Kitchen, saida ta wanke komae ta d'ebi su dublan don ta kai ma su Fauzy
harda ice cream ta d'aukar mata sannan ta koma Bedroom ta d'aukko jakar ta da takalma dama ta saka
safa tun da tasa uniform.

Bayan sun isa ya fiddo kud'i ya bata ba tay mashi musu ba don tasan ba maidawa zai ba tayi mashi
godiya ta bud'e Motar ta fita, tun kan ta shiga aji wasu da suka ganta sukai shelar zuwanta, tana zuwa
bakin Class d'in su Zainab suka fito da gudu suna mata oyoyo Amaryar su suka rungume ta tana ta masu
dariya, bayan sun saketa ta tambaye su Fauzy suka ce bata kai ga zuwa ba suka nufi cikin ajin suna ta
tsokanar ta wai k'amshin Amarci take gashi tayi Fresh ita dai sai murmushi take kawai, bata dad'e da
zuwa ba Fauzy tazo tun daga bakin Class ta hango ta ta shigo da gudu tana fad'in k'awarta Amarya tana
zuwa seat d'in ta rungume ta Fatun nata dariya, zama tay sai kallon Fatun take tana sakin murmushi tace
"ai banyi tunanin zaki zo yau d'in ba, nayi zaton zaki k'ara kwana biyu kaman yadda na baki shawara"
d'an girgiza mata kai tay alamar a'a, "wai badai duk Amarcin bane yasa baki magana" Fauzy ta fad'a baki
bud'e Fatun ta sa dariya tace mata a'a,

"Amarci dad'i, Wai kinga yadda kikai Fresh duka kwana ukku, gaskiya nima na fara jin son aure wllh" ta
k'arasa tana dariya itama Fatuu dariyar take suna haka malamin su ya shigo, bayan anyi break sun fito ne
Fauzy ke tambayar Fatuu wai ko wani abun na damunta ta lura da suna class kaman tana yawan yin
tunani a sanyaye tace mata ba komai saidae Fauzyn bata yarda ba tace in wani abu ke damunta ta fad'i
mata in na shawara ne sai ta bata barin damuwa ba zai mata magani ba har da ce mata ko bata yarda da
ita bane tace mata a'a, ganin yadda duk ta damu da son jin ko wani abu na damunta yasa a sanyaye tace
"ba wani abu ke damuna ba Allah Fauzy, kawai dai....na rasa gane kan Ya Haisam, gani nike bai so na
kaman yadda ake hasashe kawai ya yarda yaci gaba da zama dani ne ba wai don yana sona ba" idanun ta
ne suka ciko da k'walla da sauri ta fara k'ok'arin maida su, ajiyar zuciya Fauzy ta sauke duk da bata san
dalilin da ya sa tace haka ba ranta ya bata wani abu, tambayar ta tay dalilin daya sa tace haka tay d'an
murmushi tace mata ba komai kawae dai yak'i sake mata ne, hak'uri Fauzyn ta bata tace ita tana ganin a
k'ara bashi lokaci k'ilan da dalilin hakan amman tana kokonton ace bai sonta kuma ya za6i cigaba da
zama da ita to miye ribar hakan, ai indae dama ya aure ta tun farko don ya taimaka mata ne to ba dalilin
da zai cigaba da zama da ita Fatun tace bata ganin ko don abunda ya faru yaga bai kyauta mata ba in ya
rabu da ita yasa, Fauzy ta girgiza kai tace gaskiya bata tunanin hakan koda da hakan to akwae wani
dalilin wanda kuma tana ganin so ne Fatun tay shiru kawai, Fauzy na son ta yi mata Maganar magunguna
amman dalilin wannan Maganar yasa ta fasa, ana tashi Haisam yazo d'aukar ta saida Fauzy ta rakata har
bakin Mota ta gaisa da shi sannan ta wuce Hostel su kuma suka tafi........
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2066*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.........Tun bayan data shiga ta gaishe da shi ya amsa bata k'ara ce mashi komai ba ta juyar da kanta tana
kallon gefen hanya, lokacin da suka iso Unguwar suna zuwa gab da gidan su ta juya ta kalle shi yana
kallonta ta mirror ta d'an cije baki had'i da d'an yamutsa fuska, dage mata gira yay ba tare da ya kalleta
ba yace "What?" A marairaice tace mashi don Allah ya bari ta shiga gida ta gaida gwaggo idon ta akan shi
taga ya d'an girgiza kai alamar a'a, 6ata rai tayi idanunta sukai rau rau tana ta d'an kikkafta su bata yi
tunanin zai k'i barin ta ta shiga ba, suna shiga kwanar gate tace mashi ya aje ta anan ta shiga ta k'aramar
kopa ya parker ba tare da ya ce komai ba, saida ta juya zata bud'e kopar taji voice d'in shi yace ta bari
wani time zata je yanzu in taje za'ai mata fad'a ne, juyowa tay ta kalle shi fuskarta a d'an kwa6e ya bud'a
mata ido alamar taji ta jinjina mashi kai sannan ta juya ta bud'e, bayan ta fita yaja Motar ya tunkari gate
ita kuma ta shige, tana isa part d'in a bakin kopar parlor ta cire takalmanta kafin ta wuce ciki, tana shiga
Bedroom tay sensing k'amshin Haisam a ranta ta raya ko ya shigo d'akin ne, wata zuciyar ta ce k'ilan
wanka yazo yayi, wucewa tayi ciki ta aje jakar ta ta cire Hijab sannan ta dawo wurin gado ta fad'a alamar
ta kwaso gajiya, tana kwanciya taji k'amshin ya cika mata hanci fiye da yadda taji shi da ta shigo,
hancinta ta kai jikin zanen gadon ta shinshina nan ta tabbatar da k'amshin shi ne ke tashi a jikin zanen
sosae, cigaba da bin jikin zanen tai tana sunsunawa kafin ta d'ago mamaki shimfid'e akan fuskar ta,
tambayar kanta ta shiga yi mi zai kawo k'amshin shi haka a wurin in dae ba kwanciya yay ba wata zuciyar
ta bata kwanciyar yayi kenan, jikinta ne yay sanyi tay shiru a ranta tana raya kenan had'a gado da ita ne
bai son yi, sosae abun ya dame ta don har Fuskar ta ta bayyana, ta d'an d'auki lokaci haka can ta tuna da
bata yi salla ba ta saukko jiki sa6ule ta wuce laundry room, Alwala tayo tazo ta kabbara salla har ta gama
bai shigo ba ta wuce Toilet don tayi wanka, bayan ta fito shiryawa tay cikin sabuwar doguwar rigar
Atamfa tana tsaye a gaban mirror tana d'an yin light make up yayin da a ranta take ta juya kwanciyar da
yayi akan gadon tana haka ya turo k'opar ya shigo suka had'a ido ta cikin mirror d'in, ganin yayi tsaye
yana ta kallon ta ba tare daya ce komai ba yasa ta juyo ta kalle shi lokacin yace mata ga Abinci can an
kawo ta fito ta ci ta d'aga mashi kai daga haka ya juya ya fita ta bi shi da ido, Bayan sun gama cin Abincin
ta gyara wurin ta wanke komai a ranta ta yanke tafiya part d'in Hajiya don ta bashi wuri k'ilan ya k'ara
kwanciya kan gadon in zai yi bacci, tana can har yamma suka fara aikin girkin dare da Saude, suna cikin
yin girkin ne ta tambayi Sauden akan yau da safe ita ta dafa mata indomie, yar dariya tayi don ta d'ago
dalilin yin tambayar tata tace mata ba ita ta dafa ba wanda ya kai mata shi ya dafa, ganin Fatun tayi d'an
jimm yasa tace mata tayi mamaki ko ta d'aga mata kai tace "nima sosae nai mamaki lokacin dana fito na
gan shi a cikin Kitchen yana dahuwar, na kuma rud'e don abu ne da ban ta6a gani ba, ni tunda nike da
shi ban ta6a ganin yazo ko bakin Kitchen d'in nan ba balle ta kai shi da yin girki, bamma yi tunanin ko
ruwan zafi ya iya dafawa ba sai gashi da yin girki kuma da ga ji Abincin yayi dadi don baki ji yadda
k'amshi ya cika wurin Kitchen d'in ba" Murmushi kawae Fatuu ke yi a cikin ranta tana raya a haka kai
kace Saboda yana son ta ne yayi amman kawai kulawa ce, ji tay Sauden ta k'ara cewa "ni bansan zaki
Makarantar bane ai da nayi maki Breakfast din da wuri, saida ma nace ya bari in yi amma yace in bar shi
kawae dai in rink'a tashi da wuri ina maki" shiru Fatuu tay still da murmushi akan fuskar ta Saude ta
shiga tsokanar ta tana fad'in ai daga yau da tayi sallar Asuba bazata koma ba kar tayi ma Ango laifi kan
Amaryar shi, sai bayan da tayi sallar isha'i ta koma part d'in su tare da Abincin nasu, lokacin da suka yi
shirin kwanciya tana zaune akan gado tana yin rubutu ya shigo tana ganin shi ta san mi ya shigo yi da
kanta ta d'auki pillow d'in ta mik'a mashi ya amsa Fuskar shi a sake ya furta mata thanks da kuma Gud
night ya juya tabi shi da kallo ta d'an kwa6e fuska.

Ranar Laraba bayan ya d'aukko ta daga Makaranta sun gama cin Abinci ta gyara wurin, tana cikin
Bedroom ya turo kopa ya shigo tana zaune a bakin gado ta juya ta kalle shi, daga bakin gadon ya tsaya
Fuskar shi a sake itama da murmushi take kallon shi ya d'an d'auki lokaci ta fahimci kaman wani abu
yake son cewa amman kuma yayi shiru, tambayar shi tay ko akwai abunda zata yi ya girgiza mata kai
slowly taji yace in tana so taje gida yanzu da daddare zai zo ya d'aukko ta, waro ido tay baki bud'e take
kallon shi ta kasa ce mashi komai don Maganar tazo mata a bazata, ganin yadda tayi yasa shi d'an d'age
mata gira yace ko bata son zuwa ne aikuwa da sauri ta mik'e tana girgiza mashi kai had'i da yin
murmushi ta hau yi mashi godiya farinciki bayyane akan fuskar ta ta nufi wurin wardrobe don ta shirya
ya bita da ido, ba 6ata lokaci ta gama shiryawa da wata rantsattsar sabuwar shadda a cikin kayan da aka
kawo mata ta ca6a ado ta fito a Amaryar ta sak sai k'amshi take bazawa, lokacin da ta fito yana zaune
akan kujera yana lallatsa Computer ya d'ago ido yana kallon ta har ta k'araso ta tsaya daga gefen shi tana
ta murmushi shima murmushin ya mayar mata tace mashi ta tafi ya d'aga mata kai ta juya, har ta fice
idon shi na akan kopar sai bayan wani lokaci ya janye idon ya maido shi kan abunda yake, tana tafiya
tana faman sakin murmushi sai kace wadda ta shekara bata je gidan ba, lokacin da ta iso kopar gidan
shagon Kawu Amadu a kulle yake dama tunda suka wuce da aka d'aukko ta daga Makaranta taga shagon
a kulle, a ranta ta raya k'ilan yana Makaranta daga haka ta shige cikin gidan, daga bakin k'opa ta tsaya
tsakar gidan wayam ba kowa tana murmushi ta kwad'a sallama ba'a amsa ba saida ta k'ara d'aga murya
tayi wata sallamar sannan ta jiyo Muryar gwaggo ta amsa, d'an lek'o da kanta tayi don taga waye nan tay
arba da Fatuu dake tsaye tana mata murmushi, hannu gwaggo ta kai ta rufe baki sai kuma ta janye kan
ta koma ciki bada jimawa ba sai gata ta fito hannun ta ruk'e da tsintsiya ta d'agata alamar bugun Fatun
zatayi ita kuwa mi zatay in ba dariya ba ta nufe ta da gudu suna had'e wa ta k'ank'ame ta gaba d'aya
harda tsintsiyar, dariya itama gwaggon tasa tana fad'in waya fito da ita Fatun tace Ya Haisam din ne ai
yace tazo ko, d'aki suka nufa Fatun tay ma gwaggon side hug, bayan sun shiga a bakin gado suka zauna
idon su a cikin na juna sai faman dariya suke ma juna, sosae gwaggo taji dad'in yadda ta ganta duk da
Fuskar ta ta d'an fad'a amman wannan dama tun kafin ta tare ne Saboda ciwon laulayin da tayi amman
ta k'ara haske fuskar ta sai sheki take fatar nan tayi lukui ko d'igon k'urji babu, Fatuu ce ta katse shirun ta
gaishe da ita bayan ta amsa ta tambayi suna lafiya tace mata eh,

"Amman ya akai kika fito haka da wuri, bana ce banson ki rink'a zaryar zuwa ba miyasa wani lokacin
baki jin magana" tay Maganar ta d'an d'aure fuska, a shagwa6e tace "Wllh shine fa yace in zo..." tunkan
ta rufe baki ta katseta "to tunda kin matsa ba dole yace ki zo ba" da sauri ta ce mata wllh bata matsa
mashi ba nan ta kwashe yadda akai ta fadi mata gwaggon ta gyad'a kai alamar ta yarda, tambayar ta tayi
Kawu Amadu tace bai dawo ba yana Makaranta tace dama saida tayi tunanin haka, hira suka shiga yi kai
kace sun dad'e da rabuwa, suna cikin yin Hiran Fatuu ke mata Maganar kud'in da suke a cikin Account
d'in ta tace ana ta ajiyar su zata turo mata tayi wani abun dasu, gwaggon na yar dariya tace to ita mi zata
yi da su tunda nata ne tayi wani amfanin dasu mana, tace ai ita ba abunda zata yi dasu,

"amman tunda kince zaki d'aukko Mino ba sai kiyi amfani da su ba wurin karatun ta" yar harara gwaggon
ta wurga mata ta d'an girgiza kai tace "Ke da na d'aukko ki na amshi kud'in karatun ki ne, tunda ni nasa
kaina ai bazai gagare ni ba" shiru suka d'an yi can ta sake cewa "ina ganin ko a tura ma Baffan ki sai a siya
maki shanaye dama rannan yake man Maganar Sadakin ki duk da Ard'o ya amshi wasu amman yace zai
cika maki kinga sai a had'a da d'an kunnan zinarin ki a canzo" da sauri Fatun tace ita dai ba sai an bata
wani sadaki ba suyi amfani dasu kawae gwaggo na yar dariya tace ai sai ta kira Baffan nata ta fad'a
mashi tace to, sai can yamma Amadu ya dawo shima sosae yay farin cikin ganin Fatun anan d'akin
Gwaggon ya zauna harda sakata ta d'ebo mashi Abinci a Kitchen tace to gwaggo na dariya tana fad'in
yanzu fa Yayar shi ce ita ya zai sakata aiki, shima dariyar yake yace "haba dai yaya ta, ai koda goma ta
lalace tafi biyar Albarka kuma ba'a ta6a canza ma tuwo suna ai", bayan ta kawo mashi Abincin suka
cigaba da hira Kawu Amadu nata tsokanar ta yana fad'in wai ita nan Matar aure ce ko shi ganin abun
yake kamar wasa gwaggo tace "ai dole kaga hakan tunda kai baka da niyya ko Maganar auren ma banji
kana yi ba" yana dariya yace "ai shi lokaci ne, ita ai tama fi ni rashin niyyar auren tunda kin ta6a ganin
saurayi yazo kopar gidan nan wurin ta Saboda bata basu dama, komai tace ita likita zata zama sai ga shi
ta tafi gidan Romeo karatun likitancin" gaba d'aya sukai dariya, ana gama sallar isha bada dad'ewa ba
Haisam yazo shima yasha shadda wadda ta hau da ta jikin Fatuu don ajikin aikin tata akwae kalar daya sa
sai baza k'amshi yake, a parlor suka zauna suna gaisawa da gwaggo ta k'ara yi mashi godiya sosae nan
tace bari a kawo mashi Abinci yace a'a a barshi bai jin yunwa, daga baya sukai sallama taje tay ma Fatuu
dake cikin d'akinta Magana suka fito tare ta rako su har kopar gida, bayan sunyi sallama da Amadu ya
rako su har bakin Mota suka tafi, mik'ar hanya Fatuu taga yayi suka fito daga Unguwar suka hau titi
sosae tana ta kallon hanya, wani k'aton Shopping mall suka je bayan ya parker Motar a inda aka tanada
yace ta fito, da kanshi ya d'aukko shopping cart tana tsaye yazo yace ta d'auki duk abunda take so, rasa
abunda zata d'auka tay don gani take kusan komae tana dashi k'arshe dai sai shi ya shiga d'aukar mata
kayan har saida cart d'in ya cika ya bata yace ta kai wurin biyan kud'i sai ta d'aukko wani aikuwa ta
marairaice mashi a shagwa6e ta hau rok'on shi kan a barsu hakanan itafa tana da komai, har jakunkunan
kayan da Hajiya ta aiko mata ta fad'i mashi don a tunanin ta ko bai sani ba, k'arshe dole aka barsu
hakanan d'in suka je suka biya aka kai masu kayan Mota bayan an juye a manyan Shopping bags, bayan
sun baro wurin wani babban Cafe ya kaisu yace ta fito su ci Abinci, sosae Fatuu taji dad'in wurin kowa ya
za6i abunda yake so aka kawo mashi da suka gama su ka tafi, a gaban wani babban cold store ya k'ara
Parker Motar yace mata yana zuwa ta d'aga mashi kai bayan ya fita ya zagaya ya shiga wurin tana ta
kallon shi ta cikin glass, ruk'e da babbar leda mai d'auke da tambarin wurin ya fito ya zagaya driver side
d'in ya koma ciki, saida ya mik'a mata ledar sannan ya ja Motar, yana ta driving ganin ta aje ledar akan
cinyoyin ta bata ko bud'e ba yasa shi d'an kallon ta yace nata ne, da d'an murmushi tace mashi Thanks
har saida ya sake juyowa ya kalleta yaga tana dariya dama ya gane kwaikwayon shi tay, maida idon yay
kan hanya yaci gaba da driving ita kuma ta bud'e ledar, su ice cream ne da youghort ta fiddo ice cream
d'in ta fara sha, lokacin da suka iso gida tare suka d'auki kayan suka nufi part dinsu, saida ya kai mata su
cikin daki sannan yace mata yana zuwa ya fito ya nufi part d'in Hajiya, cire gyalenta tayi ta hau jera kayan
cikin Wardrobe harda nata dama tana ta so ta jera su, sosae taji dad'in kayan ba kamar English wears
d'in ciki don tana son k'ananun kaya, bayan ta gama shirya komai wad'anda ba yanzu zata yi amfani dasu
ba ta sasu daga can k'asan wardrobe d'in, takalmanta kwasa ta fita cikin Corridor suma ta jera su a jikin
shoe rack inda takalman Haisam d'in suke, bayan ta gama ta wuce Kitchen tana shiga ta saki baki tana
bin kayan Abincin da ta gani a ciki su kwalayen indomie da spaghetti, macaroni su doya da dankali harda
buhun shinkafa gasu madara, milo, Cornflakes harda custard, sugar harda crates d'in k'wai ya kai biyar
ba dai abun da babu na kayan Abinci irin na yan gayu, taji dad'in ganin kayan a ranta ta raya zata fara yin
girki kenan, shirya kayan Abincin ta shiga yi lokacin data gama ta gaji sosae ta wuce d'aki tana shiga ta
nufi laundry don yin wanka, saida ta gama shiryawa ta kwanta akan gado tay rubda ciki tana latsa
Computer d'in ta ya shigo, bayan ya cire agogon hannun shi ya d'aura kan dressing mirror ya wuce
laundry tana ganin haka ta tashi ta d'auki laptop d'in ta fito daga d'akin don ta bashi wuri ya shirya.
Washe gari Alhamis bayan ta dawo daga Makaranta sun ci Abinci a parlor suka zauna shi yana kallo ita
kuma tana typing a laptop d'in ta jikinta sanye da k'ananun kaya riga da skirt sun kamata da yake roba ne
kanta sanye da hula, suna cikin zaman taji yayi Magana ta d'ago ta kalle shi da alamun bata ji ba tace
mashi Magana yake, saida yay d'an jimm sannan yace abunda ta kawo mashi rannan zata zubo mashi
nan take ta gane su cin cin yake nufi, d'aga kai tay alamar to da d'an murmushi ta mik'e ta nufi Kitchen a
ranta tayi mamakin cewa da yayi ta zubo mashin, tunda ta mik'e yabi bayanta da kallo har ta shige cikin
Corridor sannan ya d'age kanshi ya kalli ceiling had'i da d'an lumshe ido, a saman c-table ta d'aura bayan
ta zubo mashi ta kalle shi har lokacin yana a yadda yake tace mashi gashi sannan slowly ya sauke Fuskar
ya d'an d'aga mata kai ta koma inda take ta zauna, a nutse ya fara ci Fatun ta rink'a satar kallon shi wani
lokacin su had'a ido ta d'an yi mashi murmushi, kiran sallar la'asar da aka fara yasa shi mik'ewa ya nufi
hanyar corridor, after some minutes ya fito yana gyara hannun rigar shi da gani Alwala yayi ya nufo cikin
parlon Fatuu ta d'aga ido tana kallon shi, ganin yadda ta kafe shi da ido yasa shi dakatawa ya tambayi da
wani abu ne cikin yar in ina tace dama so take ta tambaye shi har yanzu yana zuwa Gym, shiru ya d'anyi
sai kuma ya d'aga mata kai tay d'an jim tana jujjuya ido da alama magana take son yi ta kasa, d'an
moving yay ya tsaya ya tambayeta ya akai, marairaice fuska tay tace dama so take taje ne wani kallo taga
yayi mata kaman harara ta d'an tura mashi baki had'i da rausayar da kai, jimm yay can yayi sigh yace taje
ta shirya har bata san lokacin da ta saki yar k'arar farin ciki ba ta k'ame hannuwan ta had'i da d'an runtse
ido, sototo yay yana kallon ta tana bud'e idon suka had'a ido ganin yadda yake kallon ta yasa ta kai duka
tafukan hannuwanta ta rufe fuska alamar kunya yay d'an guntun murmushin gefe ya juya, yana fita ta
tattara komae ta nufi Bedroom da sauri don ta shirya, salla ta fara yi tana gamawa ta hau shiri ba 6ata
lokaci ta shirya cikin wando skin tight bak'i da top bak'a ta d'aukko sabuwar jallabiya cikin siyayyar da
aka yi mata ta d'aura saman kayan ta nufi gaban mirror tana rolling veil d'in lokacin ya shigo ya wuce
laundry, daga gida ya shirya don jakar shi bata nan tare suka fito suka nufi parking space suka hau Mota
don yanzu bike d'in shi bai nan.

Sai bayan Magrib suka dawo a cikin kwanar gate ya ajeta yace zai je ya dawo, sosae Fatuu taji dad'in
jikinta tana shiga Bedroom ta wuce toilet tayo wanka don ta had'a gumi sosae, bayan ta fito doguwar
riga mai gajeran hannu mara nauyi ta sa ta d'an shafa mai da humra ta fesa turare, saman gado ta zauna
tana latsa wayar ta a haka har lokacin isha yayi ta mik'e tayi salla, bayan ta gama jakar ta ta d'aukko ta
Makaranta anan ta fara duba books d'inta, tana cikin karatun ya shigo yayi wanka yana sanye da
k'ananun kaya tay mashi sannu da zuwa bayan ya amsa yace ta fito su ci Abinci tace to ta mik'e, bayan
sun gama ta kwashe kayan da sukai amfani ta kai Kitchen saida ta wanke komai kaman ko yaushe ta
koma dining d'in ta gyara table lokacin data gama Haisam d'in bai cikin parlon don yana gama cin Abincin
ya fita, bayan duk ta gama abunda zatayi Bedroom ta koma ta zauna a kan gado tana cigaba da yin
Karatu, ji tay ta fara jin bacci ta tattara littattafan ta maida a cikin jakar ta saukko ta maidata inda take
sannan ta dawo ta haye gado taja duvet ta rufe rabin jikinta, bata dad'e da kwanciya ba har ta fara
gyangyad'i ya turo k'opar ya shigo ta bud'e ido tana kallon shi shima ita yake kallo ya nufi gadon, duk a
tunanin ta pillow zai d'auka kaman ko yaushe amman sai taga ya zauna daga bakin gadon ta can
6angaren da yake har saida ta d'an ji mamakin hakan da yayi don bai ta6a hakan ba, shiru suka d'an yi ya
kauda idon shi yana kallon gefe ta lura kaman magana yake son yi, sai da ya d'an d'auki lokaci sannan taji
cool voice d'in shi yace "You will sleep without switching off the light" yay Maganar idon shi a kanta ta
d'an had'e lips d'inta sai kuma a hankali tace ta manta ne ta fara k'ok'arin tashi ya gane wutar zata kashe
taji yace ta bari zai kashe in zai fita ta d'aga mashi kai amman duk da hakan sai ta tashi daga zaune, shiru
suka d'an yi idon shi na kallon gaban shi ita kuma sai kallon shi take a ranta tana mi yake son ce mata ne,

"Am leaving tomorrow" bayan wani lokaci ya d'an kalle ta taji ya fad'i haka, bin shi da ido tay da alamun
rashin fahimtar Maganar tashi taji ya k'ara cewa "I mean am going back to Us, zan je Abuja gobe daga
can zan wuce" yanayin yadda yake Maganar kaman bai so don dole yake yin ta, ido kawae Fatuu take bin
shi dashi ta d'an bud'e baki da gani Maganar tazo mata a bazata ne zuciyarta ta fara bugu da k'arfi don
kaman saukar aradu haka taji Maganar wai zai koma Us duka yaushe aka kawota da zai tafi, goben fa
zata yi sati d'aya amman shine zai ce zai tafi haka take ta ayyanawa a cikin ranta, tana haka taji Muryar
shi yace bata ce komai ba sauke kanta tayi k'asa nan da nan kwalla suka fara taruwa ta shiga kokarin
maida su da k'yar murya na d'an rawa tace mashi "Allah ya kaimu, ya kiyaye hanya" shiru bata ji ya amsa
ba tasan kallon ta yake hakan yasa tak'i d'agowa don tasan data kalle shi tana iya yin kuka, sun d'an
d'auki lokaci a haka shiru can taji ya kira ta da Fatuuh ta amsa ba tare da ta kalle shi ba ya tambayeta da
matsala ne, jin tambayar tay kaman ta rainin wayau ta girgiza mashi kai kawai alamar babu komai,
mik'ewa yay ya nufi hanyar laundry sai lokacin ta d'ago tana kallon shi, yana shigewa wani irin kuka ya
taho mata tasa hannu ta toshe bakin ta da sauri ta koma ta kwanta ta kife fuskar ta jikin mattress, after
some minutes taji k'arar bud'e kopar shi da sauri taja duvet ta lullube har kanta, sanye da bathrobe ya
fito saida ya kalleta kafin ya wuce ciki, shiryawa ya fara yi yana yi yana kai idon shi kanta ko kwakkwaran
motsi tak'i yi, bayan ya gama yasa kayan bacci ya nufi bakin gadon ya kai hannu ya d'auki pillow taji yace
Good Night bata motsa ba balle ta amsa mashi irin ita ala dole bacci take saida ya kashe mata hasken
d'akin gaba d'aya ya kunna mata lamb ta gefen da yake sannan ya juya ya nufi kopa, tana jin k'arar fitar
shi ta bud'e fuskar taci gaba da kukan da take yi k'asa k'asa, saida tay mai isarta don kanta tayi shiru, duk
yadda ta kwaso gajiya amman gaba d'aya bacci ya k'aurace ma idanunta sai juye juye take tana zancen
zuci, saida dare ya raba sannan da k'yar baccin ya d'auketa shima ba wani mai nauyi ba, ana fara kiraye
kirayen sallar Asuba ta farka da wani irin yanayi mara dad'i jikinta yayi weak har wani zazzabi zazzabi
take ji, cike da k'arfin hali tayi shirin zuwa Makaranta ko breakfast d'in kirki ta kasa yi haka ta d'an
tsattsakura ta barshi, tunda suka hau hanya ta juyar da fuskar ta gefe har suka isa Makarantar bata kalle
shi ba saida zata fita sannan ta d'an juya suka had'a ido tace mashi ta gode ya fiddo kud'i ya bata bayan
ta amsa ta bud'e Motar ta fita, ko a Class ma Fauzy ta lura da yanayinta ta hau tambayar ta abunda ke
damunta tace mata kawae bata lafiya da zazza6i ta kwana amman ta sha magani, nan ta hau tsokanar ta
wai kodai har ta biya Ya Haisam saidae kawae tay mata d'an murmushin yak'e, bayan an tashi ya zo ya
dauketa, tunda ta koma ta shige d'aki ta kwanta sai daga baya ya shigo ya iske ta a kwancen ko Uniform
bata cire ba ya tsaya daga bakin gadon yana tambayar ko bata lafiya ne da k'yar ta d'aga ido ta kalle shi
ta girgiza mashi kai ya bita da kallo ta maida nata k'asa taji yace to ta tashi ta shirya zasu yi lunch a part
d'in Hajiya ta d'aga mashi kai kawai ya juya ya fita, a daddafe ta shirya don har lokacin jin jikinta take ba
dad'i tasa riga da skirt na lace iya powder da lip glow kawai tasa suma don kada a gane mata ne, lokacin
data gama shiryawa bai nan tasan bai wuce Masallaci ya tafi don an fara hud'uba ta fito ta wuce part d'in
Hajiya, bata samu kowa a parlon ba ta wuce Bedroom d'in ta bata same ta ba a ciki ta fito ta wuce d'akin
Saude itama bata nan ta raya k'ilan suna Masallaci ta nufi Katifar Sauden ta kwanta sai daga baya ta
mik'e ta nufi toilet tayo Alwala, bayan sun dawo ne ta fito ta iske su a parlor taje ta gaishe da Hajiya har
tana tambayar ta ya akai bata zo sunje Masallaci ba tace lokacin da tazo har sun tafi shine tayi a d'akin
Aunty Saude, daga baya Sauden tazo tace ma Hajiya ta shirya table tace masu su tashi suje su ci Abinci,
da k'yar Fatuu ke turawa ba don tana jin dad'in Abincin ba, ita ta fara tashi Hajiya tace badai har ta koshi
ba da d'an murmushin yak'e tace mata eh tace amman ai bata wani ci na kirki ba tace ai taci ne a
Makaranta shiyasa ta gyad'a kai Fatun ta wuce idon Haisam a kanta, d'akin Saude ta koma bayan barin ta
wurin Hajiya tace "Yanzu har sai yaushe zaka dawo in ka tafi?" Shiru ya d'an yi idon shi akan Abincin
gaban shi kaman mai nazari can ya d'ago ya kalleta yace mata saidae yaje zai gani, gyad'a kai tay da
alamun damuwa tace "banso ka tafi da wuri ba haka tunda Yarinyar nan ba'a dad'e da kawo ta ba,
amman kana da kwakkwaran dalili yakamata ace ka koma aikin kaman yadda kace tunda kusan watan ka
biyu kenan rabon ka da aikin fa, an taho bikin aboki sai kuma jinya kusan wata guda, yanzu da dawowar
mu kuma inaga sati biyu kenan, ita kanta Fanan d'in nasan ta k'agara ka koma don ma tazo Germany
d'in" d'an dakatawa tay sai kuma taci gaba "ba don karatun Fateemar ba ai da ka tafi da ita ala bashshi
kasan yadda zakai in ka je, amman dai kai k'ok'ari in ka koma ka sanar da ita zancen auren naku sannan
kayi k'ok'arin fahimtar da ita don kada kuma a tauye hakkin Fateema tunda itama zata so ku kasance
tare ba kamar yanzu dai bai kamata ace har ka tafi ba, nima zanyi k'ok'arin sanar da iyayen naku bayan
ka tafi, Allah ya shige mana gaba" a hankali ya amsa da Amin, bayan sun gama yace ma Hajiyar zai je
G.r.a ya dawo, gab da sallar la'asar ya dawo ya nufi part d'in su ganin bai ga Fatun ba ya gane bata dawo
ba, shirya kayan da zai d'auka anan yayi cikin trolley d'in shi, ba wasu kaya masu yawa ya d'auka ba ya
bar wasu bayan ya gama aka kira sallar la'asar ya tafi Masallaci, bayan an gama sallar ya dawo ya zauna
akan kujera yasa hannu ya d'an ruk'e ha6ar shi kaman mai yin tunanin, ganin lokaci nata tafiya don 4:30
jirgin su zai tashi yasa shi kai hannu ya d'auki wayar shi, kiran Fatun yay bayan tayi picking yace tazo
yana jiranta a part d'in su a sanyaye ta amsa da to, bada jimawa ba ta turo kopar parlon ganin shi zaune
yasa tayi yar sallama ya amsa idon shi a kanta har ta k'arasa shigowa ta zauna daga d'ayan 6angaren,
ganin yadda ya kafeta da ido yasa ta juyar da face d'inta gefe tana haka taji yay sigh ya fara magana, ce
mata yay yanzu zai tafi duk abunda take buk'ata tayi ma Abbas Magana, jin yayi shiru yasa ta d'an juyo
suka had'a ido da k'yar murya na rawa tace mashi to ta maida kanta k'asa, wani irin kuka ne ke taho
mata sai k'ok'arin maida shi take tana haka taji yace taje Bedroom ta d'aukko mashi trolley d'in shi ta
mik'e ba tare data ce komai ba ta nufi hanyar corridor yana ta kallon ta har lokacin hannun shi na ruk'e
da beard d'in nashi, janye da trolley d'in ta fito yana ganin ta ya mik'e tsaye, daga gaban shi ta tsaya ta
mik'a mashi a hankali tace gashi bai amsa ba ya kafeta da ido kawae, jin yayi shiru yasa ta d'ago idanunta
cike da k'walla ta kalle shi suka had'a ido da sauri ta juyar da fuskarta, k'ara ce mashi tay gashi ba tare
data kalle shi ba taji yace "Won't u accompany me to the Airport?" Shiru bata bashi amsa ba don tasan
tana bud'e baki zata saki kuka sai yamutsa fuska take ta gumtse baki, hannu ya kai ya kamo hannun ta ya
matso da ita har lokacin Fuskar ta na gefe, kiran sunanta yay aikuwa kaman tana jira ta k'wace hannun
nata ta juya da gudu ta nufi hanyar corridor, tana shiga ta nufi gado ta fad'a ta fashe da kuka mai cin rai,
ta d'auki lokaci tana ta rizgar kukan, ganin bai biyo ta ba yasa ta gane ya tafi hakan ya k'ara tunzura ta,
tashi tay zaune kallabin ta ya kwance fuskar ta jage jage da hawaye idanunta sun yi ja a fusace ta fara
magana cikin kuka "Yanzu na tabbatar baka sona Ya Haisam baka kaunata, kawae ka amince kaci gaba da
zama dani ne hakanan ba don kai rayuwar Aure dani ba Saboda ni ban kai matsayin da zan zama matar
ka ba, da kana sona na tabbatar bazaka tafi yanzu ka barni ba, shiyasa ka tafi wurin matar ka da kake so
ka bar ni, hada cewa duk abunda nike so in ma Ya Abbas Magana wato Saboda baka son in rink'a ma
magana ko, to shikenan bazan kira ka ba kasha soyayya da matar ka lafiya zan ma fita daga rayuwar ka
kwata kwata sai ka huta" tana kaiwa nan ta sake fashewa da kuka ta fad'a saman gadon, ta jima haka har
idanunta sun d'an kumbura can ta mik'e ta nufi mirror ta d'auki wayarta dama da ta shigo d'aukar mashi
trolley ta d'aura ta anan, call log ta shiga ta kira lambar Fauzy tana fara ringing ta d'aga tace "Amaryar
mu ya kika koma gida" fashe mata da kuka Fatuu tay a rud'e Fauzy ta saki salati ta hau tambayarta lafiya
cikin kuka tace "Fauzy na gaya maki ya Haisam bai sona gashi nan har ya tafi ya barni" a kid'ime ta hau
tambayar ta ina ya tafi ya barta tace mata ya koma Us, cike da mamaki Fauzy ta maimaita abunda tace
Aunty Mareeya dake gefen ta tana sauraron su ta kai hannu da Sauri tana fad'in ta bata wayar, bayan ta
amsa ta kira sunan Fatun cikin muryar kuka ta amsa tace "naji kina cewa ya koma?" Tace "Eh Aunty
Mareeya yanzun nan ya tafi kuma bansan da zai tafin ba sai jiya da daddare yake fad'i man" salati Aunty
Mareeya ta rafka ta kai hannu ta ruk'e ha6arta cikin bacin rai tace "Amman wannan anyi d'an jakar uba
wllh....ke yi hak'uri na zagar maki miji raina ne ya 6aci, to wai miyasa zai tafi duka sati guda da kai mashi
Amarya, mi ya koma yi ne yaushe yace maki zai dawo" cikin kuka tace "nifa Aunty Mareeya ce man yay
kawae zai tafi bai fad'i man ko wani dalili ne yasa zai koma d'in ba kuma bai ce man ga ranar da zai dawo
ba" salati ta k'ara sakawa sai faman fad'in kai take,

"amman Zarah wani abu bai shiga tsakanin ku bane?" Ta jefa mata tambaya, ta fahimci abunda take nufi
tace mata eh, da tsantsar mamaki tace "Yanzu kina nufin tsawon sati gudan da kikai kallon ki kawai yake
ba abunda ya wakana" k'ara amsa mata tay da eh, cike da takaici da har muryarta ta nuna tace "Amman
dai wannan anyi sak'ago wllh, sai kace ba jini a jikin shi, to ko dai bai lafiya....Amman ma ai mu shaida ne
in ma bai lafiyan tsabar iskanci ne ba wani abu ba, haka suke dama irin Mutanen nan akwae ban haushin
tsiya wllh..." Dakatawa tay tana numfasawa can ta d'aura "Yanzu ina magungunan da aka siyo maki kina
ta amfani da su ne?" tace "a'a, tun bayan da aka kawo ni na daina sha dana ga......" Shiru tay ta kasa
k'arasa Maganar Aunty Mareeya tace "Yauwa Nagode ma Allah kin yi kyaun kai gara da kika daina
amfani dasu duk da haka nasan kin k'waru, don Allah kiyi hak'uri Zarah kin ji, nasan dole ki shiga wani
hali komai anyi maki ne don a nema maki k'ima" amsa mata tayi da to, taci gaba "bari mu zuba mashi ido
muga iya gudun ruwan shi, ki k'ara hak'uri kinji in sha Allahu zaki ci ribar hakurin da kikai, ina nan dake
sai reshe ya juye da mujiya a lokacin kuma zaki murza kambun sarautar ki sai yadda kika so zaki yi, in dai
bada wani kwakkwaran dalili yay maki hakan ba bi'iznillahi ta'ala shima sai ya yi kuka share share" sosae
ta shiga kwantar mata da hankali har saida taji ta d'an saukko sannan su kai sallama Fauzy ma ta
rarrashe ta tace mata tana nan zuwa daga baya sukai sallama, tana niyyar aje wayar taji kira ya shigo ta
kai idonta taga sunan da ta sa ma Abbas ya bayyana, d'an jimm tay kaman bazata d'aga ba can ta kusa
yankewa tay picking ta kara a kunne, tun kafin tace wani abu ya tambayi tana ina tace mashi tana cikin
d'aki yace yana a parlor ta fito a hankali ta amsa mashi da to, gyalen ta dake saman gado ta d'auka ta
yafa ta nufi k'opa, dan jimm tay a bakin k'opar a ranta ta shiga raya komi ya kawo shi can dai ta kai
hannu ta bud'e kopar ta fita........

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

ASM Bk2067*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.........Tana zuwa bakin corridor ta hango shi zaune akan L-shape inda Haisam ke zama, da sauri ta maida
idanun ta k'asa ganin ya zuba mata ido, a d'ayan side d'in ta zauna sai lokacin ta d'ago ta kalle shi still
kallon ta yake a sanyaye ta gaishe da shi ya amsa, shiru suka d'an yi kafin taji ya fara magana, "dama
mun had'u da H,Zakee a Airport ne ban ga kin rako shi ba har nike tambayar shi kina ina yace kina gida
shine nace bari in zo mu gaisa" d'an d'agowa tay ta kalle shi da k'ak'alallen murmushi bata ce komai ba,
shiru suka d'an k'ara yi ganin yanayin ta yasa shi cewa "Mom Zarah ko akwae wani abu ne u look
abnormal" k'walla ne suka taho mata da sauri ta maida fuskarta k'asa had'i da girgiza mashi kai alamar
babu komae, bin ta da ido yay kaman mai nazarinta can ya kira sunanta ta amsa ba tare da ta kalle shi
ba yace ta d'ago, saida tay d'an jimm kafin ta d'an d'ago suna had'a ido k'wallan suka zubo mata sharr
kawae sai tasa mashi kuka ta kai hannu ta rufe bakinta, a d'an rud'e yace "Subhanallahi, Mom Zarah
Mike faruwa ne pls tell me" girgiza mashi kai ta hau yi cikin kukan tace mashi ba komae bata lafiya ne,
tambayar ta yay Mike damunta tace kan ta ke ciwo, shiru ya d'an yi yana kallon ta ya cije lower lip d'in
shi can yay sigh yace "ba gaskiya kika fad'a man ba Mom Zarah, in har baki lafiya na tabbatar H,zakee
bazai tafi ya barki a halin ciwo ba koda kuwa baki fad'a mashi cewa baki lafiya ba nasan zai yi noticing
don yana d'aya daga cikin Mutanen da suka karance ki sosae kusan ma zan iya cewa yafi kowa karantar
ki, so don't hesitate ki fad'a man in akwae wata matsala" cire hannun data rufe bakin tay ta fara goge
k'wallan tana yi tana kallon shi tana d'an bud'e baki, gaba d'aya tama rasa to mi zata ce mashi bata san
ta ina zata fara ba,

"Ko mun fara 6oye ma juna abu ne?" Cikin muryar kuka tace "ba kai ne ka fara ba, ka 6oye man cewa shi
miji nane" d'an shaking kan shi yay tun a Asibiti ya fahimci bata ji dad'in abun ba, "am very sorry for dat
Mom Zarah, kaman yadda na fad'a maki haka aka tsara so bai kamata ace na fad'a maki ba tunda bamu
san yadda Al'amarin zai kasance ba, duk da muna fatan auren ya d'ore ba lalle hakan ya faru ba kuma
kinga in kika sani sai kin fi shiga mawuyacin hali fiye da farko, da naga bai sake ki ba kaman yadda aka
tsara lokacin na fara sama rai na auren zai d'ore, a lokacin da abu ya shiga tsakanin ku da ace kin fad'a
man da tabbas zan bayyana maki komai ne to amman sai baki sanar man ba kema kika 6oye man har
abu mara dad'i yazo ya faru, amman nasan haka Allah ya k'addaro komae ba mu isa mu canza ba, yanzu
shikenan abar shi a munyi ma juna laifi, kiyi hakuri nima kuma nayi hakuri sai muci gaba kaman farko, in
kina da wata matsala feel free ki fad'a man ta yuwu in iya taimaka maki ko yaya ne, kinsan ance a
Problem shared is a problem half solved" idon ta a kanshi tana ta kikkifta su a kokarin ta na ta dakatar da
cigaba da yin kukan, ce mata yay yana Jin ta ta fad'i mashi Mike damun ta ta fara motsa baki cikin
karyayyar murya tace "ba wani abu bane Ya Abbas, kawai dai na fahimci Ya Haisam bai sona ne, ya za6i
yaci gaba da zama dani ne don dalili biyu, ko don abunda ya faru tsakanin mu ne yana ganin in bai cigaba
da zama dani ba bai man Adalci ba ko kuma k'ilan Hajiya ce ta matsa mashi amman ba wai don yana son
yin rayuwar Aure dani bane" da k'yar take tattaro kalaman take fad'i mashi, shiru yayi daga Maganar da
tayi ya fahimci komae dama kuma tafiyar Haisam d'in tasa shi kokonton in wani abu ya shiga tsakanin su,
nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yama rasa ta ina zai fara shi kanshi ya rasa gane ma Haisam d'in game
da auran, jin yayi shiru yasa Fatuu cigaba da Magana a sanyaye "I decided to get out of his life tunda ba
son zama yake dani ba ni bazan so in zame mashi matsala ba, yayi man dukkan Alkhairi a rayuwata bai
kamata in hana mashi kwanciyar hankali ba" girgiza kai Abbas yay "kar kice haka Mom Zarah nasan dole
ki shiga damuwa game da hakan amman ina ganin mu bashi lokaci tunda kinga duka sati guda kenan da
kasancewar ku tare" da alamun bacin rai tace "to Ya Abbas wane lokaci zamu bashi abunda komai a
bayyane yake da yana sona ba zai tafi ya barni ba, koda ta kama ma ya tafin ai a k'alla zai man bayani kan
dalilin tafiyar da kuma lokacin da zai dawo, amman fa jiya da daddare kawai yace man wai zai koma
kuma yau d'in yay tafiyar shi" idanunta ne suka kawo ruwa da alama abun ba k'aramin 6ata mata rai yay
ba, hannu ta kai ta goge k'wallan tace "gara mu rabu kawai tunda na gane his heart belongs to his wife
alone ni na hak'ura, da ai har na hak'ura dashi na amince ai man auran abun yay turning haka, ni yanzu
ya Abbas ka taimaka man kasa ya sake ni kawai, dama yace duk abunda nike so in maka magana, to ka
fad'i mashi ya sake ni don Allah kaga sai suci gaba da rayuwar shi da Matar shi cikin farin ciki ba tare
dana takura su ba, kaga bama sai ya dawo ba" fuska a kwa6e ta k'arasa Maganar Abbas dake kallonta ya
d'an yi guntun murmushi don ba abunda ke acikin Maganar tata face sheer jealous, sigh yay "kar muyi
saurin yanke mashi hukunci Mom Zarah, mu dai k'ara bashi lokacin kiyi hakuri, ina d'aya daga cikin
Mutanen dake fahimtar shi sosae amman da yawan lokutta is very difficult to understand him
completely, ni raina na bani shima yana son ki don kuwa H,Zakee adalin Mutum ne zan iya rantsuwa
akan hakan, indai yasan zai aure ki ya takura rayuwar ki bazai ta6a amincewa yaci gaba da zama dake ba
so mu bashi lokaci, in har ya dawo komai bai canza ba na maki Alkawarin da kaina zan je wurin Hajiya in
fayyace mata komai game da zaman ku na tabbatar zata raba ku bazata goyi bayan a cutar da wani ba"
shiru tay taji ta amince da Maganar ta shi, tambayar ta yay hakan yayi mata ta d'aga mashi kai,
lallashinta ya shiga yi yana kwantar mata da hankali har ta d'an saukko, tambayar ta yay yaushe zasu yi
exam ne tace mashi kafin Azumi yace to ta dage tunda Azumin ya taho kar tasa damuwa a ranta har tazo
ta samu matsala tace mashi to,

shiru suka d'an yi can ta mik'e tace bari ta kawo mashi lemu ya dakatar da ita yace daga gida ya fito yaje
Airport bai jin k'ishi tace to bari ta kawo mashi cincin nan ma yace mata ta barshi ai an basu da yawa sun
ci sosae, duk da hakan saida ta tafi tana fad'in bari ta kawo mashi ya kaima su Abdul ta nufi hanyar
corridor yabi ta da kallo har ta shige sannan ya d'an girgiza kai a fili ya furta "DESTINED HEART", bada
jimawa ba ta dawo ruk'e da leda ta d'aura akan c-table ta koma ta zauna, rok'on shi tayi kan ya kawo
mata Abdul ya zauna na wani lokaci ya nuna mata yanzu in ya kawo mata shi aiki zai zamar mata tunda
ba hutun school akayi ba kuma itama gashi tana zuwa Makaranta amman ta bari in akayi hutu yayi mata
Alk'awari zai kawo mata shi har hutun ya k'are ta ce to, shiru ta danyi sai kuma tace "yace duk abunda
nike so kai zan tambaya yanzu in ina son fita fa?" D'an murmushi yay yace ina zata ne tace a'a tana nufin
in fita ta kama ko zuwa gida haka, still murmushin yake yace ba wani abu duk inda take so ta je tunda
yasan bazata je inda bai kamata ba, daga baya ya mik'e yay mata Sallama yace zai je su gaisa da Hajiya
tace ya gaida su Aunty Feenah, bayan tafiyar shi d'aki ta koma ta kwanta rub da ciki ta fad'a duniyar
tunani wanda kusan duk na Haisam ne, can ta mik'e ta d'aukko wayarta ta shiga cikin gallery, tsofaffin
hotunan su ta shiga gani wanda yawanci duk shi ya tura mata a ranta ta rink'a jin inama ace irin rayuwar
nishad'in da suke har yanzu kenan, a hankali take kai hannu tana goge k'wallan dake zubo mata daga
baya ta kife wayar tay lamo akan gadon, tana haka har Magrib sannan ta mik'e don tayi salla jikinta duk
jin shi take kaman na wadda ta tashi daga ciwo.

Haisam ya sauka lafiya tuni dama yaje ne don ya duba jikin Mahaifin shi kafin ya wuce, ya iske ya samu
sauk'i sosae dama ciwo ne kawai Allah ya kawo mashi don mutum ne mai cikakkar lafiya don ko hawan
jini bai da shi hakan yasa ma wasu sukai tunanin ko Asiri ne ba kamar da yake d'an siyasa ne saidae shi
yace ya d'auke shi ciwo ne kawai Allah ya kawo mashi, da daddare suna cin Abinci ne Mom d'in shi ke
tambayar wai ko har yanzu bai lafiya ne taga still da rama a fuskar shi gashi kaman baida kuzari yana
d'an murmushi yace mata ya samu sauk'i sosae Dad d'in shi yace ai bai cin Abinci sosae gashi ya yi ciwo
dole yay ta zama hakan, shidai d'an murmushi kawai yake, bai ci wani Abincin kirki ba ya mik'e Senator
ya kalli Mom d'in shi yace "you see, taya zai maida jikin shi da wuri" d'an 6ata fuska tay tace mashi ya
zauna ya k'ara to shi bai iya gardama ba ba kamar kuma da iyayen shi kawae sai ya koman ya k'ara ci
daga baya ya tashi ya nufi upstairs idanun Mahaifiyar tashi a kanshi, bayan ya haye ta maido idon ta kan
Senator tace bai lura kaman yana cikin damuwa ba ya d'an watsa hannu yace ba lalle ba tunda gane
mashi nada wuya, haka ta bar Maganar amman a ranta tana ganin kaman akwai abunda yake damun shi.

Daren ranar baccin Fatuu ragagge ne, Washe gari bayan tayi sallar Asuba Al'qur'ani ta d'aukko ta fara
karatu, ta dad'e tana yi bayan ta gama ta nufi toilet don tayi wanka, tana cikin sa kaya Saude ta kawo
mata breakfast, bayan ta gama Part d'in Hajiya ta nufa ta isketa a d'aki suka gaisa tay mata ya kewar mai
gida ita dai d'an murmushi kawai tayi, nan ta bata hak'uri tace mata daga wurin aikin shi ne suka buk'aci
ya koma tasan bai rasa fad'i mata, tace ai sun ma yi mashi mutunci suda basu wasa da aiki don ma yana
yi masu wani daga nan, ita dai Fatuu shiru tay daga baya tace zata je wurin Aunty Saude, tare sukai aikin
Abincin rana, gaba d'aya ta koma sukuku da ita ga tunanin Haisam da ya addabi zuciyar ta komi take
shike mata yawo a rai har Saude ta lura da yanayin ta ta tambayi ko har yanzu ciwon kan take tace mata
a'a da Sauk'i, anan taci Abincin rana tare da Hajiya bayan sun gama suka koma falo suna kallo saidai ita
idanun nata na kan tv d'in ne ba don tana fahimtar mi ake ba wani lokacin sai ta sauke idanunta tay
shiru, Hajiya da ta lura da yanayin ta tace "Fateema anata kewar miji ko?" d'an firgit tay ta kalli Hajiya
lokacin idanunta na k'asa tay Maganar ta d'an k'ak'alo murmushin yak'e ba tare da tace komai ba,

"ko kije gida nasan in kika ga Dije Kya rage kad'aici" sosae taji dad'in Maganar a hankali tace mata to ta
mik'e, har zata tafi Hajiya tace taje Kitchen ta zuba Abinci ta kai mata nan ma ta amsa da to ta nufi
Kitchen d'in, Yau ma data je gidan saida gwaggo tayi mata fad'a kan miyasa zata rink'a zaryar zuwa a
sanyaye ta fad'i mata yadda sukai da Hajiyar, duk a zaton ta bata san Haisam d'in ya tafi ba amman sai
taji tace ai yazo yayi mata sallama kafin ya wuce jiya ma harda kayan Abinci Tk ya kawo, ta d'ora da
fad'in ai dama yakamata ya koman tunda bada shirin zama yazo ba, gwaggo ta lura da yanayin ta amman
bata ce komai game da hakan ba sai kawai ta nuna mata tayi mashi Addu'a da fatan Alkhairi in ya samu
lokaci tasan zai dawo ne Fatun ta d'aga mata kai kawai, jefi jefi suke yin fira nan Fatun ta rok'i gwaggo
kan ta d'aukko Mino yanzu sai ta taya ta zama, cikin wasa tace kenan ma ita zata d'aukko ma ita, a
sanyaye tace a'a ko kwana ne sai ta rink'a taya ta tace ta kusa zuwa ai, sai bayan isha ta koma gida a part
d'in Hajiya taci Abincin dare lokacin da zata koma part d'in su Hajiyar tace mata in tana so ta kwana anan
tace to don a tunanin ta in anan ne k'ilan ta samu tayi bacci sosae ba kamar jiya ba, komawa tay part d'in
nasu ta shiryo sannan ta dawo, a d'akin Saude ta kwanta da yake ita ba anan zata kwana ba, Washe gari
bayan sallar Azahar tana part d'in Hajiya sai ga kiran Fauzy bayan ta d'aga tace mata bata nan ne gasu
sun zo da Aunty Mareeya amman ba kowa a part d'in, da sauri tace mata gata nan tana part d'in Hajiya
ne, tana shigowa parlon ta nufi Aunty Mareeya da yar sassarfa ta fad'a jikin ta sai kuka, rarrashinta ta
shiga yi tana d'an bubbuga bayanta daga baya ta washe, sosae ta shiga bata baki tana kwantar mata da
hankali ta nuna mata sam bata ji dad'in halin da take ciki ba amman in sha Allahu komai ya kusa zama
labari, fira suka shiga yi daga baya Fatun tace bari ta d'aura masu girki suka ce suda daga gida suke sun ci
Abinci ta kafe kan ai anjima sai suci in ta dafan, ta fad'i masu bata ta6a yin girki ba sai yanzu Aunty
Mareeya tace ah lalle taje tayi masu su ci girkin Amarya harda cewa Allah yasa akwae sauran man shanu
tana yar dariya tace eh akwai ai bata ma wani amfani dashi, tare da Fauzy suka fara yin aikin girkin
wanda Fried rice ce zasu yi, suna cikin yin girkin Aunty Mareeya ta shigo Kitchen d'in tay masu sannu da
aiki kafin ta nufi drawer din da ta saka mata magunguna ta bud'e, wasu daga ciki ta fiddo tace mata zata
tafi dasu don kar su lalace in buk'atar su ta taso daga baya zata aiko mata da wasu, d'an tura baki tay
tace ita tama kwashe su duka tana dariya cike da tsokana tace karfa daga baya ta kirata tana mata yar
muryar Aunty Mareeya dama Maganar Magungunan nan ce, duk sukai dariya tace ita bazata k'ara
amfani dasu ba, bayan sun ci Abincin duk in suka ce zasu tafi sai Fatuu ta marairaice kan su bari sai
anjima a haka har dare yay sai da akai sallar isha sannan suka tafi bayan sun je part d'in Hajiya sun gaisa,
Washe gari tana yin shirin zuwa Makaranta a ranta ta raya ko wama zai rink'a kaita, k'arshe ta yanke in
ta gama shirin kawae ta tafi ta hau abun hawa, bayan ta gama shiryawa a parlor ta zauna tana yin
breakfast da Saude ta kawo mata tana cikin yi aka k'wank'wasa kopa ta bada izinin a shigo, Tk ne ya
shigo yana ganinta ya fara mata dariya ya shigo ciki, akan armchair ya zauna har suna had'a baki wurin
gaishe da juna yace mata dama zuwa yayi yaga in ta shirya nan ta gane shine zai rink'a kaita kenan, yana
zaune har ta gama taje ta d'aukko jakarta da takalma suka tafi.

A Ranar wadda ta kama Monday Haisam ya tafi U.S, Bayan ya isa Fanan ta d'aukko shi ta sha kwalliyar
k'ananan kaya, gaba d'aya Farinciki ya cikata har fuskarta bata iya 6oyewa, tun a Mota ta fara nuna
mashi tayi missing d'in shi don ma ita ke driving d'in, bayan sun isa gida zo kaga tarairaiya har wanka ita
tayi mashi, haka Abinci ma a baki ta rink'a bashi, bai dakatar da ita daga yi mashi duk abunda ta saba
mashi ba, ita kanta saida tayi Maganar fad'awar da fuskar shi tayi da har yanzu bata ciko ba, cike da
nuna damuwa ta shiga tambayar ko har yanzu bai lafiyan ne yace mata ya warke nan ta yanke harda
stress tace ya tashi daga ciwo bai huta ba ya tafi wani aiki, sosae ta bashi dama ya huta don har saida ya
d'an yi mamakin hakan harda su massage aka mashi, daga baya ne bayan ya huta sosae abu ya shiga
tsakanin su a lokacin kuma ta nuna mashi how badly tay missing nashi to shima d'in bai yi k'asa a gwaiwa
ba wurin sauke mata abunda ya tara, daga baya suka cigaba da gudanar da rayuwar su yadda suka saba.
Ba k'aramin yak'i da zuciyar ta Fatuu ke yi ba, ta matsa mata da tunanin Haisam gaba d'aya ta koma
sukuku da ita gashi tunda ya tafi basu yi waya ba ko text message balle kuma chat, sosae take daurewa a
haka har yayi sati guda da tafiya, a ranar wadda ta kama Friday bayan ta dawo daga Makaranta tana
cikin Bedroom ta fito daga wanka tana shiryawa taji wayarta ta fara ringing ta nufi bakin gado inda take
ajiye ta d'auka, har saida gaban ta ya fad'i ganin Haisam ne ke kira, tamke Fuska tay wata zuciyar ta bata
kar ta d'aga ta bi kiran da kallo har ta yanke, zama tay a bakin gadon nan da nan mood d'in ta ya canza
damuwa ta bayyana a kan fuskar ta a ranta ta shiga raya ace tunda ya tafi bai kira ta ba sai yau a haka
za'a ce wai yana son ta Abbas da bata had'a komai dashi ba kullum sai ya kira yaji ya take wata rana ma
sau biyu yake kiran nata, tana ta zancen zuci wani kiran ya sake shigowa ta k'ara bin screen d'in da kallo,
har ta kusa yanke wa wata zuciyar ta raya mata hakan ba daidai bane tunda shi ya kira ba ita ta neme shi
ba ta d'auka, picking tay ta kai wayar kunne jin shiru yasa can k'asan makoshi tay sallama, amsa mata
yay daga haka tay shiru shima shirun ya d'anyi sai kuma taji ya tambayi yadda take k'asa k'asa ta bashi
amsa da lafiya lau, sake tambayar karatun ta yay nan ma tace lafiya lau, jin sun yi shiru yasa tace mashi
sai anjima yace Ok, bin wayar tay da kallo fuska a kwa6e bayan ta cire ta daga kan kunnan ta, can ta cillar
da ita ta kife fuskarta a saman gadon.

***** ******

Ranar Friday da ta kama satin Haisam biyu da tafiya daidai, Misalin k'arfe sha biyu da rabi na rana Jirgin
su Senator da Hajiya Maryam ya sauka a Airport d'in Katsina don amsa kiran da Mahaifiyar su tayi masu
kwana ukku da suka wuce, tun ranar data kira su ta sanar dasu tana son ganin su suka hau tambayar ta
lafiya tace masu Kada su tashi Hankalin su lafiya lau sai Alkhairi kawae tana son ganin su ne in sun samu
lokaci, shine daga baya suka kira Junan su suka yanke ranar da zasu zo, gaba d'aya sunyi shiga ta Alfarma
Senator na sanye da babbar rigar shadda haka takalman shi ma fararen cover ne da hular shi hannun shi
sanye da dankareren agogon diamond yayin da Hajiya Maryam ke sanye da rantsattsiyar bak'ar shadda
data sha aiki golden takalmanta ma golden ne masu d'an tudu haka jaka da gyalen jikinta duk golden ne
tsadaddun gaske to coge d'aurin kallabi, tun daga kan kunnan ta da wuyan ta da kuma hannunta
kerarrun gold ne, dole ma ka kalle ta ko bakai niyya ba sai faman baza k'amshi suke ba kamar dai
Senator d'in, in ka kalle su zaka ga basu kama saidai kamar jini don shi mahaifin su ya biyo ita kuwa
Hajiyar Sanata ce sak, A dankareriyar Jeep aka d'aukko su Motar Escorts na biye da su suka nufi gidan
Hajiya, bayan sun isa cike da Farinciki Hajiya ta tarbi y'ay'an nata abun Alfaharin ta itama ta ca6a adon
leshi, kan kace mi kopar gidan ya cika da Jama'a Mutanen Senator, a nan Parlor suka zauna suna gaisawa
daga baya wasu daga cikin Mutanen Senator d'in Abokan shi na hannun daman shi da suka zo yi mashi
sannu da zuwa su kuma gaida Mahaifiyar tashi suka shigo a bisa Umarnin shi, nan fa hira ta 6alle baka jin
komai sai dariyar manyan mutane masu tumbin Naira, Saude da wata da aka d'aukko don ta kama mata
aiki suka shigo masu da abubuwan sha da na ta6awa kafin lokacin cin Abinci yayi, daga baya sukai ma
Hajiya sallama bayan sun mata Alheri irin nasu na manya Senator yace mata zaije Government House su
gaisa da Governor, bayan tafiyar su ya rage daga ita sai Hajiya Maryam, hannu ta kai ta kamo na Hajiya
da yake a kujera d'aya suke 2 seater da murmushi tace "Hajjajutah fatan dai kina lafiya?" itama
murmushin take tace mata tana lafiya Alhamdulillah,

"Ya k'afafun da Sauk'i dai ko" cike da nuna kulawa tay tambayar tare da d'an kallo k'afafun Hajiyar, nan
ma ce mata tayi da Sauk'i sosae da taimakon sandar ta ba inda bata zuwa, "Ma sha Allah haka muke so,
Allah ya k'ara maki lafiya da nisan kwana our Heartbeat" Hajiya na yar dariya ta amsa da Amin,

"Sai muka ji kira kina neman mu, nifa har hankali na ya d'an tashi kawae don kin ce ba komai sai Alkhairi
yasa na d'an kwantar da hankali na amman duk da hakan naji na k'agara in zo in ji miye" still da fara'a a
fuskar Hajiya tace mata in sha Allah Alkhairin ne kaman yadda ta fad'a masu tace to ta fara fad'a mata
kafin Yayan ya dawo, tace "Saurin mi kike, ki bari ya dawo kaman yadda kuka zo tare sai muyi Maganar
tare ko yau zaku koma ne?" tana yar dariya tace mata a'a kawai ta k'osa taji ne nan zasu yi mata
Weekend,

"Shine don rowa ko a taho man da d'aya daga cikin mazajen nawa ko k'awayen nawa koma a kwaso
man su duka" dariya ta saka da yar kakkausar muryarta tace "Wllh kuma sun so biyo ni k'in tahowa nayi
da kowa hakanan kai ta yawo da yaro tunda saida na je Abuja sannan muka taho nan" Hajiya tace to
miye tunda ba'a k'afa za'ai yawon ba tace a'a in suna so in akai masu hutu sa zo,

"Amman dai nasan banda uwar ji da kai aka nuna ana son zuwa ko" still dariya take tace "Wai Farha,
aikuwa kaman kin sani ko in gaida ki bata ce ba" ta6e baki Hajiya tay "taji da shi, nima ba son tace tana
gaida nin nike ba tunda inada wanda suke gaida nin ta rik'e kayanta ban so" haka suka cigaba da hira
cike da raha. Duk wannan abun Fatuu na Makaranta bata dawo ba daga can ma Hostel zata wuce sai
Fauzy ta shirya zasu taho tare a sauketa a gidan Aunty Mareeya sai ta dawo tunda akai Break dama ta
kira Tk ta sanar dashi don Kada yazo in an tashin shima kawai sai ya wuce cikin gari bai ma san su
Senator d'in sun zo ba, tare da Hajiya Maryam d'in suka tafi Masallaci sallar juma'a, bayan an gama nan
fa aka fara tururuwar zuwa gaishe dasu da yake da yawa sun santa wasu kuma sai sun zo gaida Hajiyar
suke sanin wacece wasu ma ba sai an fad'a masu ba tunda ga kama nan, bayan sun dawo ne suka zauna
cin Abinci, suna cikin ci Senator ya dawo ya nufo Dining area d'in Hajiya tace ya zauna su ci Abinci yana
murmushi yace mata sunci Abinci tare da Governor, d'an 6ata fuska tay tace to itama sai yaci nata tunda
don su akai yana yar dariya yace tuba yake zai ci ba sai ta 6ata rai ba yaja kujera ya zauna duk sukai
dariya,
Bayan sun gama cin Abincin suka dawo parlor nan Hajiya Maryam tace mata tunda Yayan ya dawo sai ta
fad'a masu abunda yasa ta buk'aci ganin su, numfasawa Hajiya tay ta gyara zaman glass d'in fuskarta
sannan ta fara Magana a nutse "Farko dai muyi ma Annabi salati" gaba d'aya suka amsa da sallallahu
alaihi wa sallam, bayan kowa yayi taci gaba "dalilin kiran ku abu ne ya taso wanda dole kuna da buk'atar
sani ko ba don komai ba don halin rayuwa, ta wata fuskar ba lalle ku kalle shi a matsayin abun Alkhairi
ba amman ina fatan ku natsu kuyi amfani da hankalin ku ku kar6e shi a matsayin Alkhairin domin duk
abunda kaga Allah yayi to mai kyau ne" dakatawa tay tana maida numfashi duk sun natsu suna
sauraronta Hajiya Maryam na gefen ta yayin da Senator ke facing d'in su acan d'ayan bangaren, Maganar
da tayi yasa duk suka k'osa su ji miye abun da take son sanar da su d'in, kasa hak'uri Hajiya Maryam tay
tace "muna jin ki Hajjaju" sauke yar ajiyar zuciya Hajiya tay ta d'aura "Haisam ne yayi aure, kuma yanzu
haka da nike maku magana Matar tashi na zaune a gidan nan acan part d'in nashi" har saida Hajiya
Maryam ta d'an zabura ta d'ago sosae idon ta akan Hajiya da alamun d'aurewar kai tace "Mi kike fad'a
haka Hajjaju, Wane Haisam d'in yayi AURE!!!" tace mata wane Haisam ta sani banda d'an su, da tsananin
mamaki akan fuskar ta tace "To ni ban gane mi kike nufi da yayi aure ba, ai dama duk mun san da yayi
aure ko" d'an ta6e baki Hajiya tay kafin tace "dana ce yayi aure baki ji nace Matar na a cikin gidan nan
ba, ko dama nan yake zaune da Matar tashi da kuka san ya aura?" da alama bakunan kowannen su ya
mutu, shi dai Senator bin su da ido kawai yake ya jingine bayan shi da kujera yatsun hannun shi na had'e
cikin na juna, Bayanin Yadda Al'amarin ya kasance Hajiya ta shiga yi masu tiryan tiryan har ta gama ba
wanda ya katse ta sannan furiously Hajiya Maryam tace "kenan don uban shi har ya isa yayi aure without
our Knowledge, Saboda bamu da amfani a wurin shi bai d'auke mu da daraja ba ko mi!!!" a tsananin
fusace tayi Maganar har huci take, kallon Senator tay tace "Yaya kana ji fa, wai yaron nan har ya kai yayi
aure bada sanin mu ba!" d'an girgiza kai kawai yay still bai yi magana ba, "ke kuma Hajjaju ya aikata
wannan d'anyen aikin har ki goya mashi baya kisa ya zauna da ita, tunda matsayin taimakon ta yayi to
miyasa bazai saketan ba zaki bashi dama suci gaba da zama" a fusace idanunta akan Hajiya tay Maganar,
Hajiya data kwa6e fuska tace "to miye amfanin sakin nata tunda abu ya shiga tsakanin su har rabo ya
shiga tsakani...." A zafafe Hajiya Maryam ta katse ta don da ta ambaci rabo tamkar ta watsa mata ruwan
zafi taji cikin k'unar zuciya tace "Don Allah ki daina wannan Maganar Hajjaju, wane rabo ba kince ya zube
ba to cigaba da zama da itan na minene???"

"Amman dai kinsan in aka saketa ai ba ai mata Adalci ba, da ya aure tan ai matsayin zai taimaka mata
akai dashi ba'a yi dashi wani abu zai shiga tsakanin su ba ko, to tunda har hakan ya kasance sai a
rungumi Al'amarin ai fatan ya zama Alkhairi ta yuwu dama Allah ya k'addara auren ba don su rabu bane"
girgiza kai Hajiya Maryam ta shiga yi tana cigaba da yin huci can tace "Impossible wllh, bazai cigaba da
zama da ita ba, duka yaushe yay Aure da za'a ce wai har ya k'ara, k'arin ma na wulakanci da kaskanci,
dole mu nuna mashi bashi ke iko da kan shi ba akwae masu iko dashi da zai je yayi gaban kan shi, in ba
iskanci ba da ya raina mutane a ina na ta6a jin irin wannan taimakon" idanunta har sun sauya kala tsabar
6acin rai, kallon Senator tay "Yaya kana jin rainin wayau ko, dole ma a raba su wllh kawai a kira shi ya
saketa!!!" tana rufe baki Fatuu ta sawo kai cikin parlon da sallama tana sanye da jallabiya ta yafa veil
d'inta duk suka maida idanun su kanta, nan take ta ja ta tsaya tana bin su da ido itama, da hannu Hajiya
tay mata alamar ta k'araso ta nufe su a d'arare don kuwa duk ta gane su, tana zuwa bakin kujerun ta
toge duk tasha jinin jikin ta ganin yadda suke bin ta da ido ba kamar Hajiya Maryam wadda bacin rai ke
kwance k'arara akan fuskarta, Hajiya ce tace "ki k'araso mana Fateema" shiga tay duk ta kame kanta,
nuna mata kujera Hajiya tay alamar ta zauna maimakon ta zauna samanta sai ta duk'e saman carpet
daga d'an nesa da Hajiyar, fuska a sake tace "an dawo?" Kai ta d'aga mata,

"amman ya akai baki shigo tun d'azu kin ci Abinci ba?" Cikin rawar murya tace "a..ai yanzu na dawo, na
tsaya a Hostel ne wurin Fauzy mun yi Assignment" da k'yar ta k'arasa sakamakon mugun kallon da Hajiya
Maryam ke jefa mata don kuwa ta santa tasan itace Matar Haisam d'in, tuni zuciyarta ta hau bugu da
k'arfi da k'arfi, kai Hajiya ta jinjina sai kuma ta sake cewa "baki gaida bak'i ba to, kin gane su?" Kai ta
d'aga mata alamar eh ta kalli Hajiya Maryam cikin rawar murya ta gaida ta tay mata banza, juyawa tay
kan Senator dake ta kallon ta shima ta gaida shi ya jinjina mata kai kawai, juyowa tay kan Hajiya Maryam
ta k'ara gaishe da ita aikuwa ta zabga wani uban tsoki ta mik'e ta nufi hanyar barin Parlon a fusace da
sauri Fatuu ta fara k'ok'arin matsawa saidai ko kafin ta bata hanya ta cimmata aikuwa ta ham6are ta
gefe ta wuce Fatun ta bugi kujera sosae aikuwa nan take ta fashe da kuka don ba K'aramin buguwa tayi
ba, yamutsa fuska Hajiya tayi ta bi Hajiya Maryam d'in da kallo har ta shige Corridor sannan ta girgiza kai
ta maido idon kan Fatuu ta mik'a mata hannu alamar ta matso ta jawo jiki tana cigaba da yin kuka tana
gogewa da gyalen jallabiyar ta da ya zame daga saman kan, rarrashinta ta shiga yi tana bata hak'uri
hannun ta guda a saman shoulder d'inta ta d'agota ta zaunar da ita akan kujerar kusa da ita tana cigaba
da rarrashin ta, tana cikin goge k'wallan ta kai idonta kan Senator suka had'a ido kawai sai gani tay yay
mata alamar tazo da kan shi, dakatawa tay tana kallon shi ya d'aga hannu ya k'ara kiranta Hajiya da ta
gani tace taje ana kiranta ta mik'e a d'arare ta nufe shi, bayan ta isa gaban shi tana k'ok'arin zama akan
carpet ya nuna mata kujerar kusa da shi yace ta zauna, zama tay tana cigaba da goge Fuskar ta tana yar
ajiyar zuciya, a nutse cike da dattako ya fara magana,

"Kiyi hak'uri kin ji, ranta ne a 6ace shiyasa tay maki hakan amman Kada ya dame ki, nasan ba ki rasa
sanin cewa in rai ya 6aci mutum na iya aikata komai ko?" Kai ta d'an jinjina mashi, d'an murmushi yayi
"Good, a wani School kike ne?" Still muryar ta rawa take don wani irin kwarjini ne dashi ta bashi amsa,
jinjina kai yay "da kyau, kinyi nisa a Karatun ne?" tace "Eh ina aji biyu kuma mun kusa yin Exam" nan ma
kan ya jinjina yace "sai ku shiga aji ukku kenan, ai kaman daga nan ma zaku gama ko don nasan kaman
karatun 3 years ne" kai ta d'aga mashi a sanyaye tace eh, "kice watarana in bani lafiya za'ai man Allura
kenan, koma har kin iya yanzu?" ya d'an bud'a mata ido sak irin yadda Haisam ke yi dabarbarcewa tay
don bata tsammaci ganin hakan daga gare shi ba tace eh ta iya, wani kallo yay mata irin na baka yarda
da Mutum ba yace "kai, ki fad'a man gaskiya fa, ko don Kada ince baki da k'ok'ari kika ce hakan" da sauri
tace "Allah da gaske nike na iya harda sa drip ma da d'inki" jinjina kai yay yana murmushi yace "kice
Daughter d'in nawa mai k'ok'ari ce kenan" d'an waro ido tay baki a d'an bud'e take kallon shi ya d'age
mata gira yace ko bata da k'ok'arin da sauri tace tana da shi, kai ya jinjina taji yace taje taci Abincin da
sauri tace to ta mik'e ta nufi hanyar barin cikin parlon duk suka bita da ido Hajiya na d'an murmushi
dama tunda suke Magana dashi take kallon su tana murmushi, Ajiyar zuciya ya sauke ya kai hannu ya
shafi fuskar shi yana kallon Hajiya yace "She's so cute" Hajiya dake murmushi tace mashi haka take sai
ma ya zauna da ita tana da dad'in zama sosae, nan ta shiga bashi labarin rayuwar da sukai da Haisam a
baya, Maimakon ta shiga Kitchen d'aukko Abincin sai ta zille ta bi ta kopar baya ta fuce, bata bi ta
6angaren da d'akin Hajiya yake ba tabi ta d'ayan 6angaren tana tafiya cikin sauri ta d'an d'age kasan
rigarta tana yi tana waigen bayanta ta nufi part d'in su.........

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2068*

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.........Har tuntu6e take yi tsabar sauri, tana zuwa part d'in su ta shiga parlor ta wuce Bedroom, tana
shiga ta maida kopa ta k'ulle harda saka Key ta juya da gudu ta nufi gado ta Fad'a sai faman numfarfashi
take ta zaro ido hannuwan ta har d'an kerma suke sai tuno abunda ya faru take Fuskar Hajiya Maryam
na mata gizo, tafin hannunta ta kai ta rufe baki tasa Kuka, Sosae Senator yaji Fatuu ta burge shi da Hajiya
na bashi Labarin ta da Haisam Fuskar shi d'auke da Murmushi, suna nan har aka yi La'asar ya tashi don
yaje Masallaci yace mata daga can zai wuce G.r.a ya d'an huta, fuskar ta da murmushi tace to ba ga
d'akinta ba in ya dawo ya kwanta ya huta yana dariya yace mata to ta bari zai zo ya kwana akan gadon
nata itama dariyar take ta mik'e don taje tayi sallar itama, Lokacin da ta shiga cikin d'akin nata anan ta
iske Hajiya Maryam aciki pacing up and down sam ta kasa zama tun d'azu abunda take kenan, sai ta
zauna sai ta mik'e ranta a tsananin 6ace, Hajiya na shigowa suka had'a ido da ita ba tare data ce mata
komai ba ta nufi hanyar toilet, Alwala tayo ta fito ta nufi cikin d'akin, saida ta shimfid'a abun salla sannan
ta kai idonta kan Hajiya Maryam da ta zauna a bakin gado k'afar ta d'aya akan d'aya idon ta na kallon
wuri guda ta cije le6en ta na k'asa tana d'an jinjina kai, ce mata tay bata ji an kira salla bane ba tare data
kalle ta ba tace taji zatayi, saida Hajiya ta fara yin Salla sannan ta mik'e ta nufi Toilet, ita ta fara tashi
bayan sun gama ta cire Hijab d'in jikinta ta aje a gefen gado ta koma ta zauna kaman yadda take d'azun
sai faman d'an jijjiga jiki take tsananin bacin rai kwance akan fuskar ta, bayan Hajiya ta shafa Addu'a ta
juyo ta kalleta na d'an wani lokaci ta d'an girgiza kai, tasan halin ta tana da d'aukar zafi sosae sam bata
6oye fushi,

a nutse ta fara mata magana "Yanzu Maryam abunda kika aikata ma Yarinyar nan daidai ne, ita miye
laifin ta a ciki ne, kusan fa ita akai ma ba daidai ba ma, an aureta bada sanin ta ba kuma sannan yazo ya
hakke mata tunda ita bata san da ya aureta ba abu ya kai ga har da samun ciki yazo kuma ya 6are wanda
hakan yasa ta a mawuyacin hali, in rai ya 6aci ai bai kamata hankali ya gushe ba sai a bi komai a sannu
asa tunani, komai ki ka ga ya faru to dama can haka Allah ya k'addara, don haka sai mu d'auka dama
Allah ya k'addaro Aure tsakanin su" Tunda Hajiyar ta fara Magana bata juyo ta kalleta ba sai da tay
Maganar k'arshe sannan ta juya a zafafe tace "Pls Hajjaju stop saying that, komai sai ace kaddara, Yes an
san komae sai Allah ya amince yake Faruwa amman harda sa kai, don uban shi in son taimaka mata yake
ai akwae hanyoyi da yawa da zai yi hakan, Why not yayi amfani da kud'i akwai abunda basu yi bane balle
kuma su da suke yan k'auye ma tuni zai sa a fasa yi mata auren in yay amfani dasu, kuma ma wai miye
nashi na damuwa da wanda zata auran kowa ai da kalar k'addarar sa, watak'il in ta aure shi ya canza
amman Saboda ya isa da kan shi shine yay gaban kan shi shiga isasshe ko, to zamu nuna mashi haihuwar
shi akai ba a komae yake da iko da kan shi ba" tana huci ta k'arasa Maganar, d'an guntun murmushi
Hajiya tay "kinga dae kenan Magana ta na kan hanya, kince kowa da kaddarar sa to suma hakan
kaddarar su ce kenan shiyasa komai ya juye hakan sai kowa ya rungumi Al'amarin a matsayin hakan"
wani kallo take bin Hajiya dashi ta yamutsa fuska cikin k'unar rai tace "Hajjaju na fahimci goya mashi
baya kike shiyasa ma har ya samu k'warin gwuiwar cigaba da zama da ita, haba! ta ya zaki goyi bayan
wannan kaskantaccen Auren, Auren wulakanci, in ma k'ara Auren zai yi ai wannan ba class d'in shi bace
wllh, kuma ba kowa za'a wulakanta ba face Fanan taya ma za'a had'a ta kishi da wancan abun" sai huci
take tayi mitsi mitsi da idanu, d'an murmushi Hajiya tay idonta akanta tace mata ba mace bace ita
Fateemar kuma miye aibunta, d'an jim tay fuska a yamutse tana ma Hajiya kallo irin na baka zaci jin
Magana daga bakin mutum ba,

"Hajjaju wato na lura dae kin za6i faranta ma bare fiye da naki ko, kin sani matuk'ar auren nan aka ce ya
d'ore ba wanda zai cutu irin Fanan, don Allah duka yaushe aka yi auren nasu da za'a ce har an yi mata
kishiya, da mi zata ji ne da damuwar lalurar dake tare da ita ko kuwa da wannan damuwar da ake neman
k'ara mata, wai ko don cikin da ta samu ne yasa kike goyon bayan auren, Saboda ance Fanan nada lalura
ai ba yana nufin bazata haihu ba, tunda anata kokarin nema mata magani sai a bari zuwa wani lokaci aga
in bata haihu ba sannan ai tunanin auro wata, kuma shi in ba don ya nuna irin halin nasu na maza ba da
ba yan goyo bane ba har alk'awari yayi mata zai zauna da ita a halin da take ciki koda kuwa bata haihu ba
shine tun ba'a je ko ina ba zai watsa mata k'asa a ido ya nemi tarwatsa mata zuciya wato ta mutu ma shi
ba damuwar shi bane, to wllh bazan zuba ido ta cutu ba Saboda wata kaskantatta can" tana kaiwa
k'arshen Maganar ta kai hannu ta warto wayar ta ta mik'e, har ta nufi hanyar k'opa sai kuma ta dakata ta
juyo ta kalli Hajiya data bita da ido ta d'an sassauta d'aure fuskar da tay tace mata sun gama Maganar
zata fita, d'an murmushi Hajiya tay ta sani duk irin zafin zuciyar ta mai d'a'a ce a gareta yanzu ma tasan
Saboda tsoron abunda zai iya faruwa da Fanan yasa ta zauna tana ta mata Magana cikin 6acin rai kuma
bata d'auki hakan a wani abu ba don ta san yadda soyayyar d'a da Mahaifi take, kai ta d'aga mata alamar
sun gaman ta juya ta nufi kofa, cikin nuna ma kopar k'arfi ta bud'eta ta fuce,

Kuka Fatuu tasha har ta gaji tay shiru don kanta, kiran sallar la'asar ya tada ita taje tayo Alwala tazo ta
kabbara salla, bayan ta gama zaune tay kan abun sallar ta langa6ar da kanta jikin gado ta shiga duniyar
tunani. Hajiya Maryam na fitowa daga d'akin Hajiya Visitor room ta nufa, tana shiga ta d'aga wayarta
tana k'ok'arin yin kira ba tare data zauna ba, d'an kai da komowa ta fara lokacin da wayar da ta kira ta
fara ringing , Haisam zaune kan kujera a cikin d'akin da yake aikin injiniyancin shi kira ya shigo wayar shi,
hannu ya kai saman desk d'in gaban shi ya d'aukko wayar, bin screen d'in yayi da ido ganin mai kiran
lokaci guda ya yanke ba lafiya tasa ta kira shi ba ba kamar da yake dare ne kuma yasan tasan lokacin da
suke ciki, shima abu ne ya ishe shi bacci ya k'aurace mashi yasa shi zuwa wurin yay zaune yayin da Fanan
ke d'aki tana bacci, saida kiran ya kusa yankewa yay picking ya kai wayar kunne, sallama yayi mata tayi
mashi banza cikin cool voice d'in shi ya gaida ita aikuwa kaman tana jira a fusace tace "Ka rik'e gaisuwar
ka ban so, ai bamu da girman da zaka gaishe da ni tunda kai isashshe ne ka kai kayi gaban kanka, ashe
Haisam baka da Mutunci ban sani ba! mu zaka wulakanta ka nuna bamu kai ba a wurin ka, kai ka Haifi
kan ka ne ko mu muka haife ka da har zakai Aure ba tare da sanin mu ba, da izinin wa kaje kai auren???"
Shiru yay bai da niyyar tanka mata aikuwa hakan ya k'ara hasala ta cikin daka tsawa tace "bazaka bud'e
baki kai man Magana ba don ubanka" d'an lumshe ido yay ya bud'e, in ba ya manta ba tunda yake ba'a
ta6a zagin shi haka ba, slowly ya bata hak'uri yace yayi ne don taimako, a fusace tace "then what are u
waiting for da baka saketa ba kaman yadda kuka tsaran? Mi ya zaunar da ita" shirun ya k'ara yi saida
tace bai jita bane sannan yace "Hajiya ce ta hana"

"Hajiya ce zata zauna da ita ko kai" d'an jimm yay sai kuma yace "I can't argue with her" shiru tay cikin
ranta ta fara tunanin kenan ba don Hajiya ba zai saki yarinyar ne, d'an sassauta murya tay tace mashi
shikenan zata yi Magana da Hajiyar he should be expecting her call kowane lokaci don ya saki Yarinyar,
amsa mata yay da toh tace tasan Fanan bata sani ba to Kada ya sake ya bari ta samu labarin har zuwa
lokacin da zai sake ta nan ma da toh ya amsa mata tay mashi sai da Safe ta kashe Wayar, bin wayar yay
da kallo tun bayan daya cireta daga kunnan shi, can yay sigh ya fara latsa ta na d'an wani lokaci ya
dakata ya zuba ma Screen ido kaman mai kallon wani abu...,

tana ta zaune a wurin cikin duniyar tunani, a hankali take kai hannu tana goge yar kwallan dake zubo
mata daga cikin idanuwan ta da har sun d'an kumbura, wayar tace ta fara ringing ta d'aga kai ta kallo ta a
saman gadon, ganin zata iya jawo ta yasa ta kai hannu ta jawo tan ta kalli screen d'in, Abbas ne mai kiran
nata har saida ta d'an ji sanyi dama duk yau bai kirata ba, d'aga kiran tay ta kara wayar a kunne muryar
ta can k'asa tay mashi sallama, bayan ya amsa ta gaishe dashi ya amsa daga haka tay shiru, jin yanayin
muryar ta yasa shi tambayar ta lafiya nan ma tayi shiru, ce mata yay ta fad'a mashi inda matsala cikin
rawar murya ta fara fad'i mashi duk abunda ya faru, sosae Muryar Abbas ta bayyana rashin jin dad'in
abunda ya farun ya shiga bata hak'uri daga baya ya tambaye ta game da reaction d'in Senator nan ta
gaya mashi komae tana gamawa ya furta "Alhamdulillah, dama nasan ta 6angaren shi ba za'a samu wata
matsala ba, itama Momy Maryam d'in kawae tana taya d'iyar ta kishi ne ba wani abu ba, so kar kisa
damuwa a ranki in sha Allah komai zai daidai ta na d'an lokaci kad'an ne" a hankali ta amsa mashi da to,

"Yanzu kin ci Abincin ne?" D'an girgiza kai tay tace mashi a'a,

"Ya zaki sa damuwa har ta hana ki cin Abinci hakan ai sai wani ciwon ya kama ki, ba wani Abincin da zaki
ci ne?" bashi amsa tay da eh tace amman bari taje ta dafa indomie yace ta d'an jira ba sai ta dafa ba, har
zai cutting kiran sai kuma taji yace bata tambaye shi Mijin ta ba, tura baki tay kaman ya gani yay yar
dariya yace koda yake ai yanzu tafi shi kusa da shi daga haka ya katse, wayar na ruk'e a hannunta ta
maida kan ta jingina da gadon kaman yadda take ada ta runtse idanu ta sake fad'awa duniyar tunani
wanda duk na Haisam ne, gama wayar su da Abbas bada jimawa ba aka k'wank'wasa kopa ta bud'e
idanunta ta kallo kopar zuciyar ta na harbawa da sauri da sauri, mik'ewa tay a d'arare ta nufe ta hannun
ta har yar rawa yake da zata bud'e, tana bud'ewa suka had'a ido da Saude tana mata murmushi itama ta
k'ak'alo d'an murmushin tayi mata a sanyaye ta gaishe da ita, hannu ta kai ta kamo hannunta guda suka
nufo cikin parlon, akan kujera ta zaunar da ita itama ta zauna nan ta fara lallashin ta tace ita bata ma san
abunda ke Faruwa ba don tana baya sai yanzu da aka kira ta a waya ai da tun d'azun ta kawo mata
Abincin kuma itama ai data kirata sai tazo ta kawo mata amman zama da yunwar ga damuwa ai sai suyi
mata illa, tasata gaba Saude tay saida tasa taci Abincin sosae daga baya ta k'ara kwantar mata da hankali
kafin ta tafi. Bayan Hajiya Maryam ta yi waya da Haisam a bakin gadon cikin d'akin ta zauna hannunta
ruk'e da wayar ta d'aura ha6arta saman shi, tunanin ta yadda zata 6ullo ma Hajiya har ta amince a saki
Fatuu ta shiga yi, ta d'an d'auki lokaci a haka kafin ta idasa hayewa saman gadon ta kwanta da tunanin
zata yi mata Magana anjima. Da daddare bayan kowa yayi shirin kwanciya Hajiya Maryam ta nufi d'akin
Hajiya ta shiga da sallama Hajiya dake zaune a bakin gado sanye da kayan bacci idanunta na sanye cikin
glasses tana duba wayarta ta amsa mata ta nufo ta, a bakin gadon daga d'an gefe ta zauna tayi mata
sannu da hutawa da d'an murmushi Hajiya data d'ago kai ta amsa mata, shiru suka d'an yi Hajiyar ta
maida idon ta akan Wayar ita kuma tana kallon k'asa, juyowa tay ta kalli Hajiya tace mata dama Magana
take son su yi ne ta d'ago tare da jinjina mata kai idonta a kanta alamar ita take jira,
"Mun yi Magana da Haisam ya fad'a man ke kika hana ya saki Yarinyar can, kinga kenan shima ba wai
son zaman yake da ita ba kawai yayi maki biyayya ne don haka ni ina ganin tunda shine mai zama da ita
kuma ba so yake ba sai ki bashi dama ya rabu da ita hankalin kowa ya kwanta" d'an murmushin dattako
Hajiyar tay jin abunda aka ce Haisam d'in yace, gyara zaman glass d'inta tay idonta akan Hajiya Maryam
a nutse ta fara magana "Kaman yadda kika ce biyayya yay man yaci gaba da zama da ita to kema ina son
kiman biyayya ki bi yadda nike so, ki yi masu Fatan Alkhairi a auren shikenan komai ya wuce" wani kallo
take bin ta dashi baki bud'e alamar Al'ajabin Maganar tata rai 6ace tace "to wai Hajjaju akan mi zaki
mashi dole ya zauna da ita ne, ya aureta don taimako da nufin zai saketa sai a sa ya saketan barin shi ya
ci gaba da zama da ita ba komai zai ja ba sai 6acin rai" girgiza kai Hajiya ta fara yi "Ba zai rabu da ita ba
Maryam dole yaci gaba da zama da ita, in kece ko Fanan a matsayin ta bazan so abunda kike so mata ba"
ta k'are Maganar tana girgiza kai bakinta a kwa6e, yarfa hannu tay ta yamutsa fuska tamkar zata saka
kuka cikin breaking voice tace "Wai Hajjaju ya kika za6i faranta ma bare ne fiye da naki, kin san idan
Fanan ta samu labarin nan ba K'aramin mawuyacin hali zata shiga ba, dame zata ji don Allah ko so kike
zuciyarta tay bursting ne, sai nike ganin kaman kin fi damuwa da ita yarinyar ma fiye da Fanan, in don
haihuwa ne a ba Fanan d'in time mana kaman yadda nace d'azun duka ai ba dad'ewa sukai da yin auren
ba ko" shiru Hajiya ta d'anyi still idanunta na akan ta sai faman huci Hajiya Maryam din take ta gumtse
baki idanunta sun Kad'a da gani kiris ya rage ta saka kuka, cikin kwantar da murya Hajiya tace "idan aka
zo Maganar Adalci Maryam baka duba bare ko naka indai Adalcin tsakani da Allah za'ai, koda Fateema
take 6are ai itama tana da dangi kuma suna son ta suna son farincikin ta, sannan Maganar halin da
Fanan zata iya shiga ita ai Musulma ce kuma inada yak'inin tana da cikakken imani hakan kuma na nufin
ta yadda da k'addara mai kyau ko akasin hakan don haka in sha Allahu ina sa ran zata rungumi hakan
matsayin k'addara kaman yadda ta rungumi ta lalurar ta ake ta neman Magani" Kuka ne ya taho mata
tace "Hajiya kar azo ai dana sani, na fad'i maki har Alk'awari fa yayi ma Fanan kan bazai k'ara aure ba
koda bata haihu ba kuma akan hakan suke zaune in taji ya k'ara auren nan har matar ta samu ciki mi kike
tunanin zai iya biyo baya don Allah, dama kuma ga yanayin ta" cewa Hajiya tay in sha Allahu ba abunda
zai faru kuma tasan lokacin da yay mata Alk'awarin ya riga ya auri Fatuu ne don haka shi yasan yadda zai
rarrashe ta, a k'arshe ta tabbatar mata da indai ba yarinyar ce tace bata son zama dashi ba to wllh ba zai
saketa ba, mik'ewa tay zumbur ta nufi hanyar fita Hajiya na kallonta ta kwa6e fuska.

Bayan ta koma d'aki kai da komowa ta shiga yi ta cize baki, abun ya matuk'ar d'aure mata kai yadda
Hajiya ta kafe, a tunanin ta koda cewa akai Fanan bata haihuwa kwata kwata Hajiya bazata matsa ayi
mata kishiya ba tunda abun na gida ne, dogon tunani ta shiga a k'arshe zuciyarta ta bata wani tunani kan
dalilin Kafewar Hajiyar, A daren Hajiya Maryam ta yanke komawa lagos a yadda take ji ba don dare yayi
ba da bazata ma kwana ba, a daren tayi duk wani cuku cukun tafiya saidae ba jirgin da zai je Lagos direct
washe gari sai dae Kano ta yanke tafiya Kano d'in daga can sai ta hau na Lagos, a ranar baccin ta ragagge
ne Saboda tsabar 6acin rai har gani tay daren yayi mata tsawo, Washe gari tana gama sallar Asuba ta hau
shiri duk da bada wuri jirgin nasu zai tashi ba, Misalin k'arfe takwas na safiyar ta kira Senator take sanar
dashi zancen komawar tata, tambayar dalilin tafiyar ta a yau yayi tace mashi hakanan ta canza shawara
yace da yaushe jirgin nasu zai tashi ta fad'a mashi, ce mata yay in ta shirya kafin ta wuce ta same shi a
G.r.a tace to, Misalin k'arfe tara da yan mintuna ta gama shirin ta tsaf cikin wani dandatsetsen leshi
ruwan Madara da fulawowi maroon da golden brown, ba K'aramin had'uwa leshin yay ba idanun kansu
zasu shaida maka tsadar shi don kuwa d'an dubu d'aruruwa ne, a da tazo da shirin fita taje wasu wurare
kafin ta koma, gyale da jaka da takalma maroon ta saka ta fiddo wasu sarka da yan kunne da yan hannu
na zinari ta saka ta fito a babbar macen ta, tana janye da d'an madaidaicin trolley d'in kayanta ta fito,
Bedroom d'in Hajiya ta wuce bayan ta tura K'opar da yar sallama ta shiga, ganin Hajiyar bata cikin d'akin
yasa ta kai idon ta wurin toilet nan ta gane tana ciki ta nufi bakin gado ta zauna, bada jimawa ba ta fito
idanunta suka sauka akan Hajiya Maryam d'in ta nufo gadon itama ta zauna, kallonta tay ta gaishe da ita
bayan ta amsa ganin tayi shiru yasa ta tambaye ta lafiya ta ganta cikin shiri da safe ko wani wuri zata ta
girgiza mata kai kafin tace zata koma ne, d'an jimm Hajiya tay sai kuma tay d'an guntun murmushi tace
"an 6ata maki rai shine kikai Fushi zaki tafi kenan" shiru bata ce mata komai ba idanunta na kallon k'asa,
Hajiya ta k'ara cewa "shikenan bazan hana ki tafiya ba Allah ya tsare, kin yi Breakfast ne?" Girgiza mata
kai tay tace in ta isa tayi ta gyad'a kai, d'an shiru sukai can ta mik'e ta kalli Hajiyar tace ta wuce, Addu'ar
Allah ya tsare ta k'ara yi mata ta kama trolley d'in ta juya, har ta kusa k'opa Hajiya ta kira sunanta ta
dakata ta juyo, "Kiji tsoron Allah, Kada soyayyar d'a ta tunzura ki kice zaki cutar da yarinyar can domin
duk abunda kai ma d'an wani kaima za'ai ma naka ne, idan ranki ya 6aci Kada ki bari hankalin ki ya gushe,
ki d'auki Al'amarin a matsayin Alkhairi sai kiga ya kasance hakan, tada hankalin ki shi zai taimaka wurin
faruwar abunda kike gudu, ki gaida man Mazajena da K'awaye na" d'an jimm tay tana kallon ta kaman
bazata tafin ba can ta furta mata ta gode ta juyo tana janye da trolley d'in ta fice,

Itama Fatuu a jiya bata yi wani baccin kirki ba wanda ta samu yake d'aukar ta ba wani mai nauyi bane
gashi cike da mafarkin abunda ya faru tsakanin ta da Hajiya Maryam, kiran sallar farko na Asuba ta farka
taje tayo Alwala, bayan ta fito ta zo ta kabbara raka'atanil fajr data gama ta d'aura da karatun Al'qur'ani
har lokacin sallar Asuba yayi, bayan ta gama yin sallar kwance tay akan prayer mat d'in cikin sa'a bacci ya
d'auketa, Misalin k'arfe tara saura ta farka jin jikinta duk ba dad'i yasa ta tafi toilet tayo wanka, bayan ta
fito ta shirya cikin riga da wando, wandon skin tight ne bak'i sai rigar ta kai mata har gwiwa tana da
gajeran hannuwa jikinta bak'i da fari ne, bata sa hula ba sai gashinta dake fake yayi tumm, bayan ta
gama gado ta koma ta zauna tay tsuru, tana jin yunwa amman fargabar fita take sai kawai ta kai hannu
ta d'auko wayar ta daga kan Bedside drawer ta fara dannata, bata dad'e da zama ba aka k'wank'wasa
kopar ranta ya bata k'ilan Saude ce amman duk da haka saida taji tsoron bud'ewa, bayan ta bud'e taga
Sauden ce suka gaisa harda ce mata tayi kyau inama Angonta na nan sai yafi ganin kyaun kwalliyar yar
dariya tayi tace ita ai ba wata kwalliya tayi ba, daga baya tace mata ta fito tayi Breakfast gashi can ta
kawo tace to, ce mata tayi ta fito suje taci a gabanta kaman jiya tay yar dariya tace mata zata ci Allah
sannan ta fito,

Hajiya Maryam na fitowa sukai kacibus da Saude data dawo daga part d'in su Fatuu, gaishe da ita tay ta
d'aga mata kai kawai ta mik'a mata trolley d'in tace ta biyo ta dashi, suna fitowa harabar gidan tay mata
nuni da parking space da hannunta tace ta kai shi can ta je ta kirawo mata Tk tace mashi ya jirata anan,
amsa mata da to Saude tay ta nufi parking space d'in tana tafiya tana waiwayen ta ganin ta nufi part d'in
su Fatuu, Har Fatuu taje dining area d'in ta tuna da bata d'aukko cup da sauran abunda zata buk'ata ba
ta juyo ta nufi Kitchen, hannunta ruk'e da plate da tea cup da spoon a saman shi ta fito zata koma dining,
tana fitowa daga corridor zatai kwanar dining area taji an turo kopar parlon da sauri ta kai idonta suka
shiga cikin na Hajiya Maryam, wani mummunan Fad'uwa gaban ta yay ba shiri ta saki abun hannunta
nan take cup d'in yay tsalle ya fad'o ya d'aki tile ya tarwatse, tsaye tay cak ta zaro idanu zuciyar ta na
wani irin harbawa ganin yadda Hajiya Maryam d'in ke jefa mata wani kallo fuskar ta ba d'igon annuri,
daurewa kawai Fatuu ke yi amman jikinta har ya fara rawa daga ta ciki a yadda take ji tamkar ta watsa da
gudu ta shige d'aki, cikin parlon ta k'araso tana tafiya a k'asaice ta tsaya a tsakiyar parlon, d'an d'aga
murya tay tace ma Fatun ta k'araso wurinta ne ta d'an girgiza mata kai kafin ta fara tahowa cikin parlon a
d'arare, a d'an nesa da ita ta tsaya murya na d'an rawa ta gaishe da ita tay mata banza still idanun ta na
akanta ba alamun sauk'i a cikin su, cike da yarinta ta Fatuu tay tunanin wai ko don bata ce mata ta zauna
ba yasa tay tsaye cike da k'arfin hali tace mata ta zauna aikuwa tamkar ta watsa mata wuta ta k'ank'ance
ido a fusace tace "Samun wuri! Wato Ni zaki kalla ki ce ma in zauna! daga gidan ku aka kawo kujerun ko
kuwa?" Da sauri ta girgiza mata kai a hankali tace tayi hak'uri....a zafafe ta amshe "Ke zan ce ma kiyi
hak'uri ki tattara ki bar gidan nan don kuwa bai dace da ke ba baki samu kar6uwa ba, idan kuwa kika k'i
to kuwa kin tattaro ma kan ki abunda bazaki iya d'auka ba, in ba ganganci irin naku ba k'auyawan
mutane ke ko a mafarki kin isa kiyi kishi da d'iyata balle kuma a zahiri, wato har kuna da k'warin gwuiwa
har haka ko? Fad'a man Asiri kukai ma shi don yaci gaba da zama dake ko??" a rud'e Fatuu ta hau girgiza
mata kai aikuwa ta daka mata wata uwar tsawa "K'arya kike! dole Asiri ku kai mashi shi da Hajiya shiyasa
har ta goyi bayan yaci gaba da zama dake" kuka Fatuu ta saka tana fad'in wllh su ba Asiri sukai masu ba
Hajiya ce tasa yaci gaba da zama da ita, wani kallon rashin Arzik'i take bin ta da shi tun daga sama har
k'asa, ada Haushin ta take ji yanzu kuwa abun sai ya juye zuwa tsana can ta buga wani uban tsoki ta
d'aga yatsa tana nunata tace "To zan baki shawara tun cikin Arzik'i ki fita daga rayuwar shi, kice baki son
cigaba da zama da shi idan ko ba haka ba to rayuwar ki zaki jefa a matsala don kuwa provided that am
alive d'iyata bazatai kishi da ke ba da kowa ma, idan har baki d'auki shawarata ba kika fita daga rayuwar
su ta lalama ba to zaki danasanin da har ki mutu bazaki daina ba don sai na salwantar da kaskantacciyar
rayuwar ki, ta yadda ko kallon gidan nan aka baki shawarar kiyi sai kin zagi wanda ya baki shawarar balle
ta kai ki ga cigaba da zama a cikin shi, kinsan Asirin ma mataki mataki ne iya nauyin jakar mutum iya
girman wanda za'ai mashi, if u wise enough nasan zaki abunda ya dace" daga haka ta juya, har tayi d'an
taku ta dakata ta juya ta kai hannu ta ruk'e kunnanta guda ta furta "idan kunne ya ji to gangar jiki ta
tsira!!!" daga haka ta nufi k'opa ta fuce, Fatuu na ganin ta fita ta juya da gudo ta nufi Bedroom, Lokacin
data fito bakin part d'in su a parking space ta hango Tk tsaye jikin Mota har ya saka trolley d'in nata ciki,
da yatsa tay mashi alamar ya fito da Motar ta tsaya a wurin, yana tsayar da Motar ta bud'e baya ta shiga
yaja suka fita su Officer na d'aga mata hannu a K'ok'arin su na su gaishe da ita don ta saba yi masu Alheri
bata ba Tk Umarnin ya tsaya ba hakan yasa ya wuce, Suna zuwa gab da gidan su Fatuu ta nuna gidan
tana tambayar Tk nan ne gidan su waccan yarinyar da aka kai gidan Hajiya ko yace mata eh, Umarnin ya
tsaya a gaban gidan ta bashi, bayan ya tsaya ta bud'e kopar ta fito tace mashi tana zuwa, cike da isa ta
nufi gidan Tk dake kallonta ta cikin glass ya girgiza kai a fili ya furta "Allah ya kad'e fitina", a bakin kopar
shiga cikin gidan ta tsaya tana bin tsakar gidan da yake wayam ba kowa da kallo, Sallama tayi shiru ba'a
amsa ba hakan yasa ta d'aga murya tace "ina masu gidan nan?" Amadu ne ya fito daga cikin d'akin shi
yana sanye da jallabiya, wani kallon rashin Arziki ta bi shi dashi shima kallonta yake don ya ganeta,
gaishe da ita yay bata amsa ba tace mashi ina take da alamun rashin Fahimta ya tambaye ta wa ya lura
da yanayin ta kaman ba Arzik'i, "Kai da waye a gidan?" Ta tambaya ta yamutsa fuska, kafin ya bata amsa
gwaggo ta fito daga cikin d'aki hannunta ruk'e da tsintsiya dama shara take shiyasa bata ji sallamar ta ba,
juyawa Hajiya Maryam tay ta kalli Gwaggo data tsaya bakin k'opa tana kallon su don ta lura kaman ba
lafiya ba,

"In k'araso ne?" Hajiya Maryam d'in ta tambaya tana kallon gwaggon shekeke, aje tsintsiyar da parker
gwaggo tay ta nufo su, daga gaban Hajiyar ta tsaya da k'ak'alallen murmushi don tana kallon Fuskar ta
tasan akwai matsala, gaishe da ita tay kaman bazata amsa ba sai kuma kaman an mata dole ta amsa
daga haka gwaggo tayi shiru, d'an matsowa gaba tay yadda gwaggon zata jita da kyau, cikin isa ta fara
Magana, "Mun ji abunda ya faru tsakanin d'an mu da jikar ki, to na zo inji cigaba da zaman su tare na
minene? Taimakon ta yay to don mi zaku goyi bayan su cigaba da zama ko baku san yana da Mata
bane?" Shiru gwaggo tay kanta k'asa abunda take ta fargaba game da Auren kenan don sarai tasan
wacece Hajiya Maryam, cigaba tay "in dai kunsan halacci to bai kamata ku goyi baya ba, tun farko
yakamata ace kun yi Magana akan ya saketa kaman yadda ku kai da shi, saidai kuma in dama akwae
wata a k'asa kuna so kuyi amfani da damar don cimma wata manufa, to idan dai hakane wannan ba
matsala bane ki fad'i man ko nawa kike so zan baki ta ruwan sanyi ki raba jikar ki da mijin Y'ata don bata
kai tayi kishi da ita ba balle har ta zame mata matsala!" Yar ajiyar zuciya gwaggo ta sauke cikin kwantar
da murya ta fara bata hak'uri tace ita wllh basu da wata manufa akan auren hasali ma itama bata goyi
bayan auren ba tun da farko kawae don abun ya juye ne kuma Hajiya ta nuna tana so, a zafafe ta katseta
da fad'in "tunda baki goyi baya ba sai kema ki nuna baki so, ba jikar ki bace ke kike da cikakken iko da
ita!" D'an jim gwaggo tay yanayin fuskar ta ya sauya a sanyaye tace "Kiyi Hak'uri, Hajiya tana da girma ne
a wuri na bazan iya musa mata ba" tamkar ta gaya mata magana taji a hasale tace "to kin mata biyayya
don tana so mu kuma sauran dangi yanzu bamu so ba muyi Na'am da auren ba don haka bazamu kar6e
ta ba sai ki maido abun ki in dai da gasken ba ki da wata manufa akan auren, bijire ma hakan daidai yake
da bijirema Farincikin kowannan ku, zan iya k'arar da duk wani abun da na Mallaka akan bijirema hakan
don kuwa ba zan ta6a zuba ido wata kaskantatta ta zama shamaki ga farincikin Y'ata, tana son Mijinta
shima kuma yana son ta don haka basu buk'atar wata ta shigo rayuwar su, a shawarce sai kiyi abunda ya
dace" ta k'are Maganar tana jinjina kai had'i da kanne ido,

ba K'aramin 6aci ran Amadu yay ba ganin yadda take ta gaya ma Mahaifiyar shi Magana daurewa kawai
yake yana danne zuciyar shi, tana zuwa ga6ar data kira Fatuu da Kaskantatta yaji bai iya jurewa ya matso
inda suke rai 6ace yace "Hajiya gaskiya ita ba kaskantatta bace, don tana talaka hakan ba yana nufin bata
da galihu ba, a wurin Ubangiji duk d'aya muke wanda yafi tsoron shi yafi bauta mashi shi ya fi ba wai mai
kud'i ba ko nasaba kawai mutane ne ke bambantawa, in Allah yayi mutum mai kud'i ba hakan na nufin
yafi son shi ba ko rayuwar shi tafi amfani ba haka talaka ma ba yana nufin Allah bai son shi ba ko
rayuwar shi bata da amfani, ki sani gaba d'ayan mu Allah yayi mu a yadda muke ne don mu bauta mashi
don haka gaba d'ayan mu rayuwar kowa talaka ko mai kud'i nada amfani, kuma Maganar aure ai bamu
muka sa ya aureta ba, hasali ma bamu san yadda akai ba saidai muka ji zai aureta balle kice ko dama da
niyya, sannan Maganar zaman su ma bamu muka rok'a ba tun farko shi ya k'i sakin ta aka zo kuma aka
buk'aci zasu ci gaba da zama tare Saboda biyayyar mu ga wadda ta buk'ata muka amince, in zaki ga laifin
mu kan hakan shi miyasa bazaki ga laifin shi ba da tun lokacin bai bijire ya nuna bazai cigaba da zama da
ita ba, mi yasa tun farko bai saketa ba kaman yadda akai dashi ba, Maganar hallaci kuma ai shi muka yi,
ya aureta don ya taimaketa daga baya kuma an buk'aci suci gaba da zama a tare in muka k'i ai kinga mun
yi butulci kenan amincewar da mukai kuma hallaci mu kai domin d'an halak shi yake maida Alkhairi da
Alkhairi, Yanzu tunda baku amince da auren ba duk miye abun zuwa da tada jijiyar wuya kusa ya sake ta
mana........! A fusace ta kai hannu zata wanka mashi mari ya goce Fuskar shi a tamke yana huci nan da
nan Fuskar shi tay jajir kaman an watsa jini abunka da Fari, itama Hajiya Maryam d'in huci take tana
mashi wani kallo mai cike da tsantsar 6acin rai zuciyarta tana boiling da burning a lokaci guda, cikin wata
irin murya ta nuna kanta da yatsa manuni tace "ni kake gaya ma magana haka!!!" D'an tura baki yay yace
"ni ba Magana na gaya maki ba saidai in ke kika d'auka haka amman duk abunda na fad'a ai daidai ne,
ikon baro gidan nata na a hannun ku sai ku sa ta......." Tsawa gwaggo ta kwatsa mashi cikin harshen
fulatanci tace ya bar wurin, wani kalan murmushin yaro bai san wuta ba sai ya taka Hajiya Maryam tayi
tace "ki k'yale shi, yay man duk rashin kunyar da ya iya ai gada yay tun daga tushe, kowa ya san baku da
kunya ai, bama iya hakan kuka tsaya ba gashi nan kun addabi K'asar mu" idonta da suka sauya kala akan
shi tay Maganar nan da nan idanun gwaggo suka ciko da k'walla, nuna shi tay da yatsa tace "Ni ba sa'ar
yin ka bace, kaff dangin ku ma ba sa'ar yi na, idan kaci gaba da yi man rashin kunya You will definitely
find ur self behind BARS....!!!" A tsiyace ta furta Kalmar Bars d'in ta cize hak'ora, Shiru yay bai ce komai
ba gwaggo na girgiza mashi kai alamar kar ya tanka sai huttai yake kamar wanda yay gudu da gani dai ba
k'aramar zuciya gare shi ba, juyawa tay kan gwaggo ta had'e yatsanta biyu suna making sound tace "Zan
yi komae don Farincikin Y'ata in kuma tabbatar bata samu wata matsala ba in kin so zaki iya yin hakan ga
Jikar ki......." Tana kaiwa nan ta juya cike da tafiyar isa ta nufi hanyar k'opa ta fice........

ASM Bk2069

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.........Tana fitowa daga cikin gidan tay ma Tk dake cikin Mota alama da hannunta nan take ya fahimci mi
hakan ke nufi ya bud'e kopar Motar da sauri ya fito, bud'e mata K'opar bayan yay tana zuwa ta shige ya
maida kopar ya rufe mata ya d'an d'age gira tare da bud'a ido ya koma yaja suka tafi, sai faman jinjina kai
take tana cije lower lip d'in ta tana d'an huci,

Tana fita Amadu ya matsa gaban gwaggo ganin yadda idanunta sukai ja shima har lokacin ran shi a 6ace
yake, kallon shi tay tace miyasa yayi abunda yayi ma Hajiya Maryam, cikin 6acin rai yace "to gwaggo sai
mu zuba mata ido taci mana mutunci son ranta, miye laifin mu a ciki ko kuwa don muna talakawa" yar
ajiyar zuciya ta sauke "kar ka manta ita d'in ko wacece, ko ba komai Mutanen nan nada k'ima da daraja a
idon mu hakan da kayi mata bai kamata ba don kamar rashin kunyan ne, duk abunda ta fad'a ta fad'a ne
cikin 6acin rai don tana ganin an mata ba daidai ba" dakata tay tana numfasawa idanunta na kallon gefe
shi kuma nashi na akan ta, cigaba tay "Wllh abunda nike ta fargabar faruwar shi kenan, nasan dole irin
hakan ya biyo baya shiyasa naso tun farko ace an tuntu6e su sun san da Maganar a nemi amincewar su
tukun...." Dakatawa ta k'ara yi ta d'age ido sama, ganin yadda duk ta damu yasa Amadu cewa "Kar ki
wani saka ma kan ki damuwa, tunda Hajiya tun farko ita ta nuna abar mata komai nasan in sha Allah
zatayi abunda ya dace komai na d'an lokaci ne zaki ga ya wuce" girgiza kai tay ba tare data kalle shi ba
tace dole tayi wani abu don ita bazata so silar hakan ace an samu rashin Fahimta ba yanzu na Hajiya
Maryam d'in aka gani ba'a san ya sauran Yan'uwan nashi suma zasu d'auki Al'amarin balle kuma ita
Matar tashi, tambayar ta yay to mi zata yi ta bashi amsa da abunda ya dace daga haka ta juya ta nufi
d'aki ya bi bayanta yana ce mata ta kwantar da hankalinta ba sai tace zatayi wani abu ba yasan Hajiya
bazata bari a cutar da Fatuu ba, tana shiga d'akin ta nufi gado ta zauna a baki Amadun ma ya shigo ya
zauna gefen ta yaci gaba da rarrashin ta kan kar tace zata yi wani abu don anzo anyi masu barazana su yi
Addu'a kawae, ce mashi tay to kawae daga baya da ya ga ta d'an saki ranta ya tashi ya tafi, Zaune tay a
wurin tana tunanin abunda ya kamata tayi don ganin Auren ya rabu, k'arshe ta yanke zuwa ta samu
Hajiya ta rok'e ta kawae a hak'ura da Auran, tana son ta kira Fatun taji halin da take ciki amman bata so
taji abunda hankalin ta zai k'ara tashi wata zuciyar ta raya mata tunda ita bata kira ta ba k'ilan ba abunda
ya faru da ita don Hajiya bazata bari ayi mata wani abu ba da wannan tunanin taji hankalin ta ya d'an
kwanta.

Bayan sun iso G.r.a sun shiga cikin gidan a gaban kopar shiga ya parker, bayan ta bud'e ta fito ta nufi ciki,
Parlon Senator ta wuce wanda Had'add'an gaske ne ya tsaru ta samu wuri ta zauna, ganin bai a ciki
yasata kiran shi ta sanar mashi ta iso, bada dad'ewa ba ya fito yana sanye da farar Jallabiya tun bayan
daya dawo daga Masallaci ya koma ya kwanta zuwanta ne yanzu ya taso shi, a kujerar gefen ta ya Zauna
Fuskar shi a sake ta gaishe dashi ya amsa daga haka tay shiru kanta a k'asa tana kallon Carpet 6acin rai
bayyane akan fuskar ta, tambayar ta yayi tayi breakfast ne tace mashi a'a sai ta isa yace bari dai a kawo
mata tayi anan, bata ce komai ba ya matsa can daga gefen kujerar inda landline take aje saman wani
table, kira yay ya bada Umarnin akawo Breakfast, after some minutes sai ga wani cook ya shigo hannun
shi ruk'e da babban tray dama aikin shi kenan girka ma Senator d'in Abinci in yazo bada iyalin shi ba, har
zai kai inda dining table yake Senator yace mashi ya kawo nan, gaishe da Hajiya Maryam yay ta amsa
k'asa k'asa ba tare da ta kalle shi ba ya d'aura a saman c-table Senator yace ya ja mata shi gabanta, saida
yayi mata Magana sannan ta fara ci shi kuma ya fara daddana wayar shi da ya fito da ita, bata wani ci
sosae ba ta cire hannunta ganin haka yasa Senator yi mata magana tace mashi ta k'oshi, k'ara kiran cook
d'in yay yazo ya kwashe kayan, shiru suka yi Senator na cigaba da danna wayar can ya d'ago ya ajiye ta
agefen shi yay yar ajiyar zuciya a nutse ya fara mata Magana yace miyasa zata tafi, kallon shi tay tace
mashi ba komai kawae ta canza ra'ayi ne, shiru yayi yana kallon ta da d'an murmushi ita kuma idanunta
na k'asa tana kallon Carpet har lokaci fuskar ta ba annuri,

cigaba yay "nasan don abunda ya faru ne, ina son ki kwantar da hankalin ki abi komai a sannu sannan ayi
fatan hakan ya zama Alkhairi kaman yadda Hajiya ta fad'a bamu san mi Allah ya 6oye a tattare da
Al'amarin ba" kallon shi tay cikin 6acin rai tace "Kenan kaima Yaya goyon bayan auren kake?" d'an
murmushi yay yace mata kawae yayi nazarin Maganar Hajiya ne shiyasa, Fuska a yamutse tace "Yanzu
shikenan ya nuna bamu da iko dashi ya yi gaban kan shi sai kuma a k'yale shi hakan Yaya ai cin Fuska ne,
gaskiya dole mu nuna mashi ba a komai yake da iko da kan shi ba kawai asa ya saketa" ta k'arasa tana
d'an Jujjuya kai, numfasawa yay yace "ni ina ganin hukuncin da Hajiya ta yanke akan shi ya nuna ana da
iko dashi, yaje yayi aure ba tare da sanin mu da niyyar zai saki Yarinyar kinga in aka sa ya sake ta shine
yay abunda ran shi ke so amman matsa mashi ya zauna da itan hakan zai sa dangin yarinyar su san ana
da iko dashi kuma mu ba k'ananun mutane bane, sakin ta kuma hakan gaskiya ina ganin zai zama
k'aranta" idanun ta ne suka ciko da k'walla cikin karyayyar murya ta fara fad'in gaskiya ita bata goyi
bayan yaci gaba da zama da ita ba duka yaushe yayi aure kuma in ma Auren zai k'ara wannan ai bata
dace da shi ba ba sa'ar auren shi bace, shiru Senator yay still da d'an murmushi akan Face d'in shi don
yasan dalilin da yasa duk take wad'annan abubuwan, rarrashin ta ya shiga yi yana nusar da ita aikuwa sai
tasa mashi kuka tana fad'in shikenan ba wanda zai yi tunanin halin da Fanan zata iya shiga duk sun goyi
bayan 6are sun za6i faranta mata da mi ake so Fanan taji ne ko don suna tunanin bazata haihu bane,
nuna mata yay bai ji dad'in wannan Maganar da tayi ba sam ai yayi tunanin Fanan ta su ce da ta haihu da
kar ta haihu hakan ba abun damuwa bane a gare su kuma don ance tana da matsala ai hakan ba yana
nufin bazata haihu ba kawai yana son ta gane shi Al'amarin irin wannan in Allah ya kawo kamata yay a
kar6a ai fatan ya zama Alkhairi ba kamar da Hajiya ta nuna tana so sai suyi mata biyayya su bi da Addu'a,
hak'uri ta bashi kan Maganar da ta yin ya k'ara lallashin ta daga baya sukai sallama ta mik'e shima ya
tashi don ya rakata. Bayan ya dawo inda ya tashi ya koma ya zauna ya d'auki wayar shi ya shiga kiran
Haisam, picking yay tare da yin yar sallama Mahaifin nashi ya amsa mashi, bayan ya gaida shi yace mashi
sun ji abunda ya aikata ya kyauta hakan ya nuna masu basu da amfani a wurin shi, hak'uri ya bashi yace
mashi yayi don taimako ne, ce mashi yay to miyasa ya k'i sakin ta kaman yadda akai dashi har abu ya
shiga tsakanin su, shiru yay bai ce mashi komai, sigh Senator yay yace mashi yana son ta kenan dama
shiyasa har hakan ta faru don yaci gaba da zama da ita, Slowly yace mashi bada niyya bane kuma Hajiya
ce tasa yaci gaba da zama da ita, d'an guntun murmushi Senator yay yace "Kenan baka son ta?" Shiru
Haisam d'in yay, da d'an d'aga murya yace ya bud'e baki yay mashi magana kaman yadda yake mashi bai
kira shi don yaja mashi aji ba, in bai son ta ya fad'i a raba su kowa ya huta, har saida Haisam d'in yay d'an
guntun murmushi jin abunda yace dama ya saba ce mashi hakan in yana jira yay mashi magana,
"Tunda Hajiya na so zan ci gaba da zama da ita" d'an ta6e baki Senator yay da murmushi irin na ka gane
Mutum ba gaskiya ya fad'a maka ba, "ita Daughter ka sanar da ita ne?" Ya tambaya yace mashi a'a,

"to kai k'ok'ari ka sanar da ita kasan yadda zaka kwantar mata da hankali don Momyn ku ta d'au zafi
sosae rashin tada hankalin ta shi zai sa ta kwantar da nata hankalin" amsa mashi yay da to, tambayar
yaushe zai dawo yayi yace sai ya samu time tunda bai dad'e da dawowa ba,

"Ok, amman kai k'ok'ari ka dawo da wuri kar ita kuma ta nan d'in a shiga hakkin ta, in ta gama Karatun
sai ka d'auketa kawai ta dawo nan" amsa mashi yay da to cike da tsokana yace "kai da alama ma sai ka
wuce ni, tun yanzu kayi biyu gaba sai ka cike biyun dama an ce kyan magaji ya zarta" murmushi mai d'an
sauti Haisam d'in yay shima Dad d'in nashi murmushin yake dama tamkar Abokai haka suke akwae
kyakkyawar fahimta a tsakanin su, ce mashi yay shikenan Haisam d'in yayi mashi godiya shi kuma ya sa
mashi Albarka sukai sallama.

Saude na shiga cikin parlon bayan ta kai trolley d'in suka yi kacibus da Hajiya ta shirya cikin doguwar riga
kanta sanye da hula, ganin ta nufi hanyar Dining yasa Saude ta bi bayanta don tay serving d'in ta
Breakfast, bayan ta zauna Saude na zuba mata ta tambayi ta kai ma Fateema tace mata eh tun d'azu ma
bayan ta dawo ne ta had'u da Momy Maryam shine ta bata trolley ta kai mata parking space, da d'an
murmushi Hajiya ta girgiza kai tace ta tafi kenan, d'an jimm Saude tay ranta ya bata ta fad'i mata inda
taga ta nufa don hankalin ta bai kwanta da zuwanta part d'in ba, fad'i mata tay cewa bata kaiga tafiya ba
lokacin da suka fita taga ta nufi part d'in su Fateema, Yanayin fuskar Hajiyar ne ya canza ta maimaita ta
je part d'in su Fateema to mi ya kaita, Saude tace itama bata sani ba, fara yin Breakfast d'in tayi Saude ta
tambayi akwae wani abu da zata yi mata, tambayar ta tayi ita tayi breakfast d'in ne tace a'a tace to ta je
tayi in ta gama ta zo zata rakata part d'in su Fateema ta amsa mata da to.

Tun bayan da Fatuu ta ruga ta shige cikin Bedroom ta fad'a kan gado tana kuka sosae, tana cikin kukan ta
fara bugun katifa da hannun ta a fili take fad'in "Ko ma mi akai man kai kaja man Ya Haisam! Baka damu
dani ba, ka tafi ka barni Saboda baka so na baka k'aunata..., ni kawai ka zo ka sake ni na hak'ura da kai,
na daina son ka, na daina......" Haka tay ta sambatu sai ta tashi zaune sai kuma ta koma ta fad'a saman
Katifar, ba K'aramin kuka ta sha ba daga baya ta sassauta yin kukan tayi lamo akan Katifa ta k'ura ma
wuri guda ido tana fitar da numfashi da sauri da sauri idanun ta sun yi jajur a ranta tana tunanin yadda
zatay Haisam ya saketa, tunanin ko ta kira gwaggo ta fad'i mata halin da take ciki tay wata zuciyar ta raya
mata hakan ba K'aramin tayar mata da hankali zai yi ba, tunanin Abbas tay shima ta raya tasan kota fad'i
mashi hak'uri zai bata, a k'arshe ta yanke kawai taje wurin Hajiya tace mata bata son Auren tasa ya
saketa tunda dama ai saida tace tana son cigaba da zama dashi sannan ta tare, tana haka aka turo kopar
Bedroom d'in tay zumbur ta tashi zaune idon ta akan kopar ta zaro su sam ta manta ta kulle Saboda a
yanayin da ta shigo, wani irin bugu da k'arfi zuciyar ta ta fara yi don a tunanin ta ko Hajiya Maryam d'in
ce ta dawo, sandar data ga an sako yasa hankalin ta fara kwanciya, shigowa Hajiya tay ta yafo mayafi
tana sanye da glass ta tsaya a bakin k'opar tana kallon Fatun, ganin haka yasa ta saukko daga saman
gadon ta zagayo inda take, daga gabanta ta tsaya cikin rawar murya ta gaishe da ita tay d'an murmushi
ta amsa kafin tace "ana nan ana ta shan kuka ko" sadda kanta tay k'asa bata ce komai ba Hajiyar tace
mata ta biyo ta ta juya, bin bayanta tay har lokacin kanta ba kallabi, cikin parlon suka shiga Saude na
zaune akan armchair Hajiya ta nufi L-shape ta zauna Fatuu na niyyar zama kan Carpet ta nuna mata daga
gefen ta tace ta zauna, bayan ta zauna ta sadda kan ta k'asa Hajiya ta fara magana, "Maryam tazo duk ta
firgita ko?" shiru tay bata d'ago ba sai d'an jan majina da take,

"Fad'i man mi tazo tayi maki ne" d'agowa tay ta d'an kalli Hajiyar a hankali tace mata ba komai idanunta
cike tab da k'walla, yar hararar ta tayi cikin wasa tace mata ba tambayar ta take ba umarni ne ta fad'i
mata duk abunda ya faru, cikin rawar murya ta fara fad'i mata tiryan tiryan duk abunda ya faru, kwa6e
Fuska Hajiya tay ta jinjina kai a fili ta furta sunan Hajiya Maryam d'in, sosae Fatun taba Saude tausayi
tana ta kallon ta tana d'an girgiza kai,

"To yanzu ke mi kika yanke kenan" Hajiya dake kallon Fatun ta tambaya aikuwa kaman tana jira tace
mata bata son Auren tasa ya saketa, ta6e baki Hajiya tay "tayi nasara kenan akan ki, ke baki san duk
barazana bace dama abunda take so kenan ta tsorata ki kice baki son Auren" kallon Hajiyar tayi da
runannun idanu kwalla kwance a cikin su tace "Hajiya tunda dai basu son Auren don Allah ki raba mu
kawai" Fuska a kwa6e take kallonta har ta rufe baki sannan tace "Waye bai son Auren, mu ba duk muna
so ba ko baki ga Mahaifin shi ya kar6e ki hannu biyu ba, itama Mahaifiyar shi ina sa ran zata amince don
duk abunda Mijinta yake so to itama tana so nasan zata fahimta, itace fa kadae ta nuna bata amince ba
kuma itama ba wani abu yasa ba kawae tana taya d'iyar ta kishi ne ba kamar da yake itama ba kishiyar ce
da ita ba shiyasa take ta wannan tada jijiyar wuyar",

cikin muryar kuka tace "to amman tace fa zata yi man Asiri ni tsoro nike tayi man wani abu ko ta kashe
ni" yadda tay Maganar har saida taba Hajiya dariya ta ta6e baki sai kace wata yar k'aramar yarinya,
Hajiya ta lura Maganar ta tsorata ta sosae, hannu ta kai ta dafa Shoulder d'inta tace "Ki kwantar da
hankalin Fateema nasan Wacece Maryam fiye da kowa tunda ni na haife ta, duk abunda ta fad'a maki ba
abunda zata yi maki don ko k'adangare bata iya kashewa balle Mutum...." Katse Hajiyar tay tace "ai
dama ba ita zata kashe ni d'in ba a Asirin da tace zata iya sakawa" yadda tay Maganar Hajiya ta
kwaikwaya tace mata "Waya fad'i maki zata iya yi maki wani Asiri, duk fa burga ce ba wani abu ba kin
wani tashi hankalin ki, kawai so take ta kwatar ma yarta mijin naku ya kasance nata ita kadai, kin san
jik'an nawa badai nagarta ba son kowa k'in wanda bai samu ba shiyasa ake rububin shi, kiga fa ita
matsayin d'a yake a wurinta itama d'iyar tata matsayin Yaya yake a wurin ta ko ba Aure akwai alak'ar yan
uwan taka amman duk da haka suke k'wak'war shi, dama kinsan shi abu mai kyau da inganci shi yake
siyar da kanshi, ko ke baki son shin ne?" ta d'age mata ido, dabarbarcewa Fatuu tay ta waro ido Hajiyar
tace ta fad'i mata indai bata son shi to sai ta raba sun, kasa bud'e baki tay tayi Magana sai faman kikkafta
idanu take ganin yadda duk suka kafeta da ido yasa ta sunkuyar da kanta zuciyarta na harbawa,
Murmushi Hajiya tayi haka ma Saude, k'ara kai hannu Hajiya tay ta dafa kafad'ar ta tace "Ki kwantar da
hankalin ki Fateema, ki jure duk wani abu da za'ai maki ki d'auki hakan matsayin yak'i akan abunda kike
so, kinsan shi abu mai nagarta wani lokacin dama ba'a samun shi cikin sauk'i" tana yin Maganar Fatuu ta
d'ago ta kalleta a hankali tace mata ita bata son shi Hajiyar ta harareta tace "K'aryar ki tasha k'arya
yarinya, wannan d'an gold d'in jik'an nawa ai ba macen da zata ce bata son shi ai na riga na gano kina
son shi tuni" d'an tura baki tay itama Hajiya ta tura mata nata harda yar harara aikuwa bata san lokacin
data saki yar dariya ba har hak'oranta suka d'an bayyana, sosae ta kwantar mata da hankali har ta washe
ta tambayi tayi Breakfast d'in tace mata a'a, Saude tasa taje ta d'aukko kayan daga kan Dining table ta
kawo su nan kan c-table tace ta had'a mata, tsare Fatun tay saida taci sosae ta tabbatar ta k'oshi sannan
tace taje ta d'aukko mayafi su tafi part d'in ta tace to, harda jakar Makarantar ta ta d'aukko don tayi
Karatu suka tafi.

Bayan jirgin su Hajiya Maryam ya sauka Mijinta Dr Mohammed ne yazo d'aukarta da yake Weekend ne
yana gida yana hutawa, tun da ya ganta ya Fahimci tana cikin 6acin rai dama kuma ba ranar sukai da ita
zata dawo ba, saida suka hau hanya ne yake tambayar ta abunda ke faruwa nan cikin 6acin rai ta
bayyana mashi, shima ya jinjina Al'amarin amma da yake mutum ne mai sauk'in kai sai ya shiga
rarrashinta ya nuna mata abi komai a hankali kaman yadda Hajiya tace, shiru kawai tayi dama tasan ba
lalle ya d'auki abun yadda ta d'auka ba balle har ya goyi bayan ta d'auki mataki, bayan sun iso gida sun
fito daga cikin Motar yaron gidan dake cikin ba flowers ruwa ya nufo inda suke yana masu sannu da
zuwa Dr ne kad'ai ya amsa mashi ya fiddo trolley ya bashi ya kai ciki suma suka nufi ciki tare, Bedroom
d'in ta suka wuce ta zauna a bakin gado shima ya zauna a gefen ta cikin salon nuna kauna ya shiga k'ara
lallashin ta kan ta kwantar da hankalin ta, har lokacin ranta a 6ace yake tace mashi kenan shima goyon
bayan auren yake yace mata a'a kawai tunda Hajiya tana so ba yadda za'ai dole suyi mata biyayya ta d'an
ta6e baki kawae, yaran su ne suka fara shigowa yi mata sannu da zuwa don basu san ta dawo ba saida
mai aikin su da ta ga dawowar ta ta sanar masu, saida Dr yaga ta d'an saki fuska sannan ya tafi, Abraham
ne ya lura da yanayin Mahaifiyar tasu da Yazo yi mata sannu da zuwa yana fita ya wuce d'akin Farha don
ya sanar mata, tana zaune a bakin gadon gaba d'aya ta rasa abunda yake mata dad'i sai tunanin ta ina
ma zata fara take lokacin Farha ta shigo tana sanye da vest da d'an guntun wandon jeans fararen
cinyoyinta tas masu k'auri don zuwa yanzu ta k'ara girma da k'iba sun bayyana, kunnuwanta sakale da
earpiece ash d'in sumar ta ta faka ta a tsakiyar kanta jelar ta saukko bayanta, had'a ido sukai da Mom
d'in nata ta sakar mata d'an murmushi ta nufe ta, a gefenta ta zauna ta kai hannu ta cire kan earpiece
guda daga cikin kunnanta tayi mata sannu da dawowa da turanci ta d'aga mata kai kawai, itama ta lura
da yanayinta da Abraham ya fad'a mata ta kai hannu ta kama hannunta guda tace "Mom what's
happening, u look all worried, kince a can zaki Weekend amman miyasa kika dawo yau?" Kallon ta
kawae tay ba tare data ce komae ba Farha d'in ta d'an yamutsa fuska a shagwa6e tace "pls Mom tell me
mi ke damun ki ne?" d'an hucin numfashi tay tace "I can't Spend the Weekend there Farha...." Shiru tay
tana jinjina kai 6acin rai shimfid'e a kan Fuskar ta, kan Farha ne ya d'aure da alamun mamaki tace mata
Mike faruwa da bazata iya yin Weekend a gidan Hajiya ba,

"Gidan Hajiya ya zama gidan 6acin rai Farha" ta kai hannu ta cize Yatsa, a shagwa6e Farha ta hau yi mata
magiyar ta fad'i mata abunda ke faruwa tana d'an jijjiga hannunta da ta rike, Labarin abunda ya faru ta
shiga bata baki sake Farha ke kallon ta har ta gama sannan da tsananin mamaki ta maimaita Ya Haisam
yayi Aure ba tare da sanin kowa ba, gaba d'aya ranta bai bata Fatuu bace da yake ba komai ta fayyace
mata ba saida ta tambaye ta wadda ya aura tay mata bayanin ta nan take ta ganeta ta wani irin zabura
sai kace wadda shock yaja, baki bud'e cike da Al'ajabi tace "U mean he married that bitch!!" Uhmm
kawai Hajiya Maryam ke fad'a, hannu Farha ta kai ta cire d'ayan kan earpiece d'in ta jefar tare da wayar
a saman gado ta mik'e ta fara kai da komowa tsananin 6acin rai kwance akan fuskar ta ta wani kalan
had'e rai sai huci take kai kace ita akai ma kishiyar, komawa tay ta zauna ta fara fad'in "impossible Wllh!
That bitch can never be Sis Fanan's rival" nan da nan Fuskarta ta hautsine tay jajir har ta fi ta uwar nuna
6acin rai, cigaba tay "That's why from the day I first saw her i hated her completely, she's a gold digger!"
shiru Hajiya Maryam tay sai d'an cize baki take tana jinjina kai, suna haka wayarta ta fara ringing ta kai
hannu gefenta ta d'aukko, ganin Hajiya ce mai kiran yasa ta d'an yin jimm kafin tay picking ta kara a
kunne tare da yin sallama, gaisawa sukayi tayi mata an isa lafiya ta amsa tace mata ana nan anata fushin
tace Uhmm akwae,

"Naji abunda kika je kika yi ma Yarinyar nan, wato don kin ji nace sai in ita tace bata son Auren shine kika
je kikai mata haka don ki tsoratar da ita ko, anya Maryam! Yanzu Saboda soyayyar D'iya kike neman
bijire man, a tunanin ki yanzu in ta nuna bata son Auren bazan gane ke ki ka sa ba? shikenan tunda kin
za6i Farincikin d'iyar ki ita kad'ai kiyi duk abunda kike tunanin yi ban hana ki ba tunda kin za6i ki kauce
hanya, sai dai ki sani a Matsayina na Mahaifiyar ki ban amince kiyi ma Yarinyar nan wani abu ba, ki
gaishe man da kowa" daga haka ta katse kiran, wurgi tay da Wayar ta kai hannu ta bugi katifa tana
yamutsa fuska tamkar zata fashe da kuka, nan da nan kwalla suka taru cikin idanunta ta fara fad'in
miyasa Hajiya zata za6i Faranta ma 6are fiye da nata, ruk'e hannunta Farha ta k'ara yi fuska a yamutse
tamkar itama zata saka kuka ta shiga lallashin ta tana tambayar mi Hajiyan tace mata, fad'i mata tay ta
hanata ta d'auki kowanne mataki akan Yarinyar, fuska a kumbure kamar zata fashe tace mata ta daina
damuwa idan suka yi hutu ita zata ce gidan sai ta fitar da ita da tsiya, jin haka yasa Hajiya Maryam samun
sassaucin k'unar da zuciyarta ke yi Saboda tasan halin Farhar bata da Sauk'i dama itama ta nuna ma
Fatun zata iya mata Asiri kawai don barazana amman sam bata bin Malamai ko bokaye iyaka ta bada ayi
mata Addu'a kaman akan business d'in ta ko wani Al'amari, yanzu kam sai taji ta samu Mafita, nan ta
fara kitsa ma Farhar wutar da zata hura ma Fatuu in ta je a 6oye ba tare da Hajiya ta sani ba har tasata
da kanta ta bar gidan.

Washe gari Lahadi da Yamma Senator ya koma Abuja bayan ya k'ara zuwa wurin Hajiya sun tattauna
game da Auran tace mashi yay k'ok'arin fahimtar da matan shi yace in sha Allah, anan ya iske Fatuu suka
k'ara gaisawa har yana tambayar ta in tana son wani abu tana murmushi tace ba abunda take so yace
mata ta dage da karatu, da daddare bayan sun gama cin Abinci ya buk'aci ganin matan nashi a part d'in
shi, bayan sun zo a nutse ya fara masu bayanin dalilin kiran nasu da Hajiya tay, gaba d'ayan su sun ji
Al'ajabin Maganar ba ma kamar Mahaifiyar Haisam d'in, bazaka gane yadda ta d'auki Al'amarin ba daga
yanayin Fuskarta ta tambaye shi mi Hajiya Maryam tace game da hakan, bai 6oye mata komai ba game
da yadda ta ji zafin abun dama abunda tay tunani kenan a cikin ranta dole tasan baza su ji dad'in abun
ba, ba kamar da taji yarinyar har ta samu ciki, jin tayi shiru yasa shi ce mata bata ce komai ba ta d'an
watsa hannu tace to ita mi zata ce kawai dae Haisam bai kyauta ba ya zaiyi abu irin wannan ba tare da
neman shawara ba tun farko gashi yanzu rayuka na neman 6aci na Hajiya Maryam aka gani ina ga ita
Fanan d'in, nunawa tayi ita tana ganin gara a raba su kawae zai fi da azo asamu rashin Fahimta,

Aunty tace "Gaskiya ni ina ganin in aka ce a raba su ba'ai ma Yarinyar Adalci ba kaman yadda Hajiya tace
tunda shi ya fara sanin ta yanzu in aka raba auren dole sunanta zai canza zuwa bazawara, kuma ni ina
ganin yana son ta ne shiyasa tun farko ma ya auretan ko kuma daga baya ya fara sonta shiyasa har abu
ya shiga tsakanin su, haka da bai son ta sai inga kaman bazai yarda yaci gaba da zama da ita ba" d'an
jimm Mom d'in shi tay alamar tunani kafin tace "zai iya auren ta don ya taimaka mata kawae and zai iya
cigaba da zama da ita tunda Hajiya na son hakan koda bai son ta" gyad'a kai Aunty tay "hakane, nasan
halin shi sarae zai iya kasancewa hakan, amman dai kamar yadda Hajiya tace ina ganin muyi masu Fatan
Alkhairi kawae don ni ina ganin dama can Allah ya k'addaro matar shi ce shiyasa ma har suka san juna"
jinjina kai Senator yayi Mom d'in Haisam da yanayin fuskar ta ya sauya tace basu ganin Hajiya Maryam
zata ga suna supporting d'in shi Saboda d'an su ne basu damu da halin da Fanan zata iya shiga ba,
Senator ne yace to tunda Hajiya haka take so ai dole su bi abunda take son sannan yasan damuwarta
Saboda tunanin halin da Fanan zata shiga ne idan Allah yasa bata tashi hankalin ta kamar yadda take
tunani ba yana ganin komai zai daidaita, cigaba da tattaunawa sukai daga baya suka bar part d'in nashi,

Bayan Mahaifiyar Haisam ta koma Bedroom d'in ta, a gefen tanfatsetsen gadon ta daya sha k'ayataccen
bedsheet ta zauna tay shiru tana kallon wuri guda da alama zurfin tunani ta shiga, sam ta kasa gane mi
take ji game da Al'amarin, wayarta ta d'ago ta fara k'ok'arin kiran Haisam, bayan ta fara ringing ya d'aga
suka gaisa tace mashi taji abunda ya aikata ba tare da sanin su ba batare da kuma yayi zurfin tunani ba
mi zai sa yayi Aure da sunan taimako bazai yi amfani da wata hanyar ba, hak'uri itama ya bata tace tunda
yaje yayi gaban kan shi ai dole suyi hak'uri amman yasan yadda zai yi ya fad'i ma Fanan ba tare da ta
tada hankalin ta ba yace zai yi hakan in sha Allah cikin nuna k'auna yay mata Sallama tace Uhmm kawai,
bayan sun gama wayar d'an jimm tayi sai kuma ta fara k'ara yin kira, Jidderh ta kirawo tace tazo d'akinta
tana son ganinta, after few minutes ta shigo tana sanye da doguwar riga kanta ba kallabi sai bak'ar
sumar ta wuluk da ta faka hannunta ruk'e da wayarta ta nufo gefen gadon ta zauna tace gata,

"Akwai wani yarinya Neighbor d'in Hajiya I can't remember her name amman sun saba da Hajiya
sosae...." Katseta Jidderh tay da fad'in "Sis Fatuu?" d'an d'age ido tay alamar tunani tace ta dai manta
sunan k'ilan itace da sauri Jidderh tace bari ta nuna mata picture d'in ta ta gani in itace, shiga cikin
gallery d'in wayarta tayi ta bud'o hoton Fatuu ta nuna mata tana gani ta shaida Fuskarta tace mata itace,
tambayar ta Jidderh tayi miya faru da ita da d'an alamun rudu Mom d'in nasu tay d'an guntun murmushi
tace ba komai she just wants know about her, cikin rashin fahimta Jidderh tace mi take son sani game da
itan, tana d'an yarfa hannu tace kaman ya halayyarta take da mu'amalarta da Mutane haka, Murmushi
Jidderh tayi harda gyara zama don tana bala'en k'aunar Fatuu nan ta shiga fad'i mata halayenta tace
tana da kirki sosae ga faran faran ga son mutane gashi tana da dad'in zama bata da wuyar sabo kuma
daka zauna da ita sai kaji ta burge ka, nan ta fad'i mata farkon saninta da ita lokacin data dawo daga Yola
tazo gidan Hajiya da kayan Fulani har hoton da suka yi ranar ta bud'o mata da tasa Haisam ya turo mata
don ta rasa shi, labarin tsakaninta da Ya Haisam abunda ta sani da wanda Hajiya ta basu labari ta shiga
bata, tace mata yanzu haka suna gaisawa don ta zama kamar k'awarta ma, tambayar ta tayi zasu yi
shekaru d'aya tace "No na girme ta da kusan 3 years ma, kawai dai she has a good shape kinga hips d'in
ta kuwa Mom wllh kyace ba nata bane in kin ganta sun yi haka..." ta mik'e tana gwada ma uwar yadda
hips d'in Fatuu suke ita dai sai murmushi take, komawa Jidderh tay ta zauna tace mata wai miyasa take
son sanin abubuwa game da ita ne, shiru ta d'anyi tana rolling eyes ta kalleta da murmushi tace "Now
she's part of this Family" waro ido Jidderh tay baki bud'e alamar mamaki cikin daurewar kai tace bata
gane ba, ce mata tay Yayan su ya Aureta cikin rashin fahimta ta d'an waro ido tace Ya Nameer, yar
harara ta wurga mata tace Nameer d'in da bai a K'asar Big bro d'in su take nufi, k'ara waro idanu waje
tay tana kallon Mom d'in nasu da itama take kallonta ta d'an ta6e baki da d'an murmushi, cike da
Al'ajabi ta tambaye ta yadda akai ta zama Matar Ya Haisam d'in nan ta fad'i mata, aikuwa ta washe baki
cike da Murna tace "Oh my God! am so Happy to hear that Mom, wllh na dad'e ina masu sha'awar auran
juna don sun dace sosae ba K'aramin fahimtar juna zasu samu ba, kaman fa shi ya raine ta Mom, bai son
6acin ranta bata son 6acin ran shi itama, sosae jinin su ya had'u baki ga yanda suke kulawa da juna ba,
tun bayan dana santa dashi naga sun bala'en yin matching saidae kuma nasan ba zai aureta ba Saboda
Maganar auren su da Aunty Fanan kuma lokacin tayi k'arama ma, daga bayan nan data girma inta ji
inama suyi aure, ashe da rabon zasu yi d'in" cike da Farinciki take Maganar sai faman washe baki take,
d'an d'aure Fuska Mom d'in tayi tace ai raba Auran za'ai nan da nan murnarta ta koma ciki tay mata wani
kallo kaman zatai kuka tace "but why Mom, Don Allah kar a raba su" d'an ta6e baki tay tace Auren na
son kawo rashin fahimta don Momy d'in su ta Lagos ta d'auki zafi sosae sannan Fanan ma tasan in taji
za'a iya samun matsala, Fuska a yamutse Jidderh tace ai dama dole hakan ya faru Saboda kishi amman
daga baya tasan komai zai daidaita zasu yi hak'uri ita dae don Allah kar su raba Auran, yar harararta
Mom d'in tayi tace da yake ba ita akai ma kishiyar ba a shagwa6e ta kama hannun Momyn tana mata
Magiya, ganin tana murmushi yasa ta gane wasa take cike da zumud'i tace bari ta kira mata Fatun su
gaisa, har ta d'ago wayar ta dakatar da ita tace ba yanzu ba ta bari aga komai ya daidaita itama kar ta
fad'i ma kowa cikin yan uwanta tace to, ce mata tay zata iya tafiya ta mik'e tana fad'in zatai ta yin Addu'a
Allah yasa komai ya daidaita da wuri su sha shagali don duk abunda akai a bikin Aunty Fanan itama sai
anyi Momyn tace Uhmm kawai ta nufi kopar fita tana ta murna ta fice.............
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM070*

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

........bayan sallar isha gwaggo ta nufi gidan Hajiya, lokacin data isa a parlor ta isketa ta yi mata maraba,
ganin tayi tsaye ta nuna mata kujerar gefen ta tace ta zauna mana, bayan ta zauna ta gaishe da ita ta
amsa tay mata ya aiki ta tambayeta Amadu kwana biyu bata gan shi ba tace yana nan, shiru sukai
gwaggo ta d'an sunkuyar da kanta tama rasa ta ina zata fara, jin shirun nata yayi yawa yasa Hajiya cewa
"Ya ya Dije, koda wani abu ne?" kallon ta tayi tay d'an murmushi kawai ba tare data ce komai, lokaci
guda Hajiya ta fahimci abunda ya kawota tana murmushi tace mata ko itama Maryam d'in taje ta firgita
ta, sai lokacin ta fara magana cikin sanyin murya tace "Hajiya dama zuwa nayi in rok'i Alfarma, don Allah
tunda basu son auren ina ganin a hak'ura kawai don hankalin kowa ya kwanta, ban so silar hakan asamu
rashin fahimta" d'an murmushi Hajiya tay ta d'an kya6e baki tace "to dawa dawa ye basu san Auren?
Duka fa ita kad'ai ce ta nuna k'in amincewa kuma itama ba wani abu yasa ba face kishi da take taya
yarta" shiru gwaggo tayi ita dai har cikin ranta tafi son a raba Auran kawae saidae bata iya yin jayayya da
Hajiyar, ganin yanayin ta yasa Hajiya cigaba "ki kwantar da hankalin ki Dije ba abunda zai faru sai
Alkhairi Fateema kuma tana nan Lafiya kuma ba abunda zai sameta in sha Allah, duk maganganun da
taje ta fad'a maki barazana ce kawai ba wani abu ba" gyad'a kai gwaggo tayi tay shiru, can tace ma
Hajiyar bari ta tafi tayi mata godiya Hajiya tace ta bari ta ci Abinci tana d'an murmushi tace mata a
k'oshe bata jima da ci ba tace to bari a zubo mata ta kaima Amadu tace mashi tunda ya manta da matar
ta shi gashi nan tana biko duk suka d'an yi dariya, Saude ta kira ta bata Umarnin zubo ma gwaggo Abinci,
bayan ta kawo har zata bata Hajiya tace ta rakata part d'in Fateema ta ganta ko hankalin ta ya k'ara
kwanciya ita dai gwaggo murmushi kawai take sukai sallama suka tafi Saude na ruk'e da Warmer d'in
Abincin, Fatuu na cikin Bedroom ta fito daga wanka tana shiryawa da kayan bacci don tafiya part d'in
Hajiya akai kopa ta nufeta ta bud'e, Saude ta gani sukai ma juna murmushi ta gaida ita tace mata ta zo ga
bak'uwa ta kawo mata, d'an jimm Fatuu tay a ranta tana tunanin wace bak'uwa ce don rabonta da wani
yazo tun cikin wanccan satin da Haulat tazo har take fad'i mata ta kusa komawa, juyawa tay ta d'aukko
hula tasa ta fito, tana zuwa bakin corridor ta d'an wara ido tana son ganin wacece bak'uwar, gwaggo ta
hango zaune akan armchair Saude na tsaye gefe aikuwa ta watso da gudu tana zuwa ta fad'a kanta cike
da Farinciki take fad'in gwaggo dama ke ce bak'uwar, gaba d'aya dariya suke yi Saude na fad'in Fateema
sai kace kin shekara baki ganta ba, ita dai gwaggo sai dariya take, sallama Saude tayi ma gwaggo tace ma
Fatuu sai ta shigo ta juya ta nufi kopa, d'ago kai Fatuu tay suna kallon juna ita da gwaggo sai sakin
murmushi suke, ganin gwaggon tak'i cewa komai yasa Fatuu tura baki a shagwa6e tace don Allah tayi
magana mana, tana dariya tace taya zata yi Magana ta sakar mata nauyi jin haka yasa ta tashi maimakon
ta zauna akan d'ayar armchair d'in sai ta haye saman hannun kujerar ta kama hannun gwaggon sai kace
zata gudu, tambayar ta tana lafiya tayi tace mata eh sai lokacin ta tuna da bata gaishe da ita ba, shiru
suka d'an yi Fatuu ta tambayeta Kawu Amadu tace ta wuto shi a shago yana gaishe da ita, shiru suka
k'ara yi Fatuu nata wasi wasin ko ta fad'i mata abunda Hajiya Maryam tazo tayi mata, itama gwaggon
tana son ta tambayeta ta rasa ta ina zata fara bata son Fatun ta fahimci taje gida kar ta tashi hankalin ta,

"Daga wurin Hajiya nike, naji tace Mahaifin d'ana Haisam da Hajiya Maryam sun zo har sun koma"
yanayin fuskar Fatuu ne ya sauya a hankali tace mata eh, "Yanzu sun san da Maganar auren kenan?" Kai
Fatuu ta d'aga tace mata eh, amfani tay da canzawar fuskar Fatun tace mata ya taga Fuskar ta ta sauya
ko da matsala ne, shiru tay tana d'an kikkafta ido tana son fad'i mata amman bata son hankalin ta ya
tashi gwaggo ta fahimci da wani abu hakan yasa ta kwantar da murya tace inda wani abu ta fad'i mata in
ba ita ba wa zata fad'i mawa, labarin abunda ya faru ta bata harda yadda Senator ya kar6eta, Fuskar
gwaggon da murmushi tace mata ta kwantar da hankalin ta komai zai daidaita in sha Allahu itama kar ta
k'ullace ta tana gudun abunda ka iya faruwa da d'iyarta ne tunda bata san da Maganar ba sai suyi ta
Addu'ar Allah ya kawo komai cikin sauk'i, tambayar Fatun tay koda wani abu tace mata a'a ta mik'e
Fatuu ma ta saukko tana fad'in don Allah ta bari su tafi tare ta kwana a can ta d'an harareta tace to bari
ta d'aukko mayafi su fita tare ta rakata ita kuma ta wuce part d'in Hajiya tace to ta juya da sauri sauri
gudu gudu ta nufi hanyar corridor gwaggo ta bita da kallo tana Murmushi.

Bayan sati guda da zuwan su Senator Fatuu na a parlon Hajiya bayan la'asar suna yin kallo tana sanye da
riga da skirt na atampa, akai akai Hajiya ke mata magana akan film d'in da suke kallo wani wurin ta bata
amsa wani wurin kuma tay dariya kawai don Hajiya bata iya in tana kallo tayi shiru, Sallama akai daga
can bakin kopar duk suka juya suka kallo mai sallamar, Kawu Amadu ne daga bayan shi kuma wata ce
tana sanye da doguwar rigar Atamfa da Hijab Fatuu na ta son ta gane ko wacece ta kasa don sun d'an
masu nisa gashi Kawu Amadu ya d'an kare ta, Hajiya ce ta d'aga murya tace su shigo mana sun yi tsaye
sai kace parlon bak'on shi ne ya nufo ciki yana murmushi wadda suka shigo tare na biye dashi, suna zuwa
bakin kujerun Fatuu tay zumbur ta mik'e da alamun Al'ajabi idon ta akan wadda yazo da ita, ganin
murmushin da take mata yasa da k'arfi ta furta "MINO" dariya minon tayi aikuwa Fatuu ta watsa da gudu
tana zuwa ta kankame ta Amadu nata dariya Hajiya ma kallon nasu take ta cikin glasses tana murmushi,
zama Kawu Amadu yay ya gaishe da ita ta amsa tace kace da babbar bak'uwa kake tafe yace aikuwa,

"To wai ni ba za'a bari in gaisa da k'awar tawa da ban sani ba sai a hoto" Hajiya tay Maganar idonta akan
su Fatuu da suka saki juna suna ta ma juna dariya, kamo hannunta tayi suka nufo wurin Hajiya Mino na
niyyar duk'awa ta gaishe da ita Hajiya ta mik'o mata hannu ta kama ta zaunar da ita a gefen ta, cikin
hausar ta dake bayyana ita bafullatana ce sosae ta gaishe da Hajiyar tana fara'a ta amsa tay mata an zo
lafiya da tambayar sauran yan'uwanta ta amsa Fatuu na tsaye gefe farinciki shimfid'e akan Fuskar tata,
Hajiya ce tace mata ta zauna mana sannan ta zauna a kujerar kusa da su,

"Ita Dije wannan shine Fateema ta tafi ga wata Fateemar ta zo" ta fad'a idon ta akan Mino da ke ta
washe baki in ka ganta baka ce daga k'auye take ba tsaf tsaf da ita ba irin kwalliyar yan k'auyen nan iya
jan baki kawae ta shafa ko jagira batayi ba don tana da gashin gira sosae kaman Fatuu gashi sai d'an
k'amshin turare take, "kusan ma tsawon su d'aya da Fateema kawai yanayin jiki ne ba d'aya ba" Hajiya ta
fad'a tare da kallon Amadu yana dariya yace eh ita da gani ma sai tafi Fatuu tsawo tace ba shakka, Fatuu
dai sai murmushi take saki farinciki fal ranta yar uwa tazo, hannu ta kai ta dafo Shoulder d'in mino ta
juya ta kalleta, tambayar ta tayi su Yadikko tace mata zasu zo amman ba yanzu ba sai daga baya Baffa ne
dai suka zo tare da shi,

"Kai haba! da Baffa kuka zo yana ina?" ce mata tay yana nan waje, kallon kopar shigowa Fatuu tayi ta
nuna ta da yatsa tace bakin kopar nan ta d'aga mata kai alamar eh aikuwa zumbur ta mik'e ta nufi kopar
da gudu, Kallon Amadu Hajiya tayi tace ya zai bar Mutum a waje yace mata shine yace ya fad'a tukun a
bada izini, dariya Hajiya tay "wannan parlon na mutane har sai an nemi wani izini kaima Amadu ai da ka
shigo dashi", ce mashi tayi yaje ya shigo dashi yace to, Fatuu na fita ta ganshi a gefe yana sanye da
manyan kaya riga da wando na shadda brown kusan sun saje da kalar fatar shi kanshi sanye da hula
saidai karin ta bai fita da kyau ba shima tsaf dashi harda su Agogo anzo gidansu suruki, da sassarfa ta
nufe shi tana fad'in sunan shi tana zuwa ta kankame shi sai kace zata shige cikin jikinshi, yana ta dariya
yasa hannu guda ya dafa ta, d'agowa tay da tsantsar farinciki tana kallon shi sai washe baki take ta kasa
yin Magana shima idon shi na a cikin nata suna ta yi ma juna murmushi, suna haka Amadu ya fito yace
mashi ance su shigo yace to, Fatuu na ruk'e dashi tayi mashi side hug suka shiga, suna isa cikin parlon ya
fara k'ok'arin duk'awa ya gaishe da Hajiya ta dakatar dashi tace don Allah ga wuri ya zauna sai a gaisa,
bayan sun gaisa tayi mashi ya aka baro mutan gidan yana ta murmushi ya amsa, kallon Fatuu dake gefen
shi har lokacin tana a jikin shi Hajiya tay tace su Fateema an ga Baba an hana mashi sakat tasa dariya
Amadu ya kai hannu alamar zai bugeta yace ta sake shi ya huta ta mak'e mashi kafad'a shi dae sai
murmushi yake, godiya Baffan ya shiga yi ma Hajiya kan abubuwan Alkhairi da aketa yi masu da Addu'oi
tana murmushi tace mashi ai ba komai an zama d'aya,
kallon Fatuu tay tace "to mage sai a tashi aje a had'a masu Abinci ko" tana dariya ta d'ago a kunyace
baffan yace a bashshi sun ci Abinci Hajiya tace eh ai tasan sun ci shima na nan d'in sai aci duka sukai
murmushi ta kai hannu ta dafa jikin Mino tace ita ai ta samu k'awa minon nata mata murmushi, cikin
parlon ta kawo masu Abincin tare da Aunty Saude da bata san da zuwan nasu ba saida Fatun taje Kitchen
take sanar mata, gaisawa tayi dasu tayi masu an zo lafiya, daga baya bayan sun gama cin Abincin suka yi
ma Hajiya sallama ta tambayi yaushe Baffan zai koma yace mata gobe in Allah ya kaimu, tambayar Hajiya
Fatuu tay wai ta bisu can gidan ta d'an ta6e baki ta girgiza mata kai alamar a'a, marairaice mata tayi tace
mata don Allah tayi yar dariya tace taje in ma kwana zata yi ta kwana, zo kaga murna harda d'an tsallen
murna. Bayan sun fito ne Fatuu tace ma Baffan suje yaga inda take yace mata ba sai yaje ba ta
marairaice mashi ta kama hannun shi guda tana mashi magiya, Amadu ne yace mashi ai ba wani abu suje
sannan suka nufi part d'in nasu, sosae yay farincikin ganin inda yar tashi take rayuwa har fuskar shi ta
kasa 6oye farinciki nashi, Mino ma sai washe baki take tana fad'in yanzu Adda Fatuu nan gidan ki ne tana
ta kalle kalle, matsa mashi Fatuu tay wai yazo yaga sauran wurare ya k'i yace ba sai yaje ba tunda yaga
nan Mino ko ai tuni ta nufi ciki.

Bayan sun je can gidan mino tasa Fatuu ta kira mata Abbas tace ashe bata manta dashi ba tace ai suna
waya dashi ta wayar yadikko, d'an waro ido Fatuu tay da d'an mamaki tace kodai wani abu ke tsakanin
su ne da sauri Minon tace mata a'a wllh kawai yana kira yaji ya suke sai suyi hira wani lokacin har yasa
tayi mashi magana da fulatanci har ma yace inta dawo nan zai siya mata waya kuma zata rink'a koya
mashi fullanci jinjina kai kawae Fatuu tay, bayan ta kira shi sun gaisa taba Mino wayar ta sanar dashi
game da zuwan su da alamun jin dad'i yace mata to yana nan zuwa, da daddare bayan sallar isha yazo a
parlor suka zauna aka kira mashi Baffan Fatuu suka gaisa shima yayi mashi godiya sosae da Addu'oi yana
ta fad'in ba komai, hira suka shiga yi gaba d'ayan su harda Kawu Amadu da gwaggo da Baffan Fatun
Mino dai na a gefen Abbas, abun gwanin burgewa yadda suke yin hirar in akayi hausa wani lokacin sai a
juye a koma fullanci Abbas yay ta murmushi har Mino nace mashi tunda tazo zata koya mashi ai, anan
yake ma Gwaggo Maganar cigaba da karatun ta tace eh inda Fatuu tayi take son taci gaba in ta huta sai
Amadu yayi mata cuku cukun samu Abbas d'in yace abar mashi komai, bayan Abbas ya tafi gwaggo tace
ma Fatuu ita sai yaushe zata tafi dare yayi fa sosae tace ai anan zata kwana Hajiya ta amince tace a'a
miya kai na wani kwana ta tashi ta koma ta marairaice kaman zata saka kuka gwaggon tace ko na jini
zata yi sai ta tafi tace su tafi tare da Mino su kwana, jin hakan yasa ta washe ta basu tsarabar Hajiya da
ta Fatun suka tafi, Bayan sun koma gida sun kaima Hajiya tsarabar suka dawo part d'in su, Bedroom suka
nufa Mino sai faman washe baki take tana fad'in "Adda Fatuu wllh gidan ki Aljannar duniya ne" ita dai
Fatuu sai dariya take, toilet ta jata don tayi wanka, a Laundary suka tsaya tasa ta cire kayanta ta d'aukko
mata towel kanta yasha kitson fulani gwanin sha'awa, bud'e injin wanki tayi ta saka kayan data ciren nan
fa Mino ta fara k'auyanci tana tatta6a shi cike da mamaki take fad'in ta ta6a ganin irin shi a kallo ashe
tana da rabon ganin shi a fili har ta ta6a, gaba d'aya ta bi ta rurruk'e saman towel d'in da Fatuu ta bata ta
d'aura, tana dariya tace mata in aka d'aure saki ake tace ai ji take kaman zai kwance ne, tare suka shiga
toilet d'in ta fara nuna mata yadda zata yi amfani da komae ta waro ido tana bin shi da kallo, had'a mata
ruwa tayi cikin bathtub ta fara nuna mata yadda zata shiga tayi wanka tana cikin mata bayani Minon
tace wai ko kaman yadda ake yi a tafki ta d'an harareta, bayan ta gama nuna mata tace zata tsaya a cikin
d'akin waje in akwae abunda bata gane ba tayi mata Magana tace toh, da yake tana da fahimta kuma
k'auyancin nata da Sauk'i bai yawa ba sai gashi tayi wankan lafiya lou ta fito sai shinshina jikinta take yi
tana washe baki tana fad'in yau tayi wanka da ruwan turare, Fatuu dai saidae tay dariya ta girgiza kai,
bayan sun koma cikin Bedroom tasata ta shafa mai ta daukko mata rigar bacci, saida ta gama shiryata ta
nuna mata gado tace ta kwanta a d'arare ta hau gadon tana yi tana tatta6a jikin shi sai kace tana jin
tsoron shi, bayan ta kwanta Fatuu ta wuce don tayo wankan itama, bayan ta fito a takure ta iske Mino
sai faman rawar sanyi take ita tama d'auka tayi bacci, rage mata Ac d'in tayi ta nuna mata duvet tace da
shi ake lullubewa tace ai ta d'aukka kwalliyan gado akai Fatun tay d'an guntun tsoki tare da murmushi.

Washe gari Baffan su Fatun ya tafi. A cikin satin Abbas ya gama yi ma Mino cuku cukun Makaranta ya
kawo mata Uniform da su School back nan yake sanar da gwaggo Makarantar da zata cigaba wadda
babbar private school ce da kusan duk an santa, da alamun damuwa gwaggo tace ya zai d'auki wannan
babban nauyin ga dawainiyar iyalin shi nan yake sanar mata bashi ne zai d'auki nauyin Karatun ba
Haisam ne shi yace akaita can tace to ai da ko wadda bata kaita ba tunda ita mai tsada ce yana
murmushi yace mata tunda shi yace kar ta damu, bayan ya tafi tasa Amadu ya kira mata Haisam d'in
bayan sun gaisa tayi mashi Maganar Makarantar tace dawainiyar zata yi yawa da asaka ta wadda bata
kai ta ba yace mata ba wani abu, sosae tayi mashi godiya tare da Addu'oi. Cikin sati guda Mino har ta
goge komai na part d'in Fatuu tasan yadda ake amfani dashi, anan take taya ta kwana da safe sai ta
koma gida don taya gwaggo aiki, cikin satin daya kama ta fara zuwa Makaranta, sosae Uniform d'in suka
kar6e ta kai kace itama d'iyar Senator d'in ce, Tk ne ke kaisu gaba d'aya kuma ya d'aukko su da yake
kusan lokaci guda ake tashin su, duk wanda ya gan su sai yayi Maganar Kamannin su.

Ranar Juma'a daya kama wata guda da sati d'aya da tafiyar Haisam bayan Fatuu ta dawo daga
Makaranta an sauke Mino ta nufi part d'in su, Bedroom ta wuce ta aje jakarta ta nufi toilet, bayan ta fito
ta fara shiryawa ta saka riga da skirt na lace da yake period take bazata je Masallaci ba kaman yadda
suke tafiya tare da su Hajiya, bari tayi a gama sallar sai ta tafi part d'in Hajiyar taci Abinci don bata son
taje tayi mata Maganar zuwa Masallaci, tana kishingid'e tana latsa wayarta har aka gama sallan, da yake
ba wata yunwa take ji sosae ba sai can bayan an dad'e da gamawa sannan ta tashi don ta tafi, saida ta
yafa d'an gyale mahad'in kayan jikinta sannan ta tafi, Tana shiga parlon Hajiya ta hango ta zaune tayi
kwalliyar Juma'a daga d'ayan bangaren kuma wata ce zaune wadda Fatun bata gane ko wacece ba, tana
kaiwa bakin kujerun taja ta tsaya sakamakon wadda idanun ta suka gani, Farha ce zaune tana sanye da
wasu matsattsun jeans da top kanta ba kallabi kunnuwan ta sak'ale da earpiece idanuwan ta na akan
wayarta dake ruk'e a hannun ta tana d'an taunar cingam sam bata ji shigowar Fatun ba, kallonta Hajiya
tay fuska a sake tace mata an dawo tace eh tun d'azu ma tace to taje ta ci Abinci, suna cikin Maganar
Farha ta d'ago ta kalli Hajiya ganin tana Magana yasa ta kai idon ta kan wanda take Maganar da shi suka
had'a ido da Fatuu, wani mugun kallo ta jefa mata nan take Fatuu tasha jinin jikinta, maida kanta tay kan
wayar har Fatuu zata juya Hajiya tace mata bata gane Farha bane, dakatawa tayi da d'an murmushin
yak'e tace ta ganeta tace to basu gaisa ba, ce mata tay taga kaman bazata ji ba tunda ta saka earpiece
shiyasa bata yi mata magana ba Hajiya tace ina ruwan uwar son kad'e kad'e, ce mata tayi taje sun gaisa
daga baya hakan ba K'aramin dad'i yay ma Fatuu ba ta juya, ji tay kaman ta koma part d'inta kawai ba sai
ta ci Abincin ba saidae ta san Hajiya dole tayi Magana, bayan ta shiga Kitchen tsaye tay gaba d'aya ta
rasa mike mata dad'i don tana zargin ba hakanan Farhar tazo ba ba kamar data ganta ita kadae, ita dake
dad'ewa bata zo ba kuma saidai suzo gaba d'aya, zuciyar ta ce ta raya mata k'ilan ma yanzu d'in ba ita
kad'ai tazo ba sai kuma ta sake raya ai kuma da taga sauran a parlorn, yanke tafiya da Abincin part d'in
su tayi ta ci acan, bayan ta zuba har saida tay d'an jimm a bakin k'opa kafin ta fito, ganin hankalin Hajiya
na akan tv yasa ta bi ta kopar baya idanun Farha a kanta, bayan fitar Fatun da d'an lokaci Farha ta mik'e
ta nufi Hanyar Bedroom, tana zuwa ta d'an juyo ta kalli Hajiya ganin bata ganinta ta wuce itama ta bi ta
kopar bayan ta fuce,

Bayan ta koma part d'in nasu kitchen ta wuce ta zubo Abincin a plate ta dawo parlor ta d'aura akan c-
table ta fara ci, bata dad'e sosae da fara ci ba taji an turo kopar parlon da sauri ta kai idonta, Farha ce ta
shigo har saida gaban Fatun ya Fad'i ta dakata da cin Abincin tana kallon ta, nufo cikin falon tay tana
tafiya cike da isa ta tsaya daga gaban Fatun suka fara kallon kallo ta wani kalan had'e rai can ta ja wani
dogon tsoki ta nuna Fatuu da yatsa a fusace tace "You bastard! how dare u married my sister's
Husband!!!" Shiru Fatuu tay tana kallonta, a hasale ta matsa ta kai duka hannuwanta jikin c-table d'in ta
d'ago shi ta kifa ma Fatun shi Abincin ya 6aro a jikinta da sauri ta mik'e don yana da d'an zafi ga c-table
d'in ya dakar mata gwuiwa, hannu ta kai ta maida table d'in ta d'ago tana kallon Farhar tana fitar da
numfashi da sauri da sauri ita kuma Farhar sai huci take, a zafafe taci gaba "U must leave dis house
tunda ba gidan uban ki bane, wllh sai kin bar shi talakan banza talakan wofi a gold digger" tsoki ta k'ara
ja ta juya har tayi d'an taku ta juya tana nuna Fatun tace "in na k'ara ganin kin je d'aukar Abinci sai na
saka maki poison kin mutu kuma ba abunda za'ai man na kashe Banzaaa" tana fad'in hakan ta juya ta
tafi, tsaye Fatuu tay a wurin tamkar an dasa ta zuciyarta sai harbawa take da k'arfi k'afafuwanta na d'an
yin rawa, ta d'auki lokaci a hana kafin jiki a mace ta zauna kan kujera, sosae Maganar Farhar ta k'arshe
tay tasiri a kanta don yadda take nuna mata tsana tasan zata iya aikata mata hakan, da k'yar ta mik'e
gwuiwowinta a sanyaye ta nufi Kitchen don ta d'aukko abunda zata gyara wurin, bayan ta gama gyarawa
Bedroom ta shiga ta nufi bakin gado ta zauna tay tsuru, in tace taji dad'in zuwan Farha tayi k'arya don
tasan yanzu kwanciyar hankalinta ya k'are ba kamar data gane dalilin zuwan nata, k'arshe dai Abincin da
bata ci ba kenan. Da daddare bata je part d'in ba balle taci Abinci sai kawae ta yanke ta dafa indomie
taci, bayan ta gama dafawar bedroom ta wuce da ita, sam tama kasa sakin jiki taci indomie d'in don har
bakinta ba dad'i take jin shi, yar kad'an taci ta mik'e ta maida ta kitchen, komawa tay Bedroom ta haye
gado ta zauna ta shiga duniyar tunani, a ranta take raya ita bata ga amfanin wannan auren ba dama su
rabu kawai ta huta don ba komai a cikin shi sai tashin hankali gashi wanda take zaune don shi ya yi
tafiyar shi ya barta ko damuwa bai yi da ita ba, daga tafiyar shi zuwa yanzu zata iya k'irga sau nawa suka
yi waya itama ba wani Magana mai tsawo ba iyaka ya tambayi yadda take ko chat basu yi, idanunta ne
suka ciko da k'walla saidai bata bari sun zubo ba don itama yanzu har ta gaji da yin kuka, tana haka Mino
ta shigo ta k'ak'alo murmushi tayi mata ta nufo ta itama tana murmushin, a bakin gadon ta zauna ta
gaishe da ita, bayan ta amsa tace mata gwaggo na gaishe da ita ta d'aga kai, tambayar ta tay ko bata
lafiya ne ko wani abu na damunta taga kaman fuskarta ta canza tana murmushi tace mata lafiyar ta lau
ta tambayi taci Abinci tace eh bata dad'e data gama ci ba, ce mata tay akwae sauran indomie data rage a
Kitchen in zata ci, mik'ewa tay tace to bari ta d'aukko. Bayan sun gama shirin kwanciya Mino ta kwanta
ita kuma ta d'aukko jakar ta don tayi karatun test da suke cikin yi Saboda exam d'in su ta matso, tana
zaune a kan gadon tana karatun aka turo kopar ta kai idon ta da sauri don bata tsammaci wani ba a
lokacin mantawa ma tayi bata kulle kopar ba, Farha ce ta shigo tana sanye da rigar bacci iya gwuiwa
kanta sanye da hula, nufo cikin d'akin tay cikin d'acin rai ta tsaya bakin gadon tana masu kallon rashin
Arzik'i, nuna Mino tay a wulakance tace "Who is she?" shiru Fatuu tay kaman bazata tanka mata ba sai
kuma ta bata amsa da kanwarta ce, tafa hannuwa Farhar ta shiga yi da alamun mamaki tace wato har
talakawan yan'uwanta ke zuwa kwakwa suma kenan" banza Fatuu tay mata tay k'wafa a fili ta furta duk
zata yi maganin su, ce mata tay anan zata kwana don haka ta tasheta ta bata wuri, Fatuu dake kallon ta
tace mata ai ga wuri nan sosae ba sai ta kwanta ba, yamutsa Fuska tay ta furta "God forbid! ni zan
kwanta da pauper kina son ta goga man talauci ne" ta d'age ma Fatun gira tana kallon ta shek'ek'e, tasan
fitina take nemanta da ita hakan yasa ta kai hannu ta fara tada Mino d'in, bayan ta farka tace mata ta
saukko daga kan gadon, tambayar ta tayi lafiya tace mata eh kawai, saukkowa tayi ta tsaya sai lokacin ta
lura da Farha dake mata kallon k'ask'anci, ganin yanayin fuskar ta yasa bata ce mata komai ba, wardrobe
Fatuu ta bud'e ta fiddo bargo tazo ta shimfid'a ma Mino a saman Carpet ta d'aukko mata filo, bayan ta
gama tace mata ta kwanta anan, da alamun rashin fahimta tace mata miya faru bazata kwanta a gadon
ba kafin ta bata amsa a fusace Farha tace daga gidan uban su aka kawo shi ne, waro ido Mino tayi baki a
d'an bud'e take kallonta ba tare data ce komai ba dama ita bata da rigima Fatuu ce mai rigimar yanzu
kuma tayi sanyi lakwas, kwantawa Mino tayi itama Fatuun ta zauna a gefenta taci gaba da karatun, bata
dad'e da zama ba taji Farhar ta watso mata zanin gadon dake shimfid'e a kan gadon da duvet harda
pillows, hannu ta kai ta cire bedsheet d'in daya rufe mata fuska rai a 6ace tace mata ba gadon take so a
bar mata ba kuma gashi nan an bar mata miyasa zata watso mata kaya tana yatsina tace ta d'aukko mata
wasu wad'annan an goga masu talauci, sosae ran Fatuu ya 6aci bata dai ce mata komai ba kaman bazata
d'aukko ba sai kuma ta mik'e taje ta fiddo wasu ta kawo mata ta aje akan gadon ganin zata juya tace
mata bazata shimfid'a mata ba ko banda gadon rashin Arzik'i harda gadon rashin iya tarbar bak'o tayi,
bata ce mata komai ba ta shiga shimfid'a mata, bayan ta gama ta koma ta kwashe wanda ta watso ta
linke su ta kai Wardrobe, gaba d'aya Fatuu ta kasa yin karatun don tun bayan data kwanta ta fara kunna
wak'ok'i gashi ta k'ure volume, k'arshe mik'ewa tay ta d'auki books da jakar tata ta fita daga d'akin ta
koma parlor, bata dad'e sosae da komawa ba sai ga Mino ta fito a gigice tana kuka jikinta sharkaf da
ruwa sai kerma take ta nufo cikin parlon, da sauri Fatuu ta mik'e ta tarbeta tun kafin ta tambaye ta
abunda ya faru ta shaida, rai 6ace ta tambayi mi tayi mata ta watsa mata ruwa tace itama bata sani ba
kawai tana cikin bacci taji ta watsa mata su da yawa, duk yadda Fatuu ta so kar tayi kuka ta kasa jurewa
sosae Mino ta bata tausayi, zaunar da ita tayi kan kujera tace tana zuwa, Bedroom ta nufa saida ta tsaya
a bakin k'opa ta goge Fuskar ta sosae sannan ta shiga, tsayawa tay daga bakin gado rai 6ace take kallon
Farha dake latsa waya tace "mi tayi maki kika watsa mata ruwa haka!" banza ta mata sai kace bada ita
take ba, k'ara maimaita tambayar Fatuu tayi saida ta mula sannan ta d'ago ido cike da isa tace snoring
take mata daga haka ta maida idon kan waya, shiru Fatuu tay tana mata wani kallo jin sharrin data ja ma
Mino na wai munshari take mata ita tasan bata yin shi tunda tare suke kwana, tunowa da ta baro Minon
a jik'e yasa ta juya ta nufi wardrobe, kayan da zata canza ta d'aukko da su bedsheet d'in da Farha ta
watso ta kinkima ta fita, bayan ta bata kayan ta canza tayi mata shimfid'a akan Carpet d'in parlon tace ta
kwanta, kallon Fatun tayi ta tambaye ta wacece Farha nan ta bata labarin ta harda dalilin daya sa take
mata hakan,

"to ki fad'a ma Hajiya abunda take mana" shiru Fatuu tay tana nazari can tace mata suyi hak'uri kawai
yanzu in ta fad'i ma Hajiya ta d'auki mataki akanta Mamar ta itama tana iya yi mata wani abun, kamar
Mino zata yi kuka tace to yanzu haka zasu cigaba da zama tana masu haka, shiru Fatuu tay gaba d'aya ta
rasa mike mata dad'i can tasa Kuka bak'in cikinta wanda duk ake mata haka Saboda shi baima damu da
ita ba ganin tana kukan yasa Mino d'in ma cigaba da yi, daina yin kukan Fatuu tayi tace itama ta daina
komai zai wuce bada dad'ewa ba, rok'onta tayi akan Kada ta fad'i ma gwaggo tace to tace ta kwanta,
zaune Fatuu tayi ta kasa cigaba da yin karatun ma idon ta akan Mino dake kwance ta lullube, wani irin
tausayin ta take ji tunani take ko tace ta daina zuwa kwanan saidae tasan dole gwaggo zata tambayi
dalili, haka tay zaune tsawon lokaci sai can dare ya nitsa sannan ta kwanta,

Washe gari da wuri Fatuu tace ma Mino taje gida sai ta k'ara yin baccin acan tace to baiwar Allah harda
ce mata to tazo suje tare tunda ba Makaranta itama tayi baccin tace mata a'a ko taje gwaggo korota zata
yi, kaman bazata tafi ba tsoronta kada ta tafi Farhar tayi ma Fatun wani abu haka dai ta tafi, bayan
tafiyarta Fatuu ta kwashe kayan shimfid'ar ta maida d'aki Farha na kwance baje baje ko salla bata tashi
tayi ba, dawowa parlor Fatuu tay ta zauna tama rasa mi yakamata tayi, tsawon lokaci tana anan saiga
Saude tazo kawo mata breakfast, akan c-table ta d'aura suka gaisa ganin yadda Fatun tayi tsuru yasa ta
zauna tana tambayar ta miya faru a sanyaye tace mata ba komai, tana shirin k'ara yi mata magana sai ga
Farhar ta fito duk suka kalleta ta wurga masu wata uwar harara ta wuce, bayan ta fita da alamun
mamaki Aunty Saude ta kalli Fatuu tace mata mi tazo yi nan ne taga ta fito daga Bedroom, shiru Fatuu
tay ta sunkuyar da kanta nan take Aunty Saude ta gane da wani abu dama gashi ta isketa tsuru a parlor,
matsa mata tayi kan ta fad'i mata Fatun ta fara fad'i mata duk abunda tayi masu da cewar da tayi zata
saka mata poison a Abinci tana yi tana goge kwalla, ran Saude ne ya 6aci tace aikuwa yanzu zata je ta
fad'i ma Hajiya dama ita tasan ba abun Arziki ya kawo ta ba, rik'eta Fatuu tay ta hau yi mata Magiya kan
karta fad'i na Hajiya tunda tasan ba dundundun ta zo ba ta k'yaleta tayi ta gama yanzu in aka fad'i ma
Hajiya tana iya cewa ta koma gida kuma Hajiya Maryam zata ga an korar mata D'iya Saboda ita koma
bata yi niyyar yi mata wani abu ba hakan na iya sawa ta cutar da ita tunda dama gani take suma kamar
asiri sukai ma Hajiyar, shiru Aunty Saude tayi tana nazarin Maganar, da damuwa tace to yanzu haka zata
k'yaleta tay ta mata rashin mutunci, d'an murmushi mai cin rai Fatuu tay tace mata ba komai kawae dai
tana son ta taimaka mata zata daina zuwa cin Abinci bata son Hajiya ta gane koda tayi mata Magana
tace tana zuwa amsa ala bashshi sai ta rink'a dafawa kawai, cewa Saude tay ta bari zata rink'a kawo
mata tasan yadda zatayi Hajiyar bazata tuhumi dalilin daina zuwan nata ba Fatun tace ta barshi kawae
tunda akwae kayan Abincin tace amman ya za'ai ace sai ta dawo daga Makaranta sannan ta dafa kawai
zata cigaba da kawo matan in yaso randa ba Makarantar sai ta dafa tayi mata godiya.
A daddafe tayi Weekend d'in nan, Ranar Monday tunda taje Makaranta Fauzy ta lura da yanayin ta tana
cikin damuwa don har fad'awa fuskarta tayi, bayan anyi break ne ta tambaye ta abunda ke damunta nan
ta kwashe game da abubuwan da Farha take mata ta fad'i mata, tun kafin ta gama yanayin fuskar Fauzy
ya canza bayan ta gama fad'i mata rai a matuk'ar 6ace tace "inta fasa kashe ki bata haihu K'wara ba don
ubanta! ke kika k'yaleta wllh" yamutsa Fuska Fatuu tay tace to ya zatayi, a hasale Fauzy tace "wane ya
zaki yi, ba ita take neman ki da rigima ba, kamata zaki ki lakad'a mata shegen duka kinsan dama irin haka
sai kun had'a jiki mutum yaji a jikinshi sannan yake shiga taitayin shi" sakin baki Fatuu tay tana kallonta
Fauzyn tace "ko tafi k'arfin ki ne? In tafi k'arfin ki ni ki bari in zo mu had'u mu had'a mata jini da mijina
wllh zaki ga ta kiyaye ki" da sauri Fatuu ta hau girgiza mata kai tace ba zasu yi haka ba a kyaleta kawai, a
hasale Fauzy tace "Wato kin fi son tay ta cusa maki bak'in ciki ko har wani ciwon yazo ya kamaki ga
jarabawa a gaban mu" watsa hannu Fatun tay ta yamutsa fuska kamar zatai kuka tace "Fauzy ko mi zatai
man tayi ba kowa yaja man ba face Ya Haisam, duk abunda ake man Saboda shi ne kuma shi bai damu
dani ba ya tafi ya barni Saboda bai sona, na tabbatar da yana sona ba yadda za'ai ya tafi tsawon wata
guda da rabi ba tare da ya waiwaye ni ba tunda yana da halin ko duk sati yaso zuwa nan hakan ba wani
abu bane a wurin shi, ni na rasa gane kan wannan Auren namu da yasan haka zai man da tun farko bai
amince yaci gaba da zama dani ba, in don abunda ya faru ne naje na bashi hakuri kuma yace ya hak'ura
to miyasa ya canza man, miyasa bai damu dani ba...., miyasa son shi yak'i barina kwata kwata, miyasa
nike tunanin shi tunda shi bai damu dani ba....miyasa ba zai sake ni ba kawai in San ban tare dashi ko na
cire shi daga cikin zuciya ta....." tana Maganar k'walla na zubo mata har tazo ga6ar da ta saki kukan mai
cin rai ta fad'a jikin Fauzy da itama kwallan ne suka fara zubo mata, wani irin tausayin ta da bata ta6a ji
ba ya kamata ta shiga d'an bubbuga bayanta tana rarrashin ta, ita kanta ta fara kokonton anya Ya
Haisam na son Zarah kaman yadda suke hasashe kuwa, zuciyar ta ce ta fara raya mata aikata wani
abu......

Kafin a tashi tace ma Fauzy zata rink'a bin ta Hostel sai yamma ta koma gidan don gaba d'aya bata jin
dad'in gidan tace to Hajiya fa ba matsala taga bata komawa da wuri tace zata fad'i mata suna tsayawa
karatun jarabawa ne tasan zata fahimta tace to, kiran Tk tayi ta sanar dashi kada yazo d'aukar ta ya
d'aukko Mino kawai ita sai yamma zata dawo kuma ba sai yayi wahalar zuwa d'aukarta ba zata hau Keke
Napep, bayan an tashi suka nufi Hostel, suna zuwa salla suka fara yi bayan sun gama Fauzy ta had'a mata
Madara da biscuit tace ta fara sha bari ta dafa masu Abinci, tana gama sha lokacin Fauzy na cikin dafa
masu Abincin ta mik'e tace bari taje ta watso ruwa har Fauzy nace mata zata iya shiga toilet d'in su kuwa
tana yar dariya tace mi zai hana, cire kayanta tayi ta d'aura towel Fauzy ta kalleta tace mata wllh duk tayi
d'an wuya tay murmushi kawai, bayan fitar ta Fauzy ta mik'e ta nufi inda ta tashi ta zauna ta kai hannu ta
d'auki wayarta, zurfin tunanin anya Ya kamata tayi abunda take tunanin yi kuwa ta shiga, fargaba ce tay
mata yawa ta maida wayar ta aje ta bar wurin, bayan Fatun ta fito tace ma Fauzy ta bata yar riga mara
nauyi tasha iska kafin ta tashi tafiya ta d'aukko mata, bayan ta gama saka rigar hayewa tay saman gado
ta kwanta suna d'an yin hira da Fauzy, a hankali ta fara lumshe ido Fauzy na fad'in kada tayi bacci bata ci
Abincin ba tace ai ba yunwa take ji ba in ma tayi sai ta ci in ta tashi, baccin ne ya dauketa Fauzy ta zuba
mata ido tana ta wasi wasin abunda take son yi acikin zuciyar ta can ta mik'e ta nufi gadon da take ta kai
hannu ta d'aukko wayarta ta dawo ta haye saman gadon zuciyarta nata harbawa hannuwanta har d'an
kerma suke ta shiga daddana ta......."

____________________

Fanan zaune asaman doguwar kujerar dake a cikin parlon su ta haye saman ta gaba d'aya tana sanye da
yar fingilar riga da iyakarta tsakiyar cinyoyinta hannun ta kuma irin na vest kaman dai rigar bacci ce ta
d'an rankwafa tana lallatsa computer d'in dake gabanta hakan yaba brown gashin ta damar zubowa ta
gefe da gefen fuskar ta, daga gefen ta kuma takardu ne lokacin su can dare ne don har anyi sallar isha,
tun bayan da Haisam ya aje wayar shi ya tafi had'o masu Coffee take ta damun ta da k'arar notifications,
dakatawa tay ta kai hannu ta d'aukko wayar don ta kashe Wi-fi d'in wayar ko sakonnin sun daina
shigowa, tana latsa power haske ya kawo jikin Screen d'in idon ta ya sauka akan sunan da tasan ya saka
ma Fatuu alamar ta turo mashi sako, d'an murmushi Fanan d'in tayi a ranta ta raya wato da ita ne ta
daina zumunci kenan, bayan ta kashe ta maida wayar ta aje, har taci gaba da abunda take kawai taji tana
son ganin sak'on miye Zarah ta turo mashi, hannu ta kai ta d'aukko wayar ta sake kunna hasken ta bud'e,
kan sakonnin WhatsApp ta danna ta shiga ciki, sak'on Fatuu ne last da aka turo hakan yasa ya kasance a
sama ta kai hannu ta ta6a ya bud'e, gyara zama tayi ta fara Karantawa...................

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

* ASM 071*

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.........A nutse ta fara karanta sak'on wanda ke bayyana sirrin zuciyar wadda ta turo wato Zarah, bayanin
tun lokacin da Allah ya jarabeta da son shi da irin wahalar da ta sha hakane ma yasa ta amince ai mata
Aure Saboda ta rasa shi har Allah ya juya Al'amarin ya aureta, Hak'uri ta bashi kan zargin shi da tayi ta
nuna bata san akwai Aure ba a tsakanin su kuma Saboda son da take mashi ne yasa taji zafin abun sosae
hakane ma yasa data samu ciki tak'i saurarar shi harta 6arar don kuma bata son girman shi ya zube a
idon mutane duk don k'aunar shi da take, a k'arshe ta nuna mashi tana cikin mawuyacin hali Saboda
canza mata da yayi a yanzu da burinta ya cika ta zama Matar shi, Hak'uri ta k'ara bashi tace in don cikin
da ta 6arar ne yake nuna mata halin ko in kula in sha Allah zata biya shi fin shi ma amman tana a cikin
matsananciyar damuwa da har tana son shafar karatun ta........., Tun Fanan na karantawa lafiya lau har
ta kai yanayin Fuskar ta ya fara sauyawa, lokacin data gama karantawa d'agowa tay da yanayin
d'aurewar kai ta kallo hanyar Kitchen da Haisam ke ciki, k'ara maida idonta tayi akan Screen d'in tana
sake biya sak'on lokaci guda hannuwanta suka fara yin kerma ta zuro da fararen k'afafuwan ta k'asa,
Slowly ta mik'e har lokacin tana cikin k'ara karanta sak'on, saida ta karanta shi sau ukku tamkar mai yin
hadda, gaba d'aya ta kasa gasgata abunda take karantawa gani take kamar ba daidai take karatun ba ko
kuma ba sak'on Haisam d'in bane hakan yasa sai k'ara maida idonta take tana k'ara karantawa, zuciyar ta
ce ta shiga gasgata mata sak'on shi ne in ba haka ba mizai sa ta turo mashi kuma ga alamu nan a
bayyane har sunanta an ambata a ciki kan ciwon da ta yi lokacin da Fanan d'in tazo......."Kenan Auran
Zarah ya yi a 6oye???" ta fad'a acikin ran ta, wani irin bugu zuciyarta ta shiga yi mata ta fara numfashi da
k'arfi har saida ta d'an bud'e baki jin numfashin na neman yi mata wuyar fitarwa, tana haka Haisam ya
shigo cikin parlon yana sanye da wando 3 quarter da armless hannuwan shi duka biyun ruk'e da mug
d'an tiriri na fitowa alamar abun ciki mai zafi ne, wani irin kallon tashin hankali ta shiga bin shi da shi
hakan yasa shi dakatawa daga d'an gabanta yana kallon ta shima har saida gaban shi ya d'an fad'i ganin
yanayinta da kuma wayar shi dake hannunta don yanayin kallon da take mashi na tuhuma ne, nufo shi
tay a fujajen tana zuwa fuska a hautsine ta d'aga mashi wayar shi dake hannunta daidai kan sak'on a
kid'ime tace "Don't tell me dis message is for you!!!" maida idon shi yay akan Screen d'in ya gane Zarah
ce ta turo saidai bai fahimci miye akace a sak'on ba, wucewa yay yaje ya aje mugs d'in akan c-table ya
juyo lokacin itama ta juyo tana kallon shi, hannu ya kai ya amshi wayar ya fara karanta message d'in a
nutse har ya gama, d'agowa yay ya kalleta ta kafe shi da idanunta da ta zaro Fuskarta har ta fara yin ja
alamar motsuwar jini, shiru yay kawai yana kallonta yama rasa mi zai ce mata don komai sak'on ya
bayyana, girgiza kai ta shiga yi tana fitar da numfashi da k'arfi cikin d'an k'araji tace "so it's true, You
married Zarah without my knowledge!" still bai ce mata komai ba aikuwa ta daka mashi tsawa a gigice
tace "tell me! is she ur Wife??" d'an cize lip d'in shi yay na k'asa Slowly ya lumshe mata ido nan take ta
gane mi hakan ke nufi, cikin fitar hayyaci ta fara ja da baya tana cigaba da girgiza mashi kai, bin ta ya fara
yi yana ce mata "I can explain myself..." a haka har ta dangane da kujera kawai sai ta haye saman ta
gudun kada ta yi ma kanta wani abu yasa shi kai hannu zai kamo ta ai kuwa ta tafi gaba d'aya ta wuntsila
bayan kujerar ta fad'a saman tiles daga jin k'arar ba K'aramin bugawa tay ba, juyawa yay da sauri ya
zagaya lokacin har ta mik'e tana k'ok'arin rugawa d'aki cikin zafin nama ya kamota ta fara kokowar
kwacewa cikin k'araji fuskarta da idanunta sunyi jawur take fad'in "Leave me alone! Ya Haisam u'r a
betrayer! u betrayed my trust, u broke the promise u have made to me! U deceived me....!" Gaba d'aya
bata a cikin hayyacin ta idanunta sun jik'e da k'walla fatar k'asan idon tayi wani irin ja kamar jini, sai
kiciniyar k'wace kanta take ta kansa sai rarrashinta yake yana ta tsaya zai mata bayanin yadda hakan ta
faru amman ina tak'i sauraren shi fad'i take ba abunda zai fad'i mata ta san don ance tana da matsala
shiyasa yayi tunanin bazata haihu ba yaje ya auri Zarah gashi nan har yayi mata ciki duk da Alk'awarin da
yayi mata, abu fa ya ture gaba d'aya Fanan ta burkice mashi duk ta rud'a shi har fuskar shi ta bayyana, da
dai taga ta kasa kwacewa kawae sai ta kai bakinta a jikin damtsen shi dake a bayyane ta daddage ta
gartsa mashi cizo aikuwa ba Arzik'i ya saketa Saboda rad'ad'in Azabar da ya ratsa shi wurin har ya fashe
nan da nan jini ya fara zubowa, ai yana sakinta ta watsa a guje hanyar Bedroom yana ganin haka shima
ya bita don ya fahimci abunda take son aikatawa haka take da ranta ya 6aci sai ta ruga ta kulle kanta a
cikin d'aki, ko kafin ya cimmata tuni ta shige lokacin daya kai hannu cikin zafin nama zai bud'e kopar data
turo tuni har tasa Key, bugun k'opar ya fara yi da d'aga Murya yana kiran sunanta yana ta bud'e karta yi
ma kanta illa, tana shiga d'akin a haukace ta nufi bango ta fara kai mashi bugu tana wani irin kuka na
fitar hayyaci, har saida knuckles d'inta suka fara fitar da jini sannan ta daina ta nufi gado ta zauna dabar
tana cigaba da kukan, a ranta ta fara tariyo sak'on aikuwa ta k'ara tsananta kukan ta fara sambatu tana
fad'in Ya Haisam da Zarah sun ci amanarta, tunowa da Maganar ciki da ta samu tasa ta kai hannu ta fara
bugun Katifar hakan bai sa ta samu sassaucin abunda take ji ba acikin zuciyarta sai ma k'ari nan fa ta
mik'e ta fara wurgi da abubuwa abun har ya kai da fashe fashe, gaba d'aya hankalin Haisam ya gama
tashi sai faman bugun k'opar yake da k'arfi yana kiran sunanta yana fad'in kada tayi ma kanta wani abu
ta bud'e kopar, har ta kai ya fara mata Magiya ko tana jin shi ma oho ba dai alamun zata bud'e,

sintiri ya shiga yi tsakanin Window wadda itama take a kulle da kuma kopar yana tunanin Mafita, zuciyar
shi ce ta bashi ya fara bugun kopar k'ilan yaci sa'a ta bud'e duk da yasan mawuyacin abu ne don
dakakkar k'opa ce, ba irin bugun da bai ma kopar ba iyakar k'arfin shi amman ba alamun zata bud'e dole
ya dakata don shi kan shi ya gaji, Hajiya ce ta fad'o mashi a rai a rud'e ya nufi cikin parlon inda Fanan ta
jefar da wayar ya nufa ya d'auka, tana fara yin ringing Hajiyar ta d'auka ko gaida ita bai yi ba ya shiga
fad'i mata abunda ke faruwa itama rud'ewa tay ta shiga tambayar shi dama bai sanar mata ba duk da
tasan inda ya sanar mata zata ji kawai ta rud'e ne, ce mata yay eh ya bari yayi 2 Months da dawowa sai
ya d'auki hutun da basai an rink'a biyan shi ba su taho nan Nigeria su kwana biyu lokacin sai ya sanar
mata dama irin haka yake gudu shiyasa, tambayar shi tayi to yanzu ya akai ta sanin yay d'an jimm
hakanan sai yaji baison fad'i mata zancen sak'on da Zarah ta turo sai yace mata kawai a Wayar shi ta
gane, ce mashi tay to yayi k'ok'ari ya 6alle kopar mana yace mata ba irin k'ok'arin da bai yi ba tak'i
bud'ewa, tambayar shi tayi anan ba masu aikin 6alle k'opa ne sai lokacin ya tuna da sauri yace mata ba'a
rasawa tace to yay hanzari don Allah ya kira azo a bud'e kar wani abu ya sameta ta razana ne sosae ba ta
haka yakamata ta sani ba.
Bai san ina zai samo wanda zai 6alle kopar ba amman da yake yana a K'asar da aka cigaba ne komai
k'ank'antar sana'ar mutum zaka samu ya d'aura a internet, yana yin searching sai gashi ya samu, kiran su
yay a waya ya fad'a masu aikin da yake so ayi mashi da Address d'in gidan, bayan sun gama komawa yay
wurin d'akin yana cigaba da knocking wai ko zata bud'e amman shiru abunda ma ya k'ara tayar mashi da
hankali jin shiru bai jin wani motsi sa6anin da yana d'an jin k'arar abubuwan da take yi, kai da komowa
ya shiga yi duk fuskarshi ta harmutse, bada jimawa ba sai ga mai 6alle kopar ya iso, ba 6ata lokaci ya
6alle Haisam har yana yin tuntu6e Saboda saurin ya shiga, a kwance ya isketa k'asa ya nufeta da sauri ya
duk'a, ganin bata motsi yasa a rud'e ya kai hannu ya fara jijjigata yana kiran sunanta yana ta bud'e
idonta, gaba d'aya bata numfashi ga hancin ta duk jini alamar tayi ha6o haka hannuwanta ma glass ya
d'an yayyanke ta, da sauri ya mik'e ya nufi closet ya bud'e ba tare daya tsaya za6a ba ya janyo wata
doguwar riga dake sagale da mayafinta ya dawo inda take ya fara k'ok'arin zura mata, kinkimar ta yayi da
taimakon wanda ya balle kopar aka sakata a Mota bayan ya sallame shi ya shiga yajata da gudu ya fice ko
tunanin ya canza kaya bai yi ba,

Tun bayan da Fauzy ta tura sak'on tay zaune tsuru gabanta na cigaba da fad'uwa sai fargabar abunda zai
je ya dawo take a ranta ta shiga yin Addu'ar Allah yasa in yaga sak'on komai ya daidaita tsakanin su,
saida aka kira sallar la'asar sannan ta tada Fatuu don tayi salla, bayan ta gama ta zuba mata Abincin ta
fara ci, ta lura da yadda Fauzyn keta faman bin ta da ido hakan yasa ta tambaye ta lafiya ta d'an yi
murmushi tace mata ba komai, kokonto Fauzy ta shiga yi na kodai ta fad'i mata kar daga baya ta gane
taga tayi mata ba daidai ba, zuciyarta ce ta bata gara ta fad'i mata kawae in ma ta nuna bata ji dad'i ba
sai ta bata hak'uri, bayan ta gama cin Abincin ne ta fara shirin tafiya, saida ta gama shiryawa ta maida
Uniform d'inta sannan Fauzy tace mata tana son zasu yi magana, zama tayi a bakin gado Fauzy na facing
din ta a d'ayan gadon a sanyaye tace "na maki katsalandan Zarah nasan yana iya zama laifi a wurin ki" da
alamun mamaki tace laifi kuma wane irin laifi, Wayarta dake ajiye gefenta ta d'auka ta bud'o sak'on data
tura ma Haisam ta mik'e ta kai mata,

zuba ma Screen d'in ido Fatuu tayi tana karanta sak'on, tun kafin ta gama ta zaro ido ta kai hannun ta
guda ta rufe baki alamar Al'ajabi, bayan ta gama karantawa ta d'ago tana kallon Fauzy dake tsaye gefe a
rud'e tace "Fauzy miyasa kikai haka don Allah? Miyasa zaki tura mashi wannan sak'on haka?" Kamar zata
yi kuka ta k'are Maganar tana yamutsa fuska idanunta har sun ciko da k'walla, zama Fauzy tay daga
gefen ta cikin kwantar da murya tace "kiyi hakuri Zarah dama nasan ba lalle Kiji dad'in abunda na aikata
ba, wllh tausayi kike bani ne abubuwa sun maki yawa daga wannan sai wannan ina gudun damuwar
hakan tasa kizo ki fad'i Exam shiyasa nayi tunanin idan na tura mashi bayanin komai tunda shi mutum ne
mai tausayi watak'il hakan yasa ya karkato da hankalin shi gare ki, nasan da kin samu kulawar shi zaki
samu kwanciyar hankali" girgiza kai Fatuu tayi kwallan idonta suka fara zubowa tace ita dai da bata
aikata hakan ba don hakan tamkar zubar da k'imar ta ne kuma yanzu koda bai son ta dalilin hakan zaisa
ya cigaba da zama da ita Saboda tausayi ita kuma bata son hakan gara in bai sonta kawai su rabu, ganin
yadda ta damu yasa Fauzy kama hannunta tace "ba wata k'imar ki da zata zube kar ki manta shi Mijin ki
ne kuma dana bayyana mashi kina son shi ai kinga nace Allah ne ya jarabe ki shima yasan bake kika
d'aura ma kan ki ba kuma tunda shi ba mutum bane mai wulakanci hakan bazai sa ya wulakanta ki ba sai
ma kulawa dake, kuma ni nasan ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba koda kin nuna mashi ya sake ki
bazai ta6a sakin ki ba domin da zaiyi hakan ai da bazai ma cigaba da zama dake ba gashi har mahaifin shi
ya kar6e ki, uwa uba kuma Hajiya da take iko dasu gaba d'aya ita ta goyi bayan kuci gaba da zama tare
kinga gara ya san kina son shi koda shi bai son ki in yana kula ki sai ki koya mashi son naki" a marairaice
take Maganar, ita dai Fatuu sam hakan bai mata dad'i ba wllh sai yamutsa fuska take tana kwalla, k'ara
duba sak'on ta shiga yi lokacin ta lura da marking d'in da yayi bai yi blue ba hakan yasa ta fara tunanin
koma bai duba ba to, zuciyarta ce ta fara gasgata mata hakan ta shiga raya da ya gani tasan k'ilan ya ce
wani abu don da wuya ya shareta, yin wannan tunanin yasa da sauri hannunta har yana rawa tayi delete
for everyone duk Fauzy na kallon ta, wani sanyi taji a ranta fuskarta ta daidaita, ganin haka yasa Fauzy
bata hak'uri tace tunda bata ji dad'i ba ta yi Addu'ar Allah yasa ba Gb WhatsApp gare shi ba Fatun tace
mata ba komai tasan don Farincikin ta tayi hakan amman tafi son ya zauna da ita don yana son ta ba don
tausayi ba idan ya dawo da kanta zata rok'eshi kan ya saketa, harda cewa in ma ya k'i zata ce mashi tana
da wanda take so ne Fauzy tay d'an murmushi kawae a ranta ta raya fad'i kawai take tasan ba iyawa
zatai ba don ba K'aramin kamu son shi yay mata ba, tare suka fito da Fauzy ta rako ta, ganin Fauzyn duk
tayi sukuku yasa Fatuu bata hak'uri tace in ta 6ata mata rai Fauzyn tay murmushi tace a'a wllh ai ita zata
ba hak'uri tayi mata ba daidai ba, Fatun tace itama bata d'auke shi a wani abu ba, saida ta hau Keke
Napep sukai sallama tace ta gaishe mata da Mino sannan ta koma.

Asibitin da take aiki ya kaita, nan da nan aka nufi Emergency da ita bayan Haisam d'in ya masu bayanin
ta razana ne kuma ranta ya 6aci sosae, nan da nan likitoci suka taru kanta duk abunda ake mata Haisam
d'in na gani ta faffad'an window d'in d'akin da yake gaba d'ayan shi transparent glass ne, Bayan wasu
mintuna d'aya daga cikin likitocin ya fito ya sanar dashi tayi doguwar suma ne za'a bata treatment d'in
daya dace zuwa kowanne lokaci zata iya farfad'owa, sai lokacin Haisam ya d'an ji hankalin shi ya kwanta
da gaba d'aya jinin shi akan akaifa yake tsoron shi kar ace ta samu heart attack, daga baya bayan likitocin
sun fito ya shiga cikin d'akin, a kan kujera dake a gefen gadon ya zauna yana kallon Fanan dake kwance
fuskar ta sanye da Oxygen mask, a ranshi yake raya irin abunda ya guda kenan yasa bai fad'i mata ba don
yasan fin hakan na iya faruwa, yana zaunen nurse ta shigo suka gaisa ta nufi gadon Fanan d'in, bayan ta
gama abunda zatayi har zata fita sai kuma ta tsaya ta kalli Haisam d'in da murmushi ta nuna damtsen shi
da jini mai d'an yawa ya taru tace mashi ya samu rauni ne, ce mata yay eh tace bari tayi mashi dressing
d'in wurin yay mata godiyar kulawa, bayan ta gama mashi zaune yay shiru nan ya fara tunanin sak'on da
Fatuu ta turo mashi, wayarshi dake ruk'e a hannun shi ya d'ago ya bud'e ya shiga cikin WhatsApp, koda
ya bud'e chat d'in Fatuu sai ya ga an goge sak'on, wani kalan murmushi ya saki yay d'an jimm sai kuma
ya fita daga chat d'in, Hajiya ya kirawo dama koda yana kan hanya da zai kawo Fanan d'in saida ta kira ta
tambayi halin da ake ciki don ta kira bai d'auka ba hankalin ta ya k'ara tashi, fad'i mata yay an 6alle kopar
da yanayin da ya iske Fanan d'in yace gashi ma a hanya zai kaita Asibiti,
Har bayan wani lokaci bata farfad'o ba k'arfe sha biyu da wasu mintuna ya bar Asibitin don su ba'a
kwana wurin mara lafiya duk abunda yakamata za'ai mashi sai dae in buk'atar ganin wani nashi ta taso a
kira, yana driving yana tunanin sak'on Fatuu har ya iso gida, bayan ya shiga parlor ya tsaya ya d'auke
Computer d'in Fanan da wayarta dasu takardun da ke ajiye ya nufi ciki, Bedroom d'inta ya wuce ya ajiye
su ya fara gyara shi, lokacin daya dawo Bedroom d'in shi toilet ya wuce yayo wanka bayan ya fito d'aure
da towel ya tsaya gaban mirror yana tsane ruwan jikinshi da short towel d'in daya ruk'o, gaba d'aya
Fuskar Fatuu yake ganin tana mashi gizo a cikin Madubin sai d'an sakin Murmushi yake, bayan ya gama
ya nufi closet ya fiddo kayan bacci ya saka, bayan ya kwanta tunanin abu biyu ya shiga yi wato Fanan da
Fatuu sak'on data turo mashi sai yawo yake mashi a rai, bazaka ta6a gane yadda ya ji ba dangane da
sak'on daga yanayin Fuskar ta shi.

Washe gari bayan ya dawo daga sallar Asuba a Motar shi ya fito jikin shi sanye da farar jallabiya,
Bedroom d'in shi ya wuce ya cire rigar ya bar short d'in jikin shi da singlet ya fito ya nufi Kitchen don
had'a ma Fanan Breakfast koda zata farfad'o in yaje, Misalin k'arfe takwas na safiyar ya gama shiryawa
cikin k'ananun kaya ya fito ya wuce Kitchen, bayan ya d'aukko basket d'in da ya zuba kayan breakfast
d'in ya fito ya tafi, Har lokacin daya je bata farka ba ya aje basket d'in ya zauna, after some minutes ya
mik'e yaje yay ma Nurse d'in dake kula da ita magana kan zaije ya dawo, bayan ya fito daga Asibitin
wurin aikin shi ya wuce don yaje yay reporting kan ciwon matar ta shi. Wuraren k'arfe goma ya dawo still
bata farka ba ya zauna idon shi akanta daga baya ya fara latsa wayar shi, bayan kusan awa guda da
dawowar shi ta fara motsi yana ji da sauri ya kai idon shi kanta, a hankali ta fara motsa idanunta ta fara
bud'e su tana yi tana lumshe su, tashi yay ya nufi gadon ya tsaya daga gefen inda kanta yake yana kallon
ta, k'amshin turaren shi da ya cika mata hanci ne yasa ta bud'e idanun suka sauka a kan Face d'in shi, bin
juna sukai da kallo Fuskarta har ta d'an fad'a, cikin cool voice d'in shi yace mata sannu aikuwa tamkar ya
tuna mata da abunda ya faru ta kai hannu ta cire Oxygen mask d'in fuskarta, tashi tay zaune cikin fushi ta
fara k'ok'arin cire cannular d'in k'arin ruwa da aka saka mata Haisam d'in na ta bari amman tamkar ma
zuga ta yake, tana gama cirewa ta saukko daga saman gado ta kai hannu ta d'auki veil d'in rigar jikinta ta
yafa saman kanta ganin abunda take shirin yi yasa shi zagayawa yasha gabanta ta fara k'ok'arin ture shi,
ruk'e hannunta yay ya fara lallashin ta yana tayi hak'uri a gama dubata in sunje gida zai mata bayanin
komai, a fusace take fad'in ya bata hanya ta wuce bin ta yay da ido sai kace ba Fanan d'in daya sani ba
mai yi mashi biyayya sam bata tsallake Maganar shi, Nurse ce ta shigo ganin abunda ke faruwa yasa ta
juya taje ta kira Dr, bayan ya shigo ya tambayi abunda ke faruwa Fanan d'in tace mashi gida zata tafi
rarrashinta ya shiga yi shima kan ta bari ta samu sauk'i sosae ta kafe sai ta tafi fuskarta ba alamun
sassauci k'arshe dole suka k'yaleta ta tafi, Haisam na niyyar bin bayanta Dr ya tsaida shi Magana yayi
mashi kan halin da take ciki yace yayi k'ok'ari aga ta rage 6acin ran ko kuma ma asan yadda za'a rabata
dashi don a halin da take ciki akwae yuwuwar ta iya samun heart attack saboda 6acin ran yayi yawa
gashi har jininta ya hau, godiya Haisam yay mashi bayan ya gama mashi bayanin, koda ya fito harabar
Asibitin bai ganta ba ya nufi inda ya parker Motar shi ya shiga, bayan ya fito daga Asibitin bai yi nisa
sosae ba ya ganta a tsaye bakin titi, tsayawa yay ya sauke glass ta cikin Motar yay mata magana kan ta
shigo su tafi amman ko kallon shi bata yi ba k'arshe ma sai taci gaba da tafiya gashi ba damar ya parker
don ba'a parking a wurin, bin ta yaci gaba da yi da Motar har saida ta tsaida taxi ta shiga ya bi bayan su,
bayan ta sun iso tana shigowa cikin gidan ta nufi Bedroom, wayar ta data hango saman bedside ta nufa
ta d'auka, gefen gado ta zauna sai nishin 6acin rai take ta shiga kiran Mom d'inta, tana d'auka ta saka
mata kuka a tsananin rud'e Hajiya Maryam ta shiga tambayar ta abunda ke faruwa cikin kukan tace mata
Ya Haisam yaci Amanarta ya yaudare ta duk da Alkawarin da yayi mata yaje yayi aure bada sanin ta ba,
cikin 6acin rai Hajiya Maryam ta tambaye ta shine ya fad'a mata tace a'a Wadda ya auran ce ta turo
mashi sak'o ta gani, nan ta shiga fad'i mata halin da ta shiga, sosae Hajiya Maryam ta razana da jin a
Asibiti ta kwana ta shiga kwantar mata da hankali tace itama tasan da Maganar Hajiya ta kira su ta fad'a
masu ta nuna bata amince ba yanzu haka ma tana k'ok'arin raba su ne, cikin kuka Fanan d'in tace mata
ita dae gida zata taho da sauri tace mata eh ta taho harda tambayar zata iya ko tazo ta taho da ita tace
a'a zata taho, k'ara lallashinta ta shiga yi sosae tana kwantar mata da Hankali tace dole ma a raba Auran
tunda bada izinin su aka yi shi ba, duk Maganar da take Haisam na tsaye daga gefen gadon tasan yana a
wurin jin k'amshin turaren shi kuma taga lokacin daya shigo ta wutsiyar idon ta, tana gama wayar ta
ajeta saman gadon ta mik'e, wardrobe ta nufa tana zuwa ta bud'eta, kayanta ta fara kwasowa ta kawo
saman gadon tana shirin juyawa ta sake d'ibowa taji ya ruk'o hannunta, cikin fushi tace ya sakar mata
hannu ba tare data juya ta kalle shi ba jin bai saki ba yasa ta juya a fusace tace "I said leave my hand!"
kallonta kawai yake sam bai yi mamakin yadda take mashi ba don iya fuskarta kawae ta bayyana
tsananin 6acin ran da take ciki, girgiza kai ta fara yi idanun ta suka ciko da k'walla cikin karyayyar murya
ta fara fad'in "I feel deeply betrayed and disappointed by ur action, you broke a promise to me and now
I can't trust you anymore...." Dakatawa tay tana fitar da numfashi da sauri kirjinta na hawa da sauka,
sigh yay yana son mata magana yama rasa ta ina zai fara, k'ok'arin matso da ita yay don ya rungumeta
aikuwa a fusace tace "Don't...!!!" ganin kallon da yake bin ta dashi ne yasa ta d'an sassauta murya
idanunta na cigaba da zubar da k'walla tace "I can't believe dat you would betray my trust like this, u
don't even care weather am gonna die.....Na daina son ka Ya Haisam! na daina, our relationship will end
now sai kaje ka d'aukko Zarah kici gaba da Zama da ita" k'ok'arin fuzge hannun ta fara yi aikuwa ya
janyota ta fad'o jikinshi ya sa duka hannuwanshi ya rungume ta gam ta yadda ko motsin kirki bazata iya
ba, Kuka ta sakar mashi tana fad'in Ya saketa, ta tsane shi bazata cigaba da zama da shi ba, ganin bazata
iya kwacewa ba yasa ta kifa Fuskarta a saman faffad'an chest d'in shi ta shiga raira kuka mai cin rai, Sigh
yay ya kai bakin shi saitin kunnen ta cikin Magana mai kaman rad'a yace "am deeply sorry Fanan, I know
I have wronged u, amman ban ci Amanar ki ba, lokacin da nayi maki Alk'awari Already akwai aure
tsakanina da Zarah, if u could remember ban so yin Alk'awarin ba a lokacin" dakatawa yay dama tamkar
Maganar na mashi wuya yake furta ta, shiru tay bata ce komai ba sai sheshsheka take, Cigaba yay "Now
give a chance to explain Everything pls" shiru tay mashi saidae shesshekar da take ta ragu hakan yasa ya
gane ta bashi damar, sakinta yay ya kama hannunta suka nufi bakin gado, zaunar da ita yay shima ya
zauna ya juyo yana kallon ta ita kuma idonta na gefe, a nutse ya fara mata bayanin komai yadda akai Ya
Auri Fatuu saida ta ji yayi shiru sannan ta juyo ta kalle shi still fuskarta a d'aure take tace mashi to miyasa
ya kwanta da ita, d'an jimm yay kafin yace mata bada niyya bane shima baisan ya akai ya aikata hakan ba
kuma ita kanta lokacin bata san ya aureta, shiru tay tana tunano sak'on data turo mashin a ciki ta
bayyana bata san da aure a tsakanin su ba shiyasa ta zubar da cikin hakan yasa Fanan d'in gasgata
Maganar ta shi wata zuciyar ta raya mata to amman miyasa zai nuna 6acin rai don ta zubar da cikin,
kallon shi tay cike da tuhuma ta tambaye shi kan hakan tace kenan dae yana son Auren, nan ma saida
yay d'an jimm kafin yace mata ita kanta ai tasan had'arin dake tattare da zubar da ciki hakan ne yasa
bayan ta sanar dashi game da cikin tace zata zubar ya hanata gudun kada wani abu ya faru amman sai
tak'i jin Maganar shi taje ta aikata sai gashi abunda ya gudan har kwanciya tayi Asibiti dalilin hakan, ji tay
ta yarda da zancen shi hakan yasa ta d'an saki fuska tace mashi to tunda don taimako ya aureta ai sai ya
saketa ko, ce mata yay Hajiya ta hana yanzu haka tasa an Kawo Zarah d'in part d'in shi, wani kalan d'aure
Fuska tayi tace tunda shine mai zama da ita kuma bai so don me za'ai mashi dole, ce mashi tay ita
gaskiya bazata zauna da Zarah matsayin kishiya ba in dai basu rabu ba to ita ta hak'ura da auren kuma
yaci Amanarta, jin yayi shiru yasa tace mashi kawai ya tura mata sakin kaman yadda ta turo mashi
sak'on, sai da ya nisa sannan ya d'an girgiza mata kai yace tunda Hajiya bata so bazai iya yin hakan ba
tasan yadda take a wurin su, hakan ya k'ara 6ata mata rai tana d'an huci tay shiru tana d'an kallon gefe
can ta jinjina kai ta kalle shi tace mashi suje Nigeria d'in tare ita zata ma Hajiya Magana shiru yay kawae
yana kallonta ganin haka yasa da alamun zargi tace kodai dama shima yana son ta, d'an guntun
murmushi yay yace mata kawai bai son a samu matsala ne dalilin hakan cike da tabbaci tace mashi ba
wata matsalar da za'a samu tasan Hajiya zata goyi bayan abunda take so tunda dai duk basu son Auren,
jinjina mata kai yay yace Shikenan ta tambayi yaushe zasu tafi yace nan da 2 weeks da sauri ta girgiza
mashi kai tace mashi gaskiya yayi tsawo cikin satin nan zasu je yace Shikenan, sai gashi ta saki ranta
harda d'an murmushi ta fad'a jikin shi cike da shagwaba take cewa an kusa asa zuciyarta tayi bursting
yanzu haka da bai cire mata bak'in cikin da take ji ba tasan da wuya bata samu Heart attack ba, shidai
murmushi kawai yake can ya d'agata yace suje tayi breakfast tace ya fara mata wanka bata jin dad'in
jikinta, bayan an yo wankan ya taimaka mata ta shirya sannan suka fita don yin Breakfast, sai gashi ta
sake sosae kamar ba ita ba suka cigaba da gudanar da rayuwar su yadda suka saba.

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM 072*

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.......Ranar Laraba bayan su Fatuu sun tashi Mino ta tafi ta kwashe kayan shimfid'ar da tayi masu don
yanzu da tsiya sun koma kwanan Falo don duk dare nan Farha ke zuwa ta kwana kuma duk abun nan
Hajiya bata sani ba don ita a tunanin ta a d'akin da ta sauka take kwana dama bari take sai ta tabbatar
Hajiya tayi bacci sannan ta taho, haka take ta faman yi masu cin kashi iri iri Harda ce ma Fatuu mayya ta
lik'e tak'i tafiya gidan su, ita dae duk abunda zata mata bata biye ta, bayan ta maida kayan Farhar na
kwance kan gado tana bacci, toilet ta wuce don tayi wanka, lokacin data fito cikin sauri ta fara shiryawa
don yau test biyu gare su d'aya da safen nan za'ai masu d'ayar kuma sai After break so take taje da wuri
don su k'ara yin karatu, bayan ta gama shiryawa ko tunanin tsayawa yin breakfast bata yi ba ta d'auki
jakarta ta nufi k'opa zata fita, tana kama handle taji Muryar Farha tana mata magana hakan yasa ta
dakata ta juya, tana kwance saman gadon ta d'an d'ago da kai tace mata wai taje tayi mata Breakfast,
wani kallo Fatuu ta bita dashi kafin tace mata ai a part d'in Hajiya ake yi don haka taje can taci, yar tsawa
ta kwatsa mata tace ita zata bata Umarni ta k'i yi mata to miye amfaninta dama in ba hakan ba miji bai
son ta ya tafi ya barta yana can wurin wadda yake so suna shan soyayya amman ita da yake mayya ce ta
lik'e to yau anan take son yin breakfast d'in, sosae Maganar ta daki zuciyar Fatuu har idanun ta sun fara
tara k'walla amman sai tayi saurin maida su tace mata Aunty Saude zata kawo nata sai taci a fusace tace
bazata ci shi ba ita take so ta dafa mata, d'an jimm Fatuu tayi sai kuma ta d'ago hannu ta duba agogon
hannunta ganin da d'an sauran lokaci yasa ta juyo ta aje jakarta ta fita, bada jimawa ba ta dafo mata
indomie ta kawo mata har lokacin tana a kwance, a saman bedside drawer ta aje mata tace gashi nan,
tasowa Farhar tayi har Fatuu zata juya ta tsaidata ta juya tana yatsina tace mata ba ita take so ba Chips
zata had'o mata, wani kallo Fatuu ta bita da shi kafin tace mata gaskiya bata da lokacin yi mata wannan
School zata tafi tana da test kuma lokaci ya k'ure, tana gama fad'in hakan ta juya Farhar na mata magana
cikin tsawa tay banza da ita ta tafi,

Saida suka hau hanya bayan sun d'auki Mino ta kira Aunty Saude tace mata ta wuce ba sai ta kawo mata
breakfast ba, tace da wuri haka ta sanar mata test gareta ne, har suka isa Makarantar tana ta tunanin
irin wulakancin da Farha ke mata. Ana gab da tashi ta kira Tk tace mashi yau ya zo ya d'auketa lokacin
tashi Fauzy tace mata yau bazata tsaya ba kenan tace mata eh akwae abunda zatayi sai dae gobe. Bayan
ta koma gida tana shiga cikin parlon wani irin k'amshi ya bugi hancin ta, da mamaki ta shiga bin parlon
da kallo tana son gane k'amshin na minene don yayi yawa kuma tasan ba haka ta bar parlon ba, hanyar
corridor ta nufa tana zuwa saitin inda su Tv suke kaman ance ta waiga taga kwalaben turaren wutar ta
dake jere a wurin gaba d'aya zube a k'asa sun yi kwatsa kwatsa turaren barbaje a koina, da Al'ajabi take
bin su da kallo aranta ta shiga mamakin yadda akai sukai haka, ranta ne ya bata ko Farha ce tayi masu
haka, da sauri ta juya ta nufi Bedroom tana tura kopar nan ma k'amshin ne ya dakar mata hanci tay
tsaye tana bin kwalaben humra d'inta dake watse a k'asa da kallo gaba d'aya an fasa su harda su turaren
fesawarta ga kayanta na cikin Wardrobe duk an watso su wardrobe d'in a bud'e, kai idonta tayi akan
gado nan ma indomie d'in data dafo mata ce a warwatse ko ina, tsaye Fatuu tay ta kasa yin wani
kwakkwaran motsi idanunta cike da k'walla take bin bedroom d'in da kallo, da k'yar taja k'afa ta idasa
shiga ciki ta nufi bakin gado ta zauna a inda ba indomie d'in, kifa Fuskarta tayi cikin tafin hannunta ta
fashe da kuka, tana cikin kukan ta tuno da Kitchen ta mik'e da sauri ta nufi k'opa ta bud'e, tana tura
kopar kitchen d'in taja ta tsaya idanu waje take kallon cikin shi gaba d'aya duk wani abun fashewa ta fasa
shi kayan Abinci ma bata k'yale su ba duka ta barbaza su harda mai duk ta zuzzubar dashi a k'asa wasu
daga cikin Warmers d'in ta ma bata k'yale su ba saida tasa ta6arya ta faffasa su sosae tayi mata Asara
abun ba kyan gani, wani irin 6aci ran Fatuu Yay tama kasa cigaba da yin kukan sai huci take, tana tsaye a
wurin Aunty Saude ta shigo kawo mata Abinci, a kan c-table ta d'aura kayan Abincin ta nufi Bedroom a
ranta tana Maganar k'amshin da take ji tayi tunanin ko turare ne ya 6are, tana shiga corridor d'in taga
Fatun tsaye ta bata baya ta isa wurinta tana fad'in "Fateema an dawo yau da wuri kenan, Tk ne ya shiga
d'aukar Abinci yake fad'a man kin dawo ai" jin shiru bata ce komai ba kuma bata juyo ba yasa Sauden kai
hannu ta ta6o ta still bata juyo ba, matsawa tay tana fad'in Fateema lafiya mi kike kallo haka itama ta
kallo cikin Kitchen d'in ba arziki ta bud'a baki tace garin Yaya haka ta faru ya akai kayan sukai haka, sai
lokacin Fatuu ta juyo ta fad'a jikinta ta fashe da kuka, tambayar abunda ya Faru Sauden tay ta d'ago cikin
kuka ta fara bata labari, Bedroom d'in Saude ta nufa ta shiga taga yadda shima tay mashi ta kai hannu ta
ruk'e ha6a ta shiga jinjina kai, fitowa tay tazo taga na parlon ma sosae itama ranta ya 6aci don ba
k'aramar asara tayi ma Fatun ba, juyowa Saude tay ta koma cikin Corridor inda Fatuu ke tsaye bakin
Kitchen rai 6ace tace "Yanzu ke Fateema kin za6i ki zuba mata ido tay ta maki wannan cin kashin, nace in
sanar ma Hajiya kin hana gaskiya to yanzu an zo ga6ar da dole ma in sanar mata" girgiza kai Fatuu tayi
cikin kuka tace "Don Allah Aunty Saude kar ki sanar mata hakan ba k'aramar matsala zai Haifar
ba...."Katseta Saude tay tace "to wai ita Mahaifiyar tasu ta isa tayi maki abunda Allah bai nufa akan ki
bane" girgiza kai Fatuu ta k'ara yi "a'a Aunty Saude, nidai ki kyaleta kawai banso in shiga tsakanin su tayi
ta gama ta tafi",

Shiru Saude tayi tana kallon ta can tace "Shikenan indai kina son kada na fad'i mata sai kinyi abu guda in
ba haka ba gaskiya bazan zuba ido ina ganin tana maki wannan iskancin ba" ce mata tay to mi zata yin,

"so nike kiyi maganinta ta daina maki wannan wulakancin, kinsan irin haka saika had'a jiki da mutum yaji
a jikin shi sannan yake kiyayar ka, nasan ba fin k'arfin ki tay ba wllh kawae jikin ne ba abunda zata iya
maki don haka ki dawo Fateemar ki ta da ki sameta ki lakad'a mata dukan tsiya wllh zaki ga ta shafa maki
lafiya" baki adan bud'e Fatun ke kallon ta jin kalaman sak irin na Fauzy, bayan ta gama tace mata tana
ganin ba matsala ita bata son Hajiya ta sani,

"Ba wata matsala, ai anan part d'in in tazo zaki mata hakan kuma tunda tasan ita ke bata da gaskiya
bazata bari a ji ba tunda dama duk abunda take maki a 6oye take yi bata son Hajiya ta sani, shiru Fatuu
tay tana nazarin Maganar, Sauden tace zata yi ko kuwa taje ta fad'i ma Hajiyar, kallonta tayi ta jinjina
mata kai alamar zata yi tace to tazo taci Abincin ta k'ara samun k'arfin yin maganin mara mutunci ta
kamo hannunta suka nufo cikin parlon duk fargaba ta cika Fatun don rabon data yi fad'a da wani har ta
manta, da kanta ta zuba mata Abincin bayan ta cire Hijab d'inta ta aje a gefe ta fara ci, har saida taga taci
ta k'oshi sannan ta bar part d'in bayan ta jaddada mata abunda take son tayi ma Farhar,

Saude na fitowa cikin harabar ta hango Farhar ta fito ta baya ta nufo part d'in suna had'a ido ta wurga
mata uwar harara ta kauda idon ta, Sauden tay d'an murmushin yau zaki gane kuran ki, bayan Fatun ta
gama toilet ta je tayo Alwala ta dawo parlon don tayi sallar anan da niyyar inta gama sai ta fara gyara
inda ya 6aci, tana kokarin sanya hijab taji an turo kopar ta kai idon ta da sauri, cikin isa kaman yadda ta
saba ta nufo cikin parlon tana yatsina, a gaban Fatun ta tsaya hakan yasa Fatuu dakatawa da saka hijab
d'in ta bita da ido gabanta nata fad'uwa kan abunda aka ce tayi matan, ce mata tayi tana fatan taga
sakamakon k'in yi mata abunda ta sakata don haka gobe ma in ta k'ara sata abu tak'i yi zata ga abunda
yafi wannan kuma tunda dai ita mayyace ta lik'e bada jimawa ba zatayi maganin ta gaba d'aya, tana rufe
baki ta tsitta ma Fatun miyau a fuska aikuwa hakan ba K'aramin fusatar da ita yay ba duk da fargabar da
take ciki a fusace ta kai hannu ta wanka mata mari ji kake Tasss! a gigice Farha ta kai hannu ta dafe
kuncinta ido waje take kallon Fatuu data d'aure Fuska tana huci, nuna kanta tayi da yatsa tace ita ta
mara a fusace Fatun tace eh taje ta mara aikuwa itama ta d'aga hannu zata sharara mata Mari da sauri
Fatuu ta goce kafin Farha tay wani yunkurin ta shammaceta ta turata sai gata ta fad'a saman kujera
tumm da alama k'ibar biredi ce dama, kan ta yunk'ura ta taso Fatuu ta haye samanta ta fara dukanta ba
ji ba gani ta shiga sauke fushin duk wani bakin ciki data cusa mata dama kuma ita a yadda ta taso bata
iya fad'an cacar baki ba tafi gane ta kai bugu kawai...........

Saude na shiga parlor ta nufi Hajiya dake Zaune akan Kujera tana kallo, tana zuwa da alamun rud'ewa
tace mata ga Farha can a part d'in Fateema suna fad'a tayi tayi ta raba su sun k'i rabuwa, ba shiri Hajiya
ta mik'e ta d'auki sandar ta tace suje, suna kan hanya Hajiya nata faman dogara sandar tana yin sauri da
alamun mamaki take tambayar abunda ya had'a su Sauden ta shiga fad'i mata asarar da tayi ma Fatun
wani irin bacin rai ne ya bayyana akan fuskar ta, Har lokacin su Fatun fad'a suke sai tumurmusa suke a
k'asa har ta fitar ma Farhar da jini, lokacin data ga ta fasa mata hanci da baki tsoro ya kamata ta fara
k'ok'arin k'yaleta saidae ita Farhar tak'i sai k'ok'arin ganin itama ta cutar da Fatun take hakan yasa Fatun
cigaba da kare kanta har jikin c-table taso bugata k'arshe ita Fatun ta buga, Saude ce ta fara shigowa sai
Hajiya tana shigowa ta rafka uban salati tare da sakin sandarta ta fad'i k'asa tay k'ara aikuwa a firgice
Fatuu ta k'wace ta mik'e tana ta huci, itama Farhar kokarin mikewa tay da k'yar tana ma Fatun wani kallo
a fusace sai nishin wahala take tun daga k'asan hancin ta har zuwa k'asan bakin ta duk jini ne haka
goshinta ma yayi jawur ita kuma ta kakkarce Fatun a wuyanta da kuma gefe gefen Fuskarta da yake
k'umbuna gareta zak'o zak'o, cikin Fushi Hajiya ta kira sunan Farhar tace Saboda bata da mutunci da
Matar Yayanta take fad'a haka, shiru tay sai nishi take ta kumburo baki da gani kiris take jira ta saki kuka
don idanunta a cike suke taf da k'walla, kallon Fatuu data sunkuyar da kai Hajiya tayi ta tambayi miya
had'a su ta d'ago cikin rawar murya ta fara fad'i mata daga breakfast da ta ce tayo mata zuwa dawowar
da tayi ta iske abunda tayi mata Saude ce ta k'ara yi ma Hajiya bayani tun daga farko, sosae ran ta ya
6aci tay ma Saude nuni da ta d'ago mata sandarta, hanyar Bedroom ta nufa saida ta tsaya taga 6arnar da
tayi mata a parlon sannan ta wuce ta gano sauran, bayan duk ta gani cikin parlon ta dawo Fuskarta a
tamke ta tsaya daga gaban Farha rai 6ace tace "dama tunda na gan ki kinzo nayi zargin ba abun Alheri ya
kawo ki ba kawae don anaso arinka kyautata zato yasa na kauda zargin hakan da tunanin mutum na
canzawa, wato ke ta turo kizo kiyi mata abunda na hanata Saboda ta raina ni son d'iya yasa ta daina jin
maganata, yayi kyau ai ga sakamakon ki nan kin zata don kina mata cin kashi tana k'yale ki tsoron ki take
ji, uhmm baki san wacece Fateema kuwa, kin ci sa'a tayi sanyi ne da sai tayi maki fiye da hakan don har
hak'oran gaban ki sai ta cire maki su, yanzu sai ki wuce muje ki tattara kayan ki kibar man gida ni ban
sauke wanda ba abun Arziki ya kawo shi ba a gidana, don ma yamma tayi da wllh bazaki kwana ba
amman Allah ya kaimu gobe ko ba Jirgin Lagos Kya hau na Kano daga can ki wuce, muje!" Ta daka mata
tsawa ta juya tu6i tu6i ta nufi k'opa dama skin tight ne a jikinta, kallon Fatuu Hajiya tay ta bata hak'uri
tace duk abunda tayi mata asarar shi za'a maida mata tace ma Saude ta taimaka mata su gyaggyra
wuraren tace to daga haka ta juya itama ta nufi k'opa, bayan fitar ta hannun Fatuu dake d'an gunji da
gani kukan zuci take ta kama ta zaunar da ita kan kujera, itama zama tayi ta fara lallashin ta aikuwa
kaman tana jira ta saka mata kuka a cikin kukan take fad'in miyasa ta fad'o ma Hajiya ba sunyi da ita
bazata fad'i mata ba Sauden tace to ba gashi ta kawo k'arshen komai ba, lallashinta ta shiga yi tana
kwantar mata da hankali kan ba wani abunda zai faru in sha Allah, saida taga ta saukko tayi shiru sannan
tace taje ta cire uniform sai su gyara wuraren tace to ta mik'e.

Suna shiga cikin parlor Hajiya ta nuna mata hanyar Bedroom tace taje ta shirya kayanta, juyawa tay ta
nufi hanyar ba tare da tace komai ba don ba alamun wasa a Fuskar Hajiyar, cikin parlon Hajiya ta wuce ta
zaune inda take da kafin Saude tazo, Wayarta takai hannu ta d'auka ta shiga kiran Hajiya Maryam, bayan
ta d'aga ta gaishe da ita Hajiyar tay banza bata amsa ba a kausashe tace "Ga yar Aiken ki nan zata dawo
gobe in Allah ya kaimu, sannan a matsayina na Mahaifiyar ki in kika k'ara yin wani yunkuri don ki raba
auren Fateema ko kuma ki cutar da ita BAN YAFE MAKI BA!!!" tana gama fad'in hakan ta katse Wayar.

Da daddare lokacin tuni su Fatuu sun gyara ko ina bayan tayo wanka ta shirya cikin kayan bacci tana
niyyar fita parlor don taci Abinci har ta kai k'opa taji wayarta na ringing ta juyo ta nufo bakin gado inda
take ajiye, zama tayi ta kai hannu ta dauka tay Jim tana kallon sunan Haisam dake kan screen d'in alamar
shi ke kira, Kaman bazata d'aga ba saida ta kusa yankewa sannan ta d'aga ta kaita kunne, shiru tay ko
sallama bata yi mashi ba shima kuma bai ce komai ba, sai d'an bayan wani lokaci taji ya tambayi tana
lafiya, sai data amsa mashi sannan ta gaida shi shima bai amsa ba ta d'an ta6e baki, tambayar ta karatun
ta yay tace mashi Alhamdulillah suka d'an yi shiru taji yace sun kusa fara Exams ne a tak'aice tace mashi
eh, tambayar ta yay tana karatu har saida ta curo wayar ta kalli screen d'in da alama so take ta tabbatar
shi d'in ne ya kira ta, bayan ta ce mashi eh tana yi shuru suka k'ara yi daga baya yay mata saida safe ya
kashe, bin wayar tay da kallo a cikin ranta ta fara kokonton kodai yaga sak'on ne wata zuciyar ta bata
inda ya gani ba iya haka zai mata ba tunda dama ai duk in ya kirata yana tambayar karatun ta, tana cikin
cin Abincin a parlor Mino ta shigo tana sanye da doguwar rigar material ta yafo gyale saman kanta daga
baya yayi tudun kitson shukun da akai mata ta nad'e da k'aton ribbom, tun bayan zuwan Farha zuwa
gidan bai mata dad'i sai jefi jefi zaka ga tazo da rana dama kuma ta fara zuwa islamiyya da daddare ne
kullum sai tazo, cikin parlon ta shiga Fatuu dake kallon ta da murmushi ta nuna mata gefen ta alamar
tazo ta zauna, bayan ta zauna ta gaishe da ita ta amsa tace mata suci suka cigaba da ci tare, bayan sun
gama Minon ta kwashe kayan ta kai Kitchen ta dawo Fatuu tasa ta d'aukko masu ruwa da lemu cikin
freezer d'in dining, kallo suka d'an yi daga baya Fatuu ta kalli Minon tace mata in tana jin bacci taje
Bedroom ta kwanta, har saida fuskarta ta kasa 6oye mamakin Maganar data ji tace mata ba anan suke
kwana ba, yar dariya Fatun tay tace yau suna da yanci a gado zasu kwana da tsananin mamaki tace mata
ina ita mai idanun magen yau bazata kwana ba, dariya taba Fatuu jin sunan data kira Farha dashi dukda
da gaske idanun nata kaman na magen suke, nan Fatuu ta bata labarin abunda ya faru tace mata gobe
ma zata tafi, zo kaga murna a wurin Mino harda mik'ewa da yin tsalle daga baya suka je suka kwanta.

Washe gari cikin nishad'i Fatuu ta tashi duk da tana d'an jin yar fargabar abun da zai iya zuwa ya dawo in
Hajiya Maryam taji abunda ya faru, Bayan taje Makaranta Fauzy ta lura da yanayin ta ba kamar yadda ta
saba ganinta ba da damuwa ta tambaye ta ko Ya Haisam d'in yaga sak'on sunyi Magana ne tace mata a'a
itafa bata tunanin ya gani don ko jiya sunyi waya bata ga alama ba, nan ta kwashe abunda ya faru
tsakaninta da Farha ta fad'i mata, cike da jin dad'i Fauzy tace amman ta burgeta wllh tuntuni abunda
yakamata tayi kenan ai da duk ba'a zo nan bama. Lokacin da Fatuu ta dawo tuni Hajiya ta iza k'eyar
Farha ta tafi.

_______________________

Ranar Asabar da wuri Mino ta tashi ta had'a Breakfast bayan ta gama ci ta tafi gida don zuwa islamiyya
lokacin Fatuu nata shan bacci, sai wuraren k'arfe 10 ta tashi ba dan ta gaji da baccin ba sai don yunwa
data isheta, bayan ta gama yin breakfast d'in toilet ta wuce tayo wanka tazo ta fara shiryawa, doguwar
rigar material tasa ta yafa d'an gyalenta bayan ta d'auki wayarta ta nufi part d'in Hajiya, tare da ita sukai
Abincin rana da Saude bayan an taso su Mino ta isketa nan, anan suka ci Abincin rana bayan sun gama
suka zauna parlor harda Hajiya da Saude suna yin kallo, wuraren k'arfe ukku da rabi Mino tayi masu
sallama zata je tay shirin islamiyya Fatuu ma ta mik'e tay masu sallama suka fito tare, part d'in su ta
koma ta wuce toilet tayo wankan rana dama kusan kullum wanka ukku take yi k'aranci tayi biyu, bayan
ta fito gaban mirror ta tsaya tana yin shafa ta k'ura ma kanta ido ita kanta tausayin kanta take game da
irin rayuwar auren da take yi, bayan ta gama shafe shafen bata yi wata kwalliya ba iya powder sai lip
glow ta shafa, wata fitted gown ta Atamfa ta fiddo ta saka, bayan ta gama shiryawa ta shimfid'a qq abun
salla ta d'aukko Hijab ta kabbara sallar la'asar, lokacin da ta gama zaune tay a wurin ta jingina da gado
tay shiru hakanan take jin ta wani iri, ta d'an d'auki lokaci a haka daga baya ta mik'e ta d'auke abun sallar
ta mayar inda yake ta cire Hijab d'in itama ta linke, saman gado ta haye ta zauna ta fara latsa wayarta
can ta aje wayar ta mik'e ta d'aukko jakarta ta fiddo littafi don tayi karatu, shima karatun ji tay duk bata
jin dad'in shi ta maida littafin cikin jakar ta zame ta kwanta ta runtse ido tamkar mai yin bacci saidae
tunane tunane kawai take, bata dad'e da kwanciya ba sosae lokacin wurin karfe biyar da rabi wayarta ta
fara yin ringing, bud'e ido tay kafin ta juyo ta kai hannu gefenta ta d'auka, ganin Hajiya ce mai kiran nata
yasa tay saurin tashi zaune ta jingina da headboard,picking tay tare da yin sallama on the other hand
Hajiyar ta amsa ta tambayi tana gida ne da sauri ta amsa mata da eh tana nan, ce mata tayi tazo part d'in
ta to yanzu tace to, saukkowa tayi daga saman gadon ta nufi wardrobe ta fiddo d'an madaidaicin gyale
da ba zai rufe bayanta ba gaba d'aya ta yafa, a cikin Corridor ta d'aukko takalma Flat shoe da suka hau da
kayan jikinta ta wuce, Wata irin Fargaba take ji tun bayan data fito, ba yau Hajiya ta fara kiran ta ba
amman wannan kiran duk sai take jin gabanta nata d'an fad'uwa, tana sanya kanta cikin parlon gabanta
yay wani irin bugu mai k'arfi ba shiri taja ta tsaya, Zuba ma Mutumin da idanunta ke ganin mata ido tay
wanda ko a nisan da ya ninninka wannan ta hango shi kallo d'aya zata gane shi, sosae tay Al'ajabin ganin
su don bata ta6a zaton zata gan su ba, Haisam ne zaune akan 3 seater jikinshi sanye da Suit bak'ak'e
saidai ya cire ta saman sai farar ciki mai santsi da dogon hannu sai bak'in wandon, daga gefen shi Fanan
ce itama tana sanye da bakar doguwar riga jallabiya mai kayataccen adon stones gyalen rigar bai a
saman kanta hakan ya bayyanar da brown sumar ta dake fake a tsakiya, gaba d'ayan su akan kujera
d'aya suke zaune Haisam ya d'an zamo ta yadda ya jingina sosae da kujerar idon shi akan Tv ita kuma
Fanan tana daga gefen shi itama ta jingina bayanta da jikin kujerar hannun ta d'aya dafe da forehead
d'inta Hajiya har magana tay mata kan taje ta kwanta amman tace a'a sai an kirawo Zarah, sun d'an jima
da zuwa don Fatuu bata dad'e da barin part d'in ba lokacin data koma tana toilet tana yin wanka suka
iso, wani irin bugu da k'arfi da k'arfi zuciyar Fatuu ta hau yi ba kamar data ga Fanan ji tay kaman ta juya
tunda ba wanda ya ganta ta koma, har zata juyan zuciyarta ta raya mata kenan k'in amsa kiran Hajiya
zata yi hakan yasa ta dakata, Kamar Haisam yaji ajikin shi ana kallon shi a wani irin slow ya juyo da
Fuskar shi ya kalli direction d'in da Fatun take nan take idanunsu suka shiga cikin na juna, zuba mata ido
yay yana bin ta da kallo tun daga samanta har k'asa kafin ya tsaida su cikin nata, Hajiya ce ta kalle shi da
niyyar yi mashi magana da yake Facing d'in su take a zaune ganin inda ya zuba ma ido yasa ta waiga ta
kalli wurin, ganin Fatuu tsaye a wurin yasa ta d'an d'aga murya tace "Fateema ki shigo mana" har saida
Fatun ta d'an firgita don bata san ta ganta ba, Fanan na jin Hajiya ta furta haka da wani irin sauri ta janye
hannunta daga kan goshinta ta juya ta kalli inda Fatun take, gaba d'aya dabarbarcewa Fatun tay Hajiya
ce ta k'ara mata magana kan ta shigo ta nufo cikin parlon idon ta a zare tana tafiya a d'arare, a bakin
kujerun ta k'ara ja ta tsaya aikuwa kamar Fanan na jiran ta k'araso ta mik'e ta nufeta fuskar nan ba
d'igon annuri, mik'ewar da tayi ta bayyana irin rigar jikinta mai bin shape d'in jikin mutum ce tayi kyau
over, wani irin harbawa zuciyar Fatuu ke yi numfashinta ta fara kokowar fitar dashi, da za'a auna bp d'in
ta a lokacin to kuwa daba makawa za'a ga ya hau, a gabanta ta tsaya daddad'an k'amshin jikin ta ya baza
wurin, kyakkyawar Fuskarta a tamke take kallon fuskar Fatuun nan da nan jikinta ya hau 6ari ta hau
kikkafta idanu, jin sun fara tara k'walla suna niyyar zubo mata da sauri ta sunkuyar da kanta k'asa, A
kausashe Fanan ta kira Sunanta "ZARAHHH!!!" murya na rawa ta amsa mata, ce mata tayi ta d'ago ta
kalle ta, da k'yar ta d'ago ruwan hawaye sun lullu6e k'wayar idon ta,

"Zaraah u married my Husband!" Fanan ta fad'a muryarta har wani vibration take, shiru Fatuu tayi tana
gunji kiris ya rage ta saki kukan, cigaba Fanan tay "na d'auke ki matsayin my own Sister Zaraah, amman
shine kikai man haka, kin san yadda nike son ki na damu dake amman duk da haka kika iya auran man
Miji?" Yanayin muryar ta tamkar itama zata saka kukan idanunta har sun canza, girgiza kai Fatuu ta fara
yi fuska a yamutse da k'yar ta bud'e baki cikin trembling voice tace "D...on Allah Aunty Fanan kiyi hakuri
wllh nima ban san ya Aure ni ba....kin ji na rantse maki..." Kuka ne yaci k'arfinta ta sadda kanta k'asa tana
cigaba da yi, d'an ta6e baki Fanan tayi tace "But u loved him Zarah, Ur Message said it all!" d'agowa
Fatun tay ta kalleta ta kasa cewa komai don ta gane sun ga sak'on da Fauzy ta tura,

"Kinsan abunda ke tsakani na dashi tun farko amman kika fara son shi kuma kinsan ya Aure ni amman
baki daina son na shi ba Saboda cin Amana!" Sautin kukan Fatun ne ya k'aru tace "Don Allah ki yi hak'uri
Aunty Fanan wllh kinji na rantse maki ni bansan abunda ke tsakanin ku ba saida kika zo, bai ta6a fad'i
man ke zai Aura ba kuma gashi can ki tambaye shi" yamutsa fuska tay "daga baya da kika sanin miyasa
kika cigaba da son shi!" A fad'ace take Maganar, shiru tay ta maida idonta k'asa tana gunji, da d'an tsawa
tace ta bata amsa miyasa ta ci gaba da son shi,

"Kiyi hakuri nasan nayi maki ba daidai ba amman na daina son shi" d'age gira tay tace shine kuma ta turo
mashi sak'o tana bayyana mashi son da take mashi, girgiza kai Fatun tay tace "Yanzu na daina son shi
wllh kin ji na rantse maki" sai lokacin Fanan d'in ta d'an saki fuska tace "Good! haka yakamata" tana
furta hakan ta juya tana tafiya cike da isa ta nufi wurin Haisam da har lokacin yana zaune a yadda yake, a
gaban shi ta tsaya ta mik'a mashi hannunta dake sanye da zoben diamond, still yay yana kallonta ta wani
yamutsa mashi Fuska, hannu ya kai gefen shi ya d'aukko wata takarda plain sheet dake nannad'e ya
mik'a mata, juyawa tay ta koma wurin Fatun, a gabanta ta tsaya yanayin Fuskarta kamar zata yi
murmushi tace "am sorry Zaraah we do not welcome u in our Fam, bazan iya yin kishi dake ba, not only
u da Kowacce mace ma because yayi man Alk'awarin zamu rayu tare mu biyu until Death do us part"
tunda ta fara Maganar Fatuu ke jinjina mata kai har ta gama ta mik'o mata takardar hannunta, tana
amsa ta juya har cikin ranta taji dad'in hakan tana fara tafiya taji Muryar Hajiya ta kira Sunanta, juyawa
tay ta kalleta da kai tay mata alamar tazo, daga gefenta ta tsaya da alamun damuwa akan Fuskarta ta
fara Magana "Kiyi Hak'uri Fateema ban so hakan ta faru ba saidae gaba d'aya sun nuna basu son Auren
ban so ki cutu ne shiyasa na goyi bayan ya sallame ki kawai, yanzu kije ki kai ma Dije ina nan zuwa" kai
Fatun ta d'aga mata idanunta sharkaf da k'walla, har zata juya Hajiya tace mata ta bud'e ta fad'i mata
saki nawa yayi mata Saboda sheda, hannunta sai kakkarwa yake ta fara warware takardar..............
ALHAMDULILLAH, Ba don na gama ba sai don nazo inda nike son in tsaya😀

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo
kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta
wad'annan nos din 09013804524 ko 0816985626

You might also like